Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan yiwa Dady sallama.

Dady ya amsa yana kallon ta ya saki murmushi ya ce,
" *Husnah* kinyi kyau!"

Murmushi tayi ta zauna suka gaisa, anan yake fada mata ginin asibitin da ake mata ya kammalu dan haka zai je yayo order kayan da za'a zuba.

Asma'u baki yaki rufowa sai murmushi take tana ta godiya ga Dady.

Ba abinda Dady yake so kamar yaga ya farantawa iyalan sa.

Hannun ta ya kamo ya ce,
" *Husnah* ki kara gwazo ba abinda bazan miki ba in dai bai fi karfi na ba kome ne indai kina so zan miki."

Murmushi tayi ta ce,
"Dady nagode!"

Abinci ta hada masa, kallon ta yayi nan da nan ta gane abinda yake nufi dan haka ta fara hada tea.

Agogo ta kalla taga har karfe takwas tayi. Yau za'ai submitting assignmenat din Sir Sabir gashi ya ce in takwas da rabi tayi monitor yakai masa.

Tana rasa dalilin da yake sata tana yawan makara.

Ba yadda zatai yiwa Dady haka ta zauna ta dinga cusa abinci har ta gama ta mike.

Kudi ya bata ta amsa tana godiya tai masa sallama ta yi dakin Yaa Buhari,

Yau taci sa'a ta same shi yana shiryawa. Murmushi tayi tana murna zai rage mata hanya. ta ce,
"Na Anty Zee barka da safiya!"

Kallon ta yayi ya ce,
"Barka kadai ya kika tashi?"

Ta ce,"
"Lafiya Alhamdulillah! Yaya dan Allah...."
Sai kuma tayi shiru

Kallon ta yayi ya ce,
"Dan Allah me?"

Kai ta dan sosa tace,
"Wallahi na makara gashi malamin mu ya ce Takwas muyi submitting din Assignment."

"Ke kika sani!"
Ya fada yana taje kan sa.

Kallon sa tayi ta kalli agogon dake hannun ta. Ido ta zaro ta ce,

"Inna illahi wainna illahir rajiun!"
Ta fada tana fashewa da kuka.

Kuka take sosai, tana bubbuga kafa a kasa kai kayi zaton dukan ta akayi.

Kallon ta Buhari ya tsaya yi, dan inda sabo ya saba da halin Asma'u na shagwaba.

Sai da yaga da gaske dai take sannan ya mike ya kamo ta.

Kukan ta cigaba dayi shi dariya ma ta bashi.

Da wannan kukan da ta tsaya yi ta dauki kusan minti uku dama zuwa tayi Baba ya kai ta amman ta tsaya.

"Yi shiru yi shiru, shige muje!"
Ya fada yana daukar hular sa ya saka

Hannun ta ya kama sukai dakin Mami, gaisawa sukai ta tsaya kallon Asma'u ta ce,
"Wannan kuma fa?"

Ta fada tana nuna Asma'u. Dariyar Buhari ya danne ya ce,
"Shagwaba daga ta makara sai kuka."

Mami ta ce,
"Ai Asma'u akwai wasa wallahi kasan Allah tin asuba bata komawa amman da ta gama taya ni aiki ta shiga wanka sai ta dauki kusan awa tana wanka bare shiryawa kuma tayaya baza ta makara ba."

Murmushi Buhari yayi ya ce,
"Uhm Ai "Asma'un Dady sai Dadyn. Mami mun tafi sai mun dawo."

Ya kama hannun ta suka fice Asma'u na dagowa Mami hannu.

Murmushi Mami tayi itama ta daga mata hannu. A ranta tana cewa,
"Asma'u kenan."

A mota ma haka ta dinga a zalzala shi amman ina tin a gida takwas da rabin ma tayi.

Tana zuwa taga da malami a ajin a haka ta shiga ta zauna suka dinga amsar lecture.

Sai da malamin ya fita Zainab ta karaso gefen ta tana dafa ta.

