Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mamah na zaune kan kujera, tana kallon suka shiga.

Suna shiga Mamah ta mike tana cewa,
"A'ah wa nake gani.kamar Asma'u!"

Ta kamo ta. Sabir ne ya ce,
"Ba kama ba ce ita ce."

A kan kujera ta zaunar da ita Asma'u ta zame ta zauna a kasa.

Gaishe da Mamah tayi cikin girmamawa da kunya.

Mamah ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar ta, yasu mami da Buhari.

Ta bata amsa. Mamah da kanta ta kama Asma'u suka nufi daining tana fadin
"ince daga aiki kike zo muje kici abinci "

Sabir kallo yabi su dashi, ba karamin burge shi sukai ba.

Bayan su yabi ya cewa,
"Mamah ta samu Asma'u yau ta manta dani."

Dariya Mamah tayi ta ce,
"Ai dole na kula da Asma'u na manta da kai."

Suka zauna. Abinci ta zubawa Asma'u. Shinkafa ce da taloya da miya da taji naman kaji, sai hadin kabeji da lemon kwakwa.

Kasa ci Asma'u tayk sai juya cokali da take, sai da Mami ta mike, sannan ta fara ci a hankali.

Sabir kam ido ya zuba mata yadda take cin abincin ma daban ne.

Jin ido akan ta yasa ta dago. Ido hudu sukai, Cokalin ta ajiye ta daina cin abunci.

Da ido da hannu ya tambaye ta
'lafiya'

Kai ta dauke kawai, murmushi yayi ya ce,
"To sorry Baby nah, kici na daina kallon ki"

Ya fada yana dauke ido daga kallon ta, abincin shi yaja gaban sa yana ci.

Itama ci ta cigaba dayi. Sai da suka gama sannan suka koma falo.

A gidan sukai sallah magariba sannan suka mike tanawa Mamah sallama.

Wani hadin turaruka Mamah ta bata, amsa Asma'u tayi tana godiya.

Gida suka tafi tare suka shiga ciki. Mami na ganin su ta ce,
"To kuna tare kenan!"

Kai Asma'u ta daga ta ce,
"Kinga kayan da Mamahn Sir Sabir ta bani."

Amsa Mami tayi ta duba tana godiya ta kalli Sabir ta ce,
"Angode Allah saka da alheri."

Murmushi kawai Sabir yayi ya zauna. Asma'u dake gefen Mami ta kalle ta, ta ce,
"Mami ina Yaa Buhari?"

Mami ta ce,
"Yana gun Zainab!"

Baki Asma'u ta tabe ta ce,
"Yaya ba a kara sauran kwana nawa ta koma gunsa gaba daya."

Murmushi Mami tayi ta ce,
"Asma'u daru."

Mikewa tayi tai sama tana cewa,
"Bari naje nai wanka. Nai sallah."

Tayi sama.





*MS Indabawa*
[1/18, 14:32] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
 ASMA'U HUSNAH


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*46-50*

Dedicated to my love mother. *Momy nah*

Really love u

An Ruwaito Cikin Littafin Ibn Sinni, Daga *Anas (ra)* Lallai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: "Shin 'Dayanku Zai Gajiya Ya Zamo Kamar Abi-Damdama?" Sai Sahabbai Sukace Wanene Abu-Damdama Ya Annabin Allah? Sai Yace: Ya Kasance Idan Ya Wayi Gari Yana Cewa: *{Allãhumma Inni Qad Wahabtu Nafsi Wa Irdi Laka, Falã Yashtumu Man Shatamahu, Wala Yazlimu Man Zalamahu, Wwala Yadribu Man Darabahu}*


*KARASHEN LBRN Munasha*

A cikin kawayen ta mutum daya ce ta arxiki. Wacce tun fara bin mazan ta take mata fada akan irin samarin da take kulawa.

Dan ke daga ganin samarin ma xaka san yan iska ne, bare in suna mu'amala suyi ta taba ta. Ko ace za'a tafa.

Ko in tana bukatar abu sai dai tace saurayi yayi mata.

Rashida yar gidan masu hali ce, dan sau tari takan bata kudi kashe wa. Sannan in an mata kaya kala uku zata dau daya ta bata.

Amman sam Maimuna bata godewa Allah. Ita burin ta tagan ta ta kula me kudi wanda zai na kashe mata kudi.

