Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita sarki ya canza shiga Ya fice ta kofar baya sannan ya rufe fuska da kafarshi Ya taka yana tafiya, ya danyi nisa Ya nufi wani gun da kwata kwata mutane basa yin gun Ma, wani bawane yazo wucewa yaga wani nayi gidan ajiya alhalin yasan an hana hakan yasa yabi bayan sarki yana dabe dan yaga inda zaije, dai dai da sarkin zai bude kofa yana inuwa alamar ana binshi ,murmushi yayi aidama yasan duk sanda zaizo wannan gun dolene yayi kisa hakan yasa yai fuska kamar baiga kowa ba ya shiga, shima bawan kuwa bai fasa biba, labewa Sarkin yayi abayan kofan saida bawan ya shiga ciki sannan ya rufe kofan yasa kwado ya rufe, bawan Ya juya baya yana dube dube sarkin yai gaba hakan yasa bawan bin bayanshi Sun danyi tafiya kafin bawa ya Fara fadin wai waye wannan? Da gudu sarki Ya kwasa hakan yasa bawan kwasar gudu shima,.
A razane bawan Ya taka burki ganin wani mutun da yayi a cikin cell, ya dago yana kallanshi a razane Ya furta SARKI ABDULSALAM?

BY HAJARA MAMI NATTY GIRL
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 6*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Da sauri ya karasa gunshi yana fadin sarki abdulsalam dama baka mutuba me kake anan? A hankali sarkin Ya fara magana ME yasa ka biyoshi bakasan bana San ana kashe mutanena saboda niba bakasan shi mugu bane, kallanshi mutumin yayi waye mugu yau zan fitar da kai anan zan fadawa sarki Abdullahi na ganka nasan zaiyi murna da hakan, hawaye sarki abdulsalam ya Fara yana jijjaga kai,.


Jin ANA tafi yasa bawan juyawa mikewa bawan yayi ganin sarkin su yasa ya karasa gunshi yana fadin sarki abdulsalam bai mutuba Ashe yana nan....... Saikuma yai shiru tanu abun da tsohun sarkin nashi yace mai mugune me yasa ka biyo shi Da sauri ya kalli sarkin nasu yana jijjaga kai, Amman ba wannan bane mugun badai sarkin muba, matsawa kusa dashi sarkin yayi nina kawo shi nan ai nana sashi anan ina jiran wani lokacine da zan kashe shi, Da sauri bawan ya kalleshi saboda me? Saboda kunfi sanshi kun sanshi akan ni alhalin nima inasan mulkin kuma nine babba saboda da ME bazan yanke wannan hkuncinba? Da sauri bawan ya kalleshi aikuwa kaiba sarki mai adalci bane kuma yau zan tuna ma asiri wlh, gadan gadan Ya nufi sarki, yana zuwa saijin saukan wuka yayi a cikinshi, kallan Cikin yayi ya kalli sarkin kafin yai kasa yana shahada nan take ya mutu,.

Kuka sosai sarki abdulsalam yake zama sarki Abdullahi yayi kusa dashi karka wani damu ni bani nace Ya biyoniba shishigine irin nashi kuma kasan duk zuwa ina samun irin su, cikin kuka sarki abdulsalam ya Fara magana wai ME kake jirane ka kasheni kawai mana, no no bazan kashe kaba ai nasan Yarka zata zo agabanta zan kashe ka ai karka wani damu, kallanshi sarkin yayi aikuwa babban kuskure zaka tabka dan ittace ajalinka itta zata tuna ma asiri inba kasaniba ,wata dariya yasa aikuwa zanso ganin wannan ranar tab kace akwai shagali, Hmmmm kawai sarkin yace bai kara cemai komaiba, haka yaitaiwa kanin nashi surutai yana bashi labarin yadda zai kashe shi, daga baya Ya mai sallama sannan Ya fita da gawar wannan bawan,.

Tunda suka shigo gombe take ta kalle kalle garin yai mata kyau tana feeling wani happy ta rasa dalili, haka suka sauka a tasha da kyar suka Sami wajen kwana dan gobe zaai sabin diba a masarauta gobe zataje dan shiga,.