Kallon ta Asma'u tayi fuskar ta dauke da damuwa. Ta ce,
"Kiyi hakuri ki tashi muje ki kai masa ki bashi hakuri."

Baki Asma'u ta rike ta ce,
"zai amsa."

Zainab ta ce,
"Insha Allahu."

Agogon hannun ta Asma'u ta kalla ta ce,
"Sis kinga fa har sha daya."

"Tashi muje insha Allahu zai amsa."
Mikewa Asma'u tayi jiki a sanyaye suka nufi wajen office din malamai.

Suna zuwa gefen office din Zainab ta ce,
"Kije ki fito ina jiran ki."

Fuska Asma'u ta bata zatai magana Zainab ta ce,
"Kiyi hakuri kisan dai malamai basa son rakiyar nan ko?"

Kai ta gyada ta tsaya ta kasa tafiya. Zainab ta ce,
"Haba Asma'u kije man."

Kamar bazata je ba kuma sai ta fara tafiya a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Zainab na kallon ta tasan halin Asma'u zuwan ne bata sonyi. Take wannan tafiyar kamar me.

Murmushi tayi ta karasa karkashin wata bishiya ta zauna.

Asma'u kuwa ji take kamar ta juya gaban ta sai dukan uku uku yake a haka ta karasa har kofa office din da aka rubata *Sabir Marzuk*

A hankali tayi knocking wanda ita kanta ba dan ita tayi ba da bazata ji ba.

Sai da tayi irin knocking din nan sau uku sannan ta samu tayi da dan karfi.

Izinin shiga ya bayar. Handle din kofar ta murda a hankali ta bude.

Wani kamshin turare hade da sanyi me dadi taji yana tashi.

A hankali ta kutsa kai ciki tana yin sallama kamar bata so.
"Assalamu Alaikum!"

Dago kai yayi jin muryar ta. Kallon ta ya tsaya yi kafin yai saurin kawar da fuskar sa, ya amsa da
"Wa'alikum salam!"

Kai tayi kasa dashi ta kasa magana. Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu.

Shi kam kallon ta yake kawai yana mamakin ta.

Tsaki tayi a zuciyarta ta ce,
"To me zan ce?"

Da kyar ta iya dago kanta ta ce,
"Uhm uhmm Sir dan Allah ina neman taimakon ka ne?"

Kallon ta shima yayi ya ce,
"Ok!"

"Uhm Uhm!"
Sai kuma tayi shiru.

Murmshi yayi ya ce,
"Ki saki jikin ki me zan taimaka miki dashi."

Yai maganar cikin harshen turanci.

Dan sanyi taji ji a ranta da bai mata rashin mutunci ba.

Dagowa tayi suka hada idon. Idon ta Cike Da kwalla kamar zatai kuka. kallon ta yayi yai saurin kawar da fuskar sa. ta ce,
"Sir Assignment nazo nai submitting"

Kallon ta ya tsaya yayi, yana mamakin ta, 'wai Assingment tazo kawo wa."

Asma'u ta ce,
"Sir Kayi hakuri na zo a makare ne."

Ta fada murya na rawa. Hannu ya mika mata kawai.

Jakar ta tai saurin a jiyewa kan kujerar dake gaban table din sa.

Dauko takardar tai a cikin wani littafi ta mika masa.

Amsa yayi ya zubawa sunan ta ido.

*Asma'u Suleiman* rubutun ya kalla yaga kamar computer ce ta rubuta shi.

Sai da ya kai hannu ya shafa ssanan ya kara kallon sunan ya ce
" *Asma'u Husnah* "

Wata faduwar gaba Asma'u taji tai sauri dago idon ta.

Dan duk duniya a wadan da ta sani take rayuwa dasu mutum biyu ke kiran ta da *Husnah* ko su ce, *Asma'u Husnah* sai kuwa yanzu da taji shi ya ambata.

Sunan yai dadi da yadda ya kira ta sai taji kamar Yaa Aslan ne ya kira ta.

Kai kadai ta gyada masa, ya ce,
"Zaki iya tafiya."

Jakar ta ta dauka, ta ce,
"Nagode!"

