Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hannu sa bai sauke ta ba haka ita ma bata cire hannun ta dake kaffadar sa ba, IMRAN ya saki 'yar k'ara yana ya mutsa face. Jawahir ta d'ago da sauri tana kallon shi dan so gani abinda ya same shi, sunna had'a ido ya kashe mata ido d'aya kana yace" hannu na zai sage.." yayi maganar yana mata nuni da ido.

Jawahir ta zaro ido waje gani halin da suke ciki aiko tayi saurin tashi tsaye, tana ka re face din ta da hannun ta dan kunyar sa take ji..

Gani haka IMRAN ya sake saki k'ara a karo na biyo, Jawahir ta d'ago da sauri tana kallon shi sai ta ga ya kama kafar sa d'aya dake lank'washe yana yamutsa face alamar tana mai zafi, cikin sauri ta isa inda yake gaba d'aya ta rud'e sai wani shafa shi take yana juya shi game da cewa" sannu My!! Ina ne yake ciwo.." ta fad'a arud'e..

Shiko kallon ta kawai yake bai ce komai ba, a hankali ya matso kusa da ita ba tare da ta ankara ba, sai da yazo saitin face din ta sanna tajiyo saukar numfashin sa a wuyan ta aiko tayi suman tsogone ta k'asa ko da motsi sai raba ido take, cikin wata wahalaliyar murya Imran yace" K'albi na!! har yanzu baki fara k'ok'ari sauya mini matsayi ba...??". ya fad'a cikin wani sabon yanayi dashi kan shi bai san yanayi ba..

Jawahir jiki ya fara rawa ta k'asa cewa komai sai auki matsa hannu..


Wallahi na so nayi muku me yawa sai kuma gashi an kawo mana nepa bye..

Comment

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce
[9/14, 7:38 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*



3⃣0⃣➖3⃣1⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Marya na rawa tace" fitsari nake ji My!!.." tana fad'ar haka ta mik'e da sauri ta bar wajen...

IMRAN ya bita da wani kallo...


" Sabida irin haka na ta nad'i wannan kayan, ki adana shi zuwa dare zaki fara aiki dashi, haka kuma zuwa dare zanyi miki bayani akan su.."

Cewar Adda samera da ta mik'awa Jameela wasu bak'ak'en kaya har da safa ta kafa da ta hannu duk bak'ak'e..

Jameela tashiga juya kayan face din ta turb'ine tace" me kuma zanyi da wannan kayan da ko kyan gani basu dashi..?"

" Duk abinda kika ga na d'auko na baki ba abin da zai cutar dake ko kya ma bane ki amsheshi hannu bibiyu, zuwa dare zaki san amfani shi.." tana kawowa nan a zance ta ta bar d'akin gaba d'aya...

Jameela ta saki tsaki a fili..



Jawahir d'aki ta shige tana sauke a jiyar zuciya ita da tunanin iri-iri, " wai dama haka My yake? dama na zauna naga me zai mini? to ko bai da lafiya naji sai nishi yake mini a wuya? kai anya kuwa ko kuma ita ce soyayyar da yace zai koya mini ?? tab'a lallai ko in ita ce zatayi wuyar d'auka dan bazan jure wanna nishin ba Allah har fitsari ne ya matso ni". sai kuma ta saki dariya da ta tuno yanda tayi da tsili-tsili a gaba shi, dariya take har da rik'a ciki...


Dariyar ta da yaji ne ya sa shi laik'awa d'aki yaga ko ba ita kad'ai bace kwance ya same ta ta juyawa kofa baya sai mutso-mutso take da alama dariya ce ta ci karfin ta..

Yace" K'albi lafiya?". ya fad'a da nufin k'arasawa inda take. aiko ta dira tsalle gefe tana k'ok'ari sanya kuka tace" Allah ba kai nake wa ba, ni bana so wanna nishin da kake kamar marar lafiya..?". ta fad'a tana tura baki gaba..

IMRAN ya sake takowa zuwa gaban ta yace" wanne nishi kuma..?" dan shi bai san yayi ba..

