Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawa jiki jikinki ya dinga tsuma kina fad'in sai kin kasheni idan ban barki kin zauna da matarki ba, ki nuna kece aljanin, ni kuma ina miki karatun ahankali har su iskomu ahaka, amman ba hakaba wlh inada tabbacin akwai babbar matsala.” Ya k'arashe maganar ya janye bakinsa daga kunnenta ya tallafo fuskarta. Ranta amutuk'ar b'ace ta daki k'ijinsa idanunta cikin nashi tace“Na tsaneka mugu mai nema ma mutum ciwo mafi muni, zanyine sabida tsira da mutuncina.” Ta idar da maganar tana janye idanunta daga cikin nashi ta shiga gwada yadda yace d'in. Janta yay suka zube k'asa ya rik'ota jikinsa ya kama kanta ya fara karatun kamar gaske. Ta daki k'irjinshi“Malam wasane karka zak'e dayawa, bari min tsawa acikin kunne d'an banza yaro kawai....” Lalubo fatar wuyanta yay ya tsinketa ta fasa ihu cikin murna da k'arfi ya d'aga murya yace“Inata lallab'arka sama da minti 40 ka fita kuma ka fad'amin meyasa kuka kawota bayan soron k'ofa?” Mai unguwa yace“Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un!! Goggo Nandou ta fashe da kuka tana fad'in kajita ko ai nafad'a maka wannan bak'ak'en arnan da suke kanta ba k'ananun shegu bane.” Ta k'arasa maganar tana fatar majina. Mai unguwa bai sake magana har suka isa bayan k'ofar. Ganin yadda Mamy take k'ak'afewa tana fizge fizge Deeni na mata karatu yana fad'in. Zaku tafi ko sai na k'oneku.....? Nandou tace“Ak'one shegu la'anannu. Mai unguwa yi sauri kawomin ruwa a kwano ka shiga d'akina zakaga wata babbar dorina lafceciya wacce Malam Allah ya jikin rai yake ba jinnu masu taurin kai kashi da ita, Iran yanama mutane Ruk'uyya. Yi sauri kawomin nayi addu'a na shafama bulaliyar yanzu na zaneshi da hannuna dan babansa arne.” Cikin sauri mai unguwa ya juya harda gudunsa ganin yadda Mamy takeyi. Mamy kuwa tanajin maganar bulala ta k'ank'ame Deeni tana fad'in. “Mu bamason bugo ai zamu tafi ka daina karatun mun tafi bazamu dawoba.....” Goggo Nandou tace“Dan ubanka k'arya kake bak'in arne munafuki dukane yau sai kacisa agidanan wlh lilis zan maka dan babanka, ina kuka tab'a jin rayuwa tsakanin mutum da aljani? Mamy sosai taji tsoron lamarin Nandou ai ba shiri tace“Ah toh ni dai na gudu dan ni ba dan iska bane zan tsaya Ku lahantani wajan laftamin bulala mai ruwan addu'ah, sai dai Ku lahanta Bilkisu ba niba ma'assalam.” Tana fad'in haka ta sulale zata fad'i Deeni yay saurin tarota ya rungumeta yana fad'in “Haba meye haka idan kinji ciwo fa?” Mamy tayi luf abinta ajikinsa, ta lalubi fatar wuyanshi danna masa yatsarta, cike da mugunta. Yanaji ya shareta yana shafa kyakkyawar fuskarta, tai lamo tana sauke numfashi irin tayi baccin na. Goggo Nandou tace“Bakada kai Deeni yo ita tasan me take shegun ne fa. Alhmdllh sai ka d'auketa ka kaita gidansu bacci take k'ila wannan sai asubah ta farka. Muje na tofeta da addu'a yaji zancan bulala ya ari ta kare, mik'e muje.” Deeni yace“Haba Goggo Nandou yanzu tsakani da Allah na d'auketa na ratsa gidan