Ta juya a hankali ta bar office din.

Zainab na hango ta ta mike ta ce,
"Ya dai ya amsa."

Kai kadai ta gyada mata ta ce,
"Muje kar malama safiya ta shiga."

Suka kama hannu suka tafi.

Sai da aka tashi suka fito sukai sallah suka yi wajen Baba da yazo daukar ta.

Munasha ce ta karaso gun da sauri tta ce,
"Hae Babies!"

Da sauri suka juya. Amsa'u ce ta danyi murmushi ta ce,
"Sannu!"

Zainab kuma ta hade rai tana yin gefe.

"Baby an tashi ko ina Yayan ki?"
Amsa'u ta ce,

"Yana nan lafiya."
Munasha ta ce,
"Dan Allah wane irin aiki yake yi ne?"

Asma'u ta ce,
"Likita ne!"

Ido Munasha ta bude ta ce,
"Wow kace gidan ku kwari ne, amman ya dace likita. in kinje ki gaishen dashi."

"Zai ji insha Allah!"
Ta fada tana juyawa.

Munasha ta ce,
"Tnc bye!"

Ta juya kawar ta na bin bayan ta.

Zainab ce ta karaso ta ce,
"Ke baza ki daina kula ta ba ko?"

Fuska Asma'u ta marairaice ta ce
"Ya zanyi kina ganin dai ita ke kula ni."

Kallon ta Zainab tayyi ta ce,
"Sai da safe."

Ta shige motar gidan su. Kallon ta Asma'u tayi itama ta shige mota tana murmushi.


*Yan uwa dan Allah ina barar addu'a ku in kunyi sallah ku sani a addu'a Allah biya min bukatuna na alheri*

*Mutane da yawa na kira da min text na yadda suke jin dadin kasancewa dani nagode Allah ya bar kauna*

Fatan alheri ga dukkan yan uwa musulmai tare da murnar shiga cikin sabuwar shekara.

*Muna rokan Allah yasa mu dace. Allah kuma ya bamu ikon masa biyayya Allah ya sa muga wata shekarar da rai da Lafiya.*

*Happy new Year*



*INDABAWA*
[1/18, 14:12] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
ASMA'U HUSNAH



By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*


Dedicated to *My Ummi*
*ALLAH BIYA MIKI BUKATUN KI NA ALHERI*


*61-65*


*Masu hikima sun ce: Rayuwa ta tambayi mutuwa, me ya sa mutane suke so na, amma ba su son ki? Sai mutuwa ta ce, saboda Ni Gaskiya cee Mai Daci. Ke kuma qarya ce mai cike da ado da Daukar hankali.*






Tana zuwa gida ta shige tai wanka sannan ta dawo wajen mami dake falo.

Mami ta ce,
"Ya makaranta?"

"Mami makaranta lafiya Alhamdulilah!"
"Allah taimaka!"

"Ameen! Mami Dady bai dawo ba, me kika dafa."

Mami ta ce,
"Shinkafa da miya."

Mikewa Asma'u tayi ta dauki waya dan taji yanzu Dadyn ta zai dawo ko sai anjima.

Yana dauka ya ce,
" *Husnah* ya makarantar ne?"

Murmushi tayi ta ce,
"Dady har na dawo kuma Mami ta ce baka dawo ba yanzu zaka dawo ko sai aajima."

Murmsuhi Dady yayi ya ce,
"Sai anjima."

Ta ce,
"To Dady bari na kawo maka abinci kar ka ci na waje kaji."

"To *Husnah* baki gaji ba."
Kai ta girgiza ta ce,
"Ban gaji ba Dady."

"Shikenan kisa Baba ya kawo ki sai kin zo."

"To!"
Ta kashe wayar.

Kitchen ta shiga ta hada musu abinci a katon basket sannan ta dauko jug ta zuba lemon da mami ta hada.

Sai da ta gama hada komai sannan ta fito ta hau sama.

wanka tayi ta saka atampa dinkin riga da siket ta dauki hijab iya gwiwa ta saka.