Rau-rau sai ga hawaye a kunci Jawahir tamkar wanda yayi mata babban aiki, tana tura baki tace" ni dai kaje zan shiga bayi.."

IMRAN ya k'asa gane mata amma ba yanda ya iya dole ya fice a d'akin yana tunanin abinda yasa ta dariya haka..

Yana fita ta datsi kofar tana sauke numfashi sai kuma ta fara k'wak'wayar sa..


Musalin 1 da rabi na dare , Jawahir na kwance a bedroom din ta taji kamar ana ja mata sawu, a hankali ba tare da ta bude idon ta ba, ta janye kafar ta tana harde su waje d'aya, can kamar minting 2 taji an sake ja mata bargo ta saka hannu ta bibiyu da bismilla ta jawo shi har kan ta ta shige ciki,, abin mamaki yanzu kuma gaba d'aya aka d'auke mata shi, aiko ta tashi a mutuk'ar tsorace bakin ta d'auke da addu'a, can gefe taga an yada mata dashi akasa wutar d'akin ta kunna sanna ta sauko k'asa ta d'auki bargon ta, ta juya ta hau gado har yanzu addu'a take, da gudu aka fice a d'aki har kofa na motsi,. Jawahir ta firgice aiko ta saki wata ingataciyar k'ara wace duk gidan babu wanda bai jita ba dan iya tsorata ta tsorata, gaba d'aya ta firgice..

IMRAN da tun motsin ta na farko ya farka shi yayi saurin shigowa yana tambayar ta lafiya, aiko tana gani shi tayi bayan sa da gudu tana addu'a, tasi rawar jiki take a haka su baffa suka same su, baffa yace" lafiya kika mawa mutane k'ara a tsohon daren nan?"

Murya na rawa tace" aljanace!!". ta fad'a tsorace dan gani take kamar zata dawo..

Kallan-kallo aka shiga, kamar had'in baki suka ce" aljana? a Ina??"

Jikin ta na rawa ta shiga basu labari abinda ya faru, ko wanne jikin sa yayi sanyi Abdullahi yace" to kai Ina ka tafi lokaci dama ka barta ita d'aya a d'aki, ka dawo nan ne ku kwanta..."


IMRAN ya sunna kai k'asa domin bai da tacewa. Jawahir ko har yanzu tana mak'alai a bayan sa, su baffa gani haka yasa suka fice a d'aki suna dariya k'asa-k'asa, Adam yace" kaga yara da shakiyanci." Abdullahi yace" to koma dai menene ai matar sa ce in ka bibiya ma shi ya tsora ta dan su kwana d'aki d'aya, yanzu ai nayi musu me gaba d'aya..."
gaba d'aya su dariya suka saka ko wanne yayi part din shi cike da nishadi..

Jameela ta sai ta gaba uwar ta ta jefa mata kayan face babu an'nurin tace" wai uban me kika sani nayi ne? kin ce in nayi haka zata dawo part din nan gashi nayi hakan kuma an had'e musu d'aki, yanzu me kike tunanin zai faru a haka ma ya suke cika bare kuma sun keb'e d'aki d'aya ba ma awa zasuyi ba ahawani zasuyi wallahi in wani abu ya shiga tsakanin su basu kad'ai ba har ke sai ta shafa..". ta fad'a cikin zafi da konar zuciya dan ko kad'ai batayi tunanin haka zata faru ba, tayi d'akin ta a zuciye..

Adda samera bakin ciki da takaici ya hannata magana ko d'aukar mataki aka Jameela kayan da ta watso mata shi ta d'auke ta tura kasan bed...

Abdullahi ya shigo d'aki yana murmushi ya kalle ta yace" a'a yanzu fa na barki kina barcci me kuma ya tasheki na ganki kamar ma ranki a bace.?"

Da yake wutar d'akin a kunne take.

Cikin inda-inda tace"eh naji tashi ka ne shine na mik'e naga ko lafiya to kuma sai ga ka dawo lafiya. ?"

