Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

* *MASARAUTAR MUCE 57*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com
Bayan an zauna aka Fara gudanar Da walimar inda aka nemi kawayen amarya suzo su bude taro da addua ganin ba Wanda ya Tashi Yasa Zuwaira taje Ta bude taro da addua sannan ta koma Ta zauna aka nemi cewa amare zasu Yi karatun Al Quran, Hindu CE Ta Fara zuwa tayi fatiha Da falaqi Da nasi, akai mata kabbara sannan sultana taje Ta Bayan Ta karatun fatiha sannan ta daura Da suratul baqra, ittama akai mata kabbara nan dai walima taci gaba akaiwa amare nasiha sosai game da rayuwar aure Da abun Da ya dace suyiwa mazajen su sannan aka rufe taro ko wanne ango ya dauki amaryar shi suka Kama hanya,tun a mota sultana ke kwada wayar kawu Amman bata shiga, kallan wayar tayi kafin taja tsaki wayan taki shiga, kallan ta sultan yayi wayar waye?kawu mana Ta fada Tana shirin yin kuka, murmushi yayi Maybe baida charge nasan wannan kauyen naku ai ba wuta kuke samuba,hmmmmm kawai tace taci gaba Da trying, yana parking Ta bude Ta five ,.

Da sallama Ta shiga, taro Ta mom tayi ya akayi ya walimar ina su aunty mairo? Suna anya mom walima tayi dai dai, OK kije ki yi wanka sannan kiyi shirin sallar magriba, to tace sannan tai sama saida Ta sake trying bai shiga sannan ta ajjiye Ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito lokacin sallah yayi tai sallah,da sallama aunty mairo Ta shigo, Da abunci a hannunta tashi sultana tai ta karba Ta ajjye sannan ta koma Ta zauna, kallan ta aunty mairo tai sultana meye naga duk kamar kina cikin damuwa,kalln aunty mairo tai aunty kawu nake Ta kiran number dinshi Amman yaki shiga kuma bai taba mun hakaba, ohhhh inajin baida charge ne, aa aunty ba zaace baida charge ba nasan yawancin lokacin Da baida charge, ta fada da Dan damuwa, riko kafadarta aunty mairo tai karki damu yana lafiya,..
Shiru tai Tana tunani sanda sultan yacewa mom gatana taje tasa rayuwarta a Cikin matsala, Mai yake nufi Da hakan kodai sarkine Yasa a kasheta shiyasa sultan ya yanke wannan hukuncin indai hakane kuwa sarki zaisa duk inda take aje anemota, Amman ina tana San tayi magana Da sultan yanzu kuwa, kallan aunty mairo tai aunty ankaiwa sultan abincin shi kuwa?kallan Ta aunty mairo Tai saikuma Ta Saki murmushi baa kaimaiba dama yace akai mishi Amman kuma Da bake zance ki kaimai ba, no aunty ki kawo in kaimai, taya zaai in Baki alhalin kinsan baa fiya fita da daddere a wannan masarautar ba, plz aunty zan dawo Da wuri in dare yayi sai in kwana acan..... Bata karasana tai saurin rufe baki tare dajin wata kunya, murmushi aunty mairo tai tun kafin a kaiki ai ba matsala tunda am daura zo muje ki karba, Da sauri Ta riko hannun aunty mairo wlh ba haka bane Allah abu zan tambayeshi nida ban sami kawoba duk hankalina ya tashi shiyasa Allah ba komai bane Allah ba abu Da zai faru, tabe baki aunty mairo tai kuka Sani ni ina ruwana zo muje taja hannunta sukai parlour,.

