Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka
hanani fadin gaskiya ba, in ban da taje ta dauko
ubana yazo nan ya haife ni me zai hada ni da
ku? In ban da ta...kan in fadi abin da zan fada
din yayi wuf ya cukume ni yayi waje dani yana
fadin tunda kinyi hauka Rabi muje gida kiyi a
100

can ba a gaban Umma zakiyi wannan rashin
mutuncin ba.
Mun fito yana kokarin tura ni cikin motarshi
saboda tuburewar da nayi, ba zan bishi ba sai ga
Umma amarya ta fito daga wurinta tana ganin
mu tayi mishi tsawa, menene haka? Ya juyo
yana kallonta kan yayi magana ta sake cewa
menene haka? Wane irin rashin hankali ne
wannan? Cikin ladabi ya ce mata gida zan kaita
Umma wani abu ya sanme ta baki ji maganganun
da take gayawa Umma ba, ta ce mishi sake ta,
ya sake ni na tsuguna a kasa inä kuka, ta ce mun
tashi ki shiga ciki, nabi umarnin da ta bani ina
shiga ta biyo bayana bata bar ni na zauna ba ta
ce inje inyi wanka na fito na gyara jikina na
sanya wata doguwar riga da na samu ta ajiye
mun, na fito na same ta a falo tana zaune abin ka
ryawa ta fara bani nasha ruwan zafi don abin da
kawai naji zan 1ya sha kenan.
Ta zuba min ido tana kallona cikin natsuwa
ta ce min, "Al haji ne yake son mijinki yayi aure
laifin Hajiya guda daya ne da taja ta tsaya kan
1alle sai ya karbi wannan yarinyar da aka bashi,
ni da naso ne ta fita cikin maganar ta barshi ya
bijirewa wannan auren kamar yanda ya bijirewa
saura da aka bashi ya ki karba, in yaso daga
baya shi yaje ya nemarwa kanshi auren da

101
kanshi tunda ita wannan yarinyar ma da aka
bashi ai munafurci ne yasa aka yi hakan ina
dalilin da za ace Alhaji duniya abi sannu ne zai
bashi aure? Tun yaushe ne mu'amalla taja baya
tsakaninshi da Alhaji? Lokacin ne na san na
dago kai na kalli Umma amarya na ce Umma
'yar gidan Hajiya Hairan kenan zai aura? Ta ce
eh ita ce, nan da nan naji gumi yana feso min a
jikina, saboda ganewar da nayi cewar da hannun
Umma Karama cikin maganar auren don kuwa
bata da wata Aminiyar da ta wuce Hajiya
Hairan, haka nan saboda daukar zafi irin nata da
taya Umma Karama kishi da take yi ko magana
bata yi da Ummana, sai in Ummance ta gaishe
ta, to wai ita ce zata baiwa yaya Almu aure,
sannan ita Umma tana sane amma wai taja ta
tsaya kan sai lalle yaya Almu ya karbi wannan
auren cikin ladabi da natsuwa, na ce mata zan je
mu tafi Umma kar yayi ta jirana, ta ce to kuje
gida lafiya karki nemi wata magana ina
amfanin wannan abin da yayi miki? Gashi ya
kunbura miki gefen fuskarki babu kyan gani,
ban ce mata komai ba nayi mata sallama na fito
banga yaya Almu da motarshi ba, abin yayi min
dadi nayi maza na kama hanyar fita gidan, ina
fitowa sai gashi a bakin get yana zaune a bayan
motar yana ganina ya diro yazo ya bude kofar
102