Tans bacci ta Fara mafarki

Dan faraaa matar take kallan sultana barka da zuwa garinku masarautar mu Amman sultana sai kina hadawa da addua fa, kallan ta sultana tai na gode Amman Dan Allah ke wace, murmushj matar tai babanki xai fada miki, kallanta ta sake yi kawu ne zai fada mun? Aa bashiba mahaifi Wanda ya haufe ki, zaro ido tai yana rayene? Kwarai kuwa, to yana ina? Yana masarautar mu, ina zuwa zan ganshi taya zan gane shi? Aa ba zaki ganeshi ba shi zai ganeki, sannan IN kikaje karki bari ina ganin fuskarki sosai dan yan garrin manya yan iskane suna bata matane, zaro ido tai bama zan Bari aga fuskata ba, dariya matar tai bance kina kin bude fuska bafa, murmushi sultana tai,.

Washe gari Ta gama shirinta har wajen masarautar kawu Ya kaita sannan ya Mata sallama mtanene a jere kuwa yana jiran kira

by Hajara Mami natty girl
ο»Ώο»ΏπŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 7*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```


Kallan masarautar tai daga wajentama abun kallone balle cikinta,.

Baccinshi yake mai dadi karar da aka sakine ya tasheshi da adduar bacci ya tashi, tare da mikewa Ya bude window, tsaki yaja yau za debi sabin bayi kenan ni na rasa me yasa ake samun bayi alhalin kullun kisa ake a masarautar mtswww yaja saki, gabanshine Ya fadi da sauri Ya dafe girjinshi tare da karanto addua, sannan ya Sami saukin dukan girjin nashi ya shiga wanka,.

Budewa musu gate din akwai ana sanarwa mata subi layi mazama haka haka kuwa sukai sannan wani yazo Ya fara musu jawahi zamu Zaga da ku KO ina Dan daukarku a kowanne sashe da ake da bukata ,basuce komaiba sudai sunyi tsaye kamar sojoji, gaba Wanda ya gama musu magana yayi suka bishi a baya,.

Wata matacw ke zaune a parlour Ta caka uban dan kwali Ta daura daya kan daya ga bayi a kusa da itta suna mata hidima, Da sallama wata baiwa Ta shigo ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, sannan ta kalli matar gimbiya sabin bayine inkina da bukata, kallan jakadiyar tayi ina bukatar masu tsafta da kyarki gudu biyar, angama ranki shi dade Ta fada tare da mikewa,.

Tana zuwa Ta zabi gudu biyar din kamar yadda ta fada sannan Sukai gaba, haka akai Ta zagawa dasu ana diba Amman har wannan lokacin ba a dauki sultana ba duk tabi Ta damu kardai aki daukanta ace ta hakura,.


Part din Maman sultan suka nufa itta Ma baiwa Ta isar mata da sako sultan dake kusa da itta ya kalleta momy me zakiyi da bayi kuma banda wadannan da kike dasu? Murmushi tai ta kalli jakadiyar autana yace basai Na dauka ba amma ki dakko min daya mai hankali saboda wata rana, mikewa tayi Ta fice dan cika aiki kallanta sultan yayi wato dole saikin dauka KO momy? Shafa kanshi tayi kawai zan daukane saboda wata rana jijjaga kai kawai yayi baice komaiba,.

Baiwar Na fita ta Fara kallan Yan matan gun idonta ya sauka kan sultana da idonta ya cika da kwalla amma fuskarta a rufe, kallan bawan kusa da itta tayi a dakko waccan ta fada tare da nuna sultana, ajiyar zuciya Ta sauke najin dadin An zabeta da sauri Ta mike Har hakan yasa baiwar murmusawa,kallan sauran bawan yayi To ku zamu wuce daku dakin girki zamu raba muku sauran aikin, Da haka sukai gaba,.

Kusa da jakadiya sultana ta karasa har kasa tana fadin ina wuni? Murmushi matar tayi lafiya qlau ya sunanki? Sultana, zaro ido tai sultana dakyau shigo muje, tai gaba sannan ittama tabi Bayan jakadiyar,.

Da sallama suka shiga parlour nan take sultana taji gabanta ya fadi idonta ya sauka kan momy dake kallanta kafin Ta kalli sultan da hankalinshi ke kan Waya, ganin jakadiya tayi kasa hakan ittama yasa tai kasa Ta fadin abin da jakadiyar Ta ke fada, kallanta momy tai ya sunan ki? Sultana ta fada kamar mai shirin kuka, dago kai sultan yayi jin mai irin sunan shi idonta kawai ya gani dan Ta rufe fuska idon ya tara hawaye, tabe baki yayi kawai yaci gaba da abun da yake, kallanta momy tai tana murmushi mai sunan danace ma ashe Ta fada Tana kallan sultan,uhmmm kawai yace.