nan jama'a suna kallona na shiga da ita har d'akinsu na kwantar da ita?” Baki Nandou ta tab'e“ Oho toh shi kenan bari ubanta yazo ya d'auketa tinda,shi ta zame masa dole, gidan kowa ya nemi wajan kwanciyarshi, zaka kawomin wani zancan banza, ko uwaka Hajara taja da mgnata bare Yaro da yake mallakina?” Mai unguwa ya iso yana fad'in “Ta samu bacci kenan? Deeni kaita ciki toh.” Goggo tace“Ah yace bazai kaiba ai.” Deeni yace“Kai Nandou ke bakisan wasa bane sabida Allah yaushe nace?” Ya fad'i yana k'ok'arin mik'ewa da Mamy tai saurin janye jikinta tana fad'in. Innalillahi! Goggo Nandou me muke anan? Abbu yunwa nakeji.” Ta k'arashe maganar tana kallon mahaifin Nata, ta shagwab'e fuska. Mai unguwa ya kamata ta mik'e yana rik'e da hannunta yace“Sannu Mamy muje toh sai kici abinci kiyi wanka.” Goggo Nandou tace“Eh lallai an dawo daidai Deeni sannu Allah yama albarka. Ki godema Deeni kina kallonshi ko magana babu tsabar iskanci, wait Bilkisu yaron nan me ya tare miki sabida Allah? Karfa ki harzuk'ani wallahi ina fad'amiki zan baku mamaki.” Mamy dan kar aganosu yasa ta kalli Nandou tana marerece fuska“Allah baku hkr daman ni bakya k'aunata sai Deeni. Deeni K'anina Ngd duk da bansan temakon da kamin ba.” Ta idar da maganar tana hararansa akai-kaice ta kawar da kanta. Deeni hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa ya nufi ciki. Mai uwanguwa yace“Babandi ai garkuwar Mamy ne awannan k'arnin da take ciki, Allah ya masa albarka.” Cikin gida suka nufa. Tsakar gidansu Mamy ba kowa an kammala aiki an gyara fili bak'in 'yan biki sun kwanta, sabida gajiya. Sallamar Goggo Nandou ta saka Ummuh wacce suke hira yaushe gamo da yayarta fitowa tana amsawa Nandou sallama. “Umma sannunku sai yanzu? Mu har mun shiga ciki.” Goggo Nandou tace“Wlh tsinannanne ya tareta asoron k'ofa Allah ya takaita wahala, Deeni ya ganta, bata abinci taci.” Mai unguwa yace“Maryama had'a mata ruwan wanka idan tayi zatafi jin dad'i.” Ummuh ta amsa da “Toh ta kama hannun Mamy tace“Je d'auko soso da sabulu kafin na had'o miki ruwan sai kije kiyi wanka kici abincin.” Mamy ta d'aga kai ta nufi d'akinta. Mai unguwa ya kama hannun Goggo Nandou yace“Muje ki kwanta ki huta.” Ba musu tace“Toh Maryama sai da safe.” Ummuh tana tara ruwa afanfo tace“Umma Allah ya tashemu lfy.” Goggo tace “Ameen” Su ka fice. Da d'aurin k'irji Mamy ta fito tsakar gidan ta nufi band'akin, tana yamutsa fuskarta.........*🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*

_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣*

Tana yatsina fuska haka ta shige band'ankin nasu. Ahankali ta cire zanin ta rata ak'usar da take kafe ajikin katangar band'akin. Anutse tayi wankanta tana sauke ajiyar zuciya sabida yadda sanyin ruwan yake shigar kowace gab'a ta jikinta. Itako ta saba da wanka da ruwan d'umi. Tana kammalawa ta d'aura zanin ta lullub'a towel d'in akanta ta wanke pant bra da ta cire ta d'auraye sosan ta nasashi agidansa ta fito rik'e da bokintin. Abbunsu ta gani da