Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma sai tak'i rungume shi ta zaune gaf dashi tana wani sunna kai tace"My!! dama kana nan naje d'akin ka ina ta neman ka." ta fad'a cikin shagwab'a fusaka, kamar za tayi kuka duk da tana cikin nutsuwar ta.

IMRAN ya sauke wata ajiyar zuciya, cikin isa da iza yace"Sorry k'albi na! ai kin san duk inda nake ina nan din na." ya fad'a yana tab'a saitin heart din sa.

ta wani tsumshe ido kana ta ware su akan face din sa, tana wani karkatar da kai gefe them tana kallon sa, tace" nafi kowa sani haka, tunda duk jini d'aya ne, amma fa sai gaya mini me yasa yanzu ka ke tafiya ka bar ni?" tana turo baki gaba, had'i da duga kafa a kasa.

IMRAN yayi wani k'asaitacen murmushi, yace"'kanwa ta ina tausaya wa mijin da zaki aure, dan sai kin kusa kashe shi da wani shagwab'ar taki." yayi maganar yana tal'kace mata hanci.

ga mamaki sa kawai sai yaga ta fara fitar da k'walla hawaye wuwi.

Aiko gaba d'aya sa ya hargitsi a lokaci d'aya shi ma yana wani rawar jiki, game da kamo hannun ta cikin nasa ya matse da kyau yace"haba k'albi na, sani kan ki ne, duk duniya babu abinda nafi tsana sama da gani ki cikin kunci, bare kuma zubar hawaye ki, fad'a mini dalili wannan hawayen ki, ni kuma nayi miki alkwari da yarda Allah ko menene mudin bai zarce kima ba zanyi miki shi insha Allah..


Jameela ta gama cika da bakin ciki, domin ji take zuciyar ta tamkar wace aka watsawa, garwashe sabida tsananin kunar da take mata, tana cikin wannan yanayi ne na bakin ciki ta hango abinda zai tarwatsa mata zuciya..


Jawahir ta zamo daga kan kujera, gwiwowin ta a kasa har yanzu tana hawaya tace"ban san da irin kalmomin da zanyi gode ya a gare ka ba My!, ka nuna mini dukan gata kula wa soyayya da k'auna, gashi ko da yaushe burin ka ka sani a cikin farin ciki, kanayi komai domin nema mini farin ciki, gaba d'aya komai naka domin na kake yin sa, ni ko da me zan saka maka wanda nan gaba za kayi alhari da hakan? tabbas kai din ka cika cikaken masoyi na, na har abada wanda bazan manta hallacin ka gare ni ba, My! ina ma son so wanda bazan tab'a canza ka ba a matsayin ka na Yaya a gare ni wanda ya nuna mini gata, a lokacin da ka ambaci aure sai naji dama ina da hanya mafi sauki wanda zamu ci gaba da rayuwa tare, ba tare da nayi nisa a gare ka ba, tun yanzu na fara jin zafin rabuwa da kai Yaya na, bana fatan wannan ranar my! Ina jin ka sosai a nan Yaya.." ta fad'a cikin kuka hannun ta na kan kirjin ta...


Idon sa har ya kawo ruwa sabida shi ma yana jin zafin wannan ranar da zata zo, amma ya iya tunda kaddar su kenan, kuma hakan da zai mata shine cikar mutuncin ta da kuma samu farin cikin ta na har abada..

kafad'un ta ya kamo duk biyun yana zaunar da ita akan kujera, har yanzu kuka take marar sauti sai hawaye kawai da yake ambaliya..

hannu ya saka yana share mata k'walla cikin rarashi yace"amma kin fi kowa sani bana son gani hawayen ki ko?" cikin sauri ta shiga goge su tana girgiza kai alamar bazata sake ba..