Bayan yawancin samarin yanzu basa yin abu dan Allah sai dai in zasu fansha.

Rashida takan mata fada.
"Haba Maimuna, yanzu da hankalin ki, kike kula wadan nan mazan.
Shin me yan mata memukeso muzamane, ina hankalin mu yake ina tunanin muyake ne, Shin iyayen mu me suka gaza yimana muke nema mudorawa kan mu akan hanyar da baza ta bulle da mu bane. Duk kokarin da Baba yake, amman kike son daurawa saurayi duk buqatar ki.
Haba yar uwata ashe kinyadda saurayinki xemiki abunda iyayenki baxasu yimiki, Maimuna ki nemo hankalinki da nutsuwar ki6oye son abun duniyarki badon komaiba sedan kitsira da martabarki taki ta 'ya mace.
saurayi nagaskiya shine wanda yake sonki da aure baya neman komai daga gareki burinsa yaga kin tsira da mutuncinki.
Saurayi mayaudari shine Wanda yake miki hidima ba don Allah ba sedan kibashi gishiri yabaki manda.
Mace wadda akasanta da kunya, tarbiyya, mutunci, Jan aji, kamala, sanin yakamata, amman kin manta dacewa yanxu xamani yasanja wasu daga cikin samari sundena abu dan Allah sedan samun riba.
wallahi Maimuna, idan saurayi yafuskanci ke kinada kwadayi akwai matsala ta hanyar haka xesamu damar isar da qudurinsa, wallhi saurayi bashida abun duniyar daxe rudeki yaxubar miki da mutuncinki bashida abunda xemiki wanda iyayenki xasukasa.
Alokacin bakida damar hanashi duk abinda yanema domin shi kika fara mora. kinsan ko farce yata6a miki yacuceki dan Allah Mainuna ki kula."

Duk lokacin da Rashida tai mata fada takan dauka.

Amman da ta hadu da yan harkar ta zata manta.

In kuma Rashida tai musu fada gaba dayan su, sai suce dan ita Rashida din yar masu Hali ce shi yasa bata san halin da suke ciki ba.

Tin asali Yayan Rashida ke son Maimuna, amman tafiyar sa karatu malesia, shi ya sa soyayar ta ja baya.

Duk da a cikin zuciyar sa bai da burin da ya wuce ya kamala karatu ya dawo ya tai maki rayuwar Maimuna da mahaifin ta ba.

Itama a zuciyar ta shi take so, dan Nasir namiji ne wanda ya amsa sunan namiji, ya hada komai kyau ilimi da gayu.

tinda ya tafi be dawo ba duk da suna waya amman karatu yana dauke hankalin sa. Ba dan baya son ta yafi bawa karatu lokacin sa ba. A'ah sai dan son da yake yaga ya kammala karatun sa ya fito da sakamako me kyau.

Maimuna kyakyawa ce ajin karshe, fara me kyaun sura. Amman duk ta zubar da mutuncin ta.

Har Kungiya ce, da ita wace take daukar yara ta kaisu wajen manyan Alhazai.

Wanda har a cikin makaranta ma, akwai wadan da suka daure mata gindi.

Yanzu haka Munasha ta zama kwarariya dan ta kama naira a hannu.

Yanzu haka da taga saurayi yayi mata zata san yadda zatayi ta ja hankalin sa.

Har wajen malamai take kai mutum a janyo mata hankalin sa. Munasha babbar yar duniya ce wcce idon ta ya gama budewa.

Ba kasar da bata fita.

A harkar karuwanci dai ta fita zakkah. Amman duk da haka, son Nasir na cikin ranta.


*-*-*-*-*-*-*-*-*

Kwance take a kan gadon ta, sanye take da hijab fuskar ta, tayi kyau da ita.

Sai futar da annuri take, allon wayar take kallo. Wannan yasa na mika kai dan ganin abinda take yi.

Aslam na gano kwance akan katon gadon sa, yana sanye da blue (ruwan omo) din T-shirt, da blue din wando, da alamar kayan bacci ne a jikin sa.

Magana ya ke fada mata kunne na kasa ina sauraro.

"Ke na bawa zuciyata *Asma'u*, ki adanata dan nasan zaki mata gata,"

Murmushi *Asma'u* keyi. Sanna tace,
"Hmm Ya Aslam. Gakiya kam zan kula maka da ita fiye da yadda zan kula da tawa."

