Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma amfana
kwarai da kawance na da ita don ita ta koya min
kwalliya da gold maimakon yawan daura zani.
Nayi kwalliya sosai na kuma yi kyau har ba'a
magana ga hakorana biyu a lokacin nan da na
sanyo sai daukar ido suke yi suna sheki suna

43

walwal saboda kasancewarsu jajaye wata mace
tayi sallama ta shigo tana tashe da danta dake ta
faman kuka yana shan majina, nayi mata sannu
da zuwa na kuma shiga gaisheta tunda banga
alamar zata karaso ba, sai dai bata wani amsa ba
ta shiga ce min kece mamansu Junaidu? Na ce
mata eh ta ce to kinga ki yiwa 'ya'yanki kashedi
don bai zamo min komai ba in sanya a nada
musu dukan tsiya sun tasa min yaro a gaba da
duka na menene hakan? Na kalle ta a lalace na
ce na menene za ki kisa ayi musu duka in baki
yi haka ba baki haihu da kyau ba, a fusace ta ce
ai abin da za ki gaya min kenan? Na ce na gaya
miki ni sau nawa yaran unguwar nan suka
fasawa 'ya'yana kai da duwatsu a garin jefe-
jefensu kin taba ganin kafata na shiga wani gida
don kai kara sai ke naki dan don an doke shi, to
dan gwal ne da ba za a dake shi ba? Ta ce to shi
kenan ta juya zata fita sai ga Alhaji ya fito daga
falonshi ranshi a 6ace, ku zo nan mai yaro kiyi
hakuri kiyi hakuri kin ji ko za'ayi musu fada
yasa hannu a aljihu ya ciro kudi ya mikawa
yaron ya ce gashi ko don Allah kuyi hakuri suka
yi godiya suka fita, suna barin gidan ya rufe ni
da fada kan me zanyi mata irin maganganun da
nayi mata ina laifi da ta kawo min kara? Na ce
tO amma ni gunwa nake kai kara? Ni sau nawa
44

ana yiwa yaran nan ciwo wa na taba gayawa?
Yau inda da Junaidu kadai ake yi da da sauki,
tunda shima ya iya dukan ya'yan Jama'a amma
Babangida fadawa yake fada ga tabon dutse nan
a kanshi har yanzu bai gama warkewa ba sai
kuma ni ta shigo min gida zata yi min bakar
magana? Haka ake yi? Ni ban taba ganin irin
wannan rayuwar ba kai kasan darajar naka
amma baka san na wani ba iyaye idonsu akan
'ya'ya babu kunya babu kawaici, yayi murmushi
ya ce to ai banbancin zaman birni da na karkara
kenan, yanzu mü a gida ka isa ma kace zaka yi
magana akan abin da aka yiwa danka? Na ce ba
a isa ba ya ce to ki rinka yin hakuri in an kawo
kara ki bada hakuri in kuma an yiwa naki kiyi
hakuri, na ce mishi to.
Tafiya daya Alhaji ya yi bayan wannan
lokacin ya dawo ya sauka a gidan su Karama bai
zo gidanmu ya ganmu ba sai da ya kwana biyu
abin da yayi matukar kona min rai, har na kasa
boyewa. Ya shigo gidan nayi kamar ban san
daga tafiya yake ba, ban da sannu da zuwan da
rfayi mishi ban kara ba, ko ruwa kuma ban kawo
mishi ba da dai ya lura ba wani tarbar arziki
zanyi mishi ba sai kawai ya tashi yayi
ficewarshi ya tafi, ban sake ganinshi ba ya gama
saura kwana biyunshi na can gidan ina tunanin
45