"duk wannan gode yar ni d'aya amma naji dadi sosai, kar ki manta aure shine cikar mutunci ko wace mace, zan fi kowa farin ciki in ga na kai ki d'akin mijin ki, wannan shine buri na, karki damu da hakan domin ko kinyi aure ai muna tare, ko bazaki gani kullum ba, karki manta yanzu lokaci ne na waya da kuma hanyoyi da dama, fatan na Allah ya baki miji na gari wanda zai kula mini da ke d'ari bisa d'ari, ya so ki kamar yanda nake son ki, buri na ya saki farin ciki marar iyaka."
ya fad'a yana sake share mata k'walla.

Allah sarki wannan shine soyayyar gaskiya, kallon shi tayi na d'an wani lokaci sannan ta fad'a jikin sa tana sauke a jiyar zuciya, hannu yasa ka yana shafa bayan ta..

Jameela ta d'unk'ule hannu ta duka biyu tana ciza laib'e k'wallar bakin ciki na zubo mata, gani suna neman kashe ta da bakin ciki yasa tashi ta bar waje babu wanda ya kula da ita..

Abdullahi da tun zuwan jawahir, yana wajen a tsaya yana kallo tsantsar kaunar juna da suke nunawa take tausayin su ya kam shi, ya d'auki a niyyar cika musu burin su, domin ya san mudin Jawahir na tare da Imran bata ba bakin ciki..



Tana zuwa d'aki tayi wurge da wayar hannun ta, har sai da ta tarwatsi, tana sakin rikitacen kuka, me cin rai.

Addan ta dake zaune gefe d'aya ta d'ago tana kallon ta, sannan ta mayar da hankalin ta kan abinda takeyi tamkar bata san da wan zuwar ta a wajen ba...

sai da tayi kuka me cin rai, sannan ta ta fara magana "sam bani da nasara akan komai nawa,ni zai kalla ya gaya wa wannan kalaman ba ita ba, wai me yasa suke abu tamkar masoyan asalin ne? sun ishe ni Adda wallahi zan saka a kawar mini da ita, na gaji na gaji Adda." ta fad'a a tsawace.

a hankali ta tako zuwa inda 'yar ta take, cikin salon ta na yaudara, ta d'ago tana zaunar da ita bakin bed, ruwa ta d'ibo mata me sanyi ta bata a baki har sai da ta shanye, sanna ta nemi kusa da ita ta zauna tace" ina so ki koyi juriya da kuma d'anne zuciyar ki akan makkiyin ki, karki manta tunda kina tare dani keko kike da nasara, bana so ki kwafsa mana akan abinda muke shirinyi, so ki bi komai a sannu dan in kika bari aka samu matsala kema bazan barki ba." tana fad'ar haka ta fice a d'akin...



Abdullahi ya tare 'kannen sa gaba d'aya a d'aki d'aya su uku kawai babu me jin su, yayi duba izuwa Adam yace"na san a cikin nan babu wanda bai san irin shak'uwar dake tsak'anin yaran nan ba ko? haka kuma babu wanda yasan matsalar da na hango a cikin gidan nan namu, kaico nayi bakin ciki mutuk'a da na gano bakin zaren, haka kuma na gane ashe *ba so bane cuta ce* tun filazal, amma har yanzu muna da sauran lokaci, a cikin nan bana so ko d'ayan ku yayi mini tambaya akan abinda na fad'a yanzu kawai ina so ku ai watar ne, *Ranar jumma'a nake so A d'aurawa Jawahir aure."*

gaba d'ayan su suka mik'a tsaya game da cewa " *aure kuma?* *waye mijin?* "

*IMRAN* dashi nake so a d'aura kuma bana son jan zance kuyi abinda nace kawai, hakan da za muyi musu shine gatan mafi dadi da farin ciki a rayuwar su, dan naga abubuwa da dama a tare da su wanda ya sheda mini cewa tabbas suna son junan su amma sun kasa gane hakan, yau na sake gazgata abinda zuciyata take raya mini ba tun yanzu ba, kuma yau na gano wata kullaliya a cikim fam din mu.."

