Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ke kadai ce ba ki da komai
Rabi in ba ki sani ba in gaya miki, a hankali na
ce mishi in mana sani amma yaya zanyi laifina
ne? Na soma yi mishi kuka, yayi maza ya soma
rarrashina ba laifin ki bane Rabi nima na sani yi
hakuri kiyi hakuri kiyi shiru amma ina so ki
fahimci cewar ba amarcine muhimman abu a
wurinmu ba, muhimman abu shiine mu samu
haihuwa kema kin san Umma da Baba suna
Bukatar ganin' danmu kema kin sani sarai cewár
babu wani da da zai debe musu kewar son ganin
wanda zamu haifan musu don haka ina rokonki
in akwai wani abin da kike yi ki daina don ina
yawan jinki kina ambaton amarci nayi miki
alkawarin daga ranar da kika tabbatar mini da
abin da nake fatan gani a tare dake zan shigar
dake cikin amarcin da baki taba sanin shi ba, a
hankali cikin sanyin jiki na ce mishi bana yin
komai yaya ya kara jawo ni jikinshi yana fadin
na yarda Rabi na yarda ba za kiyi abin da zai
cutar damu ba, don haka daga yau mu shiga yin
addu'a kinji ko? Na ce mishi to.
Tun daga wannan ranar yaya Almu ya dora
min karanta suratul Maryam, kullum bayan
kowace sallah ta asubahi, shi kuwa dama
ma' abucin karatun Alkur'ani ne. Muna gaf da
81
cika wata tara cif da yin aurenmu sai kawai
akayi waya aka ce wai Anti Aina'u ta haihu, an
samu da namiji, tafdijam na kalli yaya Almu na
ce mishi ba mu ma fa cika wata taran ba saura
kwana goma, ya daure fuska ya ce to sai me
Ance miki dole ne sai kowa ya kai wata tara
daidai? Ko kuwa a lissafinki ne ba a cika wata
tara ba awatan kalanda mu anamu lissafin an
kai, naja bakina nayi shiru saboda ganin
canzawar fuskarshi.
Mun dawo daga sunan Anti Aina'u da kwana
biyu, Anti Kubra ta haifi 'ya mace, kwana uku
bayan nan sai ga waya daga Legos cewar Anti
Rahma ma ta haihu kuma da namiji aka samu,
cikin daren muka isa Legos saboda bamu iya
hakurin bari sai gari yawaye ba.
Hankalina bai tashi ba na samu kaina cikin
tsananin damuwa sai da naga mun shiga wurin
Umma don yi mata barka, maimakon tayi
murnar ganinmu ni da yaya Almu kamar yanda
ta saba yi wai sai kawai ta fashe da kuka, kuka
kuma mai tsanani, jikina yana rawa na durkusa a
gaban Umma na ce mata Umma don ban haihu
ba ne kike kuka'? Umma ai zan haihu zan
haifanwa yaya Almu da wanda za ki rike ki rene
shi kiyi mishi riko irin wanda kika yi min,
Umma me yasa zaki yi min haka? Ina fadin
82

hakan nima na soma yi mata kuka bama irin
wanda take yi ba saboda zuciyata ta soma
karaya.
Yaya Almu yayi ta baiwa Umma hakuri
wacce ganin kukan da nake yi yasa ta hakura da
nata kukan tayi shiru, shi kuma yaya Almu sai
ce mun yake yi ke kin yi magana mai dadi kin
zo kuma kina kuka, yi hakuri kiyi shiru Rabi,
nima zuciyata tana gaya min cewar za ki haihu,
Rabi za ki haihu ya'ya masu yawa ma ba daya
ko biyu ba.
Hankalina bai kara tashi ba sai da na ga Anti
Rahma da danta a gadon asibiti suna kwance
abin gwanin sha'awa, danta gabjeje mai kyau
dashi. Nasa hannu na karbi yaron na mikawa
yaya Almu hannu biyu yasa ya karbe shi yayi ta
karanto mishi addu'o'i yana tofa mishi cikin
farin ciki da murna saboda yaya Junaidu baya
nan yana waje sai kawai muka tsaya akayi
sallama muka dauko Anti Rahma da danta muka
kawo su gidan Baba don umarnin da Umma ta
bayar kenan na a kawo mata ita tayi jego a nan.
Daga nan na wuce sunan Anti Kubra da aka
gama komai kuma na sake komawa Legos na
Jira sunan Anti Rahma inda muka samu Aliyu
wato sunan Baban Umma, bayan dawowarmu
daga sunan Baban Umma kamar yanda na ji
83

