Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan Ummana kenan
ba zan iya barin Umma ta tozarta gaban
makiyanta ba, don haka dole ne in bi umarnin
da Hajiya Hauwa ta bani na komawa kan
al'amuran gidana da kuma mijina.
Washe gari da safe na tashi bisa tsarin da na
saba, na kama hidimar gidana da sassafe ina
cikin kicin wajen misalin tara na safe yaya
Almu ya shigo kicin din sanye da doguwar
jallabiya a jikinshi ga dukkan alamu murnar
ganina a kicin din yake yi, me kike shirya mana
ne? Ban kalle shi ba na ce mishi waina ce da
miya ga kuma kunun gyada, ya ce to kin kyauta
Rabi, kamar kin san cewar da yunwa na tashi da
safen nan.
Daga yaya Almu har Baba Talatu ji dani
suka rinka yi suna ina aka saka dani saboda
119
ganin da suka yi na wastsake daga matakin da
na dauka na kwana da kwanaki.
Ina sallamar yaya Almu da ya shirya ya fita
sai na yiwa yaya Junaidu waya na shaida mishi
cewar ina bukatar ya turo min kudi don in fara
sayayyar da Baba ya ce inyi, tsawon lokaci yana
yi min nasiha da maganganu masu kwantar da
hankali kafin ya tambaye ni abin đa zai bani, na
ce mishi ba zan iya sani ba sai dai kawai yanda
ya kama ina kuma so a bani Anti Rahma don ta
taya ni, ya ce to babu laifi.
Anti Rahma baro gidanta tayi a zo Kaduna
ta zauna tsawon kwanaki hudu sai da muka
gama hada komai na kayan kamu da na aure ta
kuma jagoranci wadanda ta gayyató suka rakata
suka je suka kai kayan sannan ta kama hanya ta
koma gidanta.
An kai kayan washe gari da sašsafe ina tare
da yaya Almu a dakinshi baba ya bugo min
waya albarka yake ta sanya min kan labarin da
aka bashi na irin kayan da na hada na aike dasu
yayi min addu'o'i masu dadi ya kuma roke ni in
zamewa yaya Aimu kamar yanda Umniana ta
zame mishi na ce to Baba.
Shirin biki sosai na shiga don kuwa nasan
biki za'ayi irin 'ya'yan gata yaya Almu ta
6angarenshi ba sai na tsaya ina wani dogon

120

bayani ba, to itama Lailatu ta bangarenta 'yar
gata ce kwarai, mahaifiyarta ce uwargida a
gidansu tana kuma yin yanda taso don kuwa
amare dai-dai har bakwai akayi mata amma
babu ko daya duk sun fita wadanda suka san
sirrin gidan kuma sun ce Hajiya Hairan ce mai
korar su don kuwa 'ya'yan da suke bari a gidan
masu aikin gidan sun fi su 'yanci. Lailatu ce 'ya
mace babba a wurin iyayenta a gabanta kuma
akwai maza biyar, don haka ni da kaina nasan
da gatanta to amma na hakura na yarda da
zuwan nata na kuma shirya zama da ita zan
kuma yi duk abin da zanyi don ganin bukatar
wadanda suke shirin kawo ta bata biya ba, duk
kuwa da na san Lailatu zata iya zuwa gidan ta
haifi dan da ake bukatar samu in na tuna
wannan shi ne abin da ya kan daki zuciyata har
in kasa daurewa in hana idanuwana zubar da
hawaye, to amma yaya zany1? In da don tani ne
da tafiyata kawai zanyi in yi nesa dasu ta yanda
zan kare kaina daga ganin bakin. ciki da bacin
rai, to amma Umma tana son ci gaba da zamana
a gidan ta jaddada min cewar tana son ganin
Lailatu ta shigo ta same ni ta daukarwa Karama
abin da take son dauka a gidan ina nan cikin
shirin biki na sosai har ana saura kwana bakwai
ayi bikin rannan da hantsi sai ga Ummana tare
121