Kasa ta sauko hannun ta rike da wayar ta.

Tana sauka ta ce,
"Mami sai na dawo!"

Mami ta ce,
"A dawo lafiya."

Ta duko baske ta fita. Baba na gganin ta ya ttaso ya ce,
"Sai ina kuma?"

Ta ce,
"Wajen Dady."

Ya ce,
"To muje!"

Yai gaba tabi bayan sa. Suka dau hanya. Basu dade ba suka karasa office din Dady.

Suna zuwa wani masinja yazo ya dauki basket din yayi offfice din Dady.

Tana shiga ta dauki kudi a wata loka a cikin office din ta mika masa.

Godiya ya dinga yi dai dai fitowar. dady daga toilet.

Karasawa tayi tana cewa,
"Dady sannu ya aiki?"

Dady ya ce,
" *Husnah* ke zanwa sannu kinje kinsha makaranta.."

Murmushi tayi ta ce,
"Dady yau ba gajiya kaga biyu mun gama komai."

"To Alalh bada sa'a.
"Ameen Dady!"

Ta dauki basket din ta fara zuba masa abinci.

Sai da yaci ya koshi sannan ta ce,
"Dady bari naje wajen Yaya."

"To a dawo lafiya."
Ta fita.

Knocking tayi a office din sa amman shiru.

Tura kofar tayi kawai sai gannin shi tayi kwance ya lumshe ido yana amsa waya.

Dagowa yayi ya zubo mata ido, ta ce,
"Ina ta bugu yanzu da wani ne ya zo da sai dai ya koma."

Hannu ya daura akan lips dinsa ya ce,
"shitt!"

"Naki nayi shiru."
Ta fada tana dire masa fulas din a gaban sa tayi kan kujerar ssa ta office ta zuna.

Juyi yake yi akan kujerar tana murmushi a ranta ta ce,
"Wani lokacin tana nata office din tana duba mara sa lafiya."

Dariya ta saki ta ce
"Yaya dan Allah kallo ni a office dina."

Baki ya tabe ya ce,
"Ai ba kyau kikai ba."

Dariya tayi ta ce,
"Kyan kaga nayi.'

Ta mike ta ce,
"Uhmm bari naje na taya Dady aiki."

Ta fice ta koma office din Dady. Gyara masa ta hau yi ta gyara masa ko ina ta share sannan ta zauna.

Dady ya ce,
" *Husnah* kenan sarkin aiki mijin ki ya huta komai kin iya ga tsabta."

Murmushi kawai tayi ya zaro wayar sa ya ce,
"Zo kiga kayan da aka turo sun miki naje na karbo ko wasu kike so."

Ya fada yana dubo pics din. Matsowa tayi gefen sa ta zauna.

Mika mata yayi ta dinga kallon kayan ta ce,
"Masha Allah Dady sunyi."

Dady ya ce,
"Kin tabbata."

Kai ta gyada masa. Ya ce,
"Shikenan nan da sati biyu nake son tafiya. Da ba ckul da mun tafi tare."

"Wallahi kuwa?"
Haka suka zauna Dady na aiki tana taya shi hira har karfe shida tayi.

Buhari ne ya shigo office din ya ce,
"Dady ni zan tafi sai kun taho."

Dady ya ce,
"To muma fitowar zamuyi."

Gefen Asma'u yayi ya mata rada. Hararar sa tayi ta mike.

"Dady muje""
Ta yi gefen sa.

Mikewa Dady yayi ta kamo hannun sa suka fito.

A hanya kafin su sauka sai sallama akewa Dady jama'a sai gaishe shi suke.

Dady mutum ne mai son jama'a da taimako kowa nasa ne.

Dady yana da mutane sosai dan duk wanda ya kawo.kuka sa sai ya taimaka masa.

Suna isa gida ana magariba dan haka parking kawai sukai suka yi alwala suka tafi masallaci.

Asma'u kuma ta yi cikin gida sama ita ma tayi tai alwala tai sallah ta zauna har akai isha.

