Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa na d'akin lumshe ido tayi, game da dafe gefen kan da d'aya hannun tana ya mutsa fuska..

IMRAN ya kura mata ido sosai, can yace" sannu k'albi , kai ne yake miki ciwo ?" yayi maganar yana dafa mata kai..

Hannu shi ta kama a hankali idanun ta suka bude tar a kan shi, cikin murya marar sa lafiya tace" My! dan Allah ka d'auke ni daga gidan nan na gaji wallahi tunda na taso nake gani abubuwa da dama, har zuwa girma na, ka taimake ni ka rabani da gidan nan ko zan samu salamar rayuwa.." ta fad'i maganar hawaye na bin kuncin ta..

Babu wanda bai rud'e ba da jin wannan furicin nata, amma ban da IMRAN wanda shima tunanin sa kenan..

Cikin wata murya yace" kwantar da hankalin ki K'albi dole ma mu bar shi, ko dan samun farin cikin ki.." ya fad'a yana shafa mata gefen fuska..


A cikin su baffa ko Adda babu wanda yayi magana sai ido kawai da suke zarewa..


Suna cikin haka doctor ya shigo ya sake duba ta da kyau, gani babu sauran wata matsala yasa ya basu sallama, haka suka dawo gida ko wanne su jiki a sanyaye..

Dare nayi yace mata bari yaje ya dawo, akwai abinda zai duba tunda juyen duniya yayi da ita akan ta fad'a mai wanda yayi mata haka tak'i, da ya matsa mata sai ta sanya mai kuka, dole ya hak'ura zaje ya dawo ya gani da idan sa..

Yana fita ta tashi duk da bata jin k'warin jikin ta sosai haka ta wuce d'akin sa, laptop din sa ta hanga akan table cikin d'an sauri ta isa wajen bata wani sha wuyar cire password din ba, dube-dube ta fara aiko taci sa'a abinda taje nema cikin gagawa ta goge tass sanna ta mayar da ita inda ta ganta ta fice a d'aki tana suke a jiyar zuwa, maganar Jameela ta k'arshe na dawo mata, ita kuma baza ta so a cutar mata da IMRAN din ta ba...


Yana shigowa d'akin sa ya wuce shi ma laptop din ya d'auka, yazo nan kusa da ita ya zauna yana duba wa, mamaki ne ya kam shi gani tunda ta fita bata sake shigo d'akin ba, tunanin sa ne ya tsaya kan to ya akayi shi ya same ta a d'aki? duk yanda akayi Jawahir ta goge, aiko ran shi ya b'accci ya d'ago yana kallon ta yace" JAWAHIR me yasa kika d'aukar mini laptop har ki kayi mini goge-goge ?"

Ta kalle shi cikin shagwab'a tace" no ni bam shiga d'akin ka ba, tunda muka dawo Ina nan a kwance.." ta fad'a tana ya mutsa fusaka..

B'accci rai ya hanna shi magana domin ya sa kaf gidan babu wanda ya san da CC camera sai ita, haka kuma babu wanda ya san password din shi sai ita, tsaki yayi ya tashi ya bar mata wajen...

Jawahir ta lumshe ido a fili tace" mudin zaka kasance cikin jin dadi ni zan iya komai dan gani na kub'utar da kai My! bazan iya jure ganin ka cikin mugun yanayi ba.." ta fad'a tana share k'wallar ta da tsananni bakin ciki, ba dan komai ba sai dan gani 'yar uwar ta ke neman rayuwar ta, yanzu dama duk k'aunar da jameela take nuna mata dama *BASO BANE CUTA CE* lallai duniya cike take da abubunwa alajab'i, inko haka ne ba makawa akwai mai d'aure mata gindin, kuma yanzu ita ma zata tsanan ta bincike, wasu hawaye suka zubo mata...


IMRAN dake d'aki yana kallon ta tausayin ta ya kama shi, haka ya d'aure zuciyar sa shi ma ya fito inda take, da kan shi ya ta rarashin ta har tayi shiru..

Adda mairo ce ta shigo part din su bakin ta d'auke da sallama, duk da sun jin shigowar ta hakan bai sa IMRAN ya janye JAWAHIR daga cikin sa ba, sai ma k'ara k'ank'ame ta da yayi haka ita ma tayi lak'ur a jikin sa, kusa da su ta zauna tana kallon su da fusakar tausayin tace" Jawahir ya jikin naki ?" ta fad'a tana kallon su, zuciyar ta tanayi mata wani iri..

