Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kula da yaya yanda ya dace."

"Yawwa 'yar albarka nasan zaki iya in dai kinsa kanki, Allah ya maki albarka." tana fad'a ta mik'e ta shiga d'aki, Ummi kuma ta ci gaba da cin abincinta.

Duk tayi wani shiru da ita jikinta babu k'wari, haka su Islam suka shirya suka tafi wajen lessons yayi saura ita kad'ai zaune a falon, har saida tayi sallah isha sannan La Mama ta fito cikin kwalliya mai birgewa wanda ta dace da dattijuwa mai kamala, Ummi ba tayi mamaki dan ta san mahaifiyarta dama ko kad'an bata yarda Abbansu yaga wani abu marar kyau daga jikinta ba, kamar yanda bata gamsu mijinta ya shak'i wani abu da ba k'amshi ba daga jikinta ko gidanta.

Abba na shigowa Ummi da La Mama kusan a tare suka mike suna nufeshi da fara'ar su suna mashi sannu da zuwa, kan Ummi ya dafa yana fad'in "Mamana dama baki tafi gidanki ba?"

Kanta k'asa cike da kunya tace "Eh, Abba ban tafi ba amma yanzu zasu zo mu tafi."

Cike da jin dad'in yanda yaji Ummi ta girmama mijinta yace "ah to yayi kyau ma hakan."

Har suka zauna saman kujera Abba yana fad'in "Mamana banji dad'in abinda ki kayi ba dazu, amma kuma da kika bada hak'uri sai naji dad'i, kuma kinga Abbanki (Abban Salman) ma cewa yayi yaji dad'i dan baiga laifinki ba."

K'ara sunkuyar da kanta tayi tace "kuyi hak'uri Abba, ba zan sake ba daga yau."

"Yawwa yarinyar kirki, Allah ya maki albarka ya k'ara maki hak'urin zama da mutane a duk in da kika samu kanki."

Cike da jin dad'in addu'ar mahaifin nata tace "ameen ameen Abba nagode."

Sai lokacin ya kalli La Mama suna had'a ido ta galla masa wata harara ta kau da kanta gefe, murmushi Abba yayi dan yasa akwai rikici, cike da zolaya Abba yace "Mamana kinga ganinki yasa ban ko kula mamata ta ba ko, gashi yanzu kinsa ta fara hushi."

Dariya Ummi tayi ta kalli La Mama data rumgume hannayenta a k'irji wai ita a dole hushi take, kallon Abba tayi tace "Abba ai nasan yanzu zaku shirya in dai kune."

Tana fad'a ta tashi ta koma d'akinta, matsowa Abba yayi ya dafa kafad'ar La Mama yace "haba uwar gidana meya faru ne haka ake min wannan kumburin? kofa murmushin yau ban gani ba."

Ture hannunshi La Mama tayi ta kalleshi tace "au, ko murmushin kenan ma baku gani ba? duk wanda na maku tun shigowarku, dama ai na sani in dai kuna tare da Ummi to baku ganin kowa."

Murmushi yayi yace "haba wane ni na kasa ganinki dan tana tare dani, kawai dai shak'uwace ta d'a da uwa."

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi, jin ba tayi magana yasa yace "dan Allah to kimin murmushin nan na gani mai sanyaya min zuciya ko naji k'arfin jikina."

Wani hamshak'in murmushi La Mama ta saki tare da cewa "in dai wannan ne zaisa kaji k'arfin jikinka, to ka d'auka kullum zaka kasance cikin k'uruciya."

Hannunta ya kama yana kallon fuskarta yace "ko rantsuwa nayi nasan ba zanyi kaffara ba kan cewa nafi kowa sa'ar mata a duniyar nan, a wajen wasu AUREN HA'DI masifa ne kuma bala'i, amma a wajena wallahi yafi komai dad'i, da ace zab'in zuciyata nabi ban san ya zata zama a gareni ba, watak'ila ta zama ita ce tension d'inta da wannan nake k'ara godewa Allah daya had'ani dake."

Murmushi tayi tace "nima haka ina godiya ga ubangiji daya bani ku a matsayin abokin rayuwa kuma uban 'ya'yana, dan haka yanzu ku tashi muje kuyi wanka kuzo kuci abinci."

