Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

WACECE NI? -3


Umma ta mike ta dauko rigar baccin
dake ajiye can gefenta ta miko min.
"Karbi ki suturta jikinki." Tayi maganar ba taree
da ta kalle ni ba.
Hannu biyu nasa na karbi rigar nayi yanda
tace din, tana ganin nayi hakan ta nemi wuri ta
zauna tana kallona cikin natsuwa ta ce "menene
masalar da ta hanaki zama wurin mijinki ku
more darenku na farko?"
Nayi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda
jin nauyin maganar tata, gaba daya mukayi shiru
na dan wani lokaci zuwa can sai na kawar da
shirun namu ta hanyar yi mata tambayar
taimake ni mana Umma yau kam ki gaya mun
gaskiyar al'amarina taimake ni ki gaya mun don
in san ni wacece?" Kallon da naga tayi min shi
ne ya firgita ni, nan da nan naji cikina ya bada
sautin kululululu.... cikin rawar jiki na tambaye
ta "Da gaske ne Umma ni din shegiya ce?" Ta
dan girgiza kai a hankali tare da fadin cewa "ko
kadan ke ba shegiya ba ce Adawiyya." Na dan
samu 'yar natsuwa kadan saboda jin abin da ta
fadi, don haka sai na dan kara mats awa jikinta
na ce, "Gaskiya Umma ke din ke kika haife ni?"
Na zuba mata ido ina kallonta tare da sauraron

7


irin amsar da zata bani, sai na sake ganin ta
motsa kanta.
Da hannu biyu na bugi kirjina cikin tsananin
kuka na ce mata "Na shiga uku Umma, tunda ba
ke kika haife ni ba?" Na kama kuka mai
tsananin yawa ina fadin "Shi kenan Umma ta
rasa ku dukanku na rasa Baba kema kuma a yau
na rasa ki bani da kowa kenan a duniya?"
Umma ta jawo ni jikinta ta rungume itama
taya ni kukan take yi tana fadin "Ba ki rasa
kowa ba Adawiyya, ni da Alhaji mune iyayenki
da kika sani mune kuma iyayenki na har abada
ban taba tunanin hali zai yi da zan bayyana
wannan sirrin ba in banda tsananin son da nake
yiwa Babangida, da ban bari akayi aurenku ba,
don nasan yin auren naku yana nufin bayyanar
asirin da na dade ina boye miki.
Na sake kallon Umma a kidime na ce mata
"umma amma ai dake nake takama, gashi kuma
a baya kin taba ce min kin haifi Rabi'atu kin
kuma gaya min cewar Umma amarya tazo gidan
nan da yaro a goye to ina ce shine yaya Almu?"
Cikin natsuwa Umma ta kalle ni ta ce min,
wancan yaro da na baki labari tuni dangin
Ubanshi suka kar ba, duk da Alhaji yayi iyakar
kokarinshi wajen ganin an bar mishi rikon shi
amma basu yarda ba bisa uzurin da suka bayar
8

na cewar shi kadai ne dan uwan nasu ya rasu ya
bari maganar haihuwar Rabi'atu kuwa biyo ni
kawai kisha labari, a baya na tsaya ne a inda na
gama baki labarin isowar Maryam gidan nan to
yanzu ma daga nan zan tashi.
"Isowar Maryam gidan ya saman min da
saukin fitina ne, amma ba fita hanyata karama
tayi ba, domin duk da amaryar da akayi mata
kishinta yafi tsanani a kaina, don ita da bakinta
sai da ta rinka gayawa mutane cewar da ta zauna
dani a matsayin kishiyarta gara ta zauna da
kishiyoyi guda uku duk da ita su zama hudu."
Umma ta dan saki wani lallausan murmushi
bayan fadin hakan da tayi. Sai kuma ta ci gaba
da fadin "Baba abin da karama ta ki irin taga
Alhaji a dakina koda kuwa nice dashi sai ta rasa
kwanciyar hankali ta rasa inda zata tsoma ranta
taji dadi muna cikin wannan zama ne mutancen
gida suka gane ai Amarya ciki ne da ita, shi
kenan ana gance hakan sai kuma kishin Karama
ya kema can zaman lafiya ya gagara a
tsakaninsu fadan safe daban na yamma daban
bayan kafin ta gane Maryam na da juna biyu
duk kokarinta bai wuce na ace su biyun sun
hade mun kai ba, ita Maryam din ce bata yarda
ba rikici tsakaninsu yayi tsanani 'yar magana ba

