Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 12๐Ÿฆ‹

Bata sha wahalar zuwa gidan su Zee ba dan tayi mata kwatance kuma driver daya ษ—auke ta yasan gari har ฦ˜ofar gidan ya kai ta shiga tayi tana sallama da sauri Zee ta taso ta rungume ta cika ta tayi tana jan ta zuwa ciki, Babbar Mace ce zaune ta hakimce a kujera tana ta sakin murmushi ganin su, Zee ce ta hau cewa
"Na zata ai ba zaki zo ba, da na miki rashin mutunci gobe zamu koma Jigawa"

Kwace hannun ta tayi tana cewa "Irin wannan zuba haka, ki bari in zauna mana" ta faษ—a tana ฦ™ara sa wa kusa da Maman Zee a ฦ™asa kusa da kafar ta ta zauna tana gaishe ta amsawa tayi tana saka mata albarka ta tashi ta basu guri. zaman hira aka fara tana ta bata labarin jigawa da makaranta, har bayan Magariba tana gidan su Zee sai hira suke taji daษ—in fitar ta daga gidan sai da Mama tace dare yanayi sannan ta shirya driver su ya maida ita gida...

๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŸ๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŸ๐Ÿ’ฅ

A gidan Ummu kuwa Jaanan na fita ta dokawa Tawfeeq kira yayi maza ya dawo gida babu lafiya, yana zuwa ta hau ce masa Jaanan tayi mata dukan tsiya sannan ta fice daga gidan ita bata san ina ta nufa ba abin ya bashi mamaki kamar Jaanan da dukan Ummu yana ganin kamar haka ba zata kasance ba Ummu ce ta share hawayan sai ta ce

"Kaga nan baya na baka ji shi ba kamar ya karye wallahi Allah dai ya kwashe mata albarka" ta faษ—a tana nuna masa bayan nata shiru kawai yayi mata sai da yaji zata ฦ™ara magana sannan ya ce

"Ummu Allah ya sauwake bari ta dawo zan mata faษ—a In Sha Allah" yayi saurin faษ—a haษ—a rai tayi ta hau cewa

"Faษ—a ma zaka yi mata kenan ba saki ba, ina ce maka ka duba bayana ina tunanin na karye amma kana min zancen faษ—a zaka yi mata, maybe sai Jawaheer ta ษ—ora ni yau ฦ™ashin haฦ™arkarina kamar ya cire amma kana min wani zancen zaka yi mata faษ—a to sakin ta zaka yi"

Nan Ummu tayi ta bambamin masifa da bala'i dole sai ya saki Jaanan da kyar ta barshi yaje Sallar La'asar shima sai da yayi mata alkawarin yana dawowa zai bata takarda, har bayan Magariba bai dawo ba dan haka ta kafa ta tsare a kofar part ษ—in ta. Horn aka yi mai gadi ne ya buษ—e gate ษ—in a compound aka yi parking Jaanan ce ta fito daga ciki ganin Jaanan yasa Ummu sakin salati tana cewa "yawon banza kika tafi yanzu" ko kallon ta bata yi ba ta nufi part ษ—in ta "Jaanan" taji an faษ—a juyo wa tayi Tawfeeq ne yake shigowa
"Waya kawo ki" ya tambaye ta
ฦ˜aramar dariya tayi sai tace "Driver gidan su Zee ne, Maman ta ma tana gaishe ka" ta ฦ™arasa faษ—a ok kawai yace mata sai a lokacin ya lura da Ummu da take tsaye tana cika tana batse wa
"Bani takardar" ta faษ—a tana miฦ™a hannun ta

"Ummu ba yanzu ba dare yayi" ya faษ—a mata

"Ina wasa da kai, ka bani takarda ko ka sake ta inaji Yanzu ba da ษ“ata lokaci ba"

"Ummu ki bari da sai safe"

Saurin katse sa tayi tana cewa "Sai na ษ“ata maka rai ne Tawfeeq"

