Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜 𝗡𝗔 𝗖𝗘 💫




An Imaginary Love Story❤️




𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽



𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷




Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya bani Ikon Ƙara kawo muku wannan Littafin Allah yasa yadda na fara Rubuta shi lafiya in ga ma lafiya.

● Ƙirƙiraren labari ne idan wani Abu yayi kamanceceniya da Rayuwar Wani/Wata to Arashi ne.

● Yana ɗauke da abubuwa daban-daban kada ku bari ayi tafiyar babu ku 🫰🫰🫰


Na Chanja masa suna daga MURADIN ZUCIYATA zuwa MURADI NA CE



𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡




Follow My WhatsApp Channel




https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I





بسم الله الرحمن الرحيم





𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️




𝑃𝑎𝑔𝑒 1🦋






𝑳𝒊𝒎𝒂𝒘𝒂 𝑺𝒕𝒓𝒆𝒆𝒕, 𝑫𝒖𝒕𝒔𝒆, 𝑱𝒊𝒈𝒂𝒘𝒂 𝑺𝒕𝒂𝒕𝒆.






Tuƙi yake a hankali kamar baya son yi a bakin wani tangamemen Gida ya tsaya Horn yayi gate man ne ya leƙo ganin motar yasa ya koma ciki ya buɗe gate ɗin shiga ciki yayi tare da yin parking zaman sa yayi a cikin motar bai fito ba ya ɗauki gurin minti talatin a ciki sannan ya fito tsayawa yayi kana ganin shi kaga ƙarfaffan mutum da motsa jiki ya ratsa shi {Giant} ƙare wa compound ɗin gidan kallo ƙaton gida ne dan daga ciki yafi girma Part-Part ne gurin guda Shabiyar daga can gefe garden ne mai kyau cigaba yayi da tsaiwa a gurin jikin motar sa. Babban Mutum ne ya shigo gidan kai tsaye gurin sa ya nufo Bata fuska yayi sannan yace masa


"Daga ina kake Fawzan?" Da Sauri ya juya yana kallon sa baiyi tsammanin zai haɗu da kowa yanzu ba Ko takwas bata yi ba ya dawo Shiru yayi masa yana ɗauke Kansa daga kallon sa, cigaba da yi masa magana yayi


"Yau ma baka kwana a gidan ba kenan?" Ɗauke shi da mari yayi "a ina ka kwana nace maka" nan ma shiru ya ƙara yi masa yana cin magani da ƙunkuni ƙasa-ƙasa sai kuma ya ce masa


"Malam ka dame ni da surutun tsiya kai ba haifa ta kayi ba amma kana mari na, ɗaga maka ƙafa kawai nake amma wallahi da sai na rama"


"Rashin Kunyar taka har ta kai kace zaka mare ni Dan na maka faɗa, to zoka rama marin mara tarbiyya kawai"


"Na rasa inda ka samo wannan banzan halin mu dai duk zuri'ar mu babu ɗan iska sai kai maybe a Gurin Uwarka ka kwaso wannan mummunan halin"


"Kaga rashin tarbiyya a ƴaƴan ka tsohon banza kawai, kuma ba Mahaifiya ta ka zaga ba Tsohuwar ciki ka zaga kaji, mtwssssss" ya faɗa yana shige wa Part ɗin da yake kallon sa. Masifa ya cigaba da yi a gurin ba jima wa sai ga Tsohuwa ta fito itama daga Part ɗin ta "Kabiru kai da wane haka da sanyin safiyar nan?, Yawanci duk ba'a tashi ba kar hayaniyar ka taja hankali"


"Hajiya kema kin san wanene zai saka mutane magana iyanzu ai"


"Sai yanzu ya ga damar dawowa gidan Kenan, na rasa me yake damun Fawzan baya son kwana a gidan nan yanzu, Kabiru kira min shi yanzu ku same ni a palour na da Iyayen sa"


"Allah ya Kyauta dai Insha Allah yanzu zaki ganmu"






🔥💥💦






𝑫𝒂𝒎𝒂𝒕𝒖𝒓𝒖, 𝒀𝒐𝒃𝒆, 𝑺𝒕𝒂𝒕𝒆.