9
magana ba kumą sai ta rarumeta da danbe sai da
Baba ya gaji da hakan yasa baki yayı kashedi
akan danben shine aka dan samu sauki.
Ni kam ina gefe kallonsu kawai nake yi ina
kuma iya kokarina wajen boye halin na nake
ciki saboda ban son a gane amma duk da yake
sai da Alhaji da Baba suka gane ina zaune a kan
tabarma a dakina rannam ina dama wa Alhaji
furar da zai sha bayan dawowarshi daga kasuwa,
sai ya kalle ni ya ce min "iko sai Allah, watakila
kuma bana yan tagwaye zan samu a gidannan
da kuma shekara da shekaru babu ko daya." Na
yi kamar ban ji shi ba, na mika mishi furarshi ya
kama sha.
'Yan kwanaki kadan bayan bayan nan kuwa
ina tare da Baba muna hira sai ya ce min "to wai
ni Zuwaira da kike ta faman wannan 6oye-
boyen kin mance ne uwarki mai yi min lissafin
cikinku yau bata nan? Na sunkuyar da kaina
kasa cikin hawaye saboda na kasa daina kukan
mutuwar Baba Rabi kullum cikin kewarta nake
anyi wannan zancen babu wani dadewa sai
kawai na haifi 'ya mace abin da ya baiwa Kowa
mamaki har Alhaji da Baban da suka gane
akwai cikin balle kuma wadanda basu gane ba a
wannan lokacin yaya Balki ce ta tsaya akan
hidimar jegona don gaba dayan matan gida sun
10

Ce babu hannunsu tunda dai na 6oye musu cikin
don ina tsoron kar suyi amfani da maitarsu su
Cinye abin da yake ciki to yanzu ma da ya fito
ba za su taba shi ba don haka ita ce mai samun
ruwa ta kwashe ta wanke yarinya ta gasa mata
cibiya ita kuma Maryam tana yi mun wankin
kayana da na yarinya dama duk wani aiki da ya
dangance ni.
Ranar suna Baba ya sanyawa yarinya suna
Rabratu a wannan loka cin ba karamin karamci
yaya Balki tayi min ba don kuwa har nayi
arba'in 1ta ke sanya mun ruwan wanka ta kwashe
tayiwa yarinya wanka safe da yamma bata yarda
ta bari ba kamar yanda Alhaji ya ce ta huta da ji
da hidimar yaran dake dakin ta wajen su bakwai
ga guda biyu da ta haifa a kurkusa wadanda
basa yarda su rabu da jikinta ko ina take suna
manne da ita uwa da kuma Jumaindu.
Ba zai yiwu in tsaya kwatanta miki irin son
da Alhaji da Baba suke wa yarinyar nan ba illa
dai kawai in ce miki ba al'adar mazan gidan ba
ne daukar ya'yansu amma shi kam daukarta
yake yi ya fita da ita ya kaita wurinta Baba suyi
hira in kuwa ya ganta a bayana tana kuka ko ya
ji ta zai ce min ban ita nan, ko da kuwa a cikin
mutane ne nayi-nayi ya daina don ina jiye mishi
kunyar hakan da yake yi,amma ya ki dainawa
11

sai ya ce "ke kyale ni kin hi shekara nawa nayi
ban same ta ba?"
Mun samun wajen watanni uku a lokacin nan
tafi wani jaririn mai wata biyar girma da kuzari
gata da idanuwa dara-dara gashi ba na jin
kunyar gyarata kullum cikin tsabtace ta nake sai.
kawai ta kamu da mura mai tsanani na wuni
daya kawai sai kuma ta ce ga garinku nan.
Baba ya yi ta kuka ina bashi hakuri shima
Alhaji ya shiga cikin damuwa mai tsanani
kowane loka ci sai yayi ta fadin "oh ashe
yarinyar nan ba zama tazo yi ba?" In dan yi
murmushi in ce mishi "I, ba mai zama ba ce sai
kayi hakuri ya ce to yaya zanyi? Ni kaina boye
damuwa kawai nayi amma zuciyata takai
matukaa wajen zafi, don kuwa ina son da a
wannan lokacin ban sani ba ko Baba ya gane
hakanne sai ya ce min dakin nan naki zaiyi
mikifili mai yawa na rasghin Rabi, koda take
yar karama kin riga kin sa rai da ita. Don haka
ki dauki Uwa itama wata Rabin ce sai ta rufa
miki gurbin da ta bar miki." Nayi nurmushi na.
ce "To Baba daga wannan ranar kuwa sai na
kar6i rikon Uwa daga wurin Yaya Balki hakan
kuma sai ya kara karfafa kauna mai yawa a
tsakaninmu har muka zama tamfar 'yan uwa

