Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gatan ta.

Amman shine ya juya mata baya. Ko yasan halin da ta shiga.
Ko yasan irin jinyar da tasha. Ko yasan irin azabar da take sha a duk sanda lokacin kiran sa ko turo mata da sako yai bai turo mata ba.

Duk shekarun nan da suka wuce in dai zata kwanata bacci sai tai kuka. Dan ya riga da ya sabar mata shine mutun na karshe da yake saka ta bacci da kishoshin Annabawa da sahanabai.

Amman duk a lokaci daya ya rushe duk abinda ke tsakanin su.
Tabbas ya dawo gareta ne dan ya raina mata hankali.

Ina dayar matar tasa. Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.

Ya dawo gare ta ne dan yasan da shi kadai zata iya rayuwar aure.
Ya dawo gare ta ne dan yasan duk lagon da zai amshi zuciyar ta.

Ya dawo gare ta ne dan yasan irin son da take masa.
To yayi karya duk son da take masa baza taba sakar masa ba.

Inda da ya nuna baya sona nima yanzu na hakura da shi.
Zan zauna da koma waye amman banda da Yaa Aslam.

Bazan zauna dashi ba Yaa Aslam ya wahalar da ni.
Tana tuna irin hirar rakin su da yakan ce bazai taba rabuwa da ita ba.

A lokacin in ta kawo misalin abinda zai iya raba su har haushi yake ji.

Amman lokaci daya ya rabu da ita. Ta kan tina irin alkawarin da yake mata da irin son da yake mata to duk suna ina.

Lallai in ta kara yadda da Yaa Aslam zai kara yaudarar ta ne.

Tasan tana son Yaa Aslam amman zata danne zuciyar ta ta nuna masa ita yanzu ba son sa take ba.

Sai ta kwatar wa kanta yanci a gun sa.
Idon ta ta bude jajir da su. Aslam dake rike da hannun ta ya zuba mata ido ya kara bude idon sa ganin yadda idon ta ya kada yai jajir.

Kuka ta fashe masa da shi. Nan da nan ya hau lallashi amman sam taki yin shiru.

Sai da kyar ta yi shiru nan ma ta mike ta yi cikin gida tana sharar hawaye.

Mami dake falo ta ga wucewar ta. Kai kawai ta girgiza.
Dan tasan Asma'u na son Aslam. Tana lura da yadda take rufe daki kuma duk tasan akan sa ne.

To ai dai jikin ta yai sauki dan haka tazo su shirya su tafi dan ta fara tausayawa Aslam. Bama da tasan kafiyar ta.

Tana zaune Aslam ya shigo shima duk yanayin sa ya sauya.
Kallon sa Mami tayi ta ce,
"Ya dai?"

Kai ya dan sosa ya ce,
"Ba komai!"

Mami ta ce,
"Shikenan ka fara shirin tafiyar ku. Tinda jikin nata yai sauki nan da jibi sai ku tafi ko?"

"To Mami Allah kaimu."
Ya fada yana mikewa.

Sama ya hau Mami ta bisa da kallo.
Asma'u ta shiga daki ta shiga bandaki ta watsa ruwa tai alwala.

Tana fitowa ta shafa mai tai salla. Tana kan sallaya Mami ta shiga dakin da sallama.

Dagowa tayi ta amsa tana gyara zama. Zama Mami tayi agefen gadon ta ta ce,
"Asma"u jikin ki yai sauki dan haka ki hada kayan ki nan da jibi sai ku tafi ko?"

Wata faduwar gaba ce ta zowa Asma'u dan har sai da ta dafe kirji jin kamar zai fadi.

Dagowa tayi ta ce,
"Mami Allah da saura na."

Mami ta ce,
"Asma'u ba inda yafi dakin mijin ki dadi da gatan ki. Ki tafi ke karasa warke acan. Allah baki lafiya. Allah miki albarka."

Kuka Asma'u ta saka ta ce,
"Mami bana son na tafi na barki. Mami na rasa Dady kema kada na rasa ki Mami ni a nan zan zauna."

