Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

band'akin. Zuhura tana bud'e k'ofar ta ga AUTAH. Fuskarta d'auke da murmushi tace“A AUTA ne ina yini.” “Lfy lau qaramar momy, fatan Queen tana lfy inata kiranta shiru hankalina ya tashi?” Zuhura tace“Eh lafiyarta lau sai ciwon kai tasha magani amman da tai bacci ya bari, bismillah shigo....” “A'a amata magana ba sai na shigo tazo mu gaisa.” Zuhura hankalin AUTA yake burgeta, tana shiga ta isko Mamy na sallah. Tana idarwa ta fara kwararo addu'o'i. Zuhura tace“AUTANKI yana jiranki.” Mamy ta shafa addu'a tace“Allah sarki rigimammena, bari naje naji da shi.” Ta k'arashe maganar ta mik'e da hijab ajikinta, tana baza k'amshi ta fita. Idanunsa ya zuba mata tinda ta fito, yadda take tafe cikin nutsuwa. “Assalamau Alaikum ya habiby.” AUTA ya washe baki ya amsa da. “Ameen wa'alaiki salam my Queen.” Murmushi suka sakarwa junansu. AUTA ya matso da fuskarshi dab da tata yana fad'in. “My Queen saura kad'an zuciyata ta buga,ina kiranki ban samunki.” Fuska ta k'wak'wab'e tai narai² da idanu tace“Autana ciwon kai ya sakani bacci wlh bansan lokacin dasu Nabila suka tafi gida ba, amman yanzu Alhmdllh!”. “Ko muje hospital? Idanu Mamy ta zaro tana murmushi “Haba AUTANAH wlh na warke.” Hira suke irin ta masoya har aka Kira sallar isha sukayi sallama ya tafi domain ya samu jam'i. Tana gama sallar isha Zuhura ta Kira Deeni ta sanar da shi yazo yakai Mamy gida. Mamy tai tsalle ta dire tace“Ban gane Deeni ya kaini gida ba? Wlh anan Zan kwana tinda Abbansu Ayman baya gari.” A'a wlh ba ruwana su Ya Yaro da Kansu sukazo kina bacci sukace akira Deeni idan kin tashi.” Tsaki taja ta mik'e tace“Toh wa zai tsaya d'in wallahi sai dai na hau napep ko na Kira mijina.” “Ok su mai unguwar kika raina? Idanu Mamy ta zaro tace“Kinga Zuhura banson raini ba dan kina amsa sunan uwata ba, ashekaru bakwai na baki aduniya, ki Kama kanki.” Ta k'arashe cikin masifa ta shirya ta d'auki Jakarta ta nufi hanyar fita. Zuhura dariya tayi sabida taji tsayuwar mashin tanada yak'inin Deeni ne. Tana bud'e k'ofar sabida saurin da take bata kula da mutum atsaye ba, sai jin ta bugi k'irjin mutum tayi, tai tagal² zatayi baya ya sanya hannayensa dukkan biyun ya rik'e k'ugunta, ahankali ya matsota jikinsa, ya zuba mata fararen matsagaitan idanunsa masu lumshewa. Cikin narkarkiyar murya, wacce tai k'asa sosai, bakinsa dab da hancinta, har suna jin bugun zuciyar juna, yace“Nutsu Mamy ina zaki haka ne? Ya tambayeta yayin da yay nasara jefa k'wayar idanunsa acikin Nata. Mamy ji tayi baki d'aya an zare mata lakkar jikinta, idanunsa su jefa mata wani abu cikin idanunta masu Kama da dafi. Idanunta ta janye cikin nasa ta daki k'irjinsa muryata can k'asa, tana kallon faffad'an k'irjinshi tace. “Sakeni ban saniba d'an rainin hankali kawai.” Ta k'arashe maganar tana matsar k'walla tanaso ya saketa. Baki ya tab'a ya saki k'ugunta ya Kama hannunta tana fizgewa bai saketaba, suka shiga ciki yama Zuhura sallama wacce sbd dariya har k'walla take. Asoron k'ofar