Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannun ya d'aga mata tare da fad'in "tsaya tsaya, dan Allah ki dinga yi a hankali kinji saboda abinda ke cikinki."

Kukan shagwab'a tasa tana fad'in "ni wallahi ku mayar dani gidanmu wajen Mamana tunda yanzu kun bar sona tunda na samu ciki sai shi kuke so."

Janyota yayi ya rumgume yace "haba Mamar 'yan biyuna, ni na isa na daina sonki ai sai dai in babu numfashi na."

Kafin tayi magana yayi sama da ita suka fita daga d'akin sannan ya ajeta ya rufe d'akin suka wuce, sosai Ummi taji dad'in fitar dan yawo sukayi sosai har bakin ruwa saida ya kaita, sunyi farin ciki sosai saida yamma sannan suka hau taxi suka ciro ticket sannan suka dawo gidan hannun Ummi d'auke da ice cream da bonbon mai tsike, dan kuka ta saka mashi da yak'i ya siya mata ice cream d'in, amma gashi har yanzu bata ko lasa ba bare tasha.


Tunda ciki ya shiga wata na shida sai laulayi ya dawo mata sabo pil a leda, cikin wata shida kamar na wata takwas sosai yayi girma, haka ta dinga fama kullum da abinda zata ji sabo ga nauyin jiki kasala duk ta hargitse kamar ba ita ba, duk wani abu na jikinta bata san tab'ashi hakan yasa kanta ta daina kitso yankan farata kuma Salman ne ke mata dan bata iyawa, wanka kawai take da k'ok'arin yin saboda bata so mijinta yaji wani odeur daba k'amshi ba a jikinta, shima babu sabulu sai dai tayi tsaye ta kunna panpo ruwa na zuba in ta gaji ta kashe ta fito ta shafa turare, Salman ne ke mata da sabulu in zaiyi, kaya kam ko kad'an yanzu ko atamfa ta daina sawa bare less ko shadda kullum cikin dogayen riguna take na kantie marasa nauyi.

```CIKI SAYIN MATA```


Kwana tashi a wajen Allah babu wuya, haka har cikin Ummi ya shiga wata na *TARA* daga lokacin kuma Mama ta hana tafiya tare da suke tunda lokacin haihuwarta ya kusa, shi ma kuma tunda ta shiga watan haihuwarta ya tsaida duk wasu harkoki da zasu sa saiya bar gari ya maida hankalinshi akan jaririyarshi.

Masha Allah cikin Ummi shine rigani kwana, dan yanzu kam idan ta zauna to sai an had'a da addu'a take tashi tsaye, sosai sosai cikinta yayi girma ga tsini k'afafu kam sukace ja bani wuri saboda kumburi kai kace iska ne aka busa mata, amma duk da haka sai cikin yasa tayi kyau a fuska ga haske kamar wacce bata da jini a jiki, Mama da Salman tausayinta suke kullum haka suka duk'ufa wajen rok'on Allah ya sauketa lafiya, kuma har yau Salman Mamar 'yan biyu yake kiranta dashi.

Koda taje likita aka fad'a mata nan da sati biyu zata iya tsammanin jiran haihuwa, koda tazo gida ta tada hankalin Salman saiya kaita gida ta haihu acan, bai mata gardama ba ya kaita gida wajen La Mama, daga ranar suka tare can da zama har Salman d'in, yau ta kama asabar d'in k'arshen wata ana reunion gidan Alhaji, amma La Mama ta hanata tafiya saboda ganin yanda tayi wata iri da ita kamar dai ace mata ta haihu kuma ta haihun.

Haka akayi rΓ©union Ummi kuma bata damu ba dan ita tasan abinda take ji, ana sallah la'asar su Jawahir Nadiya Khairat Hafsat suka zo wajen Ummi anan suke fad'a mata wani sabon tsari da taji dad'inshi sosai, wai Alhaji ya dakatar da auren Islam da Abdul dan yaji abinda Soumayya ta fad'a watak'ila kuma maganar daga manyanta taji shi yasa ta fad'a ita ma, Abdul kam yana son Islam sosai hakan yasa baiji dad'i ba yaji kuma Soumayya ta bashi haushi, abin mamakin ma shine cewa da Alhaji yayi idan Islam d'in tana da wanda take so ta fito dashi tunda babu wani matashin saurayi daya isa aure, hakan ba k'aramin k'ara b'atama wasu rai yayi ba dan a ganinsu yanzu ma shige da ficen ne akayi shi yasa haka ta faru.

