Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kare ba, haka kuma Allah bai nufa ba, in kuma kun ga kunyi nasara akai na to haka Allah yaso kune silar faruwar hakan, maza jarraba mu gani, ai gani a gaban ku ban gudu ba...." Maganar ta mak'alai sakamako marin da d'aya daga ciki ya zafga mata, ta saki wata siririyar k'ara, haka kuma bata bar murmushi ba, abinda ya sake fusata su kenan, d'aya ya nufe ta da wuk'a gadan-dagan zan nutsa mata..._

_Cak ya tsaya sakamakon shigowar wani da sauri yana cewa"yallab'e ga Imran nan kan hanya fa." yayi maganar yana sake duban hanya._


_Gashin kan ta ya damk'a da k'arfi yana ja yace" ki tabbatar kiyi abinda muka ce in ba haka yarinyar ki dake waje ita ma sai kin rasa ta, domin a gaban idon ki zan saka matar nan dake tare da ita ta harbita.." ya fad'a yana tura ta waje, sanna su kuma duk suka boya cikin d'akin._

_gani basa ganita yasa tayi saurin jawo littafin dake gefen bed din ta, fara rubutu cikin sauri da rawar hannu, tana gamawa ta yage kenan d'aya ya laik'o yana cewa"wallahi kikayu wani yunkuri na sarar dashi take zai harbe shi a gaban ki." ya fad'a yana nuna mata bindigar dake hannu sa..._

_wani kuka ne ya kwace mata dan ta jawahir zata iya hakuri da ita dan ceto rayuwar Imran domin shi din amana ce a gare ta, amma ya zama dole tayi sadukarwa sabida shi,,,,_

_wannan shine abinda ya faru._

*Ci gaba*


"daga ta auta, wanna ai hanya ce mai sauki bata mutun yanzu ba sai ta wahala, sai na gara mata rayuwar ta, sai na d'and'ana mata d'aci mafi zafi wanda har ta k'wanta dama baza ta manta dani ba, sai na sata cukin maraici me zafi, wanda tana raye ne a amma sai ta gwamce mutuwa da rayuwa, ku tuna shirin mu na farko, ku shigo da ita." shine abinda babban cikin su yace duk da har yanzu bai juye inda suke ba.


wata mata suka shigo da ita, daga gani matar tasha b'akar wuya a hannu su cikin rashin imani da tausayi d'ay daga cikin su yasa ka, wukar sa ya yanka mata mak'oshi, sannan suka d'auko wani abu a ruba suka bulbula mata a fusaka cikin k'a'karin mutuwa da fitar rai tana d'aya hannu sama ga azabar abinda suka zuba mata take fuskar ta ta shiga k'wa'kwamowa kafin wani lokaci tayi wani irin duhu duk sani ka da ita babu yanda za'a ka gane ta, jikin ta ya saki hannu ta ya fad'i kasa, kayan jikin Zainab suka cire cikin sauri suka sakawa matar sanna suka fice cikin yan dak'iko kad'ai, Zainab sabida tsananin razana bata san lokacin da ta suma ba har su ka gama abinda za suyi tana nan zaune, haka suka jata tamkar kayan wanki su kayi gaba da ita..

Imran ya turo 'kofar da masifar gudu kirjin da na bugawa yana ci gaba da kiran maman nashi, iya karfin sa abinda ya ja hankali mutane wajen kenan kowa yayo part din cike da firgici..

Cak ya tsaya cikin halin furgici da d'imuwa, shi bai shiga ciki ba haka kuma bai koma da baya ba, a haka mutane suka shigo suka same shi, duk rashin imani mutun ya shigo sai ya koma da baya da sauri, take labari ya kad'ai ko ina na cikin gidan, dama mutane wajen..

Adda Samira duk irin masifar ta da makircin ta, sai ta tsorata da irin kisan da akayi ma Zainab, take tunanin ta ya tsaya cak.

Adda mairo kuwa babu abinda take sai kuka dan soaai ta gigiza da lamarin ita ma tunanin ta ya tsaya cak.