ya tsaya har ta gama tijara sabida karta tara masa jama'a awaje. Zuhura tana hangensu sai dariya take. “Kai wuce ka tafi wai kai mayene? Ni fa wlh bazan hau mashin ba.” “Sai kin hau” Ya fad'a yana kiran number mai unguwa. Bugu d'aya ya d'aga da sallama. “Abbu gata tace bazata hau mashin ba.” Daga can mai unguwa yace“Taci gidansu bani itana naci mata mutunci, tinda batada kirki.” Deeni yana rik'e da hannunta ya rankwafo fuskarshi dab da kunneta yace“Sorry Mamyna.” Ya fad'i yana hura mata iskar bakinsa mai k'amshi, ya manna mata wayar akunnenta. Mamy tana matse idanu tace“Abbu bance komaiba.” “K'arya kike Mamy Babandi baya maganar banza, shekaru kika fishi, amman ya fiki hankali ban yarda ki sake minti d'aya gidan Zuhura ba maza hau Ku taho.” “Toh Abbu.” Tana amsawa ya tsinke kiran. Fizge hannunta tai ta Saki kuka ta duk'e k'asa ta had'e kanta guiwa. Deeni yabi bayanta ya tsugunna gabanta ya sanya hannayensa ya d'ago kanta ya zubama kyakkyawar fuskarta idanu. Tsakaninta da Allah kuka take baima San me zai mataba. Rungumeta yay k'irjinshi yana buga bayanta, ya manna bakinsa saman kunnenta yana karanto mata duk addu'ar da tazo bakinta yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya yaji tana saukewa ta lafe cikin jikinsa ko motsi batayi. Kanta ya d'ago yaga hawaye baja² ya wanke mata fuska, harda guntuwar majina. Ahankali ya kirata “My Mamy!” Bakinsa ya d'ora saman idanunta ya zuro harshensa ahankali yake lashe hawayen yana hura mata iskar bakinsa. Mamy har rawar wani irin sanyi da yake ratsa sassan jikinta take. Bakinsa ta kuma ji akan hancinta yana tsotse dukkan majinar hancinta. Mamy wani balak'ek'en sanyi taji yana ratsata ta k'ank'ame Deeni ta bud'e manyan lumsassun idanunta ta kallesa. Idanunsu ya sark'e waje d'aye bakinsa cikin hancinta. Ahankali ta kirasa“Deeni Zan Sha ice cream kaji.” Bakinsa ya zare ya tofar ya shafe mata fuskarta da tafin hannunsa mai laushi da fitar da k'amshin dad'i. Yace“Ok Mamy muje Zan siya miki.” Ya k'arashe maganar yana mik'ar da ita ya damk'e hannunta cikin nashi suka fito. Zuhura tace“Tabdijam mamaki! Ga Abu azahirance, wlh son juna suke abin tausayi ga shi bazasu sami junaba, wai waga soyayya.” Yana kunna mashin d'in ya kalleta yace“Hau muje ko?” Baki ta zumburo gaba ta Kama kafad'unsa ta haye . Zagaye hannayenta tai ruwan cikinsa ta kwantar da kanta gadon bayansa ta lumshe idanunta sabida muguwar nutsuwar da take samu. Cira mashin d'in yay cikin tuk'i mai nutsuwa yake tafiya har ya hau saman titi. Mamy ta kirasa “Deeni! Bacci nakeji don Allah ice cream kaji.” “Mamy kinsan wani Abu? Kai ta girgiza masa batayi magana ba. “Wallahi ni nasan sonki da k'aunarki zai kasheni.” D'agowa tayi ta zaro hannunta daga rungumar da ta masa, ta duma masa duka abayansa cikin murya son kuka tace“Ka daina cewa kana sona idan bason 'yan uwantaka ba.” Ta k'arashe mgnar tana sakar masa kuka ta kwantar da kanta gadon bayanshi. “Ok...OK! Allah baki hkr uwar renona yi shiru mana na daina insha Allahu kinji.” Shiru