Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sake jin
wani faduwar gaban nayi maza na mike zaune
na ce mata a ina kika ganshi Uwa? Kan ta ce
min komai sai yaya Balki ta ce min ke kuwa me
yasa kike irin wannan binciken ne Zuwaira? Me
za ki iya yi ne? Kinga yanda kika maida kanki
kuwa cikin 'yan kwanakin nan? Ashe shi mai
imani ba da mika wuya aka sanshi ba? Kalaman
yaya Balki ba su hanani kuka ba, cewar da uwa
tayi da Muntaka take magana ya kara firgitani
ina kuka na cewa Yaya Balki sai yaushe zan
samu abin da nake so? Duk wanda naso rasa shi
nake yi ta ce min da dai kin tuba kin yi ta
istigafari kar ki sanya kanki cikin wata fitina,
duk abin da kika so kika rasa din ai ba naki ba
ne ajiyanshi aka baki ko sai mai shi ya fasa
karba don kina so?
Kwana biyu bayan nanne kawai Uwa ta haifi
yarta mace bayan yar gajeriyar nakuda mai
sauki bata kai awa guda bayan nan ba ta ce
62

garinku na kalle ta a kwance a shimfide na ce
shi kenan Uwa shi kenan Rabi'atu kun tafi ke da
mijinki kun bar min 'yarku shi kenan maimakon
in yi kuka mikewa nayi naje na soma shirya
ruwan da za'ayi mata wanka ni da kaina na
wanketa da taimakon Maryam da Hauwa na
sanya mata kayanta nayi mata addu'a aka zo aka
fita da ita ina kallo nayi zaman karbar gaisuwa
kwana uku da akayi bakwai kuma Alhaji ya ce
sunanki Rabi'atu ya mayar miki da sunan
Uwarki, na sa maigyada ta nemo min mai reno
ta kawo min Talatu, da aka yi sati biyu sai na
samu Alhaji na ce mishi so nake ya yardan min
in je Katagun in dan zauna a dakin Baba in dan
huta, ya ce min to in dan saurare shi tukuna na
ce to. Rannan da ya shirya zai yi tafiya sai
kawai ya ce min dauko yarki muje na ce mishi
to, dani yayi wannan tafiyar da muka dawo
kuma bai dawo dani gida ba sai ya ajiye ni a
gidanshi na Legos, bai kuma sake sha'ani za'ayi
sai bayan shekaru uku sai dai yaya Balki kanje
Legos tayi min bakunta, tun bakuntar farko da
taje mun kuwa na ce mata taje ta kwashe kayan
dakina taje ta gyara nata wurin.
Sai da aka gama ginin gidan nan na dawo
muka sake haduwa dasu Karama saboda a
lokacin kuma Alhaji yayi nufin sake hada
63

iyalinshi wuri, daya na, zo,na samu gida, çike da
iyali ga yara maza da mata don sun riga ni
dawowa.
Nadaga ido na kalli Ummana cikin
tausayawa bakin cikin da tayi na rasa wadanda
taake, so nayi ajiyar zuciya sannanna, ge mata
wato dai Umma ba ke kika, haife ni, ba mutanen
da kike so ne suka haifan miki ni? Sai da ta zuba
min ido kafin ta ce min kwarai kuwa, na
kwantar da kaina jikinta na ce mata to
sake gayawa kowa labarin nan Umma ki bar su
kawai a kan ke kika haife ni tunda ma dai a
nononki nasha na girma.
Umma tayi murmushin farko tunda, ta fara
ban labarin ta ce ban shayar dake nonona ba
Adawiyya, Alhaji bai yarda nayi hakan ba na
rene ki ne ta hanyar shayar dake da abincin
jarirai, Babangida shine yaron da na, shayar
dashi nonona, ina ganin biyu bisa ukun nonon
da ya sha nawa ne saboda kullum a wurina yake
kuma a wancan lokacin, Maryam kanyi yaji in
Suka yi fada da Karama, ta barshi kan wannan
dalilin sai ya zama nike shayar dashi.,Nan take
naji kishin yaya Almu ya kama ni na ce wato
yaya Almu ma danki ne? Ta yi maza tace nawa
mana Adawiyya, Alhajj ne fa ya haife shi
Babu kuma ya bani shi na kuma rene shi ta
64

