Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

washe ta qara gyara zanin ta hannuta ya ja suka zauna suna cin dumaman tuwon da inna ta aiko masu da shi suna gama ci bacci ya kwashe fatuha baffa ya ce ikwan Allah har kinyi bacci kenan ya tashi ya cigaba da aikin shi


Cikin natsuwa yake aikin shi a office din Masha Allah sanyi AC sai ratsawa yake sosai abokin shi majid ne ya shigo ah big man ashe ka shigo yap tun 8:00 hannu ya mika mai suka gaisa ya samu guri ya zauna big man ya mom and sweetheart lafiya lau yauma rigima tamin zata biyo ni taga uncle majid Allah sarki me yasa baka zo min da ita ba haba wallahi tana zuwa nan zata cikani da to much of surutu um kai dai ka sani mutun sai muskilan ci naji din inwannan surutun ya kawo ka to ka fita to ban fita tunda ba kaika kawo ni ba sadiq shuru yayi ya cigaba da aikin shi kiran sallah la'asar ne yasa suka fito su Kayi sallah suka koma bashi ya dawo gida ba sai 5:30 part nashi ya shige ya yayi wanka ya wuce bedroom din mom zaune take sama sofa tana karanta azikar yayi sallama ya Mata pack Jidda ce ta rugu ta bashi hug dady I miss u miss u more dear

After ya gama lunch ya shirya Jidda da kanshi ya ja hannu ta suka je parking space yaran shi har sun taso ya daga masu hannu alama su ka dai zasu kaitsaye gidan Anuty bilki ya nufa



Dai dai wani ma daidaicin gida su kayi parking mai gadi ya wangale masu gate Masha Allah gidan ya hadu sosai plat ne mai kyau su hannan na filin gida suna wasa ganin uncle sadiq ya sasu rugawa aguje suna mai oyoyo ya chabe su yana masu wasa tare suka karasa palour Maman hannan na ganin shi ta washe baki ta qwalawa talatu kira ta kawo mai abin motsa baki dangin su fruit da sauran su har kasa talatu ta duka ta gaishe shi ah baby yau kai na a gidan nawa hala mom ce tace ka zo ah yayi smile oh kina nufi ban zuminci ko kamar hakan dai a'a aunty ke ma kin san bana zaman a naija sosai but now na dawo Nigeria zanrinqa zuwa har saiki gaji dani toh shikenan Allah yas da gaske kake haba anuty billy ya ida yana shagwabe fuska ohni baby wai yaushe zaka daina shagwaba duba fa har da diyar ka budurwa dariya ya fashe da ita ni dai sister kin samin ido wallahi sannan ya kora lemo toh naji na daina um wai ina mai gidan ah bayanan yana dubai ok sai end of is week zai dawo Allah ya maido shi lafiya ameen hira sukai sosai da yar 'uwarsa Kira kirayan sallah magrib ne yasa suka tashi sadiq ya wuce masalaci


Misali karfe 5:30 baffa ya gama komai da yake a gona fatuha kwance kamar meyin bacci dare saboda yasan halin ta in ta kwanta bacci bata San a tashe ta yasasa daukar ta har suka iso gida inna na ganin su ta washe baki tare dayi malam sannu da zuwa tare karbar fatuha da ke sharar bacci baffa daura alwala yayi ya tafi masalaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i lokaci fatuha ta tashi tana cin abinci hira suka dan taba sama sama sannan suka wuce ma kwantan su Inda fatuha ta matsu gobe tayi dan ta aikata abinda ke ran ta


Bayan isha'i sadiq ya dawo yayi salama da sister nashi sannan ya raba ma su hannan tsarabar su karku so kuga murna wajan su bayan sun fito haka ya biya da Jidda wajan shan ice cream ya mata siyaya sosai sannan suka dawo tun akan hanya ma bacci ya dauke jidda dan haka tana kwance a kafadar shi cikin sallama ya shigo mom na palour tana kallo ita da baba jinmai baba jinmai ta tashi washe da baki tare da amsar jidda shi kuma ya wuce dakin shi yasa ice creams din a firijin


