Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba"

"Wallahi Ummu ciki ne da ita wata Uku, nima nayi mamaki"

"Da gaske kike Jawaheer?"

Dan jim tayi sai kuma ta cigaba da cewa

"Ummu zan Miki karya ne har test sai da nasa aka tura mu dan in ƙara tabbatar wa, Ummu in kun lura da yanayin ta kwana biyu zaki ga ta fiya kasala"

"Duk abinda nayi ya tashi a banza kenan Jawaheer"

"Haba Innnnnnaaaaa dole mu san mafita Ummu, ita ma munafuka kullum cewa take bata sonsa ta tsane sa, ko ya aka yi yayi mata ciki ma?"

"Ai sai dai a tambaye shi, kin sanar da shi ne?"

"A'a ya za'a yi na faɗa masa banyi wannan gangancin bama"

"Good Girl, kafin safiya zanyi tunanin yadda za'a yi, yanzu ki koma kar yayi tunanin wani abu"

"Tohmm Ummu" ta faɗa tana kashe wayar. Koma wa tayi gurin Tawfeeq ɗin.



✨😍🌟



Part ɗin da saurayin ya shiga wanda ya kira da Fawzan ya nufa shima nan ya shiga katon palour ne sai Bedrooms guda biyu da kitchen babu kowa a Palour'n kai tsaye kofar da ya gani a buɗe ya nufa ɗakine tarar da shi yayi a tsaye yana cire kaya
"Sai kazo Hajiya na kiran ka ai" kawai ya faɗa yana jan ƙofar ya tafi. Tsaki yaja yana Ƙara sa cire kayan toilet ya shiga ba jima wa sai gashi ya fito da hanzari ya shirya ya fita. Kai tsaye Part ɗin Hajiya ya nufa katon Palour ne da kujeru set biyu a ciki.


A Palour'n ta ya tarar dasu har da Maah tunda ya ganta yasan Maganar ta girmama dan bata taɓa shiga sha'anin gidan nasu in ka ganta ko lallai a cikin ƴaƴan nata wani yayi laifi za'a yi mata tass kenan "a yanzu wannan rayuwar da suka yi a baya ta wuce da za'a zagar musu mahaifiya a gaban su duk wanda ya fadi A akan ta sai ya rama mata" ya faɗa a ransa. Zama yayi a cikin Ɗaya daga cikin kujeru palourn. Wani Babban mutum a cikin su ne yace

"Kaima a sama zaka zauna Kamar wani sa'an mu?"
Banza yayi masa bai ce komai ba, saukowa ƙasa yayi ya zauna kusa da kafar Kabiru (wanda ya kira shi ɗazu).

Babbar Mace ce dattijuwa a ƙalla zata kai shekaru saba'in itace mahaifiyar suce suna kiran ta Hajiya. Fara cewa tayi"Wai mene matsalar ka? Me yake damun ka? Tun ɗazu muna jiran ka baka zo ba sai da ka gama duk abinda kake sannan kazo ka shanya mu sai kace ƴaƴan ka"

"Ai da ya zo wanka ya same ni zanyi sai in fito in taho Nan kenan ba tare da nayi wankan ba?" Ya bata amsa cikin gadara

"Mtwsssss wankan banza, kiran da neje maka baifi wankan banza da wofi ba, Mene matsalar gidan nan da baza ka kwana a ciki ba, shaye-shayen da muka saka dainawa kake son dawowa da shi Koh Fawzan?" Cewar Hajiya

"Wai wa yace miki shaye-shaye nake? Ni ba abinda yake damuna, kawai rayuwar ce ta juya min baya shiyasa nima na juya mata nake abinda naga dama dan ba wanda ya isa dani yanzu" ya bata amsa kansa tsaye

"Baka da hankali Koh Fawzan Hajiyan kake faɗa wa wannan maganar?" Baban sa ne ya faɗa a zafafe

"Abu meye dan na faɗa mata haka ai ita ta zubar da girman ta" shima ya bashi amsa

