Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[7/28, 10:52 AM] Mrs Abubakar 🌹: 🎊🎊🎊 *BA SO BANE* 🎊🎊 🎊

*_STORY $ WRITTEN_*
*_BY USAINA.B ABUBKAR_*
*_(MRS ABUBAKAR CE)_*



πŸ’« *DA BAZAR MU WRITEER ASS* πŸ’«




*We are here to make you happy, smile, educate and to realizd that we are best among all.......DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

1βƒ£βž–5⃣


BISMILLAHIR RRAHMANIR RSHIM



Kuka take sosai tamkar Ranta zai bar gangar jikin, har tana shid'ewa dan tsananin kuka.

Shiko yana tsaye akan ta sai aikin rarashi yake da ban baki, cikin sanyi halin, irin na shi yace"haba JAWAHIR, me kike so ki zama ne? shin wai baki yarda da kaddara bane?, Allah da ya bamu shi ya fi mu kaunar sa, karki manta duk wani me rai sai ya d'an-d'an na d'acin mutuwa, yanzu da kike wannan kukan kin kyau tawa Baffa kenan? a halin da ake ciki a yanzu babu abin da yake buk'ata a wajen ki sai Addu'a, kuka babu abinda zai kara mki sai ma dai ya ja miki wani ciwon, karki manta ina tare dake, kuma nayi mai al'kawarin baki farin ciki har karshen numfashi na." ya fad'a cikin sigar rarashi.

JAWAHIR ta d'ago tayi mai wani kallo kana ta mayar da kan ta k'asa ta ci gaba da kukan ta, gani bata da niyyar yi mai magana dole tasa ya bar d'akin, zuciyar sa na mai kuna.


yana fita tace"mugu kawai." ta fad'a tana hararar in da ya tsaya tamkar yana wajen.


yana fita yaci karo da matar Baffa, cikin nutsuwar sa yace"sannu Adda ya 'karin hak'urin mu?." ya fad'a yana mata kallon tausayi.

"Umm! hak'uri mun gode Allah, halan wajen JAWAHIR kaje ko?." ta fad'a tana mai wani kallo.

"Eh kin san ita yarinya ce dole sai anayi ana duba ta, musamma yanzu da take cikin halin kad'aci da maraici, na babu uwa babu uba Adda ina masifar tausayin JAWAHIR, dan Allah ki taya ni rok'on amanar nan da aka bani." ya fad'a yana mata kalar tausayi.

ita ma fuskar tausayi tayi mai kana tace"kar ka ji komai in dai ina gidan nan ai JAWAHIR ta ka ce Allah ya taya ka ri'ko." ta fad'a tamkar za tayi kuka.

haka yayi waje yana jin sa gaba d'aya sai a hankali, dan yana tsoron wannan kukan da take.

tana tafe tana tafa hannu wa har ta isa cikin d'akin sai da ta rufe 'kofar, sannan ta isa gare ta, A hankali ta zauna, tana me sauya fuskar ta zuwa damuwa tace"taho nan yarinya ta kinji, bar kukan haka nan, kar kan ki yayi miki ciwo." ta fad'a tana jawo ta jikin.

JAWAHIR tayi tamo a jikin Adda tana share k'walla aka-aka, in dai Adda ta dage sai shafa mata baya take alamar rarashi, sai da taji tayi shiru sannan tace"yarinya ta ya kama ta ki kwantar da hankalin ki haka nan, na gaya miki mudin ina raye bazan bari ki tare a gidan yaron nan ba, ni da kai na zan saka shi ya sake ki, kin ga sai ki aure wanda kike so ko?." ta fad'a tana d'ago fuskar ta dan ganin yanayi da zata shiga.

hannu ta saka tana share k'wallar da ta zub'o mata tace"yauwa Adda ki taimake ni, dan wallahi bana son shi, a yanzu bana ko kaunar gani fuskar sa, ina mutu'kar mamaki dalilin da yasa Baffa ya aura mini shi, ni wannan wasihar tashi ba tayi mini dadi ba wallahi." ta fad'a tana sake rushe wa da kuka.