IMRAN yace" da sauki sosai tunda yanzu ba kamar d'azu bane.."

" Ok yayi kyau Allah ya sauwak'e, Jawahir ki d'aure ki gaya mana wanda yayi miki abun nan, domin hankali mu ya tashi sosai da Ina cikin gidan nan da duk haka bata faru ba, amma abun mamakin a nan shine Addanki nan domin lokacin da zan fita na bar su ita da jameela a falo, to ban sani ba ko bayan fita na ita ko ta fita tunda tace bata san anyi ba, abun dai da mamaki gaskiya yarinya gaba d'aya tunda kika taso abubuwa sai faruwa suke akan ki ke d'aya, gaskiya lamarin akwai rud'ani a cikin sa, JAWAHIR ko da tsoratar dake akayi kika k'i fad'a ?" ta jefa mata tambayar cikin bazata..

Jawahir tayi saurin mi'kewa tana cewa" a'a-a'a babu wata maganar tsoratar wa kawai fad'ar ne bai da amfani, domin baka sani masoyin ka na gaskiya har sai wani mumun abu ya faru da kai a nan ne zai nuna kan shi, wane masoyin kuma rik'id'ewa yake ya koma makkiyi ko kuma ya nuna maka duk duniya babu ya kai Ashe duk ba haka bane ban tab'a tunani *ba so bane CUTA ce* sai yau na tabbar da hakan da ido na, amma na say Rai na ko zaa kashe ni bazan tab'a fad'ar ko waye ba mudin da rabon a san shi, to asirin sa zai tuno kowa ya ganshi, ni na bar mutun da Allah in babu a nan ai akwai can, haka kuma abinda kayi mai 'yar wani to kai mai za'ayi was taka insha Allah, wanna ba fad'a ta bace a rubuce yake, duk Wanda ya zalince ni a matsayi na na marainiya, Allah ya saka mini ko waye kuwa na barshi da malincin mu, Allah ne zai isar mini da isar say insha Allah..." ta fad'a cikin kuka..

Adda mairo har wata zufa take ji tana neman d'igo mata, amma da yake makira ce ita ma, sai ta k'washe-sheb'e fuska, tace" haka ne yarinya ta Allah ba azalimin bawan sa bane dama, Allah ya taimake mu baki d'aya ya tsare gaba, ni zan koma sai da safen ku.." ta fad'a tana wuce wa..


IMRAN ya juyo da ita saitin sa yana kallon ta yace" ina alk'awarin da kika mini na duk abinda ya faru da d'aya matsawar d'aya baya waje to dole d'aya ya sani, yanzu dama har akwai ranar da irin wanna abun zan faru dake ki gagara gaya mini, anyya JAWAHIR kina jina kamar yanda nake jinki kuwa ? idan har kina jina kamar haka bazaki ji shakar gaya mini damuwar ki ba ko Wanda yake k'ok'ari turaki kiyyama lokacin baiyi ba, bazan ta kura ki ba akan ki fad'a mun ba, duk lokacin da kika shirya sanar mini ni a shirye nake da na saurare ki.." ya fad'a yana shafa gashin kan ta..

JAWAHIR ta sake k'ank'ame shi cikin kuka tace" kayi hak'ura My!! bazan iya ka kallon cikin mugun yanayi ko hali ba, bazan bari a tagaiyar rayuwar ka ba, zan iya fanssar ka haka kuma zan iya jure komai akan kai, dan Allah ka sa ran ka babu abinda ya faru dani na muni ko nak'i, ko da nan gaba kuwa kak'iji kak'i gani My heart dan Allah kuma bana so ka tsawai ta bincike.." ta fad'a tana had'e hannuwan ta waje guda alamar rok'o...


" Bazai yuyuba JAWAHIR, bazan iya halin ko in kula da maraiyar ta ba, kar ki manta ke amana ce gare ni, bazan iya wulak'ata 'yar amana ta ba, bincike ne kuma sai nayi.." ya fad'a yana k'auda kan shi gefe..