Nafi'u yayi shiru suna ta magana amma bai ce komai, tunawa yayi da daren jiya...


yana zaune a gaba sa kamar kullum, Jawahir na d'aya gefen ya d'ago yana kallon su cike da kaunar su, gani yanda suke hira tamkar masoyin asali, suna cikin haka jawahir ta wuce d'akin barcin ta dan lokacin barcin ta yayi, da kan shin ya raka, har sai da yaga kwanciyar ta sanna ya dawo wajen baffan sa,,


cikin hikima da wayo irin nasu na manya yace"yaro na ni ko na tambaye ka mana?" bai jira amsar shi ba ya d'aura da cewa"masali kamar yanda kuke kai da kanwar din nan, ka san a ran ka cewa komai da komai da kake nuna mata haka wanda nake maka musali dashi yake, katsam sai yaji labarin an bashi ita a matsayin matar aure, yanzu in haka ta faru a gare ku wanne irin mataki zaka d'auka?...

Murmushi yayi sanna yace"baffa mudin iri haka ta kasance dani, zanyi farin ciki amma bazan fara nuna wa ba sai na tuntub'i ita kanwar tawa akan tana da ra'ayin zama dani a matsayin miji, in ta amince nima zan karb'e ta a matsayi mata, ko da ko babu ra'ayin haka ran na zanyi biyayya ga wanda ya bani ita din, kuma zanyi k'o'kari ci gaba da bata kula har karshen numfashi na, amma in bata ra'ayi na bazan bata mata rai ko lokaci atake zan sauwake mata, ko dan ta samu cikar burin ta, amma tsakani na da kanwa ta ma bana fatan hakan ta faru, dan nafi kowa sani burin ta, ba zanyi fatan na ruguza mata shi ba, fatan na aura mata wanda yafi son ta da kaunar ta, a matsayi kanwa take gare ni kuma bazan sauya mata matsayi ba..." ya fad'i gaskiyar abinda ke ran shi, dan ahi mutune mi fad'ar gaskiya baya boye-boye ko kad'ai..

Baffa yayi murmushi yace"Allah yayi maka albarka yaro na, naji dadi sosai da kasan ce me fad'ar gaskiyar abinda ke ranka, Allah yayi muku zab'i na gari.."

*mun dawo*

tunann wannan maganar da su kayi yasa shi sake kallon Yayan na, yace" a kwai matsala fa, yaran nan su nama kan su son yan uwan ta ka ne kawai, amma babu zance aure tsakanin su, domin yaro na ya fad'a mini gaskiyar abinda ke zuciyar sa.."

Nafi'u ka manta da shirman sa, kayi abinda nace kawai abinda na hango duk cikin nan bazaku gane komai ba, su ma sai nan gaba za suyi alfhairi da gata da mu kayi musu,, ka manta komai da ku kayi dashi wannan ita kad'ai ce mafitar abinda na hango.."


duk da hankalin shi wani kwanta mai ba akan zance, amma haka ya daure ya amince akan jumma'a za'a d'aura musu aure ba tare da sani yara ko iyayen su ba, wanna duk tsarin Abdullahi ne...


zaune suke da Zainab tayi shiru bayan ya gama gaya mata abinda ya faru, tsakanin su da yayan shi, gani duk ya shiga damuwa sai gaba d'aya bata ji dadi ba, ciki hikima irin tasu tace"Baffan IMRAN sam banyi tsamanin hakan daga gare ka ba, a tunanin zakayi farin ciki 'yar ka ta samu mijin na gartacece, wanda zai kula da ita fiyya da tsamani, amma sai na ga akasin hakan a tare da kai, wallahi dan ban tab'a gaya maka bane amma wannan shine buri na, kuma naji dadi sosai, da yarinyar nan ta fad'a hannu na gari ko bazan bazata wutak'ata ba, fata na Allah yasa soyayyar su ta juye zuwa na auratayiya Allah ya ka mana lokaci duk da baza'a bari ko wa yaji ba, zanyi shagali na yanda babu me fahimar na meye sai ni d'aya.." ta fad'a tana saki dariyar farin ciki..