tayi ta sakeshi ta gyara zamanta bata sake magana ba,har suka iso gida. Jamaluddin tsaye ak'ofar gida yana waya. Kana kallonsa kasan jinin Deeni ne tsabar kamar da suke, tsayi Deeni ya fishi, da girman jiki. Yana ganinsu kiran ya tsinke, ya nufi wajansu, sabida nesa da k'ofar gidan Deeni ya tsaya. A lokacin da Mamy ta sauko ta rik'e hannun Deeni Ashgwab'e tace“Deeni d'an k'anina yaron kirki ice cream d'in bazan iya cin komai ba.” Ta k'arashe maganar tana masa k'ur da ido ta shagwab'e fuska. “Mamy zo muje ciki, kiji pls, wlh bazaki kasheni ba, haba! Ya kikeso nayi da raina? Hannunta yaja suka nufi cikin gidan. Jamaluddin yace“Aunty Mamy tah! Kai Ya Deeni ina kuka shiga ina nemanku....?” Mamy tace “Yauwa Jamal d'ina zo don Allah kaji, wlh Deeni kasheni yakeso yayi ba............”*🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*

_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣*

“Baya min biyayya sai yayi ta b'atamin rai, yak'i siyomin ice cream, Jamalu ko zaka siyo min...?” Deeni da k'arfi ya jata suka shige gidan cikin d'aga murya yake fad'in.“Jamaluddin ka iya kanka jeka ina zuwa zumiyi magana shareta rigima takeji ba komai ba.” Jamaluddin jin abinda d'an uwansa yace, yayi dariya yace“Ok bro Ku sasanta.” ya haye mashin d'insa ya nufi gidan kawu Sandari. Mamy ta tirje asoron k'ofa ta daki k'ijinshi tace“Deeni kasheni zakayi da bak'in ciki ko? Alhmdllh gobe ya warhaka ina gidan mijina zai kyautata min tinda d'an uwana ya kasa farantamin.” Ta k'arashe maganar cikin shashek'ar kuka tana fizge hannuta ta nufi ciki. Deeni kansa ya dafe ya fesar da iskar bakinsa mai zafi waje. Shi Mamy tana mutuk'ar ba shi mamaki tace bata sonsa amman tana masa zallar shagwab'ar da masoyi kawai kewa masoyinsa. Yana mamakin sangartata da shagwab'arta tamkar yarinyar 'yar 15 ko dan tana siririya jikinta mai kyau haka fuskarta mata bazaka tab'a zaton takai shekaru 20 ba bare 34. K'atuwar ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata kyawawan idanunsa yadda take tafiya abin burgewa, k'aunarta yake da duukan zuciyarsa, salonta abin sone. Sautin kukanta ya gama hargitsa masa lissafi, zafi yakeji har aransa. Murya ya d'aga wajan Cewar. “Mamy zaki tarwatsamin zuciyata wlh yanzu sabida Allah da girmanki zaki shiga kina kuka kicema su ummuh da Goggo me na miki? Zo kiji pls.” kafad'a ta mak'ale tana k'ara sautin kukan. Yay saurin binta ya fizgota ya jata bayan k'ofar soron, ya jinginata da bango yay mata rumfa da faffad'an k'irjinsa, ya toshe mata baki da tattausan tafin hannunsa, wanda yake fitar da wani sihirtaccan k'amshi, ya zuba mata lumsassun matsagaitan idanunsa. Had'e goshinsu yay, yana shak'a mata numfashinsa. Ahankali ya kirata. “Mamy kinaso na mutum ki huta? Nace Zan siyo miki ice cream amman kin hanani sakat. Gantsara masa cizo tayi atafin hannun nasa yak'i janyewa yay murmushi yace“Kiyi ta cizo in dai zaki huce Ok? Kai ta d'aga ta rik'e hanninsa gam tana cizonsa iya gaskiyarta. Idanunsa ya zuba mata yana murmushi hannunsa