Jawahir ta bude baki za tayi magana, sai ga Adda samira da jameela sun shigo d'akin, ko wace idon ta akan Jawahir, gani su da tayi ba k'aramin tsora ta tayi ba har sai da ta bude baki zata gubbud'a ihu Jameela tayi nata want azalimin kallo aiko ta had'iye abinda tayi niyya..


Adda ta k'araso inda take cike da tausayin ta kamo hannu ta tana wani rausaya fusaka tace" sannu yarinya ta, ya jikin naki ? wai gari yaya haka ta faru ? sam ni ban ji komai ba ko dan Ina barci, dan tunda Jameela ta wuce dana koma cikin ban sake fitowa ba, haka kuma ban sake jin motsi kowa ba, sai Kira baffanku yayi wai kina asibiti, nayi mamaki sosai.." ta fad'a tana wani sake shafa ta..

Cikin dabara JAWAHIR ta zare jikin ya daga na Adda Samira ta koma jikin IMRAN tayi lak'ur, haka kuma tak'i magana,
sai IMRAN ne ya biye na Adda suna ta tataunawa akan matsalar..

Jameela ta matso tace" sannu sister ya naki? Allah ya k'ara sauki, wai ina brother din ya tafi ya barki haka har haka ta faru dake ? da ka fad'a mini k'in yarda nayi sabida na san tare kuke yawo kamar wasu jab'a.." ta fad'a tana kai hannu ta da zummar tab'a JAWAHIR din..

Aiko JAWAHIR tayi....

da haka kuke comments wallahi bazan ji k'iwar yi muku typing ba aradu naji dadin yanda kuka nuna sosai, in kun d'aure a haka nima zan d'aure..πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ€Έβ€β™€πŸ˜‘


Comments and shared


Mrs Abubakarusaeenah@gmail.com
[9/23, 4:09 PM] Mrs Abubakar 🌹: *πŸ’«DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*πŸ’”πŸŒΉBA SO BANE πŸŒΉπŸ’”*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*

_Rukky mama Ina taya ki murnar kamala novel dinki ALJANA CE SULA, Allah yasa kin gama a sa'a, ya bada ladan fad'ar wa, muna godeya sosai.._


4⃣2βƒ£βž–4⃣3⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


JAWAHIR ta ma mugun ruk'o ta matsi hannu ta damk'e shi, cikin k'warewa da mugun ta, haka kuma fuskar ta d'auke da murmushin k'arfin hali, Jameela zafi yayi zafi, domin ji take kamar ta saki fitsari a wajen tayi tsile-tsile da idanu wanda suka ciciko da k'walla, amma babu damar fitar dasu...

JAWAHIR tace" Anty na, ai kin san ko wanne bawa bai isa ya tsallake k'addar sa ba, kuma duk da haka ta wani tafi ta wani ni dai Allahmdulillahi da abin ya tsaya mini a iya haka, domin tun kafin na mallaki hankalin kai na, na samu miji a b'agas kin ga na zama yar gata, to babu zance wani da yayi yawa dani, ya tsaya ma mutane a zuciyar su abinda da ba'a fara komai ba yanzu muka saka hannu a fata ko My!! ?" ta fad'a tana kallo IMRAN da hankalin sa ya naga rok'on da tayiwa Jameela, a su'kwane yace" k'ware da gaske soyayya fita guri-guri, yanzu zamu fara domin bazan iya bari ki a inda za'ana cutar mini dake ba dan bazan jure gani haka n ba.." ya fad'a yana shafa mata gashin..

Jameela ta laumshe ido, azaba da rad'ad'i na shigar ta tace" yayi kyau masoyan asali ni bari na wuce.." ta fad'a tana mata nuni da ta sake ta da ido, ita ma alama tayi Mata da baza'a saki ba, a fili kima tace" Anty na daga zuwa har zaki wuce, ki zauna ma muyi hira.." ta fad'a tana aika mata da wani mugun kallo na zaki san sauran..

Jameela ta fara zufa domin Jawahir farce (kumba) ta kafamata har sai da taji sun nutse a hannu ta, dan ba k'aramar damk'a tayi mata ba...

Jameela ta ciza lips tace" a'a na gode da wannan karamawar taki k'anwata.. fad'a tana k'ank'ace idanun ta alamar ban ha'kuri...

JAWAHIR ta saki dariya kana ta sakar mata hannu tace" ok ba damuwa zaki iya tafiya.."