Kitchen sukaje Ta hada mata kayan abincin duk sai yanzu sultana taji kunyar kanta Ma, kallan aunty mairo tai aunty Na fasa gobe zakuyi magana Ma kawai, aikuwa baki isaba wlh sai kinje haka momy tazo Ta samesu take tambayar lafiya, aunty mairo tace abinci zata kaiwa mijinta, nan momy tace ina bata yadda ba Amman aunty nairo Ta dage, da kyar mom ta yadda duk Da tasan ba wani abun dazai faru kawai dai tasan sultana komai dare zatace zata dawone, badan tasoba haka sultana ta tafi ittadai burinta bai wuce taji lafiyar kawunta ba ,.
Da sallama sultana tai shiga bangaren nashi, ba kowa a parlour a hakan yasa ta ajjiye abuncin Ta shiga dakin ba kowa shima, nan Ta tabbatar yana masallaci, zama tai a bakin gadon sannan ta bude drower Ta dakko waddan hutanan ranar Tana kallo ,hutan mamanta take kallah sai hawaye, mikewa tai ta koma wajen window Tana kallan waje Da hutan a hannunta, ,.

Sultan Yana shigowa ganin abinci Yasar Yai sama sai yayi wanka Yana shiga ya hangota a wajen window Tana tsaye ,.

By hajara Mami natty girl

πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 58*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

ο»Ώο»ΏGanin Tana ciki yasa yai sallama Amman shiri bata amsaba,tunanin me take Ya fada tare da karasawa ciki, kusa Da itta ya tsaya kwata kwata batasan Da tsayuwarshi a gunba, uhmmm yai gyaran murna Da sauri Ta Kalli side din nashi sai kuma tadan ja baya tare da buye hutan a bayan Ta, kallan ta yayi shi baima lura Da hutanba Amman ganin Tana buye buye yasan bata Da gaskiya,me kike dauka mun Da gani baki Da gaskiya, uhmm uhm ba komai ni kawai abinci na kawo maka sannan za muyi magana ne, holding arms yayi kinsan me kwata kwata baki iya karya ba indai zakiyi kindinga kame kame kenan baki tsayawa gu daya, bafa karya nake Allah, eh nasan ba karya kike ba ki fada mun Me kika dauka kike buyewa, tabe baki tayi tare da mika Mai hutan, bai karba ya Kalli hotan, ashe kema kinsan kuna kama Da itta kenan? Karban hutan yayi ittace aunty inasan santa sosai mijinta shine sarkin mu a da Amman sai kuma lokacin Data haifar mun matar Da naso in Aura Ta rasu itta Da Yar Da sarkin sakamakon accident din mota, kallan shi wacce Ta haifa Da kaso ka Aura? Eh mana KO kina kishine, murmushi tai tare da shirin barin gun yai saurin riko hannunta, jin wani shock yasa yai saurin sakinta itta tai saurin janye hannun nata, ban gama magana dake ba ai tukun, eh a parlour zan jiraka sannan kayi saurin dan tafiya nake San inyi, Tana kaiwa nan tai gaba, murmushi yayi tare da shigewa toilet ,.