"A'a Ummu" shima ya faษ—a

"To Ka sake ta nace Tawfeeq, ai ba itace autar mata ba, in ka rabu da ita zaka samu wanda suka fita ba ma guda ษ—aya ba" ta karasa faษ—a tana watsa wa Jaanan wani kallo, ita dai Jaanan bata ce komai ba har a lokacin yana rike da kansa bai ce komai ba ta cigaba da cewa
"Sai na tsine maka ne Tawfeeq zaka sake ta, ina dalili kana gani baya ta karyan amma kaki sakin ta" da sauri ya matso kusa da ita yana riฦ™e hannayenta ya hau cewa

"Kar ki min haka Ummu ina matukar son Jaanan in kika rabani da ita mutuwa zanyi"

"kafi son mace a kaina Tawfeeq" tayi saurin faษ—a, Jawaheer na gefe tana kwasar dariya har da video take yi, numfashi yaja sai kuma yace

"Duk da ina son Jaanan har yanzu zan bi Umarnin ki Ummu" ya faษ—a yan share hawayen daya zubo masa sai kuma ya cigaba da cewa

"Jaanan na sake ki saki ษ—aya Allah yasa haka ya zame mana Alkhari"

Zaro idanun ta tayi waje zuciyar ta na bugawa da sauri duk da sakin take buฦ™ata a yanzu daya ce ya sake ta sai da taji kamar guduma aka daษ“a mata a tsakiyar ka lokaci guda yaji kamar an sara kanta biyu dafe kan tayi bata san lokacin da hawaye suka sauka a fuskar ta ba har rige-rigen zuba suke_________________โœ๏ธ

# ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท๐Ÿ‘ฏ

09047574404/07077791941
WhatsApp Only

Like, Comments & Share Fisabillah๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘

ADVERT๐Ÿ‘‡

๐Ÿ‘‰๐Ÿ“ฑ*OUM IKRAM DATA SERVICES*๐Ÿ‘‰We offer you the best affordable and cheapest data๐Ÿ˜

MTN
๐Ÿ“ฒ500MBโž– 150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–900
๐Ÿ“ฒ4GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1500
๐Ÿ“ฒ10GBโž–4000
*461*4#

AIRTEL
500MBโž–180
๐Ÿ“ฒ1GBโž–350
๐Ÿ“ฒ2GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1700
๐Ÿ“ฒ10GBโž–3000
๐Ÿ“ฒ15GBโž–4200
๐Ÿ“ฒ20GBโž–5600
*140#

GLO
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–800
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2500
*127*0#

9MOBILE
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–500
๐Ÿ“ฒ3GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2000
*228#

All are Valid for 30 Days

RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.

YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER ๐Ÿ‘‡
07036133868

๐”ฝ๐”ธ๐•‹๐”ผ๐•โ„ค๐”ธ๐”ธโ„โ„๐”ธโ„โœ๏ธ
๐Ÿ’ซ ๐— ๐—จ๐—ฅ๐—”๐——๐—œ๐—ก๐—” ๐Ÿ’ซ

An Imaginary Love Storyโค๏ธ

๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ ๐™ฐ๐™ฝ๐™ณ ๐š†๐š๐™ธ๐šƒ๐šƒ๐™ด๐™ฝ

๐™ฑ๐šˆ ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท

๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 13๐Ÿฆ‹

"Allah yayi maka albarka" ta faษ—a tana washe baki zuciyar ta tass burin ta ya cika. Jaanan ce tayi ฦ™arfin halin cewa
"Nagode Ummu Allah yayi min sakayya, Nagode da ba kashe ni kika yi ba kamar yadda kuka faษ—a gwara da kika saka ya sake ni" ta ฦ™ara sa faษ—a da ฦ™yar sakamakon kukan daya ฦ™ara kufce mata.

