Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake magana ba Imran ya d'auki Jawahir tamkar jaririya suka wuce ko wane da abinda take sa'kawa a ran sa, a haka har suka isa inda motar su take Jameela ta shiga ta ta, inda IMRAN da JAWAHIR suka shiga car d'aya basu wuce ko ina ba sai gida har yanzu Jawahir ba tayi magana ba..

Bari su wajen babu jimawa Nabila da ma'karraban ta suka iso wajen cike da mumunan nufin su, sai dai abin takaici babu Jawahir babu dalilin ta wannan abun ya fusata Nabila nan take ta shararawa ogan cikin su mari cike takaici..


A cikin gida kuwa Adda mairo da Adda Samira a zaune ga khadija dake gefe sai iyaye maza dake d'aya gefen, duk wanda ka kalla a cikin su zaka iya fahimtar halin da yake ciki domin gaba daya fuskar su babu an'nuri ko wanne da irin tunanin dake ran sa...

Can Baffa Abdullahi yace" yaran nan ina ji a jiki ba lafiya domin sam ba sai kai wa irin wannan lokaci a wajen, abin mamaki kuma shi ne duk wayoyin su ba sa shiga gaba daya su ukun.." Ya fad'a hankali a tashe.

Baffa Adam yace" kuma ance ko wanne da car ya fita.."

Shi dai Baffa Nafi'u bai ce komai ba dan yayi zurfi cikin tunanin..

Suna cikin haka ne su IMRAN suka shigo ko wanne sa fuska babu walwala ga Jawahir a hannu kamar wata gurguwa, a tare suka mik'a Adda samir tayi kan Jameela tana rok'o ta tace" ke lafiya kuwa kuka shigo mana gida kamar wa yanda akan ma sane?" ta fad'a cikin tsoro da furgici...


Su Baffa kan IMRAN su kayi ko wanne da kalar tambayar da yake mai, baya da duba jikin sa da suke Baffa Adam ne ya amshe Jawahir dake hannu Imran yana cewa" ita kuma me ya sa me ta? " akan kujera ya sauke ta yana duba ta gani yanda tayi futu-futu da k'asa ga ido dake a kumbure sai ya d'ago da sauri ya kai kallon sa ga Imran yace" kayi magana ma me kuma ya same ta wannan?" ya fad'a a kid'ime..

Hat Adda mairo suyi inda su Jawahir suke aka bar Jameela da Samir tsaye su biyu k'wal babu me bi ta kan su, wannan abu ba k'aramin b'ata su rai yayi ba gani yanda aka ware su gefe tamkar ba yan gidan ba, zuciyoyin su su kayi zafi ainun...


_nace kuka ware dai tunda ke kika ja yar ki tun farkon shigowa_


Cikin kuka Jawahir ta fad'a musu abinda ya faru tun daga farko har k'arshe babu abinda ta boye musu, babu wanda ta girgiza ba da jin abinda ta fad'a Baffa Nafi'u bai ce komai ba ya taka zuwa wajen da su Jameela suke hannun ta ya kama ya matso da ita inda sauran mutane suke kana yace" 'yata gaya mini me ya faru dake ke ma?" ya fad'a cikin sanyi murya..

Jameela an samu abinda ake so ai take ta shiga sharara karya tanayi tana kuka kamar gaske daga karshe kuma ta fad'i gaskiya Imran ne ya taimake ta...


Adda Samir babu ko jin kunya ta iso waje tana ma Imran mugun kallo kana tace" Imran ka fita a idona na rufe 'yata ba kamar ko wace 'ya bace da zaka mayar da ita karan farauta daga jin wannan zance ma ai an san had'a wa akayi kai me ya kai ka wajen da har ka taimake ta in da dama ba kasan da abun ba? tunda tace ita d'aya ta fita kuma babu wanda ta gaya ma inda zata je kai wanna ma rainin wayo ne, wallahi ka ci gaba da dirmar ka inda ka saba amma ina ma gargad'i ba aka 'yata ba in ba haka ba kuma zamu sanya k'afar wando d'aya da ke wallahi dan ni bazan d'auka ba." ta fad'a tana saki wani mugun tsaki kana ta ja hannu jameela suka bar wanjen...


IMRAN yayi kasa da kan shi ga wani irin zafi da kirjin sa ke mai, Baffa Abdullahi ya fad'a kafad'ar sa yana girgiza mai ka alamar ya kara juriya.