Jawahiir dake tsaye tun d'azu kamar wata zautaciya, babu abinda take sai bin mutane wajen take da ido gaba d'aya ta kasa fahimtar komai, haka kuma har yanzu taki yarda da abinda kunnen ta yake ji mata, kamar ana tura ta haka ta isa inda yake yake, ita ma cikin hali hauka ta zauna kusa dashi tana zuba mai ido...

_comment nake bid'a_
Shared

Mrs Abubakar ce🤙
[8/3, 1:45 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...


1⃣4⃣➖1⃣5⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Ta jima sosai tana kallan sa, can ta kai hannu kafad'ar sa tace"me ya saka kuka ne My!?" ta fad'a tana wani karkata kai gefe, abinda ya zama aladar ta...

Sai yanzu yaji wani d'umi aka face din sa, mutane dake waje shima ya bi da kallo cikin tsananin firgici, ya ture Jawahir gefe sannan yayi kan gawar da gudu, yana kiran sunnan ta a haukace "Mama!!" ya kai hannu zai tab'ata cak ya tsaya sakamakon d'ank'e mai hannu da akayi kam ta rik'e shi tana mai kallon tsana, idanun ta tamkar garwa shi ta watsai mai mari har biyu ajere, sanan ta nuna shi da yatsa idon ta na fitar da k'walla me zafi tace"munafiki ananamimi, mugu azalime wanda bai san halaci da mutunci ba, yanzu sakayar da zakayi mata kenan? ta d'auke ka tamkar d'an cikin ta, taci kashin ka, taci fitsarin ka, ta baka ingantaciyar tarbiya, ta baka kulawa fiyya da tamani, amma shi ne ka kashi ta!!? wannan shine sakayar da zaka yi mata kenan!!?" ta fad'a kukan ta na fitar da sauti me karfi.


Imran ya d'ago da sauri yana mata wani wula'kantace kallo, idanun sa suka kankance , sun rine da b'acin rai, jin ta ambaci kisa sai kuma gaba d'aya kwakwalwar sa ta tsaya cak, ya dan na fahimtar komai sai ido kawai da yake bin mutane gun dashi..

Jawahir ta matso kan gawar tana kallon ta, cikin mutuwar jiki zama tayi a gaban ta hawayen ta na d'iga akan gawar, ta d'auki lokaci me tsaho akan ta sannan ta mayar da kallon ta ga mutane waje murya cikin rauni tace"wannan ba Mome na bace, tabbas ba ita bace wallahi." ta fad'a cikin zautuwa..

kowa na wajen tausayi ta bashi, dan gani suke mutuwar ce ta buge ta har ta sa ta yin hak...

gani babu wanda ya kula ta sai ma kuka da suke, ta mayar da duban ta gare shi, sai ta gani kamar baya cikin hayyaci sa, a mutu'kar hasale tayi kan sa cikin kuka ta shiga jijiga shi tana cewa"kayi magana mana My!? ka fad'a musu ba mome bace dan Allah." ta fad'a tana zamewa kasa cikin matsanenci kuka..

wace ta mari Imran tazo ita ma tana hawaye, ta d'ago Jawahir tsaye tana cewa"tunda ya san shi ya kashe ta dama me zai iya cewa? Jawahir ya cuce mu ya rabu da 'yar uwar mu a lokacin da take tsaka da farin ciki.."

maganar ce ta mak'alai mata sakamakon, ingizata da Jawahir tayi cikin tsananin kuka, da bakin ciki ta nuna ta da yatsa tace"karki sake! karki sake! had'a shi da mumunan laifi, nayi imani da Allah Yaya na ba zai iya ko da kashe kiyashi ba, bare kuma mutun, shi ko kin manta duk jini d'aya ne in har duk kan ku nan kun yarda da abinda tace, to ni ban yarda ba, kamar yanda duk duniya in zasu taru akan wannan mome tace bazan tab'a yarda ba, ban yarda da My dinna shi yayi kisan ba, kuma zan sa shi ya fad'a muku da bakin sa!.." ta fad'a tana ma mutane kallo tsanan duk da sun kasance su din jini ta ne..