Da sauri ta juya ta nufi part ษ—in ta bata bukatar ฦ™ara jin komai daga baฦ™in su. Cikin Ummu ya bada wani ฦ™ululu dan bata san yaya aka yi taji plan ษ—in su ba, Tawfeeq ne yayi wa Ummu kallon ina bukatar ฦ™arin bayani bata ce masa komai ba, tayi saurin basar wa tana nufar part ษ—in ta, kamar zai bi bayan ta sai kuma ya fasa yabi bayan Jaanan. A ษ—aki ya tarar da ita tana ta kuka ganin ya shigo yasa ta tashi da sauri ta nufi wardrobe akwati ta janyo ta fara haษ—a kanyan ta zama yayi a gefen gado ya fara ce mata "kiyi haฦ™uri ba haka naso ba, ina zaki kike haษ—a kaya"

"Haka Allah ya ฦ™addara, gida zan tafi yanzu"

"Da daren nan Jaanan?,Ai na zata sai kin gama Idda ko Ummu zata haฦ™ura kafin lokacin in mai da ki wallahi ba a son raina aka yi haka ba"

Tsaya wa tayi da zuba kayan ta ce "Babu amfanin zama na, aure ne kuma ya ฦ™are dan haka gidan mu zan koma" ta faษ—a masa tana juyawa ta cigaba da zuba kayan. "To ki bari sai da safe sai in kaiki in bawa su Ammi haฦ™uri"
Bata ce masa ฦ™ala ba ta cigaba da haษ—a kayan ta sai. Yin duniya Tawfeeq yayi ta zauna sai ta gama idda amma taki karshe yace ta bari gobe zai kai ta da kansa tace bata so yau a Jigawa take son kwana. Dubawa yayi ko zai samu jirgin da zashi Jigawa yayi mata Booking ko da gobe da safe ne sai Allah yasa ya samu Flight wanda zashi Jigawa a ranar karfe goma na dare zai tashi a lokacin siya mata ticket ya sanar mata sai lokacin ta haฦ™ura zata jira time yayi ta tafi...

Thirty Minutes Later

Ta gama shirin ta tsaf komai ta haษ—a tana zaune a palour jira take ya dawo ya sauke ta yace ta jira shi. Bugo ฦ™ofar aka yi da ฦ™arfi da Sauri ta tashi ta nufa dan ganin wane yake bugowa. Ummu ta tarar turus a bakin ฦ™ofar taษ“e baki tayi ta koma cikin palour "me kike yi baki tafi gidan ku ba har dare yana ฦ™ara yi" Ummu ta faษ—a tana biyo bayan ta zuwa cikin Palour'n

"Zaman Idda Ummu" ta faษ—a ba tare data kalle ta ba

"Ko kin zauna ba zai maida ki ba kar ki saka rai dan zan Aura masa yarinyar kirki mai nutsuwa da tarbiyya" Ummu ta faษ—a

Wata irin dariya Jaanan ta kwashe da ita sai kuma ta hau cewa "karki wani ษ—aga hankalin ki nan da mintina kaษ—an zan tafi, nima ai ba zan so dawowa gidan wadda take neman rayuwa ta ruwa a jallo ba wadda take ฦ™oฦ™arin kashe ni" ta ฦ™ara sa faษ—a tana watsa mata wani kallo mai kama da gargaษ—i a harzuฦ™e Ummu tayo kanta da sauri Jaanan ta miฦ™e tsaye, Ummu ce a fusace tace
"Jaanan" ta faษ—a tana nufar ta tare da shaฦ™o wuyan ta.......

# ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท๐Ÿ‘ฏ

Kuyi haฦ™uri da wannan ina Busy ne zuwa dare ko gobe zan cigaba.