Palour ne kato an yalwata shi da kujeru masu kyau kirar Italy set Uku daga ɗayan side ɗin kuwa katon Dinning ne ba kowa a cikin palour ƙofofine gurin guda shida sai Stairs daga tsakiyar Palour'n daga gurin Dinning ɗin Ƙofa ce a buɗe da alamu kitchen ne.





Wata kyakkyawar budurwa ce tsaye take a bakin sink Doguwa ce dirarriya daga fuskar ta fara ce kal ƙaramin lips ne da ita tana da dara-daran idanu masu kyau ruwa take tara da alamu ta faɗa Duniyar tunani Wata Babbar Mace kana ganin ta kaga wadda Naira ta zauna a jikin ta cikin kitchen ɗin ta shigo a baƙin kofa ta tsaya tana kiran"Jaanan!, Jaanan!, Jaanan" jin shiru ne ya sata ƙara so wa kusa da ita


"Jaanan! Jaanan" ta ƙara faɗa shiru bata answer ba ɗaka mata duka tayi a firgice ta ɗago "Yaushe kika ƙara so ne Ummu?" Ta tambaye ta


"Ban sani ba, bacin kina jina amma baki amsa ba sai da nazo dai-dai inda kike ke ga ishashiya" ta faɗa kamar ta rufe ta da duka


"A'a Ummu banji kina magana ba ne"


"Ai dama ba zaki ji ba, kin raina kowa a gidan nan musamman Ni"


"Kiyi haƙuri dan Allah" ta faɗa tana yin ƙasa da kanta kafin ta ƙara wani laifin. wata mace ce ta fito daga ɗaki daga ita sai sleeping dress alamun ta sun nuna yanzu ta tashi daga bacci tsayawa tayi tana kallon su tabe baki tayi Sannan ta ƙara so kitchen kusa da Ummu ta tsaya tana watsa wa Jaanan Mugun Kallo ƙasa tayi da kanta magana ta fara yi musu


"ummu ya Naji kina ta faɗa tun dazu?, Hayaniyar kice ta tashe ni daga bacci"


"Ba Dole kiji ina ta faɗa ba, Yarinyar nan nake ta kir amma tayi banza dani bata amsa ba, nasan har maƙota suna jiyo mu yanzu"


"Uhmmmmm, Indai Jaanan ce ai ta saba tana jin ka kana mata magana amma tayi maka banza, wallahi na tsani Yarinyar nan ji nake kamar na kashe ta, an auro mana wahala mtwsssss"
"Ban san me Yaya ya gani a jikin Yarinyar nan ba ya nace mata sai Wulakanta shi take amma ya nace mata" ta faɗa tana galla mata harara


"Bari yazo shima zai ci Ubansa, Sakin ta zai yi nan bada daɗewa ba na gaji da halin ta"


"Ummu dan Allah Kiyi haƙuri, me za'a yi miki yanzu?"


"In kinyi laifi kin san kice ayi haƙuri, wai Uban me kike ta zaman yi baki fara wanke-wanke nan ba, Da gani ko breakfast Baki haɗa mana ba kuma kin san ɗaki na yana jiran ki zan fita aiki Kizo yanzu ki gyara" cewar budurwar


"Na kusa gama breakfast ɗin, Bari in ƙara sa wanke-wanken Sai inzo"


"Auuuuuu Har sai na ma jira kin ƙara sa?, ai tashi zaki yi Kizo ki gama da shi kafin na fita, in kin gama kya dawo kiyi wanke-wanken" ta faɗa tana fice wa daga kitchen ɗin zuwa ɗakin ta.









Tashi tayi daga wanke-wanken ta bita zuwa ɗakin kafin ta ƙara yin wani laifin cikin ɗakin itama ta shiga katon ɗaki ne an cika shi da kayan alatu kala-kala, kaca-kaca yake kamar ba mace ce a ciki ba. Ko kallon wacce take cikin ɗakin bata yi ba ta wuce Toilet shima ba kyan gani haka ta fara gyara shi tassss ta gyara shi Sannan ta fito. Harara ta watsa mata sai kuma tace "sai nace ki fara aikin nan ɗin sannan zaki yi ne?"


