Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali ta tuna ranar da suka fito tare da Salman ta rakoshi zai fita, da kuma ranar da ta fad'i saboda jiri ya d'auketa sannan ya kawo mata madara tasha.

Rayuwarsu take tunani tana murmushi ajiyar zuciya ta sauke tana mai k'ara fad'ad'a murmushinta tace "ina ma kadawo yau, da zan zauna da kai ko dukana ne kaci gaba dayi da wannan tattausan hannun naka"

Jawahir dake zaune gefe ita da Khamis ta kalleshi tace "mijina dubi mutuniyar murmushi take ita kad'ai, ina ga fa tunanin yaya Mane take"

Dariya suka saka gaba d'ayansu hakan ya janyo hankalinta, mamakine ya bayyana a fuskarta dan batayi tunanin suna nanba suma, saidai kallonsu kawai take saboda ganin k'afar Khamis a cinyar Jawahir tana masa wankin k'afa, take ta tuna da ranar da tama Salman yankan akaifu, wani murmushin ta koma saki tare da jin wani sanyi na lullub'eta, gaba d'aya taji kawai tana son ganin Salman ko fad'ane ma su dinga yi zata ji dad'i.

Jawahir ce data lura ba tada niyyar magana tace "Hajia Abu tunanin me ake ne haka?" kallonta Ummi tayi tace "ba komai"

Tab'e baki tayi tace "to naji ba komai, amma ya kamata ki shirya gobe muje muyi kitso" cikin farin ciki tace "yawwa dama nima ina so nayi kitso"

Cewa tayi "amma ai da kin bari har yaya Salman zai dawo sai kiyi" hararanta kawai tayi ba tace komai ba, Khamis kam cewa yayi "to nidai kamar kullum ne, indai har kina so kije to ki tabbatar kin kira mijinki kin fad'a masa."

Ba tada zab'in daya wuce ta kira ta fad'a masa dan haka tace "to yaya Khamis zan kira, na lura kaidai kana jin tsoron mutuminan sosai"

Hararan ta yayi yace "ke kuma baki tsoronsa ko jaruma?" dariya kawai tayi ba tace komai ba.


Ummi bata kira Salman ba saida safe sannan ta d'auki wayar ta kuna, ta danna numbershi tana fara k'ara taji gabanta ya fara dukan uku-uku, da k'yar ta iya daurewa tana sauraran ya d'aga.


Tana jin ya d'aga taji cikinta ya d'uri ruwa take taji tana buk'atar kewayawa, amma haka ta dake ba tare da tace komai ba, Salman dake saman hanyar dawowa yana ganin kiranta yaji farin ciki ya mamayeshi, ba tare daya kula ba ya samu kansa yana mai kasaitancen murmushi amma daya tuna wacece Ummi da kuma kashe wayar da tayi, kawai sai ya b'ata rai sannan ya d'aga.

"Oui je t'ecoute" ( na'am ina jinki) ya fad'a a tak'aice, cikin sanyanyen murya tace "haba ba ko sallama?"

Cikin dakakkiyar murya yace "ki fad'i abinda yasa kika kirani da gaggawa inada abinyi?" tab'e baki tayi tace "dama na kira ne dan na fad'a maka za muje wajen kitso nida Jawahir yanzu, kuma yaya khamis yace dole saina fad'ama zanje shiyasa na kiraka."

Wani buhun haushi ne ya kama shi, wato badan Allah ta kirani bama kuma saida akace ta kira sannan ta kira, ba damuwa zanyi magananinki ya fad'a a ransa.

Bud'ar bakinshi yace "baza kiba to indai nine zan bada izinin, ni dama nasan kinfi k'arfin ki kira ni ki gasheni bare ki tambayeni ya nake saboda bakisan mi ake nufi da miji ba, amma yanzu buk'atarki tasa kin kirani bayan kashe waya da kika yi."

Haushi taji itama cike da tsiwa tace "kaga nifa na kirane badan kamin masifa ba, sannan da kake cewa na kashe waya, e na kashe saboda banga anfanin kirana da zaka yiba tunda kana da wacce zaka dinga hira da ita, kuma ni ba izininka nake jira ba ina so naje kitso kuma zanje."