motar ya ce min zo ki shiga kawai, girma da
arziki kin dai san nan kofar gida ne, kafin
Umma amarya ta kawo miki agaji kin riga kin ji
jiki, ban yi musun shiga ba saboda nasan
gaskiya ya fada.
Na shiga na zauna muka kama hanyar tafiya,
na ce mishi dama 'yar gidan Hajiya Hairan zaka
aura? Bai kallen ba ya ce eh menene? Na ce ban
yarda da auren ba ne tunda kai ma kasan
munafurci ne yasa aka baka ita, in ma kaga kana
Son yin auren ne to na yarda kaje ka auri wata
yarinyar amma ba ita ba, in dai har kana so in
kayi a zauna lafiya.
Sai da ya galla min dan banzan harara kafin
yaja wani irin uban tsaki ya ce in anyi ki hana
zama lafiya, sakarya mara hankali, mara kunya,
mara mutunci, wacce gata ya maida ita
shashasha, a gabana kika zagi Umma? har kina
ce mata wai kin bar min ita? Kin taba jin ance
miki takice? Sai da ya waiwayo ya kalle ni
sannan ya ce min wai me kika dauki kanki ne
ma tukuna? Ke kin dauka kin fini matsayi ne a
wurinta? In ba ki sani ba in gaya miki, ni danta
ne da ta shayar da nononta kinga kuwa tafi
karfin in barwa wani ita na kuma fi karfin ace
an bar min ita, dama tawa ce tare kika ganmu
tare kuma zaki barmu, da cikin girma da arziki
103

ne kika ce min in bar wannan yarinyar in nemi
wata da kinyi mamakin adalcin da nayi miki,
amma tunda kika gayawa uwata maganar banza
akan idona to sai nayi aurcn inga iyakar tsiyar
da kika iya.
Har muka isa gida ban daina kuka ba, ban
kuma cewa yaya Almu komai ba saboda ban
saba irin wadannan maganganun dashi ba, ban
saba gayawa mijina bakar magana ba, gashi dai
maganganu sai zuwa mun suke yi a zuciyata
wadanda zan gaya mishi in rama abin da yake
fada amma sanin da nayi in na fadi tawa
magan ar ba kwashewa kalau zanyi ba, zunubi za
a rubuta min tukuicin gayawa miji bakar
magana sai naja bakina nayi shiru, in na ga abin
yayi yawa dai na kan rama a zuci amma ba da
baki ba, tunda sai na furta da baki ne za a rubuta
min zunubin.
Muna isa gida na samu Baba Talatu tana
jiranmu don yaya Almu yayi mata bayani ina
shiga dakina ta biyo ni' tana fadin hakuri kawai
zaki yi uwardakina, ni tausayin Hajiya ne ma ya
fi kama ni nayi maza na ce mata tausayin
Umma? Jmma ai ita ce ta ce sai yaya Almu ya
karbi auren cikin tausayawa ta ce waiyo to yaya
za tayi? Zata hana shi aure ne? Wannan kishiya
indai kina da hankali ai bake za'a yiwa ita ba.
104

Hajiya Karama ce fa sanadin auren, sannan kice
dake ake yi? Dogon bayanin da Baba Talatu tayi
min shi ne ya fahimtar dani cewar lalle kishiyar
da ake nufin yi min din ba karamin al'amari take
nufi ba, sanin da Umma Karama tayi cewar ni1
din ba zan haihu ba shi yasa tayi kutun-kutun
din da Aminiyarta tasa mijinta ya fake da tsohon
zumuncin dake tsakaninshi da Baba ya ce ya
baiwa yaya Almu auren yarshi don ita tazo ta
haihu don itama ta samu wata dama akan yaya
Almu ta haka ne take ganin zata iya karbarwa
Umma shi.
Kishi mai tsanani ya kama ni da na tuna duk
sanadin wannan abin rashin haihuwata ne, na
tuna kalaman yaya Almu game da haihuwa na
tuna kafin ya debe tsammani daga gare ni irin
alkawuran da yake yi min daga ranar da kika yi
min albishir da daukewar wannan fitinanniyar
al'adar taki da duk wata sai tazo ta takura min
Rabi ni kuma zanyi miki albishir da farin cikin
da ba zai yanke miki ba, daya daga cikin
kalamanshi na wancan lokacin kenan. Ashe ba
ni ce zan yiwa yaya Almu wannan albishir din
ba, na daga ido na kalli Baba Talatu na ce mata,
zamana ne kawai yazo karshe ni da Yaya Almu,
komai kuma yana da sanadinshi, ina fadin haka
sai ta kama kuka tana rokona kar in yi haka,
105