d'ayan yana share mata hawayen fuskarta yana shafa kyakkyawar fuskarta. Bakinsa ya kai k'ofar kunneta ya manna bakinsa ya hura mata iska yace“Ina sonki Mamy bazan Iya daina fad'aba sai na mutu duk da kuwa daga gobe Zan shiga halaka, ki tayani da addu'a pls I love u more my love Aunty. ” Ya k'arashe cikin wani irin salo yana Jan numfashi, wanda yake fita cikin kunnenta,ya manna wata wani hatsabibin kiss yana janye bakinsa. Mamy suma tsaye tayi k'afafunta basa d'aukarta bata san lokacin da ta Saki hannunsa ba ta kifa masa Mari mai ratsa jiki, ta fashe da kuka tana dukansa ak'irjinsa. “Nace ka daina furtamin kalmar so na tsani jin Kalmar daga bakinka bakaji sai ka fad'a? Toh ni bana sonk......” bata San ya akayi ba taji tattausan lips d'insa mai fitar da shegen k'amshin dad'i cikin bakinta ya cusa dukkan bakinsa cikin Nata ya sanya hannunsa saman k'ugunta ya had'eta da k'irjinsa, sun dunk'ule waje d'aya, ya zuba mata lumsassun matsagaitan idanunsa, yana girgiza mata kai, still ya danne mata baki da bakinsa ba tare da ya tsotsaba, hakan yaba yawun da ya taro daga b'angaransa silalowa tsakiyar mak'ogwaron Mamy wanda babu tsumi ko dubara sai ta had'iye. Manyan idanunta ta firfito waje lokacin da taji muryar Goggo Nandou tana fadin“Wallahi naji ihun Mamy da kukanta Ana soron k'ofar karfa ace mutanan b'oyen nan sun saceta? Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un!! Ta fashe da kuka. Mamy tsabar firgici da tsoro da tashin hankali yasa jikinta d'aukan mazari ta shiga had'iye yawun Deeni ta k'ank'ameshi gam tana sake tura bakinta cikin nashi gudun kartayi k'wak'waran motsi agano suna bayan k'ofar soro me suke aikatawa? Zazzafan hawaye ya wanke mata fuska tana k'ara kame bakin Deeni ta matse acikin bakinta ta runtse idanunta bugun zuciyarta ya tsananta, numfashinta na sama da k'asa, ganin hakan yasaka Deeni tallafo kanta yana k'ok'arin bata numfashinsa yadda numfashin nata zai daidaita amman tak'i yarda ta sassauta rik'on bakin da ta masa. Mai unguwa ya kama hannun Goggo Nandou yace“Kinaji fa da Deeni sukazo bai wuce tana wajansa ba, ab'angaransu tana masa shashancin nata ba. Amman bari mu lek'e bayan k'ofa dan naji kamar motsi wlh, Allah yasa ba la'anannan bane ya janyota wannan aljani da ya bayyana Allah ka mana maganinsa...” Mai unguwa ya fad'a yana Jan hannun goggo Nandou tana famar sharb'ar majina,suka nufi hanyar bayan soron k'ofar. Take Mamy taji fitsari na neman zubomata numfashinta na k'ok'arin tsawa cak. Deeni yay saurin zare bakinsa anata ya toshe mata da hannu yakai bakinsa cikin kunneta yace“Mamy ki taimakemu dubara d'ayace idan ba haka ba mun hallaka adangi wlh za'a mana mummunan zargi kinsan Goggo Nandou da tonon silili...” Cikin fitar haiyaci Mamy tana tsiyayar da hawaye ta rik'e fuskar Deeni da tafin hannunta,ta tsira masa manyan kyawawan fararen idanunta, wad'anda suka rikid'e suka dawo Ja,bakinta na motsawa ahankali tace“Deeni ka gama dani ka cuceni Allah ya isana na tsaneka daga yau na yanke duk wata alak'a tsakanina