Sanna ta sauko. Su Dady ta gani har sun shigo Mami na gefen sa.

Mikewa sukai suka hau sama Dady ya watsa ruwa ya saka jallabiyya sannann ya sauko suka ci abinci

Karfe Tara Asma'u tayiwa Dady sallama. sannan ta matsa gun Mami shima tai masa.

Wajen Yaya Buhari tayi, tana murmushi kafin ta karasa ya mike.

Kallon sa tayi ya ce
"Lafiya?"

Hararar ta yayi ya ce,
"Abu zanje na siyo."

Kallon sa tayi ta ce
"Dan Allah Yaya ka tahon da ice cream dan Allah!"

Wajen Dady yayi ya duka ya ce zai fita yanzu zai dawo sannan ya kalli Mami ya ce,
"Mami me zan taho miki dashi?"

Mami ta ce,
"Ni ba komai a dawo lafiya."

Ya juya zzai tafi Asma'u ta saki kuka. Da sauri ya juyo Dady ma ya mike da sauri.

Mami kuwa da tasan halin ta yasa ta dauke kai. shi wanda yai mata laifin yafi kowa son jin me akai mata.

Gun Dady tayi ta ce,
"Dady ba Yaya Buhari bane, nace ya siyon aabu yai min banza."

Kai Dady ya dago ya kalle shi. Shi kuma ya ce,
"Haba kanwata ai naji wasa fa nake miki."

Kai ta dago tana goge hawaye ta ce,
"Da gaske?"

Kai ya daga mata ta ce
"To a dawo lafiya. Ni sai da safe."

Ta fada tana mikewa tayi ta ce,
"Dady Sai da Safe. Mami sai da safe."

Suka ce,
"Allah tashe mu lafiya"
Ta nufi dakin ta.

Yaya Buhari kuwa ajiyar zuciya ya sauke, ya fita.

Mami ta ce,
"Allah Dadyn Asma'u ku kuke sa Asma'u kara sa ta gainin yarinya ce. Yarinyar nan fa girma take ji abinda tayi sai kace yar shekara biyar."

Murmushi Dady yayi ya ce,
"To in ban kula da Asma'u ba da wa zan kula."

Murmushi Mami tayi ta ce,
"Ai shikenan tai ta zama aa yarinyar kuwa "

Murmushi Dady yayi ya ce,
"In girman yayi zata girma ne amman yanzu nawa Asma'un take. Dan dai tayi nisa a karatu ne kike ganin girman ta amman waasu kamar ta ma suna secondary school."

"Ai kai dai baza ka taba yadda ba "
Daga haka suka cigaba da hirar su.

Asma'u kuwa tana shiga daki tayi wanka ta fito ta saka kayan baccin ta.

Kan gado ta kwanta tana daukar wayar ta. Missed call din sa ta gani. Ido ta bude ta tafi kiran ta.

Da sallama ya dauki wayar. Ido ta lumshe jin muryar sahibin ta.

Kwanciyya ta gyara sannan ta amsa sallamar tata.

"Baby na kina lafiya ya gida da makaranta?"
"Lafiya lou Yaya na, ya su Momy da wajen aiki?"

"Duk lafiya Alhamdulilah!"
"Masha Allah!"

" *Husnah* tin dazu nake kiran ki. zan zo wani aiki Kano nake son na fara fada miki."

Da sauri ta mike ta ce,
"Yaya dan Allah da gaske?"

Kai ya gyada kamar yana ganin ta ya ce,
"Da gaske zan zo nayi wata daya ne."

Murmushi tayi ta ce,
"Kai Alhamdulilah Allah kawo ka lafiya amman naji dadi wallahi. Yaushe zaka zo?"

"Eh nan da sati biyu zan taho."
Murmushi tayi ta ce,
"Allah nuna mana."

"Ameen!"
Ya amsa.

"Yauwah Yaya gobe zamu yi test ina son ka sani a addu'a."
Murmushi yayi ya ce,

"To Allah bada sa'a amman dai ni bana jin ki *Husnah* yanzu ma kafin ki kwanta ki dan duba littafin kinji."