Sun mik'e da nufin shiga d'aki Salman ya shigo da sallama, tsaye sukayi har ya k'araso suka gaisa kafin Abba yace "to inaga abar wankan nan har muci abinci koko?"

La Mama cewa tayi "ko baku fad'a ba nasan ba zaku rabu ba in har ba dare ku kaga yayi ba."

Dariya sukayi tare suka d'unguma izuwa dinning, Salman da kanshi ya zuba ma Abba abincin shima ya zuba suka fara ci suna hira ta kasuwanci La Mama na jinsu ita dai, dan dama tana zaune ne saboda ya zamar mata jiki ta zaune kusa da mijinta musamman lokacin da yake cin abinci.

A hankali La Mama ta kalli Salman da hankalinshi ya tafi kan hirar da suke tace "d'ana"

Cike da kulawa ya kalli La Mama yace "na'am"

"Dama ina so naji komai lafiya a gidan naku babu wata matsala?"

Murmushi yayi yace "lafiya k'alau La Mama babu komai wallahi, muna zaune lafiya."

Cikin rashin yarda La Mama ta kalleshi tace "nasan ba zaka fad'amin ba dama saboda baka so na d'auki mataki."

"Wallahi gaskiya na fad'a La Mama, ai yanzu Ummi ta kimtsu kamar ba ita ba idan tayi wani abu."

Mik'ewa tayi tsaye tace "bari na kirata ku wuce, dan dare nayi."


Tana shiga Ummi ta gani kwance akan gado ta lak'ume kamar mai bacci, daddab'ata tayi tana fad'in "tashi ke ku tafi mijinki ya zo."

Idonta ta bud'e lokacin da gabanta ya shiga fad'uwa saboda firgici, ganin bata tashi ba yasa La Mama d'aga murya tace "dan Allah ki tashi ki wuce mijinki na jiranki ko."

Tashi tayi zaune tana kallon La Mama data ci gaba da cewa "nifa bana san wannan sanyin jikin, komai ki dinga saka kasala a ciki ta yaya zaki birge miji a haka."

Wani irin d'aci ne Ummi take ji dan haka kawai ta rik'e hannun La Mama ta fashe da kuka, jikin La Mama ne yayi sanyi dan haka ta zauna kusanta ta dafata tana tambayarta "Ummi lafiya me yasa kike kuka?"

Bata bata amsa ba shi yasa ta sake fad'in "ki fad'a min mana Ummi, ko wani abu Salman d'in ke maki a gidan?"

Nan ma shiru "haba Ummi ya zaki d'aga min hankali, ko ba kya san zuwan gidan naki ne?"

Kai ta d'aga alamar Eh, dan haka La Mama tace "to me yasa, wani abu mijin naki yake maki ne a gidan?"

Bata ce komai ba dan haka La Mama tace "kinga kiyi hak'uri ki tashi ki koma gidanki, can d'in yafi maki nan daraja a can zaki fi samun sukuni da farin ciki fiye da nan, abu d'aya zan fad'a maki shine, ki zama jaruma kuma gwarzuwa sannan ki zama mai jajircewa akan duk wani abu daya danganci mijinki, sannan ki d'ora da hak'uri dan sai dashi zama keyin dad'i."

"Ummi ki dage sosai wajen farantawa mijinki rai, wallahi in ki kayi haka zaki ci riba a duniya sannan kici riba a lahira, Ummi ki zama mai biyayya ga mijinki sannan ki kiyaye ganinshi da jinshi da ma iskar shak'arshi, ma'ana karki bari mijinki yaga k'azanta a jikinki ko gidanki, sannan karki bari mijinki yaji gurb'atanciyar kalma ko magana marar dad'i daga bakinki, sannan ki kula sosai karki kuskura ki bari mijinki ya shak'i k'amshi a jikinki ko a cikin d'akinki ko ban d'akinki ke dama duk wani sassa na gidanki wanda ba kamshi mai dad'i ba."

Kai ta d'aga tace "nagode La Mama, Allah ya bar mana ke."