dakai, ka fad'amin hanyar da zamu tsira ba tare da an mana mummunan zargi ba? Ta k'arashe maganar idanuwanta na k'ok'arin rufewa numfashinta na k'ok'arin barin gangar jikinta. Deeni amugun firgice yake amman da Mamy ta suma ya gwammace arutsasu duk abinda za'ace ace badamuwarsa bace akan wani abun ya sameta. Da sauri ya had'e bakinsu waje d'aya yana k'ok'arin busa mata numfashinsa. Ta girgiza kai ta zare bakinta anashi cikin fizgo numfashi tace ina lfy numfashina normal, fad'i dubara su na dab da isowa nan idan kuma gawata kakeson gani karka fad'a...” Waiwaye adon tafiya, ya kamata muji asalin Shin su waye Zaharaddin (Babandi?) Da Bilkisu (Mamy?) Tushen su. Malam Zaharaddin Yakubu idrisa shine mahaifinsu Yahaya mahaifinsu Deeni. Asalin Malam Zaharaddin 'yan k'auyan Frandey ne k'aramar hukumace wacce take cikin jahohin dosso, wanda nema ne ya kai shi cikin garin dosson. Bazabarme ne gaba da baya, farine tas kyakkyawa tamkar buzu haka zuri'arsu take, akwai kyau gasu dogaye, wasu Nada gashi wasu basuda . Zaharaddin Talakane lik'is kuma maraya ya taso ba uwa ba uba sai 'yan uwan mahaifinsa suna gana masa azaba, hakan ta saka yabar k'auyensu, ya fito yawon almajirci. Amman sanadin almajircin, a dosso yana had'awa da aikin hannu, kowace sana'a ya samu idan dai zata kawo masa kud'i yi yake har ya mallaki k'aton fili na kansa, har ya Allah ya warware ya fara gini, ashekaran ne kuma aka masa aure da Bilkisu d'iyar kawunsa, Wanda shine mai sonsa kaf family's d'insu. Malam Zaharaddin zamane na amana sukayi da Billkisu, wacce Allah ya azurtasu da 'ya'ya bakwai, maza biyar mata biyu. Yahaya shine babba, mahaifin Zaharaddin, sai Sa'id mahaifin Billkisu (Mamy). Sai Ayuba Hafizu Mubarak, Murjanatu Zuhura, auta. 'Ya'yan malam Zaharaddin sun sami tarbiyya da karatun boko da na addini sosai, kasancewarsa mutum Wanda bai taso da iyayansa ba, yaja 'ya'yansa ajiki sosai suke rayuwarsu tindaga yarintarsu har zuwa girmansu, yayin duk Wanda ya isa aure cikin k'aton filin gidan ake masa gini d'aki uku da kitchen da band'aki duk atsakar gidansu,sabida ko kayi iyali ma. Ahaka kaf d'iyansa sukayi aure, da matansu acikin gidan. Sa'id mahaifin Mamy yanada 'ya'ya 6 Mamy ce babba yarinyar da tin randa tazo duniya takeda farin jini mutane sabida kyawunta, Masha Allah, abinda ya saka ranan suna Sa'id ya saka mata sunan Mahaifiyarsa Billkisu ake Ce mata Mamy. Sai da ta shekara hud'u aka mata k'anwarta mai sunan Maleeka sai tsakanin Maleeka da Ahmed shekara d'aya tak, bayansa sai da aka shekara hud'u aka haifi Nura sai Fauziya an haifi biyu maza sun rasu, daga nan sai auta Ihsan. Ayuba yanada 'ya'ya hud'u Kamal Sharif Sharifa Nafisa wacce suke kiranta Adama. Hafeez yanada yara biyar kasancewar matarsa akwai saurin haihuwa daga baya kuma ta tsaya lokacinta baiba. Waleeda Halima Sabilah Idris Kabiru. Mubarak nada yara uku Habib Rahina Saddiqa. 