Murmushi Mami rayi ta ce,
"Haba Husnan Dady. Kinsan sai kwana yayi ake tafiya. Kuma kinsan Dadyn ki bai da wani buri da ya wuce ya ganki a gidan Yayan ki matsayin matar aure. To ki daure ko dan Dadyn ki ki zauna lafiya a gidan mijin ki. ni kuma ki kwantar da hankalin ki zan na zuwa ganin ki akai akai. Kuma ga Yaa Fati nan ma. Ki daina kuka in ba so kike hankali na ya tashi ba."

Da sauri ta hau goge hawayen fuskar ta.


Bangaren Sabir da Nusaiba kuwa zaman lafiya suke sosai take kula da shi shima kuma so sai yake kula da ita.

Sai a yanzu yake jin son ta sosai a cikin jikin sa.




Perty kuwa tana can ta koma ga Allah yanzu Aslam take so ta gani ta roki gafarar sa

Tasan taci zalin Asma'u dan tasan soyayyar dake tsakanin su amman ta raba su.

Dole ta nemo Asma'u itama ta nemi gafarar ta

wannan dalilin ne yasa ta tafi kano dan neman inda Asma'u take.



Har gida Zainab ta zo jin Asma'u zata tafi.
Kayan gyaran jiki ta hado mata sosai, inda ta bata wasu ta ce ta tafi da su.
Haka ma Maimuna har gida tazo tai mata sallama.

Ana gobe zasu tafi suka je gidan Sabir. Gida ne mai kyau wanda aka zuba masa kayan more rayuwa kala kala.

Tinda suka je Nusiaba sai nan nan take da Asma'u duk Asma'u ta kasa sakin jiki saboda kallon da Aslam yake tsare ta dashi.

Shi yana mamakin Asma'u kamar ba ita ba.
Duk ta canja masa. Anya kuwa Asma'un sa ce wannan.

Shifa ko a gida baya ganin ta. Bare ya samu damar mata magana

To in ya ganta ma ya samu fuskar magana man.
Haka suka dan zauna sanna suka tafi gidan Mamah mahaifiyar Sabir.

Sosai Mamah tai mata nasihar zama da miji sanna ita ma ta hado mata kaya ta bata.

Gidan su Zainab suka je tayi wa mahaifiyar Zainab sallama.

Daga nan kuma suka koma gida
Duk tafiyar nan da suke kallo ne kawai nashi amman ya kasa koda mata magana.

A haka suka karasa gida ta debo kayan ta ta shige.
Sama ta hau ta ga Mami ta fito da akwati nan ta da na wajen Yaa Aslam da na wajen Sir Sabir da ya ce ya bar mata.

Zama Asma'u tayi ta ce,
"Mami na gaji. Sai kace ban saba fita ba."

Mami ta dago ta kalle ta ce,
"Kinsan jikin naki ne. Ya kamata kije asibiti yau."

"Eh sai anjima zan leka."
Asma'u ta fada dai dai shigowar Sabir.

Mami ta kalle shi ta ce,
"Kaga masu dibar kaya a kasa ko?"

Kai ya gyada, Mami ta ce,
"Kaje kace su zo so dauki kayan an gama."

Mikewa yayi ya fita. Mami ta ce,
"Tinda kince ke sai kayan Dady gasu can an saka miki su a mota."

Murmushi Asma'u tayi ta ce
"Mami ba haka bane, kinga Dady dan kar ya daurawa kowa nauyi ya siyon kayan nan. Kuma kayan nan da kyan su, bayan haka masu tsada ne to me za a canja ayi dasu. Kuma naga su aje yayi Mami dan zaman duniya dai kawai wani ma neman wanda bai kai shi ba yake amman bai samu ba."

"Haka ne! Kayan na da kyau masha Allah."
Mami ta fada.

Suna zaune aka shigo aka kwashe duk kayan.

Sai a lokacin jikin Asma'u yai sanyi ganin da gaske dai tafiya zatai.
Daki ta mike ta shiga.

Daren ranar tare suka kwama da Mami tana tai mata nasiha akan aure. Asma'u ji take kmar tace ta fasa. Wwai da da bata da burin sai ta ganta a gidan Yaa aalma amman yanzu duk bata so


Washe gari da safe Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.

Tai wanka ta shirya cikin wata Farar atamfa wacce akai mata adon da ja da baki.

