Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*



By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My soul mate. My Sweetheart Mamahh*




*71-75*

*Mai hankali yakan gane ko wane ne kai daga maganar da kake yi a kan mutane ba daga ma ganar da mutane suke yi a kan ka ba.*




TV ya kunna ya rage volume yana kallo yana kallon ta sai rubutu take. Cikin minti latalin ta gama ta mika masa. Ta ce
"Nagode!"

"Uhmm please ungo amson maltina a cafeteria."
Kin amsar kudin tayi tace zata siyo masa.

Kai ya girgiza ya ce,
"A'ah nagode karbi ki siyon ki siyo kema."

Amsa tayi ta fice ta bar jakar ta agun. Tana fita zainab ta taso ta ce,
"Ya akayi?"

Murmuahi tayi ta ce,
"Yayi min. Maltina zan siyo masa wai."

Suka wuce cafteria suka siyo masa sanna suka dawo.

Sabir kuwa Asma'u na fita ya bita da kallo sannan ya lumshe ido.

A ransa ya na fadin.
"Allah ka dauran abinda zan iya dashi."

Yana mamakin duk rashin son maganar sa inda ya zauna yana tai mata wadan nan tambayoyin.

Murmushi yayi tuno yadda take bashi amsar su.

Yana nan zaune yaji knocking din ta. Izini shiga ya bata ta shigo.

Tana shigowa ta mika masa maltinar sannan ta dauki jakar ta ta kara masa godiya ta juyo zata fita

" *Husnah* "
Ya kira sunan ta.

Juyowa tayi, table ya nuna mata ta dawo tayi wajen.

Kallon sa tayi ta ce,
"Me zan miko maka?"

Murmushi yayi ya ce,
"Dauki wannan fulas din kije kici."

Kai ta girgiza ta ce,
"Nagode sir!"

Hararar ta yayi ya ce,
"Nace ki dauka ko?"

Da sauri ta dauki fulas din ta ce,
"Nagode!"

Ta fice da sauri. Murmushi yayi ya dauki maltinar ya fara sha yana lumshe ido.

Can ya mike ya dauki paper da tayi rubutu a jiki.

Rubutun ta mai kyau ya bayyana karantawa ya fara yi yaga duk tayi dai dai.

Lallai yarinyar tana da kokari da haka a assignment din ta ma tafi kowa marks.

Tana fita ta mikawa Zainab fulas din hannun ta. Amsa tayi ta ce,
"Wannan kuma fa?"

"Wallahi Sir ne wai dole sai na amsa."
Budewa zainab tayi kamshi ya doki hancin su.

Anan suka tafi cafeteria suka siyo lemo suka wuce aji suka ci.

Fulas din Asma'u ta wanke ta ce,
"In zai tafi na mika masa."

Anan take bata labarin Maryam yar gidan Antyn Sir Sabir.

Zainab ta ce,
"Kace yau kin hadu da yar uwa irin ki mai magana "

"Dallah ni ina da surutu ne."
Dariya Zainab tayi ta ce,
"Ke zan tambaya. Allah yarinya jibi ki fito da wuri dan zai amshi assignment ba ruwana."

"Insha Alah takwas ma na fito."

"Alah yasa."
"Ameen!"

Suna zaune da yamma bayan sun gama lecture tana jiran fitowarsa taga shiru shiru gashi har anzo daukar Zainab wannan yasa ta nufi office din shi.

Knocking tayi. Yana ciki a kwance ya kasa tashi ya tafi gida duk jikin sa ya mace.

Jin knocking din ya gane nata ne dan haka ya mike kawai ya dauki jakar sa da basket din da Maryam ta kawo masa abinci.

Kofar ya bude sukaci karo da juna baya tayi zata fada yai saurin riko ta ta dawo jikin sa.

Da sauri ya dago ta yana fadin.
"Sorry!"

Baya ta ja a hankali ta ce,
"Ba komai. Daman fulas din ka na kawo maka."

basket din ya mika mata ya ce,
"Muje na saka a mota."

Ya rufo office din ta biyo bayan shi. A hankali yake tafiyar itama tana biye dashi har suka karasa wajen motar.

Kujere me zaman banza ya bude ta ajiye masa fulas din tai masa godiya ta juya zata tafi,

" *Husnah* "
Ya kira sunan ta.