dama abin da ake son gani kenan, na ce ba
komai Baba gara mun hakan ba zan iya zama da
yaya Almu ina gani wata mata tazo ta haifar
mishi 'ya'ya ni bani da ko daya ba, yau in da ina
da ko guda daya ne to da shi kenan sai in iya
fuskantar kowace irin kishiya ce zata zo min, to
amma bani da ko daya ba kuma zan haifa ba,
yaya zanyi? Baba Talatu tayi kuka har ta gaji.
Rannan ina zaune akan gadona cikin dare ina
rungume da filo akan cinyata na makalkale shi a
kirjina da hannayena duka biyu, tunani kawai
nake y1 in saka wannan in kwance 1n saka
wancan. Ina cikin wannan halin ne sai naga yaya
Almu ya turo ko far da ta hada mu ya shigo yana
sanye da doguwar jallabiya fara a jikinshi,
matsowa yayi ya karbe filon yayi jifa dashi ya
kuma sa hannu biyu ya sure ni ya nufi dakinshi
dani kan gadonshi ya aJiye ni ya kuma zauna a
gefena ya dora hannunshi kan cinyata yana
magana cikin natsuwa, kwanakin nan duka bana
bacci Rabi kar ki dauka ko ina jin dadin
abubuwan da suke faruwa ne, bana ji ni dake
bamu taba samun wani sabani ba a shekaru.
biyar din da muka yi in ban da wannan karon
ban gaya miki maganganun da na gava miki don
komai ba sai don ba zan iya hakuri dake akan
6atawa Umma ba, don haka kiyi hakuri ki kuma
106

yafe min marin da nayi miki. A hankali cikin
natsuwa na ce mishi na yafe ya ce to na gode, ya
canzawa hannunshi wuri don bukatarshi ta ci
gaba da sake taba ni, na ce mishi ka taba yi min
alkawarin ba zaka taba son kanka a kaina ba, ya
ce eh nayi ban manta ba, ba kuma zan saba ba,
na ce to na roke ka yanda kake kokarin samun
abin da kake so nima ka taimake ni in samu, ya
ce me kike so in taimake ki akai? Na ce ka
taimake ni kar ka sake taba ni ka kuma taimake
ni ka nuna min zumunci ta hanyar kin marawa
Umma da duk wani mutumin da zai nemi tilasta
ni zama da kai baya tilasta n1 zaman zai zamo
kuntatawa a gare ni na kuma san ba za ka so in
kuntata ba, cikin sanyin jiki ya ce min me kenan
kike nufi? Na ce abin da nake nufi kenan zan
tsaya kan maganata, da dama na taba gaya maka
in kuma aka nemı tilasta ni zaman to zan 1ya
daukar kowane irin matakı, to maimakon ay1
haka kuma gara ayi komai cikin zumunci da
mutuntawa juna rai. Bai sake ce min komai ba
har gari ya waye, sai dai daga ni har shi babu
wanda ya samu runtsawa.
Washe gari wurin taran safe naga wayar yaya
Junaidu wai baba yana son ganina, don haka
duk abin da nake ciki in bari inzo ni da yaya
Almu, na ce to naje nayi shirina nayi kwalliya
107

SOsai ta yanda zan boye duk wata damuwa dake
tare dani, don nasan zan samu Umma Karama a
can. Kwalliyar da na dade ban yi ba nayi, na
daura wani tsalelen leshi na kuma kawata
kwalliyar da adon gold na yane jikina da gyale
mahadin takalmina loeshoe da jakar da nake
rike da ita wadanda suka yi matukar kara wa
kwalliyar tawa kwarjini.
Ni da yaya Almu muka isa gidan kai tsaye
falon Baba muka wuce inda muka same shi shi
da Umma Karama da yaya Junaidu. Na sake
kallon Baba cikin ladabi na sake gaishe shi
sannan na ce mishi Baba ance kana son ganina,
ya ce eh uwata mijinki ne yayi waya ya gaya
min wata magana da yace wai a bakinki ta fito,
kin kuma ce mishi za ki tabbatar da cewar kin
tsaya akanta, shi ne nace bari in neme ki in ji
kina da matsala ne game da auren nashi da har
kike nema ki kawo mana wani sabani?
Na kalli Baba cikin natsuwa kamar in gaya
mishi abin da ke raina sai kuma na tuna ba a
gaban Umma Karama zan yi hakan ba, don haka
sai na ce bani da wata matsala Baba, Baba ya
dar. ji dadin hakan da na fada ya ce to maganar
da ya ce kin fada din fa? na ce baba wannan
tsakanina dashi ne bai yi tsananin da zai kawo ta
gabanka ba.
108