ummuh su na magana. Bokintin ta ajiye ta sa kai da niyar shiga d'aki Abbunsu ya kirata“Mamy ki shirya maza kizo kici abinci, sai kisha ko paracetamol ne kinji.” Mamy cike da ladabi ta amsa da“Toh Abbu insha Allah.” Ta nufi d'akin. Jikinta ta goge ta murza lotion sama², ta d'aura zani bra kawai ta sanya ta saka hijab, wani irin sahihin k'amshi yake fita ajikinta, ta fito wajan. Ummunta zaune saman tabarma kusan Abbu su na magana. Abinci ta nuna mata ta d'auka taja kujera ta zauna ta fara ci, tana yatsina fuska. Abbu yace“Ayanzu me kikeji Mamy?” Mamy ta saki murmushin k'arfin hali tace“Babu komai Abbu. Nasiya iyayan su ka mata tana jinjina kai har ta idar taje ta wanko hannunta tai musu sallama ta shige d'akinta. Kayan bacci ta sanya tabi lafiyar katifa, takaicin Deeni fal acikin zuciyarta. Juyi ta fara tana lumshe lumsassun manya idanunta, tana tuna lokacin da Deenin ya mata kyakkyawan masauki ak'irjinshi ya mata magana acikin kunnenta acikin tattausan lafazi. Da lokacin da ya sanya bakinsa cikin nata. Tsaki taja tana mai karanto addu'ar bacci... Goggo Nandou bayan mai umguwa ya rakata b'angaransu, bayan tayi shirin kwanciya ta zauna bakin katifar ta rafka tagumi tana tunanin abinda mai unguwa ya fad'amata akan Mamy aljanin yace zai kashe AUTA. “Insha Allah ta Allah ba tashiba aniyarsa ta bisa ubangiji zai mana maganinsa. Deeni bayan yayi wanka yay shirin kwanciya ko abinci bai nema ba, Jamaluddin yana masa surutu baibi ta kansa ba, ya kwanta hankalinsa amugun tashe, yanaji yana gani gobe za'a d'aurama Mamy aure? Wani irin takaici da bak'in ciki yake cin zuciyarshi ya rasa ina zai saka ransa. Juyi yayi yana gyara kwancinsa yace“ Tawakaltu Alallah.” Cikin shirin bacci yake tsaye gaban dressing mirror, kallo d'aya zakama d'akin kasan an kashe mak'uddan kud'i. Yana fesa turare, hannunsa d'aya rik'e da waya, yana kiran Mamy tana ringing ba'a d'agaba. Murmushi ya saki yana shafa kansa yace“My Queen angaji anyi bacci, gobe zamu had'u.” Ya k'arashe maganar yana kashe wutar d'akin ya haye makeken bed d'in ya kwanta bakinsa d'auke da addu'a. Kamar minti 50 da kwanciyarsa wani irin nauyayyan bacci ya d'aukeshi mai cike da mafarkin Mamy. Kamar daga sama yaji an kifa masa wani irin giggitaccan mari ajere guda uku an d'agashi sama an yadoshi tsakiyar d'akin saman carpet. An kece da wata irin gigitacciyar dariya, an damk'e masa muk'a-muk'ansa, had'i da gimbiyarsa ana matsawa da k'arfin gaske. AUTAH tsabar azaba da tsoro ya sakashi sakin fitsari baki d'aya yama manta da wata addu'a. Cikin fitar haiyaci yake fad'in“Don Allah na tuba me nayi muku bayin Allah karku kasheni inada marayun 'ya'ya inada uwa da 'yan uwa da Mamy suna buk'atata“. Wani irin bugu akama bakinsa take ya fashe jini yana tsiyaya. Cikin kakkausar Murya akace“Bahun ubanka kadai Mamy d'in d'an iska mai shiga hurumin da banashi ba, nazoma kashedi da kakkausar murya akan Bilkisu idan kana son ranka ka janye aurenta wallahi idan kak'i zaka mutu lokacinka baiyi