Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa? Ladee tace“Wai Goggo ce naji tana cewa Mamy ta kwantar da hankalinta zata koya mata dubara ta kaso auren...” Zahira tace“Wlh umma da girmanki kina abinda ni bazan yiba, Nandou zata saka akaso aure? Wlh wayone take mata, ni bari na shirya bayan la'asar zan wuce makaranta.” Ladee kunyar 'yarta taji ita sam ta mance dubarace goggo take mata. Zahira ta shigo d'akin da sallama kanta ak'asa kunyar Mamy takeji. Nandu ta amsa tana dariya tace“Su kunya manya.” Mamy ta kalli Zahira cikin sayin murya tace“Ni banson wani kunyarki zo muci dambu, dama can Tahir ba mijina bane dan haka wlh ban rik'eki da komai ba?” Zahira ta rungume Mamy tana kuka. Mamy tace“Ai sai kiyi.” Bayan sallar isha mai unguwa yana zàune tsakar gida ummuh na masa firfita yace“Wai Maryama Mamy ai ya kamata akaita gidanta tinda jikin yayi sauk'i.” Ummuh tace“Goggo tace abarta ta zauna wajanta har ta warware tinda ba yanzu zai dawoba kafin yazo insha Allah sai akaita, Zahari ita d'azu mijin ya maidata makaranta, tinda ita za'ayi biki asakata lalle.” Mai unguwa yace“A'a kawai ta tafi sai abata ihsan, bari naje naga goggon.” Ya k'arashe maganar yana mik'ewa ya fice. Bakinsa d'auke da sallama ya shigo cikin gidan. Goggo Nandou tana zaune ak'ofar d'akinta ta amsa. Gaisawa sukayi da Ladee ya wuce wajan Nandou. Zama yayi kusanta saman tabarma yana gaisheta ya d'ora da fad'in. “Umma ina Mamy kuwa?” Goggo Nandou tace“Tana ciki, inace dai lafiya? Zamansa ya gyara yace“A'a lafiya lau, daman nazo nace muku tinda taji sauk'i zuwa dare sai a sadata da gidanta, kafin ya dawo, Ihsan sai suje su zauna har Abban namu ya dawo.” Ya k'arashe mgnar yana kallon Nandou. Goggo ta gyara zamanta tace“Haba Sa'id taya yarinyar da ba wata gamsashiyar lafiya gareta ba za'a kaita gidanta ta zauna ita d'aya? A'a ai na amasheta ku barmin abata anan har mijinta ya dawo da kaina zan kaita gidanta, insha Allah.” Mai unguwa yace“Tom duk yadda kukace haka za'ayi Allah ya sanya alkhairi.” Goggo Nandou ta amsa da “Amin”. Mamy duk abinda suke tana jinsu sai da su ka idar ta sauko daga saman gadon tana mik'a ta sanya hijab ta saita nutsuwarta wajan saki fuska ta fito. Kusan Abbunta ta zauna ta d'ora kanta saman kafad'arshi cikin sanyin murya tace“Abbu ina yini? Mai unguwa ya amsa yana tab'a goshinta. “Ya jikin Mamy?” “Da sauk'i” Ta amsa tana share hawaye. “Haba Mamy meye toh? D'an uwanki fa kika aura kuma inada yak'inin zai kula dake, don Allah kiyi hkr ki ajiye hankalinki ai samun miji ayanzu mai tsad'a kamar Babandi wuya gareshi, duk fa inda ake buk'atar namiji yakai yakai, shekaru kawai kika fisa ba girmaba ko hankali ba....” Haka yay ta mata nasiyya, Mamy jinsa kawai take zuciyarta ta k'ek'ashe akan Deeni. ★★★★★★ Sannu-sannu Lokaci yake zuwa yana shud'ewa, yayin da kwana d'aya yake zama sati sati ya zama wata haka wata ya zama shekara. Yau wata biyu cif da auren su Mamy yayin da ake shirin bikin Zahira da AUTA wanda sannu ahankali soyayyarsa tai k'arfi azuciyarta, sabida kyautata mata da yake yi. 