Babu wanda ya kula da time din da jawahir ta mik'a sai gani ta kawai su kayi a jikin Imran ta wani mak'alk'ali shi tana kuka marar sauti, zuwa can tace" har kullum bani da wani babban masoyi a duniya kuma babban yaya abokin shawara me share mini kuka na sama da kai MY!!, ka nuna mini duk kan gata wanda ko wace d'iya zata so ta same shi a wajen d'an uwan ta, tabbas kai din ba macuci bane haka kuma in duk duniya zata taru akan na amince da sa hannun ka akan faruwar wani abu daga gare ni bazan lamun ta ba, domin nafi kowa sani wanene kai kai din adali ne me tausayi da adallci har kullum addu'a ta bata wuce Allah ya bani abinda zan saka maka dashi wanda nan gaba za kayi mutu'kar alfahiri dani kamar yanda na keyi da kai a yanzu, MY! bazan boye maka ba ina maka wata irin k'auna wace ban san adadin ta ba, addu'a ta a gare ka shine Allah ya baka mata ta gari wace zata kula mini da kai da kyau wace zata so ka fiyya da yanda nake son ka MY!!, Allah ya jikan Mama da baba ya ka haske k'abarin su, ina mutuk'ar k'aunar ka MY!!." ta fad'a cikin matsananci kuka..

Baffas suka kalle junna su a tare Abdullahi yayi musu wata ink'iya da ido a tare suka saki wani murmushi me k'ayatar wa..


Khadija ta saka hannun ta bisa k'uncin ta tana share wata 'kwalla Adda mairo ta dafa kafad'ar ta suka bar wajen babu wanda ya kula da su...

Imran ya rungume ta sosai a jikin sa yace" Nima haka K'albi fatana Allah ya nuna mini lokacin da zan mik'a ki gidan mijinki da hannu na, Allah ya k'ara kare mini ke a ko wanne lokaci muje ki gyara jiki ki..." ko ta kan iyayen su maza ba su bi suka shige ciki abin su..



_a nan zan dakata sai na ga kamun laudayin abun, hmmm har yanzu babu wace ta bani naman sallahr ta ina sanne da ku aradu_ 😩


Comment

And

Shared.

Please

Mrs Abubakar ce
[8/21, 1:47 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


1⃣5⃣➖1⃣6⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Tunda d'aga lokaci Jawahir bata sake gigin fita ita d'aya ba, duk inda zaje tare suke tafiya da Imran..

Ta fanni karatu kuwa sosai suke samun ci gaba dan suna da mutu'kar k'ok'ari...


Haka suka sake shafe shekaru, kuma duk da haka ba adai na farautar rayuwar Jawahir ba,

Wani abu da Adda Sameera ta fito dashi shine da zarar ta ga Jawahir da Imran sun k'eb'e gefe guda sai tazo ta zauna a wajen, dan ita a tunanin ta soyayya suke haka in zasu fita yawo sai ta hanna ace war ta yanzu Jawahir ta girma bai kama ta ana barin ta yawo da namiji ba, wannan maganar ta k'ona ma Imran rai sosai amma sai ya d'aure gudun kar ace yayi mata ba dai-dai ba...


Gani yanda sha'kuwar su tayi yawa, dan ko a gaban wa suke haka suke nuna ma junan su k'auna, ya sa iyayen su maza taruwa a inda suja saba, game da yanke shawarar gaya musu su din ma'aurata ne...


Tunda abin nan ya faru Nabila ta kasa gane kan Imran dan yanzu ko tazo bai fita haka abokin sa zai gaji ya rabo dashi...



Baffa Nafi'u ne zaune kan abin sallah yana ta addu'oi, Jawahir na daka gefen sa a zaune ta zuba mai ido har ya ida, bayan ya sallame ya ka duban sa gare ta kana yayi murmushi yace" auta na ya akayi ne?" yayi maganar cikin sanyi murya..

Kawai jiki sa ta fad'a tana sauke a jiyar zuciya zuwa can tace" My abba na haka kawai nake jin wani iri yanayi a jiki na, kamar zan rasa wani abu me girma a rayuwa ta.." ta fad'i maganar murya can k'asa..

Kan ta ya shafa kana yace" 'yata a duk yanayi da zaki tsinci kan ki, ki kasance me amabaton sunnayen Allah da kuma neman tsari a gare shi, sanna ki kasance me yarda da k'addar me kyau ko akasin haka.." sai kuma yayi shiru na wani lokaci..

Gani haka yasa Jawahir sake shigewa jikin sa tace" Insha Allah zan kasance yanda kake so Abba na, amma sai dai yanayi da nake jina kamar..." sai kuma tayi shiru tana tunanin me zata ce..


