Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama


Har yayi nisa da gida ya tuna yayi mantuwa ribas ya ci ya dawo ko da yayi sallama bai ji motsin kausar ba daki ya nufa a tunanin shi bacci ya dauke ta musanman yadda ya lura cikin mai sata baรงci ne lulufe take cikin blanket sai kyarma take ya shigo dakin har zai fita ya dawo yaye blanket din mai zai gani kausar ce a sume sai hancin ta da jini ke biyowa sosai hankalin shi ya tashi daukarta yayi kamar baby duk ya rode ya sakata cikin mota kai tsaye asibitin wajan aikin shi suka wuce wato na sojoji ya isa nurses suka fito suka basu taimkwan gagawa shiku sai zarya yake doctors sun dukufa akanta domin ceto ranta mom ya Kira yana kuka kamar qaramin yaro yana fada Mata yadda akayi aiko mom ta shirya ita da baba jinmai suka taho asibitin sosai mom ke kwantar mai da hankali kausar wajan laida biyar tasha na jini biyu na sadiq biyu na jawad daya na majid sosai hankalin su ya tashi doctor ne ya fito daga dakin yana goge zufar fuskar shi da sauri suka karasa doctor lafiya dai ko lafiya lau munshawo kanta da kyar yanzu tana samun Hutu ne shikenan sadiq ya Kira da yayi zuru zuru harda yar rama yini daya yayi ya ce yace ka same ni a office to yakub cikin sauri ya bishi suna shiga yakub ya cire glass nashi gaskiya sadiq ka bani mamaki ya za'ayi ka yadda matar ka ta samu ciki bayan kasan tana da *amenia* why sadiq what zunbur sadiq ya mike yakub ban gane mai kake fadi ba Ina tunanin kunnena bai ji dai2 oh karka raina min hankali mana kana nufin bakasan tana da shiba ko mai wasu hawaye ne masu zafi zuka zubo mai why kausar me yasa zakin min haka kuka yake sosai har saida yakub ya tausaya mashi ya rugume shi yana shafa mai baya alamar lalashi ahankali yake magana cikin sarkewa harshe yakub I don't no kausar na da *anemia* ban sani ba me yasa daza boye min why yakub she no I love her Allah nafi Santa akan baby serious yakub please ka cire Mata cikin please bana iya rayuwa bada kausar ya Kara rushewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sosai yakub ke lalashin shi har ya samu ya samu natsuwa ya bashi fresh milk mai sanyi yasha ya rage kuna da zuciyar shi ke kamai ahankali ya fita daga office din ya shige dakin da akwantar da kausar tana kwance fuskar nan tata tayi fayau alamar ciwo ya cita sosai kallo daya yamata idanunin shi suka ciciko da kwalla jikin Mom ya fada cikin dashashiyar murya ya Fara ba mom labarin abin da ya faru sosai mom ta girgisa itama har da yar kwalata mom me yasa kausar zatamin haka mom ya Kara rushewa da wani saban kuka kamar karamin yaro



*ALHERI HAUSA NOVEL*๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š. *thanks for your comments love u all fan's*



*Taku har kullu Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Blood sister jeeda*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA WRITER'S FORUM*๐Ÿ„


*๐Ÿ‘๐ŸผGodiya ta musanman ga rahama nalele marubuciyar YAR BIRNI KO YAR KAUYE ๐Ÿ˜data bani qwaringwiwa wajan rabuta wanan novel din Allah ya bar zuminci* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ




11_12

Turo kofar da akayi ne yasa.. "Sadiq tsagaita kukan da yake... "Abba ne tsaye bakin kofa cikin sasafar ya qarasa wajan abba ya qara sakin wani aban kukan.." "Abbane ya rugume shi alamar lalashi ."shhh!! Sorry son be are strong man sai ka ce ba soja insha Allah she will be fine... "Jawad ka kaishi gida ya samu hutu kaji.." Daddy.. Shhhh.. Ya isa kaji jawad ka kai shi gida kawai..