To sultana ina miki barka da zuwa wannan masarautar da fatan zaki rike amana indai kika kasance Mai hakan zanji dadi Amman fa indai kika ki rike amana anan zamu bata gaskiya, kasa sultana tai da kai tare da fadin insha Allahu zan kiyaye, murmushin jin dadi momy tai sannan tsafta ki kasance Mai tsafta hakan zaisa IN kara sanki sannan ki ksance mai addini, duk zan kiyaye insha Allahu, kallan jakadiya momy tai kije ki kaita part din bayi na wannan bangaren nawa gobe ki taho da itta zan baata aikin da Ya face Ta dinga mun, angama ranki ya dde jakadiyar ta fada, sultan ne ya katse su tare da fadin ke baki bude fuska NE?kallanshi sultana tai Dan itta kadaice mai rufe da fuska agun nan take mafarki ya dawo mata inda waccan take ce mata kartana barin ana ganin fuskarta yan iska nada yawa a wannan masarautar hakan yasa Ta dubul bulce tana fara kinkina, tsaki yaja tare da fadin you can go, Da sauri ta mike jakadiya kuwa bata mikeba tunda bata San me yace ba, shikewa mamaki yake Ta gane mai yace batai kama da wadda tai karatu ba, tabe baki yayi sannan suka wuce da jakadiya

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 8*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Suna tafiya sultana Na kallan masarautar, a hankali Ta furta MASARAUTAR MUCE kallanta jakadiya tayi me kika ce? Da sauri Ta kalleta ba komai bance komaiba kawai dai masarautar ce tamun kyau, murnushi jakadiyar tayi ai wannan ma kadan kikaga wannan ba komai bane a cikin wannan masarautar, murmushi sultana tai ,daga wanne gari kikazo nan? Daga jigawa nake masaya kauyen birnin kudu jijjaga kai jakadiyar tai kice daga nesa kike ,batace komaiba sukai gaba wani babban gune dakuna kamar Na yan bourding skull kowanne daki mutun uku da sallama jakadiyar Ta shiga dakin wasu mata dake sanye da wani kayan da gani uniform ne suka amsa suna kallan sultana da jakadiya, karasawa dakin sukai, kallansu jakadiya tai gata ukun ku da fatan zaku hade kai saboda baa mana fada a wannan masarautar da fatan kun gane? Murmushi duka sukai tare da mikawa sultana hannu a tare daya tace sunana Zuwaira daya tace Zulai murmushi sultana Tai tare da rike hannun nasa gaba daya sunana sultana naji dadin haduwa daku ina fatan zamu rike amana insha Allah suka fada, kallan gadonta sultana tai ga uniform dinta, jakadiya Ta fice kan cewa gobe zatazo Ta mayar da itta Dan taji maye aikinta,.

Kallan ta sukai bazaki bude fuskarki ba, murmushi tai tare dafara cire mayafin dake kanta gashinta ya fara zubowa sai kyakkyawar fuskarta sakin baki sukai suna kallanta, ganin suna kallanta yasa Ta saki baki tare da fadin lafiya? Masha Allah suka fada a tare, murmushi tai tare da zama akan gadon nan sukaji ana sanarwa ba, afita da daddare a wannan masarautar inba cewa kai kaje ba, kallansu sultana tai saboda me ba,a fita da daddre tabe baki sukai mu zaki tambaya muma yaufa muka zo, haka sukai Ta hira kafin suka kwanta bacci ,.

12:00 sai juyi sultana take a kan gado, ganin su Zuwaira suna bacci yasa Ta Mike tasa takalminta Ta bude kofa a hankali Ta fito, inuwa Ta gani tabi inuwar da kallo mutun biyu ne har ta daina ganin inuwar, mikewa tayi tana tafiya abunta hankali kwance,.

Tsaywa tai a bakin kofa tana tunanin Ta fita ko karta fice NE, jin ana cewa ina zamuje Bayan ance baa fita da daddare hakan yasa ta murda kofa zata bude aka finciko Ta, Da sauri Ta juya,zuwaira ce Ta hade rai ina zaki Bayan kinaji ance baa fita da daddare ai ina ganinki kifa fice tai tsaki tare da jan hannunta suka koma, sukai nafila sannan sukaa kwanta bacci ya dauketa,.

Washe gari kiran farko ana buga Musa karfe suka tashi suka fara aikinsu na dakuna da toilet kamar dai makarantar kwana sannan sukai sallah kowa yasa uniform dinsu sannan su Zuwaira sukace Sun tafi gun aikinsu,.