kowa yana kiranshi ko sati biyu bamu yi ba
muka nufi birnin Cairo don ganin wani Likita da
Baba ya tura mu wurinshi, tun daga wannan
lokaci muka tsunduma cikin maganar neman
haihuwa yau muna nan gobe muna can shiru
babu ciki babu dalilinshi ko batan wata ban taba
ba balle akai gayin 6ari, ana nan a haka daga
baya sai yaya Almu ya soma nokewa tafiye-
tafiyen asibiti da na same shi nayi mish1 magana
kan sabon halin nashi sai ya ce min mu nemi
haihuwar kawai wurin mai ita Rabi na gaji da
wadannan tafiye-tafiyen ni ban natsu na maida
hankalina kan cikina ba ke ba ki zauna a dakinki
kin huta ba, yanzu Junaidu da yake da 'ya'ya
biyu a gidan shi asibitin ina yaje aka duba shi?
Inda Likita na bada haihuwa ai da mun samu.
Gashi dai gaskIya ya gaya min amma ban ji
dadin gaskiyar ba, saboda zuciyata a yanzu babu
abin da take so irin in ganni da da in ga dai na
haifarwa yaya Almu da Umma da inga dai irin
son da zasu nuna mishi a duniyar nan,
tubburewar da yaya Almu yayi kan cewar shi
kam ya gama zama a gaban Likita don rashin
haihuwa ba wata lalura ta rashin lafiya ba ana
mishi gwaje-gwajen da suka kamata dama
wadanda basu kamata ba, na kawo wannan
kawo wancan, yasa na nufi Legos Wurin Baba
84

don kai kara Umma na ce na samu a car ban
kuma samu fadin abin da ya kai ni ba saboda
rikicin da na samu anayi a gaban Baban, yaya
Junaidu da Anti Rahma ne suka samu sabanin
da yayi dalilin da yayi mata duka irin wanda ban
taba tsammanin mutum mai hali irin nashi zai
iya yin hakan ba.
Ummana na samu a durkushe tana goye da
Zuwairiya yar da Anti Rahma take goyo, tana
kuka ga kuma yaya Junaidu can gefe a takure ya
sunkuyar da kanshi kasa itama Rahman tana ciki
kallo daya nayi mata na shiga taya Umma kukan
da take yi saboda zaluntar ta da Yaya Junaidu
yayi zagewa yayi da iyakacin karfinshi ya nada
mata dukan tsiya, ban iya zama a wurinta ba
saboda tausayinta na tashi na tafi wurin Umma
na zauna ina jliran fitowarsu sai zuwa can sai ga
Umma tana tashe da Anti Rahma sun shigo har
lokacin Anti Rahma bata daina kuka ba itama
Umma bata daina yi mata fada ba. Yau indaa
haka kawai Junaidu yayi miki wannan zaluncin
da kinyi mamakin abin da ya same shi, to amma
akan me akan me zaki yi abin da kika yin?
Rinka haihuwar su kina kawo mun su Rahma ni
zan rike ba zan gaji da su ba, ai ni na rike
ubansu Umma tana fadin ta soma kuka, a gigice
na shiga tambayarta me ya faru ne Umma? Bata
85


tanka min ba ta tashi tana cewa tashi ki bishi ku
tafi zan rike ta tare da dan uwanta in kin haifi na
cikin kima zan karbe shi ki zauna kar ki wahala
tana barin dakin na kalli Anti Rahma na ce wani
cikin ne dake Anti Rahma? Ta gyada kai cikin
takaici ni ke nan kullum ciki shi ne daga naje
don a cire min munafukin Likita yayi waya ya
tambaye shi shine yayi min wannan wulakancin,
kuma zanga.....ban barta ta karasa ba nayi maza
na mike ina kallonta, na ce mata kije ki cire Anti
Rahma kije kiyi abin da kika ga dama, ni in yi
kuka don ban samu ba ke kiyi kuka don kin
samu sun ishe ki saboda butulci, saboda rashin
adalci irin naki, kuma wai har kina kawo
maganar gaban Umma na kin mance matsayin
'ya'yan yaya Junaidu a wurinta kin manta da
cewar yaya Almu bai samu ya haifan mata ko
guda daya ba, mun gode. Na yi maza na fice na
bar mata dakin ban nemi kowa ba na bar gidan
kawai na dawo gida cikin zuciyata ina mamakin
butulci irin na mutane.
A gida ban yiwa yaya Almu tadin ba
musamman ma da yake na same shi yana fushin
na fita gida ba tare da na nemi izininshi ba, don
haka sai kawai muka ci gaba da zamanmu a
haka sai dai kuma kwana daya ne kawai da
dawowana sai ga yaya Junaidu ya biyo ni, ina
86