Baba jinmai tana zuwa daki tayi ma jidda wanka ta samata night dress nata blue rigar dai dai gwiwa shima yana zuwa daki wanka yayi saboda ya gaji sosai ko da ya fito mom har ta shinfide jidda saman bed kayan bacci shi yasa tare da jawo laptop din shi yana shan coffee ya dade yana aiki sannan bacci ya dauke shi

Kira kiran sallah asuba ne ya tada fatuha baki ta washe kai narantsa da Allah jiya da kyar bacci ya suran yadda na matsu yau tayi wallahi talihi yau Rabi'u sai ya gane kuran shi qur'an ciki sauri tatashi tayi sallah


Yau dai ba laifi fatuha ta taya inna aiki sosai ba dan komai ba sai Dan tabarta ta fita saida suka gama komai ta gyara zaman zanin ta wadda kullun jiya na leda na habar zanin san ta ce inna zani gidan su fatsima to fatuha karki dade to inna ta fita da gudu gidan su fatsima ta shige inna fatsima na tsakar gida tana wanke wanke gaisheta tayi ta amsa fatuha ya inna inna lahiya lau ki ce ina gaishe inkin koma gida to za ta ji inna ina fatsima tana uwar daka to fatsima da ke shara bacci saman tabarma fatuha ta daka mata bugu ke tashi firgigit ta tashi kai fatuha ke banza tashi muje oh na tuna fa Qur'an ban san sanda bacci ya sure ni ba dankwalinta ta daura suka fita suna tafe suna tsoka dai dai wata gona suka ci birki Rabi'u ne gindin bishiyar mangwaro da alamar rake ya gama sha bacci ya sureshi saboda duk ga abin rake zube fatuha lafe jikin bishiyar bedi ita da fatsima suna lekan shi fatsima bilahillazi yayi bacci ta kwashe da dariya ai sai ya ci uba nai quli leda ta ciro daga habar zanin ta tufi Rabi'u cikin sanda ta bude ledar ta busa mai garin ta ruga da guda bayan bedi Rabi'u da ke bacci cikin bacci ya fara jin radadi da susa Ba arziki ya tashi yana sushe sushe yayi zuru zuru su fatuha da ke bayan bishi sai dariya suke sannan suka fito daga nesa ta tsaya Rabi'u ta kwalamai Kira ya waigo ai dama na fada ma kwarankwatsin ba'a buguna na hakura fatsima ta bushe dariya ka je gida mai tafasa tama magani kaji rabe ya dago idanun shi sunyi jaaa bala'iiiii Zan ci uban Ku dama kune kuka fesa min asosa narantse na sha magani sai na zo har gida na ci uban ku yo Zan can banza ko ka zo mukarama wani injin fatuha taja hannu fatsima suka bargun suna dariya shikuma Rabi'u na soshe soshe


*Taku har kullu Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*blood sister deeja*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(We the best)

7_8

Soshe soshe Rabi'u ke yasha wuya sosai idanunan sunyi jawur sai ihu yake ado ne zai wuce ya hango shi yana birgima ya qaraso subhalillah lahiya Rabi'u me ya faru wallahi fatuha yana ihu haka malam ado ya taimaka mai ya kai shi gida jikin nan nashi yayi jawur abunka da ba fulantanin mutun inna maitafasa tana gyaran tafasa taji sallamar Malam ado ta tsame hannu ta dake cikin tafasa ta yafa mayafi lahiya Malam ado me ya sami Rabi'u ni dai wallahi ban Sani ba amma da alama sosa ce toh fa kai ko Rabi'u mai ya hada ka da sosa garin ya haka ta faru ta ida zan can tare da riqe haba zani tana matse kwalla cikin murya wanda yasha wahala ya ce inna wallahi fatu ce da wannan iskancin kambuuu alqawalin Allah ban yadda yau sai naga uban ta jauro billahilazi ta idaa zancan tana yarfa hannu sama Malam ado ya ce a daiyi hakuri yarin ya ce yarin ya uban wa tana dafe qirji yarin da aure yau haihuwa badi shegiya yarin ya mai Kama da mayu wallahi Malam ado ban hakura shigo da shi namai magani na je na samu uban nata haka aka shigo da Rabi'u yayi zuru zuru aka shinfide shi bisa tabarma