Cikin tattausan murya yace "to kenan kin fad'amin ne dan nasan zaki tafi, ko ko kin fad'amin ne dan nasan kin isa da kanki, ko kuma umarni ne kike bani akan na baki izinin fitar?"

K'irjinta k'ara tsananta bugawa yake amma haka ta daure tace "ka d'auki d'aya da kaga yafi da cewa dani saika sani a mahalin" cikin jin haushi yace "Ummi ince dai nine mijinki ko?"

Kamar tana gabanshi saida ta murgud'a baki tace "to saime mijin da baisan hakk'in matarshi ba, zaka k'ara aure amma saidai naji a gari amma ba komai akwai Allah, dan haka ni yanzu ko ka bani izini ko ka k'i bani izini, fitata zanyi in yaso in kamatsu ka fara bada umarni to sai ka bari harka kawo k'waillar matar taka saika fara mulkarta, amma ba Ummi ba."

Salman daya saki baki yana sauraranta izuwa yanzu ya fara fahimtar inda zancen, wato tana jin haushi dan zan k'ara aure, murmushi yayi yace "babu ruwanki da amayarta yarinya mai nutsuwa da hankali, sannan na fad'a maki karki je ko ina har saina dawo"

Abinda ya fad'a shiya k'ara harzuk'ata, cikin fitina tare da k'ok'arin b'oye hawayenta tace "saina je d'in, idan ka dawo ka kasheni." cike da izza yace "aiko idan kika fita bada izinina bâ, to zaki rasa k'afa ko ido"

Cikin kuka mai tsanani tace "e na rasa k'afar tunda kaine ubana da zaka min baki Ya kama ni." tana fad'a ta kashe wayar, toilet ta shiga ta wanke fuskar'ta sannan ta fito ta samu Jawahir da Khamis suna jiranta fitowarta.

Khamis ne yace "kin kirashi?" kai ta fara girgizawa sannan tace "na kira kuma yace naje, amma wai karna dad'e" hakan data fad'a yasa Khamis ya tabbatar data kirashi d'in.

Cikin farin ciki Khamis ya aje su gidan mai kitson, amma yace idan an ida su hau adaidaita sahu su koma gida tunda suce sai sun biya 'yar kasuwa sunyi siyayya.

