Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ta fito ta shiga cuisine ta fara girkin rana, tsananin yunwa da zafin jiki ga ciwon kai duk ya taru ya mata yawa, haka ta kammala girkin da k'yar kamar zata mutu.

Tana idawa ta koma d'aki tayi sallah ko wanka ba tayi ba saboda raunikan dake jikinta, tana kwance Salman ya shigo d'akin yace" wa kika aje da zai zuba maki abincin" fita yayi bai jira amsarta ba tashi tayi tabi bayanshi, tsaf ta zuba masa shinkafa da miyar kayan cikin ragon da tayi, bud'a ciki yayi ya ci abincin sosai, yana kammalawa yayi wanka ya fita bâ tare da ya bi ta kan Ummi ba.

Abun ya k'ara tsananta ma Ummi kamar za tayi hauka ta keji, ga zafin ciwo da rad'ad'i ga ciwon kai saboda kukan da take sha ga bakin ciki da kad'aici, tuna dukan da Salman ya mata yasa ta shiga cuisine dan sarrafa abincin dare, macaronie da miyar naman rago ta dafa d'an kad'an wanda zai ishe su.

Da k'yar ta watsa ruwa dan ciwon da ke jikinta ba zai bari ta cud'a ba, d'aure take da towel tana ta kai da kawowa saboda wani sabon rad'ad'i da take ji, mai ta shafa tasa turare gajeran wando tasa iya cinyoyinta sai bras da ta saka wanda taji kamar ma karta saka, maganin da Salman ya siyo mata tasha sannan ta kwanta ba jimawa bacci ya d'auketa.

Kusan awa biyu kenan da Salman ya shigo gidan amma babu ko motsin Ummi, abinci kawai ya ke so yaci amma ya k'i zubawa yana jiran Ummi, a hankali ya bud'a k'ofar d'akinta ya shigo, k'ura mata ido yayi yana k'are mata kallo tas, duk da shatin bulalar da ya gani ya fito sosai a jikinta duk jini ya kwanta ga manyan birridda duk a bayanta ya kwanta, tausayinta ya ji ya kama shi sai yaji baiji dad'i ba lokaci d'aya kuma ya ji wani abu yana tsargar masa tun daga kwanyar kanshi har babban dan yatsan k'afarshi, yana jin abun yana k'ara girmama yana fizgar shi kamar zai aikata wani abu yasa ya daddab'a k'afarta, a hankali ta juyo da kanta sannan ta tashi zaune tana murza fuskarta cikin tattausan murya yace,

"Wa kika aje da zai zuba min abincin?ko ni kike so in zuba da kaina?juyawa yayi har ya kai k'ofar d'akin ya tsaya ya juyo yana kallanta, ganin bata taso ba yasa yace" wai ba kiji ne ina maki magana?" a hankali tace" ina zuwa riga zan saka" kenan sai na zaune ina jiranki harki gama, kinsan awata nawa a gidan nan ina jiranki,ko so kike yinwa ta kashe ni?" yin k'urawa tayi ta tashi ta nufi drower, tsawa ya mata da k'arfi" ke wai ba da ke nake ba da za kice sai kin gama abinda kike, ko wata tsiya ce a jikin naki da zan kalla?dallah wuce mu tafi" ya mata alama da hannu wucewa tayi sub'ur sub'ur k'ugunta na kad'awa harda kakkaryawa bayanta keyi, kamar baturiya haka ta dinga kai da kawowa tana zuba masa, duk da hankalin sa na a waya amma saida zuciyar shi ta fizgi idonshi izuwa shagalta da kallonta musamman ma kunkuminta da k'irjinta sun matuk'ar tafiya da shi, tana zuba mashi ta kama hanya zata koma d'aki ji yayi zata rage masa jin dad'i dan haka yace" zo ki zauna nan" cikin shagwab'a ta kalleshi tace" yaya Salman kayi hak'uri na sako riga" zo nan nace" dole ta zo taja kujera nesa da shi ta zauna tana ta b'oye k'irjinta, shiru babu mai magana hakan yasa Ummi ta d'auki robar madara akan dinning ta fara sha cikin d'ari d'ari, ana cikin haka hadari ya taso iska aka fara da k'arfi, Ummi duk ta k'agu ta tashi Salman ko ko a jikinshi abincin shi yake ci hankali kwance, wutar da aka d'auke tare da sako ruwa mai k'arfi yasa Ummi matso da kujerarta kusan Salman, tunda ya lura a tsorace take kawai sai ya k'i kunna hasken wayar shi, tsawar da akayi irin mai sa hanjin mutum kad'awa yasa Ummi mak'alewa a jikin Salman ta lakayo da hannunta ta wuyanshi rik'e da robarta a hunnu tana fad'in" yaya Salman tsoro nake ji, dan Allah muje d'aki" bai tankata ba saidai duk tasa jikinsa yayi sanyi saboda yanda k'irjinsu ke had'e.