hanyar shayar dashi nonona, shi kuma bai taba
nuna min yasan yana da wata Uwa ba in ba ni
ba ce Lamido ai na wane Adawiyyah nawa ne,
ke kuwa Muntaka da uwana ne suka haifanmu
ke, don haka bani da kamarku ke dashi sai ko
Junaidu dukanku na wane hakan nema yasa na
baiwa Alhaji sunan Junaidu lokacin da ya ce in
taya shi zaben wanda zai barwa shugabancin
kamfanoninshi.
Na daga ido na kalli Umma zuciyata ta sake
raya min wasu al'amura game da ita, ban sani ba
ko ta gane tunani nake yi sai na ji ta ce min
taimake ni kar ki ji wani canji a tare da ni don
na ce miki bani ce mahaifiyarki ba, ke din kece
komai nawa kece Muntaka, kece kuma Uwa, a
duk lokacin da na daga ido na kalle ki na kan
ganki ne da kamanni guda biyu, kina kama da
Muntaka kamannin dake sawa mutane suna
ganin kamanninki dani amma ni da aka haifi
Uwa akan idona na kuma rene ta ta girma a
gabana nasan abubuwanki da yawa nata ne mafi
yawancin lokaci nakan biki da kallo ne saboda
wasu abubuwa da kike yi wadanda nake ganin
tamfar koyar dake su tayi sai dai kuma tunda
nasan baki santa ba to na sanbà koyo ba ne
gado ne.

65

Na matsa jikin Umma na kwantar da kaina a
cinyarta cikin hawayen tausayi nace mata, kece
komai dina Umma ba zan canza komai ba game
da ke sai dai ma in kara sonki....kan Umma ta
ce min komai sai naji muryar Baba a cikin falon
Umma yana cewa me Zuwaira take yi ne a
wurin nan ta barni ni kadai har yanzu? Kan tayi
magana sai Baba ya shigo ya gammu tare, ashe
baki baiwa Lamido matarshi ba shima ya samu
ya huta kamar sauran 'yan uwanshi? Umma ta ce
kayi hakuri gani nan zuwa, ya ce a'a kar ki zo
alamar yayi fushi, ya juya ya tafi.
Umma tayi maza ta dauki wayarta ta kira
Umma amarya taimake ni kije gun Alhaji kar ki
bari yayi fushi sai da safe zan shiga wurin naku
ta maida wayar ta ajiye hakan da Umma tayi
bani wani mamaki ba don nasha ganin tana
baiwa Umma amarya kyautan girkinta.
Gari na wayewa Hajiya Hauwa ta iso saboda
wayar asuba da Umma tayi mata tana shigowa
ta ce mata 'yarki zaki kai gidan mijin ta tun
Alhaji bai fito ya ce ta tafi ita kadai ba ki ce don
ni uwar miji ce yasa na bari yayi hakan Umma
Hauwa ta ce eh mana me zai hana ni fada?
Umma Karama kawai aka kai ni nayiwa
sallama saboda Umma amarya bata fito daga
wurin baba ba, a haka muka bar gidan daga ni

66

sai Umma Hauwa sai ko Baba Talatu da Ummma
ta ce ta biyo ni don dama zamana take yi a pgidan
muna tafiya ni da Umma abaya direba da Baba
Talatu a gaba Umma Hauwa ta ce to ke Talatu
ai gara ki hakura ki bar kuka haka tunda ga
uwar dakinki kuna tare.
Ni kam har muka kusa isa kaduna ina kuka,
tausayin Ummana ne ya ke damuna ko damna
can babu abin da nake so kamar Umma, amma
ban taba sonta ba kwatankwacin son da nake yi
mata a yau ba.
Mun kusa shiga Kaduna direba yana kallon
motar dake biye dashi ta cikin madubi saboda
bata wurin da yayi ta wuce taki ya ce au Hajiya
ai Lamido ne yake biye damu, Umma Hauwa
tayi murnmushi ta ce, a to, uwarshi ta ce wai yayi
gaba saboda yayi fushi da abin da Adawiyya
tayi mishi ana fushi da Amarya ne?
Yaya Almu ne ya wuce direba yabi bayanshi
muka karasa gidan babu kowa a cikin gidan
yaya Almu ne yasa makullai ya bude ko ina
muka shiga ko'ina gwanin sha'awa sai kamshi
da kamshi ke tashi komai tsaf komai a tsare a
tsaftace gwanin sha'awa ga wani sanyi na ni'ima
ai Alhaji yayi dabara daya ce kowace amarya
tabi angonta kawai ba sai an kaita ba da yanzu
duk wurin nan an lalatashi, tana wannan
67

