Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan da nan ya kira Momy ya sanar da ita Aslam ya taho.

Haka ma ya kira ya sanar da Mami. Addu'a Mami tai masa Allah yakai sa lafiya.

Momy kuwa tun karfe biyu take zuba idon ganin Aslam amman bata ganshi ba.

Hankalin ta ne ya tashi. Can kuma sai ga sshi an kira ta da wayar sa wai yana asibiti.

Asibitin taje a lokacin aka fito dashi daga emergency aka tafi dashi inda za'a bashi daki.

Gun su tayi aka basu daki sannan likita ya kira ta.

Bayanin abinda ya same shi yai mata cewar ya bugu ne sosai a bayan sa. Sai yan raunika da ya dan daddauje.

Takardar magunguna ya bata ta amsa ta tafi ta bayar aka siyo mata.

Lokacin da Momy ta buga waya tana fadawa Buhari abinda ya faru Suna tare da Sabir.

Sosai Sabir ya tausaya masa. Haka su ka rabu jikin Sabir a sanyaye.

Tunani kuwa har ya rasa wane iri zai yi.

A ransa kuwa cewa yake yanzu yana ji yana gani zai raba farin cikin mutun biyu.

Ya tabbata duk son juna su ke jefa su a halin da suke ciki.

In har ya auri Asma'u yasan ya raba ta da farin cikin ta kuma Aslam ma bai da sauran farin ciki.

Sai yanzu yake tunani anya da Aslam yana cikin haiyacin sa ya juyawa Asma'u baya

Gaskiya da kamar wuya. Dan ya gano irin son da yake mata zai iya rasa rayuwar sa.

Haka ya koma gida duk baida sukuni.

A bangaren Aslam ma yana farkawa ya farai wa Momy kukan wai dan Allah ta taimaka a bashi Asma'u.

Momy kam Mamaki ta dinga yi saboda sai da ta fada masa kar ya soma sawa ransa abinda ya riga da yai masa nisa.

Da bata bashi amsa ba haka ya dinga kuka sai kace karamin yaro.

Ganin numfashin sa na neman daukewa yasa ta ce, yayi hakuri za tai san yadda zatai.

Duk da haka bai samu sukuni ba. shi dai ba wacce yake son gani sai Asma'u.


Momy kam bata fadawa Mami abinda ya faru da Aslam ba.

Kuma sai da ta hori Buhari da shima kada ya sanar da ita.

Ita tunanin ta ma rashin zuwan ta bikin.

Sai Allah yasa kuma ana jibi kamu aka sallamo Aslam daga asibiti.

A gida ta barshi da Dady kan cewa jibi zata dawo.

Haka Momy ta tafi tana tausayawa dan ta.

Sai ta tuna lokacin da take cewa sai ya auri Asma'u amman yaki yac"e sai Preety zai aura amman shine har da suma gashi kuma yanzu ya dawo da son ta.




Bangaren Su Mommah pretty kuwa ba karamin tashin hankali Ta shiga ba.

Ganin Pretty har wata hudu ba ita ba labarin ta.

Gashi ko waya bata yi nan fa suka hau bada cigiyar ta.

Amman abin ko alamar nasara babu.

Wata kanwar Mommah ce ta ce, a dage da addu'a Allah bayyana ta

To An dauki wata ana ta addu'a da sadaka amman shiru.

Da farko Mommah ma cewa tayi ita bata ga abinda addu'ar keyi ba.

Kanwarta ce, ta ce, ai addu'a sai a hankali a cigaba da yi har Allah y amsa.

Haka aka kara kaimi wata rana kamar daga sama sai ga pretty ta dawo da yaro a baya.

Duk ta rame tayi baki sai wani wari take fitar wa.

Tana ganin Mommahn ta tasa kuka. Ta fada jikin ta.

Mommah ce ta daga ta tana toshe hanci,
"Daga ina?"

Ta tambaye ta. Pretty ta ce,
"Mommah ruwa."

Ruwa ta dauko ta bata ta kai ta bangaren ta ta ce tai wanka.

Mommah ta rike ta ce, baza ta tafi ba dan tsoro take ji.

Zama Mommah tayi ta shiga bandaki tai wanka.