'Bangaran Mamy da Deeni wajan Mamy ba sauk'i duk yadda yaso magana da ita tak'i tayi magana da shi, Goggo Nandou har tayi fushi ta gaji addu' kawai take mata, ta matsawa goggo akan zuwa aiki Nandou tace indai bazata tambayi mijinta ba sai dai ta barsa ai kuwa ta barshi dan tayi rantsuwa bazata tab'a tambayarsa ba, ganinta bai isaba, Mamy anutse take tafiya ta fito daga gidan kawunsu Hafeez ta nufi cikin gidansu. Jamalu da yake fitowa daga b'angaransu yana tura mashin d'insa waya mak'ale akafad'arsa yace“Bilkisunmu ji mana.” Mamy ta waigo tana zabga masa harare taja ta tsaya. Isowa yay yana magana, ta Kama kunnensa ta murd'e ya Saki k'ara yana fad'in Ya Deeni kaga matarka zata ciramin kunne bazata bari na bata labari ba!” Mamy taja tsaki tace“Wallahi kaiwa kanka mun raba gari.” Ta sanya kai zata tafi. Jamalu ya kamo hannunta, ya manna mata wayar akunnenta. Taji murya Deeni ta kard'e dodon kunnenta ya kirata “My lovely ni ni ni wlh zan miki kuka da zaran na iso wallahi kuka zan Fara miki ina cike da kewar rashinki tsawon wata biyu wai Mamy so kike na mutu ko me?” ya k'arashe yana shashek'ar kukan zallar iskanci da ya shiryo mata ayau idan ya iso bazai tab'a yarda yajata da nisaba. Mamy cike da jin haushi ta buge wayar ta kame hannun Jamalu ta gantsara masa cizo, ya saketa tabar wajan da sauri tana matsa k'walla bak'in cikin wannna yaron Deeni. Jamaluddin dariya yake harda duk'ewa ya d'auki wayar ya manna akunnesa. “Yah Deeni kaga zaka had'ani gaba da ita ko? Toh ni dai ba ruwana. Daga can Deeni ya bushe da dariya yace“Barni da ita zan kametane... Mamy zaune tana yamutsa fuska tana zumb'uro baki. Ummuh tana amsa waya. “Eh gata fa kusa bari na bata.” Ta k'arashe maganar tana ba Mamy wayar fuskarta babu alamun wasa. Mamy ganin hakan ya saka ta amshi wayar tana karawa akunnenta, baki d'auke da sallama, tinda batasan dawa ake wayar ba. Daga can Deeni ya amsa sallamar yana d'orawa da “Muahhhhh my lovely ina tafe yau ki shirya kwanci da muradin zuciyarki, yau iya wuya muna tare, Mamyna i miss you so much.” Ya fara mata shegiyar shashek'ar da ta tsana. Saurin zare wayar tai daga kunnenta tana rarraba idanu cikin aro jarumta tai murnushi ta maida wayar kunnenta ganin Ummuh ta tsareta da idanu, tace“Eh wlh ok toh ba damuwa eh ga Ummuh d'in.” Taba Ummuh wayar ta mik'e kamar gaske ta d'auki buta ta shige band'aki... AUTA yana zaune cikin mota yana amsa waya.