Ba tada niyar sakinshi dan haka ya kama hannunta ya kaita d'akinta, amma ina tace ai ba zata zauna ita kad'ai ba, harya aje mata wayar shi kuma yaga shi ma baya gani dan haka ya zauna gefen gadonta yana satar kallonta har bacci ya d'auketa, lullub'eta yayi da zanin rufa yana kallonta yana girgiza kai fitowa yayi ya koma d'akinshi yana fad'in" jaraba bacci da madara a hannu, kamar wata yar shekara biyu a duniya, ai ko mai shan nono ba za tayi wannan jaraba ba."tsaki yayi ya kwanta kafin bacci shima ya d'auke shi.
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah_ )🤜🤛

*Page*

4⃣1⃣-4⃣2⃣


Ummi tayi nisa a cikin baccin taji ana tsawa, zunbur ta tashi zaune tare da rik'e robar madarar da tasha bacci ya d'auketa daga nan, ganin babu wuta a d'akin sai duhu yasa ta fara k'ara tana fad'in" yaya Salman, dan Allah ka zo, wallahi tsoro nake ji, dan Allah kayi hak'uri ka zo, Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un shikenan mutuwa zanyi" shiru tayi dan tasan ba zai zo taimaka mata ba zanin rufa taja ta k'ank'ame a ciki tana rawar jiki.

Cike da k'asaita ya shigo d'akin da wayar shi a hannunshi, gefen gado ya ajeta ya zauna ya mik'e k'afafunshi saman gadon ya jingina bayanshi tare da rumgume hannayenshi a k'irjinshi sannan ya kalleta yace" haka ya maki?nasan za kice tsoro kike ji ba zaki iya bacci ke kad'ai bâ ana ruwa, to gani sai ki kwanta yanzu." ya k'arashe maganar da hararenta turo baki tayi a hankali ta sulale ta kwanta tare da gyara rufarta dan-danan bacci ya sake gaba da ita.