ta sake zuwa gaban tana goge hawayen ta duk da yaki tsaya wa, hab'ar sa ta kama tana saita face din sa dai-dai tata, tace" My! ina so ka fad'a mini gaskiya me ka sani akan wannan game din, domin ni game zan kira shi tunda na san baza ka tab'a aikata wa ba..?" ta fad'a tana d'an matsa mai hab'ar .
shiru yayi babu magana, hakan ya sake ingiza ta.


suna cikin haka sai ga su Baffa sun shigo, cikin tsananin tashin hankali, da rud'ewa domin kiran gagawa akayi musu, akan abinda ke faruwa.

Baffa Nafi'u jiki na rawa ya isa ga gawar cikin b'arirn jiki, kallo d'aya yayi mata ya kawar da kai gefe yana dafe goshin sa da hannu bibiyu , idanun sa ya rrine dan tsananin damuwa a hankali ya fara karanto duk Addu'ar da tazo bakin sa.


Baffa Abdullahi ne da Adma ne suma suka iso ciki hargitsi, cak suka tsaya suna kare ma gawar kallo, Abdullahi ne yayi karfin halin janyo zanin dake gefe ya rufe ta dashi yana fad'i" hazbinallahu wa ni'imal wakil, innalillahi wainna inalaihir raju'u.." yana dafe kan sa, dake bara zanar tarwatsi wa..

sosai waje ya d'auki sautin kuka kamar time din abun ya faru..

Nafi'u ya sake bude ta yana kallon ta can yace" No no no wanna ba Zainab bace, Wallahi ba ita bace me yasa banji a jiki na ba, time din da Yaya Bashir ya rasu a jiki na naji nayi rashin wani babban jigo, amma ita me yasa banji haka ba, taya ma hakan zata faru me ta aika ta da za irin wanna mumunar mutuwar a'a wallahi ba ita bace..." ya fad'a yana gigiza kai, tashi tayi a wajen yayi bakin window yana laik'awa ko zai gane ta a wajen, gani babu kowa yasa shi bin hanyar toilet yana zafga mata kira iya 'karfin sa...


babu wanda bai tausaya mai ba kuka kam sai da kowa na waje ya zubar da hawaye, yana dawo wa d'aki ya dube Jawahir cikin wani irin hali yace"'yarinya ta ke kin yarda wanna Maman ki ce?" yayi maganar time din da ya isa waje da suke tsaye.

cikin wani irin yanayi tace"Aa Baffa wanna ba mome bace, domin lafiya kalau muka rabu da ita, daga time din kawo yanzu bai ci har tayi wanna duhun ba, mome na farace amma dube wanna gawar daka dukan alamu tasha b'ar wuya." ta fad'a tana sake bude ta babu ko d'igwan tsoro a tare da ita...

Baffa ya rungume ta a jikin sa, a tare suka saki wani rikitacen kuka, sai a time din Imran ya dawo hayyacin sa, cikin kid'ima yake kallon su, ga wani irin jiri da yake d'iban sa...

Baffa Adma ya karasa kusa dashi yana tare shi, duk da shima karfin hali yake...

kawai gani Y'an sanda su kayi sunyi musu kewaye ko wanne su hannu sa ri'ka da bindig, ciki tsanani mamaki Baffa yayi musu wani kallo sannan yace"ku kuma wa ya kira ku?" ya fad'a yana kare musu kallo.


Suma ido suka zuba mai, ta tsakiyar su ta ratso ciki b'acci rai tace"NI CE NAN." ta fad'a tana isowa tsa'kiyar d'akin..
bayan ta kuma 'Yan jarida ne..

cikin isa tace"ku kama shi." ta fad'a tana nuna Imran..

Jawahir tayi wani mugun tsalle ta dira a gaban su, tana girgiza kai tace"babu wanda ya isa ya tab'a shi.."