daki sai yaya Almu ya shigo fuskarshi a daure
ki zo ga Junaidu yazo yana son ganinki, na ce to
na tashi na dauki hijabina na sanya na nufi falon
nashi nayi sallama yaya Almu ya amsa na shiga
na nemi wuri na zauna a kasa, bayan na gabatar
mishi da abinci da na sha ya gama amsa
gaisuwar da nayi mishi sannan sai ya ce mun
jiya sai kika taho ba kiyi sallama da kowa ba har
da Baba me yasa kika yi haka? Na ce kayi
hakuri kawu nayi kuskure hankalina ne ya tashi
naje gida don in kai karar yaya Almu ya ki
yarda muje asibiti kan mas'alar mu sai kuma
naje na samu maganar ku shi yasa na hakura na
dawo. Yaya Junaidu ya kalli yaya Almu ya ce
yaya Mustapha akwai wani abu ne? Yaya Almu
ya ce a'a ni dai ayuka sunyi min yawa ne kawai,
ya ce to ko zaka ba da izini a shirya mata tafiyar
ita taje? Ya ce eh to babu laifi amma a hada ta
da wani, yaya Junaidu ya ce Umma Amarya zata
ganin Likita ai sai su tafi tare ya ce ba laifi.
Wannan tafiyar da muka yi da Umma
amarya muka je asibiti ita ce ta baiyanar da
asirin da yaya Almu ya dade yana boyewa, don
kuwa a wannan tafiyar ne na samu damar da na
karbi sakamakon Likita da hannuna.

87

Ina zaune gaban Ummana ni da ita kuka
muke yi yaya Almu ya shigo ya same mu
saboda kiran da Umman tayi mishi.
Cikin natsuwa ya tambaye ta ko lafiya? Ta
mika mishi takardun da nazo dasu ya gamna
dubawa ya mayar a hankali ya ajiye ya ce ni ban
yarda da wannan gwajin ba, Umma ban yarda da
su ba in na samu sarari zan sake kaita ayi mana
dukannmu, don haka ki kwantar da hankalinki
kar ki samu damuwa, yayi ta rarrashin Umma
har sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya
tasa ni a gaba muka dawo gida.
Muna isowa ya balbale ni da fada ba tare da
ya ji tausayin abin da nazo dashi ba, dama
bukatar ki kenan kije asibiti ki zowa Umma da
labarin da zai bakanta mata zuciya? Kina
tsammanin tana da wani karfin da zata iya
daukan wani bakin ciki daga gare ki? Abin da ta
gani a rayuwar ta ya ishe ta kar ki sake binciko
wani mummunan labari kije ki gaya mata, ki
rike abinki a cikinki, kema ko ya zama jaruma
kina rike damuwarki ba sai kin maida ita ta
zama damuwar kowa ba.
Mamakin tashin hankalin yaya Almu naji da
ko in kula kan sakamakon LIkita dana zo dashi
na cewar ba zan haihu ba amma sai na hadiye na
daure na ce mishi amma yaya za'ayi in iya
88