da da Hajiya Hauwa sun iso gidan da hannu
biyu na karbe su cikin murna da farin ciki sai
dai abin da na gani a tare da Umma ne ya daga
mun hankali ya kuma tayar mun da hankali
cikin hawaye na kalle ta ina kuka na ce Umma
ramewa kika yi? Maganar auren yaya Almu ne
ya tayar miki da hankali haka? Umma ai zan
haihu kar kiji tsoron komai babu wani wanda zai
karbe miki danki daga gare ki zan kuma yi duk
abin da zanyi wajen ganin na tsare.....ban karasa
ba Umma ta katse ni wajen cewa kiyi bakin ciki
don kinga ta samu rabu kowa yana rayuwa ne
kan kaddarar da aka shirya mishi.
Kwana biyu da tafiyarsu Umma ta aiko aka
zo aka kwashe duk wani abin da yake cikin
gidan aka maida sababbi daga sashina zuwa na
yaya Almu babu abin da bata canza ba, Baba ma
ya aiko mun da mota sabuwa dal, Umma amarya
ma tayi min aike na wasu warawarai da zobuna
wai inyi adon biki gashi dama duk sayaiyar da
muka yiwa amarya bib1yu Anti Rahma ta sani
nayi komai dai ina dashi kenan ga yaya Almu
wanda ya tasa ni a gaba da tambaya duk da dai
bani ke hidimar auren nan ba ai ya kamata ki
gaya min me kike so in yi miki na fadan
amarya? Na ce mishi babu komai ai su Baba
sunyi ya kuma wadatar duk da haka sa da yayi
122

min kyautar wasu sarkoki guda biyu, abin dai
gwanin sha'awa kamar ace bani da wata matsala
amma ina? A duk lokacin da na kalli tarin
dukiyar da aka tara min a dalilin auren sai inga
ai ba abin da ake nema ba kenan da kamar kawo
ta za'ayi don ta kamu wani abu wurin yaya
Almu to da sai in ce ta makara don na rigata
samu, to amma ba haka ba ne da ake nema a
wurin ta babu mamaki kuma tana zuwa ta samu
tunda Likitoci da yawa sun tabbatar min da
cewar ni ke da matsalar da ta hana samun
haihuwa tsakanina da mijina wannan shine abin
da ya fi komai dukan zuciyata.
Tun ana saura kwana biyu bikin gidan ya
cika da mutane 'ya'yan kawayen Umma na kusa
da na nesa babu wacce bata zo ba.
Biki sosai Umma ta shirya ta kuma tsaya
matsayinta ita ce uwar yaya Almu komai ita ke
yi duk abin da ake nema ita ce mai bayarwa.
Biki na kasaita akayi ta kowane bangare
komai yaji nima anawa bangaren kawayen
Umma ake waye dani suke 'ya'yansu ga matan
abokan yaya Almu da muke ma'amalla mai dadi
wadanda suka yi matukar nuna min kauna da
kulawa ga yan uwa su Anti Basira da su Anti
Kubra, Anti Aina'u, Anti Rahma kam babu abin
da zan ce mata ko da yake ban yi mamaki ba
123

saboda irin tsayuwar yaya Junaidu kan
al'amarina. Ranar daurin auren wuni yayi yana
yi min waya yana tambayata babu dai matsala
ko? In ce mishi a'a babu damuwa sai ya ce too
kiyi hakuri ki kara akan wanda nasan kina
dashi, in ce mishi to anyi daurin aure yaya Almu
ya zama ango, anyi shagalin biki na halarci duk
liyafofin da aka shirya na kuma yi duk abin da
ya dace inyi wadanda basu san Lailatu ba sai a
wannan lokacin sunyi ta gaya min cewar ai babu
abin da zata nuna miki sai farar fata, bata kaiki
kyau ba bata kaiki tsayuwa ba bata kaiki iya
kwalliya ba, da kuma yin kyau da kwalliyar aike
mai kyau ce Adawiyyah dolen miji ya soki ko
don irin abin da aka kyautata miki halittar ki
dashi, nayi murmush1 kawai na kalli Naja'atu
yar Hajiya Hauwa da muke kai daya da ita na
ce mata Naja, ba kyau yaya AImu yake nema ba
wurin mace ko iya kwalliya haihuwa yake so ita
yake nema in har ya same ta to bana zaton zai
tsaya kallon wadannan abubuwa da kika lissafa
tayi maza ta ce to ai kema zaki haihu lokaci ne
kawai na ce mata abin da nake ta karfafa
zuciyata dashi kenan to amma yau kam na
karaya zuciyata kuma ta gama tsinkewa da
al'amarin na kama yi mata kuka.