yau dai ai dolenshi zai dawo nan din da ba ya so
zan kuma gaya mishi na fara gajiya da hakurin
da kullum nake yi, baya gani tunda bai gudun
bacin raina sai nasu, ban taba ganin ranar da ya
dawo ya wuni a gari bai je ya duba su ba sai ni
da ya raina. Ina cikin jira yazo in jera mishi1
wadannan maganganun sai kawai ga dan aike an
kawo min kudin cefane wai shi yayi tafiya na ce
tafidijam, ban taba yin sha'awar yin yaji ba irin
wannan ranar sai dai kuma inyi yaji inje ina?
Haka na hakura na zauna raina a bace bai dawo
ba kuwa sai da yayi sati uku ya sauka anan
gidan. Rannan kuwa kwana nayi ina yi mishi
kuka ya zuba min ido kawai yana kallona sai da
nayi ya 1she ni nayi shiru sannan ya ce min, ai
na dauka akwai wani sassauci a tsakanina dake
ban taba dauka kina lura da wani abin da nake
yi musu ba, na dauka tsakanina dake kawai kika
sani, to amma tunda haka ne shikenan ba zan
sake ba zan rinka kiyaye abin da nake yi musu
in tabbatar nayi miki kamar yanda kema zan
kiyaye wanda nake yi miki in rinka yi musu.
Kunya ce ta kama ni da yayi min wannan
maganar don nasan abin da yake nufi sai dai ban
yarda ya gane naji kunyar ba ne eh ai gara ka
rinka yin hakan, cikin raina dai na kudurawa
46

kaina cewar babu wani abin da zai sake yi min
in bude baki in yi magana.
A wannan shekarar ne Alhaji ya kaini
kasarmu ta Senegal tare da yara na tafi tare da
tsaraba mai yawan gaske, abin mamaki ashe wai
har kanine dani wanda muke uwa daya uba
daya, kuma wai tuni Alhaji ya dade da sani
amma bai taba bani labari ba sai ran da muka
isa. Bayan mun natsa sai ya kalle ni ya ce min,
ina jin fa Muntakan nan shi ne kaninki da Baba
ya bani labari da sauri na kalle shi na ce mishi
kanina? Ya ce eh ita Inna ba wurin haihuwa ta
rasu ba? Lokacin ne na tuna Babana ya sha gaya
min Innata wurin haihuwar kanina ta rasu, na
kalle shi na ce tafdijam, amma shine baka taba
gaya min ba? Yayi murmushi ya ce, "to ai tayar
miki da hankali kawai zanyi, na ce haka ne.
A zaman bakuntar da nayi, nayi kokarin jan
Muntaka a jikina muka yi sabo na kuma nuna
mishi cewar ya bini muje yaga inda nake abin
da kanin Babanmu wanda yake shine marikin
shi yaso ya ki yarda nima kuwa na tasa Alhaji a
gaba da kuka na ce mishi ai da ganin Muntaka
ba dadinsuyake ji ba, ba gashi duk sunyiwa
ya'yansu sa'o'inshi aure ba amma shi basu yi
mishi ba, ya ce ai sun ce bara rashin lafiyar da
yayi ne yasa ba ayi mishi bikin ba, na ce eh to
47

muje dai yaga wuri, ya yi murmushi ya ce to
bari muji abin da Baban zai ce.
A haka muka dawo da Muntaka gida akan
zai ga wuri ya koma sai muyi zamanmu nan da
nan ya wastsake daga duk wata wahala ya zama
santalelen saurayi gashi tunda yazo ciwon cikin
da suka ce yana dashi din bai sake tashi ba,
gashi nan da nan Alhaji ya sanya shi cikin
harkokin dukiya har ya shiga yin tafiye-tafiye
dashi Alhaji ya kara nuna mishi gatan da ya
tabbatar min da matsayina a wurinshi.
Rannan ina zaune a falona bayan mun dawwo
daga umrar da muka tafi ni da Hajiya Hauwa,
hutawa nake yi cikin nishadi sai naga Muntaka
ya shigo gida yana sanye da doguwar jallabiya
fara sol a jikinshi da farar hula 'yar karama yayi
matukar yin kyau yayi sallama a bakin kofa ya
cire silifas din wanka dake kafarshi ya shigo ya
zauna na zuba mishi ido ina kallonshi na ce,
Muntaka baka je kasuwa ba ka kuma san Alhaji
ba ya nan? Ya ce naje yanzu na dawo ina son
yin magana dake ne sai 1n koma, na ce mishi to,
na dan daga murya na kira Uwa na ce kawowa
kawunku abinci, ta ce to taje ta kawo ta ajiye
mishi ya ci kadan sai ya kalle ni ya ce so nake in
yaya ya dawo ki rokar min shi ina so in koma
kasarmu da sauri na ce mishi Senegal Mun
48