hadiye wannan maganar ban gayawa Umma ba?
Ya ce eh saboda ba kya tausayinta shi yasa ba za
ki iya hadiye wa ba da kika dawo ai ni ya
kamata ki fara gayawa ruwana ne 1n ce to mu
gayawa su Umma da Baba ruwana ne kuma in
ce to mu barwa cikinmu. Wannan test din naki
ni ban shekara hudu da samunshi ba? Tun zuwa
asibitin farko da muka yi aka gaya kin ga na
gaya miki? Saboda kar in tayar miki da hankali,
yana mikewa yaje ya kwaso takardun ya watsa
min su ya ce kin ki yarda ne da baki je kika jiwo
ba balle kije kina fada.
Tattara takardun nayi na rungume su a
kirjina ina wani irin matsanancin kuka ina fadin
shi kenan shi kenan ni ba zan haifar maka dan
da Umma zata dauke shi ba.
Yaya Almu ya durkusa da gwiwowinshi biyu
a gabana ya ce ban taba yarda da hakan ba Rabi,
shi yasa na ce miki mu nemi haihuwar kawaai
wurin mai bayarwa ban kuma fidda ran zai
bamu ba kiyi hakurin fadan da nayi miki ki bar
kukan da kike yi, amma ina so ne ki sani cewar
ni dake ba zai yiwu mu zama sanadin bacin ran
Umma ba don haka kar ki sake kai mata wani
labari da zai tayar mata da hankali na ce mishi
to.

89
An dauki lokaci mai tsawo yaya Almu yana
rarrashina kafin na dawo cikin natsuwa ta
hankalina ya dan kwanta saboda irin kalaman da
yake yi min wai kenan ance miki dole sai an
haihu ne ake farin ciki? Ba ki san wasu suna
nadamar haihuwar da suka yi ba? Ai ita rayuwaa
gamsuwa ne kawai Rabi in ka yarda ka gamsu
da ni'imar da akayi maka kayi godiya kan hakan
sai a baka kwanciyar hankalin da kake bukata,
kina sona ina sonki hakan bai ishe mu godiya
ba? Kullum irin kalamanshi kenan har dai na
dan hakura, na tasa al'amarin mijina a gabana,
na maida tattalinshi shine farin cikin rayuwata,
kowane lokaci cikin shirya mishi nau'o'in abinci
iri-iri nake a kowane lokaci kuma in dai yana
gida to ina manne dashi in ma tafiya zai yi to
mafi yawancin tafiye-tafiyen nashi tare muke yi.
Mun bar hirar haihuwar da maganar nemanta sai
dai kuma kullum a cikin yin addu'a muke ko na
ce ni na gaji zan huta sai ya ce baki da hankali
Rabi, kin taba ganin wanda ya gaji da rokon
alheri wurin mai bayarwa? In ce a'a ya ce to kiyi
ta addu'a ki kuma yawaita istigafari in ce mishi
to.
Abu daya dai da yafi damuna shine na rage
zuwa wurin Umfa na sai dai na kanyi mata aike
akai-akai, saboda na gane ganina yana tayar
90

Tmata da hankali mafi yawancin lokaci in ina tare
da ita ba ma rabuwa sai tayi kuka ko ni kuwa
cikin zuciyata mafi yawancin damuwata kan
rashin haihuwar tawa saboda Umma ne in ga dai
ta rike da a hannunta ace ni na haifan mata shi
mana wannan shine abin da yafi muntsinina
amma in don ta yaya almu ne ya hakura, ya
shanye ya boye ya, ya barwa cikinshi in ma
yana da damuwa to ban sani ba a zahirin abin da
ya nuna min shi ne nice komai dinshi, nice farin
cikinshi da kwanciyar hankalmshi ni kadai
kuma na isa in cike mishi kowane irin gurbi na
abin da ya rasa.
Aurenmu ya cika shekaru biyar banyi niyyar
tunawa yaya Almu da zagayowar ranar ba don
hakan yana nufin tuna mishi da dadewar mu ne
babu da, don haka naja bakina nayi shiru sai dai
na shirya yi mishi abinci mai dadi don in kara
mishi farin cikinshi Pasta mould na shirya
mishi.
ABUBUWAN BUKATA:
1. Shinkafa ne ko taliya, sai nayi amfani da
shinkafa saboda sanin shi Yaya Almu ba
ma'abucin cin taliya ba ne sosai.
2. Kayan kamshi
3. Mangyada

