Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaki tayi tace" wai miji, ina mijin yake anan? saidai muna maza" ji kake Tasssss, ya kasheta da mari tare da fad'in" ke har kin isa ki fad'amin haka, wallahi ko Sa'ada dake gaba dake bata isa ta fad'amin haka ba, bare kuma ke da aka haïfa a gabanta" haka ta fara wanki tana kuka tana fad'a, bata gama ba sai misalin 17:40,saboda ko a gida ita ma kayan da suka zama wajibi ne a gareta ta wanke da kanta take wankewa, amma manyan kaya mai wanki ake bawa ya wanke mata, amma yau gashi tana ma k'aton gardi wanki( inji Ummi fa).

Tana idawa ko wanka bata yiba ta d'ora girkin dare, a gajiye ta kammala aiki bayan sallah isha'i, tana gamawa ta aje Kwanukan a dinning tayi alwala tayi sallah tana sallamewa daga nan bacci ya d'auketa ko shafa'i da witri bata yiba, Salman na lek'awa yaga tana bacci ya fito yana cewa" raguwar banza, ai dama da gangan nake saka ki aikin dan babu tsiyar da kuke a gida ke da su Khairat da jawahir sai iskanci da zuwa gidajen juna ana d'aukar photo" da kanshi ya zuba abincin yaci ya koma d'akinshi yana latse latse a ordinateur d'in shi, jin an fara kad'a iska ga walk'iya da ake ana cikin haka aka fara yayyafi har ruwa suka fara k'arfi, ganin an d'auke wuta yasa ya kunna wutar wayar shi ya tashi ya nufi d'akin Ummi dan yasan yanzu zata fara neman taimako, k'aro yayi da Ummi k'ofar d'akin tana shirin fitowa daga ita sai towel d'in dake d'aure a k'ugunta tana shafa turare aka d'auke wutar, kallon juna su kayi sum sum Ummi ta haye saman gadon ta kwanta, Salman ma zaune yayi gefenta tsawon lokaci ya d'auka a zaune, ganin ba ada niyyar maido wutar ya gyara kwancinshi shi ma bacci ya d'aukeshi.



Salman ne ya fara farkawa da k'yar ya bud'a idonshi saboda haske an maido wuta suna bacci, addu'ar tashi daga bacci yayi( Alhamdu lillahi lazhi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihin nushur).

Maida kallonshi yayi wajen da Ummi ke kwance, wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarce shi ganin Ummi zigidir babu komai a jikinta komai ya fito waje, towel d'in da ta kwanta da shi ya kama gabanshi saboda gigin bacci kuma ba tasan ma an yiba, wasu irin yawune ya dinga had'iya da k'yar ga wata irin fitinanniyar sha'awa da ta taso mashi lokaci d'aya ji yake kamar ya abka mata, saidai wata zuciyar na gargad'inshi akan hakan, rufe fuskarshi yayi da hannayenshi yana fadin" a'a Salman ka zama namiji mana, kar kayi haka karka zubar ma kanka mutunci mana" maida kallonshi yayi amma ina saida zuciyar shi ce ta fizge shi ya kai hannushi a k'irjinta ya shafa, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi a hankali yace" ya salam, Allah ka kare ni" zunbur Ummi ta mik'e tare da yayumo zanin rufa ta rufe jikinta tana kallonshi tace" miye haka kuma, kai da kanka, ashe haka kake bansani ba "?" basarwa yayi kamar ba shi ba ya tashi ya fita duk takaici ya ishe shi da kunya, sallah ya fara yi sannan yayi wanka ya shirya, yana fitowa dai-dai da fitowar Ummi da hijabinta ta idar da sallah, cike da raini tace" ina kwana" kallonta yayi yace" bara na duk'a saina gaishe ki ni" durk'usawa tayi ta saké gaishe shi amma bai amsa mata ba, mik'ewa tayi zata shiga cuisine yace