"A'a ba sai Kince ba, amma ai sai kin tashi daga kan gadon sai in fara"


"Ki fara gyara kasan sai in tashi daga nan" Tom tace mata tana fara gyara wa tashi tayi ta koma kan kujera tana danna wayar ta bata daɗe ba ta tashi tana mata wani kallon banza tare da cewa


"saura in fito daga wanka in tarar Baki gama ba" tana shigewa Toilet ɗin. Da sauri sauri ta cigaba da yin aikin tana kuka hawayen daya zubo mata ta share____________________________✍️






# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



Rashin Comments na iya maida shi Paid Book.



09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم


𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝑃𝑎𝑔𝑒 2🦋








Ƙara sa gyaran ɗakin tayi da hanzarin ta kafin ta fito dan Indai ta fito ta tarar da ita sunan ta sorry a gidan. Tana gama gyara ɗakin ta koma kitchen wanke-wanken ta ƙara sa sannan ta fitar musu da Breakfast a dinning ta jera sai kafa-kafa take kar ta yarda wani abu ta sha faɗa ɗakin Ummu ta nufa nan ma aljannar duniya ce dan tafi ɗakin budurwar kyau zaune ta tarar da ita ta hakimce akan kujera tana danna waya a ƙasa ta tsuguna "Ummu na gama aikin"

"Har ɗakin Eshaal kin gyara"

"Eh na gyara"

"Kin haɗa breakfast ɗin"

"Shima na haɗa Ummu"

"To sai gyaran ɗakin nan, kar in dawo in tarar da shi haka"

"Dan Allah Ummu ki bani abinci inci kafin in gyara yunwa nake ji wallahi"

"Abinci? bayan baki gama aikin ki ba salon ina baki kiyi bacci Koh?"

"Wallahi ba zan yi ba, yunwa nake ji kamar na mutu Ummu baki ji cikina ba"

"Ai na fison ki mutu ko na huta da alakaƙai, Kinga tashi ki ƙara sa gyaran nan zaifi Miki" ta faɗa tana make ta wucewa tayi ta barta a gurin durkushe tana riƙe da cikin ta.

Har wajen minti talatin bata tashi ba tana kuka ganin zaman ba zai amfane taba yasa ta tashi da kyar ta gyara ɗakin sannan ta fito a palour ta tarar da su da alamu sun gama yin breakfast ɗin kusa da Ummu tazo ta tsugunna tana cewa
"Na gama Ummu"

"Sai ɗakin su Saabeer ai" Ummu ta faɗa

A zafafe Eshaal ta fara cewa"komai sai tace kiyi bayan kin san aikin kine"

"Ni tun randa naji tace bata sonsa tana da wanda take so na tsane ta yarinya kamar ƴar Aljanu" Wani Namiji yana zaune ya faɗa

"Kaima da kake namiji ba zama kake yi ba, sai ma ya dawo kaga yana wani lallaɓa ta tana botsarewa mtwsssss, Allah ya tsinewa Soyyayar da Yaya yake mata"

"Amin dai Sis, Nifa gani nake kamar ciki ne da ita" Ɗayan da yake Zaune ya faɗa

"Ciki, haba dai ina taga lokacin ɗaukar ciki yanzu" Ɗayar budurwar ta faɗa tana hararar ta

"Indai tayi ciki sai ta gwammace ƙida da rawa" Ummu ta faɗa tana ƙara kallon Jaanan ɗin Sai kuma tace mata "Tashi in ganki" da Sauri ta miƙe tana yin ƙasa da kanta
"Shikenan jeki" ta faɗa tana daɗa Binta da ido. Binta da kallo duk suka yi suma.


Ajiyar zuciya ta sauke tana yin gaba Allah ya gani tsoron mutanen gidan take ji tun lokacin dasu ka tsane ta farkon zuwan ta kowa kamar ya goya ta yake mata amma yanzu abubuwa duk sun chanja ɗan uwansu ne baya son rayuwar aure da shi basu ba sun ɗauki karan tsana sun ɗora mata. Har ɗakunan samarin ƴaƴan ita ke gyara musu sai kace ba Matar Yayan su bace ita sun sallami gaba ɗaya ƴan aikin su, sun maida ta kamar jaka. Part ɗin Samarin tayi tun daga Palour ta fara cin karo da kaya ɗauke wa tayi tana shiga ciki kaca-kaca ko ina kamar ba mutane ne ke rayuwa a ciki ba kullum sai ta gyara amma kullum sai sun bata wasu kayan ma duk wankakku ne aka fito dasu daga cikin Drawer gyara ɗakunan tayi ta fara sai gurin sha biyu sannan ta gama aikin lokacin ta gaji tuluss ga yunwa dake addabar cikin ta. Daƙin Ummu ta koma bata cikin ɗakin da alamu tana toilet zaman jiran ta fito tayi ta kusa minti talatin a ɗakin tayi sannan ta fito kuma da alamun taji shigowar ta shiyasa ta daɗe a ciki bata fuskar ta tayi tana cewa
"Lafiya dai ko na ganki yanzu"