Tana fitowa tai wa dan ta wanka, Mommah ce tasa a kawo musu abinci.

Nan aka cika dakin da abinci kala kala. Tin da ta fara cin abinci take turashi kamar wacce aka ce za a kwace mata.

Mommah ce ta ce taci a hankali, amman ina haka yaron ta da bai fi wata biyu ba ta dinga cusa masa abinci.

Tana gamawa suka zube a falo sai bacci.

Ido Mommah ta zuba masu tana zubar da hawaye.

Ganin yadda tayi baki, ta rame, ga yaro ko a ina ta samo shi.

Bacci sosai tayi dan har akai magariba tana bacci.

Sai da Dady ya dawo suka shiiga da Mommah ce ta same ta tana zaune, tana bawa danta nono.

Tana ganin Dadyn ta ta mike. Dady ne ya karasa ya amshi yaron hannun ta.

Magana yai mata amman da ta bude baki zata bashi amsa dai ta kasa magana.

Har kuka tayi dan jin ta kasa magana. Dady na ganin haka ya samo malami yai masa bayani.

Addu'a aka kara mikewa da ita da rokan Allah.

Cikin hukuncin Allah sai ga Preety na magana.

Anan ne take fadawa Dady duk abinda tayi da raba Aslam da Asma'u da bin malaman da take.

Har da auren da sukai da boka wannan yaro kuma dan ta ne da boka,

Bata taba zaton zata kubce daga wajen boka ba.

Sai rana daya ta ganta ta samu hanya har ta fito.

Bara tayi sannan ta samu na mota. Da kyar wata motar koso tumakai ta dauko ta.

Acikin wajen da tunakrn suke ta zauna duk da wajen kashi da fitsarin su ne.

Da haka suka karaso har kano aka sauke ta.

Da kyar ta samu ta karaso Abuja. Take fada musu a kafa ta karaso gida.

Jikin ta kuwa yayi wani iri kamar konuwa ga kaikayi.

Asibiti Dady ya fara kkai ta amman ina abin ba na wasa bane.

Da aka basu wasu gwaje gwaje aka gano tana dauke da cutar kanjamau.

Dady sosai ya razana. Preety kuwa kuka ta dinga yi tana dana sanin abinda ya faru.

Haka suka koma gida bayan an basu ranar da zasu na zuwa ganin likita da amsar magani.

Sosai Pretty ta razana da rayuwar duniyar nan, Ganin yadda take da amman yanzu ji yadda ta koma.

Ji dan da take riki dan shege, kuma ma na boka wai.

Haka nan ita ce ke dauke da kanjamau, yanzu wa zai aure ta.

Lallai *Duniya abar tsoro*







*MS Indabawa*
[1/18, 14:37] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

?? *HAJOW* ??
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*



*86-90*





Yau ta kama kamu Asma'u ansha lalle da gyaran kai.

Duk da a kwance take sosai dan yanzu haka ma wani irin ciwon kai da zazzabi ke damun ta.

Tana kwance Zainab ta shigo da mai kwalliya ta ce,
"Asma'u tashi mai kwalliyar tazo."

Da kyar ta iya mikewa idon ta jajir ta shiga bayi. Kasa sakawa jikin ta ruwa tayi sboda sanyin da take ji.

Fitowa tayi ta saka kayan da zata amfani dasu. zama tayi aka farai mata kwalliya.

Yar kadan akai mata amman ba karamin kyau tayi ba.

Ana cikin mata dauri Nusaiba ta kira ta. Dagawa tayi murya a sanyaye ta ce,
"Amarya"

Dariya Nusaiba tayi ta ce,
"Amare dai. Ya kunyi kamun ne, nifa har na gama shiri fita kawai zanyi. Yanzu Uncle Sabir ya kira ni wai ya muka tsara dinner nace ai ni ke na barwa komai."

"Uhmm kema dai. Ni ba wata dinner da zan yi. Yazo nan kawai."

Nusaiba tace,
"Ke kin isa ma. Kinji ana jira na bari naje mayi waya anjima."

Ta katse wayar. Kallo ta bi wayar da shi ta ce,
"Oh wai wannan ce kishiya ta. Ita sai murnar bikin take yi."