ba, wallahi kasheka zamuyi kanaji ko bakaji?” AUTA cikin tsoro yace“Naji zan janye ina buk'atar rayuwata.” Wata irin dariya akayi ana tafa hannu raf-raf cikin taushin murya akace“Good Tahir ka taimaki kanka da kanka Allah ya baka mace tagari Bilkisu ta Zakari Ce.” AUTA kamar almara ya gansa tsakiyar gadonsa ya shafo bakinsa wajan da yaji jini na zuba yaji ba komai ba kuma ciwon. Saukowa yayi hankalinsa atashe sai lokacin ya samu damar yin Addu'a ya cure kayan jikinsa yaje yay tsarki, ya sanya jallabiya ya d'auki wayarsa da mukullin motar ya fice. Mota ya shiga ya tayar aguje ya nufi gate yana horn da k'arfi. Mai gadi ya bud'e masa gate ya sanya kai ya fita aguje. Cikin 10 minutes ya iso gidansu. Hajiya ummee tana zaune saman darduma tana addu'o'inta ya buga k'ofar falon. Cike da mamaki ta mik'e ta nufo falon ta bud'e. “Tahir lafiya? AUTA ya shigo ya Kama hannun mahaifiyarsa suka nufi saman kujera. “Ummee yau naga abin al'ajabi arayuwa naci dukan wulak'anci.... Ya zaiyyanewa Ummee komai da ya faru. “Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! AUTA ko dai mafarki kayi? Tinda kalli ras kake babu alamun jini ko wani abun, a yadda kake fad'in ko d'agaka sama ayadoka k'asa kawai zai saka ayi jinyarka bare mazakuntarka da suka rik'e cikin mugunta ga muk'a muk'anka ga mari uku da FASA baki haba Tahir wallahi mafarki kayi, bakayi addu'a ba wajan kwanciya ko?” AUTA yace“Na rantse da Allah nayi addu'a Ummee kuma abin azahiri ya faru ba mafarki ba.” Ummee tayi tagumi sam bata gamsuba taya aljani zai daki mutum azahiri bai illataba? “Ummee idan baki yardaba shi kenan amman lamarin ya bani tsoro wallahi.” Hannunsa ta rik'e tace“Karka fasa aurenta kayi tawakali da Allah wallahi babu maiyi sai Allah, idan har ajalinka ta sanadiyar aurentane wallahi babu makawa sai ka mutu, bawa baya tab'a wuce lokacinsa, ko ka aureta ko baka auretaba bakin wa'adin da Ubangiji ya d'aukar maka bazai k'aramaka second d'aya ba, ka mik'awa Allah lanuranka, Tahir karka kuskura shed'an la'ananne yayi nasara akanka.” Sosai maganar Ummee tayi tasiri akansa ya rungumeta yace“Ngd sosai Ummee insha Allahu bazan fasa ba.” Albarka ta saka masa ta tofeshi da addu'a tace“Kaje ka kwanta babu abinda zai sameka insha Allahu.” Cikin k'warin guiwa ya koma gida ya kwanta har wayewar gari babu abinda ya sameshi. Mamy tinda tayi sallar asubah ta tafi wajan Goggo Nandou tayi kwanciyarta. Misalin k'arfe 9 na safe ya fito cikin shirin tafiya Niamey. Ladee tana wanke² ya shigo da jakarsa goye abayansa yana sanye da k'ananun kaya Wanda suka masa masifar kyau, wani irin fitinannan k'amshi yake zubawa. Takalmin k'afarsa kad'ai abin kallone zoben azurfa da suke jere yatsunsa ya gogesu guda uku sai shek'i suke, agogon zallar fata yau ya d'aura mai kyau da sauk'in kud'i, kansa ba hula iska na kad'a gashin kansa. Sallama yay atsakar gidan. Ladee ta amsa tana kallonsa. “Babandi irin wannan kwaliya haka lallai yau bikin Mamy Abu naku.” Ta k'arashe tana dariyar