“Eh toh agaskiya ban saniba meye dalilin barinta zuwa aikin tin bayan aurenta wife na k'anwartace ta tabbatarmin tana lfy, amman bari zanyi magana da mijinta naji idan shi ya hana ba damuwa sai asaka wata ko wani madadinta, amman zamuyi missing d'in k'wazonta da k'warewarta ga gaskiya cikin lamuranta. Shiru yayi ko me akace masa yace“Ok zanje d'aukota anjima makaranta zanyi magana da ita kafin muyi da shi Zaharaddin d'in dan yana yawan kirana mu gaisa tinda na barmasa abar k'aunarsa, wlh yana bani sha'awa yasan karamci.” Haka ya gama hirasa kafin yaja motar ya nufi gidan iyayansa ganin akwatinan Zahira da suka iso. Tafe suke cikin motar haya mutane nata zuba surutu, amman Deeni kallo ma basu ishe shi ba, tasbihi ma yake ga ubangijinsa, pink lips d'insa sai motsawa suke alamar tasbihi yake. Wata yarinya fara kyakkyawa wacce kallo d'aya zaka mata kasan ba daga k'aramin gida ta fito ba, ak'alla zata kai 21, duk motsinsa akan idanunta ta gama mutuwa akan gayen, mamaki take me ya sanyo shi motar haya? Sanye yake da wasu shegun k'ananun kaya, wanda suka masa masifar kyau suka amshi murd'add'an jikinsa. Idan ka kalleshi tin daga takalmin k'afarsa zuwa agogon da yake d'aure atsintsiyar hannunsa, baza ka tab'a cewa Deeni ba hamshak'in mai kud'i bane. Zobunan yatsunsa na azurfa sai walk'iya suke. Akaro na uku kenan idan anyi katari ya d'ago sai ya kamata tana kallonsa. Tsaki yaja yana lumshe kyawawan matsagaitan idanunsa. Arayuwarsa ya tsani kallo,sai ga shi ya had'u da mayyar kallo. Kwance take saman gadon Nandou bacci take abinta hankali kwance, tinda tai sallar azuhur take bacci har la'asar ta sanyo kai. Shigowarsa kenan yaran da sukaci Karo da shi suka baibayeshi, sunata murna, har b'angaransu na zama. Dakyar ya samu ya ajiye jakarsa. Deeni tarin chocolates da alawa da biscuits da yake siyo musune yasa da zaran anyi katari ya dawo yaci Karo dasu atsakar gida zasu baibayeshi. Yanzu ma itace ya raba musu kafin su barsa ya shige d'aki. Tin tsakar gidan nasu yake kwad'a sallama, amman shiru ba kowa. Deeni k'ofar d'akin Ladee ya isa yana kiran“Ummina! Wai ina kuke?” Hamrah Ce ta fito daga d'akin tana gani Deeni ta fad'a jikinsa tana murna. “Oyoyo ya Deeni ina chocolate d'ina? “Na ajiye miki ina umma dai da su Nandou?” Hamrah tace“Sun tafi gidan Malam Zaidu matarsa wai ta rasu, inaga Aunty Mamy ce kawai aka bari tace bata zuwa.” Deeni yace“Allahu Akbar. Ok ina Mamyn? “Na shiga d'akin goggo Nandou Neman kilishin da papi yake kawomata na sace naganta kwance nafito karta kamani ta dakeni.” Deeni yay mumushi yace“Wlh ki daina tab'a kayan Nandou ba ruwana, kuma babu kyau d'aukar abin da ba'a baka ba, jeki part d'inmu, Jamalu yana ciki kice inji ni ya duba jakata ya baki biscuit da alawa.” Cikin farin cikin ta fice da gudu. Deeni kuwa yay tsalle ya dire ya nufi d'akin Goggo Nandou. Kallo d'aya yama yaji har jikinsa na tsuma. Daga ita sai wata 'yar mintsinar riga wacce rabin k'irjinta duk awaje, skirt d'in jikinta irin mai laushin nan ne yabi ya lab'e ajinta Rabi ya janye cinyoyinta duk awaje farare tas 'yan matasa sai shek'i suke. Wani irin yawu ya had'i ya sad'ad'a ya haye saman gadon yabita ya haye ya ware mata hannayenta duka mik'e ya sanya hannayensa ya mik'esu yana