"Uwarka, nace Uwarka sa'ar kace ita da zaka ringa faɗa mata waɗannan maganganun"Abu ya ƙara faɗa
"Ƙyale shi Qasim, ya isa ne ya kai matsayi, da bata daure masa gindi ba ai ba zai yi min rashin kunya ba" ta faɗa tana nuna Mahaifiyar Fawzan wadda ta sunkuyar da kanta tunda ta shigo bata ce komai ba

"Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, Fawzan bana son kana haka yin iyayen ka ne, baka da kamar su duk duniya, ka basu haƙuri kar ka sake" ta faɗa tana kallon Fawzan ɗin

"Maah" ya faɗa. Ɗaga masa hannu tayi tana cewa
"Haƙuri nace ka basu kawai" ta faɗa tana haɗe rai

Girgiza kai ya fara yana cewa"Gaskiya Maah ba zan iya ba, sun Aurar da Masoyiya ta bada san ranta ba sannan suke tunanin akwai wani abu tsakanina dasu? Sun bata wanda bata so Sannan suka kai ta wani gari wanda bata da kowa a can, a cikin ku ba wanda ya taɓa zuwa ziyarar ta ko ƴaƴan ku baku taɓa tura wa suga a wane halin take ciki, kun kwance mata waya duk saboda ku tozarta ta, Haba ban taɓa tunanin bakwa son Jaanan ba sai yanzu"________________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



بسم الله الرحمن الرحيم


𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️



𝑃𝑎𝑔𝑒 4🦋



Hajiya ce ta cigaba da magana a fusace"Ai bai san wannan ba yanzu, bayan kin ɓata shi yaro ya zama ɗan iska sai shaye-shaye shi kaɗai ya sani sai bin abokan banza"

"Duk cikin gidan nan babu Wanda kuka sawa ido sai ni? Duk irin rashin mutuncin da su Aaban suke yi baku gani Koh? Sai ni kuka hana Ni Jaanan kuka aura mata wani daban duk irin rokon dana yi muku"

"Wane Uba ne zai bawa ƴar sa yaro kamar kai?, bari kaji ko Kabiru ya amince zai baka auren Jaanan Ni ba zan yarda ba Jaanan ba zata auri dan iska ba" ta faɗa masa

"Yanzu ai mutumin arziki kuka Aura mata koh Hajiya?" Shima ya bata amsa

"Fawzan tashi ka ɓace min da gani yanzu, na gaji dajin maganganun nan" Maah ta faɗa a wani irin yanayi
Ɗagowa tayi ta kalli Hajiya sannan tace
"Hajiya kiyi haƙuri zan masa faɗa Insha Allah" ta faɗa tana jan shi su fice
Maah mace ce wadda bata son hayaniya, tana da kawaici sai Kayi mata abu ko kallon ka baza ta yi ba amma tana da zafi in ta tara ka. Duk gidan sun san halin ta shiyasa suke mata yadda suka ga dama musamman Hajiya
"Ai dama haka zaki ce, Qasim ka auro mana jaraba kuma ka haifi jaraba yaro ba tarbiyya, Hhuummm Allah ya Kyauta" ta faɗa wa Maah dai-dai tana buɗe Ƙofa maganar ta shiga kunnen ta.
Da Amin suka yi ta amsawa, da ɗaya da biyu duk suka fice palourn ya dawo daga Kabiru sai Hajiya. Shima miƙewa yayi yana cewa
"Bari naje na shirya in wuce gurin aiki na kusa makara"
"ba dole ka kusa makara ba, Allah ya tsare hanya" da Amin ya amsa yana fita shima. Tashi tayi ta shiga ɗakin ta.


Fawzan kuwa suna fita ya kwace hannun sa daga cikin na Maah
"Me yasa kika fito dani"
"Na fison kullum ka kasance yaron kirki Fawzan ko zasu yi alfahari da kai wataran, na rasa abinda nayi wa Hajiya ta tsane ni da ku bacin da ba haka take min ba, please karka ƙara yin abinda kayi"
"Insha Allah Maah daga yau ba abinda zai ƙara faruwa ba zan ƙara bata miki rai ba" ya faɗa yana sakar mata murmushi itama murmushin ta maida masa tana cewa
"That's Good My Son, Allah ya maka Albarka kaje ka huta"
"Ameen Maah Tohmm" ya faɗa yana wuce wa part ɗin sa. Maah ma part ɗin ta ta nufa dan hayaniyar gidan tana wahalar da ita da gaji gwara ta shirya ta wuce aiki kafin su kuma ɓullo da wata matsalar take ayyana wa a ranta tana shiga part ɗin ta...