12

Sati uku cif da rasuwar Rabi'atu sai Maryam
ta haifi da namiji na kai wa Baba shi, bayan
nayi mishi wanka ya kare mjshi kallo ya ce
"kamarshi, daya da 'yar uwarshi da mace ne da
sunanta na mayar mishi sai ki sa hannu biyu ki
rike shi naki ne ki dauka shi da 'yar uwarshi da
ta tafi duk daya ne tunda 'ya'yan Bello ne na ce
"mishi to Baba na karbe shi na tafi na bar shi
yana share hawaye da gefen rigarshi ni Baba ya
tantaya in fadi sunan da nake so a sanyawa jariri
na ce' yasa mishi sunaishi don haka ranar suna
sar aka rada mishi Muhammadu Mustapha ni
nake kiranshi Babangida shi kuwa Baba yake ce
mishi Lamido.
Hannu biyu na saka na karbi al'amarinshi tun
yana dan jariri na kai kai shi gun Maryam ne
kawai don yasha nono tunda Junaidu yaga jariri
a dakina kullum zai zo ya zauna kusa dashi
dama kuma ga Uwa ta dawo dakin don haka sai
ya zama dare ne kawai ke raba shi da dakin
daren ma kuma sai an bari yayi bacci nake kai
shi ko kuma ita ta turo a dauke shi. Rannan ma
dai da Alhaji ya gaji da ganın hakan sai ya ce
min to wai ke me zai sa ba za ki bar yaron nan a
dakin nan ba ne kawai ki hada su ki rike? Ina
amfanin kullum sai an sako shi a dauke shi?" Na
ce mishi to.
13

Shi kenan sai gani da 'ya'ya uku a daki ina
kuma tafiyar da al'amarinmu gwanin sha'awa
kowane lokaci muna cikin tsabta ko hira zani
wurin Baba tasasu a gaba nake yi in tafi dasu,
don nasan hakan yana faranta mishi rai.
Kullum naje gabanshi tare da su kuwa sai ya
gaya mun cewar wadannan yaran da kike gani
naki ne sun kuma ishe ki kar ki yarda ki daga
hankalinki don ganin wai baki haifa ya rayu ba
kowa da kike ganin yana da irin jarrabawarshi in
kuma kayi hakuri to da irin sakamakon da za'ayi
maka in ce mishi to Baba.
A wannan lokacin ne Alhaji ya soma yi min
magana kan sha'awar da yake da ita ta fara yin
kasuwanci zuwa wasu garuruwa yana min
bayani kan muhimmancin neman halal, na ce
haka ne ko kuwa ba kya son hakan?" Nayi maza
na ce "A'a ai ni ba zan ce kar ka nemi arziki ba."
Ya ce"eh na sani Zuwairah, shi yasa na gaya
miki don ki taimake ni wurin Baba ya barni in
fara don nayi mishi magana bai amince ba,
kuma ya ki amincewar ne a dalilin wai ba ki da
kowa sai ni sai ko shi in na fara tafiye-tafiyen
wai zaki yi kewata da yawa gara sauran matan
su suna da dangi anan kusa. Bayani mai tsawo
yayi min cikin rarrashi da kamun kafar in sa
baki Baba ya amince mishi da bukatar tashi har
14

yana yi min alkawarin wai ba zai rinka yin
tafiyar yana dadewa ba, ban ce mishi komai ba
har yay1 ya gama yayi shiru ban tanka ba saboda
nima can Cikin zuciyata nasan zanyi kewarshi
amma kuma duk da haka nayi mishi yanda yake
so din wato in rokar mishi Baba cikin natsuwa
na same shi nayi mishi bayanin ya daga ido ya
kalle ni cikin kulawa ya ce "tausayinki nake ji
Zuwaira, in har ya dandani dadin neman kudi a
nesa da gida zai yi wuya ya dawo gidan ya
zauna, amma tunda kin ce a barshi yaje shi
kenan."
Alhaji ya soma tafiya Fatauci daga gida
zuwa garuruwa daban-daban na kurkusa, wani
lokaci yayi kwana biyu ko uku ya dawo gida.
Ana nan ana nan sai gashi in ya tafi sai ya kai
har kwana ashirin bai dawo ba, in na zauna
wurin Baba ina lissafin kwanakin tafiyar tashi
sai ya ce, "a to, abin da na gudar miki kenan, ki
ka ce a barshi ganewan da nayi shima Baba ba
jin dadin dadewan nashi yake yi ba, sai na daina
yi mishi zancen nayi kokarin kawar da
damuwar kewarshi cikin raina, nayi matukar
kokarina na maida hankalina kan al'amarin
'ya'yana wadanda suka riga suka fara girma suka
yi wayo, nake matukar jin dadin mu'amalla dasu
saboda tsananin son juna da muke yi suna sona
15