_Ummi kam akwai marar jin magana, ko baki ji maganarsa a matsayinshi na mijinki ba, ai kin ji ko a matsayinshi na yayanki._
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_

```OH ALLAH KABAWA 🅱K LAFIYA ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD S.W.A, ALLAH YASA KAFFARA NE```


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

*Page*

5⃣9⃣-6⃣0⃣


Saida su kayi sallah azahar a gidan mai kitson sannan suka fito, a k'afa suka k'araso 'yar kasuwa saboda duk bisa hanyane babu nisa sosai, sayayya su kayi sosai musammam Ummi, duk kud'in da Salman ya bata kaf ta kashesu ga k'ananan kaya da kayan bacci da kuma kayan kwalliya.

Ana kiran sallah la'asar suka tsaya bakin titi suka shiga adaidaita.

_Tsotsayi kenan wanda ba'a sa mashi rana, idan ya wuni tofa baya kwana_

Sun d'auki babbar hanyar da zata sadasu da gidan saiko wani mai mota daya fito daga cikin kwana da iya k'arfinsa cikin ganganci, saiko yayi gaba da adaidaitar dasu Ummi ke ciki.

B'angaren da Ummi take nan adaidaitar ta fad'a, mai adaidaitar na fad'owa k'asa kuma wani mai babur ya taka kanshi take ko shurawa baiyi ba yace ga garinku nan, tuni aka kewaye su ana k'ok'arin basu agaji, wasu samari ne suka kama Jawahir ta taka adaidaitar ta fito ta sama, sannan aka d'aga adaidaitar dan a janye Ummi.

Ana d'aukewa Ummi ta tashi zaune idonta ne suka sauka kan mai adaidaita, tana ganinshi ta dafe kanta tare da zankad'a uwar k'ara take kuma ta saké zubewa k'asa somammiya, Jawahir da jiki keta mata rawa ta kasa tsayawa daidai wani dattijo ne ya janyeta daga wajen, kafin aka d'aukesu aka nufi babbar asibiti da su.



Jawahir gurjewa kawai tayi a goshi, dan haka ana gama dubata aka amshi wayarta aka kira Khamis, Khamis bawon Allah tashin hankali ne ya shiga wanda bai tab'a shiga irinsa ba, haka ya garzayo yazo asibitin.

Saida aka bashi tabbacin jikinsu da sauki sannan ya tafi gida ya fad'ama manyansu halin da ake ciki.

Babu wanda yayi yink'urin zuwa ba tare daya fad'ama Alhaji ba, amma sam ya rufe ido yace a barta can ita da halinta, ran kowa ya sosu musammam ma iyayenta sunfi kowa shiga damuwa sai kuma Hajia Zeinabou wacce babu wanda ya kaita d'aga hankalinta.

Ganin ba zai barsu ba yasa Hajia Zeinabou ta fara rera mashi kuka tana lallab'arshi, ba zai juri kukanta ba shiyasa ya amince duk mai so yaje ya ganta amma hakan ba yana nufin ya yafe mata bane.

Dan-danan sai asibiti ta cika da yan uwa, an masu barka ta wani b'angaren kuma an jajanta masu, Khamis duk ya rud'e ya rasa ta yanda zaiyi ya kira Salman ya fad'a masa, dan a ganinshi babu dad'i ace an baka amana amma amanar ta salwanta a hannunka.

Missalin 17:20 Salman ya doko ma Khamis kira wanda yasa gabanshi tsinkewa, da k'yar ya d'aga basu ko gaisaba Salman yace "kazo ka d'auke ni dan Allah na gaji da kiranka" kashe wayar yayi ba tare daya jira me zaice ba.

Haka Khamis yaje gidan bus d'in ya d'aukoshi, kallo d'aya Salman yama Khamis yasan akwai matsala amma baya cikin yanayin farin ciki shiyasa bai tanka saba, ganin sun d'auki hanya daban yasa yace "ina kuma zaka kaini malam? ka kaini gida dan Allah yunwa nake ji" baice masa komai ba sai cigaba da tuk'insa yake har suka kai babbar asibitin.

Tunda suka shiga gabanshi keta dukan uku-uku, yana da 'yan uwa dayawa dan haka ya rasa wa zaiyi tunani ke asibiti, zuciyarshi na raya mashi wani ko wata mai mahimmanci sosai ne a gareshi ke kwance anan d'in.


Ummi na zaune an gama mata dressing d'in ciwon, sai yanzu ne take jin zafin ciwon sai kukan shagwab'a take masu Hajia dasu Mama (mahaifiyar Salman) su kuma sai rarrashi suke cike da taussayinta, kwatsam Salman ya fad'o d'akin yana zare ido yana kallon ikon Allah.

Fad'uwar gabanshi ya k'ara tsananta duk jikinshi yayi sanyi ga wani jiri daya keji yana 'dibarshi, kukan da Ummi keyi yasa yaji takaici ya rufeshi, wato rainawa mutane hankali zatayi ma bayan bata ji maganarsa ba.

Sannu da zuwa su mama suka masa cike da mamakin yanda yazo bai sanar da kowa ba, tsaye yayi kusan k'afafunta data ji ciwo k'afar dama an nad'eta da bandeji tun daga wajen ijiyar sau har zuwa cikin tafin k'afar saboda k'arfen daya karceta har farar coka ta fito, sai k'afar hagu kuma gurjewa ne a gwiwa amma saboda buguwa da k'afar tayi kuma adaidaitar ta tausheta hakan yasa tayi kumburi sutum da ita, sai kuma hannun dama data fad'a samanshi ba daidai ba ta goce.

