Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana cewa "da gaske ne ashe baki taɓa zuwa Jigawa ba, Ina wayar taki take?" zee ta faɗa fuskar ta ɗauke da mamaki
"Ta lalace wllhy, waye ya faɗa miki ban taɓa zuwa ba" ta ce mata. Ummu ce ta fito daga dakin ta tana cewa

"Dauke ta ku wuce ɓangaren ki, kun ishe Ni da hayaniya"
Thom tace sannan ta kalli zee tace "tashi muje xan" ta faɗa tana Mike wa suka fice tsaki Ummu taja tana koma wa dakin ta......



Shigar su part ɗin zama suka yi Jaanan ta cigaba da cewa
"Waye ya faɗa miki ban taɓa zuwa ba"

"Aailah ce wllhy"

"Allah Sarki gidan kika je"

"A makaranta muka haɗu da kyar ma tayi min kwatance wai Ammi ta hana zuwa"

"Ammi kuma? Saboda me to"

"Eh haka tace min, wllhy ban sani ba"

Buɗe baki Jaanan tayi zata ce wani abu sai Saabeer ya shigo ko kallon baƙuwar da tayi bai yi ba ya hau cewa
"Aikin naki kika bari kenan? Kinzo sai hirar banza da wofi kike yi"

"Yanzu zata tafi zanzo in ƙara sa"

"Auuuuuu sai mun jira ta tafi zaki zo ki gyaran ɗakin, bacci zanyi yanzu kizo ki gyara"

Zuciyar Zee ce take ta tafasa ta san dai wannan ba shine mijin Jaanan ba dan sun ga mijin ta lokacin biki sai dai ƴan uwan sa. a zafafe da ɗago tana cewa"Ba zata zo ba kaje ka gyara da kanka ko kasa ƴan uwan ka su gyara mata"

"Ke kuma a wa? zaki tsomo baki a maganar ƴan gida"

"A ƙawar ta wadda ta kawo mata ziyara, wllh in baka fita ba zan Saba maka kammani yanzun nan"
Kallon ta yayi sai kuma yayi kwafa ya fice. Maida kallon ta tayi ga Jaanan wadda kanta ke ƙasa ta ce

"Yanzu irin wannan Rayuwar suka zaɓa miki Jaanan? Ke kike gyara wa kanin miji ɗaki?"

"Bari inje zee kar Ummu tayi faɗa"

"Wallahi ba zaki ba. Tsaya ma kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga inda kika zama? Ƴar aiki kika zama a gidan Mijin ki kenan"

Murmushin yaƙe tayi "Zee kenan bari dai inje"

"Ba inda zaki na gama magana, amsa ta ma zaki bani"

"Ya zanyi to, dole inbi Umarnin Ummu ƙawar Ammi ce tun suna ƙanana fa, yanzu in banyi abinda take so ba sai ran Ammi ya ɓaci"

"Ko zaki yi amma banda gyaran ɗakin kannen miji Jaanan, kin nuna kina tsoron sune wallahi" "kina son daina aikin nan?"

"Nafi kowa son daina wannan wahalar Zee"

"Dole ki cire tsoro ki nuna musu kenan ƴar zamani ce kuma aure kika zo ba bautar su ba, zaman mijin ki kike ba su ba"


Tunda Zee ta tafi ta faɗa duniyar tunani maganganun da suka yi ne ya tsaya mata a rai tana ganin gaskiyar Zee abinda take bai dace ba
"Lokaci yayi da zan dawo daga baccin da nake in farka, in nema wa kaina ƴanci" ta faɗa a fili tana ƙada kai, Tashi tayi ta wuce ɗaki wanka ta shiga tana fito wa ta tada sallar Isha tana idar wa ta fito dan nema wa kanta abinda zata ci yanzu ta fara jin yunwa jiyo motsin Tawfeeq tayi a ɗaki alamun ya dawo, kitchen tayi wucewar ta....