Adda tayi murmushi irin nasu na manya tace"to ai duk laifin ki ne, ko ni a baya nayi tunanin soyayya kuke, yanda kuka nuna wa junan ku kula wa, ya d'auke ki ya kai ki wajen sha'katawa ku jima a can, ko kun dawo gida babu hutu haka zaku kara dasa sabon zama kuna hira har sai nayi magana sannan ku tashi, mahaifin ki bai da laifi ko kad'ai da ya aura miki shi, da tun farko kin fito kin nuna bakya son shi ai da ba'ayi miki auren zumuci ba." ta fad'a cikin kula wa.

Tamkar dolowa haka ta dawo, ta d'ago da sauri tace"to yanzu ya zanyi Adda?." ta fad'a cike da neman mafita.

Adda tayi murmushi gefen baki tace"hanya me sauki da zaki bi shine ki fito, ki gaya mai gaskiya bakya son shi, ki gaya mai ke a d'an uwa kika d'auke shi uwa d'aya uba d'aya ba wai miji ba, ki ce mai baza ki iya zaman auren dashi ba, in dai kika fad'a mai haka to ba makawa tunda yana son farin cikin ki zai sake ki, nima daga nan kin ga sai na bashi k'anwar ki gudun duniya kar ta zargin wani abu."

tayi shiru tana son tayi tuananin me tsaye amma Adda ta hanna ta, sai zance take d'ako mata, kuma duk gaskiya take fad'a mata aiko tayi na'am da maganar ta.



__________
___________

Zaune suke shi da abokin sa, yayi shiru ya tafi duniyar tunanin Abdulrahman, ya tsara mai idanun yana kallon ikon Allah, domin gaba d'aya abokin na sa ya sauya, zuwa can yace"IMARAN wai yanzu me yake damun ka ne?, gaba d'aya ka sauya tun rasuwa Baffa, kar fa ka manta kai ne kake yiwa matane wa'azi akan mutuwa ko in wata kaddara ta fad'o musu, shin yanzu kai baza ka iya hak'uri da ta kai kaddara ba, tabbas na san akwai zafin da ciwon rabuwa da iyaye amma wannan damuwar da kake sawa kan ka, akwai matsala gaskiya yana da kyau ka farga, ka rage ta ko yaya ne, yanzu irin sakkayar da za kayi ma Baffa kenan? mutumin da bai da burin da ya wuce sanya ka farin ciki, yanzu ya bar duniya addu'ar da za kayi mai ta gagare ka sai tunanin da sharar hawaye, anyya kuwa MAN din da na sani ne?." yayi maganar cike da shak'u.


ya sauke wata ajiyar zuciya kana yace"tabbas ba kayi karya ba, rasuwar Baffa na tab'a ni sosai domin yanzu ne nake jin kewar sa, amma abinda yafi damu na a yanzu shi ne JAWAHIR, ban san me yasa Baffa ya aura mini ita ba?, wallahi ban tab'a mata so na aure ba ina mata son ne kawai na 'yan uwan taka, domin kallon 'kanwa nake mata, ga kuma marainci uwa, ban san me yasa yayi wannan tunanin ba na had'ani aure da ita, yanzu fa matsayin da muke da ita tunda Baffa ya rasu yarinyar nan ko kallon mutunci bata mini, kuma kullum cikin kuka nake samun ta, ka dai duba tsayin lokacin da muka d'auka da sani akawai aure, sannan ni yanzu ya zanyi da NABEELA?." yayi magana cike da damuwa.

Abdulrahman, ya sauke ajiyar zuciya yace"kana da gaskiya aboki na, amma abinda nake so ka gane a nan shine, Baffa yayi haka ne domin JAWAHIR ta samu ingantaciyar kulawa tunda ya san duk rutsi bazaka cutar da ita ba, kuma zata samu farin ciki me d'aure wa a tare da kai, MAN ina so kayi biyayya ga wannan bawan Allah da ya riga mu gidan gaskiya tabbas zaka samu alhairi akan abinda yayi, karka manta shine komai na ka, NABEELA kuma wannan ba wata matsala bace, tunda tana da fahimata ko ni nan zan mata bayani, ka shawo akan yarinyar kawai ku zauna lafiya, kai da ka samu aure a sama malamn ai kai d'an gata ne, ni ai mini mana." ya ka karshen maganar da zolaya.