Juyowa tayi, ya ce,
"Kizo na rage miki hanya man."

Kasa tayi da kanta ta ce,
"Lah sir nagode nasan anzo dauka ta ma."

"Oh sai anjima!"
ya shiga mota

Hannu ta dan daga masa ta juya ta nufi gun drivern su.

Shiga tayi suka wuce a gida. Tin a mota suke waya da Yaa Aslam har ta karasa gida basu gama ba.

Ganin Mami a falo yasa ta tsinke wayar ta fada kan ta tana cewa
"Wash!!"

Mami ta ce,
"Ji zaki karya ni "

Murya Ta shagwabe ta ce,
"Mami na gaji."

"Kije ki watsa ruwa ki dan kwanta ki huta kafin magariba."

Mikewa tayi ta yi sama tana dailing number Ya Aslam.

Wayar suka cigaba dayi tana karasawa daki ta fada kan gado ta ce,
"Wash! Allah Yaa Aslam na gaji "

"Ayyah sannu baby na ko nazo nai miki tausa ne."

Murmushi tayi ta ce,
"Da kuwa naji dadi."

Murmushi yayi ya ce,
"To kwanta ki rufe idon ki."

Kwanciyya tayi ta lumshe idon ta. ya ce,
"Yauwah bari a fara ta kafa ko?"

"Wallahi kamar kasan sun gaji kuwa."

A hankali ya dinga cewa na miki nan na miki amcan kai ka zaci da gaske tausar yake mata.

Har akai magariba sannan sukai sallama ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta tada sallan.

Sai da tayi isha'i sannan ta mike ta nufi dakin Yaa buhari ta dauki ice cream sannan ta sauka kasa duk agajiye.

Dady ta sama a zaune gefen sa Mami sai Yaa buhari a can gefe. sannu da zuwa tai musu ta zauna gefen Dady tana cewa
"Dady wallahi yau na gaji da yawa."

"Ayyah sannu Autar dady."
"Yauwah!"

Dady ta mikawa ice cream din ta ce,
"Dady bismillah!"

Murmushi yayi ya ce
"Nagode!"

Muje to kuci abinci. Ta fada tana mikewa. Binta sukai ta zuba musu ita kuma taja gefe tana shan ice cream.

Yaa Buhari ya ce,
"Dady kaga ko shiyasa da bazan siyo mata ba dan nasan ba son cin abinci take ba."

Dady ne ya kalle ta ya ce,
" *Husnah* ajiye kici abinci kinji."

Ajiyewa tayi ta dan tsakuri abincin sannan ta ce ta koshi ta fara shan ice cream din ta.

Suna gamawa tayi sama dan yau a gajiye take.

Kwanciyya tayi ta jawo waya ta lalubo number sa.

Lokacin shima yana kwance aka katon gadon sa sai juyi yake ta kira sa.

Da sauri ya dauka ya ce,
"Baby na lafiya?"

"Uhmm lafiya lou! Yau na gaji shi yasa nazo na dan kwanta da wuri."

Ya ce
"Nifa ince nasan I yanzu kina gun Dady."

"Yau na baro Dady da wuri."
Ya ce,
"To muyi hira."

Shiru tayi ta ce,
"Ka kawo hirar to."

Ido ya lumshe ya ce,
" *Husnah* ina bukatar muyi aure wallahi. Dan na fara kosawa zama ni kadai in dawo daga aiki bame min oyoyo bare ingan ki naji dadi."

Murmushi Asma'u tayi. ya ce,
"Dani dake na shirya, aure kawai nake bukatar muyi. Kuma nasan ko yanzu nace ayi za ai mana"

Asma'u ta ce,
"Yayana ai lokaci ne."

"Uhmm haka ne, *Husnah* kin jefon kifiya tazo ta soken a zuciya ta. Amman sam ban ji zafi ba ko haushi, saboda kin turan abu me dadi a cikin ta."
Ido ta zaro tana dariya

"Nayi arangama dake a cikin rayuwa kin shige cikin jikina, munyi shakuwar da babu batun rabuwa, na kira ki mallaki na, haka nima na zamo nakine babu fargaba a cikin rai na. saboda nasan irin son da mukewa juna."