"Hmm baza ki gane bane, ni da yaron nan mu kayi magana kuma ya fad'a mini ra'ayin sa, sanin kan ki ne duk abinda zanyi dan na faran ta mai nake, me yasa yanzu zan nuna mai son zuciya, a'a ni farin cikin sa nake nema ba wai bakin ciki ba, amma zanyi hakuri da zuciya ta har naga abinda Allah yayi zai faru dan ni ban isa na sauya musu kaddar su ba wala me kyau ko akasin, Allah yasa haka ne yafi alhari a rayuwar su."

"Ameen miji na haka nake son ji kawai, amma ni ina ji a jiki na yaro na me biyayya ne ko da nan gaba ya san gaskiyar lamari bazai tab'a kin abinda mu kayi masa ba.""" tana fad'ar haka ta mik'e, dan zuwa waje da sauri wanda ke tsaye jikin kofar ta ya wuce, ita ma cikin sauri ta rufa mai baya, inuwar sa kawai ta gani amma bata ga kowa ba, sai ta sa a ranta kila wucewa akayi kawai...



A boye zainab ta fara gyara yarinyar ta ba tare da ta fito fili ta nuna mata abinda take ba, ko mutunan gidan su fahimta, RANAR JUMMA'A DUBAN JAMA'A SUKE SHEDA DAURIN AUREN, JAWAHIR AND IMRAN, FARIN CIKI A WAJE IYAYE UKU BA'A MAGANA..

Haka kuma ranar ne abin bakin ciki ya faru a ciki gidan su.

kamar yanda Zainab tace ko hakan ne ya faru , domin tayi taro na ban mamaki, wanda ya tara mutane da dama, kama daga 'yan uwan ta, zuwa na su Addas da su Baffa's duk da taki fad'ar dalilin ta, Jawahir yar auta kuma yar gata gata kuma amarya, tayi kyau iya kyau sun shiga kaya kala_kala wanda duk Imran ne yayi mata su dan ta kana nais Zainab ta saka shi ya siyo su, haka shi ma ta hana shi fita ko ina ranar dan ko sallah a masallaci gidan su yayi, duk cikar matanen waje haka basa ya rabu da k'albin sa ba, duk inda zai ratsa hannun ta yana cikin nasa, dan yana tsoron abinda yake faru kar ya sake faruwa a yau....

Wata matace da ta shigo cikin gida tana wani nuna isa da iko, duk da fuskar ta kawai mutun zai kalla yasa babu rahma a tare da ita,,

wajen Zainab taje ta tsaya tamkar ta san ta, gani mutane basa kallon ta, yasa tayi sauro jefa k'waya aciki abin shan dake hannu ta, bata wani d'auke lokaci ba abinda ta sa ya nark'e cikin dabara ta sauya shi zuwa gaban Zainab ta d'auke nata, cikin rashin sa'a Zainab dake magana da wata 'yar uwar ta, ta dauka zata kai baki,, ,

jawahir ta k'araso waje tana tura baki gaba tace"mome!! na gaji fa." fasa sha tayi ta mayar ta ajiye tana murmushi tace"zo nan 'yar gatan Imran." ta fad'a tana mika mata hannu.

Aiko kamar jira ta fad'a jikin ta, tace"ya hanna ni zuwa ko ina mome, su Anty Khadija har sun gaji sun tafi, anty jameela ce kawai ta tsaya, hannu na har ya fara zafi." ta fad'a cikin shagwab'a.

Matar dake tsaye wani abu ya tsaya mata ma'koshi, Allah-Allah take, Zainab ta d'auka ta sha, cikin rashin sani za su mik'e tsaya Jawahir ta bugi cop din ako ya tamfatsi a 'kasa gaba d'aya, har sai da kayan su ya b'acci, jawahir ta tab'a fuska gani yanda rigar ta b'acci, Zainab ta kama ta tace"kar kiyi mini shirme a nan wuce muje ciki."
babu musu suka wuce matar zuwa part din su domin sauya kaya, akan idon Imran suka shiga, har zai biso wani mutun da bai san ko daga ina yake ba, ya shaga ban sa da surutu ya hanna shi tafiya..


har ta gama shirya wa zata fice Zainab ta kamo hannun ta, tana zaunar da ita tace"ina so nayi miki wata tambaya yarinyar ta, zaki iya sauya soyayyar da kike ma IMRAN ta koma kamar miji da mata?" ta fad'a idon ta na kan ta.

