Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

24/10/2018 à 22:00 - Vous avez créé le groupe “👸PRINCESSE👸”
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

*Wannan labari ne da na yishi a farkon fara rubutu na, amma abisa wasu kura kurai da ke cikin waccen rubutu sabida rashin sanin miye rubutu a waccen lokacin, hakan yasa zan sabinta maku shi ta hanyar canza Salan rubutun da ingantashi fiye da na baya tare da canza wasu abubuwa daga ciki dan jin dad'in ku*

💗💗💗💗💗💗
Bismillahi Rahaman Rahim
💗💗💗💗💗💗

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)_ 🤜🤛

*Page*

1⃣-5⃣

Duk girman gidan bai hana shi cika ba sabida hidimar bikin da ake, kowa cikin farin ciki ya ke babu bakin ciki a nata hayaniya, shagalin biki kenan na auren da za'a d'aura nan da Minti Ashirin, Amare ne guda hud'u da angayen su.

ban an kara ba naji an bige ni har saida alkalamina ya fad'i k'asa, daga kai nayi naga ko wace shedaniyar ce, wata kosansan Budurwa na gani sai gudu take tana waiwayen bayanta kafin na kula naga wani 'Kakk'arfan Saurayi da gudu yana biyar ta da belt a hannu, bin bayan su nayi har cikin katon falon da ta shiga in da taci k'aro da wata kyakyawar tsohuwa ta b'oye bayanta tana fad'in,

"Dan Allah hajia ki taimake ni kice karya dake ni" tsaye yayi yana huci, cikin zafin ray ya kai mata duka da belt kin hannunshi yanda ya sauka a bayanta ne yasa ta saki k'ara tana Ihu, tsohuwar ce da ranta ya b'ace tace" kai SALMAN ashe ba kada hankali wai miyasa kuke hakane kamar wasu Kananan yara?" juyawa tayi ga yarinyar ta jawo ta tace" mi kika mashi nasan dai haka kawai baya biyo ki ba tunda ba mahaukaci bane shi?" cikin kuka ta fara mata bayani" wallahi hajia kawai muguntar sace ta tashi, daga naje karb'ar charger ta wajen yaya MUBARAK shine fa kawai yake kallo na daga nace ya kama bakin shine wai ya biyo ni" tana rufe baki ya kama kunnanta cikin masifa yace" kinji ko hajia dan ta raina ni ni zata ce wai na kama baki na, ina abin kallo a jikin ta yake, wallahi sai na karyaki in kika k'ara shiga harkata shedaniya kawai" fizge kunnen''ta tayi cikin zafin nama ta mike tsaye zatayi magana kuma sai ta ruga a guje sabida d'aga belt kin yayi zai buga mata, juyawa yayi shi ma yabar wajen.

Saïda tabi kowannen su da kallo kafin tace" na samu hanyar da zanyi Maganin ku tak'adaran yara kawai, kuna yan uwa amma kun zama kamar b'era da mage, Insha Allah Komai ya zo k'arshe daga yaou, idan kuka zama d'aya zaku daina duk, wannan shirmen" wuce wa tayi d'akin kakan yaran inda bata gushe'ba har saida burin ta ya cika.

09:00 aka d'aura auren Amare guda hud'u gami da wadanda aka kara suka zama biyar.

*to yan uwa ya zata kasance idan aka d'aura auren wadanda babu su a cikin jadawalin d'aurin auren yaou?*

Yan Uwa kuna san labarin in'ci gaba?


~Sai naji daga gare ku.~
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

*page*

0⃣6⃣-1⃣0⃣

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)_ 🤜🤛

Sank'ira ne ya fara fadin"(masha Allah, Allah ya nuna mana an d'aura wannan aure na amare da angaye, aure na farko shine tsakanin,Mubarak Siraj Manu da Nadiya Yahaya Manu, na biyu tsakanin Khamis Yahaya Manu da Jawahir Suleiman Manu, na uku shine tsakanin Shamsudeen Suleiman Manu da Hafsat Siraj Manu,sai na hud'u tsakanin Nouradeen Salihu Manu da Khairat Yunus Manu, sai na biyar tsakanin Salman Yunus Manu da amaryar shi Zeinab Abdul-Hamid Manu wato (Ummi)."