IMRAN ya kai mai duka yana cewa"yanzu fa ka gama maganar kirki amma sai ka had'a sha'kiyanci, insha Allah zanyi abinda kace aboki na zan gwada naga ko zanyi nasara, a wajen ta na kuma cika mai burin sa na saka 'yar sa cikin farin ciki." ya fad'a yana murmushi da d'aukar niyya..

Abdul yayi dariya yace"ko kai fa mutumi na angon shekaru da dama." ya fad'a yana tashi a wajen sa dan ya san duka zai sha.
IMRAN yayi mai wani banzan kallo sannan ya mik'a yana barin wajen.


Su biyu ne a d'aki, sai hawaye take sharewa akai-akai tace"to yanzu ya zanyi, fisabilillahi mutmin nan sabida mugun abu shine ya aure mai 'yar sa, sabida kar na samo abinda nake hari, to wallahi bazan yarda ba ko ya aure ni ko kuma ita ma kan ta yarinyar na raba ta da duniya ko wa ya huta, ni kuma na samu zab'in rai na." ta fad'a cikin kuka.

"Kwantar da hankali ki, matakin da muke akai yanzu ita JAWAHIR din na da muke komai akan ta to, ita ba ma ta shi take ba, dan bata da burin da ya wuce na saka ya sake ta, dan yanzu haka daga wajen ta nake tun safe take kuka ita lallai sai na saka an sake ta, nayi mata dabaru da wayo sosai ta yanda bazata gane ba, kuma Ahmadullahi ta hau kan hanya yanda nake so, dan sai da na tabbatar da tayi barci sannan na fito, shi kuma yaro ai kamar kin mallake shi ne, mu dai bari yazo hannu sai yanda mu kayi dashi." Adda ta fad'a tana dukan cinya.

Jameelat ta tab'e baki tace"ke dai Adda kin cika sauri, ni abinda nake so naji kawai shine ya sallama ta shine kwanciyar hankali na, dan wallahi in ban same shi ba sai na kona gida nan." ta fad'a tana wani ciza baki sabida tsananin masifa da take cin ta.

Adda tayi murmushin gefen baki tace"ai bama za'ayi haka ba mudin kina tare dani, to ko da yaushe kece da nasara, abinda nake so dake shine kawai ki cigaba da boye kiyayyer ki gare ta har mu samu abin muke so bana so ki kuskure ko a face din." ta fad'a tana mata wani kallon.

Jameelat ta wani yamatsa fuska haka ne ya bani damar 'kare mata kallo, farace ita ma kyakykyawa da ita, domin tayo gado a wajen maman ta, tubarkala kawai zamu ce domin ta had'a komai ita ma, matsalar ta d'aya shine muguwar zuciya da son abin duniya...




*ASALIN LABARI.*



Alhaji BASHIR d'an asalin garin kargi ne aiki ya kawo shi garin kano, a nan ya had'u da matar sa me sunna ASMAU'l, cikin yarda Allah su dai-dai ta har aure ya shiga tsakanin su, da yake yana da d'an abun hannun sa ba laifi.

a hankali ya ringa d'ako yan uwan sa na can gida suna dawo wa maraya da zama, cikin yarda Allah ya kwashe su kaf manya ne kawai suka ki biyo su,

su hudu ne a cikin gidan su kuma duk a cikin su shine babba, haka kuma shi ya fara aure a cikin su, Alhaji BASHIR, Abdullahi, ADAM, NAFI'U. kan su a had'e yake sam basa nuna wa juna su bam-bamci ko hassda akan abinda wanin su yake dashi, da yake mahaifiyar su taji ma da rasu wa sai mahaifin su kad'ai ya rage musu wanda ya kafe ya'ki biyo su,

zuwan su birnin su ma suka fara aiki cikin yarda Allah komai ya fara zuwa musu cikin sauki da rangwamin, d'aya bayan d'aya suka fara koma wa gida suna aure, a hankali duk su biyun su kayi aure a can gida matan su suke da zama, sai da suzo birnin suyi yan kwana ki bayan kamar sati biyu zuwa uku su koma gida, haka su ke rayuwar su cikin rufin asirin Allah, BASHIR bai rage su da komai ba haka ya kan dauki matar sa suje garin su suyi kwana biyu a can kana su dawo maraya.