murzawa ahankli ya cusa fuskarshi k'asan wuyanta yana gogawa yana shak'o dad'an k'amshin jikinta, yana manna mata wani shu'umin kiss,ya d'ago da kansa yana goga fuskarshi saman tata, yana kiranta cikin wata rikitacciyar murya. “My love my heart Mamyna ina sonki bani yawu nasha nasan zaiyi taste.”ya k'arashe maganar yana kissing d'in dukkan fuskarta, ya k'ank'ameta. Wani irin nauyi Mamy taji cikin baccinta ta fara k'ok'arin bud'e idanunta taji ankame labb'anta Ana mata shashek'ar kuka cikin bakinta an kanainayeta Ana murza mata dukkan tafukan hannayenta zuwa damtsen hannunta Ana mata shashek'ar kuka cikin bakinta Ana shan harshanta acikin wani irin slow, yawun na kwarara tsakiyar bakinta kai tsaye yake zarcewa mak'ogwaronta. Amugun tsorace ta bud'e idanunta, ido hud'u sukayi da Deeni yana mata kukan iskanci yana shan bakinta kamar ba gobe, yana murza tafukan hannayenta. Zaburu tai ta gantsara masa uban cizo aharshensa, ta shiga k'ok'arin tureshi, hankalinta amugun tashe, ta fizgo hannunta d'aya cikin nasa, ta lalubo abinda batasan meyeba lugun gadon ta kwad'a masa akai........*🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*

_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣*

Ushhhhh my love zafi kin fasa min kai, kashe mijinki zakiyi ko me?” Ya k'arashe tambayar tata yana, sake k'ank'ameta, yanzu cikin mugunta ya sakar masa nauyinta baki d'aya, ya tura kansa tsakanin wuyanta, yana lasar fatar wuyan nata yana sauke mata numfashin mai d'umin gaske, ya k'ara danneta cikin mugunta. Ihu ta saki tana nishi ta sake kwad'a masa abin hannunta ashe fitilar Goggo Nandou ta hannu, idan an cire wuta da take haskawa ce. Take k'wan fitilar ya fashe, wanda sai da tsakiyar kan Deeni ya d'an fashe ya fara fitar da jini kad'an². Azabar zafin da yaji ta saka Deeni dafe kansa still yana samanta kwance. Kuka ta sakar masa tace“Kayi hkr ka d'agani ni ban Saba da masifa da jaraba ba, kaga ka ja na fasa maka kai, wlh kad'an ka gani indai bazaka fita asabgata ba, sai na salwantar da rayuwarka, maye kawai.” Murmushi yay mai ciwo ya d'ago kanta da hannu guda ya jefa idanunsa cikin Nata, cikin taushin murya mai rauni ahankali yace“K'arya kike Mamy kukan jimin ciwo ne kike ba wai kukan na rabu dakeba kike. Na tabbata ayau na sakeki wallahi sai kin rasa nutsuwarki, so karki wani damu but ni banda damuwa da duk abinda zaki min idan ma kasheni yana baki sha'awa ki kasheni in dai ahannunki zan mutu zanyi farin cikin hakan. Bak'in cikana d'ayane makomarki wajan ubangijinmu, My love ina sonki kuma bazan daina sonki ba, haka bazan sakeki ba, aurenmu mutu kan rabane takalmin kaza.” Ya k'arashe maganar yana janye jikinsa anata, ya sauko daga saman gadon yana dafe da kansa wajan da yake fitar da jinin ya fice daga cikin d'akin bai sake ko kallon wajan da take ba. Mamy taja tsaki tana kwanci rubda ciki, ta tura kanta cikin follow tana sauke numfashi