Murmshi mugunta yayi kana yace" kalau yara ne wallahi abu ma abin dariya, soyayya fa suke sha shine yarinyar tayi ihu mu kuma bamu sani ba muka affka d'akin da sauri muka yo baya, wai dan rashi kunya irin ta dan yau shine tace wai aljani ta gani". ya Kai k'arshen maganar da zuba mata ido..

Adda ji tayi cikin ta ya d'aure lokaci gudu, ga wani abu da yake tsarga mata wanda ta rasa menene shi, gashi dama Jameela ba bayani ta tsayayi mata ba, ko magana kasawa tayi sai ta haye gado tayi lamo kamar me barci...

Abdullahi yaki wani boyayyen murmshi...


" Sake ni naje na kwanta.." ya fad'a yana bambare hannu ta d'aga rok'on da tayi mai, babu musu ta saushi tana ta raze ido, sai da ta kwanta yayi mata addu'a sanna ya sauka k'asa shima ya d'auki sallaya ya shifud'a, bayi yaje yayi alwala kana ya zo ya tada sallah duk Jawahir na kallon shi dan to yarda ta rufe idon ....

Ya jima yana kai kukan sa ga mahalicin mu, kana yayi sallama yana addu'oi, bayani ya idar yazo gaba ta yana ta kallon ta anan shi ma barci yayi awan gaba dashi Amma bai kwanta ba yana daga zaune...

Fita zanyi gaskiya.