Haka ko akayi jawad ne ke driving nasu cikin motar ba wanda yayi ma wani magana sadiq idanun shi a lumshe har suka iso gida bala mai gadi ne ya bude masu gate tare da jajanta masu parking space yayi parking.. suka fito a tare..bedroom din sadiq suka shiga ya kwanta saman bed tare da lumshi idanun shi zuciyar na wani irin suya take mai musanman inya tuna da halin da abin kaunasa ke ciki... Jawad ne ya katse mai tunani ta hanyar shafa sumar kansa.... "Ahankali ya ware sexy eye's ball's din shi kan jawad riqe yake da glass cup da fresh milk a ciki.. " Sadiq please ka daure ka ci wani abu nasan tun breakfast din safe baka qara sa komai a cikin ka ba" please ka gama ka sha magani headachen nasan yana damun ka... "Numfashi ya ja yace...insha Allah wife naka zata samu sauki kaji baby.. " kamar Ba zai sha fresh milk din ba amma saboda be ga wasa a idan yayan nashi ba ya amsa... "Sha biyu zuwa uku yayi ya aje saman stool ya qara lumshe idan shi maganin headache jawad ya badu tare da ruwa ya bashi ya sha.. "Sannan ya lulube shi da blanket ya fita...


Bacci ne mai nauyi ne ya dauke shi.. " bashi ya tashi ba sai yama liqis wanka yayi yasa Jean's n t-shirt bleu mai dogan hannu sannan yayi sallah la'asar... "ba qaramin kyau yayi ba sai dai fuskannan fayau saboda kukan da yaci sannan cike take da alamar damuwa car key nashi da ke saman stool ya dauka ya fita.."kaitsaye asibiti ya wuce yana parking motar shi a harabar asibitin aka fara kiraye kirayan sallah magrib.. Masallaci ya shiga yayi sallah zai futo kenan suka hadu da abba kausar.. " hakuri yake ta bashi ankan cewa bai San kausar bafa fada mai larurata ba..'ah ba komai abba... "Toh shikenan Allah ya bata lafiya..." Ameen.!! Kai tsaye dakin da a kwantar da kausar ya shiga mom na saman daduma tana lazimi.. Gaisheta yayi ta amsa.. " sosai taji dadin ganin sadiq haka ba kamar dazu Ba. Kausar ya kalla Wanda ke kwance saman gado kamar gawa oxygen ne ahanci ta sai jini da ake qara mata idanuwan sane suka ciciko da kwalla tabas yasan ya rasa kausar ya rasa mata.. Tagari why me yasa zaki mana haka kausar hawayan da ke Neman zubumai ya hadiye... "Mom ce ta katse mai tunani da cewa.. Baby ni zan wuce ka kulla da ita anjima matar jawad shukura zata kawo maku dinner .." Son please ka rage damu wannan tare da shafa mai gefe fuska kamar jira ya ke hawaye suka fara mai zarya..shhh!! Ya isa mana inkana kuka ita kuma me zatayi sokake ka tada ma kausar hankaline baby.. Girgiza kai yayi tare da daura hannushi kan na mom.. "Toh ko Kai fa inkasan kuka zaka cigaba dayi to sai mu koma gida Bilkisu ta kwana da ita.. "Um mom bazan sake kuka ba wasu sabin hawaye ne suka zuba mashi..." Mom nara yanda zanyi control kai nane mom nasan sarai na rasa my wife saboda wannan cikin... Ya ja numfashi mom kausar bata iya rainun cikin nan mom ki duba ki gani ita kanta duk month tana buqatar jini bale kuma yanzu data ke tare da cikin ya ida zancen hawaye na zubu mai... Mom ce ta share kwalla idan ta.." son ya isa haka kayi Mata addu'a insha Allah lafiya lau zata raini cikin ta har ta haihu kaji" kai ya gyada' mata.."pack ta mai agoshi sannan tamai sai da safe


Gashin kanta ya shafa ahankali tare da kai mata pack.. "Allah ya baki lafiya mai wife sannan ya daura kanshi saman gadan.. ahankali take bude eye's balls din ta.. " tasauke su kan sadiq da idanun shi ke lumshe kamar meyin bacci" A hankali takai hannu ta saman sumar shi tanajin wani san mijin ta na qara narke mata a zuciya..hankali ya dago sexy eye's ball's din shi ya sauke a kan wife din shi .. Murmushi ta saki tana qoqarin tashi zaune.."no ki koma ki kwanta kiji my wife ya ida zancen yana shafa cheek nata.. "My wife me yasa kika boye min sick naki why? Idanun tane suka ciko da kwalla ta bude baki zatayi magana.." Shhhh ya hada bakin su waje daya yana Mata salan sa mai kashe Mata jiki..



Rayuwa haka ta cigaba da tafiya sosai kausar ke samun kulawa wajan sadiq inda suka bude babina soyayya.."soyayya suke sosai kamar su cinye juna su inda duk month sadiq sai ya kaita asibiti an qara Mata jini..

Misalin qarfe 3 na dare sadiq kwance kausar na manne aqirjin shi.. ahankali yasa hannu yana cire Mata hula da ke kanta Wanda bata bari ya cire mata..."wasu siraran hawaye ne suka zubo mai saboda kusan rabin gashin ta ya zube saboda wannan ciwon..."kuka ya sha sosai cikin daran sannan ya tashi yayi sallah ya nemamata samun sauqi wajan Allah .. Tabas yasan ya rasa kausar ya rasa wani Bari na rayuwarsa da irin wannan tunanin bacci ya dauke shi!!

Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau kausar cikin ta ya kai 9month..sadiq ne akwance yana bacci ya fara jin.. Wash sadiq zunbur ya tashi hankali tashe... Kai tsaye asibiti suka wuce nurses suka kawo masu taimakwan gagawa.. Gaba ki da'ya sadiq ya rude har da yar kwallan shi.."waya ya curo ya kira mom ya fada Mata cikin muryar kuka.. Zirga2 sadiq ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye.. "Majid ne ya dafa shi cool down sadiq tare da rugume shi alamar lalashi.." Doctor's ne kan kausar sosai suke aikin su dan suga ta haihu da kanta amma abin ya gagara.!!


Doctor yakub ne ya fitu yana goge sumar face nashi.. da sauri sadiq ya karasa wajan su da mom da majind..a tare suka jefa ma doctor yakub tanbaya.. Ya kausar da sauki..muna kan bakin qoqarin mu ga wannan paper *captain sadiq* kasa hannu kausar ta kasa haihuwa da kanta.. "Jikin shi narawa ya amshi paper yasa hannu aka shiga *tiyata* tun dare ake abu daya sai da safe suka fito daga mom har sadiq ba Wanda ya rintsa addu'a kawai suke.. Bayan ta haihu doctor ya sheda masu ta haifi baby girl murna wajan su mom ba'a magana da sadiq


Kwance take a daki ita kadai tasan radadin ta take ji wasu hawaye ne masu zafi suka zubu Mata tasa bayan hannu ta goge.. Gefe da baby take ta kalla jin an bude kofar ya sata da'go eye's ball din ta wani lalausan murmushi ta saki tana qoqarin tashi... "Ya qaraso my wife tare da kai Mata pack a goshi yana qoqarin maida hawayan shi.."Habibina cikin sanyin murya" Baby bin sadiq ya dauko ...Masha Allah baby mai kyau da ita habibina.. Na'am" ga amanar baby mun na baka please ka kula da ita..."shhh insha Allah tare zamu raini baby mu yana qoqari boye hawayan da ke maqale a idan shi .."um ta kai hannu ta shafa sajan shi mai laushi tace.. Wani suna zamu sama baby mu.. Lalausan murmushi yayi yace..Hauwa'u suna mom za'a riqa Mata laqabi da Jidda... Fada'da' murmushinta tayi tace Jidda ta shafa cheek din baby.. Hannu ta ya riqe ya sunbata.."tarine ya subuce mata jinine ya fara bi Mata ta hanci da baki da sauri sadiq ya mike zai Kira doctor..hannu sa ta riqe tana girgiza tana motsa baki can yaji jikinta yayi sanyi......"Nooooo.. ya fadi kasa sumame



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„



15_16

Shirye shirye ake sosai kasan cewar yau ALHAJI Ibrahim zai dawo daga UK... Sosai mom ke gyara kanta kasan cewar mom irin matan nan wanda girman be hana su gyara kansu wajan miji..."abinci ne kala kala anyi domin abirge Alhaji yau kusan 2week baya nageria..


Daddy daddy please wake up daddy....saman ruwan cikin sadiq jidda ke tsale tana kiran suna shi..."oh no angel so kike daddy yayi ciwo ciki ah bakya ji ko.... Tsakulkuli ya ke mata tana dariya...."daddy stop please..ta ida zancan tana mai da numfashi... Tsakaitawa yayi da yimata tsakulkuli... Um my angel me ya tashe ki haka da wuri har kina so ki hana daddy bacci bayan kin san today is weekend ya ida zancan yana langwabe kai ala dole yima jidda shagwaba yake... ohni salma shi dai shagwababe ne ko da yake dan auta ne... Lol" um'um daddy grandpa ne fa zai dawo yau tana maganar tana wasa da maba'lin rigar sadiq na bacci... Inyee little princess of grandpa ya laka ce mata hanci..dady I miss grandpa.. "I now angel yau zakiga grandpa har ki gaji ko angel...yes daddy.."oya tashi muje na maki wanka na maki make up kifi hanna kyau ko...washe baki tayi.."good girl ya dauke ta suka wuce bathroom.....



Inna.. inna.. Na'am.."ohni fatuha wai yau she zaki girma ne Dan Allah mutun shekara goma shadaya amma mutun kullun girma yake yana cin qasa....yi hakuri inna wallahi zanina nake nema inna wanda baba jinmai ta siyo min abirni...ah yau antuno da baba jinmai kenan to zanin yana uwar daka... "Washe baki tayi.." eh inna Qur'an na matso ta zo kwarankwatsi inna...."ai zata zo insha Allah aikin san duk qarshan shekara ta ke zuwa..."amshi kwanan ki kaima baffa kinji .."to inna.. Baffa na zaune saman tabarma ta aje mai kwanan tare da gaishe shi washe da baki ya amsa.... "Fatuha yan'mata rufe fuskarta tayi ita ala dole kunyar baffa take ji ....."Qur'an baffa ni ba yan'mata ba ce su tanine yan'mata....." Hhhhh alalai diyar baffan ta ke ma ai yan'mata ce matso mu ci abincin tare nasan baki ci ba saboda baki iya cin abinci ke ka dai kuma inna nasan batayi Kala ci ba..toh baffa matsowa tayi tana cin abincin inna ta shigo washe da baki ..Kai dai Malam baka gajiya da shagwaba fatuha da girman ta amma har yanzu tare kuke kalaci baka bari muci tare....ah ke ma in zaki ci ki zo muci nasan kishi kike mun ware ki ke ka dai...murmushi inna tayi ta zauna suka cigaba da kalaci...


Misalin karfe 1:00pm fillet din su Alhaji ya sauka a hankali yake takowa ta matatatkal jirgin da kagan shi kaga babba mutun sanye yake da shada blue babba riga anmata aiki da dark blue zare sosai dikin ya haushi sosai.....sadiq ne jingi ne jikin motar shi Benz black qadan qadan ya duba agogo... Dago kai yayi yana kale kale can ya hango abba washe baki yayi ya qara sa da sauri ya rugume shi abba..."abba I miss u... "Miss u more son tare da shafa mai gefan fuskar shi... Bude mai moto yayi ya shige shima ya zagaya ya shige driver ya jasu....



Mom ce zaune a bedroom saman sofa tasha danqareran leshin ta green mai ratsin white flower anmata bubu da leshin mai kyau tasha dauri ture kaga tsiya gashin ta ya leqo sai kamshi ke tashi ba qaramin kyau tayi ba...dai dai parking space driver yayi parking.... Alhaji ya fito shida sadiq yaran sadiq sai qamewa suke tare da kwasar gaisuwa wajan Alhaji... Washe da baki suka shigo gidan cikin sallamar su..... Jidda da ke zaune a palour suna wasa da Jamal qanin hannan d'an Bilkisu....da gudu Jidda ta rugu wajan grandpa ta rungume shi ita da jamal daukar su yayi yana cewa.. Ah'ah my little grandchildren kun girma musanman angel.. Angel me daddy ke baki kin qara girma... Dariya tayi ta ce grandpa kullun daddy sai ya bani fresh milk da safe....good girl yanzu kin fara cin abinci kenan ..washe baki tayi...mom ce ke taka downstairs ahankali washe ta baki.. Ahankali alhaji ya daga kai ya hadiya wani muyau yana binta da mayan kallan...ohni salma tsohuwar Zuma tatashi lol.. Katse mai tunani tayi ta hanyar cewa..." Abban sadiq sannu da zuwa... Yauwa ya hanya ..."Alhamdulallah ..."kun zo kun fara cika grandpa da surutu ko ....."washe baki su kayi su duka Anuty bilki ta ce...oya ku wuce kuyi wasa Hanna ce ta zunboro baki... Momi nafa girme su ni ai bana wasa... Toh yayi uwar mata ..."mom ta bushe da dariya tare da jan hannu alhaji suka wuce bedroom


Ita da kanta ta taimaka mai ya cire kayan shi ya shige wanka inda yake ta zuba Mata soyayyya ...after 1hour Alhaji ne ke sa kowa daga stairs shi da mom sanye yake da jalabiya milk ya fito sak bafulatani glass manne a fuskar shi dining area suka wuce lokacin kowa ya halara... Mom ta jaa ma abba kujera ya zauna itama ta zauna... Mom ta fara serving nasu lunch cuscus ne da miyar dankali taji kaji sosai aciki sai lafiyanyan sob'o mai sanyi ta zuba ma abba.."ahankali suke lunch inda sadiq ke feeding Jidda da Jamal....


Bayan sun gama kalaci fatuha ta kwashe kwani kan ta wanke... Ta wuce gidan su fatsima suka wuce rafi... Tafe suke suna tsoka dan har yanzu da suka fara irgandangi ba dai tsokanar su kayi ba .... Fatuha kalli wancan ba dan megari bane da kandala..."Qur'an shine tap aiko ya ja ma kanshi tona asiri taho mu qarasa.... Dan mai garine da kantala suna ta aika masha'a bayan bishiya...ohni asirin ku ya toni bilahilazi kamar a gaban mai gari inji fatuha.....bala cikin Sauri ya Fara maida zariyarar wandan shi yana zare ido kandala ta fara gyara Riga zata dau tulun ......Qur'an ba inda zaku mun Kama kwartaye...hehe ...."keeee!! Ni sa'an kine zanci uban kuma fa yana magana cikin borin kunya...hehe bilahillahi.. Bala ka raina mana wayau mun Kama ku kuna iskanci shine dan baka da kunya zaka zagemu toh Qur'an sai mun tona...dama ranar kandala na dau gyadar ta tamin raini wayau to zan je na fada malam abinda kike in kin fito talla... Kwala ta Fara matsewa tana ba ma fatuha hakuri shima bala haka har ya masu Alqawarin zai basu murtala sannan suka hakura ..suka tafi suna dariya


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*

*๐Ÿ‘๐ŸผGodiya ta musanman ga masoyaโค wannan novel din CAPTAIN SADIQ๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚ Ina jin dadin comment naku๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Allah bar zuminci*๐Ÿ˜˜




13_14


Innalillahi wa'innailaihi raju'un duk wani mai rai mamaci ne yau dai kausar ta rigamu zuwa gidan gaskiya..inda aka wuce da sadiq emergency dan be san inda kan shi ya ke Ba... dangi sunyi kuka sosai saboda kausar mutuni yar kirki ce


Yau kusan sati daya kenan da rasuwar kausar sadiq na asibiti sosai yake samun kulawa wajan su jawad da majid wanda be ma san suna yi ba... Jawad ne zaune dakin asibiti saman three star yana shan coffee... "Ahankali yake bade sexy eye's ball din shi..." Ahankali yake tuna duk abubuwan da suka faru wani irin kuka ya fashe da shi mai tsuma zuciya yana qoqarin tashi ya cire dirif din da ke makale a hannu shi.. Jawad ne ya taso ya rungume shi alamar lalashi kuka ya qara fashe wa da shi yana fisfis kamar zarare... "Bros I can't live wit out my wife please bros ka barni na bita ya qara fashewa da wani saban kukan...ganin abin nashi kamar ba kai daya ba ya sa jawad yayi ma daya daga cikin yaranshi da ke tsare kofa.. Kiran Dr yakub.. Dr yakub ne ya shigo shi da nurse tana dauke da tray alururi... Dr da jawad da kyar suka samu suka danne sadiq aka mai alura bacci..sai da yayi kusan 30 minutes yana sanbatu sannan bacci ya dauke shi..."Jawad ne ya ce" Dr Ina fatan dai sadiq ba brain nashi bane ya sami problem Ba ya ida zancan yana matsar kwalla.."karka damu kawai mutuwar ta firgi tashi ne amma insha Allah ze sami sauki daya tashi komai zeyi normal Allah bashi lafiya.. Ameen Dr.




2weeks letter

Sosai Jidda ke samun kulawa wajan mom da baba jinmai da mai aikin ta Mary..." sadiq ko duk wata walwala ya daina idan kaga yana smile to Jidda na hannu shi inda ya daura mata san duniyanan wani bangare na zuciyar shi kuwa ji yake Nigeria ma ta isheshi saboda ya rasa abin kaunar sa inda ya yanke shawawar barin kasar be samu wata matsala Ba wajan aikin shi ya dau Hutu sheraka daya...mom ce zaune a palou sadiq na riqe da jidda Wanda bacci ya dauke ta acinyar shi...cikin sanyi murya kamar mai koyan magana da yanzu magana ma wuya take mai yace...mom Ina san nabi jawad londan inzai koma.."toh shikenan son..amma mom Ina San in zan koma na koma da Jidda saboda sai hankali na yafi kwanciya... Mom ce ta daka tsale ta dire tace...bata San zancan ba" ba inda ze je da ita ba yanda ya iya ya hakura wannan kenan


*Cigaban labari*


Ahankali ya dau jidda wanda ke bacci ya kaita bedroom ya kwantar da ita ya shiga wanka.." inda yake jin mutuwar kausar ta dawo mai sabuwa sai da ya zubar da kwalla sosai.... 30 minutes yayi wanka ya fito sanye ya ke da bathrobe.."Ahankali ya kai lips din shi goshin Jidda ya Mata pack.!! "ahankali ta ware manyan eye's ball din ta..."Daddy" oya tashi ayi wanka muje yawo wajan hajiya da Umma.. Baki ta washe.."ok daddy.daukarta yayi ya kaita bathroom ya wanke ta tas inda suna wanka suna wasan ruwa



Yanzu saboda Allah fatuha kin kyauta kenan..ince bana ce ki kyala Rabi'u ba eh.."yo inna ji nayi kwarankwatsi bana iya hakura.. Aikin kyauta tunda kin sa maitafasa tamin tanadi kinji dadi saiki zubar da ruwa a qasa kisha..baki ta turo gaba.. Gaskiya inna baki suna kwarankwatsi baffa yafi sona ta ida zancan tana matsar kwalla.. Fatu kenan kin taba ganin inda uwa ta haifi da tace bata so .. Kawai dai halin kine ban so fatuha ki daina tsokana.. baki ta washe .."yo ahe kina so na kwarankwatsi na daina tsokana amma bilahilazi duk Wanda ya shiga gona ta sai ya ci wuya Qur'an.. Sannan ta zuri takalman tace... Inna na tafi makarantar allo.. Toh Allah ya shirye ki.."ameen inna



Bayan sun fito daga bathroom ya shirya ta cikin gown maron mai d'an siririn hannu sai mai dugwan hannu a ciki ya ygara Mata gashin ta.. Masha Allah sosai Jidda tayi kyau kamar diyar larabawa.. Pack ya Mata a cheek ita ma ta mai..."oy je ki wajan grandma ganin zuwa... OK daddy ta ruga da gudu ta fita ya bita da kallo yana smile...shima shirywa yayi cikin jeans black and red T-shirt mai ratsin black me dugan hannu sannan ya maqala hannu shi agogo black sannan yasa takalman sa black ba qara min kyau yayi ba abin ka da farar fata dan hutu sajan nan nashi yayi liflif...ahankali yake sakowa daga downstairs mom a palou zaune Jidda na zuba Mata surutu..cikin natsowa ya gaishe ta ta amsa sannan yaja hannu Jidda suka fita mom ta masu a

Please Login or Register in order to submit comment