'Bangaran babban yaya Yahaya shekarasa goma da matarsa Jamila ko b'atan wata, Goggo Nandou ta matsa ya sake aure ba yadda zaiyi ya sake. Hajara Ladi akwai shegen kishi itace amarya amman masifarta ba kad'an bace. Jamila kuwa shiru² ce. Ikon Allah kusan lokaci d'aya suka samu cikin Jamila da ladi amarya. Sai dai Allah yayi ikonsa wajan haihuwa Jamila ta rasu bayan ta haifi d'anta zankad'ed'an k'ato fari jajir mai kyawun gaske, kowa ya jinjinawa Jamila da samun wannan kyautar ta Allah, amman ita ko ganinsa batayiba rai yayi halinsa. Ranan an shiga tashin hankali wanda ya saka Ladi nak'ud'ar dole aranan itama ta haifi d'anta cikin dare, k'aton gaske fari kyakkyawa, Wanda suke zallar kama da d'an Jamila kamar an tsaga Kara. Wannan zuri'ah ta jijjiga sanadin mutuwar Jamila mace mai kirki da kawaici., ga son jama'a Dole Ladi ta shayar da yaran ranan suna aka sakama d'an Jamila Zaharaddin yayin da d'an Ladi Jamaluddin. Haka ta rainesu kamar 'yan biyu duk da wataran tana nuna banbanci amman ba sosai ba, dan Zaharaddin bai tab'a sanin ita ba uwarsa bace dan Nandou da Malam sun hana afad'awa masa ko ya girma. Lokacin da aka haifesu Bilkisu Nada shekaru goma aduniya itace tai renansu cin kashinsu fitsarinsu, idan kaga basa wajanta tana makaranta, amman tafi shak'uwa da Zaharaddin. Tinda Zaharaddin ya bud'e ido yayi wayo aduniya yake kiran Mamy matarsa, ayi ta masa dariya, wataran idan 'yan wasan su na kanta ta biye masa wataran har dukansa take ta dawo tana kuka da aikin lallashi. Agunwarsu sai kace mijin Mamy ake gane Zaharaddin, yana k'arami. Mamy tin abin baya damunta har yazo yana damunta Ummuh tai tamata dariya tace ita ba ta yarinta ba? Haka rayuwa taci gaba har Mamy ta gama secondary school, yayin da lokacin Allah ya had'ata da Lawan wanda soyayya mai k'arfi ta k'ullu atsakaninsu. Sa'id yace ta dakatar da karatunta sai bayan tayi aure taci gaba. Mamy taima mahaifinta biyayya wajan dakatar da karatunta, har maganar aurenta da Lawan tai nisa manya su ka shiga lamarin aka sanya ranan aure lokacin Deeni yanada shekaru 8 aduniya, amman haka ya dinga kuka wai za'ayima matarsa aure, idan Lawan yazo fira Deeni kurasa yake sai Mamy ta dakeshi ta kurashi, Lawan yayita dariya yace“ Chérie karfa aje Deeni yanada rabo ajikinki? Kinsan k'udura ubangiji yawa gareta, mu muna namu Allah yana nasa kuma nasa shine daidai. Ni dai kar aje rabo ya kasheni.” Toh fa Mamy zata fara masa rigima da shagwab'a iri² harda kuka, sai yayi lallashi kafin ta sauka. Sabida Mamy shagwab'abb'iyace ta k'arshe, tin tasawarta haka take ga Saurin kuka bata raina abin kuka KO ya yake, shiyasa Deeni tin tashinsa yake tsokanarta bata ganin k'aramtarsa sai taiyi ta masa kuka shine zai hau cinyata ya rungumeta yana buga bayanta yace“Yi shiru Matata zo in goyaki bana son kukanki.” Toh fa zata kwashe da dariya idan yace goyo sabida lokacin shekarunsa biyar. Jamaluddin kuwa baya son ganin uwar rainonsu na kuka shima sai ya fara kukan, Deeni shine mai rarrashinsu. Ummuh wataran sai ta had'a dukan Mamy gani take sakarcine zallarsa budurwa gotai² batada aiki sai sangarta da shagwab'a da koke². Su Maleek Ahmed