taka? Ya sunkuyar da kanshi kasa ya ce mun eh
ai kinga ba na shekara biyu kenan har da
watanni tunda muka zo da zamu taho kuwa
cewa akayi zan zo in ga wuri in koma, na ce
haka ne. Bayan fitar shi sai nayi ta kuka saboda
ban son tafiyar tashi ina ganinshi a matsayin
dangina gashi zai gudu ya barni, to ko dai wani
laifi nayi mishi bai gaya min ba? Abin da ya
tsaya min a zuciyata kenan, sai dai bance mishi
komai ba sai da Alhajin ya dawo na bashi labari
da ya gama sauraronä sai ya ce min ina ganin
aure yake so ai ya girma bana shekarunshi
ashirin da takwas kenan tunda ke kinyi talatin
bana nace mishi hakane, ya ce to gaya mishi ya
duba yarinyar da yake so sai a aura mishi, na ce
to da na gayawa Muntaka sai ya ce min shi bai
son auren don baiga wace yake so ba, Alhaji ya
ce in gaya mishi yaje ya duba cikin 'ya'yan
abokanshi ya sake cewa baya so. Rannan nayi
kuka a gabanshi ina tambayar shi me yasa baka
Sona Muntaka me yasa baka son zama dani?
Kwana biyu bayan nan na kira Muntaka ina
rarrashinshi don ya gaya min meye
damuwarshi? Sai ya ce min tsoro nake kar in yi
abin da ba a taba yi ba, nayi maza na tambaye
shin me? Wane abu ne zaka yi wanda a duniya
ba a riga ka yin shi ba? Ya sunkuyar da kanshi
49

kasa muryarshi tana rawa kamar yanda jikinshi
ma ya dauki rawa ya ce da kin barni kawai na
tafi na ce ba zan barka ba sai ka gaya min
gaskiyarka, a hankali ya ce min nesa nake so in
yi da Uwa tsoro nake ji kar in ce ina son....ya
kasa karasawa, nan take kuma ya shiga
shisshikar kuka saboda tsananin damuwar da ya
shiga, da sauri nace mishi ai bani na haifi Uwa
ba Muntaka, bani na haife ta ba, 'yar wan Alhaji
ce ai kana da damar cewa kana sonta, na zauna
na kwashe dukkan labarina tun daga kuruciyata
a gaban Babanmu har kawo ranar da nake bashi
labarin ban rage mishi komai ba.
Shi kenan tun daga nan sai ya saki jiki ya
koma al'amarinshi da Alhaji ya dawo kuma na
bashi labari, yayi matukar jin dadi ya ce ai shi
kenan sai kiyi tuwonki manki, na ce hakane.
Ana yin haka na shiga shirin buki amma sai
da naje Katagun na shaidawa yaya Balki in da ta
nuna min bacin ranta kan hakan da nayi bisa
cewar wai ba sai na gaya mata hukuncin da zan
zartar a kanta ba.
Ina dawowa na nemi izinin Alhaji na biyawa
yaya Balki da Uwa kujera kamar yanda dama
nasan Muntaka yana cikin mutanen da Alhaj1 ya
ce zasu tafi.
50

An dawo babu dadewa aka yi bikinsu, biki
na gata don babu abin da Alhaji bai yi musu ba
na gata nima nayi gayya har daga Senegal yan
uwa sun zo biki, taro ya tashi lafiya aka watse,
kowa ya koma gidanshi aka bar ango da amarya
dani kuma da na rinka ganin tamfar ni na fi
kowa jin dadin zamani na hada aure tsakanin
kanina uwa daya uba daya da 'yar da nake so
yar da na rike 'yar da nake ganin 'ya ce.
Auren Uwa da Muntaka ba karamin al'amari
ba ne a wurina, don sai da na rinka ganin tamfar
sune dangina gaba daya da nake ganin na rasa a
baya, na rinka jin tamfa r duk wani bakin ciki da
na gamu da shi a baya ya wuce, ya zama mun
tarihi.
Gidan su ya zame min wurin zuwa in naji
zani unguwa sai in cewa Alhaji zani gidan su
Uwa in dubo su wata rana ya ce min a gaishe su
wata rana kuma ya ce bai yarda ba, wai na fitini
yara da zirga-zirga a gida itama Uwa in taga
kwana biyu bata ganni ba zata shirya tazo wuni
in zata zo kuwa zata yiwo min girke-girke iri-iri
tazo min dashi, Uwa da Muntaka suka maida ni
'yar gata sai ji dani suke yi nima ma ji dasu
komai Alhaji ya shigo dashi gidan zan raba biyu
in dorawa Babangida ko Junaidu in ce maza kai
wa Uwa.
51