Mrs Abubakar ce
[9/15, 1:14 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


```Asalam alaikum jama'a ina cikiyar sahiba ta Safeeya aliyu waki'l ta b'acce b'at bana ganin ta, duk wanda ya nemo mini ita ni kad'ai na san kyautar da zan mai```


_ban da baki godiya a gare ki yar uwa rabin jiki mimspueen marubuciyar rashin dace na gode sosai da k'aunar ki a gare ni Allah ya bar zumunci ya k'ara kare mu baki d'aya.._

*Rahma Abdullahi ina tayaki murmar kamala novel din ki, Allah bada ladan fad'a kar wa, Allah ya baki ikon kamala wanda kike typing yanzu..*


~Maryam Abdul, Maryam💕 Ina taya ku murnar fara sabon novel din ku Allah ya taimaka Mana ameen, rukky Mama ke ban manta dake ba, Mama Queen ke ma ina sanne dake, miss haajara kema ban manta dake ina muku fatan alhairi.~

3⃣2⃣➖3⃣3⃣


BISMILLAHI RRAHAMANIR RAHIM


Kiran sallar farko ya ta dashi, ji yayi wuyan sa a k'age bakin sa cike da addu'a ya farka bai kalle ko ina ba sai saitin da Jawahir ke kwance, ido ya zuba mata na dan wani lokaci kana ya sauke idon sa aka ta ya mik'e yayi bayi alwala yayi yazo ya ta da sallah kafin a shiga masallaci...


Jawahir ta mik'e ta na sallati game dayin mi'ka hasken d'akin ta kunna gaba d'aya kana ta sauko a bed din, Imran ta gani yana ta sallah tsaye tayi tana kallon shi tunanin ta d'aya ba dai tun juya da ya tada sallah har yanzu bai idar ba, mamaki ya kamata to dama haka yake kullum ko sabida ita yau yaki barcii, wani tausayin sa taji ya shige ta lokaci d'aya, jikin sanyaye ta shige bayi tayo alwala ita ma lokacin da ta fito bata tarar dashi ba, dan an shiga sallah a masallaci...


Ko da ya dawo bai kuma shiga d'akin ta ba, yaci burki a d'aki sa, tsakani ita dashi babu wanda ya sake fitowa har lokaci dining din gida kuwa babu wanda bai fito ba, amma ban da IMRAN da Jawahir hankali matan gida kuma yana kan su, gani ana shirin fara ci ga lokacin na gudu, Adda mairo ta dube Jameela tace" Jameela je ki taso yarinyar nan da Yayan ki, kar lokaci ya kure.." ta fad'a tana duban angogon bango falon..

Adda samera tace" kamar kin san abinda ke rai na kuwa, basu tab'a irin wanna jimawar basu fito ba sai yau.." ta fad'a tana kallon hanyar part din..

Abdullahi ya kalle su yana murmushi yace" Jameela zoki zaune ki ci abinci ki, yau yara na suna cikin nishadi, basu son damuwa ko takura in ma zuwan ne ke mairo in IMRAN ya fita zuwa an jima kije ki gyara 'yar ki domin Ina da tabbacin ta zama cikakiyar mace.."

Ya fad'a cike da shauk'i dan ya san koo banza yau zai hana wasu su'kuni..

Adda mairo tayi wani gwalau da ido dan tsanani mamakin maganar sa, da ko kunyar yaran sa baiji ba bangare d'aya kuma tsoro ya tsarga mata in ko haka ne tayi sake da yawa da har aka kai wanna matsayi ba tare da ta tab'oka komai, innalillahi yanzu ya zanyi..?". shi ne abinda ya fito daga bakin ta kuma a fili dan babu wanda bai ji ba..

Da mamaki ake kallon ta Adda Samira uwar son jin k'wak'wafi tace" ya zanyi kamar ya ya? me akayi miki..?" ta fad'a haka duk da ita ma tana ciki rud'ani..

" Yarinya k'arama yanzu aka barta suka k'eb'e da yaron nan a haka kamar me hankali shine, amma shine yaje yayi mata haka, aiko zai fito ya same ni wallahi Jawahir me ta sani, dudu yaushe aka fad'a mai cewa matar sa ce yaro kamar jura yake shine har ya haike mata, salon ya ma yarinya ta yoyin fitsari Allah zai game dani, kema Yaya har da laifiki me yasa kika bari ta koma part din su.." ta fad'a cikin fad'a sosai kamar gaske Nan ko abinda ke nuk'urk'usar ta daban ne..

Abdullahi yayi murmushi irin naso na manya yace" Khadija, Jameela kuje ciki zuwa an jima kwa dawo. kana ya mayar da duban sa ga Adda mairo yace" yanzu ke duk soyayyar nan da yaran nan suke nunawa junna su baki tab'a kula ba, sai yau dan kawai ya sun cika burin su shine zaki hau fad'a, ni gaskiya banga laifi d'ana ba hakan da yayi yayi mini dai-dai, ko ya kace Adamu..?" ya fad'a yana kallon k'anni sa..