maganar ni kuwa ina takure wuri daya cikin
lullu6i ina ta karanto addu'o'i iri-iri da Baba
Balki ta bani ta ce in karantasu a lokacin da na
shiga gidan mijina sai a wannan lokacin ne ta
fado min a rai wato haka ta ce ita ce mahaifiyar
Uwata, wani tausayin ya sake kama ni da na tuna
su san san uwa wato mahaifiyata nice ban san
taba ban santa ba ban san Babana ba sai Umma
da Baba na sani. Wasu sabbin hawayen suka
soma zuba abin da ya fusata Umma Hauwa tayi
tayi min fadi baba Talatu tana ta bata hakuri.
Direban da ya kawo mu ya shigo rike da
manyan iedoji ya ajiye ya koma ya sake debo
wasu ya kawo, Umma ta ce kai sun isa haka bai
ga mu uku ba ne?
Da aka natsa Umma ta sanya ni na sake
wanka na tsalla kwalliya cikin wani tsalelen
leshi mai matukar laushi ya kuma karbe ni sosai
don ya dace da kalan jikina gashi kuma dama
Jikin nawa yayi shar a dalilin lallen da ta mulke
ni dashi gaba daya.
Tunda muka iso babu wanda ya sake jin
motsin yaya Almu sai da muka yi sallar La'asar
Umma ta ce a kira mata shi don zata tafi,
lokacin ne ya shigo dakin cikin ladabi a kasa ya
zauna kamar yanda nima dama aka san ya same
ni sai Umma ce akan kujera. Sai da ta amsa
68

gaisuwar da yayi mata sannan ta ce mishi ni zan
tafi Lamido ga matarka nan na kawo maka ba
sai na ce maka komai ba, kafi kowa saninta,
kayi tayin hakuri Allah ya saba halayenku ya
kuma sa ta zame maka uwar iyali tana fadin
hakan ta mike tayi waje tana goge fuskarta da
gefen gyalenta yaya Almu ya mike cikin
natsuwa ya bi bayanta don ganin tafiyarta. Baba
Talatu kuma ta shigo tana ta bani hakuri tana
cewa aike aure mai dadi kika yi uwardakina
mijin da zai yi hakuri dake ai shi aka baki.
Yaya Almu ya sake shigowa bayan tafiyar
Umma Hauwa Baba Talatu tana ganin shi ta
mike zata fita ya ce a'a kuyi zamanku Baba
Talatu ya juya ya fita bai sake shigowa ba sai
bayan sallar Isha'i, yaya dai Baba akwai
damuwa ne? Tayi maza ta ce mishi babu
babangida ya ce to kuna son wani abunci? Ta
sake cewa a'a bamu da bukatar komai don
akwai, yayi murmushi ya ce, to sai yaushe
amaryar zata fara yin magana? Ta taya shi
murmushin don jin ya shigar da raha cikin
lamarin yace ina jin dai so take a sayi bakinta,
ya juya zai fita yana cewa, ta yata kwana Baba,
da sauri Baba Talatu ta ce mishi a'a ai ba za ayi
haka dani ba, ba girmana ba ne yin hakan bai
tsaya ba ya tafi. Da sauri na kalli Baba Talatu na
69