Simple make up tayi, ta saka jan mayafi da jan takalmi sai bakar jaka.

Sosai tayi kyau. Ba abinda tta dauka saboda komai nata an tafi mata dashi.

A falon sama ta samu Mami da Yaa Aslam wanda ya saka wata milk din shadda tai masa kyau.

Sai tashin kamshi yake yi. Yaa Buhari a gefen sa. Sai Zainab dake dakin Mami.

Gefen Mami tayi ta zauna. Yaa Buhari ya kalle ta ya ce,
"Ji 'ya Malama tashi zakiyi dan yanzu zaku tafi."

Baki ta turo ta dan harare shi. Daga kan da zatai sai taga Yaa Aslam ya zuba mata ido baki da hanci yana kallon ta.

Kai ta dauke ta kalli Mami ta ce,
"Mami ni kam in nace na fasa ai ya fasu ko?"

Kai Mami ta daga. Yaa Buhari yai dariya ya ce,
"Karya kike wallahi."

Mami ta ce,
"Ku tashi ku tafi."

Kwanciyya tayi akan kafar Mami. Zainab ta fito ta ce,
"A'ah me zan gani!"

Yaa Buhari ya ce,
"Eh man wallahi aka zan fitar da ke."

Mikewa tayi ta fara zubar da hawaye. Murmushi Mami tayi ta ce,
"To mene na kuka. Haba Husnahn Dady ki daina kuka bayan ga Momyn ki can tana jiran zuwan ki."

Kai tai kasa da shi amman hawaye ya kasa daina zuba.
Yaa Aslam kuwa kukan da take ji yake kamar yai me dan sam baya son kukan Asma'u.

Zainab ce ta kama ta ta ce,
"Haba Asma'u ki daina mana."

Suka mike suka fita har da mami ta raka su compound sannan ta dawo.

Asma'u kuwa sai jikin ta ya kara sanyi na jin rabuwa dai zatai da gida

Sai da suka fita daga gida Aslam yaji Asma'u na kuka.
Motar yasa Buhari ya tsayar sannan ya koma gidan baya.

Jikin sa ya jata yana lalashi ta a hankali a hankali.

Sannu a hankali tayi shiru. Tana rasa dalilin da yasa in har tana tare da Yaa Aslan take jindadi a ranta. Ko taji ta samu relief.

A haka suka karasa airport ba tare da sun san anje ba. Har sai da su Yaa Buhari suka fita sannan yai musu knocking.

Dogowa sukai yai musu nuni da waje. Jikin ta ta kwace daga nashi ta fita da sauri.

Jakar ta ya dauka ya fita yana murmushi. Suna zuwa aka fara kiran su.

Ba jima ba suka tashi. Asma'u na hawaye dan sai Yaa Aslam ne ya tallabe ta yana lallashi har suka shiga jirgi.

A cikin jirgin ma jugum tayi tana kwance a kan kafadar sa.


Suna sauka har motar gida tazo daukar su.

Gida sukai. Asma'u duk sai taga gidan ya canja da ta jima bata je ba. Ba kamar da da ta samu hutu taje ba.

Amman yanzu a kalla tai shekara biyu zuwa uku ba tazo ba.
Suna fitowa Momy ta fito ta kama ta. Cikin gidan ta shige da ita aka bar Aslam da daukar jaka.

Sama ta nufa da ita tana. Dakin guda aka kai ta.

Ruwan wanka Momy ta hada mata sannan ta sauka.

Bandaki ta shiga. Kafin ta fito an jere mata kayan abinci.

Mai ta shafa ta saka wata bakar doguwar riga da ta gani akan gado.

Sallah tayi tana zaune akan sallaya ya shigo dakin.

Dagowa tayi ta kalle shi ta dauke kai. Sanye yake da wando three quarter daga alamu shima wankan yayi.

A gaban faranti da aka jero mata abinci ya zauna.

Ya ce,
"Bismillah"

Kai ta girgiza ta ce,
"Alhmdlh"

Murmushi yayi ya ce,
"Humm! Ai gwara ma kici domin nasan baki ci komai ba duk yinin yau ga idanunki duk sun kumbura saboda kuka"

Fuska ta bata ta ce,
"Wa kuma yace maka banci abunci ba"?