"Nima na sani. na baki ita ne saboda bana son kowa ya taba ta. Duk wanda zai shiga ke zaki bashi izinin shigar ta"
Murmushi tayi.

Ya cigaba da magana
"Dake na fiso muyi soyayya, sannan dake nafi son muyi rayuwa. Dan Banda kamar ki a duniya, wannan yasa na mallaka miki zuciya ta"

"Kai Ya Aslam!"
Ido ya kanne mata ya ce,
"Ke ta daban ce. Shi yasa kullum yabon ki nake. Ke nake son ki kasance a kusa dani. Dan kece kadai farin ciki na."

Shiru *Asma'u* tayi tana sauraron sa, tare da lumshe idanun ta.

Kallon kyakyawar fuskar ta yake yi.
"Ke ce Taurruwa ta. ke kika hasken zuciyata. Kin kawar min da dukkan damuwa ta. Ban da bakin magana gare ki ban san irin godiya da zan miki ba. Ban san kuma me kike son na miki ba."

Idon ta, *Asma'u* ta bude, ta kira sunan sa.
"Ya Aslam!"

Kallon ta yayi kafin ya amsa da
"Na'am Baby nah!"

Ta ce,
"Alkawari nake son karike min koman wuya kar mu rabu kaji."

Murmushi yayi, ya gyara kwanciyar sa. Yana kara fuskan tar ta.
"Alkawari na rike miki kuma koman wuya bazan rabu dake ba kinji."

"Nagode!"
Kallon ta yayi yana kashe mata idanu kamar me jin bacci.

Kasa tayi da kanta.
"Wallahi rabuwar mu abu ce me wuya dan mun zama hanta da jini. Ko 'da da uwa."

Dariya ta saka tana girgiza kanta. Shima dariyar yake.
"Wallahi da gaske nake. Na fada miki duk abinda kika ji na fada daga zuciyata yake. Abinda zuciya ta take ji kenan baki na ya furta miki."

"Na yadda da kai Yayanah. a zuciya ban da kamar ka komai nawa ya zama naka. Amman dan Allah kar ka yadani ka kula da soyayya ta. Dan kai dai na aminta dakai kuma na yadda da kai. Mun shaku mun saba Ya Aslam abin da ya rage kawai auren mu ne."

Ta fada yana rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta.
"Oo please kicire kunyar nan cigaba da narka min zuciya mana."

Ido ta zaro
"tayaya zan cigaba da narka maka zuciya. Yanzu ya zanyi in na narka maka zuciya."

"Sai muyi amfani da taki ko?"
"A'ah muyi amfani da taka dai."

"To cigaba ina jinki."
"Kai Ya Aslam"

Kunnen sa ya kama yace,
"Yana jira zai kaiwa zuciyar ki abinci taci."

Dariya ta saki.
"Ya Aslam kenan!"
"Allah yunwa take ji fa."

"Toh Zan kasance me share maka hawaye a duk lokacin da zasu zuba zan hana su zuba. Zan kyautata maka in faran ta maka."

"Allah tabbatar mana da Alheri, sannan nikai na bazan taba barin ki kiyi kuka ba."
"Nagode!"

"Ba godiya a tsakanin mu."
Murmushi sukayi gaba dayan su.

"Tashi kije kiyi Alwala kizo kiyi addu'ar bacci."
"Toh!"

Ta fada tana tashi. Ban daki taje tayo alwala.

Addu'a tayi, yana jin ta har ta gama.

Wayar ya kashe, sannan ya kirata. Kamar yadda ya saba yi mata kissa Annabawa haka ya farayo mata har bacci ya dauke ta.

Washe gari ya kama asabar dan haka tin da ta tashi da asuba tayi sallah.

Ta fara gyara dakin ta, tin daga karkashin gado har su durowar ta duk da ba datti amman sai da ta gyare ta goge ko ina.

Sannan ta fita madafin su (kitchen) ba kowa a ciki wannan ya tabbatar mata da Mami na can gyaran daki.

Dan duk karshen sati sai sun gyare gida ko ina da ina tsab.

Wake ta auna tayi waje dashi. Ban garen masu aiki tayi.

Baba Lami ta sama zaune. Gaishe ta tayi, sannan ta tambaya ko Lubabatu na nan.

Kiran ta Baba Lami tayi. Lubabatu na ganin *Asam'u* ta saki murmushi.
"Ina kwana?"
"Lafiya lou."