124

Da sauri ta dafa kafadata tana ta faman gaya
min maganganu masu kwantar da hankali tana
fadin ba fa Likita ke bada haihuwa ba
Adawiyyah tsaya kawai kan yin addu'a a gida
anyi wunin biki cikin shagali mai yawan gaske
da gude-gude daga bangaren dangin amarya
anawa bangaren ma ina cikin hayyacina da
natsuwata kallon, komai nake yi don tun kafin a
watse a barin da Lailatu na riga na gane lalle
anyi mun ki shiya na kuma yarda cewar Umma
Karama tana da dalilinta na jin sanadin auren
yaya Almu da wannan yarinyar, duk abin da ke
faruwa dai ban cewa kowa komai ba, jan bakina
kawai nayi na tsuke ina kallon komai da idona,
zuciyata kuma tana yi mishi irin fassarar da ta
dace dashi, nayi kwalliya a bikin kwalliya kuwa
irin ta burgewa irin wacce zata shaidawa Lailatu
da duk wani nata duk abin da take takama dashi
na gata to bata kama nawa kafar ba, don kuwa
yanda na rinka canza zannuwa haka na rinka
canza gold din da nake sanyawa, tsawon
kwanakin bikin kuma ban fasa zuwa wurin
mijina ba don kuwa abin da ya nemi inyi mishi
kenan.
Ranar budan kai da yamma iyayen amarya
suka kawo ta falona da yamma kamar dai yanda
al'ada take na kaiwa uwargida Amaryarta don
125

bada amana sai dai kuma su da suka zo cewa
sukanyi to ga amarya nan min kawo ta gidan
mijinta ta kuma zone don ta zauna ba wai ta
leko ba ne zata koma.
Hajiya Hauwa ta kalli kanwar uwartata mai
wannan bayani tayi murmushi ta ce Hajiya joda
kenan ai mu bamu za'a kawowa amarya ayiwa
wannan jawabi ba, mu kam ai an sanmu da barin
kishiya ta zauna matukar zata iya zuba ido tayi
hakuri kin kuma san ance kowane tsuntsu kukan
gidansu yake yi, don haka in har kun kwabi
'yarku kunyi mata tarbiya to ni kuwa ina
tabbatar miki da cewar zata zauna in har zata iya
gani ta kyale, ana gama wannan bayani ta sake
6alla bakin jakarta sai da ta sake jefa wani
cingam din a bakinta sannan ta zaro daurin naira
dari biyar-biyar ta mika musu ta ce Adawiyya ta
sayi bakin amarya suka tashi suka tafi.
Yamma nayi yan uwa da abokan arziki suka
Soma yin sallama suna tafiya gida da fahimtar
juna in ce amin, ta bangaren amarya kuwa duk
wacce zata tafi sai ta fito tsakar gida sai ta daga
murya ta ce to mu zamu tafi kan badi kuma
muna sauraron a kira mu suna don ba mun kawo
ki ba ne kawai don ki rinka ci kina juyewa a
masai mun kawo mishi ke ne don ki cika mishi
gida da 'ya'ya tunda haihuwa kam ai kin gaje ta
126

sai kuma akwashe da dariya a tafa hannu kafin a
rangada wata irin matsiyaciyar guda.
Suma su Hajiya Hauwa da Hajiya Furera
suka yi shirin tafiya kan su tafi kuwa sai da
Hajiya Hauwa ta ta cafke kunnena ta rike tana
fadin bari ni da kaina in kara jaddada miki
cewar kwana bakwai ango yake yi a dakin
amaryarshi budurwa don haka kar in ji kar in
gani, nayi murmushi kawai na ce mata to Umma
ku gaida gida, Allah ya kara girma suka ce amin
Suka kuma fita da kwarin gwiwa saboda ganin
irin sallamar da muka yi.
Gaba daya an gama tafiya daga ni sai Baba
Talatu da ta gama gyara min wajena muna
zaune ne tana matsa min kafafuwana tare da
jaddada min irin kokarin da take cewa wai nayi.
na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata
shi kenan Baba yau burin yaya Almu ya cika ya
maidani uwargida a gidanshi.
Tayi maza ta ce babu komai dama abin da ya
dace dake kenan, kiyi shugabanci ki jagoranci
iyalin gidanshi baki ga kuma yanda hakan ya
kera miki kwarjini fa kika ce Baba? Zubewar da
nayi fa'? Ta ce ai bai baiyana kowa ya gane ba
saboda ke dama jikinki mulmulallen jiki ne
gashi kuma kin kame babu alamar wata damuwa
a tare dake. Shigowar yaya Almu ta katse hirar
127