" ki had'a iya bakinki, ni yanzu zan tafi" cike da mamaki tace" ina kenan?" baiyi tsammanin tambayar daga gareta ba shiyasa yace" balaguro zanyi" cikin ladabi tace" balaguro zuwa ina kenan?" Cotonou " ya bata amsa baki bud'e ta kalleshi tace" Cotonou fa yaya Salman,to idan ka tafi ni da wa zan zauna a gidan?" Kallo ta yayi yace"kamar ya,mi zai cinye ki a gidan to?" kawai sai tasa kukan shagwab'a tace" wallahi ni ba zan yarda ba, haka kawai ka tafi ka barni ni kadai cikin gida kamar manya" abu kamar wasa Ummi ta dinga tsala kuka, amma rashin imani na Salman ya ki damuwa saida ya wuce yace" idan kin zauna ke kad'ai mugun abu ya jima bai cinye ki ba"sai kud'in daya fiddo ya jefa mata a k'irji ya wuce ya barta nan, da gudu ta fito k'ofar d'akin ta tsaya tace" kaga kazo ka d'auki kud'inka, bana so tsiyar me zanyi dasu, tunda dai kai bâ kada imani zalinci kawai ka iya mugu kawai" takalmanshi ya ciro ya jefo mata, da sauri ta shige d'akin tare da rufewa da key, d'aukar takalmanshi yayi yana fadin" zan dawo ai bacan zan zauna ba, sai kinsan kin fad'amin haka, mai kama da mage kawai marar kunya"yana fita Khamis yana jiranshi dama ya d'aukeshi suka wuce suna gaisawa, Ummi kam kuka kamar ranta zai fita.

```muje zuwa dai mutane na```
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

```wannan soyayya na yarda had'in allah ce, sai dai in ce allah ya bar k'auna😘```

```-My Meelat```
```-My Heenat```

```Ku na Musammam ne ku nada karamci sosai a gare ni.
```
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜_ 🤛

*Page*

4⃣5⃣-4⃣6⃣


Khamis ne yace" wai ni ban tambayeka ba da wa kabar mutuniyar ne a gida?"uhumm to ita da wa kake so na barota to, ko kaima kana nufin na samo mata wanda zai taya ta kwana kafin na dawo kamar yanda take fad'a?" gyad'a kai Khamis yayi yace" sosai kam, kai da a tunaninka zaka barta ita kad'ai ne ba tare da kowa ba?ai kaima kasan hakan ba zai yiwuba ka bar yarinyar mutane a gida ko sati ba tayi a gidanka ba kace zaka k'yaleta ita kad'ai, dan ma kasamu ta barka ka tafi" wata irin dariya Salman ya shek'e da ita kafin yace" lallai kam akwai mahaukata da dama a garin nan, kai yanzu kana tunanin wannan yarinyar zata iya hanani yin abinda naga dama? to bâ ita ba ko wacce ta fita ma bana jin ta isa bare kuma ita" haushi Khamis ya ji yace" kai kaga wallahi da gaske nake fad'a maka, bai dace ba ace ka barta ita kad'ai a wannan sabon gidan, kai kan kafa bak'one a gidan bare ita sannan babu wanda ta sani a unguwar kaga hakk'inka ne kareta da kula da ita, idan wani abu ya sameta mi zaka fad'ama iyayenmu?" shiru yayi yana tunani kafin yace" to malam Khamis yanzu fad'amin ya kake so ayi?" to yanzu dai kaga wannan tsohon mai ran k'arfe ya hanata zuwa wajensu bare ta koma can gida, haka kuma ya hana kowa zuwa wajenta bare a d'auko ko yara akai mata can kasanta ko da wasa da yara, kenan ni ina ganin in har zaka amince to yanzu idan na aje ka zanje sai na d'aukota na kaita can gidana sai su zauna tare da Jawahir nasan za tayi farin ciki da hakan." kallonshi Salman yayi yace" kana ganin hakan babu wata matsala?ni fa bana son abinda zai raba ni da dangina" kai ya girgiza yace" insha Allah babu abinda zai faru da yardar Ubangiji zan kula sosai" d'aga kafad'a yayi yace" OK ba damuwa ka d'aukotan kawai, amma kafin ka d'aukota ka biya ka siya mata yar k'aramar waya wacce zata dinga kunna tocila da dare idan an d'auke wuta, dan karta takura maku kuna tsaka da hutawa" dariya Khamis yayi yace" saboda ta kunna tocila za'a siya mata wayar? badan ka dinga kiranta kana jin halin da take ciki ba? kumafa karka manta kai ka amsar mata waya kuma babbar waya ka amsa amma sai kace a siyo mata yar k'arama, wato ka siyar da ta-ta kud'in kuma k'arfi ya cinye ko?" dariya kawai Salman ke yi tunda Khamis ya fara magana kafin yace" e mana na cinye dan na nuna ma duniya da kai da kaya duk mallakar wuya ne." gira Khamis ya had'e tare da d'agata sama yace" eyee,lallai mutumin nan, ai banyi tunanin zaka fara irin wannan tunanin akan Ummi ba kaga kuma idan kana jin irin haka a ranka to fa wata rana za muga yar k'anwar tamu da juna biyu" yana k'arashe maganar ya fashe da dariya yana kallon Salman, shi kuma photon Ummi ne ya dawo masa cikin 'kwa'kwalwa lokacin da ya ganta babu kaya a jikinta da irin sanyin da ya ji lokacin da ya tab'a k'irjinta lumshe ido kawai yayi ya jingina kansa a kujera yana murmushi, ina ma ace hakan zata sake faruwa ko da tab'awa ne yayi, Khamis ne ya katse shi yana fad'in" to malam kawo kud'in ko?" hararanshi yayi yace" kai gafara can dallah k'anwarka d'in dan zaka siya mata abu saina baka kud'i? to bâ zan bayar ba." dariya Khamis ya ci gaba da yi yace" kaji mutum kai, baka ji ance gwamnati ta hana aikin banza ba? ka kawo kud'i matarka ta samu waya ka dinga kiranta kuna gaisawa, ka k'i bada kud'i kuma kaje ka dawo ba tare da kayi magana da matarka ba." to sai me? na fad'a maka ina san jin muryarta ne, ni bata dameni ba" wani Kallo Khamis ya watsa mashi yace" malam manu kenan har yanzu baka san mace ba amma, daga ranar da zaka san wacece Ummi to fa a lokacin zaka fara damuwa da tunani a kanta." tsaki Salman yaja yace" kar Allah ya kawo ranar da zan santa ko, yarinyar da nake Addu'a naga tsorona a idonta sai gashi yanzu d'an zaman da mukayi na fara ganin wannan tsoron, haka kawai lokaci d'aya saina b'arar dashi,Allah karya nufeni da ganin ranar da zan tub'e kayana a gaban wannan k'azamar yarinyar harna kusanceta."murmushi Khamis yayi yace" banda fariya manu, kai yaro ne baka san tasirin mace a wajen namiji ba shiyasa, amma tunda Allah ya had'aku zama a inuwa d'aya to ina tabbatar maka zaka sani lokacin zai zo, s'il plaît a Dieu."

Tsaki Salman yayi yace" insha Allah haka ba zata faru ba" shiru su kayi babu wanda ya saké magana har ya aje shi gidan Bus Sonef su kayi ban kwana, kamar yanda tun jiya yayi ban kwana dà iyayensu suka masa Addu'a sannan ya juya, saïda ya tsaya ya siya mata waya tare da sabon puce( sim card) sannan ya wuce gidan.