"Dan Allah daman waken nan zaki surfa min saboda kar na makara zan je isilamiyya."
"Bakomai kawo."

Ta mika mata. Ta juya ta fita.

Kunun gyada ta dama musu, sannan ta hau gyaran kitchen din nasu.

Sai da tagama gyara sannan Lubabatu ta kawo mata markaden.

Kayan hadi ta zuba sannan ta fara soya kosai.

Kosan kuwa yayi kyau dashi ya tashi abin sha'awa.

Tana gamawa ta gyara falon su, sannan ta jere kayan karin nasu a inda suke cin abinci.

Kitchen din ta gyara ta wanke duk abinda ta bata.

Dakin ta ta koma tayi wanka sannan ta shirya cikin riga da siket yan kanti.

Sai ruwan tokar hijab da ta dau wanda yake a wanke a goge dashi.

Dakin Dady tayi, ta gaishe dashi sannan suka sauko kasa, Mami ce ta sauko da Ya Buhari, suka gaisa. Sannan suka fara karya wa.

Suna gamawa ta mike ta haye sama. Hijab din ta! Ta saka wanda yake har kasa. Sai nikaf da ta saka kafar ta da safa.

Jakar ta ta dauka, ta fito.
"Mami da Dady na tafi sai na dawo."
"To a dawo lafiya Allah bada sa'a"

"Ameen!"
Ta fice.

Yan uwa ya daren?

Toh sai Allah ya kaimi gobe in muna da rai da lafiya.
Nagode

*INDABAWA*:
[1/18, 14:33] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*




*51-55*


don't Forget to vote

Da dare akai dinner inda yan mata sukai ankon wani pink material.

Amarya kuma ta saka golding kala, ango ma golding shadda ya saka.

Asama'u kuma ta saka Dark blue din material sosai tayi kyau.

Sir Sabir ma Blue shadda ya saka sai ya fito shima kamar angon Asma'u.

Anci ansha an yi liki, duk wanda yaga Asma'u sai ta burge shi dan komai nata da banne ga kyau ga jikin yana dauka.

Samarin wajen sun yaba da ita. Sir Sabir kuwa sai kareta yake.

Sai da sukaje suna liki ne, kuma sai kuka taga ga Mami ga Yaa Buhari gata ammn ba Dady.

Sosai ta sa mutane da yawa kuka a wajen.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Inda washe gari aka dau amarya aka kai ta gidan mijin ta dake rijiyar zaki.

Gida ne katon gaske dan Dady ne ya gina masa shi.

haka nan an zubawa Zainab kaya sosai. Sai da angwaye suka je sanna suka taho Asma'u na zolayar Zainab

Gida su Asma'u suka tafi da su Maimuna da Maryam.

Aka bar amarya da ango su kadai a gida.

A gida ma wasu dayawa duk sun tafi dan daga Momy sai matar Uncle Abubakar da Uncle iliyasu da Mama binta da zasu tafi gobe.


Washe gari da safe Mami ita ta aikawa da amarya da ango kayan kari.

Su Asma'u kuwa suna tare da kawayen ta. Lokacin su Hafsat da Maimuna sun shirya kayan su zasu tafi.

Sosai Asma'u ta hada musu kayan biki har da turmin atamfa.

Har gun Mami ta raka su sukai mata sallama.

Mami ta ce, a sa driver ya kai su gida. Haka ai kai kuwa.

Driver sshi ya kai ko wacce har gida. Gidan ya rage daga Asma'u sai Maryam da Nusaiba da ta ce baza su tafi ba.

Sai karfe daya suka shirya suka tafi gidan Amarya.

Suna zuwa suka tadda Amarya a falo taci kwalliya, sai kamshi take fitar wa.

Tana ganin su ta taro Asma'u sai da suka zauna kuma sai ta bata fuska.

Kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Lafiya?"

"Wallahi sis baki kyauta ba wai sai yanxu ni nayi zuciya."

Ta fada tana komawa gefen Maryam tana tambayar su ya gajiyar biki.

Dariya Maryam tai ta kalli Nusaiba ta ce,
"Yo ai ke zamuyi wa ya gajiya ko?"

Nusaiba ta ce,
"Lallai kam amman sai naga kamar ba ai komai ba."

Dariya Asma'u tayi ta ce,
"To ku ina ruwan ku."