Sun jima suna tattaunawa kafin suka tafi La Mama kuma ta shigo, tunda taga Ummi tasan lokaci ya kusa tunda dama kwana goma sha d'aya kenan a cikin sati biyun da aka bata, kallonta kawai take tana yamutsar fuska tare da cije leb'e amma ba tace mata komai ba, har bayan sallah isha Salman ya shigo gidan ya zauna kusanta ya mik'e k'afafu yana kallonta cike da tausayawa, ganin yanda zufa keta keto mata har ta kai fitowa take, ko uffam ta kasa cewa sai jujjuya kai take yi haka har La Mama ta kawo masu dafaffen naman kai data dafa.

Gashi dai Ummi tana so ta ci amma ina ta kasa, a hankali Salman ya dinga dib'a yana sa mata baki, amma koda ta karb'a sau uku bata k'ara na hud'u ba, cikin rarrashi yace "haba Mamar 'yan biyuna ki k'ara mana ko kad'an ne."

Kamar za tayi kuka tace "La Mama ki fad'a masu su daina cemin Mamar 'yan biyu."

Bud'ar bakin La Mama cewa tayi "haba Ummi wannan girman ciki naki masha Allah in baki haifi 'yan uku ba ko yan hud'u, ai dai kya haifi 'yan biyu."

Salman bushewa yayi da dariya yace "ahan, kinga ashe La Mama ma kallon Maman 'yan uku da hud'u take maki."

Ba tayi magana ba Islam ta shigo hannunta rik'e da Ihsan autar Sa'ada, wajen Ummi ta zauna tana mata magana amma ko jinta ba tayi, Salman ne yace "Ihsan ki rabu da auntynki bata lafiya nak'udar 'yan biyu take." ya fad'a yana shek'ewa da dariya.

Cikin d'umin yara Ihsan tace "eh tonton, ai kasan aunty 'yan biyu zata haifa ko?"

Cike da fara'a yace "ashe kema kin sani, to waya fad'a maki?"

"Wallahi ko tonton 'yan biyu ne ni da kaina na gani."

Dariya La Mama tayi tace "shi kenan ya tabbata 'yan biyu zaki haifa insha Allah, sai dai fatan Allah ya sauke ki lafiya sannan muga mi zaki haifa."


Tun Salman na hira da Abba ya lura da Ummi bata jin dad'i sosai, haka ma Abba yana kallonta duk saiya ji tausayinta ganin yanda ta canja k'afafu a mik'e ko motsin kirki bata iya yi, ai kam sai nak'uda tace salamu alaiki Ummi gadan gadan ta taso mata, tuni suka d'auketa sai asibiti yayin da Mama dasu Hajiyoyin Alhaji suka biyo bayansu, 22:30 suka je asibiti amma cikin ikon Allah da addu'o'in iyaye sai ga santalen santalen kyawawan yara maza guda biyu an fito ma dangi dasu waje su gani da misalin k'arfe 23:40.

πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

```FARIN CIKI KENAN```

'Yan biyun farko kenan a cikin famillyn Alhaji Manu mai dala (tsoho mai ran karfe), irin farin ciki da walima tare da kyaututtukan da 'yan biyu suka samu basa misaltuwa, mahaifin yara bakinshi ya kasa rufuwa komai siyowa yake wa yara da mai jego, ya bawa Ummi kyautar yaran dukansu saboda bai san me zai bata ba, amma matsayinshi na uba yayi alk'awarin kula dasu, haka aka gudanar da suna aka kashe kud'i sosai Ummi ma tayi bajinta dan ba komai take cewa Salman yayi ba ita ma nata kawai take yi da guminta.

Yara sun samu suna ```MOHAMED TAUFIK' da ```MOHAMED RAFIK', Allah ya rayaku akan sunna.