Kusa da ita ya matsa daf ya d'ora tsinin dogon hancinshi akan nata. Ajiyan zuciya ya sauke. Yana kallon ta ido cikin ido yace,
"Nasan Husnah d'ita fiye da yanda take zato. Idan tana fad'amin gaskiya ina ganewa idan kuma tana fad'amin karya ma ina ganewa. Dan haka kina sanin abinda zaki fada min. Oya So let's eat, drink and....."

Bai karasa fadar abinda xai fada ba ta ce,
"Me?"

Bai bata amsa ba sai kiss da yai mata a kumatu. Harshenta ta fito dashi a waje.

Ai kam Charaf Yaa Aslam yasashi a baki. D'an kokarin tureshi ta farayi ganin ya fara sarrafata yasa tai la'asar. Har cikin kwanyar kanta take jin kiss din da yakeyi mata. Sai daya gama da kanshi ya d'an ja da baya kad'an.

Kallon ta yayi da idon sa da sukai jajir ya ce,
"Now let's eat"

Asma'u da jikin ta yai sanyi sosai tai kasa da Kanta ta dauki cokali ta fara cin abincin a hankali.

Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya bude dayan fulas din naman kazan ne a ciki. daukowa yyai ya mika mata. Amsa tayi tana ciki a hankali duk jikin ta a sake.

Lemo ya mik'a mata, cikin sanyin murya tace
"Na koshi."

Cup d'in yai gefen bakin ta da shi. karba tayi ta kai bakin ta ta sha kad'an ta janye ta maida ta aje.

"Duka zaki shanye"
Yaa Aslam ya fad'a yana murmushi.

Hararar sa tayi ta ce,
"Haba dan Allah ni ina zan iya shanye wannan? Wallahi na koshi."

Aslam yai murmushi ya ce,
"Kokartawa xakiyi ko in maki d'ore kamar yadda da nake miki."

Kai ta dauke, tana hararra sa ta kasan ido.

Yau Kwata kwata sai take jin Yaa Aslam ya koma mata wani sabo daban. Ga shi tana kasa hana shi duk abinda yake mata.

Ba yanda ta iya illa ta sha kamar yanda yake so. Shima kai ya kafa yasha nashi. Tashi yayi ba tare dayace mata komai ba ya fara cire rigarshi. Idanu ta zubawa kirjinshi da kwanjunan hannunshi.

Murmushi Yaa Aslam yayi ya nufi wajen ta.

Duk'awa yayi da niyar daukar ta. Ta mike za tayi waje.

Kamota yayi ya dauketa ya direta kan gadon ya kura mata idanu. Cikin sanyin murya yace
"Kina sona Husnah?"

Banza tai masa kamar ba da ita yake ba.
Murmushi yayi, ya zura hannun shi ta cikin rigar ta yai kark'ashin bayanta.

Sannu a hankali ya fara d'age mata rigar jikin ta. Tana jinshi tai lamo kaman wadda batada rai. Kirjin ta sai dukkan uku uku yake

Tana son ta hana shi amman ta kasa.

Fuskan shi ya d'aura a kan nata ya fara gogo mata hancinshi. A hankali ya tallabota ya fara cire mata rigan. Tsotsan kunne ya fara yimata cikin natsuwa yana hura mata iska a ciki. Jin sanyin AC na ratsata ta ko ina na jikinta yasa ta farga batada riga.

Jawo Hijab din ta tayi ta rufe kirjinta. Ajiyan zuciya Aslan ya sauke. Kara matseta yayi da kirjinshi sosai. yana shafa bayanta a hankali hadi da mazaunanta.

Sanin zata iya guduwa a ko da yaushe yasa ya kara matsa ta a jikin sa.

Hannu ya d'ora akan gashin ta ya 'dago fuskanta ya kaimata sumba a wuya, lips d'inshi ya tura cikin bakin ta a hankali ya fara tsotsawa yana zare bra dinta... Hannunshi ta rike gam. Chaan kuma ta saki ta zubawa sarautar Allah ido...