Zainab ta ce,
"To waya fada muku sai kun gane anyi ko ba ai ba. Kowa da yanayin jikin sa haka nan wani yaji zafi wani bazai ji ba. Wani ya fitar da jini wani bai fitar wa. Wani tafiyar sa ta canja wani ba haka ba. Ke duk abinda zaku ji ana fadi ma wani vai san anayi ba. dan haka nidai baku jin baki na anan."

Asma'u ta ce,
"Dadin mutum yayi karatun bangaren lafiya kenan duk da zaku san hakan ai."

Maryam ta ce,
"Wai kuna so kuce duk abinda muke karantawa a littafi ba haka bane."

Kai Zainab girgiza ta ce,
"Ba haka bane jiki jiki ne. Wani zai ji abinda yafi na littafi wani zaiyi zazzabi wani har da suma da dai sauran su."

Kai Nusaiba ta gyada na gamsuwa da abinda taji.

Zainab ta ce
"Ku daure ku kai budurcin ku gidan mazajen ku dan ba darajar da takai wannan a idon mijin ku. Daga ranar da ya same ki a haka zaki ji dadin rayuwa aamman da ya samu akasin haka zaki gane kuranki."

Maryam ta ce,
"Sis wa yakai mu. Inda muke jin labarin wacce takai budurcin ta yadda take samun jin dadi. Akasi da wanda bata kai ba wulakancin duniya ya kare akanta ba ma wacce ta zibar da mutuncin ta."

Nusaiba ta ce,
"Shiyasa nifa Uncle Sabir yake burgeni. Ba ruwan sa bare har ya nuna yana son wani abu agun mace ko Sis."

Ta fada tana kallon Asma'u.
Asma'u da jin ta sako Sabir duk jikin ta yai sanyi ta gyada mata kai ahankali.

Daga haka suka cigaba da hira har Maami ta aiki da abinci da rana.

Sai yamma suka tafi bayan sun gyare mata gidan.

Gida suka wuce suna shiga suka zauna falo ana hira da su Momy da Mami.

Sosai Mami ke jan su a jiki sai kace sun saba.

Haka suka raba dare suna hira har Maryam tai bacci ta bar Asma'u da Nusaiba.

Nusaiba ce ta kalli Asma'u ta ce,
"Sis dan Allah in tambaye ki?"

Asma'u ta kalle ta ta ce,
"Ina ji!"

Nusaiba ta ce
"Dan Allah ki fada min gaskiya."

Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Karki damu!"

Shiru Nusaiba tayi kafin ta ce,
"Dan Allah mene tsakanin ku da Uncle Sabir."

Murmushi Amsa'u tayi dan daman jikin ta ya bata tambayar da zatau mata kenan.

Kasa tayi da kai sannan ta dago ta ce,
"Malami nane, sai kuma yanzu da yake so na."

Kai Nusaiba ta jinjina tai shiru. Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Ke fa?"

Ta tambaye ta ne  dan bata san tana son Sabir ba.

Ajiyar zuciya Nusaiba ta sauke ta ce,
"Tin da na hadu dake naji kin kwanta min abu daya ne yasa na fara jin haushin ki shine ganin yadda Uncle Sabir ke miki. Gaskiya zan fada miki ni nake mutuwar son sa. Shi kam bai damu dani ba."

Tayi shiru, sanna ta ci gaba da magana. Ta ce,
"Sis Mu biyu iyayen mu suka haifa nice auta dan haka duk son duniya suka daura mana. Maryam kawata ce, dan Mamanah da mamanta ma kawaye ne kamar yadda Dady na da nata ma abokai ne. Mun shaku da Maryam sosai, komai nawa ta sani nima haka. Dan ko zamu hutu tare muke zuwa daga family na har nata.  Tin ina primary In muka zo hutu Uncle Sabir ke burgeni ke har na girma na fara son sa. Duk yadda nake dan nuna masa ina son sa baya gane wa. Sai ni kadai nake ta haukar son sa. Ina son Uncle Sabir kamar rai na. Ina kaunar sa, wallahi amman ke kina son sa?"

Nusaiba ta tambayi Asma'u. murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Sir Sabir a matsayin wa na dauke shi. Ni malami na ne,"

Nan ta bata labarin haduwar su da labarin ta da Yaa Aslam ta karashe labarin tana kuka.