Maryam ce ta kira ta. Ta ce,
"Anty kiyi hakuri sai gobe zan taho yau zan tsaya wajen kamun Nusaiba. Jibi wai za ai dinner."

Asma'u tace,
"Nifa ba wata dinner da zanyi."

Shiru Maryam tayi a ranta tana tunani ko Asma'u bata son a hada musu dinner su biyu ne.

Sallama sukai tayi wajen Momyn ta tana fada mata gwara kowa yayi event din sa kar a wani hada.

Haka kuwa akai dan Mamahn Sabir ma haka tace kowa yai nasa.

A wajen Kamu kuwa Asma'u sai rawar sanyi take ga ciwon kai.

Anyi hotuna da kawayen su da yan uwan Dady da Mami.

Inda kafin a tashi jikin Asma'u yayi zafi kamar wuta.

Nan da nan Momy tasa aka maida ita gida. Ciwo sosai ta kwanta.

Washe gari akai Monday's even Amman Asma'u da kyar ta iya zuwa.

Asabar dinner amma ranar a kwance sosai Asma'u take dan har asibiti aka tafi da ita.

Riketa sukai suka bata gado ana mata karin ruwa. Dinner dai da ba ayi ba kenan.

Rannar lahadi da safe aka daura auren Asma'u duk da tana asibiti lokaci nayi taji wata faduwar gaba.

Kuka ta sawa Momy dake wajen ta.

Momy sai lallashi take yi. Ba wanda yazo asibiti a ranar sai Zainab.

Shima abinci ta kawo fuskar ta dauke da fara'a sai tsokanar Asma'u take wai ta kwanatr da hankalin ta ta samu abinda take so ta mike.

Kiran da Mami ke mata yasa ta mike ta tafi ba tare da ta cigaba da tsokanar Asma'u ba.

Asma'u kam zuciyar ta ta gama karaya ta rasa Yaa Aslam kenan.

Da dare aka sallamo su gida suka nufa dan gidan ma har ya rage jama'a.

Dakin ta aka kai ta. tana kwance akan gado duk ranta a bace.

Zainab ce ta shigo ta ajiye roba sai karamin towel a gefe. Saboda jikin ta yai zafi za a fan sa mata ruwa.

Kai ta dauke ta lumshe idon ta. can taji an bude dakin. A hanakli taji ana taciya har aka karaso bakkin gado.

Bata san waye ba dan haka ta kara gyara kwanciyya. Roba taji an dauka an tsoma towel a ciki.
Ji tayi an tada ta zaune, ana cire mata kayan dake jikin ta.

Karamin wandon dake jikin ta kawai aka bari. Ido ta kara lumshewa. Saboda bata son bude su fan yadda suke mata zafi.

Jin an soma goga mata towel ta ajiye wata uwar ajiyar zuciya.
Ji tayi ana ta goga mata ruwa a jikin.

Shiru tayi abu daya taji shine, an fi goga mata a kirjin ta. Duk da haka batai gigin bude ido ba.

Can kuma sai taji kamar kamshin Yaa Aslam amman kuma sai ta tuna baya garin ma.

jini shirun yai yawa yasa ta a bude idon ta a hankali. Waza ta gani?
Yaa Aslam ta gani durkushe a gaban ta.
Ido ta zaro ta mike da sauri. Murmushi ya saki.

Bandaki ta shiga da gudu tana dafe da kirjin ta.
Ta jima a bandakin tana kukan da ta rasa dalilin name ne.

Sannan kuma tana mamakin taya Yaa Aslam ya shigo har ya ke shafa mata ruwa.

Ta jima a bandakin tana kuka ita kadai  dan har sai da taji Zainab ta shigo tana kiranta.

Fitowa tayi daure da towel tana rawar sanyi. Dan wani zazzabi ne ya kara ta yar mata.


Kayan bacci ta fito ta saka. Har ta kwanta Zainab ta ce, taje falo ana neman ta.

Hijab ta dauka ta saka ta mike ta fita a hankali kirjin tane bugawa.

Falo ta fito jiki a sanyaye dan wani zazzabi take kara ji. Kan ta kuwa kamar zai rabe gida biyu.

Ta shiga falo taga Mami da Momy sai Uncle Habu (kanin Dady) sai Yaa Buhari da Sir Sabir. Taji dadi da bata Aslam a dakin ba.