Makara yayi wajen tashi ko da Salman ya farka gari har yayi haske sai lokacin yaga yanda ya kwana daga zaune, juyawa yayi ya kalli Ummi sai yaga ba tanan mamaki yayi ta tashi amma ni ta k'yaleni, tashi yayi ya nufi d'akinshi ya nata matsar wuya saboda ciwon da yaji yana yi masa, sallah yayi ya sako kayan sport ya fito dan ya yaje bayan gidan a wani hankad'ed'en d'aki in da yasa aka gyara shi ya zuba kayan motsa jiki, Ummi ya gani tana Aje kwanuka a dinning ba tare da ya tsaya ba yace" ki biyo ni da jus mai sanyi" jiki na rawa Ummi ta bud'a fridge ta d'auko dan yanzu kam harga Allah tsoron Salman ya kamata, saida ta kai farfajiyar gidan saboda sanyin da taji na ruwan da aka sha jiya ta tuna doguwar riga ce a jikinta wacce ta d'ora a kayan da ta kwana da su, juyawa tayi da nufi ta d'auko hijab Salman ya juyo yace" zaki wuce ko sai rai ya b'ace" wucewa tayi da saurinta harya bud'a d'akin suka shiga, kallo Ummi take sosai yanda aka k'awata wajen mik'a mashi jus d'in tayi dan ta koma in da ta fito, hararan daya mata yasa ta sunkuya ta aje ta tashi zata fita yace" zo nan, kinga waccen k'arfen shi nake so ki d'auko min" kallan k'arfen tayi taga ko zai kasheta ba zata iya d'aukarshi ba,dan haka ta juya ta kalleshi tace" yaya Salman ba zan iya d'aukar shi ba wallahi" wata kyakyawar waya ya d'auka yana shirin zuk'a mata ta nufi wajen k'arfen a guje ta fara 'ko'karin d'aga shi, ganin ta kasa yace ta d'auko na kusa da shi shima bata d'auko ba saida kanshi yazo ya d'auka ya fara d'agawa k'wanji na fitowa da jijiyoyi haka ta saki baki tana kallonshi, yana gamawa ya d'auki ball ya fito tsakar gidan ya fara bugawa, haka kawai Ummi taji tana san ta yita kallonshi yanda yake ball d'in da kuzari da salo, Salman na ganin ta saki baki ya jefo mata ball d'in da nufin koda ta sameta ta sameta a in da bâ za taji ciwo ba, sai ko a fuskar Ummi ji kake Timm ball ta mare ta, duk'ewa tayi tare da rufe fuskarta, jin ba tayi k'ara ba yasa Salman tunanin ba taji zafi ba, d'aukar ball d'in yayi ya ci gaba da bugawa saida yaga Ummi ta jima bata d'ago ba ya zo kusa da ita, sunkuyawa yayi ya d'ago da kanta take gabanshi yayi wata mummunar fad'uwa saboda ganin idonta na dama ya kumbura ga jini ya kwanta abin tausayi" oh mon Dieu, pardon Ummi kinji bansan haka zata faru ba dan Allah kiyi ha'kuri" hawayenta ta goge ta mike tsaye tace" ba komai akwai Allah" wucewa tayi d'akinta nan ta fara sabon kuka kamar da bakin k'warya.

Jikinshi ne duk yayi sanyi da yaji tace akwai Allah, Allah kuma ba azzalumin bayinsa ba ne dole zai mata sakayya, aje ball d'in yayi ya koma ciki saida yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya wanda suka karb'e shi matuk'a sun masa kyau ga k'amshin turarenshi mai sanyaya zuciya, haka ya shigo d'akin Ummi ya sameta tana ta kuka a tsakiyar gado, sai ya ji baiji dad'in hakan ba tausayi ta bashi sosai ( k'aro na farko kenan a rayuwar Salman da ya ji tausayin Ummi har cikin zuciyar shi) zaune yayi cikin muryar rarrashi yace" Ummi dan Allah kiyi ha'kuri ki yafemin, wallahi banyi nufin ta sameki ba" d'ago da fuskar tayi yanzu kam gaba d'aya fuskar ta d'an kumbura ido sun ida yin ja saboda kuka, kau da kanshi yayi kai lokaci d'aya kuma ya kalleta yace" kin yafemin Ummi?" bata tanka saba haka yaci gaba da rarrashinta har saida yace" dan Allah Ummi ki yafemin, wallahi ba zan iya kwana dà alhakinki a kaina ba Ummi kin had'ani da Allah kinsan kuma dole zai maki sakayya, kiwa Allah ki yafemin kinji, in kuma ba zaki iya ba to ki fad'i abinda kike so nayi sannan ki yafemin?" sai lokacin kad'ai tayi magana tace