Shiru ne ya ratsa illahirin mutanen da ke wurin dan jin aure na biyar,Kallan kallo kawai a keyi saida kowa ya tabbatar sannan aka fara farin ciki, wasu da hukuncin bai masu ba kamar zasu fashe dan bakin ciki Hajara uwar gidan baba yahaya taso ace an had'a Salman da Rumana dan taci buri akan auren su, Ummi da ke d'aki ta nata tsokanar su
Jawahir tana masu shegantaka, yayarta SA'ADATOU da RUKAYYA yayar Jawahir suka shigo suna Bud'a suna murna a nanfa suka fad'a masu halin da ake ciki, Ummi da tak'i yarda fitowa tayi tsakar gida tana tambayar Mahaifiyar ta wato HAWATAN(Hawaou) kasancewar ta buzuwa yasa ake kiranta da Hawatan, tin'da tace" eh Ummi da gaske an d'aura aurenki kema" cikin nuna rashin yarda tace" haba la mamma ta yaya za'a d'aura aure na haka kwatsam ai ba haka ake ma kowa ba sai ni za'a fara kai na?" hannunta ta d'ora a kafad'unta tace" kinga kiyi hak'uri kinji wannan hukuncin kakan kune, kuma ai ba yaou zaki tare ba ke" jaye jikin ta tayi tana fad'in" a'a la mamma hakan ba zaiyiwu ba miyasa sai yaya Salman za'a aura min"? da gudu ta koma d'akin da amare suke ta kwanta ta fara ai kin kuka kamar ranta zai fita, k'awayenta kuma yan uwanta sunyi ban hak'urin amma ina sun kasa dan haka suka rabu da ita.

tunda a kace Ummi na kuka hajia Babba tace a k'yaleta zata ji da ita, d'akin ta shigo ta tayar da ita zaune saïda tasa ta daina kukan sannan ta fara magana cikin nutsuwa da dubun hankali" Zeinab ki nutsu ki saurare ni kiji abinda zan fad'a maki kinji shaleleta"Ummi shi aure da kuke gani darajar shi ce tasa Ubangiji ya hallata shi a tsakanin bayin'sa, darajar aure da kuke gani tafi Karfin tinanin ki sabida daraja da matsayin shine yasa hatta bishiya zakiga an mata aure kafin ta fara toho, sannan aure sunna ce mai k'arfi daga sunnonin Manzo ( S A W ) kuma duk wanda ya raya ta to ha'ki'ka zai samu babban rabo, sannan aure ya nada matuk'ar mahimmanci a rayuwar mu wanda idan da babu shi da Ummi bana jin da yanzu akwai Duniya dan bad'alar da za ayi ba kad'an bace a Sakamakon haka kuma Allah Zai iya kifar da duniyar ma Baki d'aya"