💕🤞✨


Saabeer yana fita ya je ya sanar wa Ummu ƙarya da gaskiya har da sun jefe shi. Zuciyar Ummu kamar ta fito Safa da marwa ta fara a palour tana jiran Jaanan ta shigo ta ci mata mutunci har gurin minti talatin babu Jaanan ba labarin ta cigaba tayi da zaman jiran zuwan ta har La'asar ba labarin ta ganin lokaci zai kure mata bata yi Sallah ba yasa ta wuce ɗakin ta tana idar wa ta dawo har bayan Magariba babu labarin Jaanan ga ko girki bata yi musu ba yau ba na rana ba na dare, dan lokacin da Zee tazo bata gama girki ba sai Ummu ce ta ƙara sa Su Jawaheer basa nan kowa yana gun aiki. Tashi tayi zata nufi side ɗin ta sai ga Tawfeeq ya shigo basar wa tayi ta koma ta zauna ƙara so wa yayi gurin ta yana gaishe ta sai kuma yace
"Ummu ina zaki da"

"Ɗaki zan shiga naga an kusa sallar Isha" ta faɗa tana sakar masa murmushi

"Eh bari nima in shige anjima na dawo"
"Sai ka dawo" ta faɗa. Tashi yayi ya fita da tsaki ta raka shi ji take kamar ta jawo shi ta zane ya ɓata mata shirin ta, ta so taje ta ciwa Jaanan mutunci kamar yadda ta ciwa Saabeer kaɗa kai tayi tana cewa
"Akwai gobe ai, Allah dai ya kamu" ta faɗa tana tashi zuwa cikin ɗakin ta________________✍️




# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



07077791941
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029Vahgkpx23n3caLhAso3Y



بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 8🦋



Washe gari


Da wuri Ummu ta tashi jira take har gurin goma yau ma ba labarin Jaanan ta fara tunanin ko ba lafiya amma ta san bata da lafiya da tuni Tawfeeq yazo ya sanar mata, ga tun ɗazu ya fice ma. shiru take ji kamar an aiki bawa garin su.
Tashi tayi ta nufi Part ɗin Jaanan.
Kwance ta same ta a palour idon ta a rufe kamar mai bacci amma idon ta biyu tun shigowar Ummu ta ganta ƙara luff tayi kamar me bacci. Da hanzari ta fita
"Idi, Idi" take ta takwala kira da sauri wanda aka kira da Idi ya ƙara so jikin sa sai ɓari yake "Hajiya gani" ya faɗa yan russina wa sai kace wanda zai mata sujjada dan girmama wa. Tsaki taja sai kuma ta cigaba da cewa
"Kaje bishiya ka tsinko min ice Wanda zai yi zafi in anyi duka"

"Hajiya ice kuma"

"Eh ice ko na Uban ka ne icen, get up ka tsinko min yanzu" ta faɗa tana jan tsaki. Da sauri ya tashi ba jimawa sai gashi ya dawo da dalbejiya masu yawa a hannun sa, ajiye wa yayi a kasa tana cewa "Hajiya ga su"

"Ka zaɓar min wadda zata fi zafi" jikin sa sai ɓari yake ya hau lalubowa miƙo mata yayi yana cewa "ga wannan In Sha Allah ba za'a samu matsala ba" a fusace ta karba tana komawa side ɗin su...

A kusa da ita ta tsaya ta zage ƙarfin ta ta narka mata dalbejiyar a gefen ciki tsitt bata motsa ba duk da dukan ya shige ta ƙara zagewa Ummu tayi ta duƙe ta a hargitse ta farka tana cewa
"Wannan wane irin hauka be mutum na bacci za'a wani dake shi" ta faɗa kamar bata lura da Ummu da take tsaye ba tayi sumar wucin gadi jin abinda Jaanan take faɗa kamar wadda aka zungura tace
"Lallai Jaanan wuyan ki ya isa yanka, Ni kike faɗa wa haka sai kace wata sa'ar ki? Ko Uwarki bata isa faɗan haka ba wllhy"