"In dai kana so na yafemaka to saidai in ka yarda zaka mayar da ni gidan mu" kallonta yayi yace" kema kinsan hakan ba zai yiwuba, idan na kaiki gida ko da da wuni d'aya ne to nima zan shiga cikin bak'in jadawalin Alhaji, ni kuma yanzu ban shirya rabuwa da kowa nawa ba." kuka ta k'ara fashewa da shi tana fad'in" wallahi ni sai na tafi gidan mu ba zan iya zama da kai a gidan nan ba ka kashe ni, ka duba kaga yanda na koma kamar wata jaka kun same ni sai duka kuke, ta yaya zan iya zama da Kai a gidan nan ni dama ba kyau ba jar fatar ce kawai gashi kuma yanzu kun mayar da fatar ta koma kala biyu ja da bak'i, dan mugunta kuma yanzu fuskar tawa kake hari ka nakasata" mik'ewa yayi yace" kiyi ha'kuri idan za kiyi, idan kuma ba zaki yafe ba to ruwanki ne kuma." fita yayi ya zuba abinci yaci ya fita ya bar gidan.


Ganin fuskar tayi sauki yasa tayi girkin rana, bayan ya dawo yaga babu kumburi sai dai har yanzu akwai ja a idon, dan haka yayi tunanin siyo mata magani idan ya fita, abinci yaci yayi wanka zai fita Ummi tayi saurin tare gabanshi ta durkusa tace" dan Allah yaya Salman ka taimaka min ka bani waya ta ina so in kira la mamma da Abba" cikin dakewa yace" ki fidda rai da wannan wayar, dan bâ zan baki ba ki dinga taramin maza cikin gida ba" kallonshi tayi tace" Salman me kake nufi?zargi na kake?" kunnanta ya kama ya murd'e har saida ta saki k'ara yace" kar na saké jin bakinki ya kira sunana daga yau, ko dai kice yallab'ai ko kuma ranka shi d'ad'e" sabo yasa Ummi murgud'a baki tace" to sannu, kaji mun mutum wai ranka shi d'ad'e kamar wani sarki" kwaf ya buge bakinta yace" to naji bakinki ya kira ni da sunana kiga yanda zanyi da ke a gidan nan" wucewa yayi ya barta nan.



Da wuri Salman ya shigo saboda hadarin da ya taso, Saïda yayi wanka ya fito ya zauna Ummi ta zuba mashi abinci, cewa yayi ta zauna tare suka ci abinci sannan ya bata magani saïda yayi kamar ya bibbigeta sannan tasha.


23:59 Ummi ta kawo ma Salman Tea, ya ji dad'in ganin tsoronshi a idonta sannan tayi abinda ya sata, tana zuba mashi ta zauna k'asa ta jingina da gado, kallonta yayi yace" miye haka kuma?" kamar za tayi kuka tace" dan Allah kayi hak'uri karka koreni, wallahi tsoro nake ji a can, amma idan aka d'auke ruwa zan koma" Tea d'in shi yaci gaba da sha ya shareta har bacci ya d'auketa.

Bugun da taji a k'afa yasa ta bud'a ido tana kallon Salman da yasa jallabiya da sallaya a hannunshi yana 'ko'karin shinfid'awa, tashi tayi ta koma d'akinta duk jikinta ciwo saboda ta kwana daga zaune, sallah tayi tana idawa ta shigo d'akinshi da sallama, durk'usawa tayi ta gaishe shi ya amsa yau ma kamar jiya Al-Qur'ani ya bata ta d'ora a inda ta tsaya, ta jima sannan ya karb'a ta tashi ta nufi cuisine a kasalance dan aikin ya fara gundurarta tunda ko a gida bata makamancin aikin da ta keyi anan ko kad'an sai hutu.

Da k'yar ta samu ta had'a frite da omelette da Tea da yar matsakaiciyar sauce d'in albasa da petit poids ta aje mashi, wanka ta shiga ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa mai da turare kawai ta shafa ta fito falo ta zauna.