Idon ta a lumshe ta fara magana tare da murmushi a kan fuskar ta,

"Nice mahadin ka sahibina. Har abadan dakai nake son rayuwa. Ko da rana ko cikin damuna zan tsaya ka ban gujewa dukkan ruwa. Na sanar dakai dukkan sirrika na. Babu wanda zaiji tinda ka adana. Kazama shalele na guna kaine dan lele. Hanyar mu daya ce zata bulle da mun shiga za'a kulle, dadi rayuwa da masoyi shakuwa aure burin ran mu kuma insha Allahu nan ba da jimawa ba zan zama mallakin ka ta har abada."

Mikewa yayi daga kwancen da yake ya ce,
"Kalaman ki na kashe min jiki da haifar min da kasance tare dake."

Amsa'u ta ce,
"Haka nima nake ji. Kamar yadda kake koren damuwa. kai ke kawar min da kishiruwa. Bani son muyi rabuwa. Na fison kasancewa dakai har abada. Wallahi yaa Aslam da kai kadai nake son rayuwa, son ka kadai nake so na mutu dashi. Wallahi in bakai mutuwa zan yi ko ban mutu ba zan zamo ina raye kamar gawa ne. kai ne rayuwa ta Yaa Aslam "

Ya ce,
"In bake ya zanyi. In babu ke nazama tarihi, abar batu na duniya. Gangar jiki ce ke duniya amman ruhina da ke zasu kasan ce. Nafi son mutuwa ta raba mu"

"Ban son maganar mutuwa ko rabuwar mu Yayanah."
Ta fada muryar ta na canja wa.

"Yi hakuri."
Ya fada.

Dan murmushi ta yi ta ce,
"Ba komai. In munyi aure zan kula da Yaya nah!"

Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi akan ki bana bidar shauki, nasan komai wanda zaki iya. Yadda dake nayi auren mu in anyi zamu more rayuwa. Nasan zaki kula dani ki ban duk hakkina."

Ido ta rufe da tafin hannun ta. wai kunya. Tayi shiru. Ya ce,
"Kina ji na?"

Kai ta gyada tayi shiru Ya gane me yasa tayi shiru dan haka ya ce,
"Wai kunyar nan fa tayi yawa. Ba damar nayi zancen aure. Bude naga idanun ki masu kyau da haske masu haskan zuciya ta."

"Ya Aslam, Kai ne ka kasance abin anbato na a koda yaushe sai nayi tunanin ka. Dadi cikin kunnuwa na, zancen ka inkayi. ina son na kar kare rayuwa ta da kai. Ni gani nake sam babu wacce ta kaini dace, nice sarauniyar Mata."

"Kin fi haka ma. in nace zan fadi yadda kike a cikin raina, watakila ki zata na haukace. son ki nasa naji ni a wata duniyar ta daban. Buri na kawai na gan mu tare a inuwa daya."

"Allah nuna mana."
"Ameen."

Agogon dakin sa ya kalla ya ga har sha daya ta gota.

Dariya yayi ya ce
"Baby ina gajiyar ne?"

Murmushi tayi ta ce
"Yaya nah ya gusar min da ita."

"Kinsan karfe nawa?"
Kai ta girgiza.

Ya ce,
"Karfe shada da miti ashirin da uku."

"Kai tab hira dakai tafi komai dadi a guna da dauken hankali na wallahi."

Murmushi yayi ya ce,
"To muje muyi alwala muzo mu kwanta."

Ta mike shima ya mike suna dawowa sukai sallama kowa yayi addu'a ya kwanta.





*INDABAWA*
[1/18, 14:14] Maryam S Indabawa🥰:  *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*



By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My Life. My momy*



76-80


*Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kuyi Aiki Domin Kowwa Ana Saukake shi ya Zuwa Abinda Aka Halicceshi Donshi ne"* (Bukhari da Muslim).*




Ranar alhamis da wuri ta gama komai ta shirya tayi dakin Dady.

Karfe takwas da arbain ta gama komai ta shiga dakin Yaya Buhari.

Gaisawa sukai kawai ta fita duk dan kar ta makara.

Shi kansa yau yasha mamakin ganin Asma'u bata tsaya jan magana ba.

Baba ma da ya gama shiryawa ita kawai yake jira tana shiga ya tada mota suka nufi makaranta.

Suna cikin tafiya motar ta tsaya. Fita Baba yayi Ya taba motar ya dawo amman shiru.