da sauri² haushin Deeni takeji sosai kamar ta kasheshi ta huta. Deeni yana fita ya wuce b'angaransu ya duba yaga ciwon ba wani babba bane, jinin ma ya tsaya, jin ana kiran sallar la'asar wanka yay ya fito ya ya saka jallabiya fara k'all ya feshe jikinsa da d'addad'an turarensa mai sanyin k'amshi. Jamaluddin ya kalleshi yace“Yayana wai meye kake wani ciccin magani? Ko Aunty Mamy Ce? Deeni ya gyara tsayuwarsa ya zura hannayenshi dukkansu cikin aljihun wandonsa, ya had'e gira sama da ta k'asa, yace“Ina ruwanka da ma'aurata? Banson sa ido fa! Wuce muje masallaci kar atayar da sallah.” Dariya Jamaluddin yay suka fito su ka nufi masallaci. Mamy ahankali ta sauko daga saman gadon, tana yamutsa fuska, tana jan tsaki ta saka hijabi, ta fito tsakar gidan ba kowa sai Hamrah agindin fanfo tana tara ruwa a buta. Mamy ta dauki buta ta isa gindin fanfon tace“Hamrah har yanzu su Nandou basu dawoba?” Hamrah tace“Eh Aunty Mamy wai kinga chocolates d'in da Yaya Deeni ya kawo mana? Wlh dayawa naje na b'oye tawa se landi na tafi da ita école nasha abina.” Mamy ta zabga mata harara ta ce “Matsamin tin ban makeki ba wlh makwad'aita kawai.” Hamrah ta janye butar tana turo baki ta matsa can tana d'aura alwala. Mamy bayan tayi sallah tayi wanka ta shirya cikin abaya milk colour ta d'an shafa humrah ta yane kanta da mayafin abayar. K'ofar d'anki Goggo Nandou ta rufe ta fito zuwa gidansu. Karo sukaci da su Goggo Nandou. Nandou tace“Ke ko ina zuwa akasha kwalliya? Ko ta tarbar miji Ce?” Goggo Nandou ta tambayeta cikin sigar tsokana. Mamy tace“Uhmm gidanmu zanje wlh ina son zuwa gidan Zuhura ma....” Ladee tai tsalaf tace“Baga Babandi agari ba, ko bai isoba? Bari ya kaiki kawai bari na masa magana.” Mamy cikin d'anjin nauyi ta ce“A'a na fasama ba ba wai lallai zanje ba.” Goggo Nandou tace“Ai ba inda zataje yau gidanta zata kwana, bari yanzu zan tura su Didi a goge akakkab'e inda yay k'ura zuwa bayan isha da kaina zan kaita.” Mamy takaici ya sakata rab'awa ta jikin Nandoun ta nufi b'angaransu. Mamy sai shara k'wala take ta shiga gidan nasu. Ummuh wacce shigowarta kenan ta kunna gawayi tana k'ok'arin d'ora girki Mamy ta shigo da sallama. Ummuh ta amsa, Mamy ta gaisheta. Tana zama. Ummuh tace“Mamy ina zuwa akasha kwalliya? Mamy ta zumb'uro baki kamar wata k'aramar yarinya ta bud'e baki zatayi magana Deeni ya rangad'o sallama yana rik'e da hannu Ihsan. Yanzu ma sanye yake da wasu had'add'un k'ananun kaya wad'anda suka amshesa su ka fito da asalin kyawunsa, da kwarjininsa, da haibarsa, sai baza uban k'amshi yake. Kallo d'aya ta masa ta janye idanunta tana ciza bakinta, sabida kallon da ya mata ya watsar yana wani d'aure fuska. Sai taji wani iri sabida ta tsani arayuwarta Deeni ya d'aure mata fuska duk yadda takai da tsanarsa dajin haushinsa idan ya mata laifi sai taji wani iri, tafi son ita tai ta masa tsare gida. Tsaki taja Wanda ya fito fili. Sai da Ummuh