saboda suna daina buya in yi kukan kewar
Alhaji saboda in har Uwa ta gane nayi kuka ta
rinka kuka kenan saboda ita din tafi su wayo.
Ina cikin wannan zaman da yaran ne rannan
Alhaji ya dawo gida a dakina ya sauka. bayan
al'amura masu yawa sun gudana a tsakaninmu,
muna cikin hira sai ya sako mun wani zance da
ya shafi harkokin kasuwancinshi irin alherin da
yake samu da yanda kasuwa ta bude mishi, na
taya shi murna har cikin zuciyata, sai kuma ya ci
gaba da cewa "to kin san halina Zuwaira, babu
wani al'amari nawa da yake 6oye a gare ki bana
son zaman takura da kewa, don haka nace
wannan karon in zan tafi tare dake zan táfi don
na gaji da zaman kadaici."
Maimakon in ji dadin wannan bayanin da
yayi min tunda dama cikin kewarshi nake, sai na
kasa yin farin ciki a dalilin ganin ya'ya uku
dake kwance akan karamin gadona suna bacci,
wadanda basu san kowa ba sai ni ko dawowa
suka yi daga Makarantar allo basu ganni ba basa
iya jirana in dawo sun rinka shiga sashi-sashi
kenan suna nemana, ga kuma Baba wanda girma
ya riga ya kama shi ni ce mai hidimarshi nice
abokiyar hirarshi to tsallake su duka zanyi in tafi
ko kuwa yaya zanyi?"
16

Da na kalli Alhaji sai kawai na kawar da
fuskata gefe nace 'mishi "ba zani ba." Amsar da
na bashin yayi matukar bashi mamaki, don ya
saba yi ne ina ce mishi duk abin da ka gani.
Cikin natsuwa ya mike ya zauna yana kallona
da fuska mai dauke da alamar mamaki cikin
muryar da ya tausasa ya ce min "kin zartar wa
kanki da hukuncin rashin bina? Ban tanka mishi
ba ban kuma bashi hakuri kan hakan da nayi ba
sai dai nan take naji babu abin da nake son yi
irin in yi kuka kukan kuwa nayi tayi yayi
rarrashi har ya gaji ya ce min "haba Zuwaira me
nayi miki da zafi haka? Ina ta baki hakuri kin ki
ki hakura ko so kike sai yaran nan sun farka sun
ganki kina kuka sun ji zafina tunda zasu ga na
batawa uwarsu, bayan ni ba ma samun zama
cikinsu nake yi ba?" Yana fadin haka nayi shiru
na bar kukan, sai dai kuma har gari ya waye ban
sake tankawa wata maganarshi ba, abin da bai
taba faruwa a tsakaninmu ba. Don haka sai
hankalinshi yayi matukar tashi da abin da nayin.
Gari na wayewa na anmsa kiran Baba saboda
ya kai maganar gabanshi. Ya gama baiyanawa
Baba maganàr da ya ce ba a kara ba kan wannan
baba sai kawai naga ta kama kuka bayanin da ta
yiwa lajfi ban nuna bacin rai ba.