Nura Fauziyya sosai take basu dariya sabida su k'anninta ma basa irin abinda Mamy take. Mamy wata irin soyayya mai k'arfi suke da Lawan har ranan biki ta zagayo akasha biki aka kaita d'an madedecin gidanta, Wanda Lawan ya shirya musu dan suyi rayuwa mai kyau. Ranan da aka kaita ranan jini yazo mata dole sai romance d'inta yayi. Har tsawon kwana uku bai tsayaba soyayyarsu suke kwasa kamar zasu had'e junansu. (Sabida Mamy macace wacce take yawon karanta abubuwa duk wani abun da tasan na gyarane ko zata koyi salo iri² yadda zata siye zuciyar namiji ta iya sai tayi k'ok'ari wajan koyansa, da girki kala² ga tsafta da son k'amshi, ita akullun cikin k'amshi take ba dare ba rana k'unshi da kitso baya yanke mata, gata mayyar 'yar love.) Ranan da Mamy ta cika kwana 5 jinin ya d'auke, sosai Lawan yake murna bayan sallar isha ya tafi siyo kajin amarci wanda daga shi bai dawoba har tsakiyar dare Mamy da tsoro hankalinta ya tashi idan ta kirasa bata samunsa, ta Kira gidansu mahaifiyarsa tace ai tin yamma bai dawoba. Abu Lamar wasa Lawan sama da sati d'aya babu shi babu alamarsa, Mamy ta fige ta lalace sai kuka. Randa ya ciki kwana 10 aka samu gawarsa acikin ruwa, babu wasu sassan jikinsa. Ai Mamy tinda taga gawar ta zube asume tsawon sati bata San wanda yake tare da itaba. Lokacin da tadawo haiyacinta har anyi sadakar sati kowa ya Kama gabansa. Shi kenan Mamy ta zama wata iri bata magana, sai da iyayanta da 'yan uwa suka dage da rok'on Allah. Deeni kuwa murna yake an dawo masa da matarsa, dan bai tab'a zuwa gidanta ba ko da wasa, amman tana asibiti kullun yana can. Bayan mutuwar Lawan da shekara Mamy ta rok'i mahaifinta taci gaba da karatunta. Malam da Goggo Nandou da farko sunk'i amman daga baya suka amince. Shiyasa Mai unguwa bai hanataba yasan hakan zai rage mata damuwa. Ai kuwa zawarawa suka mata caaa tak'i saurarensu Sam har aka kwashe shekaru uku lokacin tana gab da gama jami'a, wani had'add'an matashin sauriya mai jini ajika, mai sunan Kabeer ya tisota agaba, tin bata yinsa har ta fad'a tarkon sonsa, sabida tsabar kirkinsa, har magana tayi k'arfi ya amince zata kammala karatunta agidansa har aikin da take buri bazai hanataba. Jin hakan Mamy ta amince, iyaye su ka shigo maganar ba b'ata lokaci aka sanya ranan aurensu.......*🙆🏻‍♀️MIJIN MAMY😭*

_GARKUWA WRT ASS..._

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*ςհɑԹԵҽɾ1️⃣3️⃣&1️⃣️4️⃣*


Ba jimawa da sanya ranan aurensu Mamy ta kwanta jinya mai tsanani, sai an kwantar an tayar, baki d'aya ta jeme kamaninta sun canza. Kabeer lokaci d'aya yaji ta fita aransa yace ya janye yama yafe kud'in auren. Ko sati ba'a rufe ba Mamy ta warke ras kamar bata tab'a jinya ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kamar wasa sai da Mamy tayi maza hud'u ajere ana saka musu ranan aure tana kwanciya jinya, da zaran sun janye sai ta mik'e daram. Ana k'arshene tace bazata sake kula kowane namiji ba. Haka kuwa akayi sama da shekaru goma maza nabin Mamy tak'i sauraronsu, Mai unguwa sun mata fad'in