Qur'an fatuha baki da mutunci yo ni ta wasa ce ai dama na fada maki saura malam dalha ai qule nake da shi kwarankwatsi hehe kai qawata ina san ki qur'an fatuha ta washe hakura nima haka billahilazi haka suka dawo gida ko da suka dawo gida fatsima gida ta wuce gidan su fatuha ta shigo gida da sallama yau zuciyar ta fes take da farin ciki inna da ke shara ta amsa sallama ta kauda kai yanzu Dan Allah fatuha kin kyauta kenan tunda safe da kika fita sai yanzu zaki dawo bata idaa rufe bakin ta ba mai tafasa tayi sallama cikin tsiwa inna ta amsa keeeee!! ta cakumo wuyan fatuha inna ta ce lahiya mai tafasa lahiya lahiya kenan bari uban ta jauro ya zo billahilazi yau ban yadda kuma duk abinda ya samu daa na ke ce ni zaki kashe ma daa har kin isa inna sai bata hakuri take amma taqi sakin fatuha wanda tayi wiki wiki da ido dan tasan tayi baki ta turo gaba ke ki cika ni tare da finci ke kanta daga ruqwan da maitafa ta Mata yo ba dan naki bane jiya ya bige ni ba kuma na Rama yau ta ida zancan ta murguda baki dan uban ki in zaki rama saiki samai a sosa inna ta ce fatuha ince jiya ban maki magana ba yo inna jinayi ban iya hakuri ta fada cikin tsiwa haka maitafasa ta gama zage zagen ta da kumfar baki ta tafi acewarta in Malam jauro ya dawo zata zo ta same shi


Daddy please muje shan ice cream sweetheart akwai a fridge muje na baki ok papa thank you ya lakace mata hanci that is my angel ta washe hakura part nashi ya kaita ya bata ice cream shi kuma ya shige gym room nashi ya dade yana gym sannan ya fito riqe da towel a hannu shi yana goge zufar fuskar shi gefen da Jidda take ya kalla har tayi bacci ahankali ya karasa saitin fuskarta yayi kala tausayi my angel I now you miss your mom why kausa me yasa kika tafi kika barni nida Jidda why kausar yana maganar kamar zautace yana share hawayan fuskarshi I miss u more my wife naso ace yanzu kina ganin angel my wife dake take Kama sosai naso ace tare zamu bata good caring ya kai lips din shi dai2 goshin Jidda ya mata pack



*Asalin labari*

Malam idi zaunan dan kauyan Kano ne wato rano su fulanine sosai Allah yayi ma malam idi rufin asiri dai2 gwargwado yana kiwon shanu sosai har ma da kaji gashi mutu min kirki shiyasa kowa ya sanshi a kauyan rano yana da mata tani sosai yake san tani Allah ya basu ya'ya 3 maza 2 mace 1 kabiru shine babba mai bimai Ibrahim sai rukayya


Zaune suke zaman lafiya cikin kauyan inda lokacin kabiru ke aji shida na secondary shi kuma Ibrahim aji 5 rukayya na aji 3 sosai suke karatun su saboda Malam idi mai san karatune


Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau garin rano zaman lafiya yayi qaran ci saboda barayi na zuwa su kwashe ma mutun dabobi sannan su kashe ka kai da iyalan ka Malam idi ne ya shigo gida cikin sallamar shi tani da ke wanke wanke ta amsa ince dai malam lafiya wallahi tani kauyan nan ba lafiya kabiru da ke uwar daka ya leko sukayi tsaitsaye can idi ya yanke shawarar saida dabobin shi su koma birni cikin garin Kano ba yadda idi ya iya haka ya saida shanun shi cikin ikwan Allah ya samu kudi mai yawa ya sama masu ma dai2 cikin gida a rijiyar zaki sannan yaba abokin shi Malam tanko kudi Wanda ke birni ya samai shago a kasuwa kwari a zuba komai ciki ya tataro iyalan shi suka dawo cikin garin kano lokacin Ibrahim ya gama secondary da yake Ibrahim yaro ne mai San karatu result nasu na fitowa ya sami admission a biyuke idan yake karanta business admin shikuma kabiru ya cigaba da kasuwan ci tare da mahaifin su sosai suke samun rufin asirin su

Kwanci tashi asarar mai rai yau Ibrahim ya gama karatun shi inda ya samu aikin kwangila sosai yake samun cigaba inda ya hadu da Hauwa'u auran soyayya ankai amarya rijiya zaki kusa da gidan kabiru inda yake zaune da matarshi Aisha tsakanin amarya da Ango soyayya sosai suke zubawa bayan wata biyu hauwa'u ta fara laulayi sosai take samun kullawa wajan mijin ta da surukar ta har ma da Aisha matar kabiru lokacin rukayya na FCE cikinta ya shiga watan haihuwa bata wani sha wahala ba sosai ta haihu dan ta mai kyau sosai ibrahim yayi murna sosai


Kwana bakwai da haihuwa akayi suna inda yaro yaci suna idiris wato suna Malam idi Ana mai lakabi da jawad sosai Rana suna anyi shagali bayan she kara biyu ta kara samun wani cikin lokaci Ibrahim yayi kudi sosai ya qara murjewa shi da Hauwa'u daka gansu kaga Hutu inda yake ba Hauwa'u kulawa sosai har ta haifi diyar ta lafiyaya rana suna taci Bilkisu sosai suke samun kulawa wajan iyayan su



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂


*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM 🐄*


9_10

Yau kusan shekara 2 da haihuwar bilkisu inda Alhaji ke sa ran Hauwa'u zata samu wani cikin amma shuru hakan yasa hankalin shi ya tashi musanma shi alhaji Ibrahim mutun ne mai san haihuwa ne haka suka cigaba da rayuwa cikin so da kauna inda alhaji Ibrahim yake faranta ran Hauwa'u amma cikin zuciyar shi nan maqale da San yaga ta qara haihuwa gidan su ko na rijiyar zaki sun rushe shi sun ginawa iyayan nasu katafarin gida mai kyau family house


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da san juna yau shekarar Hauwa'u 3 ba ciki kuma yau ne tatashi da wani irin zazabi da ciwo kai sosai hankali alhaji ya tashi haka ya kai ta asibiti akai mata yangwaje gwaje inda aka shedawa alhaji Hauwa'u na dauke da juna biyu zo kuga murna wajan alhaji baki har kunne ya daura cikin san duniya haka suma ya'ya nashi saboda basu da burin da ya wuce momin su ta haihu su shasuna locakin itama Anuty aisha nada ciki matar kabiru zo kuga yadda surukar su ke basu kulawa da nuna masu soyayya duniya ta zamar masu sabuwa yayin da mazan nasu ke rawar kafa kan cikin


Cikin su na da wata 7 akayi bikin rukayya da mijin ta aliyu ansha shagali anyi bidiri sosai ankai amarya kaduna GRA


Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau safiyar lahadi Hauwa'u tatashi da naquda kaitsaye asibiti suka wuce tahaifi tsalalen dan ta namiji kyakyawa murna wajan alhaji Ibrahim ba'a magana d Aisha ta zo barka da tsoho cikin ita da kabiru sun dade sosai asibtin ita ma aisha tunda safe take jin naquda tana daurewa kasan cewa ita haihuwar farko ne saboda sun dade basu haihu ba basu suka fara shirin barin asibitin ba sai dare a dai 2 bakin kofa ta fara naquda nurses suka aka batataimakwan gagawa Alhamdullilah itama ta Haifi san talelen Dan ta namiji zo kuga murna wajan su ba'a magana ba a salame su ba sai washe gari da fase Murna wajan family ba'a magana kamar ranar aka fara haihuwa 7 da haihuwa akayi gagari min suna a family house nasu inda dan Ibrahim yaci sunan kakan shi na wajan mahaifiyar shi wato *Abubakar sadiq* ana mai lakabi da baby shi kuma dan kabiru *Abdulmajid* sosai anyi bidiri anzubar da kudi yadda ya kamata bayan suna da kwana daya alhaji Ibrahim ya koma katafarin gidan shi daya tsara a sultan road sosai gida ya hadu inda duk wani abin morewa na rayuwa akwai agidan sosai kowa ya tayasu murna


Bayan she kara biyu sadiq yayi wayau sosai bashi da aboki sama da majid inda aka dau San duniya aka daura mai yaro kullun kara kyau yake kamar dan laraba kowa bama sha'awa yake amma sai Allah ya daura mai qiwuya kamar me gashi abu kadan bai isa yasasa dariya ba idan kaga yana dariya to yana hannu mom ko abba to wannan dariya har qyaqyatawa


20year letter wani kyakyanwan saurayi ne shida wani shima ba laifi ya hadu Ba kowa bane sai sadiq da majid awajan shakatawa sosai suke hira cikin jin dadi lokaci sun gama makaran ta har sun fara aiki su na sojoji sosai suke jin dadi wasu yan 'Mata ne nesa dasu sai Kallan su suke ba kowa ba ce sai kausar da kawayan ta suma sunzo san iska nana ce ta zuguro ta wow kawata kalli wayan can guys din sun hadu sosai kamar bazata juyo Ba tana juyowa sukayi ido hudu da sadiq takenan zuciyar ta fara har bawa wani irin sansa da kaunar sane suka kama zuciyar ta lokaci daya haka suka bar gun tana cike da kaunarsa da begen san shi shiku be ma San tanayi ba gida suka koma suma tun daga ranar kausar ta rasa na tsowarta duk wata hanya da tasan zata ga sadiq ita take bi ta sha wahala sosai kamin ta samu number shi tun tana kira be dauka har ya fara dauka suna dan taba shi



Haka rayuwa ta cigaba ta tafiya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin kausar da sadiq har ta kai ga iyayan su sosai iyayan sun ji dadin haka murna wajan kausar da sadiq ba'a magana musanma kausar da ita ta cusa kanta ga sadiq din shirye shirye biki ake sosai inda kowa ni gida ka leka abubuwa ake gudanarwa sosai ranar asabar aka daura auran *kausar Umar and sadiq Ibrahim* sosai kowa yayi murna ankai amarya gidan mijin ta dakee sultan road gida mai kyau sosai wanda daga gidan su ba nisa zuwa gidan su sadiq

Sosai sun raya wannan dare nasu da sunna manzan Allah (S A W) bayan komai ya wakana tayi kuka ranar har ta gaji saboda sadiq ba qaramin namiji bane dan ya dirje ta yadda ya kamata shida kanshi ya taimaka Mata tayi wanka sannan ya bata tayi na tsari ranar ko yasha shagwaba har ya gaji sosai yake Samata albarka kasan cewa ta zo mai da budircin ta har gidan shi sosai yake jin kaunar ta wani irin so suke ma juna su kamar su cinye juna