Mairo tayi shiru bata sake gigin cewa komai ba dan sosai take jin kunyar Yayan mijin nata, gashi yau kuma yayi mata b'aran b'arama..

Adda Samira tace" a'a gaskiya mu kam ba haka muka so ba, in san sa mu ne ai ma mata gyara kafin su tare, ba wai kawai daga fad'a musu daga Yan watani ba, muje zance marar dadi..." ta fad'a tana tura baki gaba...

" To koma dai me zaku ce ni banga laifin kowa ba a cikin su, fatan ma Allah yasa mu samu jika..". yana kawowa nan ya mik'e ya bar su a wajen...

Hakan ma Adam ya mara baya...


Adda Samira kan ta na k'asa tana tunanin ta hanyar da zata bollo musu..

Adda mairo ta ciza yatsa had'i da kad'a kai sannan tayi k'wafa ta tashi ta bar wajen, a ranar abinci da basu ci ba kenan...

Jameela tana zuwa d'aki ta zub'e akan kujera tana rusgar kuka, ba dan komai sai tunawa da tayi duk ita ce ta jawo koma menene, da bata je mata a matsayin aljana ba da ba'a had'e musu d'aki ba, garin neman gira gashi nan an rasa ido...

Khadija tayi lamo akan bed tana ta juya zance baffa na ta, to me yake nufi da jawahir ta zama cikakiyar mace to me yake nufi?? shine tunanin ta gaba d'aya ta k'asa fahimta, domin ita ba kamar Jameela bace bata da k'awaye masu budewar ido, da waye wa....


Jawahir ce ta fara tashi har zata fito falo, sai kuma ta fasa da tuna irin yanda ya kula da ita a daren jiya, kawai sai ta koma d'akin say kwance ta same shi sai barcin sa yake sharb'a, kan shi taje ta tsaya tana k'are mai kallo, tunda take dashi yau ne kawai ta tab'a kallon shi taji wani abu daban, hannu ta saka saitin heart din ta taji tana bugawa da sauri da sauri, ta lunshe idon ta tana sauke wata kasalaliya ajiyar zuciya, tana murmushi tana komai ta wuce kicin din part din su raban ta dashi tun mutuwar abban ta, da yake ana gyara wa komai ta samu fas dashi, girki ta d'aura ta samu abu me sauki kamar indome da egg, cikin d'an lokaci k'ank'ani ta kamala girkin ta, falo ta dawo nan ma ta sake gyara shi duk da babu wani datti, sanna ta shiga wanka nan ma bata b'ata lokaci ba ta fito cikin shigar ta data saba wato saka dogayan riguna, layi mutu'kar yin kyau ainu.

Falo ta dawo amma tayi jigum tana ta jiran fitowar sa amma shiru d'akin ta laik'a yana nan yanda ta barshi, tunanin ta fara ta yanda zata tashe shi, duk yanda ta k'iyasta gani tayi abun ba yuyuwa bane ta saki tsaki a fili, d'aki ta shiga ta tsaya akan say kallon shi take da tunanin ta yanda zata tashe shi..

Tun shigowar Jawahir na farko IMRAN ya tashi haka har girki da ta d'aura duk yana kallon ta, domin har kicin din ya biyo ta amma bata ganshi ba, da zarar zata juyo shi kuma sai ya boye, a haka har ta shiga wanka da kan shi ya d'auko abinda yaga bata d'auko ba ya sake gyara wajen, Jin zata fito need yasa shi koma wa d'aki ya shamamak'e yana jira yaga ta yanda zata tashe shi...


Jawahir ta kwanta kusa dashi tana ta kallon shi, can ta tashi zuwa tayi ta d'auko ruwa me sanyu bala'i ta tun karo bed din...

IMRAN tunda ya hango ta ya fara tunanin mafita, domin in ta watsa mai ruwan nan tsaf mura zata kama shi...


Jawahir tana murmushi tana komai tazo gaban shi ta tsaye...

Bari na tsaye a nan naga yanda zata kaya shin IMRAN zan tashi ne ko? zai tsaye ta watsa mai ko zai gudu,.

Allah sarki su sunnan suna shirman su su kuma manya suna can suna kishi da bakin ciki ayye har yanzu fa basu angonce ba Adda Samira kwantar da hankaliki...

Comments

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce
[9/17, 6:03 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*

_comments din ku nayi mini dadi irin sosai din nan musamma GROUP DIN BA SO BANE CUTA CE 1 gaskiya yanzu kuna k'ok'ari sosai Allah ya bar k'auna da zumunci na san masuyi na san marasayi kuma zamu gauraya nee.._