"Lafiya kalau Ummu na gama komai yanzu"

"Har lunch kin yi mana"

"A'a Ummu"

"In kin gama lunch din sai ki ci abincin, indai kika sake kika ci kafin kiyi lunch sai ranki ya ɓaci kinji koh?"

"Naji Ummu" ta faɗa tana fice wa. Kayan Breakfast ɗin suna nan yadda ta kai kowa da ya gama ci a gurin ya bar mata kwashe wa tayi ta gyara dinning ɗin kitchen ta shiga girki ta ɗora tana wanke kwanukan. Tuwo tayi musu dan kar tayi laifi Ummu ta fi son tuwo Sharp-Sharp tayi ta gama.

Tana gama wa part ɗin ta tayi da abincin ta ko Ummu bata cewa ta gama ba dan kar ta sata wani aikin ta gaji hutawa zata yi zuwa La'asar sai ta fito ko zaman minti goma bata yi ba sai ga ɗaya daga cikin samarin ɗazu ya shigo ko sallama baiyi ba ya hauta da masifa
"Kin san bana cin Tuwo shine kika dafa Koh, to Ummu tace kike yanzu tana neman ki mtwsssss stupid girl" ya faɗa yana fice wa

Yarone ƙarami dan ta girme shi nesa ba kusa ba duk gidan babu kamar sa a tarbiyya amma yanzu shi yake mata rashin kunya har da tsaki kamar sa'ar sa da kyar ta tashi ta nufi part ɗin Ummun ta hakimce akan kujera Facing Ƙofa tana ƙarkaɗa ƙafa ta ɗora ɗaya kan ɗaya lokacin data ɗibar mata kawai take jira ya cika taje har part ɗin taci mutuncin ta ko zata ji sauƙin tsanar da tayi mata a zuciya. Sa Ko sallamar da tayi bata amsa ba A harzuƙe ta hau cewa

"Jaanan kin raina Ni Koh?"

"Ummu ya za'a yi na raina ki" a tsorace ta bata amsa

"Ba nace ki daina yi mana tuwo a gidan nan ba?, Ce Miki akayi nan irin gidan kune da ko wacce kazanta dafawa muke kin taɓa ganin Saabeer yana cin tuwo?, Dan kin ga Tawfeeq ya ɗaure Miki gindi komai kike so shi yake miki, to Ni ba Tawfeeq bace, maza ki tashi kije ki dafa masa wani abin yaci"

Maida kallon ta tayi zuwa ga Saabeer
"Son me kake son ci yanzu"

"Ummu kawai ki barshi naje restaurant inci"

"Ga Cook a gidan ku sannan ka tafi restaurant innnnnnaaaaa bazai taɓa yiyuwa ba"

Alaqar kallon ta maida ga Jaanan sannan tace
"ko Pasta ce ki dafa masa yanzu yaci bana son ganin shi da yunwa"

Tohmm tace Muryar ta a shaqe alamun kuka take yunkurawa tayi zata tashi Ummu ta dakatar da ita tana cewa
"Auuuuuu kuka kike saboda na miki faɗa akan ba dai-dai ba" ta faɗa a harzuƙe
Sai kuma ta cigaba da cewa "Jaanan yanzu Ni zaki yi wa kuka saboda na miki faɗa" tana fashe wa da kuka.

Sallamar sa ce taja hankalin Jaanan juyo wa tayi ta kalle sa sai yanzu ta gane dalilin canja maganar da Ummu taso tayi Tawfeeq ne ya dawo kenan
"Ummu me ya faru kuma?" Ya faɗa da Sassarfa ya ƙara so kusa da ita yana riƙe hannun ta yana son Ummu sama da komai a rayuwa baya son ɓacin ran ta. Tunda Ummu ta gane haka take abinda ranta yaso dan yayi wa mutum faɗa indai suka samu matsala da wani haka zata zo tayi ta kuka a gidan har sai ya dau mataki Ummu makirar mace ce sai wanda ya zauna da ita ne zai gane halin ta.