_Hum dama 'yan magana sunce, in haka ji bari ba kaji hoho_

Da k'yar ya tambayi abinda ya faru, ana fad'a masa ya kalli Jawahir dake gefe da 'yar gurjewarta a hannu yace

"Kingani ko Jawahir da yake ke kina jin maganar mijinki, kinga baki ji ciwo sosai ba Allah ya k'ara kiyayewa"

Take La mama ta maida kallonta ga Ummi, Ummi kam da hannu ta mashi alamar yayi shiru, dan inhar La mama taji to abinda zata mata sai yafi ciwon dake jikinta yi mata zafi.

Zagayowa yayi ya zauna kusa da ita, saida ta sauké ajiyar zuciya saboda shak'ar kamshin turarenshi har cikin zuciyarta taji dad'in zaman da yayi kusa da ita, ji tayi kamar ta fad'a jikinshi ya rumgumeta, kallonta yake sosai dan har yanzu yana mamakin abinda ta aikata, baiyi tsammanin zata tafi ba daya hanata ashe da gaske take zata tafi.

Cikin shagwab'a tace "yaushe ka dawo?" kafin ya bata amsa La mama tace "abinda ya kamata ki tambayeshi kenan?" k'ara kwab'e fuska tayi tace" kazo lafiya, ya hanya?"

Tsawa La mama ta mata tace "Ummi mijinki kike kira da kai, babu girmamawa a ciki ba zaki iya cewa kunzo ba, saidai kazo?" kamar zatayi kuka amma ba tace komai ba, Hajia Zeinabou ba zata juri ganin b'acin ranta ba dan haka tace,

"Kai kuma ka amsa mana, yarinyar dake cikin halinnan ai tayi 'ko'kari ma data iya gaishe shi." kallon Hajia yayi yace "ba zan amsa ba Hajia saboda bakisan méta aikata ba"

Yana fad'a ya mik'e ya fita harabar asibitin, La mama tashi tayi tabi bayanshi, tsaye tayi tana Kallonshi kafin tace,

"D'ana ka fad'amin meta maka dan Allah?" kallon La mama yayi cike da kunya sannan yace "La mama babu komai wasa nake mata"

Murmushi La mama tayi tace "Salman yaushe ka fara b'oyema mahaifiyarka farin cikinka da damuwarka dama sirrinka?" baya b'oyema La mama komai, idan har bai fad'a mata abinda zata nutsu ba to ya san zata iya huce haushinta akan Ummi dan zata titsiyeta saita fad'a mata.

"A'a La mama bawai na b'oye maku bane, kawai jiya munyi wayane da ita kuma munyi akan ba zata saké kashe waya ba, amma nayita kira tun safe bata d'auka ba sai yanzu nazo na tarar da abinda ya faru."

Ko kad'an La mama bata yarda ba, amma bata so ta takurashi dan haka tace "shikenan ba damuwa" ciki La mama ta dawo amma badan mutanen dake d'akin ba da sai ta tambayeta abinda ya faru.

Salman ya jima yana jin babu dad'i yana tunani akan abinda Ummi tayi "me yasa tayi haka, me yasa da nace ta zauna tak'i zaunawa, shin abinda ya fad'ane da wasa dan ya hanata fitar shine ya faru da gaske, shin dama haka bakin miji keda ta siri akan matarsa, inko hakane dole nasan me zan dinga fad'a mata tunda dai ita ba zata ji maganarshi."


"Yanzu gashi abinda ya faru da ita, yanzu da ita ce fa abinda ya faru da mai adaidaita sahun ya faru da ita fa saime ya faru da ni?" ya tambayi kanshi.

Zunbur ya mik'e tsaye daga kan tabarmar da yayi sallah la'asar, cikin sauri ya nufi d'akin da suke yana fad'in "ina babu abinda zai sameta insha Allah, tana nan tare da ni ba zata mutu ba muna nan tare."

Tsaye yayi k'ofar d'akin saboda mutanen dake ciki, idonshi akan Ummi wace idonta sukayi jawur alamar har yanzu tana kuka, juyawa yayi ya fita daga d'akin gida yasa Khamis ya kaishi.

Wanka yayi ya shirya sannan suka fito tare restaurant (maqui) ya ajeshi dan yaci abinci amma saiya kasa, tunaninshi ya koma kan Ummi da ciwonta dan gani yake kamar shine silar hatsarinta, haka suka dawo asibiti suna zuwa lokacin magrib yayi dan haka suka tsaya masallaci sukayi sallah sannan suka wuce d'akin da Ummi take.

Sun samesu sun shirya suna jiransu zasu tafi gida, Hajia ce ta kalli Salman tace "kaga tunda ba zata iya takawa ba, ka d'auketa ko"

Ido ya fiddo ya kalli kowa dake d'akin yace "haba Hajia ai k'wara na d'aukeki na goya akan wannan b'ulleliyar, dan zata iya karyani gashi dama ina jin yunwa, kinga saimu fad'i daga ni har ita."

"Kaga banasan rainin wayo, in zaka d'auketa ka wuce muje ka d'auketa, in kuma ba zaka d'auka ba nasa Khamis ya d'aukarmin 'yar leleta." ta fad'a tana kashe ma Khamis ido.
05/03/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_