Tun tana jiran jakadiya harta gaji Ta koma bacci wajen 8:0 jakadiya tazo Ta tasheta suka kama hanya yaudinma Ta rufe fuska da dankwalin kanta,.

Bangaren Maman sultan sukai ki shiga bari inje can tana kaiwanan tai gaba, kirjinta na duka Ta nufi ciki kanta a kasa, kawai saiji tayi taci karo har yasa tai kasa timmmm Ta fadi

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 9*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```


ο»ΏWashhhh Ta fada Dan taji faduwar sosai, dagowa tayi dan ganin waye wannan da bai iya taimako ba,ke baki iya tafiya bane KO baki gani, a dole mutun ya wani rufe fuska ba dole ba, mtswwww ya wuce Ta gefenta, momy dake sama taiwa sultana sannu tare da cewa Ta karaso, murmushin yake tai ta Mike tai ciki har kasa Ta zube tana kwasar gaisuwa, kallan ka Momy tai to y'all kadaici kin kwana a masarautar mu ko? Eh kawai tace, biyoni momy ta fada tare dayin gaba ittama tabi bayan Ta, wata kofa suka shiga wani hadden parlour yai musu welcome, da kallo sultana tabi parlour dan kuwa ya hadu wanncan Na kasan banzane ai kallan parlour tai ba kowa a ciki GA TV Da aka kunna ansa sunnah TV sai karatu ke tashi, zama momy tai a daya daga cikin kujerun parlour, sultana ta zukunna a kusa da itta,.

Sultana kinga nan shine inda nake kwana wannan parlour nane saican tai mata nuni da wata kofa dakinane ni tunda nake da bayi bana Bari suna shigomun wannan gun KO abinci IN angama jakadiya kawai naba dama take shigowa Ta kawo min abinci sai indai Tana da sako shine abun da kawai yake kawota,kinsan dalilin da yasa nake miki wannan bayanin? Aa ranki ya dade, murmushi tai saboda ke zaki dinga aiki a nan ke zaki dinga gyaramun KO ina na wannan bangaren harda Ma dakine kinsan me yasa na zabeki ba tare da Na zauna na fahimceba tukun? Aa sultana ta fada, ajiyar zuciya momy ta sauke saboda zuciya tace tashi daya Ta amince dake kawai naji ba zaki cuceniba shiyasa na zabeki, sannan ina San sanar dake karki GA Na sake miki ki dauka zakiyi yadda kikaga dama no hakan bazai yuyuba ina fatan kin gane Dan wlh innna gane baki da shirri ke mai cin amanace wlh korar Ki zansa ayi, insha Allah zan kiyaye, Allah yasa momy ta fada, yanzu saiki buden fuskarki Inga, waida me yasa baki San bude fuskar ki ne? Inda inda Ta Fara, a zuciya momy taba kanta amsa saboda ana yiwa mata fadene oho Mata, cire Dan kwalin sultana tai tare dayin kasa da kai, kallanta momy like tasan wannan face din a inama ajikinta na bata a wannan masrautar Ta Santa wannan face din ganin zata wahalar da kanta yasa Ta hakura tare da mikewa in angama abinci zaki je kitchen ki dakko min sannan yanzu zaki fara aikin ki ,tam sultana tace tare da dukar dakai momy kuma Ta tashi tayi ciki abunta,.

Da kallu sultana tabi parlour ba wani daddi Amman dole tai abun da aka sata, nan kuwa Ta Fara aikinta baji ba gani sai share share Da goge goge take kamar gidan yayi daddi dama can,.

Matar dake sakkowa daga stairs Tana taku Cikin kasauta da murmushia fuskarta saka makon wayan da take, Allah ya kaimu Ta fada sannan tai sallama da Mai wayan Ta kashe nan take ta hade fuska kamar bata taba murmushj ba dan itta kwata kwata basan raini, itta a dole matar sarki, nan bayi Ta suka zube suna kwasar gaisuwa, a hankali Ta Fara magana jibi hindu wato yata zata dawo saboda aikin yau dana gobe zasufi yawa sannan duk waccce tai dare wlh haka zata tafi dan bamai kwanan mun a nan, nan take cikin Zuwaira yaba da kulllll, kallanta matar tai tare da fadin ke kizo ki sameni a parlour na aikinki da ban ne,.

Jki ba kwari Zuwaira tabi bayanta, kamar yadda Momy ta amince da sultana haka ittama Ta amince da Zuwaira,.