Suna fitowa zaune suka samesu kai kace abokaine, hira suke sosai har da tab'a hannu suke idan tayi dad'i, cikin ladabi Ummi tace ma Salman "sannu da zuwa yaya."

Cikin dariya yace "yawwa sannu, ya gidan?"

Cikin shagwab'a tace "ni gidan ma nake so na kwana."

Kallonta yayi yace "to ki kwanta mana idan kina so, nima saina koma gidanmu na kwana."

Take murmushi ya bayyana a fuskarta tana fad'in "da gaske yaya ka yarda na kwana a nan?"

Tsakin da La Mama tayi tare da jefarta da wata harara yasa tace "muje kawai na fasa."

Haka suka baro gidan dukansu suna ji kamar karsu rabu da iyayen nasu, saida Salman ya tsaya a hanya ya siya masu fruits da chocolat wa Ummi da kuma madararta sannan suka wuce gida.


Suna zuwa suka tub'e suka shiga wanka tare duk da Ummi a d'an tsorace take, amma tayi niyyar zama jajirtanciya kuma jaruma dan gane da duk wani abu daya shafi mijinta domin ta birgeshi.


Cikin wata kyakyawar rigar bacci Ummi ta shirya sabuwa colour ruwan powder ta matse k'irjinta amma gaba d'aya daga k'irjinta har zuwa in da rigar ta tsaya bakin gwiwa duk a bud'e take, mulke jikinta tayi da turare tare da shek'a kwalliya mai ban sha'awa, d'akin Salman ta shigo in da ta sameshi tsaye gaban madubi yana duba wayarshi.

Bai kula da zuwanta ba saida yaji ta sakaya hannayenta ta tsakiyar nasa hannayen ta rumgumeshi ta baya, lumshe ido yayi tare da shak'ar k'amshinta mai dad'i, sumbatar bayansa tayi har saida jan-bakinta ya fito hakan yasa tayi dariya tace "ga shaidar bakina nan a bayanku karku gogeshi ko wurin wanka."

Janyota yayi ta gabanshi ya rumgumeta sosai yana fad'in "Ummi ina sonki, ina son kasancewa tare da ke har abada, ina mamakin yanda nake k'ara jin k'aunarki a zuciyata."

D'agowa tayi daga jikinshi ta fara shafar bud'add'an k'irjinshi dako riga babu har ta kai kan cibiyarshi, a firgice ta kalleshi tace "kun manta baku fad'a min komai game da ciwon nan ba?"

Ajiyar zuciya ya sauke tare da kamo hannunta ya zauna kan gado ita kuma ya d'orata akan cinyoyinshi yana shafar duk wata gab'a ta jikinta ya fara mata bayani kamar haka.

"Ummi shekara d'aya data wuce baya, wani abu ya faru dani wanda ko a mafarki banyi tunanin faruwarshi ba, Ummi nasan kina da ilimi kin kuma san yanda Allah yake halittar bayinshi yanda yaso, dan haka babu buk'atar saina fad'a maki raba raben 'yan adam."

"Abun ya faru ne a lokacin da muka tafi cotonou ni da Khamis, to a wannan lokacin ne wani ciwon mara da nake fama dashi tsawon lokaci ya takura min sosai wanda takai ta kawo idan ya taso min ko kaina bana iya ganewa saboda azabar ciwon, lokacin ne Khamis ya addabeni akan dole muje asibiti dan a gane meke damuna."

"Bayan munje ne aka fad'a min abinda naji kunyar d'an uwana sannan naji kamar k'asa ta stage na shiga, Ummi kinsan me docteur d'in yace?"

Kai ta girgiza dan gabanta fad'uwa kawai yake yi, ci gaba yayi da fad'a mata "Ummi cewa yayi dole amin opération (thearther) wai saboda sperm (maniyi) ya tarar min a mara dole a cireshi, sannan na hanzarta yin aure da wuri kafin na illata kaina tare da bani shawara akan na daina cin kayan marmari duk saboda lafiya ta."