```DEDECATED TO```

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

_Kunada karamci a gareni matsayinku da girmanku ya mafi haka, domin daga cikinku ne na samu makusanta masu nunamin k'auna a kowane lokaci *Yan ZAMAN AMANA* ina k'aunaku dukanku._

'KUNGIYATA ABAR ALFAHARI MAI NUNA DAMUWA GA WANDA YAKE CIKINTA


*Page*

6⃣1⃣-6⃣2⃣


Matsowa Khamis yayi kamar zai d'auki Ummi, saiko Salman ya hankad'eshi yana fad'in" dallah malam gafara daga nan" bushewa sukayi da dariya, shi kuma sunkuyawa yayi ya zura hannunshi ta bayanta ya tallabota, d'aya hannun kuma ta k'asanta nanma ya ciccib'ota gaba d'aya.

Kamar zuciyarta zata fasa k'irjinta ta fito haka yake jiyo bugun zuciyarta, yana sama da ita Ummi ta rufe ido ta kau da kanta gefe, Salman kam wucewa yayi su Hajia na gaba suna baya, tafiya kawai yake fuskarnan a had'e kamar hadarin gabas gashi babu wani alamu daya nuna yana jin nauyin abinda ya d'auka.

Dan kuwa a tsaye yake k'yam, dan shi anashi b'angaren kawai bai d'auketa mai nauyi ba duk da k'ibarta, dan k'arafan da yake d'auka ma sunfita nauyi, suna haka ne wayarshi ta fara ruri, ba tare daya kalleta ba yace,

"Malama fiddomin wayata".

Sai lokacin ta juyo da kanta, a hankali tasa hannu a cikin aljihun rigarshi na gaba ta ciro wayar kamar ta d'auko maciji, tana ganin sunan daya fito a écran d'in wai *REINE*(sarauniya).

Hawaye taji sun zubo mata haka kawai saiko ta jefar da wayar k'asa, Salman na ganin haka ya tsaya cak tare da kallonta yace "miye haka Ummi kina lafiya kuwa, kodai had'arin harda kanki ya tab'a?"

Kawai saita k'ara fashewa da kuka tana fad'in "azzalumi kawai dama kasan wacce zata kiraka wato sarauniyarka shiyasa kace na d'auka dan dai naji haushi ko, to wallahi sai Allah ya sakamin mugu kawai."

Sai lokaci yasan ko wacece ta kirashi, tabbas Nuseiba ce dan ita ya sama sunan sarauniya, (kenan abinda Jawahir ta fad'a gaskiya ne, Ummi tana kishin shi, to amma miyasa?),.

K'ara matseta yayi a jikinshi ya sunkuya ya d'auki wayar data fashe yasa aljihu, sannan suka wuce.

Jiniyar kukan da take ne yasa yace "kenan wannan kukan na kishi ne ?"

Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "Allah ya sawak'e nayi kishinka"

Ba tare daya kalleta ba yace "kenan najin dad'ine kike saboda na d'aukeki?"

Mitsiniya ta fara tana cewa "kaga ni saukeni dan Allah zanje da k'afata, abinda hannun ma sai tauri kamar katako"

Tana fad'in haka hannunshi dake kusa da k'irjinta ya ida zurawa ya matse mata mama, yar k'aramar k'ara ta saki saboda yanda taji zafi, kallonta yayi ya d'aga mata gira yace "mi kika ji 'yan mata?"

Cike da shagwab'a tace "Allah saiya sakamin kuma ban yafe ba mugu"

Rufe idonshi yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e, harga Allah baya so yaji tana fad'a mashi irin haka, amma ya zaiyi bakinta ya riga ya saba ba zata iya dainawa ba.