Cigaba da cewa tayi "Jaanan ce ta tsinkawa Eshaal mari kawai dan ta bangaje ta bata sani ba, dan na kira ta na mata faɗa shine take kuka. Jaanan kamar ƴa take a wajen fa"
ta faɗa tana share hawayan fuskar ta

"Me sa haka Jaanan kin san bana son tashin hankali a gidan nan"

Da sauri ta katse shi tana faɗan"Tashi kuje kawai Tawfeeq" bata so ya tambayi ba'a si dan tasan tass yarinyar sai ta faɗi abinda ya faru dan ta taɓa yi mata irin haka shiyasa tayi saurin katse shi.

"Ummu tayi zaman ta kawai a nan, dama wani file na manta na dawo ɗauka sai na jiyo hayaniyar ku nace bari in duba"

"Jaanan ki ringa hakuri dasu Eshaal yara ne sai a hankali, Ummu Ni na tafi" ya faɗa yana fice wa
Fuskarta ta kautar gefe dan bata son ganin sa haushin sa take ji kamar ta dake shi.

Tashi Ummu tayi tana raka shi tare da cewa "Allah ya tsare Hanya Yaron Kirki sai yaushe zaka dawo"

"Yau zan kai takwas ma za muyi baƙi a Office ɗin" yace yana buɗe motar sa

"Okay to Allah ya tsare ka kula da kanka"

"Insha Allah Ummunah" ya faɗa yana rufe motar tashin ta yayi ya fice daga gidan.


Sai da taga fitar shi sannan ta saki ajiyar zuciya ciki ta koma har yanzu Jaanan na zaune tana share hawaye Duka ta ɗaka mata a baya tana masifa
"Shegiya mai baƙin hali tashi ki shige kiyi abinda na saka ki, saura in ya dawo ki faɗa masa"

"Ummu mai zata faɗa masa bayan ba sonsa take ba ina taga damar sanar da shi abinda muka yi mata" Saabeer ya faɗa yana harar ta

"Sai na ji mata ciwo ai in ta faɗa ma, ba zaki tashi bane sai na buge ki da ƙafa ta ne" da hanzari ta miƙe tana shiga kitchen ɗin______________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم



𝑃𝑎𝑔𝑒 3🦋






Pasta ta dafa masa kamar yadda Ummu ta faɗa kawo masa tayi sai wani bata rai yake tashi yayi yaje ya fara ci sai complain yake wa Ummu akan girkin kiran Jaanan tayi ta mata masifa. Tasa shi Ummu tayi a gaba tana bashi da kyar ya cinye ya fita daga gidan.

Kamar jira take ya fita ta kira ta kamar ko yaushe tsugunawa tayi Ummu ce tace
"Karki ƙara yin tuwo a gidan nan, daga yau na soke shi"

"Tohmm Ummu Ina Sha Allah zan kiyaye"

"Jawaheer ta kusa dawowa ki ƙara gyara mata ɗaki kafin ta shigo, sai ki ɗora dinner"

"Tohmm, kafin in ɗora bari inci abinci"

"Me kika tafi yi side ɗin naki da baki ci abincin, ba kin san bana son ana haɗa cin abinci da aiki"

"Kiyi haƙuri Ummu"