"Ummu ashe kece tafe barka da safiya, fatan kin tashi lafiya" ta faɗa dariya na cin ta amma ta dake

"Ban sani ba Jaanan" ta faɗa a fusace sai kuma ta cigaba da cewa
"Daga cewa kuzo nan keda ƙawar taki kun dame ni shine har yanzu baki dawo ba ko girkin dare baki yi ba balle aikin yau" Ummu ta faɗa kamar zata rufe Jaanan da duka

Ɗagowa Jaanan tayi ta kalli Ummu zuciyar tace ta harba dake wa tayi ta maida kanta ƙasa tana cewa "Ummu ba hakki na bane yi muku girki ba, kuma bani ya dace in ringa gyara muku ɗaki ba" ta faɗa tana rufe idon ta. Bata yi tsammin faɗa wa Ummu haka ba ko a mafarki gani take Ammi zata ji ba daɗi in taji tayi haka.
Ido Ummu ta gwalalo waje tana ƙada kai da jinjina maganar sai kuma tace "Wuyan ki ya isa yanka Jaanan" ta faɗa tana riƙe haɓar ta sai kuma ta cigaba da cewa "To ki sani kamar a bakin Hauwa kika yi maganar nan, in itace ai ba zata min haka ba" ta faɗa Muryar ta na rawa kamar mai shirin kuka

"Ammi daban ke daban Ummu, na gaji da wahalar gidan nan wllh Ummu aure nake amma kun mai dani yar aiki" ta ƙara sa faɗa tana yin ƙasa da Muryar ta
"Kin gaji kika ce koh, sai ki kama hanya ki koma can gidan ku ai". Ita ma Ummu ta faɗa a fusace
"Ummu ba inda zani tunda ba mijina ne yace in bar gidan nan ba wllhy" ta faɗa tana tashi fuuuuu ta wuce bedroom ɗin ta tare da bugo kofar da ƙarfi. Bin bayan ta da kallo Ummu tayi har ta shige data bugo kofar sai da Ummu ta tsorata kaɗa kai Ummu tayi ta fice fuuuuu daga part ɗin_____________✍️




# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Sai kunyi min uzuri kwana biyun nan ina busy bana samun damar typing da yawa 😩
Comments ɗin ku shine ƙarfin gwiwa ta Habibties🥰🌹



07077791941
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029Vahgkpx23n3caLhAso3Y


بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 9🦋


A bangaren Maah kuwa suma tayi su Aailah ne suka yi kanta Fa'oz kuka ya fashe da shi da sauri Faheem ya dauko waya Abu ya fara nema yana ɗaga kiran ko jiran sallamar da Abu yake yi masa bai amsa ba yace "Abu Maah ta suma fa" daga can Abu ya bashi amsa da "kuyi saurin ɗaukar ta ku wuce asibiti gani nan zuwa" Thom yace yana kashe wayar Aailah ce tace "Yah me yace"
"Yace mu haɗu a asibiti" tashi tayi ta fita ɗakin ta taje ta ɗauko Hijab tana dawowa ta tarar sun ɗauke ta ba kowa a wajen a mota suka saka kanta yana kan cinyar Aailah ba wanda suka faɗa wa a gidan suka nufi asibiti....


Asibiti...


Suna zuwa aka karɓe su dan Abu ya riga su zuwa Emergency aka yi da ita dan ta fara fita hayyacin ta likitoci Uku ne a kanta da kyar suka samu ta farfaɗo allura suka yi mata suka fito.
A waje gurin su Abu kowanne yana cikin rudani Aamilah da Fa'oz kuka kawai suke doctor ne ya fito ya nufe su Abu yace ya biyo shi kusan lokaci guda zuciyoyin su suka buga *kar dai ta mutu* shine abinda suka ayyana a ransu ƙarfin hali Abu yayi ya bi bayan doctor. A Office ɗin sa ya same shi yana zaune nuna masa gurin zama yayi yana cewa "have a sit Alh" daure wa yayi ya zauna yana kallon doctor jira yake kawai yace masa ta cika. Murmushi doctor ya saka kana ya fara cewa "mun samu ceto ranta ta farfaɗo yanzu tana bacci, amma da akwai babbar matsala"
Ƙatuwar ajiyar zuciya Abu ya sauke yana Hamdala sai kuma yace "mene matsalar" doctor ne ya nisa sannan ya cigaba da cewa