91
4. NikaRken nama
5. Tumatur
6. Alaiyaho
7. Maggi
8. Butter
9. Albasa
Na tafasa shinkafa, ta dan fara dahuwa kadan
sannan na juye ta na tsantsameta na barta tasha
iska kafin na soyata a cikin Butter. Nasa a abin
da zai iya zama a oven na ajiye a gefe.
Na kawo rabin butter na soya da albasa na
zuba naman, tumatur, kayan kamshi da magi, na
hada na dafa sannan na dan dafa alaiyaho da
magi kadan.
Na hada alaiyaho da naman nan na wuta na
gauraya na zuba akan shinkafar na rufe da foil
paper nasa a oven na barshi cikin madaidaiciyar
wuta, tsawon minti arba' in.
Na kuma shirya mishi abin sha mai dadi,
shima ga abubuwan da nayi amfani dasu.
Kankana
Lemo
Sugar
Citta
Lemon tsami cokali (1)

92
A cire jan kankanan a bar bakon asa a
bulanda a markada, a markada lemon zaki
bayan an cire fari-farin abin da ke jikinshi, a
matsa ruwan lemon tsami cokali daya akan
ruwan kankana da lemon nan sai asa citta kadan
da sugar daidai yanda ake bukata.
Gaba daya na hada na juye na shirya mishi
yana zaune yana kallon abincin sai ya kalle ni
yace min hala dai an shirya min wannan abincin
ne yau don a tuna min na sheka ra biyar yau da
angwancewa?
Na sunkuyar da kaina kasa cikin zuciyata na
ce ashe shima yana sane da zagayowar ranar, na
dago kaina a hankali na kalle shi na ce mishi eh
yaya yau shekarunka biyar da angwancewa sai
dai har yanzu....bai bari na karasa abin da nake
shirin fadin ba, sai yasa hannu ya tallabe habata
ya ce, har yanzu amarcinmu yana nan kullum
kara son juna muke yi ni da ke babu abin da ya
taba shiga tsakaninmu muna da fahimtar juna
muna ganin darajar juna saboda akwai kauna
mai yawa a tsakaninmu, don yi min alkawari a
yau kamar yanda nasha yi miki a sauran shekaru
hudu da suka wuce, na kalle shi cikin murmushi
na ce alkawarin me zanyi maka yaya Almu? Ya
zuba min ido yana kallona ya ce irin wanda
93

nake yi miki a rana irin ta yau, na ce ai ni bani
da abin yi maka ko baka yayi maza ya ce kina
da su da yawa Rabi, don haka zan roke ki kiyi
min alkawarin har abada zaki yi tayi min
abubuwa guda uku, na ce sune me? Ya ce zaki
yi ta sona ko da kuwa a wane hali muka samu
kanmu? Na yi murmushi na ce wannan ai
rubutacce ne a zuciyata, ya ce to na gode yi min
alkawari Rabi za ki bani hadin kai a duk lokacin
da na nemi hadin kanki kan wani abin da ya taso
min, na ce zan baka, ya ce to ina so ki zama mai
taimakona a kowane lokaci na nemi taimakonki,
na sake cewa zanyi hakan ya ce to na gode, yana
fadin haka ya mike ya shiga dakinshi ya fito
wata 'yar leda ya dauko da ya fito da wani dan
akwati daga cikinta ya bude shi ya fiddo wasu
warawarai masu asalin kyau ya kama hannuna
ya zare wadanda nake sanye da su ya maida
mun sabbin ya ce tukuci ne na kin shekara biyar
kina hakuri da mijinki.
Na kalle shi nayi murmushi na ce, na gode
Yaya, abin da duk kake nema na alheri a rayuwa
Allah ya baka shi, ya ce to amin.
Da daddare ranar ina tare da yaya Almu
bayan na tsala mishi kwalliyar da tayi dalilin
al'amura masu yawan gaske, yana kwance can
gefe kan faffadan gadon nashi cikin