Tana ganin ya fito ta tashi cikin ladabi ta sunkuya tace" ina kwana" sama da k'asa ya kalleta ganin fuskarta tayi sauki yasa ya wuce bâ tare da ya amsa, bin bayanshi tayi da harara, ganin ya nufi hanyar fita tace" yaya Salman abin karyawar fa?" juyowa yayi ya kalleta yace" kin manta ko wace rana ce yau? ni ba kamar ki bane mai bawa ciki wahala" shiru ta dan yi ta tuna yau alhamis yana azumi, amma kuma ba taga yayi sahur ba, mik'ewa tayi ta tari gabanshi ta tsaya tace" yaya Salman, dan Allah" katseta yayi da fad'in" me na fad'a maki jiya akan kiran sunana?" rufe baki tayi sannan tace" kayi ha'kuri, dama ina so ne ka kiramin la mamma ina so nayi magana da ita" mtssss, dogon tsaki yayi ya zauna saman kujera ya fiddo waya, dad'i ne ya kama Ummi dan tasan zai kira mata mahaifiyarta ne.

Mik'a mata wayar yayi ta d'ora a kunne, tana jin an d'auka ta mik'e dan ta bar wajen da hannu ya mata alama da ta koma ta zauna, jiki a sanyaye ta zauna tana fad'in" wa'alaiki salam, la mamma ni ce, ina kwana" a dak'ile la mamma ta amsa da" lafiya lau" cikin farin ciki Ummi tace" la mamma ina Abba da su Islam duk Suna lafiya?" lafiya lau suke" jikin Ummi ne ya danyi sanhi jin amsar da Mahaifiyarta take bata hakan yasa tace" la mamma ko dai fushi kike da ni?dan Allah kuyi ha'kuri wallahi la mamma ba nida laifi, kawai Alhaji yayi kuskuren fahimta ne amma ban aikata komai ba" hawaye ne suka fara biyo fuskarta Salman ko sai wani b'ata rai yake yana hararanta, la mamma ce tace" kinga ni yanzu banda lokacin wannan maganar, koma miye ai aikin gama ya riga da ya gama tunda kin ja mamu fad'a, ta kai har gaisuwar mu yanzu Alhaji baya amsawa ni da Mahaifinki, kuma kinga ke ma kinci riba tunda yanzu haka ya kafa ma kowa doka akan kar wanda ya kuskura yaje gidanki ko da cikin yara ne, kuma ke ma yace kar mijinki ya yarda ya kawoki cikin iyalenshi dan baya buk'atar ki yanzu." tana gama fad'a ta kashe wayar saboda kukan daya taho mata, tana kashe wayar Ummi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Salman karb'ar wayar shi yayi ya fice ya bar mata gidan shi kam ko a jikinshi.

Haka ta wuni jiki babu k'wari ko girki bata yi ba tunda Salman ba zai dawo ba, haka yamma tayi ta fara shirya mashi abin bud'a baki ba tare da ita taci komai ba, ta kammala da wuri yana zuwa ta shirya komai haka ta kula da duk wani abunda zai ci har ya fita bayan sallah isha'i sannan tayi wanka ta zauna tsakiyar gado ta nata runguzar kuka kamar yarinya saboda takaicin abinda ya isheta.
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑

_Samira Harouna_

```Luv you my fans```


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜 🤛

*Page*

4⃣3⃣-4⃣4⃣


Ko da ya shigo d'aki ya sameta tana ta faman kuka saï sharbar majina take alama taci kukan ta koshi, zaune yayi yana fuskantar ta yace" wai har yanzu kuka kike? to miye la mamma ta fad'a maki ne haka?" dama tana neman wanda zata fad'ama damuwarta ko zata d'an rage zafi sai ko ta fara magana cikin kuka" yaya Salman wai miyasa Alhaji yake mana haka ne, miyasa baya k'aunar mu, miyasa har yanzu shine mai alhakin ruwa da tsak'i a al'amuran mu, miyasa baya fahimtar soyayyar dake tsakanin Iyaye da yayansu shi kawai kansa ya sani.?"

"Ka duba kaga abinda ya min, ya min aure bada sani na ba ba tare da na shirya ba na hak'ura, amma saïda ya kawo ni gidan miji kawowar da bana jin akwai wata ya mace a tarihin duniya da aka tab'a mata ita sai ni shi ma na hak'ura, amma bai ishe shi ba shine yanzu zai zareni daga cikin yan uwana ya hana ni zuwa inda suke, kuma suma ya hana su zuwa inda nake, wannan wace irin uk'uba ce dan Allah, wallahi ni ba zan iya zama a gidan nan ba yaya Salman, ni dole na tafi gidan mu dan in na zauna nan to kasheni za kayi da duka" rigar baccin da ta saka ta tub'e da k'arfi tana nunawa Salman jikinta da fuskarta tana fad'in" ka duba ka gani yaya Salman jikina duk shatin bulala ne, dukan da Alhaji yasa aka min a gaban mahaifana da kuma wanda kai kamin, wallahi ba zan iya zama a gidanka ba yaya Salman saboda bâ kada imani ko kad'an k'eta kawai ka iya" fad'awa tayi jikinshi tana kuka da k'yar Salman yasa hannu ya fara shafar bayanta amma da ya ji laushi sai ya fara mata wani salon shafa har yana 'ko'karin kaiwa a k'irjinta dan haka ta d'agashi ta kwanta akan gado taci gaba da kukanta, a kasalance Salman ya koma d'akinshi ya kwanta gaba d'aya ta rikita mashi lissafi ko kad'an bai iya tuna abinda ta fad'a ba, shauk'in da ya ji lokacin da ta rumgume shi kawai ya keji, da k'yar bacci ya d'aukeshi cikin wannan mawuyacin halin da bai taba jin irin sa ba a rayuwar shi.

23:00 Ummi ta shigo d'akin cikin sallama da muryarta data dakushe wajen kuka, har ta aje faranti ta zuba mashi duk yana bacci bai san ta shigo ba, saida ta daddab'a pilow da yake kwance sannan ya tashi aje masa tayi ta ta koma d'akinta.


Tun 07:30 Ummi ta kammala had'a abun karyawa amma bata ji d'uriyar Salman ba haka ta zauna tana jiran taga fitowar shi, 09:20 ya fito da dogon wando sai singlet fara k'al kallonshi Ummi tayi ganin ba wani shiri bane yayi amma ya yi masifar had'uwa a cikin zuciyarta tace(na tabbata yaya Salman bâ yada burin auren mace irina, shi ma zaiso ace ya auri kyakyawa kamar shi amma Alhaji ya masa yankan k'auna).

Zaunawa yayi ya karya dan Ummi har tayi nata break d'in, yana idawa yace mata" ki fito min da kujera waje" yana wucewa ta mik'e ta d'auki d'aya daga cikin na dinning ta kai masa zata juya ta tafi yace" zauna nan" jujjuyawa tayi ganin babu wata kujerar yasa tace" bara na d'auko kujera" kallon daya mata yasa ta cire takalminta ta zauna in da ya nuna mata, k'afa ya d'ora mata a cinyarta tare da mik'a mata abin yankar akaifu kallonshi tayi baki bud'e tace" wannan kuma fa, miye haka?" bai tanka taba hakan yasa ganin babu wasa a al'amarin yasa ta fara masa gyaran akaifun, kuma