ce mata me yasa kika gaya mishi haka? Ta ce
wane ni ai kawaici yayi mun so kike in jira shi
sai ya ce in bashi wuri? Tana Cikin maganar wai
kawai naji yaya Almu ya sake shigowa ta wata
kofar daban san da ita ba Baba Talatu tana ganin
haka tayi maza ta fice ta tafi wurinta shima yana
karasowa ya maida kofar falon ya kulle ya dawo
inda nake zaune cikin murmushi nazo sayen
bakin amarya ne, yana maganar yana kallona ya
miko hanmu a hankali ya tallabi habata ya
karanto wasu addu'o'i ya tofa min a fuskata
sanan ya mike ya sure ni zuwa daya daga cikin
dakinan kwanan da suke wurin.
Da Asuba na bi umarnin da ya bani na
komawa daya dakin na kwanta bayan na idar da
sallar Asuba kas ancewar tsawon daren ban samu
na runtsa ba ga kunma gajiya da rashin bacci na
kwana da kwanaki bacci mai nauyi Sosai nayi
ban farka ba sai bayan shabiyu ko lokacin ma
kuwa dana farkka dana lura sai na gane Baba
Talatu ce ta taslhe ni saboda ganinta da nayi tana
matsa min kafata, na kalle ta cikin natsuwa
maimakon in gaya mata wata magana saboda
kidimewa sai na ce mata bani da lafiya Baba
tayi maza ta ce na sani uwardakina ko daga farin
cikin maigidan da na gani na san abin da ake
ciki balle tun safe ya wanke shinfidun da suka

70

lalace ya shanya su ga kuma alheri mai yawa da
yayi min turaren atamfofi da turare gami da
kudi ya bani Allah dai yayi muku albarka ya
kuma sa ku zame mishi uwar iyalinshi.
Ban tanka mata ba don ba abin da nake nufin
gaya mata kenan ba na so ne kawai ta fahimci
zazzabi ya kama ni. Mikewa nayi cikin karfin
hali na shiga bandakin na dan hora kaina da
ruwan zafin da na zubawa detol tunda na riga na
girma ba sai na jira an gaya min abin da zan
taimaki kaina dashi ba, na fito na samu abincin
da ta kawo min na gama koma1 na sanya kayana
bayan na gyara kaina nayi matukar yin kyau
zani da riga na sanya na yadin material mai
kyaun gaske, har na zauna da shirin ka ryawa
sai na tambayi Baba Talatu yaya Almu ya fita
ne? Ta ce a'a na ce to me aka kai mish1? Ta ce
bai karbi komai ba na dai ce mishi akwai.
tsallake abin karyawan nawa nayi na nufi kicin
din don ganin abin da zan shirya mishi tunda na
gane shima ba karya ba nan da nan na shirya
mishi abubuwa masu sauki na hada da farfesun
kajin da Baba Talatu tayi da na koda naje na har
falonshi na kai mishi sai dai ban yarda na zauna
mun karya tare ba kamar yanda ya nemi inyi
fitowa nayi na dawo wajena na zuana ina
karyawa da Baba Talatu tana yi min hira sai dai
71

gaba daya hirar tata yau kan budurcin ya mace
ne ni kam ina jinta.
Tun daga rannan na shiga kicin don girkin
abincin da yaya Almu zai ci ban yarda amarci ya
hanani yin hakan ba saboda irin kalaman da
Umma na tayi mun kan muhimmancin aure da
kuma kula da miji, sai dai kuma na kasa
daurewa in barshi ya sake matsowa kusa dani
saboda gani nake tanfar ya kware ni ko kuma in
ce ya so kanshi da yawa a kaina don haka ina
kai mishi abincin nake dawowa wurin in shiga
in kulle ko'ina in yi kwanciyata.
Rannan da safe ina kicin zan shirya mana
abin karyawa rannan kuwa satina guda ne a
gidan sai ya shigo kicin din yazo ya same ni ya
ce amuna dai kin san tunda kika zo baki yi mun
shinfida ba cikin ladabi na ce mishi bari in gama
in zo in yi ya ce a'a bar wannan aikin kije kiyi
mun wancan din tukuna, don ya fi muhimmanci
a wurina na ce to na yi maza na wanke hannuna
da sabulu na goge shi da tawul kafin na shiga
dakina naje na dauko wani zanin gadon da zan
canza mishi sai da na shiga can cikin dakin
dakin wanda sai ranar na fara shiga naga komai
a kintse a tsabtace ga kamshi mai dadi dake
tashi a ciki, lokacinne na gane wayon da yaya
Almu yayi mun saboda ganinshi da nayi a jikin