" Ummi wani abun farin ciki anan shine duniyar nan munacin Albarkacin Annabi Muhammad (S A W) ne sannan yara ma suna taka rawa a cikin rangwamen da Allah ya keyi mana, to yanzu Ummi in har hakane mi zaisa ki k'i aure har ki tsaya kina bata lokacin ki wajen kuka, ke da zaki samu wannan manyan mayan rabon, Bugu da k'ari kuma Salman dan uwanki ne kinfi kowa sanin tsakaninki da shi, nice nan na haifi iyayen'ku maza da ke da shi to miye matsala a ciki, nasan dai za kice sabida ba bakwa shiri ne da shi, wannan kuma mai sauki ne In har ki kayi abinda zan fad'a maki" share Hawaye tayi tace"hajia a gaskiya ba'amin Adalci ba, ta yaya za'a d'aura min aure da mutumin da Kusan tsakani na da shi kunsan mugu ne shi ko kad'an ba yada tausayi" kai ta girgiza tace" kash, Ummi ina baki kina rok'o, Salman fa ba kamar yanda kika d'auka bane kece kawai kike masa Kallan mugu shi ma kuma ke kike ja ma kan ki sabida kinsan abinda baya so amma se kika maida wannan abu kamar 'dabi'arki duk lokacin da kika gan shi sai kinyi" amma hajia to miyasa za'a aura min shi ni gaskiya bana san shi?" Ummi kiyi Hak'uri kamar yanda nafad'a maki, idan har kika yi hak'uri kika bi Umarnin mu to basai na fad'a maki ba kisan za kifi kowa jin dad'in Alhaji, amma in kika ki kika bijere tofa kinfi kowa sani wallahi zaki shiga matsala" Ummi ke da Salman duka jikoki na ne naji dad'in wannan HAD'IN AUREN dan ba'ataba irin Shi, ki kwantar da kanki ki zauna lafiya da dan uwanki kiyi masa biyayya domin yanzu shine k'ofar shigar ki Aljanna, kiyi duk abinda yace in dai kina so ki rabauta Duniya da Lahira, ki kyautata mashi idan kina so Allah ya yarda da ke ya saki a cikin bayinsa mafifita, ki zama mace ta gari a wajan Mijinta ki zama mace mai biyayyar aure ki zama yar Aljanna" bayanin da Hajia tayi gaba d'aya amaren sun k'aru da shi kuma sun d'auka saidai a wajan Ummi ba haka abin yake ba.


Tunda Salman yaji sunan sa ya fito a cikin wannan résult wanda shi a wajan shi kamar an kafe sunan yan wuta ne kuma sunan shi ya fito, rud'ewa da kid'imewa da tashin hankali ya ma rasa wanne ne a ciki ya shiga, zai iyya zama da kowace irin yarinya a duniya daga ciki har da karuwa amma banda Ummi dan kuwa yarinyar ta mugun raina shi hakan yasa ya tsane ta duk da suna yan uwa kuma makotan juna yana wuni gidan su tana wuni gidan su amma hakan bai sa suka jitu ba, Hakuri da rarrashin da Abokan shi da sauran angayen ne suka fara bashi ganin ba zai'iya ba dan bâ abu bane mai yi yuwa yasa ya shiga motar shi ya kama gaban shi ko ya ji Sauki a ran shi.

Yan Uwa dai bakin su suke sha babu kama hannun yaro, har lokacin da aka gama kintsa amare izuwa gidan mazajen su, a lokacin ne Alhaji USMANE( Manu) ya tara su a Babban falon su ya masu Nasiha mai ratsa jiki tare da gargad'in su anan Kowane ya kula da Hakkin da Allah ya d'ora mashi akan shi na dab Abokin zaman shi, sannan ya maida akalar akan Ummi da Salman, wanda ya kwadaitar da su akan in dai sun zauna lafiya to za suji dad'in zama da shi in kuma aka samu akasin haka to akwai matsala.

Mahaifiyar Ummi ta nemi Alfarma wajen Alhaji akan ya amince Ummi ta zauna har nanda sati biyu sai ta tare,amma yace sam baiga dalilin da zata zauna gida ba da aure a kanta dan haka sati 'daya ya basu akan sun gama duk yan tsirfe tsirfen su kafin nan.


*To Allah ya kai mu ranar Tariyar nan muga mi zai faru*
27/02/2019 à 17:29 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜🤛

*Page*

1⃣1⃣-1⃣5⃣


An nufi da amare gidan mazajensu inda Ummi kuma suka tafi gidan su tare da Mahaifiyar ta, dama gidajen suna kusa ne, suna shiga d'akin ta ta shiga ta soma wani sabon kuka har saida bacci ya d'auke ta duk da La mamma najinta amma ta kyaleta dan yanda ta d'auki Salman bata d'auki Ummi haka ba shiyasa bataga abin daga hankali a ciki ba.