har sun gaji, abinda yasa basu matsaba ganin da ansanya mata ranan aure ba lafiya. Awannan halin kakansu Deeni ya rasu sakammakon 'yar gajeran jinya da yayi. Sunyi rashin kaka mai kirki da son jikokinsa. Mamy jikinta yanada kyau bata tsufa k'anninta duk sunyi aure dan yanzu agidan ba manyan 'yan mata sai masu tasawa, duk sunyi aure da yaransu. Hakan yana tayarma da Ummuh hankali addu'a take ba dare ba rana akan Allah ya kawoma Mamy mijin aure ya rabata da ciwon nan. Ta tsare mutuncin kanta, tin bayan kammala karatunta, ta jima kafin ta fara aiki a company su Autah wanda anan ne Allah ya had'asu. Mamy sam bazaka tab'a cewa ta tab'a auren shekaru dayawa da suka shud'e, dan dayawa kallon budurwa ake mata sabida jikin yara gareta haka fuskarta ta b'oye shekarunta. Ahaka su Deeni suka tasa suka zama samari har suka shiga university, yayin da ya addabi rayuwarta da kalaman soyayya, ga nuna azababban kishi akanta, da zaran ya ganta da wani sai ya ladabtar da ita da salonsa mai kashe jiki. Mamy ta tsani jin Kalmar nan taso wajan Deeni yaron da ta raina da hannunta. Deeni had'add'an gayene na nunawa sa'a dogo fari ingarman namiji mai cikar hlitta, yanada yawan fara'a da son 'yan uwansa ga shi da kyauta kamar me saidai idan bayada shi 'yan uwansa mata kowace indai yana gari da ansha kwana zai siyi wani abu ya kai musu shiyasa yakeda frin jini cikin 'yan uwansa kowa Deeni. Haka tsakaninsa da Jamalluddin akwai shak'uwa mai k'arfi suna k'aunar junansu sosai. Deeni mutum ne mai tsananin son gayu ga tsafta da son k'amshi, shiyasa 'yan mata suke rubibinsa 'ya'yan masu kud'i da talakawa, amman basa gabansa. Karatunsa ya maida hankali a Naimey yake karatunsa université Abdou Mounmouni. B'angaran Business. Deeni mutum ne mai masifar son business arayuwarsa Sam baya k'aunar aikin gwamnati yafi son yaci gashin kansa. Ahaka Mamy ta had'u da Autah wanda yafi shekara yana naci kafin ta amince ta soshi har ta yarda da maganar aurensa. Kowa a dangi dad'i yakeji wannan gamin Mamy bata kwanta jinya ba, sai yau da aljanunta suka bayyana. Tahir Habibu Hambali Autah su ukune wajan iyayansu shine babba Ammar na bisan sai Hibbah dukkansu sunada aure. Allah yaba mahaifinsu arzik'i Masha Allah, kowannesu awaje yayi karatu, sunada nutsuwa da tarbiya arzik'in mahaifinsu bai saka sun b'ata tarbiyarsu ba. Autah auren soyayya sukayi da Siyamah matarsa, yaransu uku, Haneefa Ramlat sai Abduljalil wanda ta mutu wajan haihuwarsa. Tin bayan mutuwarta saman da shekaru biyar bai tab'a jin son wata 'ya mace ba sai akan Mamy wacce yaci wahala kafin ya samu kanta, har ta amince da shi, Mamy tana son Autah sosai, tana k'aunar su rayu tare sabida kirkinsa da addininsa. *Dawowar labari.* Deeni ya tsareta da kyawawan idanunsa masu lumshewa, ya rik'o fuskarta ahankali yakai bakinsa k'ofar kunnenta cikin sansanyar murya mai fitar da daddad'an sauti mai dad'i yace“My Mamy dabara d'ayace kiyi aljanun k'arya, ki k'akk'afe idanunki ki fara

Please Login or Register in order to submit comment