3⃣4⃣➖3⃣5⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ta wajen kan shi ta ajiye robar ruwan kana ta dawo kusa dashi ta zauna, shiru tayi tana k'are mai kallo murmushi tayi ta sunkuya dai-dai saitin face din sa kamar za tayi kissing din sa, sai kuma ta zame matashin da yake kai tana dariya, tace" na gano ka, dama ka jima da tashi shine kayi mini lik'imo in har barci gaske ne kake bai ci a ce har yanzu kana nan yanda kake ba to wallahi sai ka tashi..." ta fad'a tana haye wa kan shi, hannun ta duk biyu ta zuba acikin sa tana mai cak'ul'kuli had'i da sakin dariya...

IMRAN ya saki dariya shima ya shiga tare ta game da kama hannun ta duk biyun, shi ma ya shiga ramawa, dariya suke suna shewa alamar duniya tayi musu dadi.

Haka suka cigaba da yi, tunda suka fara har ya dawo suna yar d'anne d'anne, ta murgi shi ta haye kan shi, shi ma ya murgi na ta ya haye kan ta, cak'ul'kuli kuma ba su fasa yi ba, IMRAN ya rungume ta tsam a jikin sa a hankali cikin wata murya yace" INA SON KI JAWAHIR SO NA HAK'IK'A INA MUTU'KAR K'AUNAR KI MATA TA..."


JAWAHIR ta sak'e ta k'asa cewa komai, sai tayi luf a kirjin sa tana jin wani iri a zuciyar ta...

D'ago ta yayi yana had'e fuskar su waje d'aya, hancin su na gogar na juna yana kallon yanda ta runtsi idon ta cikin kasataliyar murya yace" K'albi na, ki kalle cikin idon na ki gaya mini abinda kike ji, please Jawahir ki gaya mini gaskiya ko zuciya ta zata samu nutsuwa, shin me kike ji a kan a yanzu...?"
yayi maganar yana sake d'ago kan ta wanda ta ke k'ok'ari kawar wa gefe...

Jawahir ta shigar mutsu-mutsu tana son k'wacewa, cikin murya me raurauwa tace" My!! yunwa nake ji..."

"Ok.." ya fad'a duk da ran shi bai mai dadi ba..

Sakin ta yayi ta tashi, inda ta jera abinci nan ta koma ta zauna tana jiran sa, shi kuma shiga yayi k'imtsa kana ya fito cikin shirin fita, ta gaba ta yazo zai wuce cikin wata murya tace" My!! ga abinci fa a nan.." ta fad'a tana mi'kewa tsaye..

" Eh na gani sauri nake zanje inda za'a gaya mini abinda nake bu'katar ji, kin san akwai Nabeela!!.". ya fad'a yana kashe mata ido d'aya...

Jawahir ta kar kata kan ta gefe, tana kallon shi sannan ta tab'arb'are fuska tana shirin fara kuka tace" amma fa domin ka nayi duk wanna hid'imar ka bari in ma zuwan ne kaci abinci tukuna..." tana maganar ne hawaye na zubo mata...


IMRAN ya kalle a gogon bango yana k'ank'ance ido yace" gaskiya zan makara kuma kin san Nabeela yanzu zata iyayin fushi, so kici kawai in dai nine na gode, in kuma kina so naci to sai kin gaya mini abinda na tambaye ki...""" ya fad'a yana kawu da kai gefe...

Jawahir tayi shiru kamar baza ta sake cewa komai ba zuwa can kuma tace" tom naji kaci abinci.."

"" Kinyi alk'awari...""" ya fad'a yana mik'a mata hannu..

Ita ma hannu ta mik'a mai suka sark'e yatsun hannu su waje d'aya kana suka saki ko wanne ya nemin wajen zama, cikin nutsuwa da kwanciya hankali suka fara cin abinci IMRAN yana ta kod'ata da zuzuta dadin abinci, Jawahir dadi kamar ya kashe ta sai murmushi take tana dariya, a haka har suka kamala...

" Tom ina jinki.." ya fad'a yana kama hannun ta had'i da matse su a cikin nashi hannu...

Jawahir ta mik'e cikin tsantsar shagwab'a ta Haye cinyar sa tana wani langwab'ar da kai tace" My ba ka yarda da k'aunar da nake maka bane? a tunanin ko ban fito fili na gaya maka ina k'aunar ka ba, baza kayi sha'ku ko tunanin ba sabida so ko ban fad'a kana ganin shi a aikace My!! ina mutuwar son ka da k'aunar ka domin kai ne jinin jiki na, bana ji zanji dadi rayuwata idan babu kai a cikin ta My!!! ILOVE YOU SO MUCH MY heart, ban san ya zanyi da soyayyar ka ba, dan Allah kar ka guje ni ko da nan gaba domin kai ne gata na abin alfahari abin tun'kaho na bani da wanda zan gani naji dadi fiyya da kai my heart..."
ta fad'a cikin matsananci kuka domin jin son shi take har cikin mak'wararar zuciyar ta da ran ta game da gangar jikin ta...


Comments

And

Shared


Mrs Abubakar ce
[9/18, 11:29 AM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )






Please Login or Register in order to submit comment