Yana shiga ɗaki yayi stool ya janyo ya ajiye a gaban wardrobe hawa yayi akwati ya dauko a saman wardrobe ɗin sauko wa yayi ya buɗe wardrobe ɗin kaya ya fito dasu ya zuba a akwatin rufe ta yayi tare da janya da karfi har yana tuntube ya fice.

Fitowar sa ce yaja hankalin mutanen da suke compound ɗin be kula kowa ba ya ƙara sa kusa da motar da ya buɗe booth wata budurwa ce ta ƙaraso gurin sa tana cewa
"Yah Fawzan ina zuwa da safe na ganka da akwati"
"Baki da haɗi da inda zani Aamilah" ya faɗa mata Bata ƙara ce masa komai ba ta nufi part ɗin Hajiya.

"Fawzan ina zaka kuma" cewar Maah da take fitowa daga part ɗin ta zata tafi aiki
"Bar musu gidan su zanyi na gaji da zama Maah, shine kawai mafita da bazan ƙara saba Miki ba" ya faɗa a taƙaice yana sa akwatin tare da rufe booth ɗin.

"Ai baka da inda yafi nan" cewar Hajiya wadda ta fito a fusace daga part ɗin ta
"Ina da shi mana kuma zaki gani" ya faɗa yana zagaya wa ya buɗe motar tada ta yayi yay ficewar sa yana baɗa musu ƙura ba tare da kara wai wayar su ba.....


🫧🔥🫧🔥🫧


Zagaye ɗaki ta fara yi dunkule hannun ta tayi tana dukan ɗayan "menene abin yi" ta faɗa da sauri kuma ta janyo wayar ta kira tayi ringing baifi biyu ba aka ɗaga
"Lafiya kika kira ni da wannan daren ƙawa" aka faɗa daga can
"Ba lafiya ba, duk irin kullin da muka yi amma wai ace kaii innaaa" ta faɗa kamar zata yi kuka
"Me ya faru wai bana so Alhaji ya farka"aka ƙara bata amsa

"Jaanan ce take da ciki"

"Ciki kuma?" "Zubar da shi kawai za'a yi ƙawa in aka barshi kin kaɗe Bahija ta gama dake"

"Innaa bata isa gama wa dani ba, nawa take"

"Gashi kuwa, Ni bansan me yasa kika aura wa Tawfeeq Jaanan ba"

"Ƙaddara ƙawa, ƙaddara ce da rabon cikin nan wllh"

"Ba wani rabon ciki Zubar da shi kawai za'a yi kowa ya huta"

"Ba kyau ganin da matsala in an zubar kar a gane"

"Ai ba wanda za'a faɗa wa bare a gane, Tawfeeq ɗin ya san da shine?"

"Bai sani ba"

"Da sauƙi kawai ki kira Jawaheer ɗin kice su zubar"

"Tohmm bari in kira su in faɗa musu"

"Yauwa ai haka za'a yi ma, da safe zan kira inji ya kuka ƙare" ta faɗa tana kashe wayar. Zama tayi akan gado zare wayar tayi daga kunnen ta tunani ta shiga can sai ta janyo wayar huɗu saura agogo ya nuna mata number Jawaheer tayi dailing har ta katse ba'a ɗaga ba ƙyale ta tayi watakila tana wani aikin tana ajiye wayar.