Jawahir tayi shiru sai can tace"aa mome karkiyi mini wannan fatan, buri na yaya na ya samu mata ta gari wace zata kula mini dashi, fiyya da zato na, ni ina mai so ne kawai a matsayin sa na yaya na, haka ina son farin cikin sa, da cikar burin sa amma bazan iya canza mai matsayi ba." ta fad'a tana murmushi.

Zainab sai taji wani iri tace"abinda nake so dake ko da nan gaba, tabbas akwai wani abu da zai bullo, ina so ki zama me biyayya ga iyayen ki Jawahir kin san har abada ba zamuyi abinda zai cutar dake, ki kasance me biyayya duk da lokaci har yanzu bai kure mana ba kinji."

"karki damu mome zanyi komai dan faran ta muku." "Yauwa yarinyar ta Allah yayi muku albarka, ya inga ta rayuwar ku ya sa ku cikin farin ciki madauwami, kije ki kira mini Yayan naki kinji.."

"Ameen yanzu kuwa." tana fad'ar haka tayi waje da sauri.


idan idanun sa bai mai karya ba kamar hawaye yaga maman! nashi tana goge wa.

cikin sanyi jiki ya karasa kusa da ita, hannu yasa ka ya tab'a, cikin sauri ta sake share hawayen ta, kana ta juyi tana kallan sa tace"yaro na har ka shigo?"

Jiki a sanyaye yace"eh mama na! wani abu akayi miki ne?" ya fad'a idon sa na kan ta..

"Ko d'aya kawai ina tunanin yau da gobe ne da kuma murnar wanna ranar, ka san me yasa na kira ka kuwa yaro na!, ina so na sake baka amanar 'kanwar ka ne, Imran nima ban san dalilin wanna kuka nawa ba , amma ina ji a jiki na kamar na kusa nayi muku nisa, wanda banji zamu sake had'u, dan Allah Imran ka kula da kanwar ka wanna ita ce nasiha ta, ka rik'e ta da hannu bibiyu, karka bari tayi kukan maraici Imran, bata da tamkar ka a duniya, ko da ace nan gaba gaskiya tayi halin ta, ka ri'ke mini ita da hannu bibiyu, wannan alfarma kawai nake nema a wajen ka in kayi mini haka ka gama mani komai, kayi hakuri imran ina son ku, ina kuma san farin cikin ku, ka kula da kawun ka da kyau, ka kuma kula hagun ka da damar ka, dan ba'a gane makiya a fusaka."

ta kama hannun sa tana manna mai wata takkada ta yanda babu wanda zai kula da abinda ta bashi, da ido tayi mai nuni aka ya ri'ke tana kuka tace"bana so naji komai daga gare ka tashi kaje ka tabbatar da kanwar na kusa da kai sanna ka duba hannun ka." tayi mai maganar a juye.

shi ma kuka yake, amma jin tace ya tabbatar da kanwar sa tana tare dashi, yasa shi saurin mi'kewa bai ko kula da gaban sa yayi waje da sauri dan sam bai gane inda kalaman maman shi suka nufa ba, gaba d'ayan sa ya rik'e ce..


Imran na fita mutane dake tsaye jikin bayan labulen d'akin sanyi da bak'a'kan kaya suka fito, hannu su rik'e da wu'kak'e d'ayan yace" wato ke mai taurin kai, bazayi abinda muka saka ki ba, shikenan kin cuci akan ki dan yanzu zaki she'ka barzahu." ya fad'a yana d'aura wuk'ar a ma'koshin ta......