"Khamis yasha fama sosai dani kafin na amince na yarda amin aikin amma a can garin, dan ba zan iya kallon dangina alhalin ina da wannan matsalar ina jin kunya sosai, haka aka min aikin cikin nasara aka kammala, bamu samu wata matsala da gida ba saboda a kullum muna waya dasu muna fad'a masu muna cikin k'oshin lafiya hakan yasa basu d'aga hankalinsu ba har muka kwashe wata d'aya a can kafin muka dawo gida, amma duk da haka babu wanda muka fad'a ma munja bakinmu munyi shiru."

"A lokacin kuma nayi niyyar yin aure, sai dai a ganina babu wata yarinyar da zata iya d'aukata a lokacin dan ni nasan kaina nasan zanyi takura da jaraba ga iyalina, duk a cikin yaran dake akwai a lokacin babu wacce take da shekara shabiyar a duniya, ke kad'ai ce keda sha shida a lokacin amma kuma saboda abinda ke tsakaninmu yasa a waccen lokacin nake ji gwara na auri mai zaman kanta dana aureki."

"Dole na k'ara hak'uri na ci gaba da shan maganin da aka bani har lokacin da wata tafiyar ta kamani, bayan tafiyata kuma aka saka auren su Khamis wanda banji dad'i ba da babu ni a ciki, ya rage yan kwanaki kuma na dawo a lokacin naga Nuseiba sai naji nutsuwarta ta birgeni sai nayi tunanin neman aurenta idan an gama bikinsu Khamis duk da dai bai zama lallai a bani aurenta ba dole sai wanda Alhaji ya zab'a min."

Ajiyar zuciya yayi tare da sumbatar kumatunta yace "ashe kana naka Allah yana nasa, ashe ni Salman nine zan zama mijin Ummi, a ranar da aka d'aura aurena dake naji kamar na sake ki a lokacin, amma saina hak'ura saboda bana so na zama na farko da zai kafa tarihi na saki a familyn Alhaji, bayan tarewarki kuma naso na mayar dake gida sannan na fad'a masu ba zamu iya zama a matsayin ma'aurata ba, amma kuma sai tunanin La Mama da Abba ya hanani, bayan kuma wani lokaci saina fara jin wani abu a tare dake da ban tab'a jinshi a game da wata 'ya mace ba."

"Yau, yau gani gaki mun zama kamar wad'anda aka haifa suna son junansu, Ummi Allah ya bar min ke, ina kuma fatan zaki iya hak'uri da juriya dani."

Cikin kukan shagwab'a ta rumgumeshi tana fad'in "Allah sarki mijina na kaina, ashe kasha wahala."

Murmushi yayi yace "sosai kam, dan idan ciwon nan ya taso min wallahi kamar zan mutu."

Kallonshi tayi tace "yayana insha Allah na maka alk'awarin hak'uri da kuma juriya a duk yanda na sameka, kuma zan zama mai amsa kiranka a duk lokacin daka kirani ba zan tab'a gajiyawa ba bare kuma k'orafi, zan d'auke hankalinka daga wajen matan banza dan na taya ka kare mutuncin addininka dama naka da nawa da namu baki d'aya, sannan na godewa Allah da yasa har tsawon wannan lokacin baka tab'a neman sauk'i ko biyan buk'atarka ta hanyar haram ba."

Cike da jin dad'in kalamanta ya rumgumeta suka fad'a kan gadon, nanfa suka fara bayyana wa junansu tsantsar k'auna da soyayya kamar ba gobe, Ummi ta darje ta cire kunya ta farantawa mai gidanta ta hanyoyi da dama wanda ta sani a matsayinta na 'yar zamani, Salman yayi ihu yayi kuka yayi dariya yayi....kai sauran ma basu fad'uwa.🤣


_Daga wannan lokaci komai ya sauya zama sai farin ciki kawai a gidan ma'auranta._💋😍😍
25/03/2019 à 16:14 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

_WANNAN PAGE *SADAUKARWA* CE GA *RAHEENAT* MY HEENAT DA KUMA AUNTYN MU *AISHA UMMA* TAKU CE KUYI YANDA KUKE SO DA ITA. INA SONKU 😍_



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

*Page*

9⃣5⃣-9⃣6⃣


Haka rayuwa ta dinga tafiya ma Salman da Ummi cikin farin ciki da k'aunar juna, sun dunk'ule sun zama d'aya yayin da suka zama abokan juna suna hira da kuma shawartar junansu akan duk wani abinda ya shafesu.