Tunda Salman ya fita Ummi ta zauna saman kujera ta fara kuka, Sallamar Khamis ne da taji ya sata saurin goge hawayenta tana amsa sallamar, tunda ya shigo ya fahimci kuka take amma da yake mutum ne shi wanda bai san shiga rayuwar kowa dan haka koda suka gaisa yace" k'anwata ko dai dan ya tafi ya barki kike kuka?" kai ta girgiza ba tace komai ba dan haka shima yace" to kinga tashi ki had'o kayanki zan tafi da ke can gidana ki zauna tare da yar uwarki har lokacin da zai dawo" kai Ummi ta girgiza tace" a'a yaya Khamis ka barni anan idan yaji na tafi can bada izininshi ba zai min fad'a ko ma ya daké ni, kawai ka barni zan zauna ni kad'ai Allah zai kareni" tausayinta yaji ya kama shi sosai amma sai yace" haba hajia Zeinabou karki damu fa, shi yace nazo na d'aukeki" da sauri ta d'aga kai tace" da gaske yaya Khamis ? " k'warai Kuwa tashi ki had'o kayanki mu wuce" tashi tayi da gudu tana farin ciki Khamis kuma a zuciyar shi cewa yayi,lallai duniya ta kusan tashi wai yau Ummi ce take tsoron fad'an Salman ha'ki'ka yayi gaskiya da yace ya fara ganin tsoronshi
a idon Ummi kuma ga dukkan alama labarin Salman da Ummi ya kusa canzawa.

Tsaf ta had'o duk wani abun buk'atarta ta rufe gidan suka tafi bakinta har kunne.

Suna shiga gidan suka fashe da k'ara ita da Jawahir suna ta tsalle kamar yara tsabar farin ciki, Khamis dai fita yayi ya barsu bayan ya had'a mata wayar ta ya bud'a mata WhatsApp,haka suka wuni Ummi nata bawa Jawahir labari irin muguntar da Salman ke yi mata ita dai Dariya kawai take, tare su kayi girkin dare suka kammala suka shirya Suna zauna anan Jawahir ta bawa Ummi numbobin k'awayensu da nasu Nadia nan fa aka hau charting k'arshe ma d'aki ta shige tare da maradarta tana kurb'a tabar Jawahir tana jiran mijinta ya dawo.
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜_ 🤛

*Page*

4⃣7⃣-4⃣8⃣


Tunda Khamis ya dawo ya tambayi Jawahir ina Ummi, data fad'a masa tana d'aki wayar shi ya ciro ya turawa Salman numberta sannan ya shiga harkokin gabanshi.


Ummi hira kawai take da k'awayenta a groupe d'insu musamman RAYUWAR MÛ A YAU, tana jin dad'in hirar sosai dan duk ta k'aruwace a keyi, 23:30 ta wuce bak'uwar number ta shigo wayarta, dubawa tayi dan taga ko waye sak'one a rubuce kamar haka,