Ana nan a haka rannan muna hira da Alhaji
sai ya ce min, ni Zuwaira in nace ki bani dava
cikin 'ya'yanki in kaishi Turai yayi karatu wa za
ki ba ni? Na zuba mishi ido cikin kaduwa ina
kallonshi na ce ban fa wastsake daga kewar
rabuwa da Uwa ba shine har ka fara tunanin
sake raba ni da wani kuma? Ya ce to yaya zaki
yi ai dukansu ma kwashe su zanyi in kaisu ka
ratu ke dai mutum daya zan fitar daya zai yi ne
a nan a gida amma ba zan bar miki gidan babu
yara ba, zan kawo kanana in sa su suyi karatu
manya kuma su taya ni harkokin kasuwanci na
ce mishi to, na kuma yi mishi addu'a.
Kwana biyu ya bani inyi tunani don haka da
kwanakin biyu suka cika sai na gaya mishi akai
Babangida Turai shi kuwa Junaidu a barshi yayi
anan bai nemi sanin dalilina na fadin hakan ba
nima ban tsaya yi mishi dogon bayani ba tunda
naj ya ce to shi kenan sai nima nayi shiru.
Tun daga nan bai sake ce min komai ba nima
ban sake komawa kan maganar karatun nasu ba
don ha Son tafiyar tasu nake yi ba rannan kawai
sai Alhaji ya ce mun shirye-shiryen tafiyar
yaran nan sai ta kammala ina ganin tatiyar ta
matso, nayi maza na ce au a haka suna yan
kanana ne za'a tafi dasu, ai na dauka sai sun
girma tukuna? Gaskiya in dai yanzu ne na fasa a
52

bar mun su kawai sai sun kara hankali tukuna ya
ce min to.
Kwana hudu bayan nan daga fita sallar asuba
$ai kawai naga yara shiru basu dawo ba sai da
na gaji da jiran shigowarsu bayan na kammala
abin karyawa na ce aje a kira mun su su zo mu
karya sai kawai Alhaji yace mun ai an riga an
tafi dasu za'a kai Junaidu wata makaranta a
Akure shi kuwa Lamido za'a wuce dashi.
Ihu na rinkayi da iyakacin karfina yana bani
hakuri daga baya ma naga hakan ba zai mun ba
na kama hanya na nufi katagan naje na bude
dakin Baba da aka riga aka gyara tas na zauna a
ciki zuwan Alhaji biyu naki binshi na ce ya
barni anan kawai ai ya riga yasan ba zan iya
zaman gidan babu yaran ba yarbani dasu ba tare
da ya gaya min tafiyar tasu ba.
Satina biyu a Katagun in ban da bacin rai
babu abin da nake yi naja na tsaya kan lalle
Alhaji ya dawo mun dasu kafin in dawo ko
kuma ya bar nil in yi zamana anan. Rannan dai
ya sake zuwa na ce a na riga na ce ba zan koma
ba, ya ce ai na kawe wasu yaran nace to ina
ruwana dasu? Ni nawa nake so in gani.
Rannar dai yayan tudu yayi min fada irin
wanda aka dade ba ayi min ba abin da ya tuna
min da Baba nayi ta kuka a haka na biyo Alhaji
53