17

Baba ya gyara zama yace, "to yaya zaka
nuna bacin rai bayan abin da kake so tayi maka?
Ai dole Zuwaira tayi kuka tunda ta gane duk
abin da kake nufi bai wuce son ka kwashe
matanka ka tafi dasu ka barta ba, tunda su biyun
dai babu wadda zata yarda ka dauki 'yar uwarta
ka barta to kaje ka dauke su ka bar mu a nan.
Hannu biyu Alhaji yasa ya dafe kanshi
saboda tsananin tashin hankali bai taba zaton
abin da Baba zai gaya mishi kenan ba, nima
kuma nayi mamaki yanda akayi ya gane abin da
ya darsu mun cikin zuciyata.
Baba ya ci gaba da magana yana fadin "Zata
tsallake ya'yanta ta tafi ne ko kuwa so kake ta
kwashi 'ya'yan ku tafi ta bar ni? Ai tasan ko
tuwo bana cin na wata a gidan nan in ba nata ba
ne." Nan da nan Alhaji ya sunkuyar da kai kasa
yayi ta bai wa Baba hakuri yana fadin "ya yi
kuskure da bai yi wannan tunanin ba, amma
tunda haka ne to a bar maganar tafiyar kawai na
tashi na tafi na barsu saboda Baba ya sallame ni.
Nayi matukar jin dadin yanda Baba yayi
mishi wanda yasa nan da nan ya janye tafiyar da
kowa saboda gudun bacin rai, amma kuma daga
baya sai naga to ribar me naci in nayi hakan?
Nasa an hana shi tafiya da matanshi alhalin ni
ina da uzurin da ba zai yiwu in bishi ba, zanje ya
18

ci gaba da zama cikin kewa da kadaicin da yake
cewa ya ishe shi, bayan ga matanshi guda uku a
gida suna zaman jiranshi? Kwana biyu bayan
nar sai na koma gaban Baba na ce mishi a bar
shi ya tafi da duk wacce yake son tafiya, Baba
ni na hakura na yafe mishi, Baba yayi tasa min
albarka alamar ya ji dadin abin da nayin, sai dai
kuma abin da Baban ya fada ne ya tabbata
lokacin da Alhaji ya ce zai tafi da Maryam sai
Karama ta ce bata yarda ba, don haka Baba ya
ce ya tasasu a gaba dukansu ya tafi dasu. Hakan
kuwa akayi.
Shi kenan sai sashin namu ya zama ba kowa
daga ni sai ya'yana muka sake muna ta
sha'aninmu, in gari ya waye muna idar da sallah
in na fito Uwa zata biyo ni ina abin karyawa
tana wanke-wanke, kafin in yi dumame in dama
kunu in toya kosai tuni har ta gama share wurin
nan tas, har taje ta share turken dabbobi, ta kai
musu dusarsu da ruwa tana dawowa sai mu
kwashi abin karyawan mu ja kofar kara mu rufe
wurin namu don kar kaji ko Akuyoyi su shiga
suyi mana barnma, sai mu nufi wajen Baba can
muke karyawa in mun gama in tura su
Makaranta ni kuma in yi mishi abubuwan da zan
yi mishi kamar su ruwan wanka da wanki da

19

share-share in rana tayi in dawo wajena don in
yi mana abincin rana.
Muna zamanmu a haka ko tunanin zuwan
Alhaji ban fara ba saboda ganin dama can da
yake shi kadai yana yin sati uku sati hudu balle
kuma yanzu da ya tasa matanshi a gaba ya tafi
dasu, don haka sha'anin gabana kawai nake yi.
Kwatsam! Rannan sai naga Uwa tana tsalle
tana murna cikin tsananin farin ciki ko magana
bata iyawa a dalilin tsananin murnar da take yi,
sai fadi takc "Babanmu yazo Umma, Babanmu
yazo, Baba yana jin haka shima ya kama murna,
ni kuwa nayi kamar ban damu ba.
Wajen Baba ya fara shigowa tsarabar da
yazo da ita ma a nan nasa aka jibge ta nan take
na dibi ta yara na raba musu na kuma shiga kasa
tsarabar gidan ina bayarwa Uwa tana kaiwa
sassa-sassa tana dawowa na gama na juye
naman saniya da yazo dashi na wanke na dora
akan wuta sai naga wucewarshi zuwa daki nayi
maza na shirya mishi abincin da ya samu nayi
mana na kuma hada da danwaken da na jefa
mishi don shi mai son danwake ne, na kawwo
ruwa na ajiye mishi ina kallon shi yana cin
danwaken sai ya dan kallen yace min dama
kinyi zaton zanzo ne yau? Nayi maza na ce ko
kadan, me ka gani? ya ce na same ku cikin
20