Suna kaiwa Jawahir ta bud'é masu k'ofa ya ajeta sannan kowa ya shiga suka wuce, gaba d'aya gidansu suka wuce, Hajia saida ta d'ora ruwan zafi ta barma Salman sallahun ya gasa mata k'afa ya kuma tabbatar tasha magani sannan ta kwanta, haka ma mahaifiyarshi saida ta saké jaddada masa kula da ita sannan suka bar gidan Khamis ya mayar dasu gida.

Ruwan nayin zafi ya d'auko tare da d'an k'aramin towel, kusa da ita ya zauna inda ta mik'e k'afafunta, towel d'in ya tsoma cikin ruwa ya fiddo ya matse sannan ya aza mata a k'afar, k'ara ta saki tare da janye k'afar da sauri, saidai ina ta manta ciwon da take mata, runtse ido tayi saboda azaba ta fara matso k'walla.

Salman kam in banda d'aci babu abinda zuciyar shi keyi masa, ji yake kamar ciwon ya dawo jikinshi zaifi mashi sauk'i, rik'e k'afar yayi yace "sannu ko, bari na maki hankali"


Mamaki ne ya lullub'e Ummi dan haka ta saki baki tana kallonshi, a hankali ya dinga gasa mata k'afar Ummi kam tun tana jin zafi harta fara jin dad'i, kallonshi kawai take zuciyar ta na k'ara narkewa akan son wani abu da bata so taji tana jinshi akan Salman d'in.

Idonshi na kan k'afarta yace "mina fad'a maki a lokacin da mukayi waya?"

Gabanta taji ya fad'i, amma ganin ko kallonta baya yi yasa cikin tattausan murya tace "kace karna fita"

"Sai kuma nace mi a gaba?"

Murya na rawa tace "kace idan na fita zan rasa k'afa ko ido" har yanzu yak'i d'agowa ya kalleta yaci gaba da cewa,

"Sai ke kuma ki kayi mi?"

"Saina fita"

"Bayan kin fita kuma miya faru?"

"Nayi accident a hanya"

"Sai mi ya faru bayan had'arin ya faru?"

"Ciwo naji"

"A me kenan?"

Kamar zatayi kuka tace "a k'afafuna da kuma hannu"

"Me kika fahimta daga abinda ya faru?"

Cikin muryar kuka tace "na dinga jin maganarka, idan kace nayi to nayi, idan kace na bari na bari."

Jinjina kai yayi yace "da kuma mi?"

"Tasirin bakin miji akan matarsa"

"To yanzu idan na hanaki zaki hanu?"

Kai ta girgiza ta k'ara fashewa da kuka tana fad'in" kayi hak'uri yaya Salman wallahi ba zan saké ba daga yau, duk abinda kace nayi zanyi"

Sai lokacin ya d'ago kai ya kalleta yace "kin tabbata?"

Saida ta sharb'i majina tace "wallahi zanyi na maka alk'awari, amma dan Allah karka fad'ama La mama"

Kafeta yayi da ido yace "kenan yanzu zaki dinga jin maganata idan na maki?"

"Wallahi zan ji yaya Salman"

Ajiyar zuciya ya sauké yace "shi kenan na yafe maki tunda kince ba zaki saké ba, nima kuma ki yafemin dan bai kamata na fad'a maki haka ba, kamata yayi na tsoratar dake ta wata hanyar daban ba wannan ba."

Kallon shi kawai take baki bud'e, karo na farko kenan a tarihin rayuwarsu da taji makamancin wad'annan kalaman daga bakin shi.

Yana gamawa ya bata magani tasha, amma ta dinga tsala kukan shagwab'a wai ita ba zata shaba, saboda tausayi yasa Salman rarrashin Ummi , amma fafur tak'i tasha sai baud'ewa take tana botsarewa, dole dai tasa ya koma Salman d'insa na ainihi, tsawa d'aya ya mata ta karb'a tasha jiki na rawa, dan Salman ba daga nan ba wajen tsare gida.

Tashi yayi ya maida robar cuisine ya aje ya dawo ya d'auketa ya kaita d'aki ya kwantar da ita yaja zanin rufa ya rufeta sannan yace "kiyi bacci" yana fad'a ya bar d'akin.


Ummi na bacci cikin farin ciki saiko tayi mafarkin mai adaidaitar nan da taga ganshi a fashe, girgigit ta tashi tare da fad'in "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, innalillahi wa'ina ilaihir raju'un, Hasbunallahu wani'imal wakil."