A Parlour ta jirashi har ya fito saida yaci abinci sannan ya zo yaji maganar Da take San ta tambaye shi, gani nazo fada mun abu Da ke tafe dake, gyra zama tai Yaya sultan sanda kazo kasa na rubuta wasika ga Hindu a wannan gun me dalilinka na Sani hakan? OK yanzu dai tuciyene zakiyi sai na fada miki kenan dan kin samu na ceceki KO? Plz wlh ba haka bane Allah hankalina bai kwanta Da kawu wlh jikina naban wani abun na faruwa dashi, kallan ta yayi OK sarkine yasa aje a nemomai ke, zaro ido tai a nemoni KO kuma basu ganni ba wlh nasan tunda basu ganniba cewa zaiyi aje garinmu a taho Mai Da wani nawa shine zasu dakko kawu,dan Allah yaya sultan ka bari inje in sami sarki ince mai Nice bana San wani abun ya sami kawu na wlh, ganin duk Ta rikemai yasa Ya riko kafadarta, ke ki tsaya baki Da hankaline kinsan waye sarkin nan kuwa? Eh na sani shi makashine mai kashewa yana sawa ana kashewa meye ban sani ba wlh Daya taba lafiyar kawu gara ya kasheni....... Squad sauri ya rufe mata baki,baki Da hankali ya kasheki inya kashe ki mutane nawane zasuyi asara, ina nufin kinsan momy ba zata ji dadi ba Aunty mairo yadda naga Tana wani janki a jiki ance miki Bari zatai kumama baki Da tabbas ya kamo kawun nakine KO aa Amman duk kinbi kin daddage, to wlh Bari in fada miki kikace zakisa ranki a cikin mutuwa niba ruwana, cire hannunshi tai daga bakin Ta, eh ni naji gara inje in fada Mai koma maye ya faru kuma yanzu zanje, ta fada tare da mikewa, kallan ta yayi wlh in kika fita a daga parlour nan zan saba miki sultana, ko kallan shi bataiba itta a dole fita zatai ganin Da gaske take yasa yai saurin mikewa tare da rikota Ta baya ke me yasa bakijin magana ne Bari in kira momy in fada mata, ganin Tana san kwacew yasa kawai ya rufe kofan Tare da cire key din, Ya koma ya zauna, ittama zatai a bakin kofan kuka kawai take wai zai kashe mata kawo kawai ya bari taje Ta fada Mai gaskiya,.

Momy Ya kira ya fada mata yadda sukai Da sultana, sosai hankalinta ya tashi tace karya Bari Ta fice Ma, gobe Za suyi magana, Da haka sukai sallama, .

TV ya kunna yabarta zaune abakin kofa Ta hada kai Da gwiwa Tana kuka, kallan sultan tayi yanzu hakama Da hadin bakinka a komai, murmushi yayi baice mata komai ba, mikewa tayi kazo ka bude mun kofa zan tafi bangaren mu, kallan ta yayi nanma bangaren mijinkine kiyi kwananki anan bamaiyin gulmar ki ai, Dan Allah kazo ka budemun ni IN tafi, kallan agogo yai kinsan karfe nawa yanzu, 11:00 ki tashi kije ki Kwanta dan nima tafiya zanyi ya fada tare da mikewa yana kashe TV din,.

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 59*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com
Har ya gama kashe TV bata motsa bama, kallan ta yayi KO so kike inzo in dauke ki kinsan ku amare haka kuke baki Da matsala sai in daukeki in kaiki din, tsaki taja bari Ma in fada maka wannan auren aiba aure bane saboda haka karka Ma bari jikinka ya taba nawa barinma yanzu dana gano cewa Da hadin bakinka a komai, dariya abun ya bashi aikuwa ya dara, zan kashe wuta kizo ki wuce, ba inda zanje a bangaren momy zan kwana ni, murnushi yayi tare da wucewa switch Ya kashe wuta,nan take parlour Ya koma duhu, kallan parlour sultana tai yayi duhu sai yanzu kuma Ta fara jin tsoro tsaki taja tare da Fara lalube Tana neman hanyar stair din, jin Ta taba abu yasa ta fara shafawa har fuskar sultan, jin shine yasa tai saurin dauke hannunta tare da fadin sorry Da ME ya kawoka kusa dani plz ka kunna mana wuta, rikota yayi tare da fadin daukarki zanyi bake kika fada kinfisan in daukekiba kuma Ma aike kika zo bangarennnan amarya Mara kunya wacce ba zata bari akaita dakin mijinta taba tazo Da kanta, tsaki taja Tare da fisge hannunta zata juya yai saurin rikota tare da daukarta, wannama ai iskancine nace bana so ana dole ne, baice mata komaiva har saida yakaita dakin Data saba zama indai ya cutota Da daddere sannan ya direta, tsaki taja Ta kalleshi ya wani hade rai,kallan dakin tayi an gyarashi sosai an sake kayan dakin komai da komai yayi kyau sosai, kujeran madubi yaja ya zauna tare da fadin zauna zamuyi magana ganin Ya hade rai Yasa taji wani iri, zama tai,.