tamu, tayi mishi murnar tashin taron lafiya
kamar yanda nima nayi mishi sannan ta tashi ta
tafi wurinta.
A natse yaya Almu ya kalle ni ya ce mun
nasan agajiye kike to amma kuma yaya zanyi?2
Nayi maza na ce mishi me ya faru? Ya ce
matsananciyar yunwa nake ji.
Cikin hanzari na mike na shiga kicin don
shirya mishi abin da zai ci mcat roll ga
abubuwan da nayi amfani dasu.
(1) Naman cinyar baya na yanka sa (2)
albasa guda uku (3) mangyada ko butter, (4)
murmushen biredi (5) kawai guda daya (6)
tumatur manya guda hudu (7) maggi. (8) karas
(9) Green beans, sai (10) kayan kamshi
Na fara da yin amfani da wuka mai kaifi na
rinka yiwa naman nan yankan faifai tanfar dai
irin na masu tsire sai dai wannan yafi na mai
tsire fadi tsayi da kuma kauri, sannan na dora
pan a kan wuta na soya butter da albasar da na
riga naa yanyanka kanana na kawo sauran
kayaiyakin nan amma banda karas da green
beans na zuba, sannan na koma murza naman
nan akan rolling boad da kwalba har sai da na ga
yayi fale-fale sai kuma na soma debo kayan
cikin pan din nan wato su murmushen biredin
nan da maggi da albasa chese da na hada da
128

butter ina shafe fallen naman na gaba da baya
ina ajiyewa har sai da na gama da su duka
sannan na koma na nade su kamar tabarma ina
jefawa cikin ruwan buttern da na dora yayi zafi
akan wuta na kuma zuba albasa har na gama
soye shi tas sai da yayi jajajaja sannan na zuba
tumatur da kavan kamshi a ciki na kuma zuba
ruwa kadan na rufe tukunyar ya dahu sosai, sar
na kawo plate masu kyau na shirya yankakken
karas din nan da green beans a ciki sannan na
tsamo roll din naman nan na jera su akai romon
kuwa sai da yayi kauri tukuna shima sai na juye
cikin plate din wato kan roll din naman.
Sai kuma abin shan da na shirya mishi, ga
abubuwan da nayi amfani da su.
1. Tanjarine guda takwas (8)
2. Sugar
3. garine captard cokali daya
4. Madarar gongoni guda daya
5. Madarar shanu rabin kofi..
Na kammala komai cikin natsuwa na dauko
shi akan tire nazo da shi falona in da na bar yaya
Almu na same shi kishingide har bacci ya soma
daukarshi, saboda tsananin gajiya cikin natsuwa
na tashe shi na ce mishi ga abincin an kawo ya
mike zaune cikin yanayin gajiya da wahalar da
yayi, ya kalli abincin cikin sha'awa da farin ciki
129
yayi min godiya tare da addu'o'i masu dadin ji
har ya mika hannu zai fara ci sai na ce mishi a'a
ango muje dai can sabon masaukin naka babu
mamaki itama amaryar tana tare da yunwar yayi
maza ya mike cikin jin dadin maganar da nayi
yana fadin, gaskiya ne Rabi, lalle kuma na yarda
uwargida ta sosai kike shirin zama.
Na bi bayan Yaya Almu da tiren abincin a
hannuna naje zan shiga dakin sai naji Lailatu
tana magana cikin shisshikar kuka giurkina ne
fa yau amma kaje ka mike a dakinta har kana
yin bacci, gabana ya yanke ya fadi da jin ana
yiwa yaya Almu togaciya da kashedin zaman
shi a dakina, karo na farko kenan da aka taba
yin hakan a rayuwarmu.
Sallama sosai nayi kafin aka iya amsawa har
nayi kamar in juya da tiren dake hannuna, sai
kuma na fasa nayi ta jira dai har na samu aka
bani izinin shiga ita kam fuskarta a daure babu
alamar wasa shi ne dai yake ta kokarin
murmushi da jawo hankula wuri daya don ya
daidaita al'amura.
Na kalle su nayi murmushi na ce amarya
sauko daga nan don kiji dadin ci ban jira
amsawarta ba na juya na koma dakina inda na
samu Baba Talatu tana jirana, to ke kin kai
musu abinci kin dawo kin hau gado kin kwanta
130