tsokana. Jakar ya ajiye yana yamutsa fuska ya k'araso dab da ita ya duk'a har k'asa ya gaisheta yace“Umma ni zan wuce jiya fa na fad'a miki gobe litinin munada jarabawa, ina yaran gidan ne?” Ladee tace“Suna gidansu Mamy ai ina gama musu d'umame sunaci suka tafi can, nima yanzu zan gama na tafi. Toh Babanka ya sanine? Deeni yace“Eh mun gama sallama tin a masallaci.” Kansa ta shafa tace“Allah ya tsaremin kai aduk ind kake ya baka sa'ar jarbawa. Ina Jamaluddin d'in?” Deeni yace“Ameen yana can yana wanka wai rakiya zuwa tashama sai yayi wanka, nace ya iskoni kafin na muku sallama keda Goggo da ummuh ya gama k'walisar.” Ladee tayi dariya tace“Ai bai kai ka k'walisaba jininka ne fa ai dole yayi k'walisa. Yanzu me Kaci?” Deeni ya yamutsa fuska yace“Uhmmm Jamalu ya dafamana tea munsha ya wadatar idan na sauka zanci abinci, bari nama Goggo sallama bacci take KO?” Ladee tace “Anya kuwa yau biki nasu k'ila tana shiri dai rabona da ita tin safe da muka gaisa, shiga ka gani.” Deeni ya isa k'ofar d'akin yana sallama ya cire takalminsa yana fad'in “Kinga ba aji zaki jaminba sallama nazo muyi.” Ya k'arashe maganar yana shigowa d'akin. Wani sansanyan k'amshi irin na Mamy ya daki hancinsa ya lumshe matsagaitan idanunsa, ya bud'e yana waige² yana kiran“Uwar gidana Nandou Hajja Bilkisu ina kika shigane ko kina baccine? Ya k'arashe maganar yana shiga uwar d'aka. Cikin sa'a akwai k'wan fitilar akunne, tar ya hasko masa ita. Tozali yayi da Mamy saman gadon Goggo mai rumfa ta baje d'ai-d'aya tana kwasar bacci, hankalinta kwance zanin jikinta ya janye kyawawan cinyoyinta duk awaje. Rigar jikinta 'yar yaluluwa batada hannu rabin k'irjinta duk awaje, cikin nutsuwa take fitar da numfashi tana baccinta kamar ba yau bane aurenta. Da sauri ya runtse idanunsa, zuciyarshi na wani irin bugu, k'aunar da yakewa Mamy babu algus acikinta, yana tsananin k'aunarta fiye da kansa zai Iya sadaukar da rayuwarshi akanta. Juyawa yayi da sauri domin fita. Ringing d'in da wayar Mamy ta d'auka wacce ta mak'ale a chaji ya saka shi tsayawa. Yana kallon wayar. Haka kawai yaji son d'aukar wayan. K'arasawa wajan wayar yayi ganin sunan mai kiran ya saka Deeni jin wani mugun haushinsa ya sunya ya fizge wayar a chajin yay picking d'in call d'in. Wayar ya manna kunnenshi ba tare da yayi maganaba. Daga can AUTA ya rangad'a sallama yana d'orawa da cewa“My Queen ina kwana? Fatan kin tashi lfy? Amaryata kinsan irin azabar da aka ganamin akanki? Wallahi aljani ya iskoni har saman gadan baccina yamin tsinannan duka da k'wak'waran kashed'i na janye aurenki.” Ya fad'i yana dariya. Deeni cikin tuk'uk'in bak'in ciki da jin haushin AUTA bai San lokacin da canza muryaba irinta aljanin Mamy yace“Kai AUTA zaka mutu yau ga matata Mamy na saceta mun tafi birnin k'udi's......”Dai-dai lokacin da Deeni yake wannan bayanin Mamy ta bud'e idanunta sabida yadda murya Deenin take fita da k'arfi itako daman bata nauyin bacci. “Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! Deeni me kake haka? Shine abinda Mamy ta fad'a tana saukowa daga saman bed jikinta har b'ari yake........*🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*