muka dawo gida na same shi cike da yara da ya
kawo gaba daya ya'yan yan uwa ne da na sani
nasan lokacin da aka haife su amma basu debe
min kewar Junaidu da Babangida ba, basu hana
ni kukan tafiyar su ba. Ban taba samun kaina
cikin kuiyan yin girkjin gida ba sai a wannan
lokacin duk abin da nayi niyyar girkawa in na
tuna Junaidu da Babangida ba za su ci ba sai
inga to wa zan girkawa akan dole Alhaji yasa
Hajiya Hauwa ta nemo mishi mai girki inda ta
kawo mishi wata daga baya kuma ta kawo mishi
mai gyada don ita mai gyada tafi wancan tsabta
da iya girki akan dole na bar wa mai gyada
girkin gidan saboda na kasa, kasala ta kamani
bani da wani aiki sai na tunanin yaran in kuwa
rufe ido nayi da sunan barci in yi ta mafarkinsu
a wannan lokacin kullum daga gidan Uwa ake
kawo min abincin dare kowane kwana biyu
kuma sai tazo gida wai tazo duba ni.
Ana cikin haka ne na gane Uwa ciki ne da ita
wai ban iya fadin farin cikina na hakura na
kwantar da hankalina na koma kan lissafin cikin
da Uwa ke dashi da kuma zumudin ganin abin
da zata haifa, Uwa ta kanma zazzabin laulayi,
kullum sai naje dubata in girka mata wannan in
girka mata wancan sai dai bata iva ci saboda
kurarrajin baki sun dame ta amma dai an samu
54

taji sauki sai dai kurarrajin kam sunki jin
magani, dole aka hakura aka barta sai dai
kullum zan dama mata kunun gyada na shinkafa
da na tsamiya in hada da kindirmon dana sa mai
nono tana kawo min in aike mata dashi shi ne ya
zamo mata abinci.
Duk da kurarrajin baki sun takurawa Uwa
basu hanata murmurewa tayi kyau tayi fari sol
ba duk da ita din ba fara sol ba ce, asalin kalar
jikinta yana tsakanin fari da baki ne, wato a inda
babu farare ita fara ce a inda kuwa suke da yawa
to ita baka ce, tayi matukar yin kwarjini don
kuwa dama doguwa ce sambal a mike take gata
da idanuwa dara-dara wadanda a wannan
lokacin suka kara fitowa suka kuma yi fari tas
bakin kuma ya kara baza ba mijin uwa ba da
yake matukar sonta yake ganin tanfar ita ce
komai dinshi, don kuwa na taba zuwa gidan na
gane Uwa tana kokarin boye min bacin ranta
dana koma gida na neme shi na nuna mishi
rashin jin dadi kan bata mata ran da yayi sai ya
sunkuyar da kanshi kasa ya ce min ita ce mafi
darajar abin da nake dashi, ita ce mafi soyuwar
abin da nake so amma hakan ba zai hana in tayi
kuskure in mata fada ba nace mishi haka ne
amma maimakon fada rinka yi mata nasiha da
abin da na raine ta bishi kenan zata bar duk wani
55