Sosai Nusaiba ta tausayawa Asma'u. Dan itama sai da tai kwalla dan itama tasan yadda so yake.

Hawaye Asma'u ta goge ta ce,
"Sir Sabir shike neman soyayya ta amman ni ba son sa nake ba. Amman nai miki alkawarin zan nusar da shi son da kike mas....."

"A'ah......"
Nusiaba ta dakatar da ita.

"Karki so ma. Akan me a tinda yana son ki wallahi gara ya aure ki ina son farin cikin sa ko da zan kasance a cikin bakin ciki zan ji dadi in shi yana cikin farin ciki. Ki bari kawai Allah tabbatar da mafi alheri."

Asma'u ta girgiza kai ta ce,
"Bazan taba iyawa ba. Bazan iya ba kina son sa sai na san yadda ya aure ki."

Nusaiba ta ce,
"A'ah!"

Banza Asma'u tai mata ta shige bayi tai wnaka ta dauro alwala ta zo ta saka kayan bacci ta hau kan sallaya.

Tin Nusaiba na jiran ta idar suyi magana har bacci ya dauke ta.

Washe gari da safe kuma suka hau shirin tafiya.

Duk yadda taso su yi magana da Asma'u. Asma'u ki tayi.

Da kanta ta dauke su har gida bayan Mami ta basu kayan biki suma da turamen atamfofi.

Suna zuwa gida suka ci karo da Sabir shima zai fita.

Kai Asma'u ta dauke tai packing sannan ta fice tayi cikin gida da sauri.

Mamah ta sama a falo ta zauna a gefen ta suka gaisa. Suna cikin gaisawa su Maryam suka shigo.

Zama sukai gaba daya ana ta hira sai yamma sanna Asma'u ta koma gida.

A washe gari kuma Momy zata tafi. Ranar tin yamma suna tare da Momy.

Momy na tambayar ta aiki sannan tana son bugar cikin ta ko akwai wanda yace yana son ta.

Haka dai ta roke ta kan ta samu taje tai mata kwana biyu.

Asma'u ta amsa ne kawai badan zata je ba.

Har ga Allah tana son ganin Yaa Aslam sannan tana son ta san a halin da yake ciki.



*HHHH INA MASU JIB GAUSHIN ASMA'U AKAN SON DA TAKEWA ASLAM. UHMM KUN SAN SO KUWA?*



*MS Indabawa*
[1/18, 14:33] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa

*HAJOW*
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*





*56-60*


*Masoya nagode kwarai da gaske*
Team *ASMA'U-ASLAM
Team *ASMA'U-SABIR
Hhhhh lallai kuna bani dariya yadda kuke taya Aslam ko Sabir kishi.

*Inayin ku, sosai. Sis Bela'u ta hannun daman Sabir ita da Sis Sady. Inayyin ku.*

*Sis Maryam Yusuf, ke da Ummu Ayda hannub faman Aslam*

*Sis Fatitih ta both side an rest.
*Nidai ta hannun daman Asma'u ce.*





Washe gari Momy ta tafi. Haka gidan ya koma daga Mami sai Asma'u.

Yaa Buhari yana zuwa da safe da dare.

Ba abinda Asma'u ta sa a gaba sai aikin ta.

Zumunci kuwa sun kara kullawa da Nusaiba.

Yau tana zaune a garden tana sanye da wani Ash less dinkin doguwar riga.

Kanta ta yafa karamin bakin mayafi. tana zaune ta zubawa wata shuka ido. Ta lula can duniyar tunani.

Kamshin turaren sa da taji shi yasa ta juyo dan ganin wanene?

Sir Sabir ne, yake tsaye yana sakar mata murmushi.

Itama murmushin tayi. Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta.

Ido ya zuba mata, kasa tayi da kai, murmushi yayi ya ce,
"Baby nah!"

Shiru tayi, ya ce,
"Me yasa kike boyar min ne, bayan kinsan ganin ki shi zai samin sassauci a zuciya ta."

Dagowa tayi idon ta jajir ta ce,
"Dan Allah Sir ka kyale ni kaima kaje wajen mai son ka."

Kallon mamaki yake mata ya ce,
'Me sona kuma? Wace mai so na?"

Mikewa tayi ta ce,
"Kai ma kasani ai, dan Allah Sir ka so Nusaiba!"

Ta fada tana tafiya. Mikewa Yayi yabi bayan ta.