94
matsananciyar gajiya, lumshe kuma da ido yana
maida numfashinshi a hankali, zuwa can sai naji
ya ce min "kinyi bacci ne Rabi? Na ce mishi a'a,
ya ce to kar kiyi bari in zo muyi magana, na ce
mishi to. Mikewa yayi ya shiga toilet yayi
wanka ya fito nima ya bani umarnin yin hakan,
naje nayi nazo nima nayi sallah raka'a hudu
saboda abin da na samu yana yi kenan, ya gama
addu'a ya shafa fatiha nima na shafa tawa sai ya
juyo ya kalle ni cikin natsuwa babu alamar wasa
a tare dashi, sai ya buda baki ya ce min, wannan
maganar da na zaunar dake zan gaya miki a yau
Rabi ta dade tana katse min dadin baccina
saboda nauyinta a wurina yana da yawa, to
amma babu yanda zanyi in yi ta boye miki ita
musamman da yake abin kara matsowa yake yi,
zuba mishi ido nayi ina kallonshi ina kuma
sauraron bayanin nashi, sai ya ce min ni dake
akwai fahimtar juna a tsakaninmu shine kuma
muhimmin al'amari dama a tsakanin ma'aurata,
ni na yarda dake na amince miki don nasan ba
za ki taba yin wani abin da zai cutar dani na
Kuma sani kema kin san in zan hango abin da
zai cuce ki to zai gama dani ne kafin ya iso gare
ki, ban taba zaton zanyi abin da nake shirin yin
ba a wannan lokacin in ban da wasu al'amura
masu tsanani da suka tasa ni a gaba.
95

Na ce mishi menene ya faru Yaya Almu?
Menene ya taso mai tsanani da zai saka kayi
abin da baka shirya ba? Ka gaya min kawai ba
sai ka tsaya kana yi min dogon bayani ba, ya ce
natsuwarki nake bukata so nake ki bani hadin
kanki don hakanne kawai zai taimake mu ni da
ke na ce na baka ka gaya min menene? Ya
sassauta magana ya ce aure nake so in y1, ammna
bani na nemi auren ba, bani yarinyar akayi na
zuba mishi ido ina kallonshi cikin kaduwa ban
taba tsammanin abin da zai gaya min ba kenan,
na daga ido cikin natsuwa na kalle shi na ce don
ni ba zan haihu ba kenan? Yayi maza ya ce a'a,
a'a ba haka bane, kinsan shi aure zuwa yake yı,
kuma don kisan ma babu wani abin da zai cutar
dake Umma ta sani ita ce ma ta ce dole in karbi
auren don da nace bana so nayi maza na ce
Umma? Nan da nan ya canza zancen da cewar
ba Umma nake nufi ba, amma ni dama can kin
san ina gaya miki cewar sha'awar uwargidanci
nake yi miki, na rinka yi miki hakanne don in
fahimtar dake cewar ni din bani da burin zama
da mace guda daya na ce haka ne, amma tun
lokacin nima na gaya maka cewar bai bani
sha'awa ba kuma zan taba yarda in yi shima har
ma na taba gaya maka cewar kara auren mijina
alama ne na shi din ya gaji dani, don haka yanzu
96

ma kan abin da zan tsaya kenan ka gaji dani ai
ma kayi kokari ban haifar maka kowa ba bayan
kana ganin duk wadanda muka yi aure tare
'ya'ya uku-uku suke shirin samu, gidan Yaya
Junaidu kuwa tuni akayi ukun na hudu ake
nema, lokacin ne na fara kuka sosai musamman
da na kara tunawa cewa ni da kaina na karbo
sakamakon Likita da ya tabbatar da cewar ba
zan iya haihuwa ba ban da wanda yaya Almu ya
dade yana boyewa.
Hakan da nake yi ya kara sanyaya jikin Yaya
Almu, ya matso kusa dani ya rungume ni "kiyi
hakuri Rabi, ina tabbatar miki bana murnar
wannan auren na san1 ban taba sha'awar zama
mijin mace daya ba, amma lalurarki sai tasa ni
jin tausayinki matsanancin tausayin da yasa na
hakura na hakura da duk wadannan abubuwan,
to amma a yanzu ya Zama mUn dole inyi Baba
da Umma sun tasa ni a gaba ta kaima nayi
watanni ban je in da suke ba amma basu hakura
ba sai kuma kwatsam ga maganar wannan
yarinyar ta taso. Umma kuma ta ce in karbi
auren kin kuma san ba zai yiwu in ki bin
umarninta ba.
Ko da yake nasan yaya Almu kullum kan bin
umarnin Umma yake amma sai na kalli wannan
biyayyar tashi har da dama yana so, duk yanda