07077791941

๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 14๐Ÿฆ‹

"Haba Ummu mene haka ki cika ta" Muryar Jawaheer dake Laษ“e a can gefe ta ratsa kunnen su a bazata Ummu ta juya tana kallon ta bata san lokacin ษ—ata saki Jaanan ba tana cewa "Me kike yi anan Jawaheer?"
Bata ce komai ba ฦ˜araso wa tayi tana Jan hannun Ummu tare da cewa "Mu tafi Ummu, babu amfanin zama kina yi mata magana tunda kin raba su burin mu ya cika" ta karasa faษ—a tana hararar Jaanan. Buษ—e baki Ummu tayi zata yi magana Jawaheer tayi saurin rufe mata baki tare da jan hannunta suka fice daga part ษ—in. Faษ—awa cikin kujera Jaanan tayi tana sauke ajiyar zuciya...

Ba jima wa da fitar su sai ga shi ya shigo a zaune ya sameta ta zabga tagumi sallama yayi shiru bata amsa ba ya ฦ™ara wata, nan ma shiru bata amsa ba, a kusa da ita ya zauna yana kiran sunan ta a ษ—an firgice ta kalle shi sai kuma tace "Ka dawo?" "Eh" yace mata sai kuma ya ฦ™ara cewa "Me yake damun ki nayi ta sallama baki amsa ba" "Babu komai kawai mu tafi" ta faษ—a tana tashi da sauri tare da ษ—aukar wayarta ta fita, "It's Ok" ya faษ—a tare da ษ—aga kafaษ—a sai kuma ya tashi yaja akwatin nata ya fice. A bakin mota ya same ta tsaye buษ—e wa yayi suka shiga. Ummu tana daga balcony ษ—inta tana kallon ikon Allah Jawaheer ta hana ta magana wani iri take ji a cikin zuciyar ta yanayin gaba ษ—aya ba daษ—i a kan idon ta suka fice daga cikin gidan da sauri ta juya ta nufi ciki. Tsaki Jawaheer taja tana komawa ciki itama...
Suna fita daga gidan basu zarce ko ina ba sai airport zama suka yi suna jiran lokacin tashin nata yayi, kallon sa tayi a karo naba adadi ษ—auke kan tayi tana maida shi kan wayarta, gyaran murya yayi yana cewa "Lafiya kike kallo na?, kuma kin ฦ™i magana"
Girgiza kai tayi tana cewa "Ba komai fa" "Allah akwai" shima ya bata amsa ฦ™aramar dariya tayi tana cewa "dama cewa zanyi ba zaka koma gida ba kuwa? kar Ummu tayi faษ—a" ta ฦ™ara sa faษ—a tana kallon shi
ฦŠauke kansa yayi daga kallon ta yana cewa "In kin tafi zan koma ai ba kwana zan yi anan ba" jinjina kai tayi tana maida hankalin ta kan wayar tata.
Fara kiran su da aka yi ne ya sata saurin miฦ™e wa tana riฦ™e akwatin ta tashi tsaye yayi shima.
Magana ta fara muryar ta a raunace tana cewa "Nagode da soyayya da kulawa, Allah ya haษ—a ka da macen kirki wadda ta fini, ka cigaba da yi wa Ummu biyayya kar ka saษ“a wa umarnin ta" ba ta jira Abinda zai faษ—a ba tayi saurin barin gurin, da wani irin yanayi ya koma ya zauna kwalla na cika idon sa bai son yana matukar ฦ™aunar Jaanan ba sai yanzu Ummu ta raba shi da macen da yake tsananin kauna.
Har sai da jirgin su ya tashi sannan ya bar airport ษ—in yana jin wani irin kewarta, dan Jaanan macen ฦ™warai ce duk da bata son sa biyayya kawai tayi ta zauna da shi...