Around 4:00AM



Zaune suke ita da Tawfeeq tunda suka zo basu rintsa ba suna zaune a ɗakin da aka kwantar da ita ruwa ake ƙara mata tayi-tayi da shi su tafi Office ɗin ta su zauna yaƙi dole yasa ita zama ta zauna anan ɗin kira ne ya shigo wayar ta tashi tayi tana ce masa
"Bari inje in dawo" jinjina mata kai kawai yayi da sauri ta fice Office ɗin ta taje kiran har ya katse ƙara kira tayi tana ɗagawa daga can Ummu tace
"Na yi tunani mai zurfi Jawaheer kawai gwara a zubar da cikin kafin ma ya sani"

"Zubar wa Ummu? Kar a samu matsala ta mutu zan rasa aiki na fa"

"Banza yanzu sai ki yarda a samu matsala har ki rasa aikin ki, bari kiji gwara ki rasa wannan aikin da in bari Jaanan ta haihu zaki samu wani ai"
"Gaskiya Ummu ina son aiki na fiye da komai a yanzu kawai ki chanja wata Shawarar banda wannan"
"Ni kike faɗa wa haka Jawaheer kina son aikin ki, to ki cigaba da son aikin naki ina kallo Jaanan ta haihu ke ko Aure baki yi ba"_________________✍️








# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel



https://whatsapp.com/channel/0029Vahgkpx23n3caLhAso3Y


بسم الله الرحمن الرحيم



𝑃𝑎𝑔𝑒 5🦋


_______________________________________________________________________________________________________________



Maah ce zube a kasa kuka ta fashe da shi tana surutai
"Haka zamuyi da kai Fawzan tafiya zaka yi ka barni a halin da nake ciki" shine abinda take ta faɗa
Da sauri wata budurwa ta fito daga part ɗin da Maah ta fito a guje ta ƙara so kusa da ita tana riƙe ta
"Maah! Masu!! Maah!!!" Ta faɗa da ƙarfi a guje ta nufi inda take, mutanen gidan ne suka fara fito wa. Tana zuwa ta riƙe ta, ɗora ta akan cinyar ta tayi"Maah" ta faɗa hawaye na kwararowa daga fuskar ta da sauri mutanen gidan suka yo kansu.
Abu ne ya fito daga Cikin part ɗin shima da sauri ya ƙara so kan su yana cewa
"Lafiya Aailah, meke faruwa"

"Abu Maah ce ta suma, ga Yah Fawzan ya bar gida"

"Ya bar gida kamar ya?, Ina Faheem"
Wani daga can gefe ne yace "Abu gani"

"Zo ku ɗauke ta daga nan wurin" ya faɗa yana wuce wa gurin Hajiya

"Tohmm" yace yana ƙara so wa, ɗaukar ta suka yi zuwa ciki.

Gurin da Hajiya take ya nufa ko ƙara sa wa baiyi ba ta hau faɗa tana cewa

"Qasim ka haifa mana jaraba, ina Magana da yaron nan amma ya buɗa min kasa a ido yayi wucewar sa, bashi da inda yafi nan dai"

"Wai Hajiya mene haka kuke yi, da sanyin safiya sai faɗa duk maƙota suna jin mu"

"Kai ka damu da su Qasim, tunda kana da yaro kamar Fawzan dole ka ringa kare shi ba kwa son laifin sa ko kaɗan"

"Hajiya kiyi haƙuri ki koma ɗaki"
Da kyar suka lallaɓa ta ta shige ciki sai faɗa take. Wasu daga cikin mutan gidan sai murna suke Fuskar su wasai sunji daɗin lamarin


A cikin part ɗin Maah kuwa a bedroom suka kwantar da ita Aailah tana kusa da ita sai kuka take. Abu ne ya shigo zama yayi akan kujera Doctor ya kira azo a duba ta ba jimawa sai ga doctor yazo allurai yayi mata ba jima wa tayi bacci shawarwari ya basu sannan ya tafi har lokacin Aailah bata daina kuka ba. Faheem sai trying numbers din Fawzan yake amma switch off. Abu police ya kira ya sanar musu har dare shiru babu batun ganin Fawzan. Hajiya tazo ta musu tass akan Fawzan.

A bangaren Hajiya kuwa yini tayi tana faɗa. Wasu a gidan suna bata baki ta yi hakuri wasu tunzura ta suke yi akan maganar taje tayi faɗa zuwa tayi ta musu faɗa harda gorin ba yaro mara kunya a gidan kamar Fawzan Allah yasa Maah ta mutu su huta. Tana gama faɗan tayi tafiyar ta ko bi takan Abu da yake bata hakuri bata yi ba.