_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣*


Mamy ranta yayi mugun b'aci, jin abinda Deeni yake fad'ama Autanta. Kansa tayo gadan-gadan, ji take zata iya shak'eshi har sai yabar numfashi. amman toh ina zata iya da ganjememan k'ato mai ruwan sadaukai. Deeni ganin Mamy d'in da gaske take tana magana cikin masifa idanunta ya rufe, asiri zata tona masa yay saurin cewa“Kajita na satota na koma siffar k'aninta Deeni kaji sai kirana take amadadinsa...” Jin Mamy tace“K'arya yake karka...” Bai barta ta gama maganaba yay saurin damk'ota ya cillata saman gadon mai rumfar yabi bayanta, samanta ya haye ya sakar mata nauyinsa, ya sanya tattausan hannunsa ya rufe mata baki. Yaci gaba da cewa“Zaka barmin matata ko kuwa ya abin yake, ya kai bil'adam?” Yama AUTA tambayar yana danne dariyarsa. Daga can b'angaran AUTA hankalinsa amugun tashe jin kukanta kamar an kamata da kokowa, ya mik'e tsaye har wata irin zufa take karyo masa yace. Don Allah don Annabi karka cutarmin da ita ni na yarda kacutar dani akan ka cutar da ita, naji na yarda idan dai aurena da itane bakaso zan hak'ura akan ka cutar da ita, yanzu maidota wajan iyayanta bani ita muyi magana wallahi zan hkr indai zaka maidota.” Deeni yay wata irin dariya yace“Toh ka temaki kanka da kanka yanzu zan baka ita kayi magana sai na mayar da ita.” Ya k'arashe maganar yana cire wayar daga kunnenshi ya maida bayansa yana rik'e da ita ya d'ago kanta da hanunsa d'aya ya k'uramata mayun idanunsa yanajin yadda zuciyarta take bugawa da mugun k'arfi, jikinta na wani irin tsuma kuka take sosai tana kallon Deeni irin tijara da yake mata. Fuskarshi ya kifa saman tata yana sauke mata numfashin sa mai zafi. Yayin da ya matse mata baki sosai ba'ajin kukan nata. Ahankli ya d'ora bakinsa saman kunnenta cikin wata irin murya mai taushi yace“My love ki nutsu kuyi magana na rantse da Allah idan kika kuskura kika tonamin asiri zanyi matuk'ar gigita miki rayuwa da gaske zan saceki ayau na shiga duniya na aureki ko akasin hakan na rayu dake ina sonki na kasa hak'ura ga hanyar mallakarki mai sauk'i ta samu wallahi idan kika b'atamin shiri rayuwarmu ni dake duk zan wargaza mana jin dad'in mu, zan addabi rayuwarki ko na kasheki na kashe kaina, tinda ke bakisan kawaici ba, idan na fasa abinda na fad'a miki ni ba d'an Yahaya jikin malam Zaharaddin Yakubu nake ba, zan tadawa kowa hankali maza amsa masa aljani ya satoki amman yace zai rabu dake idan ya janye aurenki Oya.” Ya k'arashe maganar yana manna mata wayar akunnenta, ya gama kanainayeta ya mata k'awanya ya zuba mata mayun idanunsa yana shafa had'add'an kitson kanta. Mamy tinda take aduniya bata tab'a jin tsanar wani Abu ba kamar Deeni arayuwarta, wani irin tuk'uk'i zuciyarta take mata, ranta yayi masifar b'aci. Amman tuna abinda yace d'in tabbas zai aikata. Zuface ta karyo