Baffa Abdullahi yayi mata wani kallo yace"ke kuma a suwa? menene hurumin ki da shiga abinda babu ruwan ki? me kuma yayi miki da kika 'kwaso mai 'Yan sanda kamar wani d'an ta'ada?"


"Ai wanna yafi d'an ta'ada hatsari da hatsabibanci, domin shi din mugune kuma makiri munafiki b'akin azalime, wanda bai san hallaci da alkhairi ba, maganar wacece ni kuma kafi kowa sani, tunda yayi sanadiyar 'yar uwa ta nima sai na zamo sanadin sa na zama a gidan kaso har karshen rayuwar sa." ta fad'a tana share hawayen da suka zubo mata..

Baffa Adam yayi mata wani bazan kallo yace"Ki ma dae na tunani makamanci wanna, Imran bazai iya kisa ba, bare kuma uwar ru'kon sa, ina tantama akan ki zayi wuya kema da wata kulaliyar kika zo, abu mafi sauki shine ki tatare munafikan da kika zo dasu ku fice mana a gida tun kan na nuna miki matsayin ki.." ya fad'a ciki tsanani b'acin rai..

Baffa Nafi'u ya kalle, Imran cikin sanyi jiki yace"yaro na fad'a mini gaskiya me ka sani akan wanna cas din?" ya fad'a cikin rarashi.

Imran yayi mai wani kallo aran sa yana tunani baffa ma ya yarda da abinda aka yayi kenan, kawai sai ya fashe da wani mahaukaci kuka..

kowa na waje ya zuba mai ido ga 'yan jarida da suke ta d'aukar shi pic da video, suka k'ara bada k'ami wajen abinda suke..

Jawahir ta tsuguna a gaba sa cikin kuka me fitar da sauti tace"dan girman Allah My! dan kaunar ka da fiyyan halita, ka bude baki kayi magana kar ka saka mini wasiwasi a cikin kai na, dama mutane baki d'aya, ka taimake ni kayi magana My!...??"

Baffa Abdullahi yazo gaban shi, shima yace"na san k'azafi akwai zafi, amma ka daure yaro na kayi magana ku koma zamu ji salama a ran mu, da gaske ne abinda a kace..?"


Baffa Adam shima ya matso yace" na yarda da kai yaro na, in duk duniya zasu zarge ka, ni bazan zarge ka ba please kayi magana...?"""

"Wai menene aiki ku ne ku kama shi mana.." Anty Nafeesa Yaya a wajen Zainab tayi maganar ciki karaji..

Aiko cikin sauri su kayi kanshi caaa....

cikin kuka da tashin hankali Jawahir tace"zafa ku aikata kuskure a rayuwar ku, karko tab'a mini shi, wannan ba Mome na bace.." ta fad'a cikin wata murya.


kan sa a kasa yace"Kiyi ha'kuri Jawahir wannan Mama ce..."

Cak ta tsaya da kukan ta haka mutane falo tsantsanr mamaki ya kama su..

su baffa suka juyo a tare, ciki rud'ewa da tsananin ki d'ima....

_Sai kuyi hakuri nayi baki babu gyara_
Comment
And
Shared


Mrs Abubakar ce🌹
[8/6, 12:07 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...


*_Asalam alaikum ina fatan kuna cikin 'koshin lafiya, ina me neman afuwar ku akan shirun, da kuka ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sabida wani dalili nawa daban, da fatan babu wace na b'atawa rai._*



1⃣6⃣➖1⃣7⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Hawaye kawai suke bin kuncin ta, gaba d'aya ta mak'alai a wajen da take, ta kasa ko da k'wak'waran motsi, sai ido kawai da ta zuba mai cike da tambayoyi.