Baba yayi maza ya ce haka ne Uwata, na
kuma yarda da cewar ke ba za ki so kiyi abin da
zai tayar mana da hankali ni da Uwarki ba, don
haka komai zaki yi kiyi shi cikin fahimta da
sanin cewar babu wata mata da Lamido zai aura
ta kaiki balle ta wuce ki a wurinshi, ke matarshi
ce auren saurayi da budurwa, ke kanwarshi ce
da ku ka girma daki daya, sannan shi din kanin
mahaifiyarki ne, yanda kema ke da shi ku ka
girma gaban Zuwaira haka shi da uwarki suka
yi, bisa wadannan dalilai ne na kira ki in gaya
miki cewar zanyi bakin ciki in har kika yi abin
da Lamido ya cemin kina shirin yi ina kuma so
in kara jaddada miki cewar girman Zuwaira a
wurina yana da yawa, don kuwa babana bai bar
min wasiya kan komai ba sai kan abu biyu, na
farko in rike zumunci na biyu kuwa in rike
mishi amanar Zuwaira, kar kiyi abin da zai
kawo matsala tsakanina da ita tunda kin san tana
sonki."
Na sunkuyar da kaina kasa na ce Baba tana
Son yaya Almu fiye dani....da sauri yaya
Junaidu ya katse ni ta hanyar daka min tsawa, ke
Adawi yya! dakata kai Junaidu, shima Baba ya
dakatar dashi kyale uwata tayi min magana
gaya min menene damuwa rki? Me Zuwaira tayi
da ya nuna miki cewar tana yiwa wani irin son

109

da take yi miki? Kin san su wanene suka haife
ki? Kin san matsayinsu a wurin Zuwairah? Kin
san Uwa? Kin san yanda take a gaban Zuwaira?
Kin san Abdulhakam? Ko kinsan Zuwaira bata
taba mu'amalla da wani nata ba sai a kanshi? Ko
kin san har yau din nan shekaru kusan ashirin da
rasuwarshi ni da ita ban taba yarda hirarshi ta
hada mu ba? Kina nufin amincewar da tayi na
Lamido yayi aure fifitashi tayi a kanki? Adalci
ne kawai irin nata da irin wannan adalcin nata
ne kuma dama ta zarcewa sauran 1mata ita babu
son zuciya a cikin al'amarinta yanda kike 'ya
haka Lamido yake haka Junaidu dukanku
ya'yanta ne dukanku kuna bukatar tayi muku
adalci amma tunda har maganar tazo gabana to
gaya min abin da kike so ni inyi, na daga ido
cikin natsuwa nace mishi, bani da wata bukata
baba bani da damuwa kan maganar auren nashi.
Baba ya ji dadin zancen nawa, ya ce yauwa
Uwata maza kiyi koyi da halin uwarki ki zama
jaruma mai yiwa kishiya adalci, ba don ita ba sai
don mijinki cewar da zuwaira tayi Lamizo ya
karbi auren da aka bashi tayi hakan ne don ta-
mutuntani ni uban 'ya'ya mata ne kin sani akan
idonki nasha bayar da uarensu ba tare da na
tuntubi wadanda zan baiwa din ba, in na
zubawa mijinki ido kowacce aka bashi ya ce
110

baya so saboda gudun bacin ranki, uwata in
nima akayi min haka na bada kannenki aka
dawo mun da su aka ce ba a so ba za ki taya ni
bakin ciki ba? Na ce zan tayaka baba, ya ce
tunda kuwa haka ne ai muma bai dace muyi ta
maida na wasu ba ko kuwa na ce haka ne.
Tsawon lokaci Baba yana yi min kalamai na
kwantar da hankali zuwa can sai ya ce min
yanzu me zaki gaya min da zai kwantar min da
hankali in san ba za ki yi abin da zai batawa
Zuwaira ba, na kara sakin fuskata nace zan
karbi auren yaya Almu da hannu bibbiyu baba
zan kuma yiwa matar da zai aura irin abin da
Umma tayi wa nata kishiyoyin. Da sauri Baba
ya shiga sanya min albarka, ya kalli yaya
Junaidu yace mishi kai Junaidu a gabanka nace
na danka al'amarin auren Lamido a hannun
uwata taje ta shirya duk wani abin da tasan ana
yi tun daga kayan zane har na aure ta aike dashi
sai ka shirya bata kudin hidimar da zata yi duk
abin da ta nema a bata, yaya Junaidu ya ce to
Baba, ya sake waiwayowa wurina ya ce min
Iwata kije ki shirya duk wani abin da ya dace in
zaki yi kuma kar ki kalli Lamido ni za ki duba.
Na ce to Baba, ya sallame mu muka tashi
muka fita na bar Umma Karama a zaune rai a
bace, ga dukkan alamu ba abin da taso ji ba
111