"Sakamakon damuwar da take ciki ga hawan jini da take fama da shi ciwon zuciya na barazanar kamata"

A firgice Abu ya kalli doctor "ciwon zuciya kuma" ya faɗa a matsanancin tashin hankali gumi ne ya fara keto masa, doctor ne ya cigaba da cewa

"Alamu sun nuna akwai abinda ta saka a rai ya kamata a nemo mata shi gaskiya" shiru yayi sai ya ƙara da cewa

"Ku kula sosai da ita kar a ringa ɓata mata rai komai na iya faruwa, Allah ya bata lafiya" Ameen kawai Abu ya samu damar faɗa itama bai san yaya aka yi ta fito daga bakin sa ba...
Jikin Abu a sanyaye ya tashi ya fita kawai Allah ne kawai ya kai shi inda suke suna nan a yadda ya barsu anan ya same su zaune jigum-jigum gaba ɗaya kansa suka yi ganin hanlin da yake ciki
"Ta mutu Koh" cewar Faheem "Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, Allah ya isa Yah Fawzan ka kashe mana Maah" Aailah ta faɗa tana fashe wa da wani marayan kuka, suma ragowar duk kuka suka fara, da ƙyar Abu ya tattaro maganar dake zuciyar sa yace "Bata mutu ba,tana raye zuwa Safiya zata farka yanzu tana bacci" ajiyar zuciya suka yi ta saukewa shiru ba wanda ya sake magana jigum-jigum suka cigaba da zama har safiya.....


Washegari


Da safe Maah ta farka doctor ya duba ta ya sanar da su ta tashi nan ne hankalin su ya fara kwanciya amma banda Abu da har yanzu a tsorace yake hana kowa shiga inda take aka yi, Gurin goma Abu ya kira Hajiya ya sanar da ita tsaki tayi sai daga baya tace Allah ya ƙara sauki, jin hakan daga bakin ta yasa shi kiran duk ƴan uwan sa ya sanar musu kar wani yace ba'a faɗa masa ba. Har gurin La'asar babu ƴan gidan su a gurin sai dangin Maah ne kaɗai a gurin ana sanar musu suka zo Mahaifiyar Maah tana gurin ta sha kukan ta ta koshi duk da ance ta tashi amma gani take karya ne tunda sun hana su shiga su ganta____________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Kuyi haƙuri da wannan ina Busy ne zuwa dare ko gobe zan cigaba.


07077791941
WhatsApp Only


Like, Comments & Share Fisabillah🥰👏


ADVERT👇

👉📱*OUM IKRAM DATA SERVICES*👉We offer you the best affordable and cheapest data😍

MTN
📲500MB➖ 150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖900
📲4GB➖1300
📲5GB➖1500
📲10GB➖4000
*461*4#

AIRTEL
500MB➖180
📲1GB➖350
📲2GB➖700
📲5GB➖1700
📲10GB➖3000
📲15GB➖4200
📲20GB➖5600
*140#

GLO
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖800
📲5GB➖1300
📲10GB➖2500
*127*0#

9MOBILE
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖500
📲3GB➖700
📲5GB➖1300
📲10GB➖2000
*228#

All are Valid for 30 Days


RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.


YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER 👇
07036133868


𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷



𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡



بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 10🦋


ᴀʀᴏᴜɴᴅ 9ᴘᴍ


Zaune a cikin ɗakin da aka kwantar da Maah bayan sallar Isha aka bar su shiga su ganta shima sai da Abu ya nema musu alfarma basu daɗe da shiga ba sai ga Hajiya da tawagar ta matar ƙanin Abu ce da babbar ƴar ta suka rako su sai yatsina fuska sai kace wanda taga najasa gaisawa aka yi sai suka duba Maah wadda bata daɗe da yin bacci ba. Bai fi minti goma ba sai ga Yayan Maah ya turo ƙofar ya shigo gaishe da Hajiya yayi kallon kowa yayi sai kuma yace
"Ku tashi mu tafi gida Koh" Babbar Mace ce tana zaune kusa da Mahaifiyar Maah tace tohmm, sai kuma Yayan ya ƙara cewa
"Wai ina Fawzan ne? Tunda nazo ban ganshi ba" Yayan Maah ya tambaya yana kallon Matar tasa. Hajiya ce tayi craf tana cewa

"Hmmmmm ina zaka ganshi ai shine musabbanin wannan matsalar"

"Kamar ya kenan, ban gane ba Hajiya?" Cewar Yayar Maah wadda take zaune kusa da mahaifiyar ta daga ɗaya side ɗin tana tashi tsaye a fusace

"Ya gudu shine ita kuma ta yanke jiki ta faɗi, yaron bashi da Kirki ko kaɗan" ta ƙara sa faɗa tana taɓe baki "Fawzan ɗin, to ina ya tafi"

"Yawon duniya mana"

"Ban san Fawzan da wannan halin ba Hajiya duk Soyyayar dake tsakanin sa da Mahaifiyar sa amma kice ya tafi yawon duniya, Fawzan yaron kirki, ki tuno dai inda ya tafi maybe tsufa ya fara kama ki"

"Mtwsssss shirme ba ga su nan ba ka tambaye su, duk sunyi tsuru-tsuru alamun rashin gaskiya" Hajiya ta kara faɗa tana watsa musu wani irin kallo,
Kallon Aailah Yayan Maah yayi yan jiran ta yi masa ƙarin Haske dauke kai tayi tana share hawayen fukar ta sai kuma ta hau cewa
"Abba faɗa suka yi da Hajiya ya bar gidan" Aailah ta faɗa tana ƙara yin ƙasa da kanta

Hajiya ce ta rafka salati tana tafa hannaye sai ta hau cewa
"Ni zaki wa sharri, saboda rashin mutunci ko uwar ki bata isa tayi min sharri ba wllhy bare wannan abar da take zaune a gefe" ta kara sa faɗa tana nuna mahaifiyar Maah
"Karki kuskura Wllh" Yayar Maah ta faɗa a fusace tana hararar Hajiya.


Abu ne ya turo ƙofar jin hayaniya duk ta cika asibitin ya daɗe a tsaye yana kallon drama da suke yi zuwa yayi ya musu sallama ya tafi tunda Mama anan zata zauna da ita har a sallame su, ba wanda yasan da zuwan sa sai Muryar sa data doke su lokaci guda
"Dubiya kuka zo ko faɗa kun cika asibiti da surutu, please ku fita ba'a san ayi mata hayaniya bacci take" ya faɗa a ɗan tsawace muryar sa a kausashe alamun ransa a ɓace yake kallon sa Hajiya tayi sai kuma taja tsaki tana cewa
"Ban san yaushe ka lalace haka ba Qasim ka zama sauna saboda mace, Allah dai ya kyauta" maida kallon ta tayi da ƴan tawagar ta da suka zo "sai ku tashi mu tafi Koh tunda ya kore mu" kamar jira suke duk sai gasu sun miƙe ba suyi wa kowa sallama ba suka yi ficewar su dan haushin juna ake ji. Miƙe wa matar yayan Maah tayi itama tana yi musu sallama ta fita Yayan Maah ne yace "Mama zamu tafi mu" "Allah ya tashe mu lafiya" tace masa "Aailah ku tashi ku bishi" Mama ta faɗa ɓata fuska tayi tana cewa "sai an sallame ta zan koma gida" kawai tace tana tashi ta nufi toilet su Fa'oz Mama ta sa shi ya tafi dasu tunda su sunyi yara________________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯


Kuyi haƙuri da wannan ina Busy ne zuwa dare ko gobe zan cigaba.