Baffa Nafi'u ya k'arasa kusa da shi cikin wani mayuwacin yanayi, murya can ciki yace"ummm ama.a yaro na san ka ba tun yanzu na jima da sani waye kai, domin da wannan hannu na raine ka, ka ga ko baka isa kayi mini wayo ko karya ba, ka fad'a mini tsakani da Allah bana san wasa, ni a jiki na san wannan ba Zainab bace, jiki na yana bani tana raye amma tana cikin wani hali. ka taimake ni Imran ka fad'in gaskiya domin rashin ta babbar ilace a gare ni..." yayi magana yana jijiga shi...

cikin sanyi jiki ya fara fad'awa musu abinda tace mai time din da ya shigo, d'akin da kuma kukan da ya sa me ta tana yi, jiki sa na b'arii ya mik'awa Baffa nasa letter da ta bashi lokacin da ya shigo, yana fitar da wani hawayen bakin ciki..

Jikin baffa na rawa yasa hannu ya amsa, sai da ya rantsi idon sa yana fitar da wata kalar kwalla sannan ya bude ta, kallon farko yayi wa Letter ya tabbar rubutun Zainab ne, cikn mutu'kar kad'uwa ya fara karantawa jikin sa na rawa kamar mazari, yana zuwa karshen ya zub'e a wajen babu ko d'igwan numfashi...



Jawahir ta sake rud'ewa, gaba d'aya face din ta ta dawo jawur da ita sabida tsananin kukan da tasha, duk rashin tausayin ka in ka kalle face din ta sai ta baka tausayi, har yanzu tana nan inda take bata motsai ba..

Imran yayi kan kawun sa da mahukacin gudu, a jikin sa ya karasa fad'uwa cikin rud'ewa ya fara magana yana kuka yana komai yake cewa"a'a baffa kar kuyi mini haka, a'a baffa ban cancanci haka ba, bazan jure ba Baffa, dan Allah ka tashi bazan iya jure rashin ku a time d'aya ba dan Allah ka motsi, karka barni baffa..." ya fad'a cikin matsanancin kuka..


Anty Nafeesa ta saka hannu cikin isa da k'asai ta, ta dauki letter tana ya mutsa face ta fara karantawa a fili, take jikin ta ya fara rawa, idanun ta suka furfuto waje, sabida tsananin firgita tayi wargi da letter tana saki wani marayan kuka, sannan ta zube akan kafar ta kukan takaici na zubo mata..

Baffa Adam ne yayi k'arfin halin karantawa shi ma kuma a fili kowa yaji, jikin sa yayi mutu'kar yin sanyi, ya juya ya kalle inda gawar take yana fitar da kwallar tausayi...


Anty Nafeesat ta dube yan sanda tace"kuyi hakuri kuje kawai zanyi magana da ogan ku." ta fad'a tana had'a hannuwan ta waje gudu..

ba musu tunda sun santa suka fice a gida suna cike da jimami.

Kan yan jarida ta koma suma cikin lalame da ban baki ta samu su kayi delete din abinda suka d'auko duk da ran su bai so ba, amma yawan kudin da ta basu yasa suka goge amma fa banda wasu abubuwan da d'aya daga cikin su yaki goge wa...


Baffa ya kalle mutanen da suka cika d'aki cikin hawaye yace"mun gode Allah yasaka da alkhairi za ku iya tafiya." ya fad'a yana nuna musu hanya aiko cikin sanyi jiki duk su ka watsi, yan uwan Zainab kawai aka bari amma ragowar duk sun fece..

Baffan sa ya kama da taimakon Baffa Adam suka fita dan kai shi asibiti.

Baffa Abdullahi da ragowar mutanan gidan ne suke ta kokarin gyara gawar domin kai ta makwacin ta, kuka kam iya kuka sun shashi..

har yanzu Jawahir tana tsaye bata motsa ba, sai ido kawai dan yanzu ko kukan ta dai nayin sa.


Kafin a gama shirya Zainab, Adda Samira ta fito domin zuwa part din ta, ta kula da halin da Jawahir take ciki, tunda take ba tab'a jin tausayin taba sai yau, cikin taushin murya tace"yarinya ta hakuri za muyi wanda ya bamu ita ya amshi abar sa, ki dau dangana kinji." ta fad'a tana kama hannu ta, kamar wata sokuwa haka ta bita har zuwa part din ta, d'akin jameela ta saka ta game da cewa jameela, "ga yar uwar ki nan ki kula da ita sosai jameela kin dai san halin da take ciki a yanzu, bana son jin zance ko fitina ki kula da ita yanda ya kamata." tana gama cewa haka tayi waje abin ta tana share kwalla..