Dukkan su murmushi ne akan fuskar su sai hira suke.

Kirjin ta ne ya buga ta ce,
"Allah yasa ba cewa za'ai na fito mu tafi ba."

Karasa wa falon tayi ta zauna a gefen Uncle Habu.

Mutanen dakin ta gaisar daya bayan daya sukai mata sannu.

Kasa tayi dakai. Uncle Habu ne yai gyaran murya ya ce,
"Alhamdulilah Asma'u yau Allah ya nuna mana ranar Auren ki. Muna fatan zaki zama mace ta gari a wajen mijin ta. Kafin nan Asma'u. Asma'u duk abinda ya faru gareki ki dauka taki kalar Kaddara ce."

Yai shiru, sannan ya ce,
" Auren ki dai bai dauru da Sabir ba."

Dagowa tai da sauri ta kalli Uncle Habu sannan ta kalli Sir Sabir.
Murmushi ya sakar mata. Uncle Habu yacigaba da magana,
"Yau a wajen daurin aure anzo daura auren ku Sabir ya dakatar ya ce, a daura auren ki da yayan ki Aslam."

Nan ma da sauri Asma'u ta dago tana kallon Sabir tana girgiza kai.
Murmushi ya sakar mata, yana mai girgiza mata kai ganin hawaye na shirin fitowa daga idon ta.

Uncle ne ya cigaba da magana ya ce,
"Ko da na tambaya akan me za'a fasa da shi sai ya kawon dalilan sa kamar haka:- Sabir ya ce, Uncle ina son Asma'u amman nafi son samuwar farin cikin ta. dole na hakura da ita tunda suna son juna su ita da Yaa Aslam. Dan ciwon da Aslam ya kwanta ma akan tane, haka ma kema kina son sa."

Kai Asma'u ta fara girgizawa, Uncle yace, haka
"Haka sabir yacigaba da bani dal'lan sa. Ya ce, Na yadda Yaa Aslam na son ta kuma in na aure ta mutum biyu zasu rasa farin cikin su. In ni na hakura ni kadai ne zan ji ba dadi kuma nima na lokaci ne tinda na samu wacce ke sona tsakani da Allah. Nagodewa Asma'u dan ita tai min wannan gatan bazan taba mantawa da ita ba. Ina son Asma'u amman na hakura da ita Allah bata zaman lafiya da mijin ta."

Kukan da Asma'u take boyewa shine ya fito fili ta fashe da kuka.
Zainab da shigowar ta kenan ta karaso tana lallashin ta.

Uncle ya ce,
"Ki daina kuka ki godewa Allah. Ina miki fatan Alheri Allah ya baki zaman lafiya. Ina farin ciki yau burin Yaya Suleiman ya cika. To Allah ya tabbatar da alheri. Ki kula da mijin ki. Allah miki Albarka."

Ya mike ya fita. Mikewa Momy da Mami sukai suka fita.
Haka ma Yaa Buhari ya mike ya fita, bin bayan sa Zainab tayi ya rage daga Asma'u sai Sabir.

Mikewa yayi ya karaso gefen ta. Ya ce,
"Haba Husunah mene na kuka. Ki godewa Allah da ya sa na gane irin son da Aslam yake miki na tabbata Aslam na kaunar ki fiye da yadda nake kaunar ki, akwai dalili mai karfi da ya hana shi auren ki a baya zai iya zama ko bayin kan sa bane."

Dagowa tayi idon ta jajir kamar gauta ta ce,
"Ni na fada maka yanzu ina son sane, bana son sa. Bana son sa sam. meyasa zakai min haka Sir. Yaa Aslam ba sona yake ba. Mutumin da yaki ni me ya dawo dashi gare ni......"

Sai kuma ta fashe da kuka. Sabir ya ce,
"A'ah Asma'u kar zuciyar ki ta dauki Aslam da wannan tunanin ki yadda da Aslam. Aslam na son ki. Aslam na kaunar ki, ni na yadda kuma nasan zaki ji dadi da Aslam amman dan Allah ki daina cewa bakya son sa. Nasan kema kina son sa. Ki amshi kaddara da Alalh ya saukar akan ku. Baki san me gaba zai faru ba. Nagode miki Asma'u da kika zaba min abokiyar rayuwa. Yau an kawo min Nusaiba daki na kuma duk a dalilin ki nagode."