ta kalleta ta zabga mata harara. Ummuh ta amsa tana fad'add'a fara'arta. “Babanmu saukar yaushe?” Deeni ya zauna saman tabarmar da Mamy take amman nesa da ita, bai KO kalleta ba, yace“Wlh Ummuh d'azu na shigo akace kunje wajan rashi, ashe matar Malam Zaidu lokaci ya yi? Allah ya jik'anta da rahma. Ummuh fatan na sameku lafiya?” Ummuh ta amsa da“Wlh lokaci ya yi Ameen ya Allah, lafiyar mu. Ke Mamy baki Iya gaisar da bak'o bane? Tashi ki kawo masa ruwa.” Mamy wani tuk'uk'in bak'in cikine ya tokare mata a k'asan zuciya ta shagwab'e fuska tace“Ummuh munfa gaisa na basa ruwa agidan Nandou.” Ummuh tace“Gidan Umma daban gidan nan daban, kin tashi ko sai na jefeki?” Deeni banza yama Mamy sabida ya gane so take ya tankata, bai kalleta ba. Yace“Ummuh ai nan gidanmu ne idan inada buk'atar abu ba sai an bani ba.” Ihsan tace“Ummuh kalli chocolate da biscuits d'in da Yaya Deeni ya kawo mana kowa da nasa.” Ummuh tace“Masha Allah sannu Babandi Allah yayi albarka.” Deeni yay murmushi ya gyara zamansa ya ciro wayarsa ya Kira number Zuhura bugu d'aya ta d'aga. “Auntyna Aslm barka da yamma ayimin zob'o mai dad'i zanzo yanzu ina baby Rauda da Ayman? Kice chocolates d'insu na tafe.” Daga chan Zuhura tace“Ango kasha k'amshi, barka da zuwa ai kuwa kaci sa'a wlh da rana na had'ama Abban su Ayman yayi sanyi sosai bari na d'orama abu mai sauk'i kafin ka iso ina Mamynmu?” Deeni ya kalleta da tsinin ido yaga kanta gefe tana karkad'a k'afafunta da suke mek'e. “Uhmm gata fa zaune.” Zuhura tayi dariya tace“Agaisheta ni kam an fasa zuwarmin.” Deeni yace“Auntyna sai nazo.” Ya katse kiran, ya mik'e yace“Ummuh zan fita sai nazo cin abincin dare.” Ya sanya kansa ya fice. Ummuh ta d'ora tukunyar tazo ta zauna kusan Mamy tace“Wallahi Mamy kibi asannu kiyi hankali aure ba wasa bane ba, meye laifin yaron nan? Me kika fishi idan ba shekaru ba? Girma hankali duk ya fiki wlh sabida haka ki kama mutuncin ki ina fad'a miki gaskiyane amatsayina na mahaifiyarki, wacce tasan ciwonki fiye da kowa, ki ajiye hankalinki kiyi zaman aure agidanki ki ajiye maganar kin girmeshi ki nemi aljannarki, ak'ark'ashinsa, ke ba yarinya bace kinsan komai akan aure dan haka sauran bayanan ba sai na miki ba, sabida sanin wacece ke akan b'angaran neman sani akan rayuwar zaman gidan miji rok'ona gareki kibi mijinki ki ajiye girman kai, za kiji dad'in zama da shi Sam hanyar da kika bi ba mai b'ulowa bace.” Haka Ummuh ta tisata gaba tana mata fad'a had'i da nasiya. Goggo Nandou ce ta shigo da sallaam. Ummuh ta amsa. Goggo tace“Maryama ki gama mata duk nasiyar da zaki mata tazo muje akwai tsumin da zan mata idan anyi sallar isha zan kaita gidanta, na kira mai unguwa munyi magana na kai sun Didi su gyara ko ina asanya turaren wuta Jamaluddin ya tafi kai kayan Deeni dan haka afito mata da akwatinanta, Ahmed da Sharif su kai mata.” Ummuh tace“Masha Allah Umma Allah ya qara lafiya da nisan