Jameela ta d'anne zuciyar ta, kana ta sauko wajen da Jawahir take, cikin tausayi tace"'kanwa ta, zo nan kin ji." ta fad'a tana bude mata hannu..

Jawahir ta kalle ta tana karkata kai gefe, fuskar ta cike da rauni ta isa gare ta tana tangad'i tamkar yar kwaya.

A jikin ta jameela tayi mata ma sauki, tana jin ta jikin yar uwar ta, ta saki wani marayan kuka duk rashin imani ka sai ka tausaya mata sai da tayi me isar ta sannan ta dawo tana ta sauke a jiyar zuciya akai-akai, jameela ko babu abinda take sai auki shafa mata kai alamar rarashi.


Yan uwan Zainab da makota gaba d'aya sun zo haka yan uwan mijin ta dama akwai yan tsirari, sai ragowar da suke iso su ma, duk wanda yaji labarin mutuwar ta sai ya girgiza, haka baffa dangin ta in suka gan ta sai su ce ba ita bace sam, maza da mata sun had'u a babban falon gidan kowa yana jimamin abinda ya faru..

Adam ya dawo gida inda aka bar Imran a can yana kula da Baffa Nafi'u, Allah sarki abin tausayi sai a time din Jawahir ta fito jikin ta sai rawa yake tana wani irin kuka, Anty Nafeesa ta kama ta har gaban gawar tace" kiyi shiru 'yata Zainab addu'ar ki take buk'ata yanzu ba kuka ba." ita ma ta fad'a cikin kuka.

Jawahir kasa tab'a gawar tayi ban da nishi da take sama-sama sabida tsabar kuka, ko wa sai da ya share k'walla saboda tausayin ta, bakin ta na rawa tace"Allah ya jikan ki." ta fad'a tana fad'uwa kasa, domin kafar ta ta gaza d'aukar ta, ji take kamar ba mome bace wannan dan sam bata ji a jikin ta tayi wani rashin ba, me yasa Imran zaiyi mata karya me yasa zai ce wannan mama ce... sai ta fara wani kalar tari idanun ta nayi sama da wani kalar fari kamar me shirin tada isaka. babu wanda hankali sa bai tashi ba gani yanayi da take ciki gwani ban tausayi.



Imran kuwa hankali sa ya gaza kwanciya, tunanin sa d'aya halin da ya bar gida a ciki gashi doctor yace yana so mutun d'aya ya zauna a wajen sa domin yana gaf da farkawa, duk da sun sha walaha kafin dai-daituwar numfashin...


Allah sarki Zainab kamar yanda ake ma ko wane mamaci gata in ya mutu a kashi makwancin sa haka ita ma akayi mata...


suka dawo gida maza sun daga harbar gidan in da mata suke daga cikin gidan, duk wanda ka kalla take zaka hango tsananin damuwa, jawahir tayi zuru-zuru da ita bata um bata umum sai ido kawai, bata da burin da ya wuce tasa idon ta akan imran ba, dole ya gaya mata gaskiyar ina momen din ta take...


Baffa Nafi'u sai da yayi kwana biyu asibiti sannan ya farfado, yana tashi babu abinda ya farayi sai sallolin dake kasa, bayan ya idar ya jima a zauna sosai yana ta addu'a sannan ya tashi, maganar farko da ta fito a bakin sa shine" ina take?" Abinda yace ma Imran kenan time din su baffa basu jima da tafiya ba..

Kan sa a k'asa yace"an kai ta gidan ta na gaskiya." ya fad'a yana share k'wallar da ta zubo mai...



Mrs Abubakar ce💃
[8/13, 10:21 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_*

Please Login or Register in order to submit comment