_"waya baki izinin bud'a WhatsApp, sannan mi kike har yanzu da kike en ligne?" take Ummi ta fahimci ko waye, amma tayi niyyar raina masa hankali dan haka ta maida masa ita ma tace" wanda ya baka izinin bud'awa a lokacin da ka bud'a, sannan abinda kake yi nima shi na keyi" bada jimawa ba ya maido mata yace" karki raina min wayo, ina hira ne da budurwata mai deb'emin kewa" dakewa tayi ta maida masa ita ma" kenan jirgi d'aya ya d'auko mu ni da kai, dan nima nayi kewar samari na ne shiyasa nake rage dare da su" wani irin takaici ne ya kama Salman dan yasan ta aika, maida mata yayi" ke bana san iskanci wallahi ki sauka ko kuma ranki ya b'ace" dariya Ummi tayi ta maida masa da" 😏😏😏😏😏😏" take ya maido mata yana fad'in" wa kike juyama bakin? wallahi ki kiyaye ni" dariya tayi tâ koshi sannan ta maida masa" kaga malam dan Allah nifa matar aure ce ka kemin mad'e, idan mijina ya sanka to zai kashe ka, dan haka sai anjima" harta koma cikin groupe ya aiko da wani sak'on dubawa tayi taga yace" har haka mijin naki ke sonki dama?" maida mashi tayi da" sosai kam, yana sona fiye da ransa, nice mahad'in rayuwarshi" dariya yayi yace" to ko zan iya ganin photonki da na mijin naki?"cewa tayi" mi zai hana, amma karka ce mijin yafi matar kyau idan ka gani" kafin ya aiko ta dunk'ule photo kusan talatin ta aika masa wanda Jawahir ta tura mata d'azu, bud'a photunan yayi ya fara kallo, sak'onta ne ya saké shigowa tace" idan ka fiddo ni a ciki zan maka kyauta" sai lokacin ya saké duba photunan da kyau, babu inda take ita kad'ai duk ita da su Jawahir ne sai kuma k'annanta su Islam da Mubbashir, inda ya ganta tare da su Jawahir da Khairat Kwance akan gado tana tsakiyar su tayi dariya sosai hak'oranta sun bayyana ga kumatunta sun lotsa kamar ka saka k'wandala kuma ta zauna daram, babu ko d'igon Kwalli a fuskarta amma tayi kyau, shi ya aika mata yace" wacce tafi zama bak'a a ciki to ke ce ita, kuma banga mijin naki ba?" dariya ta aika masa tace" ka canka dai-dai, dan haka ka zo da kumatunka ka karb'i cadeaux d'inka, banda photon mijina" _tambayarta yayi" ban gane kumatuna ba? miyasa baki da photon mijinki?" maida mashi tayi" kaga nifa ina da abinyi , dole ne saina samu photonshi?nida nake ganinshi kullum a cikin zuciyata, dan haka sai anjima_ " _tana aika masa ta sauka ta kwanta sai bacci_ .


Tunda Ummi tayi sallah ta koma ta kwanta sabon bacci, dan rabon da tayi baccin safe harta manta, lokacin da Khamis zai fita yana break ya tambayi Jawahir Ummi, data fad'a masa tana bacci dariya yayi yace" to wannan baccin haka take yin shi ko gidan malam manu?inko hakane akwai dangwarma dan shi nasan ba yada da'bi'ar siyan abincin waje, kuma yana fita da wuri to kenan ya yake oho"Jawahir ce tace" ai in fad'a maka yaya Salman yanzu ya fara gyara mata zama, dan jiya zuwanta nasha labari , nidai har cikina ma ya fara ciwo tsabar dariya" da gaske kike?" ya tambayeta, " e mana, amma gaskiya yaya Salman baya kyautawa dan inda kaga jikinta duk duka ne,wallahi sai taban tausayi kuma da naga jikinta a farfashe" wani iska ya hurar yace" ni nasan dama sai haka ta faru, dan Ummi ba taji, Salman kuma ba yada hak'uri ga zuciya" to mijina me zai hana ka masa magana akan dukanta, kaga fa hakan babu kyau tunda yanzu tana yin abinda ya sata" ajiyar zuciya ya sauke yace" zan masa, amma sai ya dawo daga tafiya, dan kinsan halin shi murd'add'an mutum ne" haka su kaci gaba da tattaunawa harya gama break ya fita.


Jawahir ce zaune a falo tana charting, Salman ta gani en ligne dan haka ta gaishe shi ya amsa, tambayar ta yayi ina Ummi tace tana bacci, cewa yayi taje ta tasheta, haka taje tasa Ummi gaba tana tadi amma tak'i tashi, dole ta fad'a masa tak'i tashi, kiranta yayi appel vidéo yace ta bata wayar, da k'yar Ummi ta bud'a idonta ta kalli wayar sai magagin bacci take da hamma,