kenan, ina fitowa wurin Umma na na shiga na
nemi wuri na zauna ina kallon hotonmu dake
dakin ni da ita ne tun ban fi shekaru goma ba,
cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ya dai
tabbata kenan yaya Almu zai yi aure tunda har
gashi baba da kanshi ya danka al'amarin bukin a
hannuna, ina cikin haka sai ga Yaya Almu ya
shigo, nan zamu kwana ne ko gida zamu tafi?
Na kalle shi cikin natsuwa na ce wanne yafi1
maka daidai? ya ce duk inda kika zaba duk daya
ne Rabi, illa iyaka dai ina so ki zabar mana inda
za mu fi sakewa tunda ni ban saba irin wannan
abin da kike yi min ba, ban saba kina yi min
rowar jikinki ba ki daina kinji Rabi? Ki bar ni
inyi yanda na saba yi dake aike tawa ce Rabi kin
kuma sha gaya min cewar komai naki nawa ne
ke din mallakina ne har abada kuma ni kadai ne
zan mallake ki, na daga ido kawai na kalli yaya
Almu wani sabon kishin ya sake mamaye
zuciyata, sai dai ban ce mishi komai ba har na
kammala duk wani abin da zanyi nazo na hau
gadon Umma na kwanta da shirin yin bacci sai
gashi shima ya shigo gadon nata yazo zai hau,
nayi maza na kalle shi na ce mishi gadon
Umman zaka hau? Ya ce menene? Gadon uwata
ne tunda kika hau ai nima kin san zan hau tunda
Kin san na gaya miki wurin da zamu sake zaki
112

kai mu, na sake kallonshi a natse nace mishi wai
me kake nufi da sakewa ne? Ni fa ina nan akan
maganata ba kuma zan canza ba, cikin kaduwa
ya zuba min ido yana kallona, maganganun da
kika yi a gaban Baba fa Rabi? Kina nufin
yaudararshi kika yi? Kina nufin ba za kiyi mishi
alfarmar da ya nema a wurinki ba na ki barshi
ya zauna lafiya da matarshi?
Na daga ido na kalli yaya Almu na ce mishi
nike rike da aurensu? Kafin namu auren ai nasu
ya shekara arba'in suna yinshi kar kuma ka sake
kai karata gaban Baba in kuwa ka sake yin
hakan to zan tabbatar da cewar baka sake ganina
ba nayi shiru na juya nayi kwanciyata.
A haka muka dawo gida ni da yaya Almu
abin babu dadi sai dai kuma bai bari wani-ya
gane hakan ba balle aje ga kanwa gaban Baba,
ni dashi dai abin ya ki dadi babu irin rarrashin
da banyi min ba naki in sauko to ki bari mana
sai anyi auren kinga anyi miki ba daidai ba in
yaso duk matakin da zaki dauka sai ki dauka
maimakon kice daurin auren kawai yana nufin
naki auren ya kare, ina alkawuran da muka
tayiwa juna Rabi? Kina nufin don kana son
matarka ta gida sai hakan ya hana ka karo wata?
Shi nanmiji fa mijin mata hudu ne an halatta
mishi yin hakan sai wanda yasan ba zai ya
113
adalci ba ne aka ce mishi ya zauna da guda
daya, ni kuwa ai ba mara adalci ba ne balle ko
kice kan haka ban cancanci zama da mata biyu
ba, ban tanka mishi ba shiru kawai nayi yayi ya
gama yaja bakinshi yayi shiru.
Kwana biyu bayan wannan maganar ina
zaune a falona wajen karfe goma na safe tunda
gari ya waye ban leka wurin yaya Almu ba balle
inyi tunanin abin da zan shirya mishi don
karyawa, zuwan Baba Talatu biyu tana
tambayata ko za'a dama kunun gyada ne tunda
taga yana so na ce mata a'a kyale shi kawai yana
azumi ta ce to ta juya ta tafi ta kama aikinta, ina
nan wurin a zaune cikin kwalliya sai dai kuma
kwalliyar ce kawai amma can cikin zuciyata
abin babau dadi, ina cikin tunanin abin da zai
faru tsakanina da yaya Almu matukar bai je ya
ce ya janye daga wannan auren na gulma da
munafurci da ake shirin kullawa ba, sai kawai
naga Hajiya Hauwa ta shigo cikin gidan babu
wata wadatacciyar sallama ta kuma sha kwalliya
cikin wata tsaleliyar atamfa da ta yiwa kanta
wani irin dauri mai kama da rawani ta kuma
turo shi gaban goshinta. Cikin zuciyata na ce kai
Allah kadai yasan irin kwalliyar da Hajiya tayi
sanda take cikin kuruciyarta, kas din da naji ya
fito daga bakin Hajiya ne yasa na gane cingam