"Insha Allahu da asuba ma zan kara dubawa."
"Yauwah Allah bada sa'a!"

"Yanzu ki dauko littafin kiyi karatun awa daya zan kira ki anjima."
"To!"

Ta kashe wayar. Mikewa tayi ta dauko jakar ta.

Test din Sir Sabir zasu yi gobe dan haka ta kuduri aniyar gobe da wuri zata fita.

Sai da ta gama karatun kamar yadda Yaa Aslam ya ce, tayi sannan ya kira ta.

Alwala yasa tayo ta shiga tayo tazo tai adduu'a ta kwanta.

Karfe sha biyu Mami ta leko dakin taga Asma'u kwance akan gado. Addu'a tai mata ta tofa masa sannan ta fice.

Don't forget to vote




*INDABAWA*
[1/18, 14:13] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
 *ASMA'U HUSNAH*



By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My habibaty. My Ummu*


*65-70*


*Idan ka Dauki Alqur'ani Shedan yakan fusata. Da zaran ka bude shi sai ya fashe da kuka. Kana yin Bisimilla zai fadi qasa warwas. Da ka shiga cikin karatu sai ya suma ya fita hayyacinsa. Mu yi qoqari mu rinjayi Shedan*





Washe gari kamar yadda ta tashi tin asuba ta tashi.

Sallah tayi ta zauna tai karatun al kur'ani sannan ta janyo littafin ta ta kara dubawa ta jima tana duba littafin sannan ta mike ta sauka kasa. Mami ta dan kamawa abubuwa ssannan ta koma sama.

Wanka tayi ta shirya cikin wata maroon kalar doguwar riga mai dogon hannu.

Golding din takalmi da jaka ta dauka sai bakin hijab da ta saka iya kar sa kirji.

Ba karamin kyau tayi ba fuskar ta tayi fes a ciki.

Idonun ta sun kara gaske da girma girar nan tata a kwance luf luf. Leben ta sai kyallin man lebe yake.

Dakin Dady ta shiga suka karya sannan tai musu sallama ta fito ta tafi dakin Ya Buhari.

Yana zaune a gaban system ta same shi. Karasawa tayi ta ce,
"To su Yaya me ake aka tashi da sasafen nan.""

Bai kula ta ba. Dan durkusawa tayi ta gaishe shi. amsawa yayi yana dagowa ya kalle ta.

Baki ya tabe ya ce
"Baki kyau ba."

Murmushi tayi ta ce,
"Kyan kaga nayi."

"Ahakan?"
Kai ta gyada masa.

"Uhmm dauki abonki afirij."
Ya fada yana nuno mata firij din.

Gun firij din tayi ta bude. Ice cteam ta gani a ciki dayawa. biyu ta dauka ta ce,

"Yaya in na dawo na dauki sauran."
Kallon ta yayi ya ce.
"A dawo lafiya."

Sannan ta fita. Dakin Mami taje tai mata sallama sannan ta sauka kasa.

Baba yana ganin ta ya taso yayi wajen motar ya fito da ita.

Sai da suka gaisa sannan ta bude gidan baya ta shiga.

Kiran Yaa Aslam ne ya shigo dauka tayi,
Bayan sun gaisa yake cewa "amman dai tana ckul ko?"

"Aah Yaya yanzu dai zan tafk.""
"Amman dai kinsan kin makara a yadda kika fadan kina da test ko?"

"Ah haba dai!"
"Eh man tara saura minti goma. Minti goma zai kai ki ckul ne."

"Insha Allahu!"
"To Allah bada sa'a sai kin dawo ki turon pics din ki ina jira."

Ta katse wayar selfie ta dauka ta tura masa sai anan taga ashe dai da gaske Yaa Aslam yake ta makara ta tabbata nan da minti goma da kyar zasu karasa.

Addu'a take Allah yasa kar ya shiga har sai ta shiga.

A hankali Baba ya dinga jan su har suka karasa makaranta.

Lokacin tara da minti goma. Da sauri ta fita daga motar.