Kwana biyu da biki Inna da aunty Fateema suna shirin tafiya, Salman ya shigo d'auke da ledoji biyu d'ayar ya bawa su Inna d'ayar kuma ya mik'awa Ummi wai na 'yan biyu ne, tana bud'awa kayan yara ta kuma gani kuma abin dariyar kowane iri hud'u hud'u, cikin jin haushi Mama tace,

"Wai kai miye haka, abu kamar hauka ina ma laifin ka siyo kala biyu, amma saika siyo kowane har hud'u hud'u, duk me za ayi dasu ka duba kaga gudan tarin tilin kayan da yaran nan suka samu fa."

"Ayi hak'uri Mama, ai sai a aje ko wasu an bawa idan anyi haihuwa." cewar Ummi da taji babu dad'i kalaman da Mama ke fad'ama jarumin nata.

Haka suka dinga tafiyar da sabuwar rayuwarsu tare da yaransu masu kama da mhaifinsu sai dai kumatunsu suna lotsawa ko murmushi sukayi kamar dai mahaifiyarsu haka kuma jikin mahaifiyarsu dan 'yan lukutayene yaran, Islam da Momy ne suka zauna gidan bayan tafiyar mai tsaronta suke tayata kula da yaran, gashi har yanzu bata iya masu wanka ba sai Salman keyi masu, nono kad'ai ke had'ata dasu da sunsha su Momy zasu karb'e su suyita jagula sai in sunyi bacci kawai, idan kuma babansu ya dawo to suna hannunshi dan ko bacci sai dai ya d'orasu akan k'irjinshi yana shafasu har suyi bacci.


```Muje zuwa```πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹
29/03/2019 Γ  20:22 - Mamar LatifπŸ’ƒ: πŸ’‘AUREN HA'DI πŸ’‘

_Samira Harouna_


*FIN*
```{k'arshe}```


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

*Page*

9⃣9⃣-1⃣0⃣0⃣

πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

Salman ne zaune k'asa ya mik'e k'afafu yasa robar wankan yara tsakiyar k'afafunshi da Taufik' a hannunshi yana masa wanka sai lumshe ido yake alamar bacci yake ji, Ummi kuma na gefensa da Rafik' tana shiryasa cikin k'ananan fararen kaya masu kyau, masha Allah yaran sun girma dan har sun iya zama suna k'ok'arin fara rarrafe, wasa take masa shi kuma yanata dariya yayin da kumatunshi keta lotsawa ciki kamar na Ummin, doguwar hammar da Salman yayi ce yasa ta kalleshi amma ba tace dashi komai ba, saida ya k'arashe sannan tace "haba 'yallab'ai irin wannan doguwar hamma haka, duk ta kwanan ce?"

Cikin muryar bacci yace "Eh mana, ya kike so nayi to? tunda kin kasa barina nayi baccin."

Tab'e baki tayi tace "hum, to nidai ku kula karku sakawa yarona kunfa a hanci, dan in haka ta faru ba yarda zanyi ba." ta k'arashe tana murguda baki.

Kallonta yayi yace "ke yanzu ko kunya ba kiji ba da ki kace d'anki, to d'anki dawa ya baki?"

Cikin kuri tace "Allah ne ya bani."

Ci gaba yayi dayi masa wankan yana fad'in "hum, amma kuma har yanzu baki san yanda zakiyi kiyi masu wanka ba, watansu biyar a duniya amma bana jin kin tab'a masu wanka ko sau d'aya."

Turo baki tayi gaba tana fad'in "to ai dai zan iya nima, kuma kune ku kace kun d'auki alhakin yi masu wanka , dan haka ni kuma bana masu."

Kallonta yayi yace "shi yasa kenan kike tayar dani daga bacci yanzu dan nayi masu wanka?"

"Eh mana." ta fad'a tana sumbatar kumatun Rafik' data gama masa shirinsa.

Yana gama d'auraye ma Taufik' jikinshi ya sakashi cikin towel ya mik'a mata ta karb'a dan ta shiryashi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "dan Allah kiyi zuciya ki iya yi masu wanka da kanki, sannan zanje na kwanta kiwa Allah karki tasheni ki bari na k'arasa hantsewa."