Jameela ta saki a jiyar zuciya game da kama hannu ta da d'aya hannu me lafiya, bata sake cewa komai ba ta fice a d'akin a mutu'kar gigice, domin jini ya fara fitar mata...


Adda ta zubawa JAWAHIR ido na d'an wani lokaci can tace" to Allah ya sauwak'e yarinya ta kina kuka kinji, IMRAN ka kula da ita da kyau kaji.." ba suce komai ba, har ta fice a d'aki..

IMRAN ya juyo da Jawahir da nufin tambayar ta, ai kafi yayi maganar tayi sauri rufe mai baki da d'ayan hannu ta, tana kallon tsakiyar idanun shi tace" a'a bana su tambaya ko bin ba'asi MY a hankali kai ma zaka fahimci komai, amma ko da nan gaba na rok'e ka kar kaga laifi na, domin dole akayi mini.." ta fad'a wasu siraran hawaye na fin k'uncin ta, dan tana jin tsanani zafi a kirjin ta, musamma in ta tuna Jameela fa... kawai sai ta sake saki wani rikitacen kuka mai kona zuciya...


IMRAN ya d'ago face din ta ya had'e da tashi, cikin murya rarashi yace" JANA'A!!! kalle ni nan kinji, kalle k'wayar idanu na ki fad'a mini sirin zuciyar ki ?" ya fad'a yana kafe ta da ido..

A hankali ya ware fararan idanun ta a cikin nashi, kalla juna suke babu k'wak'wautawa can ta k'auda kan ta gefe, ya sa hannu ya maido ta, kafin ta ankara ya had'e bakin su waje guda, sun d'auke lokaci suna kissing din juna su cike da so da k'auna ga tsananin k'warewa...

Sakin bakunan juna su su kayi kamar had'in baki suka rungume juna cikin tsananin shauk'i da an'nashewa, cike da zallar k'aunar sa tace" ina mutuwar son ka My heart, Ina maka son da ban tab'a mai wani kamar sa ba, a matsayi masoyi, ka raine ni da tsantsar k'aunar ka, wace har abada banaji zan d'anne ta, ILOVE YOU SO MUCH MY HEART!! Allah ya bar mu tare har gaba da abada..." ta fad'a tana sake shigewa jikin sa...


" I LOVE YOU 2 MY JANA'A, ALLAH ya k'ara tsare mini ke a duk inda kike, Allah ya bani ikon rik'e alk'awari da amana, Ina miki son so My K'albi son da ban tab'a ma wata budurwa ba sai a kan ki domin na rayu da son ki ne tun kina zanin goyenki, a zato na shak'uwa ce kawai Ashe abin yace haka, na godewa Allah ya sa tun kafin na sani kika zamo matata, naji dadi hakan sosai Allah ya biyi su baffa da mama da gidan aljanar fidaussi, Allah ya saka musu da mafificin alhairi Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahi..." shi ma yana saki matsi ta a jikin sa...


_ikon Allah halan wanna masoyan kun manta da ciwon dake goshin ta, sai wani matsi-matsi kuke a gaba na babu ko kunya, dadi abun ma Ina da miji a kusa_. πŸ˜’



Jameela tana zuwa d'aki bayi ta nufa cikin rawar jiki ta hau wanke hannun, ga rad'ad'i zafi na shigar ta, haka ta d'aure ga bak'ak'en maganganu da JAWAHIR ta yab'a mata, zafin zuciyar ta ya k'aru ta kasa jure wa aiko ta saki wani masifafan kuka me cin rai, hakan yayi dai+ da shigowar Adda bayi, gani Jameela na kuka sai kawai ta tsaya tana kallon ta sai da ta bari tayi me isar sanna tace" to in kin gama zo ina jiran ki.." ta koma d'akin ta tayi zauniyar ta...

Jameela ido jawur ta biyo bayan ta, har jin hanci take..

" Ki nutsu magana zamuyi mai mahinmaci.."

Daga na nima waje nayi tunda maganar bata yara bace..


Bayan kwana biyu,
a yanzu JAWAHIR ta ruga da ta gano lagwan Jameela sosai, babu dama su had'u sai ta sata kuka me cin rai, tunda ta fahimci bata son a mata gorin aure ko matsi mata hannu, to Jawahir ta samu waje da zarara sun had'u to insha Allah sai ta fitar mata da jini, haka ne ya sa da ta hango JAWAHIR ko me take sai ta gudu a wajen, a cikin gidan babu wanda ya fahimta sai IMRAN da Adda Samira...