97
na kai da son kaina ya zama dole in yarda da
cewar yaya Almu zai bukaci kara aure don
samun haihuwa ko da kuwa kullum hadiye shi a
ciki nake yi ina fito dashi, don tsananin
kyautatawa, shi ne da guda daya da baba yake
dashi ko kafin in mallaki hankalin kaina kuwa
nasan babu wani abin da ke da daraja a gidanmu
irin haihuwa, to yaya Almu bai samu ba an
kuma ce nice mai matsalar, in baba ya sanya shi
yayi aure bai yi laifi ba, don nasan yana son
ganin danshi koma in ce 'ya'yanshi yanda duk ya
kai da sona kuma ba zai bani mamaki ba in ya
fifita wanda yake yi mishi akan nawa, to amma
ita Umma fa, don me zata shiga zancen auren
nashi? Tana nufin itama tafi sonshi a kaina?
Wadannan sune tambayoyin da suka zo cikin
zuciyata na kuma kudurawa raina ganin Umma
don ta bani amsar su.
Har gari ya waye ban sake daga ido na kalli
Yaya Almu ba, balle in bashi amsar
maganganun da yake ji, har yayi alwala ya fita
sallar asuba nima na idar da sallah ban tsaya jan
carbi ba don kar ya dawo ya same ni na yiwo
waje mota na nema shata zuwa gida don nasan
Umma bata Legos.
Na iso gida wajen karfe goma, don haka kai
tsaye sashin Ummana na nufa na kuma yi sa'a
98

sanyin da ake yi yasa Baba maigadi ne kawai a
waje, ina shiga sashin Umma 'ya'yan yaya
Junaidu na fara gani su uku, baban Umma,
Zuwairiya da Halimatus-Sadiya cikin tafka-
tafkan suwaitu suna wasan tseren kekuna, suna
ganina suka nufo ni da gudu suna yi min oyoyo,
nasa hannu na dauki Halima na karasa falon da
ita Umma tana ciki tana zaune ita kadai na
durkusa gabanta da nufin in gaisheta, sai dai ban
iya cewa komai ba saboda hawayen da suka
kama zuba daga idona, ban gama kukan ba sai
ga yaya Almu ya shigo da alamar dama ya riga
ni zuwa gidan, koma yana ganin shigowata ban
fasa yin abin da ya kawo ni ba, na ce mata me
nayi miki Umma da zaku hadu ke da Baba ku
yanke min hukunci iri daya? In shi yafi sonshi
dani kema za ki fi sonshi dani ne?
Daga ido tayi cikin natsuwa ta kalle ni ta ce
min kiyi hakuri Adawiyya, babu wani wanda
yafi son Babangida a kanki tsakanin ni da Alhaji
dukkan ku 'ya'ya ne, hukunci na adalci aka
zartar a tsakaninku, ba zai yiwu babangida yayi
ta zama dake ke kadai ba tare da lalurar dake
gare ki, koda baki da wata lalura ma yana da
yancin yin mata hudu don haka kiyi hakuri ki
koma dakinki ki zauna mu rungumi kaddarar da
ta same mu ta rashin haihuwa sai dai n....ban

99

san yanda akayi ba jina kawai nayi na katse
Umma ina ta fadin maganganu, bani da wata
kaddara da zan unguma Umma, in ku kun
yarda da cewar ba zan haihu ba toni ban taba
yarda ba, ba kuma zaku tilasta ni in yarda ba, ba
kuma zai yiwu ku fake da hakan ku taimaki
yaya Almu a kaina ya cuce ni ba, ba zan yarda
ba ban yarda da cewar ni dashi daya ne a
wurinki ba, kin fi sonshi dani na bar mishi ke,
na barwa yaya Almu ke Umma, ki maida ni
kawai in da kika je kika dauko uba...ban samu
karasawa ba na jini kife a kasa, saboda wani irin
wawan marin da aka kife ni dashi, tsawon lokaci
ina kife kafin na dago kaina na kalle su Umma
tana zaune ta sunkuyar da kanta kasa yan
yatsun hannunta take kallo. Shi kuwa yaya
Almu ni ya zubawa ido cikin matsanancin bacin
rai, abin da ya tabbatar min da cewar shi ne yayi
min wannan dukan na tare jinin dake ci gaba da
zuba daga hancina ta tafin hannuna, na sake
kallon shi na ce mishi, ko zaka kashe ni ba

Please Login or Register in order to submit comment