72

kofa r dana biyo ya tsare ko'ina ban ce mishi
komai ba don na riga na gane abin da yake nufi.
Abin da yaga dama yayi shi da kanshi kuma
nasan yasan ya kware ni tunda duk wani abin da
yayi na ya gamsar da kanshi ne kawai, na
kwance a gefe ina kallonshi cikin hikima a
zuciyata dai tunani nake yi ko kowa haka yake
ko kuwa yaya Almu ne kawai mai irin wannan
halin? Ban ankara ba da idona ya kai kan agogo
sai naga wai sha biyu ta wuce na yunkura cikin
karfin hali na fita na bar dakin yana kirana rabi,
ban tanka mishi ba na koma dakina na zauna
Baba ta biyo ni za'ayi miki wani abu ne? Na ce
mata a'a in dai kin karya shi kenan ta ce to ta
juya ta fita nima nayi abin da zanyi na kwanta.
Tun daga rannan na yiwa yaya Almu ya ji
ban sake yi mishi girki ba ban sake leka koda
falonshi ba ne balle in kai ga shiga ko tsakar
gida bana shigowa.
Kwanana hudu da daukan wannan matakin
ina kwance a dakina tun safe ban fito ba shima
yaya Almu yana wurin shi sai kawai na ji
sallamar da ta yi min kama da muryar Ummana
da gudu na yiwo waje ashe kuwa ita ce sai dai
har ta shiga wurin yaya Almu can na same su
yana ta faman ina yaka saka da ita. Fadawa nayi
Jikinta na kwanta ina tumurmusarta kamar wata
73

yar yarinya yaya Almu ne ya kawo mata abin
sha ya koma gefe ya zauna cikin farin ciki yana
cewa Umma ba ki ce mana zaki zo ba.
Ta ce eh ai zuwan nawa ba na shiri ba ne
Talatu ce tayi mun waya ta ce bata gane kan
matar gidan ba da farko dai ta kar6i hidimar
gidanta gwanin sha'awa amma yan kwanakin
nan bata gane mata ba shi ne na ce to bari in zo
in ji me ya faru? Na nemi wuri na zauna cikin
natsuwa saboda jin maganar tata ban ga kuma
alamar wasa a tare da ita ba, ta sake kallona ta
ce me ya same ki Talatu ta ce kin saki hidimar
mijinki? Ban yi magana ba na soma kuka
saboda ganewan da nayi cewa dan kankanin
laifi zanyi tayi min fada ganin ina kuka sai ta
juya wurin yaya Almu ta tambaye shi nayi zaton
ba zai yi magana ba sai kawai naji yace wai
daga nasata ta shigo dakina ne Umma.
Umma tayi shiru ba ta ce mishi komai ba, ta
dai yi wasu yan maganganu ta mike zata tafi na
ce baki shiga wurina ba fa Umma, ta ce sai
randa na sake zuwa tunda ba kya jin magana ta
fita waje Baba Talatu ta fito tana yi mata
magana ta kawo kudi ta bata ta shiga mota ta
tafi ta barni ina cizon yatsa saboda takaicin kin
shiga wurina da tayi yan kwanaki kadan bayan
wannan lokacin har nan kuma ban yarda mun
74