Cikin dare Ummi ta farka ta fito falo ta bud'a frige ta d'auki madarar shanunta wanda Mahaifin ta ya sabar mata shan ta tin tana karama yanzu haka in bata shaba har kan ta ke ciwo, tana sha takoma d'aki tayo alwala tayi Sallah Isha'i da bata yiba ta d'auki AlQur'ani tayi karatu sannan ta kwanta.
tana tashi da safe La mamma tasa aka fara mata gyaran jiki mai zafi dan ba suda lokaci wanda aka basu kad'an ne.

kwana uku aka kwashe har yanzu Basu had'u da Salman ba, Abba ne kad'ai ke rarrashinta da su hajia idan suka zo gidan sai kuma Mamar Salman kin wato Hajia HALIMA, yaou kam Mahaifiyar Salman ta tiso shi gaba akan yazo yaga matar shi ba karamin d'aci yake ji ba idan yaji sun kira Ummi da matar shi haka ya daure ya zo gidan, tin'da tayi Sallah Magriba bata saké fitowa ba sabida kiran da JAMAL ya mata, bud'e k'ofar da taji yasa ta saurin aje wayar tana muzurai duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, Kallan tuhuma Salman ya ke mata har ya k'araso in da take cikin rashin yarda yace,

"mi ki keyi da wa kike waya?" wata harara ta dalla mashi tace" to ina ruwanka da ni miye matsala ka?" hannunta ya fizgo da k'arfi ya karbi wayar ya duba number ce babu suna dan haka yace" da wa kike waya?" cikin b'acin rai tace" a'ah Malam wai miye haka ina ruwanka da ni to?" cikin hassala ya matse mata kumatu yana fad'in" bana ciki da iskanci kar ki d'auke ni sakarai, ni yanzu mijinki ne dole nasan mi kike ai katawa" duk da tayi 'kok'arin fizge hannunta amma ta kasa dole tace" aw kenan kai ka d'auka da gaske ni matar kace, to wannan kishi ne ko mi?" sakinta yayi yace" Allah ya tsareni nayi kishi a kan ki, wallahi ke kinsani in banda darajar aure ke baki isa ba kira ki da matar aure na ba" nunata yayi da wayar yace" daga yaou babu ke babu waya har lokacin da naga damar ki rik'e" wucewa yayi zai fita da sauri ta sauko daga gadon ta tare gaban shi tace" kaga Malam dan Allah bani waya ta sai kace wani kai ka siya min" nuna mata wayar yayi yace" ki k'wata mana idan kina da k'arfi" shiru tayi tana k'are mashi kallo tasan bazai bata ba dan haka tana ganin yasa ta cikin aljihun rigar shi sai ko tasa hannu, cabke hannun yayi ya murd'e mata yan yatsu yana fad'in" marar kunyar banza, sai ki saka ma mutum hannu a cikin aljihu wannan salan halin b'era kenan" duk da tana jin zafin murd'ar da yake ma hannunta bai hana tace" b'eraye dai ai kai ne ma babban b'era gashi kamin gaba da waya" tsaki yayi ya gitta ta ya wuce ya bar gidan.
su Abba ne zaune suna cin abinci kallan La mamma yayi yace" wai ina Ummi take ne?" tab'e baki tayi tace" tana d'aki mana tunda ta d'ora ma kan ta larura" girgiza kai yayi yace" ki dinga hakuri mana kema, kiyi la'akari da yanda nata auren ya kasance ba kamar na kowa ba, itace ta farko a famille nan da aka mata aure babu saka rana bare raba goro sai ki mata uziri ko" k'ara tab'e baki tayi tace" amma miye na damuwa a ciki Salman fa dan uwanta ne tasan shi tunda tare suka tashi to miye saban abu a ciki?" hakane amma kuma kinfi kowa sanin tsakanin ta da shi, ba shiri suke ba" to ai auren da aka had'a su kaga sai su fara shirin watakila ma su so junansu nan gaba kad'an" to Allah yasa haka, idan haka ta faru ai za mufi kowa jin dad'i" gaskiya ne Allah ya tabbatar da Alkairi, ya basu zaman lafiya" Ameen Inji Abba.