114

take taunawa, nan da nan na shiga taitayina don
kuwa na santa kamar yanda na san yunwar
cikina, cikin sanyin jiki na ce mata sannu da
2uwa Umma, yaushe ki ka dawo?
Ta zuba min ido tana kallona, ta ce ran
Uwarki kinjini ko baki jini ba? Ungo nan, ta sake
miko min dakuwa da hannayenta duka biyu tare
da fadin ja'ira mara kunya marà hankali, mara
wayo, sakarya wacce bata san ciwon kanta ba,
haka kawai Zuwairah ta kyale ki kina shashanci
tana kallonki tana nema ta barki sai kin ja mana
abin kunya a gari, in baki bar gidan Mustapha
ba yau to baki haifu da kyau ba, tana fadin haka
naga ta yaye safcecen gyalenta ta ajiye ta cire
dan kwalinta data bata lokaci wajen nadewa ta
ajiye, gashin kanta ya bayyana wanda yasha
gyara cikin tsabta duk da furfura ta ratsashi. Ina
cikin kallon wannan abin mamaki da ya soma
tsoratani sai kawai naga Umma ta kama rigarta
zata tubbe ni kam nan take na fashe da kuka
yayin da ita kuma baba Talatu ta shiga bata
hakuri kiyi hakuri Hajiya, kiyi hakuri taja ta
tsaya tana kallon Baba Talatu cikin huci barni
kawai in tube Talatu a gaban yarinyar nan yau
don ta nuna min tabon da kishiya tayi min a
jikina, wanda take tsoron ita kar tazo tayi mata
shi, Baba Talatu ta shiga bada hakuri da ban
115

baki kala-kala da kyar ta samu Umma ta hakura
da tubewan ta maida rigarta har taja gyalenta ta
rufo ko' ina a jikinta ta gyara zama ta kalle ni ta
ce min tunda kika san Zuwairah a rayuwarta kin
taba saninta ita kadai a wurin mijinta? Nayi
maza na ce mata a'a, ta ce ni anawa gidan mu
nawa ne? Na ce ku hudu, ta sake kallona a
saninki guda nawa aka yi min? Na ce ban sani
ba Umma, ta ce to goma sha uku goma sun tafi
mna tare da uku kin taba zuwa gidan kin samu
wals a zaune a kaina? Na ce mata a'a, ta ce to
yan uwanki da akayi musu kishiyoyi kin taba
jin snyi wata magana? Kin taba jin wata
magar.a ta fito bakinsu? Na girgiza kaina cikin
zuciyaia kuwa ina tuna gaba daya ya'yanta mata
amare ne da su, na ce kin taba jin su suna irin
sakarcin da kike yi? Na ce a'a kan in gama rufe
bakina sai kawai tayi caraf ta rike min shi da
iyakacio karfinta tana fadin sai naki bakin ne
baya iya yin shiru saboda ba a farsa miki shi da
kyau ba? Na shiga fadin uh'un cikin zafi da
kokarin kwatar kaina daga hannunta sai dai na
kasa sa'boda irin rikon da tayiwa bakin nawa
B.ba Talatu ta sake shiga wani sabon ban
bakin da ba da hakuri, ita kuwa Umma ko a
jikinta sai fadi take yi bárni da ita kawai Talatu
ai wannan laifin na Zuwaira ne data zuba mata
116