"ke dallah tashi malama, wato an samu dama ko?" juya baki tayi tace" dole kam na dama, tunda nazo gidan yanci, ba kamar wancen kurkukunba" tsaki yayi yace" yanzu ai kin fad'i komai, tunda kinga bana kusa dake" d'an karamin tsani tayi tace" wai ni malam miye na sawa a tasheni ina bacci na dan Allah? kuma kai bâ wani abu mai anfani zaka fad'amin ba, ko dai harka fara kewata ne tun yanzu?"cike da takaici yace" waye zaiyi kewar ki? ni? Allah ya kiyaye" a cikin muryar baccinta tace" in dai hakane to kashe wayar" tana gama fad'a yako kashe wayar, tsaki tayi ta koma ta kwanta.


k'arfe 10:15 tana ta baccinta saiko Ihu da kwaramniya anata jinjigarta ana fadin" ki tashi ki tashi ke" cikin Farin ciki ta bud'a ido dan ta d'auki muryar yan uwan nata, Kallonsu tayi tace" Khairat daga ina kuke yanzu?" kinga kedai taso muje falo" hannunata taja suka wuce da kayan bacci a jikinta riga da wando k'anana,falo suka fito, tana fad'in" wai ku kuma miya kawoku nan ne ku dukan ku?" Nadia ce da duk yayi wani yaushi tace" dama mun san yaya Salman zaiyi tafiya, shine yaya Khamis yace kina nan , shiyasa muka zo dan munyi kewarki" gyara zamanta yayi tace" amma kuma su yaya suka kawo ku?" cikin zumud'i Khairat tace" e mana, kuma sunce ma zasu dunga kawo mu har lokacin da zaki koma" aifa nan hira ta b'arke Ummi ko wanka ta kasa yi saboda dad'in hirar da suke, haka lokacin ya tafi har azahar kafin Ummi ta kalli Jawahir tace"uwar gidan Khamis ba kishan furarki saida nono" dariya tayi tace" kai yar uwa duk wannan kirari haka, ai saiki fasamin kaina" ita ma dariya tayi tace" to ai girman ki ne, kinga nifa yunwa nake ji, me kika dafa mana ne?" hararan ta tayi tace" saidai kije ki dafa, dan wanda na dafa munci ni da Mijina" baki bud'e Ummi tace" lallai ma yarinya, kina nufin ina bak'uwarki amma zanje na dafa abinci da kaina, kamar a gidan wancen mugun, ai kam ba zata sab'u ba"dariya Jawahir tayi ta mik'e tsaye tace" to uwar gidan yaya manu mi kike so in dafa maki?" k'ara shigewa tayi cikin Kujera tace" ki kawo min Tea da bred,sai ki soya kwai yaji albassa sosai,amma karki samun arom ( d'and'ano),gishiri kawai ya isa." wucewa tayi tana murmushi ta shiga cuisine, Khairat kuma cewa tayi" yayi dai hajia Abu, kenan haka kike bawa Yayana umarni ko a gidan?" tab'e baki tayi tace" ke wannan yayan naki? wanda ko murmushi ba yayi bare dariya ai shi kibar shi inda kika ganshi kawai"

Tana gamawa ta kawo mata, k'asa ta zauna tana ci suna hira harta kammala, haka suka wuni a gidan cikin farin ciki, tare sukayi girkin rana dana dare, suna idawa Jawahir ta shiga wanka ta cab'a kwalliya wa mijinta, tana fitowa ta d'auko blander tasa jik'akk'en dabino data jik'a da ranke da kanunfari a ciki ta markad'a, ta koma tasa kankana ta markad'a ta tace ruwan, sannan tasa maltina a ciki da madara peak da k'ank'ara (glasse).