Ahmadulillahi ta wani bangare kuma dukiyar sa na kara hab'aka da bun'kasa, domin yana samu sosai lokacin tun duniya na kwance kudi na daraja, sai yayi dabara da zarar ya samu kudi masu dama da nauyi, sai ya siyi kadara ya ajiye a haka, a haka har ya tare filaye da gidaje sosai a garin kano da kauye, a cikin k'anne sa babu wanda ban mallakawa fili ba hata matar sa na ta daban, basu da wata matsala a rayuwar su da ya wuce rashin haihuwar ta, basu d'aura kan su damuwa ba sai suka mi'ka lamarin su ga Allah buwayi gagara musali, su ka dage da Addu'a babu dare babu rana,

NAFI'U ne kawai ya rage acikin su wanda bai yi aure ba shi ma iyayen su ne suka hana shi, domin yayi k'an'kanta a lokacin, RASHIR ya d'auke shi gaba d'aya suka dawo maraya zama tare dan ko ganin gida zaje to ba ya jimawa yake dawo wa, sun shak'uwa tsakanin su sosai wanda duk cikin yan uwan yafi ji dashi amma bai fito ya nuna a fili ba, haka abin yake a wajen NAFI'U,

kwacin tashi babu wuya a wajen Allah su sake shafe shekaru da watani, har Nafi'u ya samu matar aure a nan cikin garin kano BASHIR ya tsaya mai akan komai har akayi aure a nan jikin gidan sa ya bashi waje shi ma ya zauna tare da matar sa ZAINAB, suna cikin haka Allah ya bama su BASHIR karuwa wace tazo ma da ASMAU'L da larura, kullum cikin ciwo da jalen zuwa asibiti, a haka har Allah ya sauke ta lafiya bayan b'akar wuyar da taci, ta samu d'an namiji wanda ya samu gata wajen dangi biyu na mama da baba, yaro d'an gatan NAFI'U ranar sunnan yaro ya ci sunnan IMRAN , fari ne sosai na karshe ga kyau da yayi gado a tsatso biyu, haka aka cigaba da rainon yaro cikin yarda da amincin Allah.

Bayan shekara biyu da haihuwar IMRAN jikin Asma'ul yak'i dadi yau da lafiya gobe ciwo,
batai wani dogon ciwo ba Allah ya amshi abar sa,BASHIR yashi ga tashin hankali da rud'ani, haka yayi hakuri ya ci gaba da rayuwa inda aka mi'ka yaro ga zainab ta ci gaba da kula daIMRAN tamkar d'an da ta haifa a cikin ta, domin iya gata da kula war da d'a yake nema a wajen iyaye, zainab na k'o'karin ganin tayi mai ita, haka yaro ya ci gaba da girma shi ma cikin tarbiya me nagarta, lokacin da ya fara magan aka saka shi a makaran ta,

Me karatu iya gata IMRAN ya same shi domin zainab da Nafi'u sun d'auke shi tamkar d'an su na cikin su.

duk tsayin wannna lokacin da aka d'auka, BASHIR bai sake aure ko neman sa ba, haka yake rayuwar sa tare da baigen matar sa sai dan sa da yake ganin yaji dadi, a hankali damuwa ta taru tayi mai yauwa, ba a farga ba sai wayar gari akayi ya fad'a.

Ranga-ranga akayi asibiti dashi, BASHIR ya sha b'akar wuya da jinya me tsaye, komai na shi ya tsaya cak nakasuwan ci sa, a hankali da yarjejeni da kuma shedu ya bawa Nafi'u komai nashi, akan ya juya mai duk lokacin da Allah ya sa IMRAN ya girma yayi hankali had'i da aure ya malaka mai komai nashi, a lokacin ya raba komai biyu sannan ya bashi rabi akan shi ma ya juya ya bashi halak malak.
sannan ya saka a mayar da gidan sa, irin babban gidan nan, aka daura mai baine ka sake ginna wasu bangaren har uku, ga babban falo da akayi shi a tsakiyar gida ta yanda duk wanda zai shiga bangaren wani sai ya bi ta cikin sa, bayan an kamala komai gida yayi kyau da tsari, ya kaffa naci har sai da yan uwan sa gaba d'aya suka d'auko matan su suka dawo gidan da zama, ya kasance mata biyo ko wace da 'yar ta mace d'aya sai mazajen su biyu, NAFI'U dama shi yana gidan tun da aka gama gyara.
Babu jima wa dayin wannan yarjejeniyar Allah ya amshi abin sa, fad'a tashin hankalin da wannan a halin ya shi ga bata baki ne, shi kan shi IMRAN yaga tashin hankali domin lokacin yana da wayon sa sosai, yana da shekara 18 a duniya, dan haka sai ya saka abin a ran sa ya ringa rama da damuwa. hankali Nafi'u ya tashi, gaba d'aya ya mayar da kulawar sa ga IMRAN duk wani abu da ya san zai saka shi a farin ciki, shi yake mai.