shirya da yaya Almu ba don nasan abin da shirin
namu yake nufi sai kawai Umma ta bugo mun
waya dana dauka sai ta ce min shiryawa zaki yi
kiyi wa Lamido rakiya zuwa kasar Philipine
kuje can kuyi amarcin daga nan kuma akwai
aikin da zai yiwa Alhaji in kuma har ku ka dawo
ba ki saki jiki dashi ba zan sa Talatu ta koma
gida abar ku ku biyu a gidan ai kunyarta yake ji
da bai yarda da wannan sakaran ba.
To hakan kuwa akayi ba karamin morewa
amarci yaya Almu yayi ba a wannan tafiya da
muka yi tunda daki daya muke bayan haka
kuma na kara yarda da maganar Umma ta cewar
kunyar Baba Talatu yake ji. Cikin sati ukun da
muka yi ya tilasta min sabawa da lalurarshi akan
dole na hakura da hakan don babu dama yaga na
bata rai sai ya ce min raguwa kawai, yara
kanana ma ana aurensu su zauna kalau da
mazansu balle ke bari muna komawa gida naga
za ki sake kawo min wani sakarci sallamar Baba
Talatu zanyi daga nan ta koma gida ta zauna
tunda ba ki fahimci adalcina ba kina so ki fake
bayan kunyar ta da nake ji ki takura min.
Ban ce mishi komai ba har muka gama abin
da zai yi muka dawo gida, a Legos muka sauka
wurin Baba don yi mishi bayanin komai,
Ummanane a wurinshi don bhaka ba karamin
75
sauka muka samu ba. Bayan mun gama cin
abinci falon Baba ni da Umma muka dawo
dakinta muna shiga ta ce mun kinga kyan da
kika yi kuwa, ko kuwa dai kin tsallake wata ne?
Na ce kai Umma kenan, na ki maganar ta ce
cika na soma yi mata kukan shagwaba ina fadin,
bana son abin da kike yi min Umma, ta ce to na
daina, na daina Adawiyya.
Ba mu dawo gida ba sai da muka je gidan
yaya Junaidu wanda a yanzu na fahimci
kawunane kanin mahaifiyata uwa daya uba
daya, ita tasha nono ta bar mishi.
Wata sabuwar mu'amalla muka yi tsakanina
da Yaya Junaidu, girman darajarshi ya karu a
idona shima ya kara kamewa sosai alamar dai
ya na game matsayinshi a wurina, itama Anti
Rahma kauna mai yawa ta nuna min da kulawa
da zamu tafi kuma sai ta ce min ke 'ya ce a
gidan nan kawunki ya riga yayi min bayanin
komai don haka bai yiwuwa ki shigo gidan nan
ki fita ba tare da kin ce ga abin da kike so ba, na
yi murmushi na ce Anti Rahma Philipine muka
fito kan hanyarmu ta dawowa kuma mun tsaya a
Dubai.
Ta ce ko a ina kika tsaya ai bai wuce in yi
miki kyauta irin ta uwa ga 'yarta ba, na ce haka
ne Anti, to hijabin dake iikinshi yayi min kyau
76

ina son shi, warddrop ta bude ta debo mun sabbi
guda shida tana zuba min su cikin ledar shagon
da aka saye su tana gaya min ai fitinar. kawunki
yawa ne da ita wai har a cikin gida bai yarda in
rinka yawo haka ba, saboda masu shigowa
gidan nayi murmushi na ce yana da gaskiya
Anti, mun fito falo inda su yaya Almu suke na
zauna cikin ladabi ina yiwa Yaya Junaidu
sallama sai ya ce min haka za ki fita ba ki dauki
komai a gidan ba? Na ce na dauka na samu
hijabai masu kyau wurin Anti Rahma, ya ce to
madalla ku gaida gida.
Mun dawo gida ni da yaya Almu abin
gwanin sha'awa amarci sosai muke yi ni da shi,
jin juna a rai muke yi yaya Almu ji yake tamfar
ya lashe ni don dadi, ganin na saki jiki dashi na
daina tsananta yi mishi rowar kaina sai dai in yi
mishi shagwaba. Munyi matukar shakuwa
tamfar dai auren namu ba sabo ba ne, ko da dai
dama can akwai sabo da shakuwa mai yawa a
tsakaninmu, to amma kuma ai shakuwar miji da
mata daban ne tunda shakuwa ce ta aure.
Muna isowa gida a dakin Yaya Almu muka
tare abin da ya ce kenan hakan kuwa nayi mishi
sai in wuni in kwana ban shi sa wurina ba in har
ba bakuwa ce tazo ba ma dakinshi komai zanyi
anan nake yi nasa hannu biyu na karbi hidimar
77