Lokaci gudu yake yayin da kowace awa ke wucewa cikin gaggawa, kwana kuma tamkar k'yabta idone a lokacin kuma kwanaki ke taruwa suna zama shakara, a haka kuma har aka fara k'idaya shekaru.

*BAYAN SHEKARA HUD'U*


Abubuwa sun faru da dama a cikin shekarun nan, Ummi ta kammala karatunta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tare da taimakon mijinta d'aya tilo kuma gwarzonta, wato Salman.

Tun kafin Ummi ta kammala karatunta Salman ya mayar da ita 'yar kasuwa ta hanyar siyo mata takalma da jakunkunan mata tana siyarwa, duk abinda Allah yasa ma albarka to tabbas akwai nasara da ci gaba a ciki, tun ana kawo mata guda hamsin har aka fara kawo mata guda d'ari har d'ari da hamsin daga nan kuma sai ya fara kawo mata less, atamfofi, material, da boyel, da mayafai, had'e da takalma da jakunkuna.


Kasuwanci na tafiya yanda ya kamata saboda jajircewar Ummi akan harkarta, ko kad'an babu wanda ya isa yama Ummi wasa da al'amarin kud'inta, tofa za kaga tijara tana da sauk'in kai wajen mu'amula amma idan ka fara mata wasa da hankali wajen biyan kud'i to ba zaka ji da dad'i ba, lokuta da dama Salman yakan sha dariya idan yaji tana waya tana fad'a akan k'in biyan kud'i, wani lokaci kuma yakan sa ta d'aga ma wata k'afa musamman idan yaga mai shirin biya ce, duk lokacin da zata tafi karb'ar kud'i da kanta to Salman ne ke kaita in dai har yana gari, in kuma basuyi tafiya tare ba saboda karatu to dama ya bata izinin zuwa ko ina in dai akan maganar data shafi kasuwancinta ne akan babur d'inta daya siya mata.


Yanzu dai haka Ummi ta zama gwaska a kasuwancinta, tana yinshi yana kuma tafiyar mata yanda take so, yanzu haka burinta d'aya take so ta cimma wanda ta shawarci Salman ya kuma girmama tunaninta.

Salman kanshi yanzu duk wani abu da zaiyi mai mahimmanci to saiya shawarci Ummi akai, akwai lokacin da wani mutum ya bashi fili a maimakon kud'in da yake biyarsa, suna zaune da Ummi ya kira Khamis yana fad'a mashi cewa bai san yanda zaiyi da filin ba, dan haka kawai ya samo masa mai siya ya sayar dashi, Ummi na jin haka tayi shiru saida suka kammala hira ya kashe waya sannan ta gyara zama tana kallonshi cikin nutsuwa tace,

"Mon sweet, saina ji kamar kuna magana akan zaku siyar da filin ko?"

"Eh, ina so in siyar dashi, dama na karb'a ne saboda in ban karb'a ba to bai zama lallai kud'in su fito ba."

"Amma da ba zaku damu ba da nace wani abu?"

Murmushi yayi yace "damuwa kuma, tame kenan? fad'i kawai ina jinki."

"Sai nake ganin fili kadarace bai kamata ku siyar ba, wanda ya baku shi ya baku ne saboda rashin sanin mahimmancinshi da kuma rasa yanda zaiyi, shi yasa nake ganin me zai hana ku tayar da gini a wajen tunda kunce filin yana cikin mutane ne akan titi, kunga kenan zai iya yin amfani."

"To ke yanzu me kike ganin ya kamata ayi a wajen idan an gineshi?"

"Zaku iya tayar da shago a wajen, ko dai ku dinga zuba kayan da kuke kawowa, ko kuma ku mayar dashi wata babbar super market in har kuna ganin aljihunku yana da nauyi zaku iya yi, amma fa wannan tunanina ne."