suna cikin wannan halin ne shi ma matar sa ta samu juna biyu, wayo zu kuga murna, wajen dangi da abokan arziki, shi kan shi MRAN ba'a bar shi a baya ba, dan ganin yake kamar sune suka haife shi, ya d'auki son duniya ya d'aura wa cikin, kullum yana tare da Zainab a gida duk wani abu da ya san ya kama ta, shi yake mata, matan kawun sa su biyu, ko wace ta saka burin akan IMRAN ya dawo k'ark'a shin ta, ba dan komai ba sai dan dukiyar da suke hange mallakin sa ce, haka kuma duk yanda suka kai ga nacin su IMRAN bai ko yarda yayi zaman minti biyar da su a waje d'aya domin shi yaro ne me tsananin yawo da iza, ga basira da yake da ita, ga saurin fahimtar mutane, duk da har yanzu babu a wace ta fito da maitar ta a fili, haka kawai yaji basu kwanta mai a rai ba.


Comment
And
Shared
Please


Mrs Abubakar ceπŸ’ƒ
[7/29, 11:07 AM] Mrs Abubakar 🌹: *πŸ’«DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*πŸ’”πŸŒΉBA SO BANE πŸŒΉπŸ’”*
( *CUTA CE* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*








LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

_momyn mufeedah na gode Allah ya saka da alhairi_



6βƒ£βž–7⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Haka suka ci gaba da rayuwa, har Allah ya sauki Adda Zainab lafiya, murna a wajen IMRAN har ba a magana, ta samu mace kyakykyawa da ita tubarkala, Ranar sunna yarinyar ta ci sunna JAWAHIR, kishin saurin ta babu wanda yaji dadin wannan haihuwar da tayi, musamma ganin yanda IMRAN yake rawar jiki akan abinda ta haifa, sai gaba d'aya bakin ciki ya taro yayi musu yawa, gaba d'aya tunanin su ya tsaya akan yarinyar da uwar ta na gani sun bar duniya gaba d'aya, su ka shiga yi musu bita da k'ule kuma ko a fuska basu tab'a nuna wa ba, sai ma tsantsar kauna da suke nuna mata haka su mayar da bangaren su wajen zaman su, ba dan komai ba sai dan ganin suncin ma burin su akan ta.

Matar Abdullahi sunnan ta ADDA SAMIRA, tana da d'iya mace me sunna JAMELAT, sai matar ADAM, me sunna ADDA MAIRO tana da d'iya mace ita ma me sunna maman su BASHIR, wato KHADIJA, a tsakanin SAMIRA DA MAIRO babu wanda ya san abinda dan uwan sa yake 'kullawa, akan IMRAN, ko wace burin ta ya so yar ta, yara tun su k'anna, duk da shi ma lokaci ban mallaki hankalin kan sa ba, amma babu wace take gaban sa kamar JAWAHIR duk wata kula war duniya ya d'aura akan ta, ko abu zai siya to sai ya had'a da ita.

wannan dalilin yasa suka k'ara tsanar ta a zuciyar su domin ji suke tamkar su sha'keta a take ta mutu..

A hankali yarinya tana kara girma da wayo, ga shak'uwar dake kara shiga tsakanin su, tsakanin ta da yan uwan ta kuwa su ma ba'a bar su a baya ba, duk da sun girme ta sosai dan ko wace ta bata shekara biyar-biyar, tsakanin jameelat da khadiji babu wani tazara me yawa 'yan kwanaki ne kawai.


bangaren Adda Mairo da dan sausauci dan ita bata uzura kamar yanda Sameera ta dage ba, a cewar ta zata bari yara su girma a lokaci ita ma

Please Login or Register in order to submit comment