*kar ku manta sai naga comment din ku zan ci gaba*

Mrs Abubakar ce🌹
[8/2, 11:02 AM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

Happy juma'atu mubark

1⃣2⃣➖1⃣3⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Har ya kusa fita a part din sai kuma ya tsaya, yana duba abinda ta bashi, kamar haka:

" _bana son abinda zai cutar da ku yaro na, tabbas na san kashe ni za suyi, ka kula mini da k'anwar ka da kyau, karka manta makashin ka na tare da kai, ka kula da dukiyar ka duk akan ta ake komai, na san ko mintin goma baza su bari na kara ba, ina son ku yara na!! Wanda ya aiko sunna shi...._ daga nan hannuun ta yayi rawa daga gani a tsorace tayi rubutun..

da masifafan gudu ya koma da baya, yana k'walla mata kira iya k'arfin sa..


_Abinda ya faru kuwa, shine bayan fitar Jawahir daga d'akin, Zainab na shirin fita ita ma sai taji kamar ana hura ma isaka ta bayan ta da sauri ta juyo, ga mamakin ta sai taga babu kowa, wayar ta d'auka tana shirin d'anna kira sai ta ga wucewar mutun da sauri, take tsoro ya kamata amma sai ta d'aure cikin tsoro tabi inda ya shiga tana fad'i "waye a nan??"_

_tana shiga suka maka mata wani abu a goshin ta, take ta tafi luuuu zata fad'i cikin sauri macen cikin su ta tare ta, a ka'sa suka zaunar da ita ko wanne face a rufe take, ta dafe kaita dake mata rad'ad'in zafi, a hankali ta bude idon ta gaba d'aya tana kallon su d'aya bayan d'aya, cikin muryar galabaita tace"su waye ku?"_

_'Karamin cikin su ya matso inda take yace"tambayar ba shi ne fa'ida ba, kiyi abinda zamu ce miki in ba haka kuma ki rasa ranki dana 'yarki." ya fad'a yana nuna mata pic Jawahir dake cikin mutane tana ta murmushi suna magana da wata mata._

_bakin ta na rawa tace"au dama kune? wai dan Allah me muka tsare muku a rayuwar duniya, kun hana 'yata sakatt kun adabi rayuwar mu, shi wai ku baku da iyali ne? Ya za kuji abinda kuke mana in akayi wa naku? Anyya kuna da imani kuwa? karfa ku manta duk abinda kuke Allah yana kallon ku, kuji tsoran Allah ku bar mu haka nan." ta fad'a cikin daka'kiyar zuciya._

_D'aya daga cikin su ya matso kusa yana molemata baki yace"ba wa'azin ki muke son ji ba, kiyi abinda mukace kawai shine fasan ranki, yanzu Imran zai shigo ki tabbatar kin gaya mai an d'aura mai aure da 'yar, sannaki saka shi ya sake ta, sannan ya saka hannu akan wannan takaddun." yayi maganar yana watsi mata su a fuska._

_Tsantar tsoro ne ya kama ta cikin kid'ima tace"ya akayi kuka sani? wannan ta kaddun na meye?" ta fad'a tana duba su.._

_"kin d'auka yanda muka k'wallafa rai akan wannan dukiyar zamu zuba ido kawai muna kallon ku ne ke da mugun mijiki, to kima bar wannan tunanin dan mufi k'arfin tunanin ku daga ke har mijin naki, ina so na sani waya bada shawar auren? na rantsi miki da Allah wanda ya kawo wannan shawarar ko waye sai naga bayan sa a cikin wannan gidan." yayi magana yana dukan ciyyar sa..._


_take wani abu ya tsaya ma Zainab a mak'oshi, zuciyar ta tsik'e cikin taurin rai tace"to nu ma me kuke jira dani? kuyi maza ku kashe ni tun kan dare yayi muku, amma na rantsi da girman Allah babu wanda ya isa ya saka ni nayi abunda banyi niyya ba ko uban waye, aure kuma yanzu za su fara zaman shi naga uban da ya isa ya kashe shi, maza muyi mini abinda kukayi niyya, dan na yarda da k'addara me kyau ko akasin haka, Allah ne ya busa mini rai da rayuwa, a cikin ku nan babu mahalukin da ya isa yace zai rabani da rayuwa ta, mudin lokacin bai

Please Login or Register in order to submit comment