haka aka k'ara wani kwana ukun ana gobe Ummi zata tare an gama kimtsata yanda ya kamata kama daga kunshi kitso gyaran jiki har dama gyaran d'aki, gobe ake jira tayi saidai duk abinda Allah ya tsara zai faru to babu makawa, Ummi ce da kewa da damuwa ta mata yawa ta d'auki wayar La mamma ta kira Jamal sabida irin soyayyar da yake mata tana jin dad'i dan shine na farko da ta fara soyayya da shi, hira sukayi sosai har saida yace mata" kinsan wani abu a gaskiya ina so na saké ganinki?" gabanta taji ya fad'i amma sai ta dake tace" um a gaskiya bazai yiwuba" da sauri yace" miyasa Ummi baki san gani na ne?" cikin i'ina tace" ba haka bane kawai dai akwai matsala ne" matsala kuma ta mi?" rasa abinda zata fad'a mashi tayi dan haka yace" kinga Ummi zan zo gidan ku yanzu ruwan kine ki fito ko ki 'ki fitowa amma kisani idan ma baki fitoba to ni har cikin gidan zan shiga in da na ajeki a ranar da muka fara had'uwa da ke" kashe wayar yayi yabar Ummi baki bud'e gabanta ya tsananta fad'uwa.

Minti talatin kenan Jamal ya kira Ummi yace gashi nan K'ofar gida ta fito ko ya shigo tunda shi da aure yake santa, cewa tayi ya jira ta a bayan gidan su tana zuwa, duk da tace mashi tana zuwa amma ta d'auki Kusan minti sha biyar kafin ta fito ba tare da kowa yaga fitar taba, tana so ta fad'a mashi Komai akanta da auren da aka d'aura mata dan taba shi hakuri suyi sallama.

*To Allah ya kauda b'acin rana*😞👏
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛_


*page*

1⃣6⃣-2⃣0⃣


zaune ta same shi cikin mota k'afafun shi a waje, yana ganin ta ya fito ya rufe k'ofar bakin shi har kunne, gaissawa sukayi a gurguje Ummi tace" am Jamal na fito ne dan na fad'a maka ko wacece ni, muna cikin halaka Jamal" cike da mamaki yace" halaka kuma wace irin halaka Ummi?" kanta k'asa tace" Jamal ni fa ba yanda ka d'auka b'ace, a yanzu haka ina da aure a kai na kuma na fito dan na fad'a maka haka, Dan Allah muyi hakuri da juna kaje ka nemi wata wacce ta fini,watakila ita ce mafi alkairi a gare ka" cikin wani irin yanayi yace" a'a Ummi dan Allah karki min haka, wallahi ina sonki, kuma na fad'a maki Komai a game da ni kinsan koni waye kinsan labaran soyayyata har guda hud'u, Dan Allah Ummi ki amince ki aure ni ko zaki canza wannan labaran nawa marasa dad'in ji, idan kuma baki so na ne basai kin b'ullo min ta wannan hanyar ba"
"A'a Jamal ba haka bane, wallahi an d'aura min aure yanzu haka gobe zan tare idan Allah ya kai mu" haba Ummi kar ki raina min Wayo mana, ki fito ki fad'amin gaskiya kawai" cikin kossawa tace" kaga Jamal na fad'ama gaskiya ina da aure dan Allah kar ka saké kira na kuma ka manta da ni a rayuwarka, ka gafarce ni ban d'auka haka zata faru ba" zata wuce ya rike hijabinta yayi dai-dai da karasowar Alhaji Manu wanda ya tsinkaye su tun daga nesa amma yana tinanin ko su waye, yana ganin haka ya kunna tocilar shi dake hannunshi, da sauri Ummi ta juya sai ko yaga fuskarta, Ummi ma ba ganin Alhaji ta tsora ta sosai kubce hijabin''ta tayi ta ari na kare da gudu ta shiga gida, yayi dai-dai da fitowar La mamma da Abba tare da Salman suna tambayar k'annanta dake wasa a tsakar gidan.