Sai da yafita sau uku ana hudun Asma'u ta ce,
"Baba me ya samu motar."

Baba ya ce,
"Asma'u kinsan ance karfen nasara bai da tabbas motar nan lafiya muku fito amman kinga ta tsaya taki tashi."

Fitowa tayi ta duba agogo tara saura minti biyar.

Waya Baba ya dauka ya kira mai gyara motocin gida ya fada masa inda yake

Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Baba bari na hau napep dan na makara gashi zanyi submitting aasignment "

"To bari na tsayar miki da Napep din.'

"Aah Baba na gode."
Ta fada tana dan matsawa.

Mamaki take ganin karfe tara amman ji yan makaranta sai zirga zirga suke bama maza yan makarantun gwamnati.

Duk Napep din da zai zo a cike yake zuwa.

Wata Mota ce ta tsaya a gaban ta. Matsawa Asma'u tayi.

Kara binta akai ta kuma matsawa. Fitowa yayi daga cikin motar.

Wani hadaden saurayi ne ya fito. Fari ne, yana sanye da Ash kalar shadda kafar sa da bakin takalmi haka hannun sa daure da bakin agogo.

Kansa bbabu hula sai gashi dake kwace luf luf. Yana da idanu, haka nan hancin sa dogone har baki.

Karasawa yayi gun ta cikin nutsuwa ya ce,
"Assalamu Alaikum."

"Wa'aikulum salam!"
Ta fada tana dan matsawa daga wajen.

Kara bin ta yayi ya ce,
"En mata ina zaki?"

Ko kallon sa batai ba ta fara tsaida wani Napep.

Bai tsaya ba sakomakon cikar da yake.

"Naga kamar makaranta zaki kizo na rage miki hanya."
Dagowa tayi ta watsa masa wani irin kallon sannan ta matsa wajen wani napep da ta tsayar.

Kallon ta yayi har ta shige ciki sannan yayi murmushi ya shiga motar sa ya tafi.

Tana zuwa ta tadda har an yi submitting ga wani malamin yana musu lacturrle.

Kuka ta saka. tana zaune har lecturer ya fito.

Ta shiga ajin ta kifa kanta a benci tana cigaba da kuka.

Zainab ta matso gun ta tana bata hakuri sai ga. sir Sabir nan.

A haka ya shigo har ya gama lecture Asma'u bata dago ba.

Sai da zai fita ya dan matso gefen ta ya ce yana son ganin ta. Sannan ya tafi.

Asma'u duk ta tsure dan tasan akan bai ga assignment din ta ba.

"Zainab Allah bazani ba ni nagaji da kullum complain wallahi."
"Kiyi hakuri kije baki san me zai faru ba."

Da haka Zainab ta lallabata ta tafi office din nashi.

Da sallama ta shiga bayan tai knocking an bata izinin shiga.

Kai daga kallon ta ma zaka san ta sha kuka dan idon ta yayi ja dashi.

Sir Sabir ne zaune a wata kujera sanye da Wata brown shadda. Gefen sa gayen da ta gani dazu a hanya ne yaso ya rage mata hanya.

Waya taji Sir sabir yana yi yana cewa,
"Ki nifa ban san ta ba a ranar nima na taba ganin ta."

Shiru yayi sanna ya ce,
"Sai kinzo. In kuma na fita ne shikenan."
Ya kashe wayar.

Kallon sa ya maida kanta ya ce,
"Mene?"

Kallon sa ta tsaya yi ta ce,
"Uhmm uhmm!"

Sai ku a tayi shiru. Fauwaz dake, gefen sa ya dago dan ganin da wa yake.

Ido ya zaro ya ce
"Kai kece?"

Kallon sa tayi ta dauke kai ta ce,
"Sir kace nazo."

"Me yasa banga assignment dinki ba."
Shiru tayi.

Sai da ya kara nanata tambayar sannan ta dago ta kalle shi

Fauwaz ne ya dago ya ce,
"Friend ita ce wacce nake baka labarin na hadu da ita fa dazu. Motar suce ta lalace,"

Hararar sa Sabir yayi ya kalle ta ya ce,
"Ke me yasa kullum kina da matsala ne, in tayi baki makara ba yau abu kaza ya faru me yasa ne *Husnah* "

Fauwaz ya ce,
"Haba aboki kayi hakuri man."