๐Ÿ…ณ๐Ÿ†„๐Ÿ†ƒ๐Ÿ†‚๐Ÿ…ด ๐Ÿ…ธ๐Ÿ…ฝ๐Ÿ†ƒ๐Ÿ…ด๐Ÿ†๐Ÿ…ฝ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ†ƒ๐Ÿ…ธ๐Ÿ…พ๐Ÿ…ฝ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ…ป ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ…ธ๐Ÿ†๐Ÿ…ฟ๐Ÿ…พ๐Ÿ†๐Ÿ†ƒ, ๐Ÿ…น๐Ÿ…ธ๐Ÿ…ถ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ††๐Ÿ…ฐ ๐Ÿ†‚๐Ÿ†ƒ๐Ÿ…ฐ๐Ÿ†ƒ๐Ÿ…ด.

A hankali take fitowa daga cikin jirgin riฦ™e take da waya a hannun sai hand bag dake rataye a kafaษ—ar ta numfashi ta fesar tana sakin murmushi ฦ™arasa sauko wa tayi, akwatinta ta ษ—auko tana nufar parking space nan ta tari Cab tana shiga faษ—ar inda za'a kaita tayi suka fice daga airport ษ—in..
A ฦ™ofar gidan yayi parking fitowa tayi tana jan akwatin ta Kallon Unguwar tayi dare ne sosai amma ko ina haske wani irin abu ne ya daki zuciyar ta lokaci guda tana matuฦ™ar tsoron haษ—uwa da Ammi ga wani irin son Fawzan daya ฦ™ara shiga ranta, kusa da gate ษ—in gidan ta ฦ™ara sa tana kwankwasawa rungume wayarta tayi a ฦ™irgin ta tare da cewa "Alhamdulillah gida me daษ—i, zan haษ—u da My camp after a year"___________โœ๏ธ

Wai ina Fawzan ne Jama'a ๐Ÿ˜Œ๐Ÿƒ.....

# ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท๐Ÿ‘ฏ

Kuyi haฦ™uri da wannan ina Busy ne zuwa dare ko gobe zan cigaba.

07077791941
WhatsApp Only

Like, Comments & Share Fisabillah๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘

ADVERT๐Ÿ‘‡

๐Ÿ‘‰๐Ÿ“ฑ*OUM IKRAM DATA SERVICES*๐Ÿ‘‰We offer you the best affordable and cheapest data๐Ÿ˜

MTN
๐Ÿ“ฒ500MBโž– 150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–900
๐Ÿ“ฒ4GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1500
๐Ÿ“ฒ10GBโž–4000
*461*4#

AIRTEL
500MBโž–180
๐Ÿ“ฒ1GBโž–350
๐Ÿ“ฒ2GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1700
๐Ÿ“ฒ10GBโž–3000
๐Ÿ“ฒ15GBโž–4200
๐Ÿ“ฒ20GBโž–5600
*140#

GLO
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–800
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2500
*127*0#

9MOBILE
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–500
๐Ÿ“ฒ3GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2000
*228#

All are Valid for 30 Days

RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.

YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER ๐Ÿ‘‡
07036133868

๐”ฝ๐”ธ๐•‹๐”ผ๐•โ„ค๐”ธ๐”ธโ„โ„๐”ธโ„โœ๏ธ
๐Ÿ’ซ ๐— ๐—จ๐—ฅ๐—”๐——๐—œ๐—ก๐—” ๐Ÿ’ซ

An Imaginary Love Storyโค๏ธ

๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ ๐™ฐ๐™ฝ๐™ณ ๐š†๐š๐™ธ๐šƒ๐šƒ๐™ด๐™ฝ