Hararan sama da k'asa tayi masa kafin tace "sannu, na barku kuyi bacci?ai bazai yiyu ba tunda baku gama dani ba."

Dafe k'ugu yayi da duka hannayenshi biyu yace "duk ni kad'ai keda wannan hararan?to na gode, amma dan Allah ki barni na huta, kefa kinfi kowa sanin gajiyar dana deb'o kuma ban shigo garin nan ba sai cikin dare har kunyi bacci, amma shine duk da haka kin kasa barin mijinki ya huta."

Dariya tayi tace "shikenan kuje ku kwanta, ba zan tayar daku ba, amma zan shigo kumin wanka ku shiryani saboda lokaci yayi na tafiya gidan Alhaji, ko kun manta yau k'arshen wata ne?"

Wucewa yayi yana fad'in "to ni dai zan kwanta ba yanzu zanje ba saina huta gajiya."


Tana gama shirya Rafik' cikin shiga irinta Taufik' ta ajiyeshi kusa da Taufik', ita kuma ta d'auke robar da akayi masu wankan ta gyara wurin sannan ta aje masu kayan wasa a gabansu ta sunkuya tace masu "zanje wajen papanku yamin wanka, kuyi wasa kafin na dawo."

Tana fad'a ta shiga ciki, kwance ta sameshi cikin blanket, yaye blanket d'in tayi ta haura kan gadon ta hayeshi ta fara mashi magana cikin kunne "ku tashi kafin na tayar daku."

Saida ya k'ara dunk'ulewa yace "um um, ba zan tashi ba, dan Allah ni ki d'agani kin wani zo ki sakar min nauyinki."

K'ara mak'alewa tayi a jikinshi tace "wallahi ku tashi kafin na tayar daku, kunsan dai zan iya ko?"

"Nak'i d'in, kiyi abinda za kiyi." ya fad'a yana tutsa kanshi tsakiyar pillow.

Dagewa tayi iya k'arfinta ta fara k'urma mashi ihu cikin kunnen b'arin dama, k'ok'arin rufe kunne ya fara dan haka ta rik'e hannayenshi duka biyu, haka suka dinga turmushe turmeshe akan gadon saida yayi sarander ya d'aga hannayenshi yana fad'in "shikenan nayi sarander."

Kafin tayi magana ya juyo ta yanda yake fuskantarta hakan yasa tayi zaune akan k'ugunshi suna kallon juna, hannayenta ya kama yace "naga ke har yanzu baki san kin girma ba, kullum k'ara yarinta kike yi alhalin kin aje yara har biyu a gabanki."

Saida ta masa fari da ido tace "girma fa? to ina abin yake, ni d'in ta nawa ce da har zan maida kaina tsohuwa? ai ko ku da kuka girmeni ba za kuce kun girma ba bare kuma ni."


Wani shu'umin kallo ya mata yace "ni kam na tsufa yanzu na bar maki duk wani girman, ni dake da yara a gabana an kusa kawo min surukai."

Itama wani kallon ta masa tare da sunkuyowa kusan kunnenshi ta dinga mashi wani irin salo mai d'aukar hankali, hannunta tasa ta fara shafar duk wata gab'a da tasan tana tayar masa da sha'awarsa, yayin da kuma ta dinga motsa mazaunanta akan k'ugunshi da take zaune akan, cikin wata irin murya tace "fad'a min, me kuke ji a halin yanzu?"

Kasa magana yayi sai mik'ewa da yake yana rufe ido tare da cije leb'en k'asa, hakan yasa ta kalli fuskarshi ganin halin da yake ciki yasa ta kama leb'enshi na k'asa tad'an ciza a hankali lokaci d'aya kuma ta saki ta kama kunnenshi tana lasawa, saida ta gama rikita mashi lissafi yakai mak'ura wajen san abinda take masa, kawai tayi saurin direwa daga kan gadon da sauri ya murgino ya rik'o hannunta, tana had'a ido dashi ya mata alama da ido akan ta dawo, kai ta girgiza masa tace "wanka zanyi lokaci na tafiya."