Gashin dai kumba dafi ne da ita, gashi kuma ba sake waje ake ba, inda tayi mata a nan farko nan take sake ji mata wani, aiko wajen yayi duhu duk da hasken fata irin na Jameela..

Ohh su JAWAHIR an k'ware a mugun ta..



Kallon baffa yayi da rashin fahimta yace" baffa ni fa gaba d'aya bangane ba, yanzu menene amfani dawo mini da takkardun nan waje na, ni a gani na zaifi kyau ka ci gaba da rik'e su a hannu ka, tunda kaga ni har yanzu ba wai wani wajen ajiye ne dani ba mahimmi..."

" A'a yaro na tunda har kaga na baka to lokacin da mahaifin ka ya d'iba ne ya cike, maganar a jiya kuma a kwai waje-je da dama me zai hana ka kai su bank, na san a can babu abinda zai faru dasu, ban so ko JAWAHIR ta san inda suke domin su din abubuwa ne masu matuk'ar mahimamci a rayuwar ka IMRAN kar kaga ba dawo maka da ragamar kud'in a hannu ka ka fara sha-shanci duk da na san ba halin ka bane, Amma na san kud'i suna iya sa mutun yayi komai a kan su, ga hakin ka nan ni na baka abinka hannu da hannu, Allah ya baka ikon rik'e su cikin kwanciya hankali..." ya fad'a da murmushi akan face din sa..

IMRAN yace" insha Allah zanyi abinda kace, na gode sosai baffa Allah ya biya ki da mafificin alhairi, amma banjin zan kai su bank, Ina da wani waje maimahimmaci zan adama su a can, sai magana companies ku ci gaba da rik'e su kamar yanda kuka saba, na gode sosai baffa...".


Nan su kayi musabaha Baffa ya fice a office din, IMRAN kuma ya fad'a duniyar tunanin dalilin da yasa baffa ya dawo mai da komai hannun shi, anyya lafiya kuwa...? babu amsa dole yaje bakin sa yayi shiru..



Bayan wata biyu,

Tunda ta matsawa Jameela ta samu salamar a rayuwar ta babu me hantar ta ko kyarar ta, lafiyar ta kalau yanzu ga soyayya da take k'ara bunk'asa, tana cinyyar sa yana shafa kan ta gefe gudu kuma, su Adda ne da yanzu abin ya zame musu jiki, Amma da Allah kad'ai ya san zuciyar su, cikin shagwab'a tace" My!! ya maganar sabon gidan namu ne?"

Gaba d'aya hankali su ya dawo kan su, IMRAN ya danyi jimm can kuma yace" sorry K'albi maganar gaskiya yanzu sai dai ki k'ara ha'kuri har su baffa su samu abinda suke nema yanzu, domin maganar da nake miki duk wata dukiya da kika sani yanzu ta dawo hannu na ba tun yanzu ba, so duk da su baffa ba wai basu dashi bane kawai Ina so naga sun sake samu ne sosai yanzu nauyi zaiyi musu yawa ne, in har na bar gidan nan so ni kuma bazan so haka ba, domin ina k'aunar su baffa da Adda ga k'unne na, kema na san bazaki so mu tafi mu bar su ba ko.?" yayi maganar yana laik'a fuskar ta..

Murmushin ta sakar mai game da cewa" haka ne My!! Allah ya zab'a Mana mafi alhairi, Allah ya baka ikon juya dukiyar ka ta hanyar halal, Allah ya tsare maka zuciyar ka ya kare ka ga duk wani abun ki mutun ko aljan.." ta fad'a tana shafa mai sajan face din sa..


" Ammeen Ameen matata Allah ya bar mu tare naji dadi addu'ar nan taki.." ya fad'a cike da farin ciki..

Adda mairo tace" au dama yanzu kana nufin dukiya ta bar hannu Abdullahi kenan.??" ta fad'a cike da sha'ku.