Abba har zayi magana sai ga Imran ya shigo d'aki bakin sa d'auke da sallama, Jawahir babu ko kunya ta koma cinyyar sa ta kwanta Abba ya kalli su cike da kaunar su,

Kana yace" Allah yayi muku albarka yara na Allah ya kare muna ku a duk inda zaku tsinci kan ku yayi muku tsari da makkiya na fili da na boye, IMRAN ga k'anwar ka nan na bar maka ita amana ko bayan rai na ka kula mini da ita fiyya da zato na, bani da sha'ku akan kan shi yasa na baka amanar ta.

IMRAN ita din yarinyar ce k'arama sai kayi hak'uri da duk abinda zaka gani na san nan gaba za kuyi alfahir da hakan, a tsakanin ku din nan akwai wata alak'a me girma wanda nan gaba kad'ai zaku sani, fatan shine ku zamo masu biyayya ga iyayen ku dan Allah yara na kar kuyi watsi da abinda muka jima da shirya muku shi tabbas nan gaba za kuyi alfahiri da hakan, Jawahir ki zamo me biyayya ga wanda nan gaban zaki san shi din waye a wajen ki, bana so ko kad'ai ki bijire ma umarni mu dan bani kad'ai banr har da momeki muka shirya haka ki bishi sau da kafa wata rana sai labari.." Ya saci kallo su kana ya share yar k'wallar da ta zubo mai..

Gaba d'ayan su jiki su yayi sanyi maganganu abba kamar wanda yake bar musu wasiya, a kusan tare su kayi wannan tunanin da sauri suka kalle shi..

Alama yayi musu da hannu baya su yaji komai daga gare su, kana yace" amsa d'aya nake son ji a bakunan ku shi, ku amsa mini zakuyi farin ciki da abinda mu kayi muku? kuma zaku amsheshi da hannu bibiyu shin zaku cika mini buri na??"

Gaba d'ayan su kuka suke cikin had'i baki suka ce" Insha Allahu Abba ko menene muyi alk'awarin cika maka shi, ko da ko hakan zai zamo sanadin watsiwar farin cikin mu ne na har abada domin kayi mana komai a rayuwar duniya wanda ko wanne d'a yake maradin samu.."

Abba ya bude musu hannu alamar su zo gare shi aiko babu musu suka rungume junan su cike da zallar 'kauna gashi ko wanne su hawaye yake zuciyoyin au cike da tambayoyi dalilin da yasa abba yake wanna furinci...

_Nima da nake gefe na share k'wallar tausayin su_


Sun jima a haka sosai sai zuwa can suka saki juna Abba ya kama hannun Jawahir dana Imran ya had'e su waje d'aya kana yace" Ni Nafi'u na baka y'ata halak-malak kuma na san ko da nan gaba baza ka bari tayi kukan bakin ciki ko maraici ba, kema ki bi yayan ki sau da kafa domin baki da kamar sa a cikin duniyar nan, kuma bana so na sake jin komai daga gare ku, gobe in Allah ya kamu da musalin karfe 8:00 ku shiryo ku fito babban falo a nan ne zaku gane inda magana ta dosa, kuje na sallame ku.." Ya fad'a yana kawar da kan sa gefe...

Haka suka mik'a jiki a sanyaye gashi duk ba haka suka so ba, suna tafiya suna waigen sa shiko yaki juyo wa duk kan su hawaye suke har suka bar d'akin, Abba ya kalle bayan su yana share k'wallar sa domin gaba d'aya zainab din sace ta fad'o mai, ya laushe idanu kana yace" Allah sarki mata ta ko a wanne hali kike ciki yanzu??" ya fad'a yana lumshe idanu..


"" Tana nan cikin k'oshin lafiya sai dai tak'i kwantar da hankalin ta akan lallai sai ta ga ahalin ta.."

Yaji wata murya da bai tab'a jin ta ba a rayuwar sa, ta amsa mai tambayar sa cikin sauri ya bude idanu sa aiko caraf ya sauka kan mutane uku ko wane fuska a rufe da bak'ar hula hannu su d'auke da bindigo Nafi'u ya ware idanu waje cike da tsantsar tsoro da razana kana ya koma gefe d'aya hankalin sa a tashe...


Suka fashe da dariya gaba d'ayan su wanda ya fara magana ne ya nemi waje ya zauna kana yace" kwantar da hankali dattijo abu d'aya za kayi mu rabu dai har ma da tukuyici me girma da zayi maka wanda na san har yanzu baka d'ena jin rad'ad'in sa ba, amma fa sai kayi biyayya sannan zaka samu ko ba haka bane gayes?" wanda suke tare dashi suka amsa da cewa haka ne boss..