Tasan ita halak dinsa ce to amman kuma tana tuna abunda yai mata.

Tana can tunani taji ya fara wasa da ita sosai da sosai.

Sosai jikin ta ya fara rawa, Duk sun fita a cikin hayyacinsu daga ita har shi.

Hannun sa ta rike tana girgiza masa kanta. Ta ce
"Dan Allah ka daina Yaa Asl......"

"Shhhhhhhhhhh. Enough" ya fad'a yana k'ank'antar da murya chan k'asa 'kasa.

Fuskantar ta juyar saboda ya matse ta ba damar tashi. ta fashe da wani irin kuka.

Kuka sosai takeyi. Ganin ya kasa shawo kanta yasa Aslam sakin ta yana maida numfashi yana ajiyan zuciya.

Da sauri ta mike ta saka kayan ta ta fice da sauri.

Yana kallon ta ya saki ajiyar zuciya ya gyara kwanciyya.

Tabbas yasan da duk abinda ya faru bai faru ba da yanzu yaga jinin sa a tare da Asma'u.

To amman ji yadda Asma'u ke gudun sa kamar dodo.
Asma'u da inda yaje gida suke tare kullum amman yanzu sai dai daga nesa.

Har gara yau ma ya samu damar zama kusa da ita har ya umarce abu tayi.

Yana son Asma'u so bana wasa ba. Amman ya rasa ta yadda zai nusar da ita ta yadda.

Asma'u na fita tayi dakin Momy, Momy na zaune suna waya da Mami tana fada musu sun sauka lafiya.

Asma'u na shiga ta ce,
"Ga ta nan ma."

Ta mika mata wayar. Gaisawa sukai tai musu ya hanya.

Kan gadon Momy ta hau. Momy ta kalle ta ta ce,
"Kinci abincin ne?"

"Eh naci."
Momy ta ce,
"Me kike bukata?"

"Ba komai!"
"To kwanta ki huta."

Ta kwanta.







*MS Indabawa*
[1/18, 14:39] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐

Dedicated to *My lovelly Mum*

*101-105*




Yau kwanan su biyu a gidan Momy amman zai iya cewa rabon sa da Asma'u tin ranar da suka zo.

Kullum tana daki a rufe bata fitowa falo ko da fito da ta ji shi take komawa.

Ya zuba ido yaga Momy ta ce, su koma gidan su amman Momy tayi shiru.

Haka ne yasa aka je aka share gidan a goge dan ya kagu ya tare.

Momy kuwa tana can tana shirya musu walima da za'ayi ne kafin su tare tinda ba wani biki akai ba.

Yau ya cire kunya ya ce zai fadawa Momy shi ta bashi Asma'u su tare.

Yana shigowa ya same ta akan kujera tana duba wasu takardu.

Yana zama ta mika masa wasu takardun. Amsa yayi yana dubawa.

Dagowa yayi yana kallon ta. Murmushi tai masa ta ce,
"Eh ai dole a hada maka walima Allah yayi Asma'u matar ka ce."

Murmushi yayi ya koma gefen Momy ya kama hannun ta sai hawaye.

Kallon sa tayi ta girgiza masa kai. Ta ce,
"Mene na kuka?"

"Dole nai kuka Momy. Momy kina sona Allah ya biya miki bukatun Alheri Allah yasa ki kyakyawan karshe."

"Ameen! Duk wannan addu'ar ta mece?"
"Momy kina sona da Asma'u kiga lokacin da nace bana son ta ke kika ce A'ah amman na ki sam. Wallahi Momy ban san me ya raba ni da Asma'u ba dan ban taba jin kin ta ba. Kullum da ita nake kwana nake tasho. Ina son Asma'u Momy."

Asma'u da fitowar ta kenan taji yana maganar tai saurin komawa daki.

Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ga hawaye nan ta rasa hawayen me take yi.

Momy kuwa, hawayen sa ta share masa ta ce,
"Ai Allah zaka godewa da yada Asma'u taka ce, gashi har ka mallake ta."

"Haka ne Momy ina gode masa a ko da yaushe. Kuma ina gode muku."

Ya mike ya ce,
"Bari naje na fara rabo."