Adda Samira tace" haba wallahi ba a bazan ba ni fa nace, amma kai yanzu IMRAN ko kunya baka ji na amshe dukiyar ka ahannu k'anni uban ka, yanzu kai ka kyauta kenan? lallai yaran yanzu sai a hankali ai BANYI tunani zaka mai irin wanna sakayyar ba wallahi, lokacin da take hannu NAFI'U baka amsa ba sai yanzu da shi yake k'ok'ari gani ci gaban ka a kullum, to wallahi ka dai ji kunya IMRAN mace ta zugaka ka zama kamar ba imran din da na sani ba, ga zallar rashin ta ido da ta koyar da kai a gaba mu ko kunyar idanun mu bakwaji zaka mamak'e yarinyar k'aramar a kirjin ka, ni dai Allah na gode maka da ban haifi iri wanna mugun iri ba wallahi, to ka amshe kud'i saura kadarori ko suma ka amshe...?" ta fad'a cikin hargowa, dan ko kad'ai ba tayi tunanin haka zata faru ba..

JAWAHIR tayi shiru tana tunani da nanata maganar da addan ta fad'a na mugun iri, yanzu ita ce mugun iri, take Taki wasu hawaye masu zafi suna fito mata, Adda mairo ce ta kula aiko ta amshe da cewa" sannu gyare uban 'yan kuka, uwarki akayi miki da zaki sa mutanen a gaba da kuka, yarinya kamar wata kyand'ir d'aga magana sai d'iga to ko mutuwa zakiyi sai na mu fad'a marasa kunya futsararu.."
ta fad'a kamar zata kai musu duka...

Khadija wace ta muto akan son IMRAN ta had'e Rai tace" haba mama meye haka dan Allah, ko banza su mafa tamkar 'ya'yan ku ne, yanzu ni a cikin maganar nan ma gaba d'aya bangane abin zagi ko cin fusaka da gori ba, kud'in shi ne fa yana da ikon da zai amsa a duk lokacin da yake so, bare kuma na san yayana ciki da bai, ko da ku baza ki yarda ba baby yanda za'ayi yace baffa ya bashi kud'in sa, ki tsaya baffa ya dawo shine kad'ai zai warware muku komai, kar kuje kuyi abin kunya n...." Maganar ce to mak'ale sakamakon bige mata baki da Adda tayi, da k'arfi har sai da jini ya fito..

Ta galla mata harara tace" shasha kawai me mahaukacin tunani, na sake jin bakin ki a nan ki ga yanda zayin dake.."

Khadija Yar baban ta aiko ta saki kuka me tab'a Rai game da cewa" wallahi sai na fad'a wa babana.." ta wuce part din su da gunjin kuka..


Jameela tace" kai ma dai baka kyautawa kan..." Tsawa da ka mata me k'arfi gaske wace ba ita d'aya ba hata su Adda sai da suka tsorata kowace tayi wuk'i-wuk'i da ido, ya shiga kad'a mata hannu cikin zare idon da yayi jawur murya a k'ausashe yace' wallahi na sake jin kiyi magana na lahira sai ya fiki jin dadi, da iyayen ki nake ba dake ba kar na kuma jin maganar ki a nan.." ya fad'a game dayin mata alama da hannu..

Jameela jiki na rawa ta wuce tayi part din su, dama albarkacin Jawahir suke ci har ya saki jikin sa a cikin su yanzu, to yau kuma gashi a tab'o shi har ya dawo ainahin IMRAN din sa...

Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da sauraron su...

" IMRAN ai baza mu san ran ka ne ya b'aci ba sai ka rufe mu da dukan tunda k'arfin ka ya kawo, yoke kiyi wanna maganar mutumin da ya iya amshe kud'i ai babu abinda bazai iya ba, b'acin rai ba ko mutuwa zamuyi sai mun fad'a.." su fad'a a tare game da barin wajen ko wace zuciyar ta na mata kunnar gaske, gaskiya yanzu su ka rage basu kud'i ba kamar dah ba..

Khadija na zuwa d'aki way ta bugawa babanta ta gaya mai duk abinda yake faruwa aiko babu shiri ya fad'awa Dan uwan sa su kayo gida ran su a b'ace..


JAWAHIR ta d'ago tana kallon mijin nata, can kasan idanun sa ta hango tsantsar bakin ciki da b'acin rai amma yana k'ok'ari boye mata, kau da ido tayi ita ma tana share k'wallar, cikin sanyi murya yace" oohh kuka ko K'albi??"

Tausayi ya bata gani yanda aka zagin sa tas, amma yana k'ok'ari kwantar

Please Login or Register in order to submit comment