Sarki dake fada a zaune yana shirin tafiya makwancin shi ya kira Wanda yasa aiki yace su hadu dashi a inda suka saba haduwa Da misalin karfe 1:00pm na dare su zomai Da kawu yana san za suyi magana,.

Kallan ta a sultan yayi sultana karki ga ina sake miki fuska kice hakn zai kawo mana raini dake bana San raini bana San inawa mutun magana yana nuna KO ajikinshi banasan raini ki kiyaye karki manta matsayinki na baiwa kinsan ke baiwa ce haryar har gobe sannan karki dauka wai dan kin aurenin kin Tashi daga baiwa a guna ba haka bane kinanan a matsayinki inasan kina tunawa Da hakan Da fatan kin gane, kallan shi tai da hawaye a fuskarta aranta fadi tade Data gama abun daya kawota shikenan kuma wlh yau zata Fara Ta tsani ya dinga kiranta Da sunan baiwa dinnan, ganin taki magana sai hawaye hakan yasa Ya mike Ya fice,.

Kallan dakin tai kawai tai kwanciyarta tana hawaye tare da tunanin kawunta ko a wanne hali yake yanzu Allah masani ,.

1:00pm
Sarkine azauna a farfa jiyar masarautar shida Yan aikinshi sai kawu dake kan kujera a daure, kallan shi sarki yayi Da gani baka gama tsufa ba zaka Dan jigata kafin ka mutu IN kuwa bakai taurin kaiba ka fada mun abun Da nake nema shikenan zan sallameka Da abun alkhari, kallan shi kawu yayi inaji meye abun Da kake nema? Murmushi sarkin yayi wannan Yar taka yama sunanta itta nake San Ka fada mun inda take, kallan shi kawu yayi tunda baisan sunanta Bari ya sa mata wani au wai ummina dama wai kaine sarkin bata gama dakaiba aina dauka har ta gama dakai Ta fadawa duniya kokai waye me ta tsaya yi, kallan shi sarki yayi fuskarshi a daure, ohhhh Da saninka tazo wannan masarautar daukan fansa kenan? Eh mana nidakaina na kawota kuma nasan tana kan hanyar yin hakan, sign Ta ido sarki yayi na kusa Da kawu bashi wani duka a kafa Da saida ya sashi sakin wata kara Ta wuya,.
A razane sultana dake bacci Ta tashi Tana salati ,ya kamata Tasaba Da wannan hali irin na wannan masarautar kaitaji ihu Da daddare sannan inkayi tambaya ace aljanun masarauta ke fada itta kan ihun yau ya fitar mata daban dole taje taga Maye, ta window ta leka, ganin haske a farfajiyar masarautar yasa ta Mike tare da daukan mayafimta Da dauki phone dinta, ta fito parlour,.

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 60*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com
A hankalj take sakkowa parlour duhu ba kowa, kunna wutan tai Tana neman key a akan Centre table din daya zauna Ta gani, hakan yasa ta dauka Ta bude kofan Ta fice Da addua abunta,. Tafiya take haske masarautar dake akwai hasken farin wata, Da raba rabe Da komai har takai wajen gun da suke Ta buya ta can bayansu bataga fuskar kawuba Amman Tana ganin ta sarki, gabanta banda dukan hamshin hamshin ba abunda yake, wayarta Ta ciro dukda bazai fito sosaiba Amman a haka zatai video record din ya kaamata ace ta Fara abun daya kawota,a hankali Ta saita wayan itta abun Da take bukata bai wuce Ta dauki fuskar sarkinba Amman da yake duhune bai fito sosai ba, Amman a hakan Ta tsaya take abunta,.

Dukka batajin abun Da yake fada Amman Tana ganin abun Da suke,.