Ya mike ya fita. Kallo ta bishi da shi. Kuka ne ya kwace mata ta kifa kanta a kan kujera tana ta sharar kwalla.

Da kyar ta mike tayi daki tana wani irin kuka. Kan ta kuwa ko ya ta motsa ji take kamar zai fashe dan azaba ko wuyanta bata son motsa shi.

A haka Zainab ta same ta ta zata ma bacci take.

Shirin kwanciyya tayi ta kwanta da danta. Can cikin dare Zazzabi ya tada Asma'u sai kuka take.

A daren suka kara tafiya asibiti ba shiri.






*MS Indabawa*
[1/18, 14:37] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*


Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers Association *
*Gidan Amanci da albarka*


Dedicated to *My Lovelly Momy*

*Mahaifiya ta abar alafahari na. Allah ya sa ki gama da duniya lafiya*zn

91-95

*Wani mutum yacewa Hasanul Basry:Ya Aba Sa'id ina kawo maka kukana akan 'Ke'kashewar zuciyata saiyace masa:Ka ladabtar da zuciyarka da ambaton Allah*




Aslam ne ya shigo shima gefen Dady yayi shida Asma'u suka sa shi a tsakiya suna masa sannu da zuwa.

Yaya Buhari ya ce,
"Wallahi Mami a gidan nan ba a so na."

Sai a lokacin Aslam ya kula da shi. Dariya yayi ya ce,
"Aah 'kanina ashe ka dawo,"

Kai ya dauke wai yayi zuciya. Dariya sukayi.

Asma'u tayi gefen sa ta ce,
"Sannu bro ya aiki?"

Banza yai mata. Kukan karya ta fashe dashi in kaji yadda ta fashe dashi kayi zaton na gaske ne. Nan da nan Yaya Buhari ya jata yana bata hakuri.

Dariya ta saki ta ce,
"Daman nace sai ka.kula ni."

"Kai amman yarinyar nan kinga lago na."
Ya fada yana daga ta daga jikin sa.

Daga haka suka hau hira. Har karfe goma suna falo sannan Aslam da Asma'u suka tafi gun cin abinci.

A can ma sun jima suna hira sannan suka ci abincin cikin so da kauna.

Aslam ya ce,
" *Husnah* ji nake ina ma anyi abin nan gidan mune mu sha soyayyar mu."

"Lokaci dai. Allah nuna mana."
"Ameen! Allah har na hango yadda zamuyi soyayya nake."

"Kai Yaa Aslam! Kana son soyayya."
"Dole naso ta *Husnah* dan wanda bai soyayya bai son dadin duniya nan ba soyayya tayi. Allah kuma ya bar mu da masoyan mu."

"Ameen!"
sannan suka mike suka koma daki. Sallama sukai wa su Dady kowa yayi dakin baccin sa.

Duk abinda ta saba tayi sai da ta gama su sannan ta kwanta.

A haka ma sai da suka kara yin waya kafin su kwanta.

Sun jima suna waya sannan sukai sallama bayan sunyi alwala.

Washe gari lahadi yini sukai tare. Ko gajiya da zama tare ko hira basa yi.

Sai dai ka jiyo murmushin su ko kaji dariyar su.

Mami dai bar musu falon tayi, haka suka yini a gidan.

Tare suka ci abinci suka yini sallah ce ke daga su.

Bayan sunyi sallahar la'asar, ne ya ce, Asma'u ta shirya ssu fita.

Wanka ta shiga tayi, ta fito ta saka Wata doguwar riga fara an mata ado da jan stones sai Jan mayafi da jan cover shoe. Wata jar jaka ta dauka.

Turare ta fesa ta fito tai dakin Mami.
Mami na zaune tana kallo Asma'u ta shiga

Kallon ta Mami tayi ta ce,
"Sai ina kuma?"

Murmushi Asma'u tayi ta ce,
"Zan raka Yaa Aslam ne."

"Toh! A dawo lafiya."
"Allah yasa."
Ta mike tayi waje.