kwalliya dukanku har da Baba gashi kuma ke da
Uwa lallenku sai sheki yake yi, na yi murmushi
nace ai yau Juma'a ne amma ni kam ai ban ma
soma sa rai da zuwanka a yanzu ba, na dauka sai
nan da wata biyu ko uku tukuna amma ba yau
ba sati biyu kacal da tafiyarka, daga ido yayi ya
galla min harara saboda ya gane abin da
maganar tawa take nufi.
Karba sosai nayi mishi a wannan zuwan da
yayi don kuwa maimakon kwana uku ko hudu
da yayi niyyar yi bai tafi ba sai da ya kwana
bakwai cif. Sati biyu kuma da tafiyarshi sai
gashi ya sake dawowa, a haka sai ya ajiyewa
kanshi yin sati biyu ko uku a can in ya dawo
kuma sai yayi kwana biyar ko bakwai ya tafi.
Nan da nan kuma sai maganganu suka soma
yawo wai ya kwashi mata biyu ya kai birni ya
ajiye ya dawo ya tare a wurina, ni kam ko a
jikina jinsu kawai nake yi a wannan lokacin ne
kuma kasuwa ta kara budewa. Alhaji duk wani
abin da ya taba da nufin sayarwa sai ya ci riba a
kanshi duk abin da ya kawo don sayarwa kuma
sai ya zama tamfar warwarcnshi ake yi saboda
saurin karewarshi, don haka in yazo gida zai tafi
zai kawo kudi masu yawa ya bani ya rinka gaya
min cewar komai zaku ci kuci mai kyau in ce
mishi to yanda yake bani kudi haka yake baiwa
21

Baba shi kuma Baba in baya nan baya barina in
sai komai ko da kuwa fura ne da nono komai
saya mana yake yi don haka nan da nan sai ga
kudi a hannuna na tara.
Rannan ina hira da Baba sai ya tambaye ni.
"Babu komai ne a hannunki? Ko mijinki bai
baki komai ne?" Na ce mishi "Akwai Baba,
yana bani in kawo maka su ne?" Ya ce min "eh
to kawo." Naje na kawo mishi su dukansu, ya
karba ya kirga su ya ce "eh lalle kina da kudi to
bari yayanku na tudu yazo sai in tura shi yayi
miki cinikin wata fadamar rake da akayi min
tallanta na ce mishi to Baba." Da haka sai na
mallaki fadamu guda biyu ga wacce Baba ya
bani ga kuma wacce ya saya min da kudina.
Cikin shekaru uku na samun kudin Alhaji da
nayi ina tare da Baba a gida yayi min tattalin
dukiya mai yawa bai bari na in sayi komai da
kudina, gashi kuma ko fita yayi yaga wani abin
sayarwa da za'aci riba zai dawo yace min "kawo
kudin nan a dan gwada juya su ko za'a samu
wani abu akai in ce mishi to, a wannan lokacin
suma su Karama tuni suka goge suka zama
matan birni sai dai dukansu a rame saboda-
zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu, fitinar safe
daban ta yamma daban, gashi gidansu su biyu
saboda Alhaji ya sai nashi gidan sun tashi daga
22

gidan hayan da suke zaune a duk lokacin da
suka zo gida suka yi bakunta suka tafi in muna
hira da Baba zai zolayen da maganarsu ya ce
min yan uwanki sun zo suna kyalli sun baki
sha'awa ko?" Ni kuwa sai in yi murmushi in ce
"ai kyallin kawai na' gani Baba, amma naga
kamar na fisu cika ido." Shi kuwa sai yayi
dariya ya ce, "ai ba ki sha mamaki ba ma sai
randa kika hadu dasu wuri daya kika ga suna
neman rance a wurinki lokacin ne za ki kara
gane kyallin ne kawai, su matan birni da kike
gani ba duka ne suke da hikimar juya kudi ba,
zama suke su mike kafa wai su nan ga masu jin
dadi kin taba ganin jin dadi ga wanda bai da
anini?" In yi murmushi in ce "A a, sai ya ce to
kar ki yarda ki zauna ba kya sana'ar komai ko ba
kiyi da kanki ba rinka baiwa wani amintacce
yana juya miki, in ce mishi to Baba.

23

Alhaji ya kwaso matanshi suka dawo gida
gaba daya, gida hankali ya tashi ganin halin da
Baba yake ciki, ni kam nayi kuka har na gaji
tunanin mutuwar Baba Rabi ya dawo min da
halin da na tsinci kaina a ciki bayan mutuwar
tata, ban taba samun ta kare min wasu abubuwa
ba sai da bata nan na gane ashe ita din idonta ya
tsare al'amura masu yawan gaske,

Please Login or Register in order to submit comment