Da idon shinnan kamar na mayu ya sake mata alama da tazo, Ummi kam sai taji ya bata tausayi saboda yanda duk taga yayi wani iri yakai k'uloluwa wajen tashi, murmushi tayi tace "kufa ku kace kun tsufa, amma ya haka daga d'an abinda bai taka kara ya karya ba sai duk ku fita hayyacinku."

Janyo hannunta yayi da k'arfi ta fad'o kan k'irjinshi, cikin zafin nama ya juye da ita ya mata runfa yana fad'in "yaushe nayi tsufan da har zan kasa azabtuwa da salonki mai rikita duk wani namiji mai cikakkiyar lafiya?"

"To amma ai kun tsufa shekara arba'in fa ba wasa bace."

Kallonta yayi da ido waje yace "ke, waye yayi arba'in d'in, duka duka fa talatin da shida ne gareni, ai ni yanzu ma nake jin wata sabuwar k'uruciya, dan duk lokacin da kika kusantoni to na kan ji wata sabuwar wuta na ruruwa a gaba d'aya illahirin gabb'an jikina."

Yana gama fad'a ya fara aika mata da nashi sak'onnin cikin salo da k'warewa, haka suka lula wata duniyar suka manta da yaransu dake falo har saida suka samu kansu sukayi wanka suka fito sannan suka fito wajen yaran cikin shirinsu ta shigar farin kaya.


Kasancewar yaran ba suda rigima yasa suka tarar dasu kowa ya kama gabansa duk suna k'ok'arin d'auko abinda yayi masu nisa alamar rarrafe suke san yi, Taufik' ta d'auka shi kuma ya d'auki Rafik' sannan suka fita daga gidan, haka Salman ya d'ora Rafik' a k'afafunshi kuma yana tuk'i har suka kai gidan Alhaji.


Suna shiga gidan yara sukayo masu cah kowa na k'ok'arin karb'ar yaran, haka aka rabasu dasu sukayi cikin gidan dasu suna murna, su Ummi kuma gaisawa suka dingayi da iyaye da sauran 'yan uwa yayin da kowa ke tambayarsu ya yara, suna shiga babban falo suka tarar dasu Jawahir dasu Nuseiba Rumana dama Soumayya, kallonsu sukayi da gani ba magana kasan ma'auratan suna cikin farin ciki , bugu da k'ari ga wata k'iba mai birgewa da dukansu sukayi fatarsu ta kwanta sosai, musammam Salman da kyawunshi ya sake bayyana hakan yasa Ummi fargaba, dan tasan dole wasu matan zasu dinga kawo masa farmaki, kuma ta sani tunda ba kyawun fuska gareta ba za'a iya samun wata data fita zata iya shiga tsakaninta da farin cikinta, wannan ne yasa ta dage sosai wajen ganin ta kyautata masa ta kuma cika zuciyarshi da soyayyarta da farin ciki tare da kewarta a lokacin da yayi nesa da ita.

Da gani kasan arzik'i ya kwanta fiye da baya, kallo d'aya za kama less d'in dake jikin Ummi kasan cewa tsadaddene haka ma gyalenta da takalmanta da jakarta duk jajaye kalar duwatsun da aka mata ado dasu a rigarta, har saida Salman ya zauna Nuseiba bata daina kallonshin ba cike da birgewa dan har yanzu bata daina jin ina ma ace Salman ne mijinta, yaranta uku amma har yanzu tana son yaya Salman, su Momy da Islam ne suka shigo d'auke dasu Taufik' Hajia takwarar Ummi ce ta karb'i Taufik' mahaifiyar mahaifin Ummi da Salman ne wato (Hajia babba) ta karb'i Rafik'.

Hira suka fara yayin da Soumayya zuciyarta keta tafasa saboda bak'in ciki, ko kallon Ummi da yaranta bata san yi Rumana kam rayuwarta take bata damu ba dan dama bata sa a kai ba, Jawahir ce ta kalli Salman ta kalli Ummi tayi murmushi tana fad'in,

"Duniya kenan, yau ga Ummi da Salman a inuwa d'aya a matsayin ma'aurata masu k'aunar junansu."