Wani kallo ya bita dashi ya jima yana kallonta, hakan yasa ta tsargu dan bata san me kallon yake nufi ba, fad'awa tayi jikinshi tana fad'in "kuyi hak'uri dan Allah idan na fad'i wani abu ba daidai ba, shawara ce kawai."

Rumgumeta yayi sosai a jikinshi yace "Ummi na kin had'u sosai gashi kin bani shawara akan abinda banyi tunaninshi ba, nagode sosai kuma insha Allah zanyi yanda kika ce."


Daga wannan lokaci Salman ya zama komai zaiyi ya kan shawarceta, idan shawarar ta masa ya d'auka, idan akasin hakane kuma zaiyi tunani akai, wasu lokuta ma idan ta baya shawara akan wani abu ya kan fad'awa Abbanshi ko Abban Ummi, amma sai ayi katari sun bashi shawarar data bashi, wannan ne ya k'ara karfafa masa gwiwa akan shawartar ta, gashi kuma duk abinda suka tattauna babu mai ji koda mahaifiyarta ce.

Bayan wani d'an lokaci ya gine filin kamar yanda tace, yayin da ya mayar dashi had'add'iya kuma matsakaiciyar mall, ya bawa Ummi zab'in sunan daza a saka a wajen, bud'ar bakinta cewa tayi "asa US super market."

Dariya yayi yace "US kuma kamar wata turai?"

Cikin salon yarinta tayi maganar "Eh mana, U yana nufin Ummi, S yana nufin Salman."

Sai lokacin ya fahimceta dan haka aka lak'abawa wajen US super market, _to dai zanje na siyowa fans d'ina chocolat acan😉_

Salman bai gushe ba saida ya sake tambayarta yaran da za'a saka a wajen dan tsaro, shawarar da Ummi ta bashi baiyi tsammaninta ba, bai kuma tsinke da al'amarin ba har saida ya bincika ya samo matasa daga cikin 'yan uwa wanda ba suda abinyi ya d'orasu a wajen, irin farin ciki da godiya tare da sa albarkar da iyayensu suka dinga saka masa yaji dad'i sosai, hakan yasa ya k'ara girmama duk wani tunani na Ummi, yanzu haka duk wani lissafi da zaiyi a gida to tare sukeyi, wani lokaci da gangan yake yin kuskure a take Ummi zata fad'a masa ba haka bane.

_MATA SUNA DA ABIN MAMAKI, WALLAHI WATA SHAWARAR IDAN MACE TA BAKA ITA ZA KAYI MAMAKI, AMMA MAZANMU BASU SON SHAWARTARMU AKAN KOMAI SABODA SUNA MANA D'AUKAR MASU K'ARAMAR K'WAK'WALWA._😏 Hum.


Duk shekarun nan da aka d'auka ko sau d'aya Ummi bata tab'a koda b'atan wata ba, saboda yanda Salman ke kula da ita da kuma farin cikin da suke ciki yasa ko kad'an Ummi bata damu da rashin samun cikinta ba, da farko ta fara damuwa a duk lokacin da suka had'u wajen wata sabga ko réunion d'in gidan Alhaji idan suka had'u da sauran 'yan uwanta kuma abokan aurenta su Jawahir, to tabbas ta kanji babu dad'i tana ji ina ma itama ta samu nata, hakan yasa duk ranar da akayi wata sagba Salman yana fahimtar damuwa a tare da ita, daga wannan lokaci ya k'ara zage damtse wajen ganin ya sakata farin ciki, yanzu kam koda tana damuwa to ba kullum ba, dan harkokinta ma sun isheta suna kau da hankalinta daga duk wani abu da zai sata tunani marar kyau.

Duk da abin na cikin ranta amma bata yarda ta nuna damuwarta a fili ba, musamman a gaban Salman dan kowane lokaci suna tare, dan tunda ta kammala karatunta to ya daina tafiya shi kad'ai sai dai su tafi tare, dan ko lokacin tana makaranta ko hutu akayi to tare suke tafiya baya yarda ya barta saboda sabo da sukayi da junansu.