Nafi'u yayi musu wani kallo kana yace" su waye ku kuma ya akayi kuka shigo cikin gidan nan har kuka shigo cikin d'aki na??" ya fad'a cikin k'arfin hali da jarumta irin ta mazan jiya...

" Wannan ai duk abu ne me sauki kuma zaka san su nan da ba da jimawa ba, Nafi'u kashe ba wani abu bane me wahaka a waje na ba to amma ba zanyi haka ba sabida ba tsari na kenan ba abu d'aya nake so daka a yanzu wanda inda kayi shikenan ka fanshi kan ka da na matar ka.." Yayi maganar yana nuna mata face din wayar dake hannu sa..


Cak Nafi'u ya tsaya mamaki da alajab'i da rud'ewa suka baiyana akan face din sa gani matar sa Zainab d'aure da igiyoyi, face din nan tayi jawur da tsananin wuya da taci abinka da farar mace jikin sa ya d'auki rawa kana yace" Zainab!!!" a ciki wani irin yanayi me tsamuwa..

Zainan da idon ta yake a rufe jin muryar da take maradi tayi maza ta bude idon ta da sauri wanda yake cike da 'kwallar bakin ciki, tace" Nafi'u!!!" Ita ma cikin wani yanayi..

Tabbass ita ce shine abinda yace kana dariya da murmushi suka subuce mai a lokaci gudu ya d'aura "wa yayi miki haka mata ta ? me saya makkiya suke san rabani dake Zee na ? me suke so haka a wajen mu eeyy Zee na? me yasa mu kad'ai ne muka tsolai musu ido ne??"
ya fada cikin matsanacin kuka..

Bata damu da bashi amsa ba tace" abinda nake so da kai miji na shine duk rintsi duk wuya kar kayi abinda suke so ko da ko a gaban idon ka zasu kashe ni makkiyan mu suna tare da mu sunne..." kiti ya datsi wayar kana yayi wata muguwar dariya..

Yace" ka dai gani da idon ka ba labari muka baka ba, shin za kayi abinda muke so koko?" ya fad'a cikin d'aure face..


Soyayya kenan Nafi'u tunanin Zainab kawai yake cikin wani yanayi yace" ......


😢😢😢😢😢😟

Comment

And

Shared

Please


Mrs Abubakar ce 💃💃
[8/27, 1:06 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


_Gida me dadi na gode sosai da addu'in ku, Allah ya biya kowa buk'atar sa ta alkhairi amen. Ina taya d'au'kacin hausawa murnar hausa ta duniya Allah ya k'ara had'a kamu ameen.._


1⃣7⃣➖1⃣8⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Soyayya kenan Nafi'u tunanin halin da zainab take ciki kawai yake, amma tuna wa da abinda tace mai take yaji wai k'warin gwiwa ya tsarga mai...

Cike da dakakiyar zuciya yace" me kake so nayi maka..?"

Boss yayi murmushin samun nasara kana yace" so nake ka fad'awa IMRAN kun jima da yi musu aure, bayan nan kuma ka sa shi ya sake ta a gaba ido na da idon ka, in ba haka ba kuma hmmm.." yayi maganar yana karta wuk'ar hannun sa..

Nafi'u yayi mai wani mugun kallo kana yace" ko zan iya sani dalili ka nayi hakan ? da kuma wanda ya aiko ka..?"

Dukan gilas din dake gaba sa yayi take ya tarwatsi cikin fusata yace" tsakanina dakai babu tambaya ka aikata abunda nace kawai shine mafita.."

Nan suka shiga jan zance shi ya fad'a Nafi'u ya fad'a a haka har zuciyar Boss ta tunzira aiko ya d'aga bindigar sa ya saita kan Nafi'u cikin fushi, yana shirin harba kunamar..

Cikin gigita yara sa suka mik'a a furgice suka had'a baki wajen cewa" ya labai. tace banda kisa.." sai da su kayi maganar kuma suka rufe bakin su ciki wani sabon tsoron dan sunyi k'atobara..

Ranshi ya sake b'acci wanda ya fara maganar yasa bindiga ya harbe shi a tsa'kiyar kai bulet din ya bunlo ta k'eyar sa, take a wajen ko surawa bai yi ba ya mutu. sauran yaran sa suka tsorata iya tsoro ko wane ya shiga hankalin sa..