Ya kalli Asma'u ya ce,
"Beauty mene matsalar ki yanzu?"

Banza tai masa tai kasa da kai idon ta na cikowa da kwalla dan ita da kai mata fada gara ka dake ta. Bata son fada a rayuwar ta yanzu zata fara kuka.

Kallon ta Sabir yayi ya ce,
"Mikon Assignment din naki kuma ki kara samun matsala na rashin submtting ko makara ki gani."

Da sauri ta dauko ta mika masa. Ta ce,
"Nagode!"

Tayi hanyar fita da sauri Fauwaz ya mike zai bita Sabir yai saurin riko hannun sa.

kafin ta bude kofa aka bude. Maryam ce ta shigo cikin shigar ta mai kyau ta saka doguwar rigar atamfa a mata dinkin mai dogon hannu.

Mayafin ta dan yafa kai ba dan kwalli sai jaka dake kafadar ta.

Tana ganin Asma'u ta saka dariya ta ce
"lah Asma'u!"

Sai kuma ta kama hannun ta. Ta kalli Sabir ta ce,
"Uncle kace, baka santa ba a ranar ka taba ganin ta."

Sai a lokacin Amsa'u ta tuno da statement din sa da ta shigo taji yana waya.

Kamo hannun ta tayi suka shigo office din ta ce,
"Ke nazo nema muyi sallama gobe zan koma garin mu gashi ban da number ki."

Murmushi Amsa'u tayi wanda Fauwaz ya kasa dauke ido daga kallon ta.

Hannun Maryam ta kama suka fita kallo Fauwaz da Sabir suka bisu da shi.

Wajen Zainab suka karasa ta zauna sannan sukai musayar number sai hira ta balle.

Dan har lecture tare suka shiga suka fito sukaje sallah sannan suka je cafteria suka ci abinci.

Sai karfe biyar sannan suka rabu shima dan an tashi.

Har bakin office din Sabir suka rakata suna daga mata hannu sannan suka juya.

Sabir da ya zata ma ta tafi ta shiga ta zauna akan kujera ta ce,
"Wash! Wallahi Uncle na gaji haka nima zan sha fama in na fara karatu."

Kallon ta yayi ya ce
"Daman baki tafi ba."

Kai ta daga masa ta kalli Fauwaz ta ce,
"Uncle Fauwaz ya kake?"

"Ni ba ruwana da ke. Kin tafi kin barni."
dariya tayi ta ce,
"Ayi hakuri wallahi Uncle Fauwaz. Asma'u ce ta burge ni na dawo amsar number ta kasan gobe zamu shige."

Kai ya daga ya ce,
"Dan bani number na gani."

"Tab ta ce, kar na bawa kowa wallahi."
Sai lokacin Sabir ya ce,
"In ba kwana zamuyi ba mu tashi mu tafi dare na yi biyar da rabi fa."

Mikewa yayi ya dauki jakar sa da basket ya mikawa Maryam Amsa tayi suka fito tana ta basu labarin Amsa'u in ka kalli Sabir zaka zaci ba jin ta yake ba amman gaba daya hankalin sa na ga ita yana jin abubuwan da take fada.

Da haka suka je gida haka tai ta bawa Mamah labarin Asma'u ranar dai har dare bata da magana sai Asma'u daga ta ce, tayi kaza sai ta ce tayi kaza.

Ta ce,
"Mamah baki ga ba yarinya karama ta na karanta medicine kuma a final year wallahi ta burge ni ga kokari da muka shiga lecture ita ke bada asma."

Mamah ta ce,
"Sai ki koyi da ita to."

"Ai insha Allahu Mamah kuma nayi 'kawa."
Shi dai yana zaune yana ji yana kara jin Asma'u na kara burge shi.


Asma'u ma da taje gida sai da ta bawa Mami labarin yarinyar.

Mami ta ce,
"Daman haka rayuwa take wani na son ka wani kuma kin ka yake yanzu dai ita kince daga haduwa Allah ya sa mata son ki. To Allah ya bar mu ga masoyan mu."

"Ameen!"
Ta mike ta hau sama.

Yaya Aslam ne ya kira ta bayan sun gaisa yake tambayar ta makaranta ita ma take tambayar sa wajen aiki.