๐™ฑ๐šˆ ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท

๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 15๐Ÿฆ‹

Mai gadi ne yazo ya buษ—e mata jikin sa sai tsuma yake kan sa ya leฦ™o ganin mace ce ya sa shi sauke ajiyar zuciya hanya ya bata alamun ta shigo a hankali ta shiga cikin gidan sai sauke numfashi take a kusa da shi ta tsaya ganin kamar bai gane ta ba yasa ta cewa
"Baba lafiya na ganka haka?, Baka gane Ni bane? Jaanan ce fa"
ฦ˜ara kallon ta yayi da kyau tare cewa "Jaanan kece a daren nan? Ina Mijin naki?"
"Yana gida" tace tana wuce wa ciki shiru alamun kowa bacci yake yi. A bakin part ษ—in su ta tsaya a hankali ta kwankwasa ฦ™ofar ta ci sa'a lokacin Jumaymah ta fito shan ruwa taji kamar an taษ“a ฦ™ofar kitchen ta shiga ta ษ—auko ruwan tana fitowa taji kamar an ฦ™ara bugawa agogo ta kalla ganin lokaci yasa ta zare ido tana cewa "Da tsohon daren nan? Waye kuma? Allah yasa dai lafiya" ta raya a zuciyar ta, ฦ™ofar ta nufa dan ganin wane yake bugawa tana buษ—e ฦ™ofar taci karo da Jaanan tsaye "Yaya" ta faษ—a da ษ—an ฦ™arfi da sauri Jaanan tasa hannunta ta toshe mata baki "Kiyi shiru" ta faษ—a tana shigowa tare da cika mata bakin "Ya na ganki da tsakar daren nan?, ษ—aya ta wuce fa" Jumaymah ta faษ—a karษ“ar akwatin tayi daga hannun Jaanan, Jaanan ce ta cigaba da cewa "Labarin da tsaho mu shiga ciki bacci nake ji" "Ok" ta faษ—a suna shiga cikin ษ—akin Jumaymah....

AฬธSฬธUฬธBฬธAฬธHฬธ

Tana idar da sallah ta fito palour dan tana son suyi magana da Papa kafin ya fita Office, ga Jumaymah ta takura mata da zancen me yasa ta zo gida shiru kawai tayi mata dan ta rasa me zata ce mata. zaman jiran shi tayi bata daษ—e da zama ba sai gashi ya shigo truss ya tsaya ganin ta zaune ฦ™asa ta sauko ta zauna tana gaishe shi bai amsa ba ya hau ฦ™walawa Ammi kira "Kizo ga Jaanan"
da hanzarinta ta fito tana cewa"Jaanan kuma?"
"Eh ita fa" itama truss tayi ganin ta a zaune "Yaushe kika zo ban sani ba?" Cewar Ammi
"Anan na kwana tsakiyar dare nazo" Jaanan ta faษ—a
Papa ne yace "Kwana kuma? Meya faru kika baro gidan ki?"
"Ya sake ni Papa" ta bashi amsa kanta a ฦ™asa
Dukar zuciyar su maganar tata tayi harษ—e hannun sa yayi a kirji yana sauke numfashi sai kuma ya zauna yana cewa "Tashi ki koma ciki in Safiya tayiza muyi maganar" Thom tace tana miฦ™e wa ta shige ษ—aki. Guri Ammi ta samu ta zauna "Saki" ta maimaita kalmar dan ta tsaya mata a rai......

๐Ÿ’ฃ๐Ÿ’ฅ ๐Ÿ’ฃ๐Ÿ’ฅ ๐Ÿ’ฃ๐Ÿ’ฅ

Washegari

10:00ฮฑษฑ

Zaune suke a cikin Palour tsit baka jin ฦ™arar komai sai Muryar Jaanan da take magana tana kuka shiru tayi alamun ta kai ฦ™arshen zancen jigum-jigum duk suka yi Hajiya ta zabga Uban Tagumi jikin su duk yayi sanyi jin halin da ฦดar su ta shiga babu wanda ya taษ“a neman ta a cikin su, Hajiya ce ta ฦ™ore shirun nasu da cewa
"Ya sake ki fa kika ce Jaanan? anya ba gudo wa kika yi ba?" Hajiya ta maimaita. Gyaษ—a musu kai tayi "Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, Ina Ummu take har ya sake ki bata hana ba?" Ammi ta faษ—a ta kallon Jaanan ษ—in
Jaanan ce ta ษ—ago ta kalle ta sai kuma ta sunkuyar da kanta tana cewa "Ammi tana nan nace miki ita ta saka ya sake ni".....