Hango shi tayi yana nufar ajin cikin takun kasaita yake tafiya.

Yana sanye da golding kala shadda ya saka brow kalar takalmi da hannun sa rike da waya ya kara a kunne daga gani amsawa yake.

Ba kara min kyau yayi ba. Fatar sa ta kara kyau da sheki. Gashin kansa ya kwata luf luf dashi.

Ganin ya karasa ajin ma. yasa ta tsaya daga inda take hangen sa.

Waje ta samu ta zauna daga gefen ajin ta kifa kanta akan jakar ta ta fashe da kuka.

Ta dade tana kukan dan har karfe goma bata dago ba tana ta shesheka.

Karfe goma dot ya fito daga ajin rike, da takardu a hannun sa. Yana karasowa inda take akai kiran wayar sa.

Daukar wayar yayi, ya kara a kunnen sa yana kallon Asma'u da ta kifa kai.

A wajen ya tsaya ya amasa waya, tana jin yadda yake maganar a hankali amman ta kasa dagowa.
"Yanzu zan karasa office din kin karaso ne?"

Ya tambaya.
"Ok!"
Kawai ya ce ya kashe wayar.

Sai da ya kara kallon ta sannan ya bar wajen. yana barin wajen zainab ta karaso tana dago kanta.

"Kuka!"
zainab ta fada tana share mata hawaye.

"Ba dole nai kuka ba. Wannan course din kar ya jawon Matsala fa"
Ta fada tana kara fasa wani kukan.

"Haka ne, amma kinsan Sir Sabir yana da sauki kai da kin shigo zai iya barin ki."

"Haba Zainab sau nawa nake makara yake kyale ni so kike a fara kawo wani zargin bayan kinsan baya bari a shigar masa aji duk wanda ya makara daya ga ya shiga juyawa yake."

"Kinga bar wannan zancen kije gun sa, kawai ki baahi hakuri kiji me zai ce,
ya kara bada wani Assignment din ma in bai miki ba kinga kina da assignment balantana ma insha Allahu zai miki."

"Uhmm fa Zainab kar naje yaki min. Ni dai wallahi na hakura"

"Dallah can tashi muje!"
ta kamo hannun ta suka nufi office din sa.

A bakin office din ta bar ta. Yauma kamar rannan ta dade tsaye a kofar amman ta kasa kwankwasa kofar

Cikin sanda ta dan kwankwasa. Izinin shiga ya bada. wata faduwar gaba ce ta sameta.

A hankali ta daura hannun ta akan kofa, ta murda ta budo. Nan ma ta dau minti biyu kafin ta tura ta shiga.

Tana shiga taji wani sanyi me ddi hade da kamshin turare na dukan ta.

Tsayawa tayi a gun kafin tayi sallama. wata yarinya dake gefen sa, tana bude masa fulas din abincin data kawo ta zuba mata ido.

Yarinyar zata yi shekara goma sha shida zuwa sha bakwai Kyakyawa ce suna kama da Sabir kamar kanwar sa.

'Yar yayar sa ce tazo musu hutu shine Mamah ta aiko ta, ta kawo masa abinci dan tasan halin sa da kyar zai ci wani abu gashi ya fito bai karya ba.

Kallon Sabir yarinyar tayi ta daga masa kai.

Ya ce,
"Uhmm Maryam zo ki tafi nagode kar Mamah ta tafi ta barki."

Maryam ta ce,
"Kai Uncle wallahi Mamah ta ce, in tabbatar da kaci tukkunna "

murmushi yayi wanda ya kara fitar da kyawun sa ya ce,
"Da yake, ni yaro ne ko. Ko ni yaro ne, ina uncle din ki zaki ce sai naci abinci ne, maza zo ki tafi kice naci kinji."

Ya fada yana daukar dankalin da aka soya a cikin kwai da attaruhu da albasa yana ci.

Gefen kuma kunun gyada ne da yaji madara.

Jakar ta ta dauka ta ce,
"Allah Uncle haka zan ce baka ci ba."

