Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo lafiya



Zauna suke suna karatu fatuha tace... kwarankwatsi na gaji... yo hi haka akeyi ya tasamu gaba Ana abu daya.. Rabu da shi Qur'an nan kadai ya iya a karatun dariya suka kwashe da ita...Ashe Malam dalha ya ji dariyar ya fido so waje yana zare masu idanu... Dan buhun uban ku kun raina muta ne ko yau zaku ci uban kune... Sai da ya zane masu jikin radau sannan ya kyale sun inda suka rinqa jeramai Allah ya isa


Dai dai parking space yayi parking ya fitu riqe da hannu Jidda part din hajiya suka fara shiga... cikin sallama suka shiga"hajiya da ke zaune saman two star ta washe hakura.."Ah'ah yau kaine a gidan namu amma yau batan kai kayi maigida... Smile yayi ya langwabe kai .. Kai hajiya sokike ki ce bana zuminci ko" sannan ya samu waje ya sauna... "Dama yi kake ta ida zancan tare da qwalawa Asiya mai aikin ta ta kawo masu kayan motsa baki.."oh ashe da wannan yan neman ka zo tare da jan Jidda ta daura a cinya.. Kawo ta nayi ta maki bana.ah tap aiko da taci na jaki su duka suka kwashe da dariya.. Sun dade sosai suna hira sannan suka wuce part din umma cikin. "Sallama suka shiga Umma dake kitchen ta leko..ah'ah yau za'ayi ruwa da qanqara.... Jidda ta ruga da gudu ta rungume umma... Shagwabe fuskayayi tare da zama.." Umma har da ke cikin masu ce min bana zuminci.. Daga bayan shi ya ji ance.. Toh yin zuminci kakeyi ..juyawa yayi dallama majid harara.. Sanye ya ke da kayan ball green da alama daga ball yake ..Toh dan Hana ruwa gudu...hehe yana dariya ya hau upstairs...basma ce ta fitu qanwar majid baza ta wuce 15years ba ta gaishe da sadiq ya amsa ta ja hannu Jidda suka je dakin ta...sun dade sosai suna hira da Umman sannan ya biya majid... dakin majid ya shiga ya zauna saman sofa lokacin majid na wanka... Sanye da bathrobe ya fito.. Ashe ka biyo ni harara ya balla mai...ah bani na Kai zoman Ba rataya aka bani ka zo sai yi ma mutane borin kunya kake ya ida zancan yana dariyar shaqiyan ci..basu suka bar gidan Umma ba sai isha lokacin rai su Alhaji sun dawo da kauya


Fatuha da fatsima ne bakin rafi suna shan mangwaro..tap bilahillazi mangwaran ga zaqi garai.. sosaima Qur'an inji fatsima..kin San wani Abu na matsu baba jinmai ta zo mu ci dadi nifa tsarabar nake mawa.. ke dai bari fatuha ni wallahi duk cikin tsara wannan bakin abin yafin dad I ta washe baki wato(chocolate) lol

*Fan's kuyi hakuri da wannan page din har na gama typing ya goge sai dai wani na sake*

*Taku har kullu Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Blood sister deeja*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„


*yabo da jinjina๐Ÿ‘๐Ÿผ nake wa masoyaโค wannan littafin๐Ÿ“– gaskayi Ina jin dadi yadda kuke comment kan littafin nan๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ Allah ya bar soyayya*๐Ÿ˜˜


17_18

After lunch sadiq ya kwashi su jidda da hannan da Jamal zuwa shan ice cream sosai sunje yawo daga nan ya wuce dasu munjibir park..cikin jin dadi suke wasan su duk inda ka kalla a wajan yara ne da manya ke hutawa har ma turawa...resting chair ya samu ya zauna yana Kallan su Jidda yadda suke wasannin su cikin ni shadi... Daga nesa kuwa yan'mata sai yaba kyan shi suke da tsarin shi wasu mamaki su kar dai ace duk yaranan nashi ne iya kar hadu sadiq ya hadu wasu ma sai jan su hannan suke a jiki dan su samu damar yi ma sadiq magana ganin ba wasa a fuskar shi ya suka hakura basu suka bar munjibir park ba sai gab da magrib...