A kasa ta samu Ya Aslam ya na sanye da farin wando da jar riga. Takalmin kafa sa ma ja ne.

Sai tashin kamshi yake yayi kyau. Yana ganin Asma'u yasaki murmushi ya ce,
"Wow My baby tayi kyau munyi anko."

Murmushi ta yi ta ce,
"Ka fini yi."

Wayar sa ya zaro ya ce,
"Zo mu dau selfie."

Gefen sa ta karasa ta tsaya matsowa yayi jikin ta, ya dauke su.

Ya musu fin kala biyar sannan ya dinga daukar ta.

"Yaa Aslam ya isa haka."
Ta fada saboda taga ba alamar tsayawa.

"To muje."
Ya fada yana kamo hannun ta. Fita sukai ya karasa gun Baba ya amso key mota suka shiga.

Shoprite suka shiga suka wuce cinema. kallo suka danyi sannan suka fito suka shiga ciki.

Sun shiga suka nufi gun kayan sakawa. Sosai yake jidar mata dogayen riguna masu kyau da tsada.

Haka ya nufi gun takalma da jakun kuna. Sosai ya kashe mata kudi sannan suka nufi gun alawa ya siya mata ice cream.

Bayan anyi total ne aka dibi kayan akayi wajen mota dashi.

Suna tafe suna hira taji ta bugi abu tayi baya zata fadi.

Da sauri ya rikota ta fada jikinsa. Kafin ta dago taji Yaa Aslam ya dago ta yana cewa,
"Ba dai matsala ko?"

Kai ta daga masa, kamshin turaren da taa shaka shi yasa tai saurin dagowa.

Ai kuwan shine, yana sanye da bakin wando da jar riga, yayi kyau sosai dashi.

Ba kowa bane face Sir sabir.
"Sorry!"
ta furta a kasan leben ta.

Yaa Aslam ne ya kama hannun ta suka bar wajen.

Sabir kowa kallo yabi su dashi. Yana me lumshe idon sa.

Suna fita ya ce,
"Sannu Baby na ko na dauke ki ne."

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah nagode zan iya tafiya ai."

A hankali suka karasa gefen Mota suka shiga suka bar wajen

Suna zuwa gida ana kiran sallah isha'i

Daki suka shige sukai sallah sannan suka sauko kasa.

A kasa suka samu har Dady ya dawo. Saannu da zuwa sukai masa sannu da zuwa

Abinci suka ci sannan suka koma falo ana hira.

Sai karfe tara suka tafi makwancin su.

Washe gari Monday. Tana gama abinda zatai ta shirya cikin wata pink kalar doguwar riga. Milk mayafi da takalmi ta saka. Sai pink kalar jaka.

Batai kwalliya ba fuskar ta daga hoda sai man lebe. Wajen Dady taje. Tare suka karya. Sannan ta fito.

Yaa Aslam ta gani a falon sama. Karasa wa tayi gun sa. Yana sanye da Bakin wando sai blue kalar riga mai dogon hannu.

Yayi kyau sai tashin kamshi yake.
"Yaya nah ina kwana?"

Ta gaishe da shi tana zama a hannun kujerar da yake.
"Lafiya lou. Ya Baby na ta tashi."

Murmushi tayi ta ce,
"Lafiya Alhamdulilah."
Sannan ta mike ta sauka kasa.

Basket din abincin sa ta dauko wanda ta zuba masa komai a fulas din sa.

"Mu tafi?"
Ya fada yana tambaya.

Kai ta gyada masa, dakin Mami suka yi sukai mata sallama sannan suka wuce zasu sauka.

Mantawa tai bata je gun Yaya Buhari ba. Wannan yasa tai ce
"Ina zuwa!"

Dakin yaa Buhari ta dosa, yana kwance ko alamar tashi bai yi ba.

Kara tai masa a kunne da sauri ya mike a firgice. baya ta dan ja ta ce,
"Ina kwana?"

Ta fada tana ja da baya a hankali. Ganin ya mike yasa tai saurin fita a dakin tana dariya.

Yaa Aslam dake tsaye yana jiran ta ya ga ta fito har ta sauka shima yabi bayan ta yana murmushi dan yasan tayi tsokanar da ta saba.