2years letter kausar ce asibiti ita da doctor kuka take mai sosai wallahi doctor bazan iya jurewa rashin haihuwa ba saboda ko ban haihufa ba wannan ciwon zai iya kashe ni kowani lokaci wannan cuta anemia inasan na haihu doctor bana naso sadiq yasan cewa Ina da wannan ciwo why kausar ya kamata ki sanar da mijin ki ko shine yaji haka zai tausaya maki be taba yadda ki zauna da wannan cikin saboda wannan cikin ajalin ki ne bawai nasan gaibu bane amma duk wani mai cutar anemia bai iya daukar ciki ki duba ki gani ke kanki duk month sai anmaki karin jini bale kuma yanzu har da baby a jikin ki wani irin kuka mai ban tausayi ta Saki gaskiya doctor bana iya zubar da cikina doctor bana iya zubar da jinin sadiq no I can't doctor turo kofar da akayi ne yasa doctor saurin miqewa kausar kuma tayi sauri fara goge hawayanta da bayan hannu ta tare girgizawa doctor kai alamar karya tona Mata asiri washe bakin karfin hali yayi congratulation sadiq matar ka na da juna biyu what ya zaro ido yana washe baki thank you god tare da kai ma kausar hot kiss a lips dinta yana shafa cikinta murna yake sosai inda doctor ke ta binsu da kallan tausayi sosai sadiq yayima doctor tukwici kaitsaye gidan mom suka wuce suna shiga da sallamar su kausar sai sunne kai take kafadar mom ya daura kan shi tare da lunshe ido jawad da ke zaune da yake ya zo da iyalan shi Nigeria kasan cewa shi ba kasa yake zaune ba yana zaune a London da matar shi da danshi jawahir Wanda ke da shekara3 yana zaune saman three star wai yaushe zaka girma ne baby hhh sai ranar da my wife ta haihu ka fara qirga month daga yau am going to be a father wani irin dadi ne ya lilibe mom ita ko kausar sai sunne kai take da jin kunyar abinda sadiq keyi da tausayin kanta kuma Bilkisu ce ta dungure mai kai ita lokacin hanan na da 6year kai dai baka da kunya wallahi ah ki kyale min da tome dan ya fadi min yauwa mom love u ya kaimata pack a cheeks mom ko ta zage sai nan take da kausar ita da Bilkisu da matar jawad sosai suke gwada mata soyayya hakan yasa ta shige toilet tayi kuka ta gaji tabas tasan tayi dace da dangin miji burinta bai wuce ta haihu ba tasan zasu riqe mata amanar babyta tare da shafa cikin ta tana share hawayanta da bayan hannu ta



Sosai take samun kulawa da so da kauna wajan sadiq inda yake gwada mata tsantsar soyayya har take jin dama karta mutu ta dangwama dashi a gidan duniya in ta tuna haka kuka take sha sosai sannan ta share hawayan ta cikin ta har ya kai wata 5 bata samun wata matsala ga kuma sadiq da ke tatalin ta kamar akwai


Sadiq ne yana facing dress mirror yana shiryawa cikin uniform nashi ba karamin kyau yayi ba kausar ta qaraso wajan shi tana sanye da night dress nata Fara dai2 gwiwa habibina na'am honey um tana gyara masa mabalin rigarshi gaskiya kayi kyau sosai ko eh mana ta shagwabe fuska Allah yasa kar yan'mata su kalle min kai hancin ta ya ja honey bame kalle miki miji kinji tam ya kai hannu ya shafa cikin ta ya lafiya babyna lafiya shi lau habibi smile ya saki mai sanyi yayi kissing goshin ta da cikin ta mika mai briefcase nashi yana fita da gudu ta shige toilet ta fara aman jini jini ta hancin ta jini ta bakin ta jiri take gani sosai har bata iya ganin gaban ta a dadafe ta rarafa ta hau gado tana nunfashi sama

Please Login or Register in order to submit comment