Soyayyar Asma'u da Aslam abin sha'awa ce da burge wa dan ba karamin son juna su suke ba kowa da son dan uwan sa son da basa son su taba rabuwa da junan su.

Kowa na kula da tarairayar juna. Ga shi soyayyar su mai tsabta da kyau suke.


*Haka rayuwa yake wani daya ganka yake jin son ka a zuciyar sa. Son Allah kenan wanda wani dabi'un ka su suka burge shi. Wani kuma halayar ka abubuwa da yawa dai. Allah ka bar mu da masoyan mu,*

*Ameen!*


Mutane na tambayata wai *Sabir* Mijina ne ko saurayi nane to daga *Sabir* har *Aslam* da *Fauwaz* all are my lovelly children. Really love then.

*Husnah* kuma ina son sunan ne.


*Masoya na nagode nagode Allah bar soyayya.*

*Muje zuwa ga wani ya dadu a masoyan Asma'u shin ya kenan*



*Ina mai bada hakuri na jina shiru da kukai jiya da night da na morning da ban ba. Nagode*

*INDABAWA*
[1/18, 14:15] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*



By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*



Dedicated to *My whole Number. My Momy!*

*Allah kara girma da daukaka. Allah yasa ki gama da duniya lafiya. Ur love is special.*




*81-85*

*_An Tambayi *, *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kuyi Aiki Domin Kowwa Ana Saukake shi ya Zuwa Abinda Aka Halicceshi Donshi ne"* (Bukhari da Muslim)._*





Pretty ce zaune a gaban wani boka. Kai sufar bokan ma kanta abar kyama ce da tsoro bare kuma warin da yake yi.

Abinda take bukata ta gama fada masa.
buga kasa yayi yai dube duben sa sannan ya ce,
"Kin kawo aiki me wahala dan mutanen nan ba a zaune suke ba wajen ibada sai dai zan san yadda zamu yi muga ta wacce hanya zamu bi."

"Yauwah ni na fi so ma ita yarinyar a haukata ta yadda dole zai hakura da ita ko ta mutu ma."

"Kull!"
Yai mata wata tsawa ya ce,

"Wannan yarinyar har tafi Aslam tsari da riko da addini baza mu iya da ita ba. Tafi karfin mu."

Da haka ta zube masa kudi masu waya sannan sukai akan nan da wata daya ta dawo.

Daga nan ma Pretty ba gida tayi ba wajen wani bokan ta karayi suka karai mata alkawarin komai zai wakana yadda take so.

Da haka ta koma gida da murna abinda take so zai zo gare ta.

Dan har ta fara shirye shiryen auren ta da Aslam.


Aslam kuwa bai son wainar dake soyawa ba.

Shi dai bai da buri da muradin da ya wuce ya ganshi tare da Asma'u.

Kowa da yasan Aslam yasan Asma'u dan kowa yasan irin son da yake mata.

Abokan sa har tsiya suke masa su ce, ya makalewa karamar yarinya me ya gani agun ta.

Shi dai sai dai yai dariya dan son Asma'u daga Allah ne. Allah shi ya sa masa son ta a zuciyar sa yake jin bazai taba iya rayuwa ba ita ba.

Yasha fadawa Asma'u bazai taba barin ta ba ko ya ce,
"Ba zai taba daina son ta ko mata kishiya ba."

Duk kishin Asma'u sai dai ta ce,
"A'ah Yaa Aslam ka daina min irin wannan al kawarin Baka san me Allah ya tsara mana ba."

Shi in ta fadi haka wani lokacin har haushi yake ji.

Ita kuma tana tsoron ta sawa zuciyar ta haka Allah ya riga da ya tsara wani abun daban.

Tana son Aslam tana kishin sa kamar yadda shima yake son ta da kishin ta.

Dan yawancin wasu dogayen hijaban ta shi ya siyo mata dan zuwa makaranta. Daga doguwar riga sai hijabai su take sawa.


*********
Munasha ce zaune da kawar ta. Kallon ta kawar tayi ta ce,
"Wallahi ko mayya sai haka."

Munasha Ta ce,
"Da me fa?"

"Wannan yaron mana Aslam dan Allah ki kyale shi ki kama samarin harkar yanzu ba kudi basa shigo mana sosai saboda kin rage kula su wallahi."