A bakin mota ya ganta a tsaya budewa yayi ta shiga ya rufe sannan ya shiga bangaren sa.

Tafiya suke a hankali suna hira abinsu. Har kofar department din su ya kai ta sannan ya kara mata kudi akan wanda Dady ya bata.

Sallama yai mata ya ce,
"Sai ya dawo daukar ta."

Sai da ta ga tafiyar sa sannan ta nufi ajin daukar darasin su.

Tana shiga taga Zainab zaune, karasawa tayi gun ta suka gaisa.

Batai minti biyar da zuwa ba sai ga Sir Sabir nan ya shigo.

Sanye yake da Milk din shadda ana mata aiki da milk din zare. Yayi kyau dashi.

Kasa tayi da kanta tuna haduwar su jiya. Lectures yake musu da yayi tambaya zai yi pointing din ta.

Tin tana jin kunya har ta sake tana bashi amsa. A haka suka gama lectures din.

Da zai fita ya duka zai dauki wayar sa, yai mata magana a hankali cewar ta same shi a office.

Wata faduwar gaba taji ta doke ta. A hankali ta daga kai ta kalle shi. Ita yake kalla saurin kawar da kan ta tayi tana wasa da yatsun ta.

Waje ya fita. Wata ajiyar zuciya ta sauke, ita bata san hadin ta da malamin nan ba amman dai tana ji yana burge ta ko dan saukin kansa.

Da kamar baza taje ba sai kuma ta ce da Zainab zataje ta dawo.

Fita tayi ta nufi office din nashi jiki a sanyaye.

Knocking tayi ya bata izinin shiga. Da sallama, ta shiga office din ta tsaya daga bakin kofa. Kallon sa tayi sau daya ta dauke idon ta.

Yana zaune a kan kujera gaban sa, farfesun kifi ne da Doya da kwai.

Kamshi ya cika office Din ci yake kamar baya son ci fuskar sa kuwa sai bata ta yake kamar mai cin magani.

Kallonsa ya maida kan ta ya kasa dauke ido daga kallon ta. Yana son yarinyar nan amman bai san ta inda zai fara ba.

Kawar da tunanin da yake yayi ya ce,
"Zo nan!"

Da kamar baza taje ba sai kuma ta dan matsa.

Kallon ta ya kara yi ya rasa mene dalilin kiran nata.

Kai ya dan shafa, ya ce,
"Zo kici!"

Kai ta girgiza ta ce,
"Na koshi."

Fuska ya bata, ya ce,
"Zamu bata inda zan na baki abu kina kinci. Maza zo kici."

Matsawa tayi ta zauna a kasa ba dan zata cin ba. Fulas din ya matsar mata dashi ya ce,
"Bismillah!"

Agogon hannun ta kalla sannan. Ta ce,
"Zan je nayi Assignment fa."

Ta yi maganar murya a shagwabe dan har ga Allah ta riga da ta saba da shagwaba in tana abu. bama in tana bukatar abu.

Sabir kuwa jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.









*INDABAWA*
[1/18, 14:38] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

?? *HAJOW* ??

Dedicated to *My lovelly Mum*




*96-100*

Kina Ina Fateema kibiya. A gaakiya ina yaba hankalin ki. Da kokarin ki. Allah ubangiji ya kara basira da zakin hannu ni Maryam ina son ki


Mikewa yayi ya durkusa a gaban ta. Hannun sa ya daura a kan cinyar ta

Da sauri ta bude idon ta. Kallon sa ta tsaya yi kamar yadda shima ya kasa dauke idon sa daga kallon ta.

Hannun ta ya kamo ya fara murzawa a hankali.
Ya kira sunan ta a hankali. Ya ce,
"Husnah ki yadda dani wallahi ina son ki. Duk abunda ya faru ki manta da shi."

Ido ta rufe dan ita ta kasa mantawa da abinda Yaa Aslam yai mata.

To wai mema tai masa da har ya guje ta bayan yasan bazata ta iya rayuwa ba shi ba.

Bayan yasan duk farin cikin ta yana gare sa.
Bayan yasan shine ruhinta. Shine sirin ta daga mahaifinta sai Mami sai Shi da Yaa Buhari sune kadai

Please Login or Register in order to submit comment