โ™กฦ‘ฦ›ฦœศคฦ›ฦโ™ก
_____________โœ๏ธ

# ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท๐Ÿ‘ฏ

09047574404 / 07077791941
WhatsApp Only

Like, Comments & Share Fisabillah๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘

ADVERT๐Ÿ‘‡

๐Ÿ‘‰๐Ÿ“ฑ*OUM IKRAM DATA SERVICES*๐Ÿ‘‰We offer you the best affordable and cheapest data๐Ÿ˜

MTN
๐Ÿ“ฒ500MBโž– 150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–900
๐Ÿ“ฒ4GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1500
๐Ÿ“ฒ10GBโž–4000
*461*4#

AIRTEL
500MBโž–180
๐Ÿ“ฒ1GBโž–350
๐Ÿ“ฒ2GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1700
๐Ÿ“ฒ10GBโž–3000
๐Ÿ“ฒ15GBโž–4200
๐Ÿ“ฒ20GBโž–5600
*140#

GLO
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–600
๐Ÿ“ฒ3GBโž–800
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2500
*127*0#

9MOBILE
๐Ÿ“ฒ500MBโž–150
๐Ÿ“ฒ1GBโž–300
๐Ÿ“ฒ2GBโž–500
๐Ÿ“ฒ3GBโž–700
๐Ÿ“ฒ5GBโž–1300
๐Ÿ“ฒ10GBโž–2000
*228#

All are Valid for 30 Days

RECHARGE CARD, CABLE SUBSCRIPTION AND ELECTRICITY BILL ARE ALSO AVAILABLE.
AFTER THAT ALSO WE DO GRAPHICS DESIGN TO DECORATE YOUR BUSINESS WITH LOGO/FLYR AND YOUR INVITATION CARD.

YOU CAN CONTACT ME VIA THIS PHONE NUMBER ๐Ÿ‘‡
07036133868

๐”ฝ๐”ธ๐•‹๐”ผ๐•โ„ค๐”ธ๐”ธโ„โ„๐”ธโ„โœ๏ธ
๐Ÿ’ซ ๐— ๐—จ๐—ฅ๐—”๐——๐—œ๐—ก๐—” ๐Ÿ’ซ

An Imaginary Love Storyโค๏ธ

๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ ๐™ฐ๐™ฝ๐™ณ ๐š†๐š๐™ธ๐šƒ๐šƒ๐™ด๐™ฝ

๐™ฑ๐šˆ ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท

๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก

ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…

๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 16๐Ÿฆ‹

โ™กฦ‘ฦ›ฦœศคฦ›ฦโ™ก

A bangaren Fawzan yana fita daga gida bai zarce ko ina ba sai gidan wani Abokinsa YASAR. Rashin jin magana ta lokacin yarinta duk tare suke shi yana shaye-shaye amma Fawzan baya yi sau ษ—aya ya taba ya daka ta tasu yayi shima lokacin Birthday ษ—in sa ne ya dawo gida a buge ranar Maah tayi masa mugun duka sai da yayi cuta. Tun daga nan ya rabu da shi bai kara kula shi ba. shine Dalilin da ya sa su Hajiya suke ce masa ษ—an shaye-shaye. Rabon shi da shi tun da suka gama secondary school sai kwanaki suka haษ—u shine yasan yana garin yazo har gidan sa.

A ฦ™ofar gidan ya tsaya horn ya danna maigadi ne yazo ya buษ—e masa a guje a shiga gidan fito wa yayi daga motar da sauri mai gadin yazo gurin sa Yana gaishe sa bai amsa ba yace
"Yana ciki?" Eh yace da ษ—an gudu ya shiga cikin gidan. Ba wani babban gida bane palour ne madaidaici babu kowa a ciki sai ฦ™arar TV da take tashi wucewa yayi zuwa bedroom

Please Login or Register in order to submit comment