abin da baka so in ka gaya mata cikin natsuwa
ya ce mun to, to ba mijinta dake yi mata irin
wannan son ba ni da kaina bana gajiya da
kallonta.
A wannan lokacin duk wata hidima ta gidan
Muntaka ya dauke mata ita sbaoda zuwan da
nake yi in same shi yana aikace-aikacen gida
yasa na daina yin sammakon zuw agidan sai na
da' daici ya gama zai fita kasuwa ni kuma in
dani mata hira. Muntaka da kanshi ya gano
hikimar yi mata farfesun kanta yayi laushi
sannan yayi amfani da turmin karfe mai tsabta
ya dan daka shi don sauwake mata tauna
ganewau da nayi cewar uwa da Muntaka so mai
tsanani suke yiwa juna sai dadi ya kamani na
kara sonsu wani irin son da ba zai yiwu in iya
kwatantashi ba.
Ana cikin wannan hali ne rannan Alhaji ya
dawo dagga sallar Asuba naji shi yana kwalawa
daya daga cikin yaran da suke gidan kira, yana
fitowa bai ma saurari gaisuwar da yake yi mishi
ba ya ce mishi maza tafi ka dubo min Muntaka
me ya hana shi zuwa masallaci yau? Yaron ya
fita da gudu ni kuma na fito ina ce mishi ko sun
makarane? Ya ce to ban sani ba amma shi ba
mai makara bane ni dashi mukanyi rige-rigen
zuwan Masallacin ne watarana in riga shi wata
56
rana ya riga ni, muna tsaye a wurin har yaron ya
dawo ya nemi wuri ya tsuguna ya shaidawva
Alhaji bai jin dadi ne ciwon ciki na damunshi.
Da sauri Alhaji ya fita ni kuma na tsaya ina
fadin ikon Allah, yau kuma cikin nashi ya dan
motsa kenan, ganin da nayi Alhaji bai dawo ba
sai nayi zaton asibiti suka tafi gashi ya fita ban
tambaye shi ba balle in je can gidan don haka
Sia na tura maigyada na ce mata taje tazo min da
Uwa.
Isowarsu ne na gane Ciwon bana wasa ba ne
saboda ganin yanda Uwa ta rude in ban da kuka
babu abin da take yi na shiga rarrashinta ina
fadin haba Uwa, in mijinki yana ciwo sai kiyi ta
kuka haka? Tana kukan ta ce min ba kukan.ciwo
nake yi ba mu..bata karasa ba saboda ganin
da tayi na zuba mata ido ina kallonta kiyi hakuri
Umma kiyi hakuri ta koma kuka tana bani
hakuri, hankalina yayi matukar tashi na rasa
inda zanyi na surn gyalena na yafa na tasa Uwa a
gaba muka nufi asibitin don muga halin da suke
ciki muna isa. Alhaji n2 maibindiga muka fara
gani da sauri ya ce mun me ya fito dake? wa ya
ce miki ki zo nan? Maza koma kiyi hakuri muna
zuwa, muka dawo gida. Ba mu wani dade ba sai
gasu sun dawo sai gashi ana ta shigowa gida ana
diban butoci ina tsaye tsakar gida ina sauraron
57

Alhaji ya shigo ko wani wanda zai gaya min
abin da ke faruwa ji nake tamfar inyi wajen in
gananwa idona saboda tsananin bugun da
zuciyata keyi, a cikin tsayuwar sai ga Hajiya
Hauwa ta shigo kuka take yi sai ga Karama da
Maryam sai ga matan abokan Alhaji da
makwabta suna ta shigowa ashe wai Muntaka ya
rasu ne, a wannan lokacin bata kaina nake yi ba
saboda halin da Uwa take ciki suma take yi ana
shafa mata ruwa inta yi kamar ta farfado sai
kuma ta koma suman gata da ciki don haka
akayi maza aka nufi asibiti da ita aka kwantar da
ita ni kuma ina gida wai ina karbar gaisuwa
daga baya naga zama ba nawa ba ne nasa aka je
aka rokar min Alhaji ya barni inje asibiti wurin
Uwa don tunda akayi mutuwar ya ki shigowa
gida sai turowa yake yi wai a bani hakuri, bai
hana ni zuwa asibitin ba don haka can na tafi
naje wurin Uwa. Tsayuwa nayi na zama Jaruma
nayi ta rarrashi ina bada hakuri ina kuma tuna
mata da cewar mu din dukanmu zamanta muke
yi sai dai in wa'adi bai cika ba, in nayi ta
rarrashi sai kuma in koma kwadaitar da ita game
da rayuwar da mai lmani ke sa ran samu bayan
mutuwa, shi kuma imanin ba zai cika ba sai in
zaka karbi.kaddara a yanda tazo maka, don haka
kiyi hakuri saboda ki samu ladan musibar da ta
58


same ki da irin wannan ban bakin da irin
wadannan kalaman na samu Uwa ta dawo cikin
natsuwarta ta koma ambaton Ubangiji
maimakon tsananin tashin hankali na neme
sallama muka dawo gida.
Ranar da aka cika uku ne nayi sammako
tunda asuba na shiga wurin Alhaji tun bai fita
sallah ba yana kan sallaya yana addu'a na jira
shi ya shafa fatiha na gaishe shi nayi mishi
ta'aziya na tashi na fito na dawo cikin gida.
Alhaji ya karbi gaisuwa har tsawon kwana
bakwai saboda Jama'ar da ke ta zuwa mishi
ta'aziya.
Bayan an gama karbar gaisuwa ne aka barni
daga ni sai Uwa sai ko sauran mutanen gida.
A wannan lokacin ne na samu kaina cikin
wani irin tsanani ga dai zuciyata dake cike da
dacin mutuwar dan uwana da na rasa wanda
bani da kowa sai shi ban kuma same shi ba sai
bayan da na dandani azabar zama ni kadai, to na
same shi ina murna gashi kuma na rasa shi
rasawa na farat daya a lokacin da ban taba
tunanin hakan ba, da Muntaka ya danyi jinya
nema watakila da ban dandani azaba mai yawan
haka ba to gani kuma tashe da uwa mai ciki
wacce bata taba daina kukan mutuwar mijinta
ba, wacce ta kaurace wa cin abinci na zama bani