07077791941
WhatsApp Only


Like, Comments & Share Fisabillah🥰👏


ADVERT👇

👉📱*OUM IKRAM DATA SERVICES*👉We offer you the best affordable and cheapest data😍

MTN
📲500MB➖ 150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖900
📲4GB➖1300
📲5GB➖1500
📲10GB➖4000
*461*4#

AIRTEL
500MB➖180
📲1GB➖350
📲2GB➖700
📲5GB➖1700
📲10GB➖3000
📲15GB➖4200
📲20GB➖5600
*140#

GLO
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖800
📲5GB➖1300
📲10GB➖2500
*127*0#

9MOBILE
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖500
📲3GB➖700
📲5GB➖1300
📲10GB➖2000
*228#

All are Valid for 30 Days


RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.


YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER 👇
07036133868


𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡



بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 11🦋



Damaturu.


A can gidan Ummu kuwa Jaanan sabon salon rashin mutunci ta fito da shi duk wanda ya faɗa mata cuta sai ta faɗa masa mutuwa ta daina tsoron kowa a cikin su. In sun ga tana mutunta su to Tawfeeq ne yake gida koda wasa bata taɓa nuna masa akwai wani abu tsakanin ta da su ba. Ummu tana attempting faɗa masa abinda take musu sai kuma ta fasa. Saabeer har shakkar yi mata magana yake yi yanzu dan wani mugun tsoron tane ya shige shi tun ranar da yaji ta gayawa Ummu magana ta bangaje ta tayi wucewar ta.


Saturday,
8:50Am

Tafiya take a hankali fuskar ta a haɗe ranta a ɓace yake haka kawai yau ta tashi da fushi gashi Tawfeeq yace dole tazo gaishe da Ummu yanzu ba sai anjima ba tura ƙofar tayi ta ci Sa'a a buɗe take kanta tsaye ta shiga ciki ba kowa a Palour'n amma tass an gyara shi sabuwar mai aikin da Ummu ta ɗauko har ta gama aiki sama ta nufa zata ɗakin Ummu dan tasan yanzu dai bata sauko ba a daidai ƙofar tana ɗora hannun akan handle ɗin ji tayi kamar hira ake a ciki take ji ana yi fasa murdawa tayi ta kasa kunnen ta cigaba da cewa magana aka yi ana cewa
"Kashe ta kawai zamu yi tunda mun kasa samun damar ya sake ta, ga ko azabar kin daina mata"
Gaban Jaanan ne ya fadi "to wa zasu kashe?" ta tambayi zuciyar ta ohhhho ta bawa zuciyar Tata amsa ji tayi Ummu tace

"Gwara sakin akan kisa gaskiya, in aka kamamu fa kin san Tawfeeq da bin didigi dole sai ya nemi wanda ya kashe ta" ta faɗa tsaki ɗayar tayi tana cewa
"Ke kuma sai ki yarda ayi binciken ai yana cewa bincike zaki ce baki yarda ba"
Da sauri Jaanan ta juya jin kamar motsi za'a hawo sama sauko wa tayi zuciyar ta na bugawa da sauri tunanin wa zasu kashe ta fara a waje ta tarar da shi alamun fita zai yi tambayar ta yayi taje da ehh kawai ta amsa masa tana wuce wa ciki yayi mamakin ganin ta haka amma da yake yasan fushi take sai bai bi takan ta ba yayi ficewar sa. A kan gado ta faɗa ta fara tunanin wa zasu kashe zancen su zuciyar ta ta bata ita zasu kashe da kyar ta yarda da zancen zuciyar tata akan maganar. Tun daga lokacin raini ya ƙara shiga tsakanin ta da Ummu neman hanyar da za'a sake ta kawai take yi dan ba zata so ta mutu a cikin gidan ba gwara ta koma gida ta auri Fawzan ko me za'a yi sai dai ayi...