Aikinta sultana take yanzu kitchen take gogewa Ta gama parlour har 10:30 tayi gashi kamar ba aikin take ba, jin An turo kofa yasa ta leka, sultan Ta gani tsaye yana kallan a Gogo ,ina kwana? Dan ban kwanaba zaki ganni NE, tabe baki tayi zata juya yace ji mana,.

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 10*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Juyowa tayi Tana kallanshi ganin yana mata kallan sama da kasa yasa ittama Ta kalli jikin Nata kafin Ta sake kallanshi, tabe baki yayi nifa wlh ke bana San ganinki Ma Amman bansan me yasa momy ta kawo ki nan bama itta da bata Bari ana shigo mata, murmushin yake tai batace komaiba, kallanta ya sake yi haka baw kewa Uban gidan Sa ya wani tsaya ya tsare shi da ido?aa Ta fada da sauri tare dayin kasa, kallanta yake yasan ganin fuskanta Amman itta kullun fuskanta a kulle KO me yasa oho mata,.

Me yasa kika Bari aka Sa miki sultana alhalin kinsan sunana NE? Kasa tai da kai sosai tana murmushi dan dariya kesan kwace mata wannan waishi waye yana da abun da dariya wlh, kakace me, da sauri Ta dago ba komai ganin tana murmushi yasa ya kare hade rai karfa Ta rainashi, ina abinci jakadiya bata kawo bane? Aa momy tace IN an gaama inje IN dakko, to ME kike jira har yanzu baki dakkoba wannan ai shashancine. Mtswww yai gaba,.

Mikewa tai ta fice Ta kuwa samu angama abincin haka tai ta dakkowa saida taje tana dawowa sau wajen biyar sannan ta samu Ta gama,.

Aikinta taci gaba dashi Ta gama gobe kitchen Tana fitowa taga momy da sultan na sakkowa sai murmushi yake abunshi, gaida momy ta, ta amsa da Fara, a tana kallan parlour Ya gugu sosai ba kadanba,.

Zama sukai a dining din momy tace tazo Ta zuba musu, kallan sultan momy tai son waikai me yasa baka cin abinci naka part din alhalin kana danaka masu girkin? Momy duk basu iya girkiba wlh nina nan yafi mum dadi inci da momy Na murmushi tai zan samoma Mai maka girkin karka damu banasan kana shan wuya, to kawai yace,.

A hankali sultana ta Fara magana ranki ya dade yanzu na gama saura aikin dakin, murnushi momy tai to jeki gyara kinga inkin gama ma saikeje part din son kimai abincin rana aikin iya KO? Gabanta ne ya fadi ittafa bata San abun da zai hadata dashi kwata kwata wlh Amman banda yadda Ta iya eh a fada tare dayin ciki,.

Dakin yai mata kyau sosai ba kadanba, hutan sultan Ta gani da momy shi haka Ta gama aikin sai wajen 12:00 Ta gama sannan taci abincin da suka rage ta wanke kwanikan,.

Sannan ta zauna Dan hutawa, 3:00 momy tasa jakadiya Ta rakata part din shi Dan tamai abincin ranar saboda 4:0 suke tashi a aiki, har kofan park din jakadiya the kaita sannan ta koma,.
Ya sanarwa da masu girkinshj kan zataxo su koya agunta abincin, zama tayi a kasan parlour duk Ta gaji tayama zata Fara abun da Ya kawota kullun tana cikin aiki daga nan ta koma nan, saida Ta huta sannan suka fara abun da ya kawota,


By Hajara mami nagty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 11*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```

Da sallama Hafiz Ya shiga part din mahaifiyar tashi bata parlour farko hakan yasa yayi Ciki a bakin kofa sukaci karo da Zuwaira da sauri Ta koma baya tai saurin zubewa kasa tana bashi hakuri kare mata kallo yayi kafin ya tabe baki yai wucewar shi da kallo Ta bishi kafin Ta sauke ajiyar zuciya Ta mike tare da ficewa, Dan zuwa aikin da aka sata .

Kusa maman shi ya zauna Ta kalleshi kasan cewa jibi hindu zata dawo KO? Eh Na sani duk tazo Ta dagawa mutane hankali akan wannan sultan din, ajiyar zuciya Maman tashi Ta sauke akiwa dolenka ka karbo mata soyayya agun sultan a matsayin ka na yayanta, turo baki yayi amma mama kinfi kowa sanin bana San rainin hankali irin na wannan yaron KO wlh ya fada

Please Login or Register in order to submit comment