𝑫𝒂𝒓𝒆
9:00 𝒑𝒎


Zaune suke gaba ki ɗayan su a ɗakin har da yara guda biyu masu tsananin kama da Fawzan mace da namiji Abu ne kawai baya nan. motsi hannun Maah yayi Fa'oz ne dake riƙe da hannun yayi magana
"Aunty Aailah hannun Maah na motsi"
"Fa'oz ba yanzu zata farka ba, gizo yake maka kawai" ta bashi amsa. Shiru yayi "Maybe gizon yake yi min" ya raya a zuciyar sa can sai ya ƙara jin hannun ya motsa shiru yayi bai faɗa ba dan ya fara tabbatar wa gizo ne kamar yadda Aailah tace. A hankali idon ta ya fara buɗe wa dishi-dishi take ganin su "Fawzan" shine abinda ta fara ambata ta faɗa a hankali. Hankalin su ne ya dawo gare ta duk suka yi kanta
"Maah kin tashi" suka faɗa a tare
"Ina Fawzan" ta ƙara tambayar su duk shiru suka yi dan basu san amsar da zasu bata ba. Ayraah da take ƙarama a cikinsu ce tace "Maah har yanzu bai dawo ba an kira wayar sa a kashe" ta ƙara sa faɗa tana karyar da kai
"Innalillahi shikenan na rasa Fawzan" ta faɗa a dai-dai lokacin da idanun ta suke rufe wa numfashin ta ya tsaya chakkkk..........



✨😍🌟



"Ummu gaskiya ɗaya ce fa, ke Mahaifiya tace matsayin ki daban na aiki na ma daban" ta ƙara sa faɗa tana murguɗa baki sai kace tana gaban Ummu
"Kiyi yadda kika ga dama Jawaheer" ta faɗa tana kashe wayar ta. Ajiye wayar Jawaheer tayitana taɓa baki.
Neman guri tayi ta zauna
"Ummu fa ta fini gaskiya ina kallo wannan ƴar da aka haifa a gabana ta haihu da Yah Tawfeeq" "kai ba zai yiwu ba dole in bi Shawarar Ummu" ta raya a zuciyar ta. Da sauri ta bude wata locker kusa da ita allura ta fito da ita ta haɗa dan jimm tayi sa kuma ta tashi da sauri ta nufi ɗakin da aka kwantar da Jaanan. Kamar ɗazu data barshi a cikin ɗakin yanzu ma yana nan zaune a gefen gadon riƙe da hannun Jaanan. Kyaɓe fuska Jawaheer tayi ta nufe su tana cewa "Yaya kaɗan fita zan duba inga ya jikin" bai ce mata komai ba ya tashi ya nufi waje. Allurar da ta taho da ita tayi mata da sauri ta fita shi kuma ya dawo. Lab taje wanda yake duty taja suka fita a gefe suka tsaya tayi masa magana sai washe baki yake da alamu maganar da tayi masa tayi daɗi komawa ciki yayi. Raka bayan sa da Harara tayi tana jan tsaki ta koma Office ɗin ta. Ko Ummu bata kira ta sanar wa ba.


Da sassafe Ummu tazo asibitin dan ƙarfe bakwai a Asibitin tayi mata Jaanan ko farka wa daga bacci bata yi ba Tawfeeq ya kwantar da kansa a gefen gadon yana bacci tana shigowa dasu tayi arba taɓe baki tayi bubbuga bayan sa tayi ya tashi
"Da gani ko Sallar Asubah baka yi ba, Tawfeeq me yake damun ka ne haka?"

"Nayi Sallah fa Ummu, Ina kwana"

"Ok, ka tashi lafiya" kawai tace tana zama akan kujerar dake facing ɗin sa tana cewa "me yake damun ta?"

"Basu sanar ba sai doctor yazo"

"Allah ya kawo shi lafiya, ina Jawaheer din take"

"Tun dare data shigo ban ƙara ganin ta ba"

Jinjina kai tayi tana cewa "Kuma baka neme taba" shiru yayi mata sai ta cigaba da cewa
"Bari inje office ɗin ta in gani" t faɗa tana tashi "sai kin dawo" ya ce mata shima yana tashi ya fita a ɗakin.

Tunda Jaanan ta tashi Ummu ta dawo kusa da ita da zama kome take nema Ummu zata ce gashi sai nan Nan take da Jaanan. Da doctor yazo ya sanar musu ɓari tayi Tawfeeq yaji babu daɗi har Fuskar sa sai da ta nuna da yamma aka sallame su. Direct gida suka nufa_______________✍️



# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



07077791941
WhatsApp Only


Comments din ku shine ƙarfin guiwa ta Fans🥰


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️

💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel



https://whatsapp.com/channel/0029Vahgkpx23n3caLhAso3Y



بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 6🦋


_______________________________________________________________________________________________________________


Suna zuwa gida a Compound yayi parking fito wa suka yi tsayawa Ummu tayi tana cika hannun Jaanan da take riƙe da shi tana cewa
"Daughter ku wuce ciki kije ki huta kar ki takura kanki da aiki zan turo Eshaal ta gyara miki guri kinji"

Tawfeeq ne daya gama rufe motar ya ƙara so kusa da su Yana cewa "Yauwa Ummu dama ko abincin kirki bata ci ba tayi mata girki ta kawo mata"

Murmushi tayi tana cewa "Yanzu zata zo karka damu"

Tohm yace yana riƙe Jaanan suka wuce part ɗin su Ummu ma tana ganin sun shige ta wuce.

Parlour kaca-kaca kwanikan abincin da suka ci yana nan da ledar takeaway ɗin da suka yi ko shara ba'a yi ba balle asa ran mopping "Eshaal, Eshaal" ta kwala mata kira shiru ba'a amsa ba a fusace tayi ɗakin Eshaal ɗin da ƙarfi ta tura kofar.
Sakin baki tayi ganin Eshaal dai-dai akan gado tana bacci hankali kwance da fusace ta ƙara so kusa da ita tana ɗaka mata duka. A furgice ta farka daga baccin tana murza idon ta kurr idon ta ya faɗa cikin na Ummu da take ta huci
"Ummu yaushe kuka dawo?" ta tambaye ta tana Mike wa daga kwanciyar harara Ummu ta balla mata sannan tace
"Ban sani ba, Baki san yadda gidan yake ba ne?"

"Ummu me gidan yayi, wani abu ya faru ne ban daɗe da kwanciyar ba" ta faɗa tana sauko wa kasa

"Yanzu ba abin kunya bane a shigo gidan nan, ace ko parlour baki gyara ba balle in sa ran zaki gyara ɗaki na har shida ta wuce"

"Magariba ashe ta kusa ko Sallar La'asar banyi ba" ta faɗa tana kwalalo ido waje

"Allah yayi wadaran naka ya lalace, sai kiyi sallar ki fito ki gyara parlour" tana gama faɗa ta fice. Tashi Eshaal tayi ta shiga toilet. Sharp-sharp ta fito ta tada Sallah tana idar wa ko addu'a bata yi ba ta tashi ta fice parlour. A zaune ta tadda Ummu gyara parlour'n tayi ta wuce kitchen Indomie ta dafa ta fito ta zauna tana ci. Taɓe baki Ummu tayi tana cewa "yanzu ke kaɗai kika yi girkin baki dafa dani ba"

Eshaal ce ta cigaba da cewa "A'a Ummu taki tana kitchen na ajiye miki"

Jinjina kai Ummu tayi sai kuma tace "Ai kin san bana cin Indomie ki dafa min ko shinkafa ne"

Ido Eshaal ta zaro tana cewa "Ummu da wahala wllh ba zan iya ba"

"Sai kiyi tayi in kinyi aure kya koya" ta faɗa tana tashi ta shige dakin ta
Murmushi Eshaal ta saki tana cewa "ai sai dai ya nema min ƴar aiki dan bazan iya ba wllhy".........