ke ba za ki ci komai ba ne? Na ce bana jin
yunwa Baba cikina a cunkushe yake ban ci
komai ba tun safe in ban da ruwan sanyi da nayi
tasha amma kuma har yanzu ban ji kamar ina
bukatar ci ba fatana dai kawai bai wuce in samu
in yi bacci ba.
Baba Talatu ta kara matsowa kusa dani tana
yi min tausa tare da fadin uhun ai namiji da kike
kallonshi kyale shi kawai ya kamata kiyi in har
kika ce zaki biye mishi to sai yayi dalilin da zaki
rinka tafiya kan hanya kina sanbatu, baki san
lokacin da kika yi hakan ba mutanen gari kuma
maimakon su tausaya miki sai suce dama aka
hada su bada ke ba? Tunda in kishiya ce ai ba a
kanki aka fara yinta ba, ai ni nan da kike kallona
ni na san kishiya tunda dai ita ce tayi dalilin da
na hakura da zaman aure tun a shekaruna na
kuruciya ta raba ni da mijina, bayan kuma ina
sonshi kamar inyi yaya?
Cikin sauri na zubawa Baba Talatu ido ina
mata kallo na ban mamaki da kaduwa na ce
amma baki taba sanya wannan labarin cikin
jerin labaran da kiká yi ta bani ba, taja wata irin
ajiyar zuciya mai karfin gaske ta ce uhun to
wannan labari in ba dalili yayi dalili ba me zai
sa kayi ta bai wa yara shi? Kamar yau din nan
dai da hali ya kama ai kinga zan gaya miki
131

komai, na kasa kunnuwwa na saki baki na zare
ido ina sauraron labarin da Baba Talatu take
shirin bani, sai kawai na jiwo ihun Lailatu daga
tsakar gida tana kiran taimako, da iyakacin
Rarfinta take fadin waiyo ta shiga uku waiyo
za'a kashe ta, sanin da nayi na baro dakin tana
kunkumin girkinta na yaya Almu yazo ya zauna
a nawa dakin sai nayi nmaza na zabura zan kai
mata taimako ga zatona maganar ce tayi tsanani
har yaya Almu ya tunzura ya rufe ta da duka, sai
naga Baba Talatu tayi wuf ta cafo ni ta maida ni
kan gado ta danne da hannayenta duka biyu
cikin haki saboda zafin naman da ta gwada
wajen kamo nin, take tambayata, ina zaki haka
da saurinki kamar kin ji ana neman ki, na kalı
Baba cikin damuwa na ce yaya Almu zanje in
bai wa hakuri ya kyale yarinyar nan kar ya ce
zai biye mata.
Baba Talatu ta zuba min ido cikin takaici
tace, lalle ke kam da sauranki to ina ruwanki
ina ganin ki da abin da suke yi? Ko kuwa wane
karanbani ne zai kai ki ba da hakuri don kin ji
ana kama hannun kishiyarki? Da sauri ciki
wani irin mummunan faduwar gaban da ban
taba jin irin shi ba na alli Baba Talatu a firgice
na ce mata kama hannu? A hankali cikin
natsuwa ta ce min eh nmana wannan ihu ai yai
132

kama da ihun shakiyanci da amare keyi yayin
kama hannunsu, ban sake tankawa Baba Talatu
zancen ta ba a hankali cikin karaya na maida
kaina kan filo na kwantar yayin da wasu zafafan
hawaye da suka fi kama da hawayen kishi suka
yi ta zubowa daga idanuna cikin zuciyata kuwa
sai fadi nake yi ka cuce ni yaya Almu, ka cuce
ni.."


Mu gamu a littafi na hudu don mu ji yanda
za'a kwashe tsakanin Rabi'atul Adawiyyah da
wannan kishiya tata.
Littafin ya fito tare da na ukun, don haka a
neme shi a karasa shan labarin.

Na gode,
Taku, Hafsat C, Sodangi.

133









An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment