Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tuna da zaman yan borin da sadiq yayi sai ta dara a haka har bacci ya kwashe ta.



Duk juyi dayayi sai ya zabga tsaki saboda bacin rai ola ne ya juyo ya ce boss are u ok , lumshe ido yayi yace "Yess" ok good night, boss if u need something talk to me please, ok tare da juyawa ya gyara kwaciyar shi a hankali ya shafa gashin jidda sannan ya lumshe ido, daya lumshe ido fatuha yake gani tana mai dariyar qeta wata irin iska ya furzar mai zafi daga bakin shi ba abinda zai hana shi yima fatuha horo mai tsanani Wanda ko wani aka ce tayima irin cin kasin da ta mai ba zatayi marmarin maimaitawa ba, tsaki ya kuma ja saboda takaici a haka har baccin barawo ya dauke shi.


*Asuba ta gari..*

Tunda asuba fatuha ta tashi saboda tasan in yau bata tashi da wuri ba Allah ka dai ya san jarabar da sadiq ze mata ,dan tsaki ta ja can kuma tayi murmushi tace, ko ba komai ina ganin mai kyau Qur'an naji dadi, sannan ta shige toilet tayi wanka tare da yin brush da dauro alwala tayi sallah sannan tasa uniform komawa tayi ta zauna saman bed tana kallan agogo karfe shida take so ta shiga part din sadiq.


Ba laifi daya tashi sallah asuba kafar ta saki tunda har ya taka bada taimakwan ola ba, toilet ya shiga yana shiga abinda ya faru jiya ya fara dawo mai kamar yanzu, murmushi yayi yace fatuha baki ji sannan ya qara jan tsoki ya dauro alwala tare da yin wanka ya fito ko da ya fito jalabiya white yasa ya tada sallah yana gamawa ya koma ya kwanta saboda har yanzu jikin nashi yana jin shi wani irin.

Bude handle din kofa tayi ta fito direct part din sadiq ta wuce kai tsaye, bedroom ta shige kallo daya tayi ma daki hango ola tayi kwance yana ta share bacci har da munshari saboda dadi, dariya ta so ta kubuce mata ta guntse dariyar kallan bed tayi sadiq kwace rungume da jidda murmushi tayi a hankali ta qarasa tare da leka fuskar sadiq ta ga dai bacci yake cikin dubara ta shiga janye jidda daga jikin shi, hannu ta ya kama a tunanin shi jidda ce zaro ido waje fatuha tayi tare da fara matsar kwalla a tunanin ta tashi yayi jin beyi magana bane ya sata lumshe ido a hankali ta zare hannu ta ta dau jidda suka fita, direct bathroom ta dire jidda ta fara yi mata wanka , washe da baki jidda tace Anuty good morning , tap ke kika san wannan dariya jidda tayi ta ce inakwana fa nake nufi Anuty aiyo aini ban sani ba, a ina ake koya maki wannan abun wai washe baki jidda tayi tace "A school "aiyo wai makarantar da zaki yanzu daga mata kai jidda tayi Alamar eh, murmushi fatuha tayi tare da daukar jidda suka fito bedroom ta dire ta saman bed tare da janyo lotion tana shafa mata, kai Amma gaskiya yarannan nada dadi jidda zaki rinqa koya min ko murmushi Jidda tayi tace Anuty kije daddy ya fara koya maki nima ai shi ya fara koya min ta ida zancan tana washe hakura, fatuha zaro ido tayi tace tap lalai yarin ya har yanzu baki san bakin halin ubaki ba Qur'an wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta, washe baki fatuha tayi tace ah ni nafi san ki kowa yamin kinji kinga daddy aiki yake zuwa ko, daga kai jidda tayi tare da cewa toh Anuty zan koya maki murmushi fatuha tayi tare da zurawa jidda uniform suka fito dining area lokacin su baba jinmai sun gama jera komai bude kololin ta fara marfesun kaji ne da soyanyan chips da egg da tea, murmushi fatuha tayi dan tunda ta zo birni ba abinda keyi mata dadi kamar chips shiyasa duk sanda akayi sakin tunbi take taci sosai zuba ma jidda tayi a plate tare da jamata kujera ta zauna ,zata fara feeding nata kenan sai ga su mom sun iso , gaishe su tayi cikin ladabi suka amsa plate ta janyo ta fara saving nasu mom sai murmushi take ita dai fatuha ta mata ko Dan abin dariyar ta ta cikin saving nasu sai ga sadiq ya qaraso dining yana tafiya a hankali yana dingishi ,a hankali fatuha ta kalli qafar wata irin dariya ce ta zo mata saboda yadda yake harba kafar kamar tsangal gumtse dariyar tayi ta cigaba da abinda take shiko sai aika mata mugun kallo yake , cikin na tsuwa ya qaraso wajan mom tare da yi mata pack a goshi ita da abba, abba murmushi yayi tare da shafa sumar shi, baby ya jiki shagwabe fuska yayi yace abba da sauki ,good amma dai gaskiya yau baza kaje aiki ba ko dan bata fuska yayi ya ce zani abba, gaskiya baby bazaka office yau ba ka bari zuwa gobe ka warware sosai, abba,shhh kawai ka hakura kaji ya ida zancan yana shafa gefan fuskar sadiq fatuha ko Sakin baki tayi da hanci, tace "Ohni sangami duk wani shaqiyanci ya iya, yo in banda iskanci qatoto da shi sai zuba shagwaba yake sai ka ce Jidda kai kwarankwatsi mai kyau dan bariki ne "duk wannan maganar tana yinta ne a zuciya kallan da sadiq ya wurga mata ne yasa ta dawo hankalin ta Jidda ya janyo jikin shi yau daddy ne zeyi feeding angel so bana buqatar ganin ki a nan tare da warce spoon din hannu fatuha, mom ce ta bala mai harara bata fuska yayi kamar qaramin yaro ya cigaba da feeding din jidda tana mai surutu, fatuha ko qoqari tashi tayi mom tace,"Ah fatuha aike sauki kika samu zauna ki ci abincin ki kan lokaci" murmushi tayi tare da kada kai ta zauna ta zuba dai dai cin ta tasa hannu ta fara cin hankalin ta kwance tana ci tana lumshe ido saboda tana san chips sadiq bala mata harara ya ke tayi wata loma da tayi sai da abin ya kusa bashi dariya da haushi duk suka hade mai ita ko ko a jikin ta su mom ma har karsu suke.

Bayan angama breakfast har bakin mota sadiq ya raka jidda, fatuha na riqe da lunch box din jidda sai da ta tafi sannan suka juyo zasu koma gida, da gudu fatuha ta wuce sadiq sai da taje bakin kofa sannan ta juyo ta mai gwalo tare da kwakwayar yadda yake tafiya ta fashe da dariya ta shige da gudu cije lips din shi yayi tare da tura hannu shi cikin sumar sa, oh Allah ka bani inkwan cima yarin yar nan sannan shima ya qarasa parlour ko da ya shigo ba kowa sai baba jinmai da ke kwashe kayan breakfast, gaishe ta yayi ta amsa washe da baki, part din shi ya wuce ya murda handle din kofar ya ji rufe mamaki ne ya rufe shi fatuha da ke jingine jikin kofar tace, me kyau kwarankwatsi ban budema kofar nan sai na gama aiki na Dan nasan halin ka kai mugune wallahi, ka na shigowa zaka bigeni sadiq da ke wajan kofa yayi sororo yana mamakin raini da fatuha ta mai cige lips yayi tare da barin gurin saboda ya san idan ya cigaba da tsayawa har kashe ta sai yayi dan bacin rai ,fatuha jin ya tafi yasa ta cigaba da aikin ta tanayi tana yan'wake wakyan ta har ta gama tuni daki yayi kyau sosai sannan tabi part din da turaran wuta tuni part din ya dau kamshi da kyau sannan ta qara gudun AC dakin ita kanta sai da taji kamar tayi bacci dan Kyan da part din ya mata.


A hankali taje bakin kofa ta murda handle ta leqa taga ba kowa, sannan ta fito da sauri ta wuce sadiq da ke kwance saman three star idanuwan shi lumshe kamar me bacci yana kallan fatuha ta ruga daki da gudu ta kule, tsoki ya ja tare da tashi duk kiyi ki gaba zan kamaki ne tare da wucewa part nashi dan bacci yake ji ko da ya shiga part din shi da kanshi sai da yayaba kyan da part din yayi, ga kamshi se tashi yake da sanyi irin yadda yake so lumshe ido yayi ya ja jiki ya hau bed ya kwanta.

Tana shiga bedroom kayan jikin ta ta rage ta shiga toilet, tayi wanka sosai dan yanzu ba qaramin jin dadi take ba in tana wanka amma da a kauye sai anyi da gaske ,yanzu ko fatuha ansan muhinmancin wanka, daure da towel ta fito ta goge jikin ta tare da shafe jikin da lotion mai kamshi da feshe jikin ta da turare yar huda da murza duk ba wata kwalliya tayi ba masha Allah fatuha tayi kyau, uniform din ta ta zura sannan tataro gashin ta Wanda ya cure gudaya tana qoqari kamashi amma ta kasa saboda yawan shi da tsaho bata fuska tayi tace, "Allah sarki inna da kina kusa da kin gyara min magana da su kayi da mom ce ta fado mata daure kan tayi da sauri ta haura upstairs dakin mom ta shiga ba ta nan neman ta ta shiga yi, kitchen ta shiga tare da tanbayar su rabi'a ina mom, tace mata tana part din abba ,toh tace tare da komawa parlour ta samu wuri ta zauna tana kallan film din India tana washe hakur.


Mom ce zaune da abba a bedroom din shi tana zaune saman kujera a hankali ya qaraso ya rungume ta ta baya, murmushi tayi, madam kullun qara kyau kike baki tsufa gashi har da jikoki, dariya tayi tace "Ya za'ayi na tsufa bayan mijin kullun yaro yake komawa" hancinta ya ja cikin tsokana , um next week zan koma uk kan maganan gaskiya this time around ban tafiya ni ka dai, tare nake so mu tafi murmushi mom tayi tace "Kamar kasan abinda ke raina kenan smile yayi um kuma sai gashi na rigaki fada ba, ya ida zancan tare da yi mata kiss a kumatu, ni ko abban sadiq kunyi waya da jawad kuwa? dan murmusawa yayi yace "Eh jiya munyi waya ya ce min yanzu shukura tsohhon ciki gare ta, so yake in ta haihu sai su zo ganin gida murmushi mom tayi ,Allah ya sauke ta lafiya kamar kasan nayi missing nashi wallahi ya kamata jawad ya dawo Nigeria da aiki amma nasan ba lalai ne yazo ba saboda na lura yafi san London sosai , um ke dai ki ce danki kike san gani yauwa gobe ki shirya ina so muje wajan ammi muyi masu sallama kafun mu tafi ,to tace mai tare da tashi zata fita janyo ta yayi jikin shi please in kinje karfa ki dade ki bar tsohon mijin ki da jira kinji murmushi tayi tare da kashe mai ido.. lol ah tsofafi na konewa hehe.

( shawara ga mata please mata ya kamata musani tsufa baya hana soyayya karki ce dan kina da manyan ya'ya ki ce ke kin girma ita soyayya bata girma, kuma gyara da tatalin miji shi ke qara dankwan soyayya, so da yawa wasu matan suke jawa maza jansu bin mata saboda kina ganin kin girma komai sai ki daina ,in mijin ki mai so ne daga nan zai fara bin ya'ya cikin shi a waje suna mai yana jin dadi please mata mu kiyaye) .


Fatuha da ke zaune saman kujera tana kallo, mom ce ta sauko daga upstairs, cikin ladabi fatuha ta gaishe ta tare da tuna mata maganar gyaraan kai , toh shikenan je ki shirya mu tafi , mom bada wannan kayan zani ba eh kisa kayan gida toh tace mata ta shige bedroom , mom ko part din abba ta koma ta tanbaye shi zata fita ya bata izini, sannan ta dawo dakin ta ta shirya cikin atamfa black mai ratsin red n yellow bubuce mai kyau tuni mom ta fito sosai bedroom din fatuha ta wuce tsaye, ta same ta ta rasa kayan da zata sa washe da baki mom ta qaraso, fatuha har yanzu baki shirya ba shagwabe fuska tayi taca "Wallahi mom na rasa kayan da zansa ne, zabamin dan Allah "to tace mata wata hadadiyar gown mom ta janyo brown colour mai ratsin milk da Stone's a jikin rigar mai dogwan hannu ce sai veil milk , masha Allah fatuha ba qaramin kyau kayan suka mata ba cib suka mata qirjin ko kamar tasa bara saboda yadda kayan suka mata rolling veil din tayi da gashin ta data daure sai abin ya bada kala ta fito fes, takalmi tasa black mai kyau suka fito , direct parking space suka wuce mom ta jasu suka fita sai fatima salon da ke gandu.


Basu wani dade ba a Solon din ba sosai an gyara gashin fatuha Dan ko ba'a sa mai ba saboda laushishin gashin ta dan in aka sa mai, ze iya konewa gyara shi kawai akayi masha Allah ita kanta fatuha sai da ta tsorata da gashin ta saboda har qugunta ya kai, da yaji gyara amma sai ya rage yawa su Kansu yan wajan yaba gashin su kayi ana gamawa suka dawo gida, a parking space mom tayi parking suka fito har zasu shiga gida sai ga driven jidda ya kunno kai yayi parking da gudu jidda ta qaraso tare da rungume fatuha tace "Anuty kinyi kyau ,waya maki kawalliya?" dariya fatuha tayi dan ita ba Wanda ya mata kwalliya daukar jidda tayi suka qaraso parlour sadiq na zaune saman two star yana shan coffee gefensa kuma baba jinmai ce tana dan taba hira da shi da alama tafiya zatayi.


Cikin sallama suka qaraso, sadiq ya amsa sallamar, fatuha ke dauke da jidda , jidda ta zame daga jikin ta ta Ruga wajan sadiq ta rungume shi wasa ya shiga yi mata tana dariya qarasowa Mmy tayi ta zauna saman three star ta ce "Oya a wuce aje a cire uniform, kin bar Anuty na jiran ki " sadiq ne ya dago ya kalli fatuha ya wani tabe baki tare wurga mata harara ya miqa mata jidda, baba jinmai ko sai yaba kyan da fatuha tayi take tare da yima su mom sai da safe fatuha kuma ta ja jidda zuwa bedroom.



*Taku har kullun mai qaunar Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


*๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*fan's ana mugun tare dinnan sosai*๐Ÿค๐Ÿฝ

39_40

Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt tasa mata.. riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta. Aiko tuni jidda tafito tayi kyau masha Allah. toilet ta koma ta dauro alwala kasan cewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallan gashin ta a mirror tana washe baki, jidda ce ta ce "Anuty gashin kine haka.. jiyowa fatuha tayi washe da baki tace "kema kin gani ko. Ai Allah daga yau na gama yawo da dankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa ba. "gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.. Jidda ta ida zancan tare da washe hakura.. Murmushi Faruwa tayi tare da maida dakwallin ta janyo hijabinta dana jidda suka wuce wajan malam


Sosai suke karatun. Damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya mata jiya ta juye mai shi.. Shikansa yana yabawa da qoqarinta.. qara musu yayi. Dan haka basu suka shiga gida ba sai 6:00pm


Sadiq dake tsaye gaban dress mirror yana gyara sumar shi a hankali ya ji anbude kofar dakinsa... Aiko cikin zafi rai ya juyo a tunanin fatuha ce ta zo mai da wani saban rai ni sai idanuwan shi ya gane mai majid...๐Ÿ˜€
bata fuska yayi tare da juya mai baya.. smile majid yayi ya qaraso with full confidence nashi , "big man fushi kake dani ko.
kauda kai sadiq yayi ya nufi wajan drowe yana ciro kayan shi.
murmushi majid yayi tare da zama saman sofa tsaf.
sadiq ya gama shiryawa fuskar shi daure ya dau phone inshi da ke bedside drowe. ze fita majid ya riqe mashi hannu tare da shagwabe fuska sorry bros, juyawa sadiq yayi ya wurga mai harara "leave me alone tare da fisge hannu shi ze murda handle kofar kenan majid yace, "haba sadiq. am sorry nine fa majid. juyawa sadiq yayi ya kalle shi , ya qara bala mai harara "kasan da haka shine ka manta dani ko. "sorry kasan bana zama sosai shiyasa amma ai na kusa dawowa nan da aiki. Kaga dawo ka zauna muyi magana.
Jin hakan yasa sadeeq sakin handle din ya dawo ya zauna , "baby meya samu qafar ka naga kamar kana dingishi
jan tsaki sadiq yayi ya ce "tsautsayi ne kawai.. "eyya sorry , " Tashi muje parlour na gaji da zama a bedroom, "OK.. Majid yace
parlour suka koma suka dasa sabuwar hira basu suka daina hira ba sai magrib.. dauro alwala sukayi tare da wuce wa masallaci


"Anuty.
"na'am... "dan Allah ki koyamin qarin dazu ban iya ba sosai, "to shikenan nima zaki koya min na boko ko. "eh zan koya maki mana Anuty. "To bari mu fara yin sallah
Tashi sukayi tare da dauro alwala suka gabatar da sallah bayan sun idar fatuha ta qara biyawa jidda karatun sannan jidda ta fara koyawa fatuha ABCD karku so ku ga... kwamatsala da kyar da kyar ta dan iya shima ba sosai ba amma tasa ma ranta sai ta iya ko dan ta rinqa jin abinda sangami ke cewa wani locaki

Bayan sun dawo masallaci majid ya fada two star "wash am tied...
Guntun tsaki sadiq yace "kai dai Ka bani daga zuwa masallaci har ka gaji sai ka ce ba namiji ba mtss.. fruit ya curo a fridge ya fara ci majid ya zuro hannu suna ci suna hira, "ni fa kaga wallahi na gaji da wannan gwaranci aura zan zo nayi wallahi..
smile sadiq yayi ya ce "aiya kamata kam,

"aikaima ya kamata kayi wani auran sadiq.. Duba da yau kusan shekara kausar 5 da rasuwa. sadiq ya kamata kayi aure haka ko saboda angel.. bata fuska sadiq yayi yace, "majid bana tunanin zanyi wani abu wai shi aure yanxu. tunda na rasa kausar na rasa wani bari na rayuwata. majid kafin a samu mata kamar kausar sai antona.. kausar tatara komai dana ke so agun mace. bana tunanin akwai wata ya'mace da zata iya maida gurbinta... ya ida zancan hawaye masu zafi na zubomai,
kallan tausayi majid ya mai da cewa. "sorry baby. na famama inda kema ciwo ko. girgiza kai yayi tare da goge hawayan shi da bayan hannu yayi smile yace .. "majid baka famamin komai ba. indai tunanin kausar ne ba yau na fara ba. yau kusan 5 year da ita nake kwana da ita nake tashi majid , murmusawa majid yayi tare da qoqarin canza topic dan a duniya ba abinda ya tsana irin damuwar sadiq haka shima sadiq ba abinda ya tsana irin damuwar majid , kallan ball suka shiga yi tare da yin musu dama sun sama ba yau suka fara ba damma yanzu sun girma ne. dada ne har kuka sai Sadiq ya sa majid cikin nishadi suke kallo


"Kinga zo muje mu ci abinci muyi sallah na maki wanka kafin baban ki ya biyo mu. washe baki jidda tayi parlour suka koma dining area suka wuce fatuha ta fara saving nasu tuwo shinkafa ce miyar taushe taji Alayahu da kaji cikin nutsuwa suke ci a plate daya...