💥💫💥💫💥




Fitowar ta kenan daga toilet wayar ta ta ɗauka gani tayi har takwas ta kusa amma bata ƙara so ba wasu numbers tayi dailing ringing uku aka ɗaga. Magana ta fara da
"Naga har dare ya fara baki zo ba, ko kin fasa sai gobe"
"Komai dare ki jira ni zanzo karki kwanta" aka bata amsa daga can
"Tohm, amma Kawa shawarar ki tayi yanzu mun rabu da ƙaya" ta faɗa tana sakin dariya
"Me kike ci na baka na zuba , ki jira ni gani nan yanzu zan ƙara so ai sai muyi duk maganar da zamu yi" aka kara bata amsa
"Ok sai kin zo" ta faɗa tana kashe wayar...
Bata zo ba sai bayan tara na dare Ummu har ta cire ran zuwan ta. Zaune take a palour tv take kallo amma gaba daya bata gane abinda ake yi a ciki bini-bini sai ta duba waya sai kuma ta kalli ƙofa. Turo ƙofar palour'n aka yi kallon mai shigowar tayi Babbar Mace ce a ƙalla zata yi sa'ar Ummu ko ta girme ta sanye take da baƙar Abaya fuskar ta ba kwalliya sai wani ƙaton glass data kafa kana ganin ta kaga gogaggiyar ƴar duniya. Wata bahaguwar ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana cewa
"Har na fidda ran zuwan ki Hajiya Zubaida"
Wani malalacin murmushi ta saka tana cewa
"Ai zanzo nace miki duk dare yau sai na shigo"
"Ƙara so ga guri ki zauna" Ummu ta faɗa. Shigowa palour'n tayi ta nemi guri ta zauna "Eshaal" Ummu ta kwala mata kira. Fito wa tayi ranta a ɓace tana cewa "Gani Ummu" ta faɗa muryar ta a cunkushe

"Baki ga nayi baƙuwa ba, kawo mata lemo mana"

"Ok, Ina wuni" kawai ta faɗa ko kallon bakuwar bata yi ba tayi wucewar ta zuwa kitchen. Ba jimawa sai gata ta dawo da tray a hannun ta ajiye wa tayi ta koma ɗaki
"Ga ruwa nan ki sha ƙawa"

"Bar ruwan ba yanzu ba muyi maganar kawai"

"To mu shiga daga ɗaki" ta faɗa tana mike wa ɗaki suka shiga zama suka yi ta fara bata labarin duk abinda ya faru ajiyar zuciya Hajiya Zubaida ta sauke sai kuma tace

"Yanzu azabar da kike yi mata zaki ƙara akan ta da, ai ba'a barin ɗan maƙiyi ya huta"__________________✍️




# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯



07077791941
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah🥰👏



𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
💫 𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡𝗔 💫




An Imaginary Love Story❤️



𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽


𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷


𝗠𝗜𝗞𝗜𝗬𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡


Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029Vahgkpx23n3caLhAso3Y



بسم الله الرحمن الرحيم


𝑃𝑎𝑔𝑒 7🦋


_______________________________________________________________________________________________________________



Hutun kwana Uku kawai Ummu ta bata hutu shima dan Tawfeeq yana gida ne ta cigaba da aikin gida. Kwana Ukun nan da bata yi ba ba wanda yayi aiki a cikin su gidan kaca-kaca tasha wahala ranar da ta cigaba da aikin.

Tsaye take a cikin kitchen Girki take yi a kitchen ɗin motsi taji a bayan ta alamun mutum ne ke kallon ta juyo wa tayi a dan fusace dan ganin waye Ummu ce a tsaye ƙara sa shigowa ciki tayi tana yatsina fuska
"Kizo kina da baƙuwa a Palour" ta faɗa tana fice wa. Tunanin waye zaizo tayi dan tasan ƴan gidan su ba zuwa gurin ta zasu yi ba. Fito wa tayi parlour hannun ta ɗauke da tray Mace ce zaune tana facing Tv bata ganin fuskar ta sai bayan ta ƙara so wa kusa da ita tayi. Sakin baki ta yi tana cewa "Zee" ta faɗa da ƙarfi "yaushe kika shigo Damaturu?" ta ce tana ajiye tray ɗin gaban wadda ta kira da zee ɗin tare da zama kusa da ita

Dagowa tayi tana cewa "Ai ba ki da kirki Jaanan ba kira ba ziyara tunda kika yi aure baki taɓa nema na ba" ta faɗa tana hararar ta

Murmushi tayi tana cewa "Bani da waya yanzu, ko gida ban taba zuwa ba tunda nazo"

Ido Zee ta waro

Please Login or Register in order to submit comment