ido tana yin abin da taga dama bata sanar dani
ba, ai da tuni nayi maganin rashin hankalinta, da
kyar na samu ta sake ni a dalilin jinin da taga
yana bin yan yatsunta ina ganin haka na kama
kuka, ita kuwa ko a jikinta, sai fadi take yi
Lailatu zaki barwa mijinki? Karama da
Aininiyarta sunyi nasara kenan akan Zuwairah?
Baba Talatu tayi maza ta ce ai fa kam nima abin
da ya fi kona min rai kenan, Umma ta ce barta
kawai ai mun gamu da ita jiya a wurin wani
buki muka gaisa ta ce min ashe kuma Lamido
biki yazo? Na ce mata ch, ai kinyi Rokari da
kika yi hakan gara ke da Zuwairah ku sake
haduwa a gidan Mustapha don wannan kishin
naku na gidan Alhaji Bello ya tsufa gara ku sake
sabunta shi.
Nayi maza na katsc kukan da nake yi saboda
umarnin da Umma ta bani na in hanzarta kawo
mata abin karyawa sai dai Baba Talatu bata bari
nayi hakan ba, ta karbe ni ta hanyar shiga kicin
don ta shirya mata, tana baria dakin ta sake
kallona ta ce min duk abin da kuke ciki ke da
mijinki ya gaya min, ina so kici gaba da yin
hakan ba zan ce miki ki daina ba, in kinga dama
ki shirya kayan aure ki jagoranci hidimar da
za'ayi don ki mutunta kanki kamar yanda Alhaji
Bello ya mutunta ki ya danka lamarin a

117

sannunki in kuwa ba ki ga dama ba ki bari biki
sai za'a yi shi don Zuwairah ta tabbatar mun da
cewar zata tsaya wajen ganin Lamido yayi
wannan auren don tana son ganin Karama tavi
amfani da Lailatun wajen samun abin da take
nema wurin Lamido ko ubanshi, ita kam
Zuwairah ai bata da matsala, jaruma ce bata taba
sai wa makiyi damar da yayi mata dariya ba, sai
dai in ke kika ja mata hakan.
Yaya Almu yayi sallama ya shigo ya nemi
wuri ya zauna a kasa yana gaisheta cikin
girmamawa, ita kuwa sai ta amsa mishi cikin
natsuwa da sakin fuska da suka gama gaisawa
sai ya sake rage murya ya ce mata Umma na
kasa yin shiru ne kan abin da Rabi take yi min
saboda bana son azo a same mu a haka, ta ce eh
to in ta gane abin da ake nufi ta gyara ai shi
kenan in kuwa bata gyara ba ba kowa ta
wulakanta ba sai iyayenku, in kuwa bamu da
mutunci a wurinta ai sai kawai ka zuba mata
ko.
Rannan da daddare yaya Almu yana dakina
dan dole na sallama mishi komai nawa yayi
yanda yaso dani, kasancewar kuma na janye
wunina daga gare shi na tsawon lokaci hakan ya
jawo al'amari mai tsanani a tsakaninmu ina
kwance daga gefe ina kallon shi yayin da shi
118

kuma yake ta bacci saboda tsananin gajiya, kishi
mai tsanani ya sake mamaye zuciyata yaya
zanyi in yi hakurin mallakar yaya Almu tare da
wata mace? Yaya zanyi in iya zuba mishi ido
yana yi mata irin abubuwan da na san yana yi
min in mun kebe? Lokaci mai tsawo ina cikin
wannan tunanin kafin lokacin da zuciyatata
tabbatar min da cewar dole ne in koyi
jarumtakar kaina don ba zai yiwu in barwa
Lailatu yaya Almu ba tunda hakan yana nufin
Umma Karama tayi nasara

Please Login or Register in order to submit comment