Ido Munasha ta lumshe ta ce,
"A duniya mutum daya na taba so kuma shi insha Allahu sai na aure shi shine Nazir. Ko da na rasa shi Kuwa na rasa shi to bazan rasa Aslam ba wallahi Aslam ya min surar sa abar so ce ga kowacce mace da tasan 'da namiji. Kingan shi kuwa,"

Ta girgiza kai ta kwanta wallahi ba wanda yanzu nake sha'awa in ba shi ba. Shi kadai nake son nai tarayya da shi sai kuma my oga at top."

"Ni dai naji ki dauri kije gun Alhaji Usman kinsan babar harka ne, ko nawa kika nema zai baki kinga ko dasu masan yadda za ayi a jawo hankalin Aslam gareki."

Munasha ta ce,
"Kuma fa kin kawo magana wallahi dan Aslam zan je."

Ta mike ta fada wanka cikin minti biyar ta shirya cikin wani dan mini siket wanda ana gano kasan ta.

Sai yar half ves da ta saka ta bazo da gashin dakin ta gadon baya.

Tayi kwalliyar karuwai ta jefa cingum baki tana tauna sai kara take dashi.

Turare ta bade jikin ta dashi ta fita ta shiga mota sai guesthouse din Alhaji Usman.

Yasan da zuwan ta dan yafi sati yana jiran zuwan ta.

Yana falo a kwance yana trying number ta sai gata kamar daga sama.

Kan cinyar sa ta dane, tana masa wani kallo tana shafa shi.

Nan da nan ta burkita masa tunani tun a falo suka fara masha'ar su har suka koma daki.

A ranar a gidan ta kwana dan washe gari ma kin barin ta yayi ta tafi.

A kalla sai da tai sati biyu a gidan sannan ta tafi da milliyoyin kudi banda mota da ya mallaka mata.

Haka ta koma gidan ta da ta siya ta tadda Bulkis.

Mukkullin motarta ta da ta jefawa mata ta ce,
"Na bar miki."

Tsalle Bilki ta duka tana cewa da
"Da gaske!"

"Eh man! Kinsan ni yanzu na zama babar hajiya. Zan miki transper kudi. Amman ina son naje gida yau naga ya Baba take ciki."

Bilki ta ce,
"Sai yaushe kuma?"

"Sati daya zan yi."
Munasha ta bata amsa ta mike tana debo kayan da gida suka san ta dasu ta zuba a jaka ta shiga tai wanka ta saka wata kodadiyar atamfa dikin riga da zani.

Tana fitowa Bilki ta saka dariya ta ce,
"Amman fa da ace a haka kike da kin bada mata."

Dariya itama tayi ta ce,
"Ke dai bari baki ji yadda zanin nan ya dame ni ba."

"Wai dan Allah satin.kuwa zakiyi dan Allah kiyi kwana biyu ki dawo."
Bilkis tafada

Munasha ta ce,
"Aah bilki duk rashin iyaye na ina son su. Naje gun wani kato na yi sati biyu bare gun iyaye dan nayi sati. Aah wallahi."

Baki Bilkis ta tabe ta ce,
"Shikenan. Ki gaida su Baban."

"Zasu ji "
Ta dauki jakar ta tafi.

Napep ta tsayar ya kai ta har gida. Kannen ta sai murna suke sun san zasu samu dan abin tabawa.

Gun Babar ta taje ta gaishe ta. Baba sai addu'a take mata na samun nasarar karatu sannan ta gaida mahaifin ta.

Kayan abinci ta siyo musu bubun shikafa da katon din tafiya da macaroni.

Ta bawa Baba dubu goma Mama dubu biyar.

Daman ta fada musu tana dan siyar da abubuwa a makaranta wannan yasa suke zaton tana take samun kudi.

Duk abinda take akwai ta da ibada da biyayya ga iyayen ta.

Dan ita tazo gida ita ke yin komai haka zasu ta sa mata albarka.

Taje gidan su Nasir saurayin ta wajen kawar ta Rashida.

Anan Rashida take labarta mata Yaya ya kammala karatu sun rike shi zaiyi aiki shekara daya ya dawo.

Ba karamin murna Maimuna ta taya shi ba.

Anan suke hira da Rashida akan makaranta.

Rashida ta ce,
"Maimuna ki godewa Allah duk cikin mu ke ce kika samu jami'a mu duk

Please Login or Register in order to submit comment