Ummi data saki baki tana Kallonta tace" Jawahir kema harkin fara wannan tsirfa tsirfen na bawa kai wahala ko?"dariya tayi tace" wannan aiba na bawa kai wahala bane, wannan har lafiya zai k'ara maki, ko ba kiga da kanana a ciki ba? ga madara sannan ga dabino da kanunfari"mik'a mata tayi tace" sha kiji kema" waro ido tayi waje tace" ni, rufamin asiri kinji, wannan ai saiku masu maza" hararanta Khairat tayi tace" bana san iskanci, ke kuma fa ina kika kai mijin naki, nasan Yayana fa wallahi namiji ne na gaske, kisha dan Allah kiji akwai dad'i fa" ke wannan mutumin babu abinda zai shiga tsakaninmu, dan na tsaneshi babu ta yanda zan bashi kaina wallahi" Hafsat ce ta tab'e baki tayi tace" kinga karb'i in kinsha, in kuma ba zaki sha ba ta bamu musha" Kallon mamaki ta bita dashi tace" oo Hafsat kema wai har kinsan anfanin wannan, keda mijin naki nawa kuke?" dariya suka saka mata kafin Nadia tace" ke namiji fa namiji wallahi baya kad'an" kau da kai Ummi tayi tace" ni dai kam na rainashi gaskiya" Hafsat ce tace" lallai baki san shi bane shiyasa, amma wallahi ina jin abinda yake ko mijinki baya yinshi" Jawahir ce tace" ku baku san dalilinta na fad'ar haka ba, yaya Salman dai duk ya girme ma mazajen mû, a shekaru dama girman jiki, kinga kenan ita kad'ai tasan azabar da take ji, amma in za'a fad'i gaskiya Hafsat kinsan babu ta yanda za'a had'a yaya manu da yaya Deen" ido ta fiddo tace" ke rufamin asiri, ina ni ina wannan ai sai ya kasheni" dariya suka saka mata, Jawahir kuma ta saké mik'o mata, sannan ta karb'a ta kifa kai, bata sauke ba saida Jawahir tace" ke bani nan malama, sai kin shanye?" dago kai tayi tace"kai gaskiya da dad'i" dariya su kayi Jawahir tace" dad'i a baka, dad'i a k'asa ba" tab'e baki Ummi tayi tace "humm, kina nufin wannan dad'in a baki haka yake ko a wajan mai gida?" shigowar Khamis ne yasa su shiru, da sauri Jawahir ta mik'e ta tare shi,nan ya fad'a masu su tashi mazajen su na jiransu, haka kowace ta kama gabanta su naji kamar kar su rabu.

Ummi na ganin hankalin Jawahir ya koma wajen mijinta ta d'aga kai ta shanye sauran, cikin sand'a ta mik'e ta shige d'akinta dan tasan akwai tashin hankali inta fahimci ta shanye.



~Kuja muje~
05/03/2019 à 17:28 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

*Page*


4⃣9⃣-5⃣0⃣



Da safe Ummi da Jawahir suna zaune tana since mata kai suna hira, Abba ta kira bayan sun gaisa take fad'awa Abba tana neman gafara akan abinda ya faru, budar bakin Abba yace,

"Haba Mamana babu komai fa ni nasan ba laifinki bane, dan haka ki kwantar da hankalinki kinji."

"Abba na gode amma ku nema min gafarar La Mama itama tana fushi dani?"

Cewar Abba "a'a ko kad'an mahaifiyarki ma bata fushi dake"

"To Abba na gode sosai ku gaishe min da kowa da kowa"

"Zasu ji insha Allah, nasan mijinki ya tafi yanzu to ke kad'ai ke zama a gidan?"

Dariya tayi tace "a'a Abba ina gidan yaya Khamis, amma fa Abba karku bari Alhaji yaji."

Dariya Abba ma yayi yace "karki damu ba zai ji ba"

Haka su kayi sallama, Ummi da Jawahir haka suka wuni suna shan hirarsu suna aiki har dare Khamis ya shigo yace masu Nadia bata da lafiya.

Bud'ar bakin Ummi cewa tayi "haba ni nasan sai anyi haka dama, dan tunda naga Nadia jiya nasan akwai wani abu a cikin cikin nan nata data aje."

Jawahir ce tace "ke kuma ina ruwanki da cikinta to?"

"Haba wane ina ruwana dan Allah kina ganin yarinya ta d'auki ciki duka ko sati uku ba

Please Login or Register in order to submit comment