Tayi gefen Asma'u dake tsaye tana jin su.

"Sannu!"
Ta fada tana mika mata hannu.

Dagowa Asma'u tayi ta kalli yarinyar kamar su daya da Sabir.

Dan murmushi Asma'u tayi ta mika mata hannu ita ma suka gaisa.

Murmushi Maryam tayi ta ce,
"Sunana Maryam Suleiman ni 'yar yayar Uncle Sabir ce."

Kallon ta Asma'u tayi da idon ta da suka canja kala ta dan yi murmushi ta ce,
"Ni kuma Asma'u Suleiman!"

Maryam ta ce,
"Lah suna Baban mu daya amman wallahi Asma'u kin burge ni kawai naji ina sonki."

Murmushi Asma'u tayi ta ce
"Nagode sosai."

Sabir dake zaune yana cin dankali yana kallon su ya ce,
"To Maryam kije kar Mamah ta tafi ta barki dai Allah ke kadai zaki zauna a gida har magariba."

Sakin hannun Asma'u tayi ta ce,
"Na tafi sai nazo gun ki wata rana."

Murmushi Asma'u tayi ta daga hannu tana mata bye bye har ta fita.

Kai ta juyo ga sabir da ya zuba musu ido sai fitar da murmushi yake

Tana juyowa ya mai da kan sa ga abinda ke gaban sa.

Asma'u ta ce,
"Sir dan Allah ka taimaka min!"

"Dame fa?"
Ya fada yana cin dankalin sa cikin kwanciyyar hankali.

"Sir Test wallahi makara na yi shiyasa "

Bai dago ya kalle ta ba ya ce,
" *Husnah* wai ke kullun sai kin makara!"

Da sauri ta dago kanta jin sunan da ya ambata.

Ido suka hada wannan yasa tai saurin dauke kan ta.

"Ji idon ki me ya same shi? Kuka ko?"
Kai ta girgiza.

"To mene?"
"Ba komai."

" *Husnah* baki ban amsa ba. Me yasa kike makara?"
Shiru ta karayi.

"Tin yaushe kike tashi?"
Ya tambaye ta.

Asma'u ta ce,
"Asuba!"

Kai ya jinjina ya ce,
"Me kike yi har kike makara?"

"Ba komai!"
"Ba komai amman kuma kike makara?"

Kai ta gyada.
"Ki fadan abinda kike in kika tashi tin asuba."

Kasa tayi da kai ta ce,
"Mami nake dan tayawa aiki sai nai shirya. Kuma in nace bazan karya ba sai Dady ya zaunar dani sai naci. daga nan sai naje na tashi Yaya Buhari na gaishe shi na taho makaranta."

Murmushi yayi jin yadda take maganar cikin shagwaba. ya ce,
"Ku nawa ne a gidan ku?"

"Daga Dady sai Mami, sai Yaya Buhari sai ni!"
Ta fada tana wasa da hannun ta.

"Kina da kanwa ko kani?"
Kai ta girgiza ta ce
"A'ah!"

Ya ce,
"No wonder ashe shiyasa kike shagwaba ko dan kece autah ko?"

Fuska ta dan bata tayi shiru. Ya ce,
"Eh mana. In ba haka ba menene na kuka dan baki shiga class ba."

Shiru tayi ya ce,
"Dauko takarda."

Tai saurin ajiye jakar ta tana daukar wata takarda.

Kujera ya nuna mata ya ce,
"Zauna!"

Ta zauna. question din ya karanto mata ta rubuta.

Abincin sa ya cigaba da ci cikin kwanciyyar hankali. Sai da ya gama ya koma cikin office din inda aka zuba masa wasu hadadun kujeru da kayan kallo.

TV ya kunna ya rage volume


*Wai ya kuka gani? Shin wa yafi dacewa da Asma'u. Yaa Aslam ne ko Sir Sabir*

*kuna jin dadin lbrin kuwa?"




*INDABAWA*
[1/18, 14:13] Maryam S Indabawa🥰:

Please Login or Register in order to submit comment