kwana.” Ummuh ta fad'a tana cikin farin ciki sosai jin wannan labarin. Goggo Nandou tace“Ameen. Bilkisu maza tashi ki gyara had'a kayanki waje d'aya, su Ahmed zasu shigo yanzu, idan ki gama ki sameni.” Goggo Nandou ta fad'a tana ficewa. Mamy takaici kamar ya kasheta ba yadda zatayi ta mik'e da k'udirin yau sai taci mutuncinsa. Cikin fushi ta had'a komai ta fito rai b'ace ta nufi gidan Goggon. Wasu irin tsumi Goggo Nandou ta shiga bankawa Mamy nasha wajan kala uku, cikin masifa ta tsareta fuskarta ba alamun wasa, dole ta Sha tana kuka kamar wata yarinya. Bayan ta gama ta saka uwar d'aka ta cire kayan jikinta ta murjeta da dilke wanda yasha had'e² da turaruka, kala² da lalle, bayan ta gama mata ta d'aura zane tace ta zauna ta fita ta juye ruwan zafin da ta d'ora wanda ta zuba ganyan icen turare da kafi amarya acikinsa ta kawo ta ajiye gabanta ta rufa mata k'aton bargo. Mamy ihu take harda kuka da majina kace wata yarinyace 'yar 15 years. Sosai sai da ta turaru Gaggo Nandou ta bud'eta tana masifa.“ Muje maza kiyi wanka lokacin magarib ya yi raguwar banza kawai yau zaki fad'a musu wallahi da kaina zan sakashi bazai ragami ki ba, muga k'aryar iskanci.” Mamy ta wuce tana matsar k'walla tana goge majina ji take kamar ta gudu tabar garin, rana zafi inuwa k'una. Goggo Nandou da ruwan zafin turaren ta had'ama Mamy ruwan wanka ta kai mata bayi ta d'auko mata sosonta da sabulu, ta shige bayin tana kukan takaici ace duk sabida Deeni ake mata uban gyara haka......? 'Bangaran Deeni kuwa yana fita ya hau mashin d'insa ya nufi gidan Zuhura. Lokacin da ya iso k'ofar gidan yana sauka ya kulle mashin d'in ya zura key d'in cikin Aljihun wandonsa yana takunsa ya isa bakin k'ofar gidan yaa k'wank'wasawa. “Asslamu alaikum.” Ya tsinci murya wata matashi bayansa. Juyowa yay ya amsa. Idanu suka had'a da yarinyar wacce suka zo amota tindaga Niamey. Fuska ya had'e yana amsa sallamar... Murmushi d'auke a fuskarta ta ce“Nasan ka ganeni? Tin lokacin da muka sauka agidan bus nake dakon binka, duk inda ka saka k'afa, nida k'awata a motarta da tazo d'aukana. Sai da mukaga gidan da ka shiga muka juya, so yanzu ma na matsa mata akan tazo muje gidan naku, haka kawai naji inada buk'atar shiga gidan ko da wani nakane nayi magna da shi. Pls ka bani dama na bayyana maka ni wacece me ke tafe dani akanka, don Allah kaji.” Ta k'arashe maganar tana goge hawaye. Deeni ya gyara tsayuwarsa yana zura hannayensa cikin aljihun wandonsa yace“Baiwar Allah me yake tafe dake? Maganar idan bazata wuce 2 minutes bismillah ina sauri ne” Farhana ta goge hawayen fuskarta ta ce“Tinda na maka kallon farko naji Allah ya had'ani da Garkuwata, bangon da zan jingina naji sanyi wallahi kallo d'aya na maka naji na kamu da sonka mai tsanani, don Allah kabani ko da 30 minutes ne na fad'a maka me ya fito dani daga garinmu...” Idanunsa ya zaro yace“Oh! Yawon duniyama kika fito yarinya k'arama