Momy ta ce,
"A'ah sai na ji ta bakin ta tana son naka ne har yanzu ko aah."

Dariya yayi Ya fice, yana cewa,
"Momy tsokana"

dariya Momy tayi dan a duniya tana son dan nan mata daya guda tilo. Duk farin cikin sa shi take fata.

Abinda ta dade bata gani a tare da shi ga shi yanzu ya dawo kullum farin ciki da annushuwa ne dauke a fuskar sa.

Tasan duk wannan bazai rasa nasaba da samun Asma'u da yayi bane.

Mikewa tayi ta yi sama. Dakin da Asma'u ta shiga.

A kwance ta same ta. Mikewa tayi tana gyara zama.

Zama tayi a gefen ta.
Ta ce,
"Asma'u kina son Aslam har yanxu ne?"

Shiru Asma'u tayi a aranta ta ce ko bana son Aslam ai ba zan taba fada miki ba Momy bare ina son sa.

Momy ta ce,
"Karkiji komai ki fada min."

Kasa tayi da kai ta daga mata kai, murmushi Momy tayi, ta mika mata katin hannun ta.

Amsa tayi ta kalla. Murmushi tayi dan tasan Momy na son ta.

Dagowa tayi ta ce,
"Momy har wata hidima za'a kara."

Kai Momy ta gyada ta ce,
"Auren da muka dade muna fata ba dole ba. Yau Allah ya nuna mana kowa yaxo ya taya ni farin ciki na hada 'dana da 'ya ta aure."

Murmushi Asma'u tayi tai kasa da kai. Wai yanxu Momy sirikar tace.

Washe gari Aslam yai tafiya dan ya ce, shi zai je ya yo musu order kayan da zasu saka.

Tin ranar Asma'u bata kara ganin Aslam ba, kuma bata neme shi ba.

Shi kuwa yana can yana fama da rashin ta. Duk yadda yaso ya ji muryar ta baya samu, dan ko Momy ya kira ya ce a hada su da ta amsa bata magana wani lokacin ma kashewa take.

Murmushi yake dan shi, yasan yai wa Asma'u ba dai dai ba. Amman bari zai wanke laifin sa ne bari da su tare.

Cikin kwana biyu aka kara yiwa Asma'u gyara inda akai mata lalle da gyaran kai.

Sosai tayi kyau ta koma amaryar tata dai.

Yau ce ranar walimar da Momy ta hada a yau kuma zata tare a gidan ta.
Har su Zainab suna hanya, ita da Mami da Yaa Buhari.

Asma'u na ganin su ta rumgume su. Sai murmushi take.
Dakin ta ta ja Zainab tana dauke da  Dadyn ta.

Tunda su zainab suka je take kallon ta ta ce,
"Ke Asma'u wannan kyan fa tin kafin ki tare ko dai har anyi wani abu ne."

Duka Asma'u ta kai mata ta ce,
"Ai shi ba ruwan da.'

Dariya Zainab tayi ta ce,
"Ma gani dai."

A ranar Yaa Aslam shima ya dira da kayan da ya taho masu da shi.

Yana ganin Buhari ya yi wajen sa, ya fe,
"Bro har kun zo."

"Eh man kun taso mu."
murmushi yayi ya ce,
"Wallahi Momy ce."

Suka shiga ciki yana daukar akwatin hannun sa.
Dakin sa suka nufa shima.


Karfe hudu har an gamai mata kwalliya. Kyan da Asma'u tayi ba zai fadu ba.

Amman tayi kyau sosai. Ta saka wani Material Milk kala wanda akai mata ado da dark brown din material.

Ta dauki dark brown din takalmi da jaka, da mayafi.

Ta saka milk din fashion. Ruwan turare akai ma. Tayi kyau kamar ka sace ka gudu.

Kowa yayi kwalliyar sa cikin shiga mai kyau. Dan lokacin ma har Maryam ta zo ita ma.

Da yake a harabar gidan Momy za'ai har wajen ya cika da jama'a
Bangaren mata daban na maza ma daban.

Momy da kanta ta shiga dakin da aka shirya Asma'u ta kamo ta.

A falon da ta zaunar da ita. Aslam ta kira ya fito shima cikin wata milk shadda da akai mata aiki da dark brown din zare.