Kallan shi sarkin yayi badai zaka fadi gaskiya bako shikenan mu zuba nida kai zan baka nanda sati daya inkaga zaka iya fitowa kana fadi gaskiya shikenan in bazaka iya ba Elgar kasheka zan yi Da kaina kamar yadda dakaina zan kasheta ittama, sannan in kashe mahaifinta Da kaina, mikewa yayi ya kallesi kuje dakin ajiya Ku nuna mai mahaifinta sannan ku bashi a zaba sannan ku sanar Da abdulsalam gobe inna dawo daga wajen taron bikin Hindu zanzo in sameshi, kallan gun da sultana take yai kamar Da mutun agun matsawa yai gun, hantar sultana kuwa bugawa take kawai Amman bata fasa daukan record dintaba, yanzu fuskanshi ya fito sosai, zan kamata kuma zan kasheta su kadaine makiyana a duniyar nan, sannan ya juya yai musu alama su tafi dashi, sannan shima yai gaba ,ajiyar zuciya sultana ta sauke saida Ta Bari sunbar gun sannan ta kama hanyr komawa bangaren sultan din,.

Dakin ajiyar suka kaishi har gun sarki abdulsalam,kallan kawu sarki yayi bawan Allah me ya hadaka Da wadannan mugayen? Kallan sarki yayi babu shakka kaine mahaifin sultana, riko hannun sarkin yayi karka damu yarka nada dakarkiyar zuciya nasan zata fitar dakai anan KO ba dade KO ba jima kaidai adduar ka take bukata, bawan Allah ban ganeba? En nine Wanda na rike yarka har ta girma koma tazo nemanka, to bansan taya ya gano taba shine yake San in fada mai inda take Dan naki yace akawo ni nan, Amman karka damu nasan Tana zuwa, murmushin jin dadi sarkin yayi,.

A hankali sultana ta tura kofan parlour ta shiga sannan ta rufe kofan zuciya daya Ta juyo zata wuce idonta ya sauka kan sultan dake gaban fridge da ruwa a hannshi Yana kallan ta,.
Cikintane ya bada wani kuluuuuu luuuuu Ta hadiye wani uban yawu ,ajjiye ruwan yayi ya nufin inda take,da sauri Ta juya zata bude kofan Ta koma tai hada Da gudu tare da dawo Da itta ya rufe kofan ya hadata Da jikin kofan, kallan ta kawai yake, kamar yayi kuka, a hankali ya fara magana sannu Da zuwa aunty jaruma waike wacce irin Mace Mace Dan Allah ki fada mun abunda ya kawoki masarautar nan Dan da gani bawai aikine ya kawo kiba nifa kin fara ban tsoro banda aljanar Mace wacce macence zata iya ficewa a wannan uban daren fisabillahi kuma ko ajikinta Dan Allah ki fada mun, kallan shi tai uhmmmm uhmmm damafa bangaren momy zan tafi shine kuma dana fice naga naji tsoro shine Na dawo, ta fada tare dayin kasa dakai,dago habarta yayi ban fada miki baki iya karya ba Yau saikin fada mun abun Da Ya kawoki marautar nan,.


By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 61*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com