Fitowar ta kenan daga Part ɗin ta tayi kyau cikin shigar ta blue ɗin Abaya ce a jikin ta ta yane kanta da mayafin ta ba wata kwalliya tayi ba powder ce kawai a fuskar sai lipgloss da kwalli tana riƙe da jakar ta tafiya take a hankali sai kace wadda bata son taka ƙasa. Da kyar ta samu Tawfeeq ya barta taje gidan su Zee shima dan ya ga tazo mata ne da yawa ya yarda taje, tunda tazo gidan bata taɓa taka ƙofar waje da sunan fita unguwa ba. da sun fito Ummu take hana wa sai dai ta haƙura. Dai-dai zata wuce part ɗin Ummu taji an kwala mata kira basarwa tayi kamar bata ji ba ƙara kwala kira aka yi "Ke Jaanan" kamar daga sama aka kiran nata ɗaga kai tayi dan ganin waye yake kiranta dan yanzu duk sun daina kula ta basa shiga harkar ta ita kuma ta ƙyale banzaye dama wahalar suce take sawa su kira ta Ummu ce tsaye a balcony tana kallon ta fuskar nan a haɗe babu alamun wasa "Ki koma ciki ba inda zaki" ta faɗa a dakile kamar bata son magana wani kallo Jaanan tayi mata sai kuma tace "kamar ya in koma ciki Ummu?" ta faɗa tana ɗan hararar Ummu tana folding hannun ta a ƙirji tare da kaɗa ƙafa
"Yadda kika ji, ni kike harara, kizo yanzu" ta faɗa tana nuna kanta sai kuma ta koma ciki, tsaki Jaanan taja tana nufar Side ɗin Ummu bata kai ga ƙarasa sauko wa ƙasa ba dan haka ta nemi guri ta zauna tana jiran ta. Bata yi zaman minti ɗaya ba sai ga Ummu ta sauko sai huci take kallon ta tayi daga sama har ƙasa sai kuma tace

"Ina zaki" ta jefo mata tambaya tana tsare ta da idanun ta

Ɗagowa Jaanan tayi ta kalle ta ɗan bata ji shigowar ta palour ba sai magana kawai taji "Unguwa" Jaanan ta faɗa kanta tsaye ko shakkar Ummu bata ji ba
Kallon lallai yarinyar nan Ummu tayi mata sai tace "Ki koma ba inda zaki"

Ido Jaanan ta zaro ta samu wannan damar da zata fita sannan a hana ta chabbbbb tana kallon Ummu ido cikin Ido sai kuma tace "In na koma Allah ya tsine min ba Uban daya isa ya hana ni fita"

Tafa hannaye Ummu tayi tana cewa "Ok ni kike cewa ba wanda ya isa ya hana ki fita Koh"

"Eh ke ɗin, ko da abinda zaki yi"

"Zaki gani ne" Ummu ta faɗa kawai

Tsaki kawai Jaanan taja ta tana ɗaukar Jakar ta ta fice fuuuu daga part ɗin wani gwauron numfashi Ummu taja tana neman guri ta zauna bata yi aune ba ta jita a ƙasa ta faɗi______________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



07077791941 / 09047574404
WhatsApp Only


Like, Comments & Share Fisabillah🥰👏


ADVERT👇

👉📱*OUM IKRAM DATA SERVICES*👉We offer you the best affordable and cheapest data😍

MTN
📲500MB➖ 150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖900
📲4GB➖1300
📲5GB➖1500
📲10GB➖4000
*461*4#

AIRTEL
500MB➖180
📲1GB➖350
📲2GB➖700
📲5GB➖1700
📲10GB➖3000
📲15GB➖4200
📲20GB➖5600
*140#

GLO
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖600
📲3GB➖800
📲5GB➖1300
📲10GB➖2500
*127*0#

9MOBILE
📲500MB➖150
📲1GB➖300
📲2GB➖500
📲3GB➖700
📲5GB➖1300
📲10GB➖2000
*228#

All are Valid for 30 Days


RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.


YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER 👇
07036133868


𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷




Please Login or Register in order to submit comment