Dafe kanta tayi ta fara rera kuka, saboda abunne kawai ke dawo mata a kai yana mata yawo a k'wak'walwa, a hankali take rera kukan hannayenta biyu a kanta.

Salman dake tsaye yana nafilfili yaji tashinta dan haka ya shigo cikin azama dan yaga mike faruwa.

Zaune yayi kusanta yana fad'in "Ummi lafiya miya faru?"

Tana d'aga kai ta kalleshi kawai saita fad'a jikinshi ta k'ara fashewa da kuka, rigar shi kawai take ta cukuikuyewa tana k'ara tusa kanta cikin k'irjinshi tana fad'in "yaya Salman shi nake gani wallahi tsoro nake ji, zamu k'ara fad'uwa, dan Allah karka tafi duk jini ne a jikinshi ga kanshi ma ya fashe"

Shiru yayi yana tunani (dole ne abun ya tsaya mata a rai, dan yanda aka fad'a masa gawar mutumin dole ko namiji yaji abu bare kuma mace mai rauni), hannayenshi ya dora a bayanta yana cewa "shikenan to ya isa haka kinji, insha Allah bazai saké dawowa ba, calme toi"

Haka yaci gaba da shafa bayanta har bacci ya d'auketa, a hankali ya maida kanta saman pillow yayi mata addu'a ya shafa mata, idonshi akan fuskarta, mik'ewa yayi ya shinfid'a sallayarta yaci gaba da sallarshi.

Har aka kira sallah asuba Ummi na bacci, Salman ne ya taso ya tayar da ita dan tayi sallah, saida ta tashi zaune tayi addu'ar tashi daga bacci sannan ta kalleshi.

"Malama ki tashi kiyi sallah" yana fad'a ya juya zai fita, yunk'urawa tayi ta tashi amma ina k'afafu sunyi tsami.


_Wayyo Ummi wallahi irin ciwon da naji nima kenan lokacin da na fad'i da moto, saida na zama gurguwa ta kwana uku_

Da sauri tace "yaya Salman dan Allah kaini toilet"

Dawowa yayi ya tsaya yana kallonta kafin yace "haka ake neman taimako cike da bada umarni?"

Turo baki tayi tare da zabga uwar harara ta kau da kai gefe tana wani jijjiga, k'ura mata ido yayi yana jiran yaji ko zata rarrasheshi amma shiru kake ji.

Ummi tunaninta shine ya zatayi ta rarrashi mutum, batasan yanda zatayi ba dan tunda take bata tab'a rarrashi ba idan tana son abu, ita dai idan taga abu tana so koba nata bane to kawai za tace ne abata, idan ba'a bata ba ta fashe da kuka su Hajia Alhaji maman Salman mahaifinta suna kewaye da ita su zasu goyi bayan abata ko sun san ita ce marar gskiyar wannan shine.

Jin fitsari na shirin kubce mata yasa ta saké kallonshi tace "dan Allah haba ka kaini fitsari nake ji fa"

Kallonta kawai yake kamar gunki, kwab'e fuska tayi tace "ni dai inba zaka kaini ba wallahi zanyi shi a nan"

Baisan sanda dariya ta sub'uce masa ba, amma saiya dake yace "to kiyi mana gadonki ne fa ba nawa ba"

Hawaye ne suka fara taho mata tusa hannayenta tayi tsakankanin cinyoyinta tana ta matsewa wai karya fito, saiko taji fitsarin ya fara zubowa, fashewa tayi da kuka tana fad'in "dan Allah ka kaini wallahi zai taho"

Cak ya d'auketa yayi toilet da ita ya aje tsaye, ina yana ajeta fitsarin ya ida tahowa, Salman kam mutuwar tsaye yayi yana kallonta kafin ya fara shek'a dariya har yana rik'e ciki.

Ummi kam ko a jikinta dan inta nuna masa taji kunya to ta shiga uku kenan zai dinga tsokanarta kullum, cikin shagwab'a tace "ni dan Allah ka fita to na gyara jikina"

Da k'yar ya dakata daga dariyar ya nunata da hannu yace "ke yanzu ko kunya bakya ji kamar wata k'aramar

Please Login or Register in order to submit comment