A wannan lokacin kuma Jawahir da Khairat suna da 'ya'ya bibbiyu da kuma tsohon ciki wato na uku, Hafsat tana da d'iya uku sai Nadiya dake da biyu, cikin hakane kuma mijin Khairat yaya Noura da mijin Jawahir yaya Khamis suka k'ara aure na biyu, mijin Hafsat ma haka wato yaya Shamsu yana nan yana shirin k'ara aure.

A lokacin auren ansha badak'ala sosai, amma dama duk abinda Allah ya hukunta babu wani mahaluki daya isa ya dakatar face Ubangiji, duk da dai Khamis ba zab'inshi bace domin kuwa Mamarshi ce ta zab'a mashi yarinyar d'iyar k'anwarta ce, hak'uri kawai Jawahir tayi tare da kau da kanta daga duk wani abu da zai sata bak'in ciki, lokacin kuma Khairat ta kasa hak'uri da b'oye kishinta har saida ta baro gidan mijinta tayi yaji, amma tana zuwa ta samu Salman a gidan hakan yasa ya fafarota da kanshi ya mayar da ita gidan mijinta tare da mata kashedi akan kar ta sake maimaita wannan kuskuren.

Lokacin hankalin Ummi ya tashi sosai saboda a tunaninta ai Salman da Khamis kullum suna tare, dan haka in dai har Khamis zai k'ara aure to Salman ma dole zai k'ara wataran, musamman ma ita da bata haihuwa, hakan da Salman ya fahimta ne yasa ya fara kwantar mata da hankali ta hanyar sake kusanci da ita, kuma hakan yayi amfani saboda ta shiga farin ciki sosai.


Daf da bikin Khamis Ummi da La Mama da Sa'ada da Islam suka tafi AGADEZ wajen bikin d'iyar aunty Fateema k'anwar La Mama, sun tafi da niyyar yin sati biyu dan suga 'yan uwa saboda jimawa da sukayi basu je ba, a ranar da suka je Inna ta kalli Ummi tace,

"Ummi kenan, gashi yanzu an girma hankali kuma yazo maki?"

Dariya tayi tace "Inna dama ai ina da hankali, girman daine ya k'ara zuwa yanzu."

Murmushi Inna tayi tace "humm, haka kika ce dai, ya mai gidan naki babu wata matsala dai ko?"

"A'a Inna babu matsalar komai, lafiya k'alau muke."

"Ai koda matsalar ma ba fad'a zakuyi ba daga ke har shi d'in, dan shima abinda yake fad'a kenan duk lokacin da mukayi waya."

Cikin mamaki Ummi tace "Inna dama suna kuranku?"

Hararanta tayi tace "kin d'auka shima mara kula ne kamar ke, ai duk safiya ta Allah saiya kirani ya gaishe ni."

Dariya Ummi tayi tace "to amma ai nima ina kiranki ko?"

"Eh, kina kira sati ko kwana biyar ba."

Dariya sukayi gaba d'ayansu, Inna kuma ta d'ora da "gaskiya yaron nan yana da kirki sosai, wallahi ko 'ya'yan dana haifa basa min abinda yake min, kinga duk wata saiya aiko min da kayan abinci da kuma kud'i, kuma abinda yake min dad'i kullum godiya yake min da nuna jin dad'in zama da jikanyata."

Murmushi Ummi tayi tace "to yanzu kin tabbatar muna zaune lafiya ko?"

"Eh mana, dama tsokanarki nake."

Haka akayi biki aka gama cikin farin ciki, yayin da a gida kuma ake bikin Khamis cikin rikici da tashin hankali, domin kuwa amaryar akwai rawar kai dan ko fad'a da akayi amaryar ce gaba, Ummi data samu labari ta waya ji tayi kamar tayi hira tazo wajen bikin.

Kwana d'aya da gama bikin nan Inna tace su tattara su koma in da suka fito, nan suka fara mata magiya da ban hak'uri akan ta barsu su kara koda kwana uku, amma ina tace sai dai su kuma su kula da mazajensu, jin haka yasa La Mama tace to su sutafi su barta ta k'ara kwanaki, bud'ar bakin Inna cewa tayi,

"Au, kenan ke zaki

Please Login or Register in order to submit comment