mata, amman sai dubara ta fad'o mata idan yanzu ta gama wayar da AUTA idan Deeni ya fita sai ta Kira AUTA ta fad'a masa komai ba aljani bane Deeni ne yake son rabasu. Da wannan shawaran ta amince cikin kuka tace“Autana karka tashi hankalinka zanma bayani daga baya ka amince ka fasa auren sai ya maidoni gida.” Ta k'arashe maganar cikin kuka tana runtse idanunta sabida kallon k'urulla da Deeni yake mata ya wani k'ank'ameta ko tsoron Allah bayaji. Hakan take kisimawa aranta. AUTA daga can hankalinsa atashe yace“Karki damu My Queen insha Allah bai isa ya miki komaiba na amince zan janye ya maidoki gida. Fatan dai bai miki komai ba? Mamy tace“Eh ka kwantar da hankalinka bai isa..... “No! Queen yi shiru ki basa wayar.” Mamy tace“Ni janyemin wayar yana magana. Deeni ya janye jikinsa anata yana fad'in. “Wlh kikace Uffan zaki sani. Wayar ya maida akunnensa yana sauka daga saman gadon yace“Ya kai Bil'adam inaji? AUTA yace“Maidata gida na janye Allah yasa haka yafi zama alkhairi, zan kirata zuwa anjima naji ko ka maidota.” Deeni yace“Insha Allah ngd bil'adam ka barni muradin zuciyata. Kitt ya yanke kiran ya jefa wayar cikin aljihun jeans d'in jikinsa. Mamy ta fashe da kuka ta had'a kai da guiwa bata ma ko son kallon Deeni arayuwarta. Murmushi yayi yace“Allah baki hkr aure dai dani za'a d'aura sabida na gama raina muku hankali, ni kam kinga na tafiyata makaranta kuma da wayarki zan tafi.” Ya k'arashe maganar yana isowa bakin gadon ya sanya hannayensa ya d'ago kanta ba b'ata lokaci ya fito da harshensa ya shiga lashe mata hawayen fuskarta, yana buga bayanta, jin zai had'e bakinsu ta had'iye kukan ta runtse idanunta, ta jimk'e bakinta tana sauke ajiyar zuciya ranta na matuk'ar k'una. Deeni ya kwantar da ita bakinsa dab da wuyanta, yana shafa fuskarta yace “My love bazan hanaki kuka ba, amman ki sani idan an d'aura aurenmu ki karemin mutuncin igiyata ehe kuma wallahi idan ba nan gidan ba ko sauran gidajen namu, k'ofar gida kika fita Allah ya isa ban yafe ba, ban yarda aje aiki ba ba da yawu naba. Ni na tafi sai na dawo zan Kira goggo Nandou zuwa dare ta bani ke.” Yana gama fad'in hakan ya manna mata kiss agoshi, ya fice daga d'akin. Mamy kasa komai tayi banda wutar tsanarshi da take ruruwa cikin zuciyarta. Deeni yana fitowa Goggo Nandou na k'ok'arin shiga d'akin. “Ah Deeni anzo wajan mutuniyar kenan?” Deeni ya rungume Nandou yana murmushi yace“Hummm Goggo wannan aljanin na Mamy d'an iskane wlh karku biye masa yanzu mukayi dambe dashi, wai ta fasa auren AUTA ni zata aura, kuji sa kai a uku. Shine fa ina cikin mata rukiyya Autah ya kirata na d'auka Ashe wai aljanin ya kirasa wai ya sace Mamy sai ya janye aurenta zai maidota, gida. Nace masa yayi tawakali da Allah ya aureta ba abunda ya isa ya mata yak'i fafur yace bazai Iya da tarun aljannu ba, jiyama duka yaci cikin dare, shi ya fasa na temaka na aureta yaga zan fishi jarumta nace A'a ina zan shiga da ita ba ruwana wlh can su k'arata shi ne fa aljanin yace sai na aureta ko