Dukanta Ummi tayi a kafad'a tace "ke kuma da tashin tashina, miye na tado abinda ya wuce?"

Khamis ne ya harareta yace "karki sake dukar min mata, an tuna bayan."

Salman ne ya doki kafad'arshi yana fad'in "an doka d'in me zaka yi?"

Jawahir ce tace "wannan fa zalinci ne, kawai dan kuna gaba damu sai ku dinga d'irkanmu."


Hajia babba ce tace "to ai dole ne Ummi, dan idan aka had'a rayuwarku ta dah data yanzu dole kowa zaiyi mamaki, kullum idan muka ganku sai mun tuna da shiriritarku ta baya."

Kallon juna sukayi da Salman lokaci d'aya suka k'yabtawa juna ido tare da siririn kiss, dariya tayi tace "to Hajia ai dai aikin gama ya gama sai a daina tuna baya."

Hajia Abu ce tace "ank'i a daina tuna bayan, rayuwa in ba'a d'an tab'o abinda ya faru baya ai babu armashi."

La Mama ce tace "to ai bata da gaskiya ne shi yasa take so abar maganar."

Mama ce tace "ai shine mai laifi tunda shine mai dukanta ko ba tayi laifin komai ba."

Daga gefe Salman yace "haba Mama ta yaya za'a doki mutum baiyi laifi ba, ai da kunga na daketa to wani abu tamin."

Hararanshi Mama tayi tace "dubeshi dan Allah har wani dad'in fad'a kake ji."

Sa'ada ce tace "kuma su La Mama ai kun zama kamar b'era da mage idan su Ummi suna tare kuma saiku koma mafad'ata."

Dariya akayi Abba ne da Rafik' ke hannunsa yace "to ai kowa akwai team d'in da yake, kowa baya so aga laifin nashi."

Alhaji dake zaune a kujerarshi yana kallon kowa yace "to waini abinda ma ban gane ba, bansan miye ya haddasa wannan rikici ba a tsakaninsu? ni dai naga kawai suna fad'ansu."

Kallon juna sukayi ita da Salman sukayi dariya, Ummi ce tace "to nima dai ban sani ba, amma ku tambayi papan 'yan biyu kuji."

Wata harara Soumayya ta jefi Ummi da ita ta gefen ido jin abinda ta fad'a, Salman kam cewa yayi "a'a nima ban sani ba, ke zaki iya tunawa."

Hajia babba ce tace "uhum, kun gani ko, a k'arshe ma basu san akan me suke wannan shirmen ba kawai rashin hak'uri ne da k'uruciya dake damunsu."

Ummi ce tace "a'a Hajia, ni dai nasan cewa a waccen lokacin yaya baya san ana murgud'a masa baki da harara, uwa uba kuma ka masa tsaki, to ni kuma kawai saina ji inayi idan muna tare dashi amma bawai dagangan nake ba."

Wani kallo Salman ya mata yace "ai ko yanzu bana so, kawai dai na daina dukane yanzun saboda na samu hanyar da tafi ta dah."

Wani kallo Ummi ta masa tare da wurga mashi ido alamar akwai mutane fa, Alhaji ne yace "to koma dai miye yanzu ai gashi nan suna zaune lafiya kamar ba sune lokacin da aka d'aura auren suketa kururuwa ba suna fad'in basa so, amma yanzu na tabbata da za'a ce a rabasu to sai dai ku jisu a asibiti."

Abin mamaki bakin Salman dana Ummi ne suka had'u wajen fad'in "sai dai k'abari."

Tin tsirewa akayi da dariya Hajia ta d'ora da "ja'iran yara kawai, ku kun d'auka *AUREN HA'DI* da ake maku ana maku dan ba'a sonku ne, amma idan har zakuyi hak'uri kuyi biyayya to ku zaku fi kowa jin dad'inshi da moriyarshi."