Kafin ya karasa ta shiga mota ta tayar harta danna horn mai gadi ya bude mata gate.

Mota shima ya shiga yabi bayan ta. Gidan Zainab ta tafi. Sabir kuwa yana biye da ita a baya.

Tana shiga shima ya shiga. Da sauri ta fita a mota tayi cikin gidan.

Tana shiga taci karo da Zainab, kallon ta Zainab tayi ta ce,
"Lafiya?"

Ganin ta da tayi ta shigo a firgice, bata rufe baki ba Sabir ya shigo.

Murmushi tayi ta ce,
"Au ashe tare kuke?"

Ciki Asma'u tayi ta barsu a nan falo. Zama yayi yana kallon hanyar da Asma'u tayi.

Murmushi Zainab tayi duk da yanayin Asma'u ya bata tsoro.

Lemo da ruwa ta dauki masa. Bai sha ba sai magana da ya farai mata.

"Zainab ke kadai kika fi kusanci da Asma'u a kawayen ta dan Allah ki taimaka ki shawon kanta. Wallahi ina son Asma'u amman ita taki ta gane"

Murmushi jin Dadi zainab tayi ta ce,
"Kar ka damu zan sanar da ita."

Kai ya girgiza ya ce,
"Na fada mata, amman taki ta fahimci irin son da nake mata ne"

"Ka barni da ita. Ina zuwa."
Ta mike tayi

Tana daya daga cikin dakin da ta ce na ta ne.

Saboda shi karami ne kuma komai na ciki kalar ta ne.

Tana kwance akan kujera idon ta lumshe hawaye na zubo mata.

A ranta take cewa
'Duk Yaa Aslam ne ya jawo mata. Yanzu ita bata da wani kwanciyar hankali. Daga wancan sai wancan. To wai ita tayaya zata auri Sir Sabir bayan tasan irin son da Nusaiba ke masa. Ai kamar ta zama azaluma ne "

Wata zuciyar ta ce,
'To ai shi baya son ta. In kinso shi ba wani abu bane."

Juyi tayi ta bude ido ta. Zainab ta gani tsaye akan ta.

Zaune ta mike ta ce,
"Ya dai?"

Kai ta girgiza ta zauna agefen ta. Ta ce,
"Lafiya naganki haka?"

"Uhnm Nida Sir Sabir ne!"
Ta fada mata duk abinda ke faruwa.

Zainab ma tana son Asma'u da Yaa Aslam to amman ba yadda zasu yi tinda shine ya nuna baya son ta.

Tinda haka ne gwara ta amshi Sabir din tinda shi yana son ta.

"Asma'u nima a gaskiya ina son ki da Yaa Aslam, but amman tinda haka ta faru ki yi hakuri ki rumgumi wanda yake son ki. Bance ki Yaa Aslam baya sonki ba, amman ki karbi Sir Sabir kuma ki yi istihara Allah zaba mafi alheri. Kiyi hakuri."
Zainab ta dafa kafadar ta.

Dagowa tayi da idanun ta dake zubar da hawaye ta ce,
"Zainab kinsan so amman baki san zafin sa ba. Nusaiba na kaunar Sir tin tana yarinya take son sa. Tayaya xan raba wannan soyayyar da take masa. Ki tayani wannan abin ina son Sir ya fara son Nusaiba ni na hakura dashi. Ina tausayawa Sir saboda yana sona ni bana son sa, kuma ni ba kinsa nake ba, kawai dai Yaa Aslam nake so. Gwara ya auri wacce yake so zai fi jin dadin yasan yai aure da ya aure ni ni kuma zuciya ta na wani wajen ki duba magana ta Zainab nasan ke zaki fahimce ni."

Ta fashe da kuka, jikin ta Xainab ta jata tana lallashin. Sai da tayi shiru sannan Ta ce,
"Zan sanar da shi amman ki daina kukan nan."

Kai ta gyada. Mikewa Zainab tayi ta fita. Ta sanar dashi indai yana son Asma'u to sai dai ya hada da Nusaiba. Sosai hankalin sa ya tashi. Lallabashi tayi kan yaje yai tunani sannan ya tafi gida.

Wajen Asma'u Zainab ta koma. Kallon ta tayi ta ce,
"Sis nai miki shishigi fa"

Kallon ta Asma'u tayi

Please Login or Register in order to submit comment