ya kasheta. Da na amince yanzu wancan ya tafi wani rigimamme yazo yana fad'in ya tsaneni bazan auretaba ni kuma nace tunda shi arnene zan aureta d'in sai ayi abinda za'ayi.” Goggo Nandou ta janye Deeni tana rafka salati tana tafa hannayenta. “Oh! Ni Bilkisu wannan wace irin musuba ce take shirin samun mu? Daga wannan sai wannan? Ladee wacce ta fito cikin shiri take tambayar Nandou“Umma lafiya dai ko? Babandi wai daman baka tafi ba? Deeni ya d'auki jakarsa yace“Yanzu zan tafi Mamana.” Goggo ta kalli Ladee tace“Ba komai Hajara ba gidan biki zakije ba? Jeki kawai an fara aiki.” Ladee tace“Toh Allah ya kyauta.” Ta kalli Deeni tace“Shige muje ko sai kayi rana tafiya ne?” Deeni yace“Goggo ni zan wuce sai na dawo gobe jarabawa garemu.” Ya manna mata kiss goshi ya nufi wajan uwar tasa. Goggo tace“Allah ya tsare hanya Mai gidana.” Da “Ameen” Ya amsa. Hannunsa ta Kama suka fice Nandou ta raka Ladee da harara tana fad'in “Munafuka asamu na yayatawa gidan biki, ai d'an naki ma da kika ja inada tabbacin bazai fad'a miki ba.” Ta shige d'akin. Ak'ofar Ladee ta tsaya tana tambayar Deeni“Babandi wai meye Goggo take b'oyemin? Deeni yace“Tab kamar bakisan halintaba? ba wani abu kawai kukutawace nima batakai ga fad'amin ba fa kika katse mata hamzari.” Kansa ta zungura tace“Kai kasani mai zurfin ciki kawai.” Jamalu ne ya iso yana dariya“Kai umma da d'anta haka za'ayi salamar? Dariya tayi tace“Na saka masa albarka. Atare suka shiga har gidansu Ummuh, jama'a sai bak'i da 'yan cikin gidan kasancewar safiya. Har k'asa ya gaishe da bak'in suka keb'e da ummuh yace“Toh ummuh ni zan tafi sai na dawo Allah yasa ayi auren cikin nasara ya basu zaman lafiya da kwanciyar hankali.” Ya ciro dukkan kud'insa ya ciri na mota da wanda zaiyi 'yan buk'atunsa yaba ummuh sauran. “Wallahi Babandi bazan amsaba amshi k'ara maka zanyi kaida idan ka tafi sai ka shafe wata biyu haba rik'e amshi had'a da wannan banson musu” Dole Deeni ya amsa yasan halin Ummuh sarai bazata masa uzurin cewar akwai kud'i wajansa ba. Haka sukayi sallama Jamaluddin ya goyashi a mashin suka nufi gidan bus mai tashi k'arfe 11:30 am. Goggo yadda taga Mamy kwance hawaye na bin fuskarta tasan lallai sunyi artabu da Deeni. “Oh! Ni Bilkisu ke Bilkisu kukan me kike ko sune bake bace?” Ta tambayeta tana d'ago da ita zaune. Still Mamy batayi magana ba hawayen takeyi. Goggo Nandou “Oh! Kune kenan?” Mamy kallon Nandou tayi batace komai ba, sai langwab'ar da kai gefe. Goggo Nandou tace“Kai! Ifiritu ma yaci k'undun babansa kaji shegu 'yan iska, so kuke mu kwad'ata mu cinyeta ko ya abin yake? da bazatayi aureba? Yanzu jaririne akanta kome ake langwab'armin da kai?” Mamy ta rungume Nandou tana kecewa da kuka tace“Bana k'aunarsa na tsaneshi karku bari ya rabani da AUTANA, wlh ida kukayi gigin bin makircinsa zan kasheshi na gudu kubar daukar maganata wasa...” Goggo Nandou tace“Au abin kam Deeni zai dawo? Tanan kuka dawo kenan? Ai kuwa zakuci

Please Login or Register in order to submit comment