bayan sun kammala fatuha ta kwashe kwanikan ta kai kitchen jidda kuma ta haura upstairs dan tayi missing daddy tun da ta dawo daga school bata qara ganin shi ba. bata iya jira har sai an mata wani wanka. a hankali ta murda handle din kofar a zaune ta gansu a parlour rugawa tayi jikin majid tana cewa. " small daddy I miss u.. smile majid yayi. "miss u angel how are u, "fine uncle , sadiq ne ya murmusa yace "ni fa yanzu fushi nake da angel tunda tayi new Anuty take mantawa da daddy. bata fuska tayi kamar zatayi kuka "uncle bafa haka bane new Anuty na da kirki kuma tana min wasa kuma kasan wani abu daddy sai ta zamo daga jikin majid taje ga Sadeeq tahau yimai rad'a akunne. jin abinda take gayamai yasashi yin wani killing smile... {Wanda koni Salma ban san me jidda take cemai ba,}
"Na zo maki da ice cream amman tunda dadynki kawai kika fadamawa bana baki ice cream din.
Jin abinda majid yace shiyasata tsalle tana kuka sai ya bata ganin da gaske kukan ta ke sanyi na gaske shiyasa shimata ta bari se ze tafi ya dauko mata.. washe hakori tayi tace "thank u small daddy tare da yimai pack tanamaici gaba da cewa.. Aunty bata San na guduba dan wanka zata min fa๐Ÿ˜€.. murmushi majid yayi ya ce "to diyar Anuty kice ina gaida Anuty.
kallan shi sadiq yayi a zuciyar shi yace da kasan wacece fatuha da ko hanya daya baza ka so ta hada ku ba balle kuma wata gaisuwa tabe baki yayi tare da jan tsaki ciki ciki

Tana fitowa daga kitchen ta fara neman jidda ba ita ba alamar ta upstairs ta haura saboda tasan bata wuce part din sadiq tana last stairs kenan sai ga jidda ta fito daga part din washe da baki murmushi fatuha tayi tace.. "shine baki jira na maki wanka ba sokike daddy yamin fada ne... girgiza kai jidda tayi fatuha ta dauke ta direct bathroom ta dire ta ta fara yi mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito ta aje ta saman bed ta janyo lotion da night dress din jidda sai da ta shafe ta dashi. sannan ta zura mata kaya


"Big man bari na zo na wuce dare nayi.
"tun yanzu dare be wani yi ba na dauka fa kwana ka zo min wallahi kaga mun dade bamu hadu ba. murmushi majid yayi.. yace "next time zankwana.. "To shikenan.
har bakin mota ya raka shi ya Ciro ice cream din jidda ya bashi "gashi aba angel nasan Anuty ta maqale ta shiyasa bata fito ba ka shafa min kanta , "ok ka gaishe min da Umma da ammi "to zasu ji Alhaji da baba fa me suka tsarema da baza ka ce a gaishe su ba... dariya sadiq yayi tare da kai mai duka "wallahi majid ka rainani tunda na ce a gaida mutan gida ai suma sun shiga, harara majid ya bala mai ba "waninan ammi da Umma kawai ka ce kuma da yaushe ma ka girmeni har kake fadi na raina ka , harara sadiq ya qara wurga mai aidai na baka 4 hours ko qarya nayi. Ya qarashe tare da hade ran wasa. dariya majid ya fashe da ita tare da ba mota wuta.
Sai da safe ace ma mom na zo tana part din abba. "Toh sadiq yace mai da daga mai hannu har sai da motar shi ta fita sannan sadiq ya koma cikin gidan ,

dauke da jidda fatuha ta fito. Aiko nan take sukaci karo da sadiq a parlour...
B'allama fatuha harara yayi da kauda kai...
Itako tayi kamar bata gani ba. yana gaba suna bayan shi jidda na zuba surutu suna shiga part

Please Login or Register in order to submit comment