Saida akayi sallah azahar aka ci abinci sannan Alhaji ya tara iyalin nashi ya masu nasiha tare da gargad'i da mahimmancin had'a kansu, ya kuma nuna masu da lokacinshi ya kusa dan haka yace "yanzu ya rage naku ku ci gaba da had'a 'ya'yanku aure, ko kuma ku barsu su auri zab'insu, amma ni dai Allah ya sani nayi yina wajen ganin na had'a kan iyalina na k'ulla zumunci a tsakaninsu ko bayan ba raina, wasu tunaninsu kawai ina masu *AUREN HA'DI* ne saboda ina gaba dasu da iyayensu, amma ba haka bane babban dalilina shine naga kun tashi kanku a had'e kuna son junanku sannan ranar lahira fiyayyen halitta (S A W) yayi alfahari da zuri'ata, da wannan nake bawa duk wani wanda nama ba daidai ba hak'uri nake kuma neman yafiyarku."

"Sannan ku zama tsintsiya mad'aurinki d'aya, ku had'a kawunanku ta yanda babu wani mahaluki da zai iya ganin bayanku, kar wanda ya ware kanshi daga cikin 'yan uwanshi dan duk lokacin da wani bala'i ya taho, to zai fara tunkarar wanda ya ware kanshi shi kad'ai, dan Allah ku zama masu k"aunar junanku kuso junanku ku zauna lafiya, dan da hakane zan samu kwanciyar k'abarina cikin lumana, sannan ina rok'on duk wanda yaji dad'in abokin zaman dana had'ashi dashi, to ya aikamin da sak"on addu'a a k'abarina a lokacin da nabar duniya, dan shine kad'ai tukuicin da zaku iya yimin."

"Sannan daga yanzu na daina saka hannuna a al'amuran da suka shafi rayuwarku, kowa zai iya cin gashin kanshi amma kuma kowane mahaifi ko mahaifiya zata iya yanke hukunci akan d'an da koda ba daga cikinka ya fito ba, haka kuma duk wani daya girmema wani koda da kwana d'aya ne to yana da damar da zai iya tsawatarwa dana k'asa dashi, da wannan nake cewa Allah ya maku albarka, Allah ya albarkaci rayuwarku, Allah ya had'a kawunanku, Allah ya sakama zuriarku albarka, Allah ya kareku daga sharrin masharranta, Allah ya kawar da idon mak'iya daga kan wannan zuria tawa mai tarin albarka, duk wani mai son ganin bayanku Allah shiryashi idan mai neman shiriyane, idan kuma ba haka ba to Allah ya mana maganinshi."

Kamar yanda suka dinga amsa masa da ameen, haka a k'arshen addu'ar ma suka amsa da "ameen."

Ana gama sallah la'asar kowa ya koma gida, Mama da k'yar ta basu 'yan biyu suka tafi dan ji take kamar su bar mata su su kwana anan, suna zuwa gida Ummi ta cire masu kayan ta saka masu marasa nauyi itama ta canja sannan ta shiga girki.


Salman na kwance akan gado yana kallon tv da bai jima da yasa aka mak'ala mashi ita ba, remonte ce a hannunshi ko riga babu a jikinshi sai dogon wango, Ummi ce ta shigo d'akin cikin wata had'add'iyar kwalliya mai d'aukar hankali, doguwar rigar bacci ce a jikinta kad'an ya rage ta sauka k'asa sai dai shara shara ce da siraren hannuwa, best colour d'in da Salman yafi sone wato bleue sai fari da bak'i sosai rigar ta mata kyau, ga wasu dogayen takalmi data saka suma bleue sai gashinta data saki ya sauka a bayanta, tafiyar da take yi ce ta d'auki hankalinshi sosai bai d'auke ido daga kanta ba har saida ta cire takalminta tabi ta kanshi ta kwanta gefenshi suna kallon juna.

Wani hamshak'in murmushi yayi mata tare da fad'in "wannan kyau haka, kinga yanda kika had'u, ai da farko ban ganeki ba na d'auka wata sabuwar amaryarce Alhaji ya auramin ban sani ba."

Wata yar k"aramar dariya tayi hakan yasa ya lotsa hannunshi a dinple d'inta, cewa tayi "ai ko a mafarki idan kaga wata mace ta shigo d'akin nan, to ka tabbata ZEINAB ce, wato Umminka."

Janyota yayi jikinshi ya rumgumeta suna

Please Login or Register in order to submit comment