kamarki? Toh b'ace anan bazan saurareki ba.” K'asa ta zube tana sakin kuka tace“Don Allah bawan Allah kamin rai ka bani lokaci namaka bayani idan baka gamsuba sai kamin korar kare.” Deeni yaja numfashi yace “Okey amman ba yauba zuwa gobe da yamma idan ya miki sai kizo nan mu had'u k'arfe 5 na yamm?” Cikin murna tace“Eh yamin Ngd sosai bari na tafi gatacan tana jirana.” Kai ya girgiza. Tafiya tayi, ya dafe kansa ya koma ya d'auki leda mai chocolates d'insu Rauda. Ya sanya kasan gidan da sallama, wanda tin d'azu Zuhura ta bud'e ganin ya na tsaye da mace ya saka ta koma ciki. Zuhura na zauna a tsakar gidan ta amsa tana fad'in su Abba ina kuma aka samo wannan yarinya? Ai kuwa se na fad'ama Mamy.” Rauda da Ayman su ka tarbesa sunata murna,ya rungumesu yana murmushi. “Eh Rauda nan da 'yan shekaru zanyi suruki wlh. Aunty Zuhura Mamy bata sona kinga dan nayi wata ai baza damuba.” Ya fad'a yana zama saman tabarmar da Zuhura take, ya bek'ema su Rauda ledarsu, sunata murna. Zuhura ta mik'e tana dariya tace“Uhmm son naka sai ya kasheta ko?” Deeni ya Sosa yalwataccir sumar kansa yana tab'e baki. Jug mai d'an girma taje ta ciro masa ad'an k'aramin fridge d'inta ta kawo cup ta tsiyaya masa, ta basa tace“Sai ayita Sha ko aragema Mamy atafi da shi.” Dariya yay yace“Mamy ta raina min hankali nima zan raina mata fa! Humm ba dai dan taga ina sonta bane.” Ya k'arashe maganar yana kurb'ar daddad'an zob'on. Zuhura ta ajiye masa plate gabansa mai d'auke da k'osan couscous wanda yaji kwai da nama. “Zuhura tace“Kunfi kusa fa! Ba ruwana ba'a shiga tsakaninku abayama bare yanzu.” Deeni ya cika tumbinsa dam, suka tab'a hira ya mata bayanin yarinyar da ta gansu tare yace gobe idan tazo ta kirasa. Yamata sallama ya tafi sabida lokacin sallah ya matso. Mamy bayan ta fito daga wankan ta d'auro alwala lokacin ana k'iran magarib. Bayan ta idar da sallah ne tana zaune taa azkhar, taji murya Deeni ak'ofar d'akin suna magana da Goggo Nandou. “Deeni shine sai yanzu kazo nemana koh?” Dariya yay yace“Haba! Ni na isa my love? Wlh na shigo Hamrah tace kuna wajan rashi. Fatan na sameku lafiya? Bari na fito daga wajan Ummina.” Ya k'arashe magana ya na juyawa. Goggo Nandou tace“Zo zauna muyi magana ta mintina biyar.” Zama yay kusanta. Ta ce“ An kaima komai naka gidanku, anjima da anyi sallar isha zan kaita da kaina ka rik'emin ita amana don Allah mai gida, Ku zauna lafiya da junanku, kayi k'ok'arin cire mata k'iyayyar da take ikirarin tana maka, acikin kwana biyu kacal ka nuna mata k'arya take ka nuna mata itad'in takace kuma kaima natane, ta hanya da ilimi da siyasa, ta shi kaje wajan mahaifiyarka na fad'amata.” Deeni yace“Insha Allah uwar gidana zan aiwatar da uwarninki, ta guntso zata fesar.” Goggo Nandou tace“Yauwa nawan jeka abinka Allah yama rayuwarku albarka.” “Ameen Deeni ya amsa ya mik'e ya nufi wajan Ladee. Mamy

Please Login or Register in order to submit comment