59

da aiki sai na rarrashi da ba da hakuri da nasiha
tare da yin wa'azi in na dan samu ta dan sake ta
dan soma zata yi magana yanzu ne zata soma
hirar Muntaka daga haka kuma sai ta kama
kuka, ni ba abin in ce zanyi mata yanda Alhaji
yayi min ba, baya yarda maganar mutuwar tashi
ta hada mu sai kawai ya mike ya fita a haka na
zauna da Uwa wacce renonta yafi na dan jariri
wahala, har cikinta ya kai wata takwas na shiga
nuna don ganin sun kusa rabuwa itama ta huta
watakila kuma in taga danta zata mai ya ce ta
hakura dor ganin ga dan Muntaka a hannunta.
A wannan lokacin tuni na gama shirin
baihuwarta komai na tanade shi sai jiran zuwan
haihuwar kawai nake yi itama ta danyi kuzari
har na soma zuwa makarantarmu tare da ita.
Rannan muna tsakar gida ni da ita zogale ta
ce min tana sha'awa na aika aka sayo min
danyenshi na gyara shi tsaf na dafa mata na
tsiyaye ruwan a wani kofi na gyara ganyen na
kwadanta mata shi yayi kyau yayi dadi na
dauko na kawo mata na ce gashi nan ga kuma
ruwanshi in kin kasa tauna ganyen sai ki
kwankwade ruwan don dama yafi ganye amfani
a jiki maigyada tana yi mana dariya tana fadin
Hajiya kenan na ce eh to in banda dai sha'awa
60

mai sama da wadannan kurarraji yaushe zai iya
cin ganye?
Uwa ta tasa ganyen nan tana kallo nima ban
tanka mata ba tunda dai ta yarda ta shanye
ruwan sai ta kalle ni tayi murmushinta a hankali
ta ce Umma ina son yi miki wata magana, ina
tsoron nayi maza na ce haba Uwa tsoro ya hana
ki gaya min magana, to wa za ki gayawa in ba ni
ba? Ta dan saki wani lallausan murmushi ta ce
kar hankalinki ya tashi ne nayi maza na ce mata
gaya min kawai ba zai tashi ba ta ce idonane
Umma bai gane kalan abu komai sai nake
ganinshi baki gashi kuma sai in rinka ganin
mutane suna rabuwa mun bibbiyu.
Yanke jiki nayi na fadi a kasa saboda
tsananin firgita da nayi da wannan bayani na
Uwa, ciccibata akayi aka kaini daki nayi kuka
rannan har na gaji ban daina ba, da Alhaji yazo
dubani don anje an gaya mishi abin da ya faru
na ce mishi aje a dauko ban boye mata komai ba
ban ki gaya mata abin da nake tsoro ba don ta
riga ta zama min 'yar uwa da na gama yi mata
bayani sai kawai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce
to kina ganin kamar in muka hadu a nan da wani
abin da zamu hana ne? Nayi maza nace mata
bamu isa komai ba taya ni zaman gidan zaki yi,
ta ce to shi kenan. Muka tasa Uwa a gaba ni
61

kam komai tayi idona yana kanta sai dai banga
wata alama ba.
Rannan muna kwance ni da ita a gado dama
kuma tare muke kwanciya ita kuwa yaya Balki
tana daya gadon sai naji tamfar Uwa tayi
magana na ce mata me kike fadi? Sai da nayi
mata tambayar sau biyu sai ta ce bada ke ba ne
nace da waye? Ta ce da wannan ne

Please Login or Register in order to submit comment