mijina da gidana, gaba daya kowane lokaci
cikin shirya mishi nau'o'in abinci iri-iri nake
yaya Almu mutum ne da ya san darajar mace ba
mutum ba ne da ya damu da ya zauna komai sai
anyi mishi in ma yaga zanyi dawainiya mai
yawa zai taya ni zai kuma gaya min duk wannan
abin da kike yi fa yi kike yi kawai don neman
lada amma muhimmin aikinki anan gidan shine
gyara mun shimfida.
In ce mishi kai yaya Almu kar fa Baba
Talatu ta ji ka, murmushi yake yi ya ce ba
komai don ta ji ni tasan gaskiya nake fadi.
Ina jin dadin zama da Baba Talatu ina kuma
son zama da ita din a yau kuma ban dauke ta
mai yi min hidima ba na dauke ta wani bangare
nawa tanfar uwa musamman da na gane son da
take yi mun na gaskiya ne, tunda taga zan bata
wa mijina tayi maz ata shaidawa Ummana tazo
tayi gyara ban da haka baba Talatu mai kamun
kai ne mai rike girmanta ganewan da tayi yaya
Almu ma'abocin shiga kicin ne in har ina ciki in
ta ganni zan yi girki tasan yana gida kauda
jikinta take yi ta shige wurin ta, da nayi mata
magana sai ta ce min Lamido mai kunya ne bai,
kamata in rinka nema in takura mishi ba,
ganewar da nayi Baba Talatu tana sona tana

78

kuma son mijina sai na kara sonta da ganin
girmanta.
Rannan muna hira da Baba Talatu a tsakar
gida saboda yaya Almu baya nan yana Abuja,
don yana da case a babbar kotun Abuja, wato
(Court of Apeal). Baba Talatu bani wani tsohon
labari na wani abin da aka yi tun ina 'yar karama
sai da na gama sauraronta naji tayi shiru sai na
ce mata Baba za ki yi mana girki ne yau? Ta
kalle ni ta ce saboda Lamido baya nan shi ne ba
za ki yi mana ba ko? Na yi murmushi na ce a'a
Baba bana jin dadi ne kawai yau kuiya nake ji
shi yasa na ce bari in huta, ta yi murmushi ta ce
sai in yi mana ai ma ina ganin kokarinki ke
cikinki bai saki wani laulayi mai tsanani tanfar
ba cikin fari ba.
Nayi murmushi na ce tafdijan, wai ni me
yasa ake yi min haka ne Baba? Babu dama in
dan yi wani abu sai ace ciki Umma ta ce ciki
yaya Almu ma haka gashi kema kin fara, ta ce
eh ai kinyi kama da mai cikin ne kinga yanda
kika dawo kuwa? Na ce to bani da komai sai na
gama cin amarcina tukuna, tayi maza ta ce uh'uh
kar dai kiyi wani abin da za ki kwari kanki ciki
ba zai hana ki Cin amarci anan gidan ba sai dai
ma ya kara miki ba sai na tsaya ina gaya miki
darajar dan da za ki haifarwa Babangida ba, kin

79


kuma Sani sarai uwarki zata fi kowa murnar
ganin hakan.
Kwanaki kadan bayan nan na samu kaina
cikin al'ada, yi alwala ki zo muyi sallah kinga
ban samu jam'i ba a masallaci, yaya AImu ne ya
ban wannan umarnin, sai na kalle shi cikin
natsuwa na ce mishi, ai da na je wanka dazu sai
naga al'ada tazo min shi yasa ban yiwo alwala
daga can ba, abin da kawai na gaya mishi kenan
ya tsuke fuska tanfar wani mummunan labari na
bashi.
Cikin dare muna kwance na farka daga bacci
na ganshi ido biyu, me ya faru yaya Almu kko
kana da wata shari'ar ne gobe? Ya dan yi ajiyar
zuciya kadan ya ce, al'adarki ce ta ishe ni, ni
tana takura min a dalilin in tazo bata daukewa
da wuri, gashi kuma dama na tsani ganin kina
yinta, na ce ba ka son ganin ina yi fa ka ce?
Yayi maza ya ce eh bana so shiga tsakanina
dake take yi tsawon kwanaki bakwai ban da
haka kuma na gaji da ganinki haka so nake in
ganki da ciki Rabi, ya zuba min ido cikin
natsuwa yana kallona, na dan matsa kusa dashi
don in kwantar mishi da hankali sai na ce mishi
ai amarci muke yi yanzu yaya, yayi maza ya ce
bana son amarcin ya ishe ni haka tunda ke a
wurinki in an samu ciki amarci ya kare ne, kina
80

nufin ki ce min sauran 'yan matan dukansu sun
daina amarckine?

Please Login or Register in order to submit comment