abin takaicin ma babu wani abinda za'a cire haka kawai tayi iya yinta ta cire na cirewa tana idawa dana k'afa ya mik'o hannu, nan ma Kallon shi tayi tace" yaya Salman wai miya samu hannayen naka?" Hararan ta yayi yace" wallahi zan zubar maki da hak'ori" turo baki tayi ta rik'e hannun, Kallonta yayi ya kalli hannunta saboda wani sanyi da ya ji tattausan hannun Ummi ma'abocin zufa a kowane yanayi zafi da sanyi, haka hannunta yake cikin zufa kowane lokaci, sab'anin nashi mai cikakkar tsoka da dogayan yatsu da santsi haka Ummi ta gama masa gyaran tsaf tana idawa yace" to maza kije d'akina ki d'auki d'aya daga cikin jakunkuna da ke da kwai ki shiryamin k'ananan kayana a ciki da duk wani abu da mutum zai buk'ata idan yayi tafiya." kai ta dafe cike da nuna damuwa kafin tayi magana yace" ba zaki yi ba ko?" kai ta girgiza sannan ta wuce jiki a sanyaye, Saïda ta b'ace ma ganinshi sannan ya kau da kanshi.

Tsaf Ummi ta had'a mashi kayanshi tare da duk abinda zai buk'ata, kama daga turare maclean brush mai zanin rufa kayan bacci ect...., tana idawa ta shiga cuisine dan had'a abincin rana dan 12:50 tayi, tana cikin aiki ya lek'o yana fad'in" ina aikin dana saki?" cikin sauri tace" na kammala suna d'aki" hararanta yayi yace" amma ba kisan ki ce kin gama aiki ba idan an saki?" turo baki tayi tace" kayi ha'kuri"wucewa yayi ya barta, d'akinshi ya shiga ya bud'a kayan sosai ya ji dad'in ganin yanda ta had'a masa kayan ba tare da ya nuna mata ba harda ma abinda shi kanshi bai taba tunanin d'aukaba duk lokacin da zaiyi tafiya wato maclean da brush, duk lokacin da yayi tafiya saidai ya siyi sabbi idan zai taho kuma ya baro su dan sun gama mashi aiki, wanka yayi ya shirya cikin dogayen kaya da hula yayi kyau sosai yana fitowa ya k'walla kiran Ummi har tuntub'e take wajen sauri tana zuwa ta zube k'asa tana fad'in

"Gani"d'auko min sallaya" mik'ewa tayi ta d'auko mik'a masa tayi, hararanta yayi yace" bara na sunkuya saina karb'a ko?" turo baki tayi sannan ta sunkuya ta mik'a masa, yana karb'a yace" wuce muje " binshi tayi tana guna-guni har saïda ya shiga mota sannan yace" oya, kimin Addu'a zan fita" dalala ta kalleshi tace" yau dai da alama bokan naka ce maka yayi saina maka addu'a sannan harkokin zasu tafi yanda ya kamata ko?" cikin zafin rai ya bud'e k'ofar mota yana shirin fitowa, da sauri ta maida k'ofar ta rufe tana fad'in" sai ka dawo to" juyawa tayi zata wuce yace" ke wannan ce addu'a, haka ake a garin ku?" murgud'a baki tayi tace" in dai sai na maka addu'a zaka tafi, to ka kwana anan" da gudu ta shige d'aki, shi kuma k'wafa yayi yaja mota yana fad'in" lallai da sauranki har yanzu, amma zanyi maganinki nan ba da d'ad'ewa ba."


Tana gama aikinta tayi sallah tana idawa ta shiga gyaran d'akinshi tana kammalawa ya dawo gidan, saïda yaci abinci sannan ya shiga d'aki ya tattaro mata kayanshi k'anana yace ta wanke, saida tasha mari sakamakon cewa da tayi" haba dan Allah wannan wane irin rashin imani ne? wannan kayan ina zan iya wanke su, nifa ko a gidan mu bana wanki bare kuma nan" bakinta ya murd'e yace" nan ai ba gidan ku bane gidan mijinki ne, kuma daga yau karna saké jin kince min mara Imani, in kuma ba haka ba wallahi saina sauke maki Kafad'a"

Please Login or Register in order to submit comment