ο»ΏShiru tamai batace komaiba, shima kuma bai matsaba,kallan shi tai KO a jikinshi, ranka ya dade nifa baiwace ba uban gidan mutun baikama yana takurawa baiwarshi hakaba ni bacci nakeji plz zan wuce, baccin kike ji kika fice Da daddare? Yaufa sai kin fada mun ,OK naji Dan matsa to muje mu zauna sai in fada maka Amman saika ban amsa tukun Da alkawarin duk abin dana sakaka zaka mum, kallan ta yayi sosai yanasan karantar Ta Amman baiga komaiba illah zillar rashin tsoro, OK naji Ta fada tare da matsawa, zama yayi akan kujera yana kallan ta Ta Sami daya ittama Ta xauna, uhmmm so nake ka fada mun wai me yasa baaa fita a wannan masarautar Da daddare? Saboda yawanci duk Wanda ya fita da daddare a wannan masarautar mutuwa yake, OK kuma itta wannan masarautar me take tunanin Yana wannam kisan, gyara zama yayi aibansan sanda kika zama yar jarida ba, uhmmm kaifa kace saina fada maka me ya kawoni wannan masarautar to maye Dan ina Maka tambaya kuma saida na fada maka ka amince maye a ciki to, OK naji, a iya bincike na wannan masarautar mum gano cewa aljanun wannan masarautar ce wadda akai musu gini a tasu masarautar suke kashe Yan garin nan da daddare, wata dariya Ta sake wadda saida Ta dade Tana yi kafin Ta kara kallan shi tana murmushi kuma kai ka yadda da hakan? Eh mana me yasa bazan yadda ba ,tabe baki tai OK to meyasa ni basu taba kasheni ba duk fitar Da nake sannan kuma abun mamaki ban taba gamo Da aljanuba sai mutane dake yawo Da addare me hakan yake nufi kenan, murmushi yayi tare da gyara zama hakan yana nufin kema aljanace shiyasa mutanen basa iya kamaki, OK ni aljanace Amman harda Mai taimakata ko? Ta fada Tana daga mai gira, hade fuska yayi ke banasan shashanci kawai ki fada mun abun daya kawo ki wannan masarautar, OK bari in maka tambayar karshe,ai gwannati ya kamata ittama Ta bada gudin mawa me ta bayar, taba dpo dake bincike Amman iya binciken shi bai gano komaiba Yaya iya dawa wuce yai hakuri, Hmmmm Ta sauke ajiyar zuciya zaka iya hadani Da dpo din? Sakin baki yayi Yana kallan ta me zakice Mai, gudun mawa zan bashi tunda shi ya kasaa aikinshi, tsaki yaja bani amsata plz mikewa tayi sarkin ku nada nazu fitowa dashi sannan in tuna asirin mugawaye, kallan ta yayi gwannatice Ta aiko ki? Aa nina aiko kaina gobe zamu karasa magana saboda ina bukatar taimako, saida safe tai fada tare da yin sama, Ya bita Da kallo tunba yauba yake tunanin sultana Nada aljanu may be yanzuma aljanun nata ne suka tashi banda hakan mutumin daya dade Da mutuwa tace tazo dakkoshine aya, mttswwww yaja tsaki tare dayin sama ,.

Washe gari tunkan gari ya gama haske sultana ta wuce bangaren Momy lokacinma basu tashiba,.

Saida tai sallah sannan ta koma Ta kwanta,.
Da sallama momy Ta shiga dakin nata, ganin Tana bacci yasa ta tasheta, ina kwana mom? Lafiya qlau sultana, sultana me yasa bakijin magana ne so kike kamar yadda muka Rabu da mamanki kema mu rasa ki? Aa momy wlh hankalinan jiyan yaki kwanciya shi Yasa Amman bazan sakeba, murmushi mom tai tare da shafo kanta karki sake plz, daga kai tai alamar to, mom wlh yau bazan Sami damar zuwa wajen party dinnamba kaina ciwo yake mun, OK zan fadawa sultan din Amman kinsan ana dawowa zaa wuce dake bangaren kiko? Eh momy na sani Allah ya dawo dasu lafiya, ficewa mom tayi Ta barta, murmushi sultana tai aikina zan Fara yanzu kamata yayi ace Ma har na gama Tara shaiduna Amman ina abun yakici yaki cinyewa, Da sauri Ta Mike Ta dauki wani hijab sannan ta fice bangaren bayi Ta nufa, sai gaidata ake Tana amsawa Tana zuwa tacewa marka gun su Zuwaira tazu saboda dasu tai kawaye agun walima, har dakin marka Ta kaita sannan ta fice, Da sallama Ta shiga tare da fadin ina kewar dakin nan, kallan sukai me ya kawo ki taya akai kika fito Da wannan uwar safiyar?

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘.

Please Login or Register in order to submit comment