"Ɓace min da gani, kuma saura ki zauna cin abincin karki yi aikin har inzo"
Sim-sim ta tashi kitchen ta nufa girkin ta ɗora kamar yadda ta faɗa sai ta wuce ɗakin Jawaheer tass yake ba abinda ya ɓaci zama kawai tayi duniyar tunani ta faɗa tunda ta Auri Tawfeeq Ummu ta maida ta kamar ba matar gida ba ta koma ƴar aiki duk irin gatan data samu a gida da Farkon Amarcin ta amma yanzu duk babu tana a wahala ga ko waya bata da ita balle ta kira ta sanar da gida halin da ta ke ciki yanzu duk ƴan gidan su sun tsane ta haka take gani, tunda suka kawo ta babu wanda ya kuma zuwa inda take har yanzu ko wani a gidan sa kira ya haɗa su amma shiru take ji tun tana sa rai har ta cire
"Ya Allah ka dubeni kawo mun Mafita da gaggawa" ta faɗa tana share hawayan fuskar ta tashi tayi ta shiga toilet wanke fuskar ta tayi ba jimawa ta fito palour ta nufa gurin Ummu ta sanar mata ta gama Thom kawai tace mata kitchen ɗin ta koma ta cigaba da girkin sai daf da Magariba ta gama hana ta tafiya suka yi wai ta jira Ummu tazo zata yi mata tausa. zaman jiran fitowar Ummu tayi har gurin takwas sannan ta fito har dare tana part ɗin Ummu gashi ko abinci bata ci ba daga su saka ta wannan sai wannan sunki barin ta ma ta zauna balle har ta huta sai da suka ga tara tayi sannan Ummu tace taje dan Tawfeeq ya kusa dawowa.


Around 10:00PM


Kwance take a kan gado ta lulluɓa da blanket ba'a ganin ko ina a jikin ta har kanta a rufe yake rawa jikin ta yake yi sosai turo ƙofar ɗakin aka yi shiru tayi tana jiran taji waye zai shigo sallamar sa taji ƙasa-ƙasa ta amsa
"Babe" yace shiru bata amsa ba cigaba da cewa
"Har kinyi bacci?"
"Jaanan Rigima har Fuskar aka rufe kenan" ya faɗa yayi tunanin ko fushi tayi dan ya mata faɗa ɗazu. kan gadon ya haura, a kusa da ita ya zauna buɗe fuskar yayi huci ne ya dake shi sai a lokacin ya lura da jikin ta da yake ta kyarma da sauri ya taɓa jikin ta zafi zau

"Subhanallah, Baki da lafiya ne? Me yasa baki kira ni ba" Ya faɗa a rikice

"Sanyi nake ji, ka lulluɓe Ni" ta faɗi Muryar ta na rawa

"Amma me yasa baki faɗa min ba, ko Ummu kika faɗa wa ta turo Jawaheer ta duba ki ai"
Shiru tayi masa. Tashi yayi ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo tare da Ummu da ɗaya daga cikin ƴammatan gidan da sauri Ummu ta ƙaraso kusa da ita tana taɓa jikin ta

"Innalillahi Daughter me ya same ki haka baki sanar dani ba" ta faɗa
"Jawaheer zoki duba ta, Allah yasa ba wani abu bane ya same ta, tunda ka fita ta taho bamu sake haɗuwa ba, na zata tayi bacci shiyasa ko neman ta banyi ba"
Matsowa tayi kusa da ita sai wani bata rai take dubata ta fara yi zafi taji jikin ta juyo wa tayi ta kalli Ummu sannan tace
"Ummu ina ganin muje asibiti naji jikin ta da zafi maybe Fever ce"
"Nima naji haka ya kamata gaskiya" ta faɗa tana maida kallo ta ga Tawfeeq sannan ta cigaba da cewa
"Tawfeeq ɗago ta ka kaita mota mu tafi, ke kuma Jawaheer muje ki saka Hijab ki bisu Ni in kin daɗe na biyo ku"

Ta faɗa tana yin gaba Jawaheer ce ta bita suka fice daga ɗakin. Drawer ya buɗe kaya ya ɗebo da hijab ya saka mata daukar ta yayi suka fita.


𝐇𝐎𝐒𝐏𝐈𝐓𝐀𝐋


Tunda suka zo aka karɓe ta da gaggawa ba jima wa sai ga Nurse ta fito daga ɗakin da suka shiga test ta tura su suyi. Lab suka nufa aka yi test ɗin suka dawo har gurin ɗayan dare suna ta zirga-zirga a asibitin.


Fito wa tayi daga ɗakin da aka kwantar da Jaanan ɗin Tawfeeq yana tsaye magana tayi masa Sannan ta wuce Office ɗin ta waya ta ɗauko daga jakar ta kira ta fara ba jimawa aka daga da sauri tace
"Ummu muna cikin Matsala"

"Matsala kuma? Wace iri" aka bata amsa daga can
"Ummu ciki ne da Jaanan"

"Wane irin ciki kuma Jawaheer ba mun gama da wannan matsalar

Please Login or Register in order to submit comment