A takaice dai anko sukai kuma sosai sukai kyau.
Tinda ya fito ya daura idon sa akan Asma'u ya kasa daukewa.

Sai da Momy tai masa magana sannan ya kalle ta yana sosa keya.
Hannun Asma'u ta kama ta kamo hannun sa suka sauka kasa.

Mami dake zaune a kasa tana ganin su ita ma ta mike.
Momy da Mami su suka fitar da yayan su.

Har wajen zaman su suka kai su. Akai hotuna da kowa da kowa sannan aka ci aka koshi akai musu addu'ar zaman lafiya.

Duk wanda yaga Aslam da Asma'u yasan sun dace da juna. Dan suna kusan dibar kamanni da sai shi fari ne tas.

Ana kiran magariba aka tashi daga taron kowa yai cikin gida maza suka tafi massalaci dan da anyi isha'i za'a kai amarya gidan ta.

Suna shiga ta shige toilet dan yin alwala amman sai ta ga ba hali dan period din ta yazo.

Wanka kawai tayi ta fito. Momy ce ta shigo ta ce, tai sallah ga wani ruwan turare nan tai wanka dashi.

Da toh ta amsa mata kawai. Bayan mintina kadan Momy ta dawo dakin.

Ruwan wanka ta hada mata da wani hadin turare, mikewa Asma'u tayi tai wanka.

Tana fitowa Momy ta kawo mata garwashi da wani turaren ta turarre jikin ta.

Wani hadin humra Momy ta kawo mata da wata atamfa ruwan ganye da ruwan daurawa.

Simple make up akai mata. Aka saka mata alkebba Golding kala.

Momy tai mata ruwan turare sannan ta saukar da ita wajen kawayen ta da Mami.

Nasiha sukai mata da addu'ar zaman lafiya. Sannan mutum biyu daga kawayen Momy suka fito da ita.

Dakin Dady suka kai ta shima nasiha yai mata mai ratsa jiki.

Sosai Asma'u take kuka dan sai yanzu ta san tayi aure.

Daga nan suka tafi da ita gidan mijin ta. Sai Zainab dake can tana kintsa gidan.

Gida ne katon gaske dan harabar gidan kanta katuwa ce, banda bayan gidan.

Garden da swimming pool ne sai bishiyun kayan marmaru kala kala. Da lilo.

Harabar gidan an kawata ta da fulawoyi. Kofa daya ce zata sada ka da shiga cikin gida. Da ka shiga kuma zaka ga katon falo aka saka masa wasu royal furnitures Coffee kala da adon milk. Haka ma labulayen kofi da milk ne.

Daga gefen sa yar stair ce da wajen daining da kitchen. Kitchen din ta an cika mata da kayan amfani zamani.

An mata adon sa irin na, Island kitchen plan akai. Daga can bangaren kuma Toilet ne.

Sai kofofi biyu dake kallon juna. dayar tana dauke da falo, da bedroom guda biyu. Ko wanne an zuba masa kaya masu kyau da tsada. Daki daya akai masa adon pink dayan kuma aka zuba masasa irin kayan Babban falo. Kamar yadda falon ta ma adon pink din akai mata

Dayar kofar ma, yar barende ce wacce zata fito dakai harabar tsakar gidan.  Sai bandaki da falo da dakin bacci.

Wannan shine bangaren mai gida Aslam, sai arabi'an cusin da aka saka masa red nd white. Haka ma bedroom din an zuba masa red an white kaya.

Kayan kallo da kayan electronic duk masu kyau da tsada aka zuba su

Gida sai sanyin AC da kamshin turaren wuta da yake.

Kowa ya je yaga gidan sai ya sanya albarka da addu'ar zamab lafiya.

Haka suka ajiye Asma'u a dakin ta, suka karai mata nasiha sannan suka mike suka tafi.

Zainab ce kadai a wajen ta, Asma'u kuwa har lokacin in banda kuka ba abinda take.

Jin kan ta take kamar zai fadi dan ciwo. Zainab ce ta zauna a gefen ta, ta kamo hannun ta.

Dagowa tayi

Please Login or Register in order to submit comment