Sosai Nafi'u ya tsora ta amma jin abinda suka ce ya san duk runtsi baza su kashe shi ba, cikin wani yanayi na nuna halin ko in kula yace" kayi abinda nace kawai ka kashe ni shina mafita a gare ka amma ko me za kayi baza'a raba auran nan ba, kai bani kad'ai ba ko yayi na zaka bi d'aya bayan d'aya babu wanda zai yarda a raba auren nan ko da ko zaka ringa kashe mune a gaba idon mu.." Yayi maganar yana gyara zaman shi..


Boss ya ciza yatsa kana ya mayar da kallo shi ga gawar dake wajen yayi murmushin mugunta, sanna ya mayar da kallon sa ga Nafi'u yace" dama an gaya mini kana da taurin kai amma zan koya maka hankali yara ku motsa..." sa rai sun me yake nufi aiko babu b'ata lokaci suka damk'e Nafi'u, kamar yanda ya faru akan Zainab haka ne ya faru akan Nafi'u domin k'walbar suka sake fidowa suka wanke ma yaran boss face da ita take fuska tayi bak'ik'irin kayan jikin sa suka cire mai aka mayar da na mamacin jikin sa da yake wanda ka harb'a babban mutune kuma shima har da farin gashi kamar yanda na Nafi'u yake, duk wata hanya da suka san za'abi domin bincike su sai da suka shafe ta kafin su tafi, Nafi'u yayi bakin ciki sosai amma duk da haka yaki yarda yayi abinda suke buk'ata yana ji yana gani suka raba shi da gidan sa da kuma ahalin sa baki d'aya...

Da safe kowa ya tashi cikin walwala da jin dadi amma banda Jawahir da take jin ta kamar marar lafiya, gida ya kaure da hayani da aike-aike jama'a suka fara taruwa haka su Baffa Abdullahi su ma suka d'au wanka kowa ya k'afe a mazauni sa, duk wanda ka kalla a gida farin ciki ne akan face din sa duk da mutanan gidan basu san mak'asudin taron ba...


Jawahir na hango ta d'au wanka kyau iya kyau, ta sha wata doguwar riga marar kafad'a pink cool kai fan's Jawahir fa ta had'u irin sosai din nan wallahi ga wata kwaliya da akayi mata abin ka da farar mace take ta haska wajen tana wani d'aukar ido, tubarkala na iya cewa kawai..


IMRAN KENAN kyakykyawan matashi meji da iza da k'asai ta yaro me zamani wanda kaf garin kano babu wanda bai sanshi ba, dan yaro ne wanda kudi ya zaunawa ga kyauta da taimakom tallakawa burin ko wace budurwa taga tayi taraiya dashi..
shine ya fito ciki wata shiga ta manya kaya masha Allah domin IMRAN ya wuce tunanin me tunanin dan ni kai na sai da na girgiza da _amma fa duk had'uwar sa bai ka Abubakar din na ba domin shi din.na daba ne yasin. lozzz

idanun kowa ya koma kansu, sai kallon su ake ana sanbarka..

Suma iyaye fitowar su ta musamma ce ko wanne su ya d'au wanka, iyayen su mata kenan ga kaya masu tsada da suka saka ko wace sai wani yauk'i take da bud'e hanci su a lallai ga masu gida...

Jameela ma tayi kyau mutu'ka ita da Khadija kayan su irin d'aya suma masu tsadar bala'i domin ta kanas IMRAN ya siyo musu haka kayan dake jikin Jawahir da kan sa ya zab'a mata, iri d'aya dashi...

Maza sun gama shiryawa amma shiru babu NAFI'U Abdullahi ya kalli 'kanin sa ciki soyayya yace" ka sa IMRAN ya kira mana sirikin sa.." shima cikin murmushi yace" angama.."

Comment

And

Shared

Na Gode sosai kawayen kirki da iyaye na Allah ya biya ku...



Mrs Abubakar ce
[9/2, 11:43 PM] Mrs Abubakar 🌹: *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*💔🌹BA SO BANE 🌹💔*
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYi DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


1⃣8⃣➖1⃣9⃣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Baffa Adam da kan shi yaje ya fad'awa IMRAN dake hard'e akan kujerar girma, babu musu ya amsa da to, bayan tafiyar sa har zai tashi sai ga wasu abokan sa da suka jima basu had'u, sanni domin shi suka zo sai ya koma wajen JAWAHIR cike da so da kauna yace" k'albi na, in babu damuwa ki kira Baba na mana su Baffa na son ganin sa.." ya fad'a yana kashe mata ido d'aya.

Bata ce komai ba sai kallon sa da take face din ta cike da murmushi ta mik'e tsaye, sai da suka tsaya gaf da gaf numfashin su na gogar na

Please Login or Register in order to submit comment