yana ganin ta daka da gudu ya ciro wayar shi ya kira AUWAL Babban d'a ne ga baba Yahaya, yana d'auka yace" kai kana ina?" cike da ladabi yace" yanzu na shigo gida zan gaida su Mamma" to mu had'u da kai gidan baban ka Hamidu" bai ko amsa ba ya kashe wayar, tunda Ummi ta shiga d'aki ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tasan yaou kam sai ta Allah babu abinda zai hana a dake ta a gidan nan, Addu'a ta ke koda za'a dake ta to kowama ya dake ta amma banda yaya Auwal.

kai tsaye falo ya shiga ya zauna yana 'kare ma su La mamma kallo babu wanda ya iya tambayar shi lafiya saïda Auwal ya shigo sannan ya kalli La mamma yace" Hawatan kin bani kunya banyi tsammanin haka daga gare ki ba,na d'auka amanar da na baki zaki kula da ita ashe ba haka bane" cikin rashin fahimta jiki na rawa La mamma tace" mi kuma ya faru wallahi bansan Komai ba Alhaji" maida kallan shi yayi ga Salman yace" kira min ita"wucewa yayi yana tinanin komi ta aikata hatsabibiyar oho.

yanda yaga tana ta safa da marwa yasa yace" wace tsiyar ki kayi?" hararan shi kawai tayi taci gaba da kai da kawo warta," to wuce muje Alhaji na kiran ki kuma Allah yasa ya bani bulalar da kai na na zane ki" yan cikinta ne suka kad'a da sauri tace" bulala kuma?" gira ya daga yace" ai ke da kinga Auwal kinsan yana tare da bulalar shi sabida ire irenku" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un na shiga uku, Dan Allah yaya Salman ka taimaka min wallahi babu abinda nayi, kace karya dake ni" ke wuce mu tafi ni babu ruwa na nasan mi kika aikata, ina mijinki amma bansan fitar kiba saidai naga kin dawo" wucewa yayi ya bar tanan kamar zatayi fitsari daga tsaye, jin muryar Alhaji ne yana fad'in" kaga kace in ba zata fito ba ni sai naga shiga na fiddo ta" a hankali ta bud'e K'ofar d'akin tana raba idanu ganin Auwal ya k'ara kad'a mata yan hanjinta, kusa da La mamma ta durk'usa kamar zata shige jikinta, cikin b'acin rai Alhaji yace" Ummi ni zaki zubarwa da mutunci, ni zaki tozarta a unguwar nan da aurenki ki fita kije wajen wani dan Iska har yana rik'e hannunki" to bari kiji wallahi baki isa ba ko ubanki bai isa in shinfid'a doka ba ya 'ketare bare ke yar da ya Haïfa" carbin dake hannunshi ya tilla ma Auwal yace" zanemin ita ta yanda bazata saké tinanin saba Umarni na ba nan gaba" tsabar rashin imani da tausayi yasa Auwal jayo Hijabin Ummi ya fara tsula mata carbi kamar Allah ya aikoshi, Ihu take tana ba Alhaji hakuri amma ina ga Abba zaune amma babu yanda zaiyi koda Ummi taji duka yana ratsa har cikin ruhinta sai ta fara kiran sunan" wayoo La mamma kice yayi hakuri wallahi bazan sake ba, Abba ka bashi hakuri wallahi babu abinda nayi, wayoo yaya Salman dan Allah kace yayi hakuri" har saida hijabinta ya fita ta zama daga ita sai doguwar riga, ganin yanda take ta k'o'karin shigewa jikin Auwal tana so ta rike carbi yasa Salman jin ba dad'i, mikewa yayi ya rik'e carbin ya kamo

Please Login or Register in order to submit comment