Dai dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu jidda..Jamal kuma na kafadar sa yaran shi yayi ma alamar su kwaso kayan da ke cikin motar su biyo shi da su haka ko akayi suka kwaso kayan ba komai bane sai kayan zaqi kala Kala da teddy da kayan wasa da ya saima su.... Anuty bilki na zaune a parlou saman three star Hannah ta rugo momi...yeee yan'matan Momi sun dawo bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo... Ah sister ke kadai ce a parlou Mom fa..."tana part din abba.."ok ina baba jinmai.. Tana kitchen.." ok hannan Kira min rabi'a ta amshi kayanan ta kai maku su dakin angel... "OK uncle rugawa tayi kitchen ta Kira rabi'a.. sanye take da farar riga mai dogwan hannu sai mini skirt da alama wannan kayan unform ne na yan'aiki....


Har qasa ta duqa ta gaishe shi tare da amsar kayan ta wuce da su bedroom din Jidda.."sister ni Zan wuce masallaci may be sanda zan dawo kin tafi...Ai kwana zanyi a gida..waro ido yayi ya ce.. Gidan naki fa ...hehe ka manta me gidan be nan sai gobe zan koma...oh haka har yanzu be dawo ba ..."eh sannan ya sa kai ya fi ce zuwa masallaci


Duk wata gona dake da bishiyar mangwaro sai da suka leqa suka tsunko nunanu daga nan suka biya wajan shafi'u mai rake suka amso bashi acewar duk sanda bala dan mai gari ya basu Murtala zasu miyashi..."Kai wallahi na gaji..."ai sai da nace maki mu zubar da ruwan tulun mu zuba mangwarayan mu cikin tulun in mun koma gida sai muce biyo mu akayi muka fasa dibar ruwan.." kwarankwatsi ke dai fatuha wayau gare ki amma kinsan wani Abu..a'a saikin fada qara muje da ruwan Qur'an saboda mun dade... Haka kuma fa ga wancan Malam dalha din sai sauri ya ke yaje ya Fara zalinci...ke dai bari ta qara gyara tsayuwar tulun ta..kinko iya qarin jiya fatuha..hehe yo tun yaushe na iya shi... Ke nifa Malam dalha ne bemun ba shiyasa bana bashi hada amma Qur'an na iya..."toh bilahillazi yau sai kin bashi saboda yau ban shirya ma bugu ba..


"Ko bishiyar nan da muka hau na maqale duwawuna sai zinga yake.. Fatuha ta kwashe da dariya.. Sai ki je gida kiyi gashi da ruwan dumi.. Inmaki na maitafasa..


Cikin sallama ta shigo gida inna ta amsa.. Inda Sabo ya kamata ta saba da wannan baqin hanlin na fatuha in ta je diban ruwa sai ta shekara bata dawo Ba


Inna Ina abinci na yana madafi kwanan samira ta jawo tuwo ne miya kuka yasha manshanu sai kamshi yake loma daya zuwa biyu fatsima tayi sallama cikin shirin ta na zuwa makarantar allo... Tare suka zauna suka ida cin tuwo zanta dau hijabin ta kenan inna ta leko daga uwar daka...


"Yanzu saboda Allah fatuha sai na ce kiyi wanka zakiyi kome raban ki da wanka tun shekaran jiya wuce kiyi wanka nan ku tai makarantar... Baki ta turo gaba tana dire dire gaskiya inna ki bari sai na dawo nayi... Aifa baki fita sai kinyi wanka..


Da kuka da komai fatuha tayi wanka sannan ta fito suka wuce makaranatar allo



Zaune suke a parlou suna hira cikin ni shadi su Jidda sai wasa suke..

Ku dai baku gajiya da wasa ko inji Anuty bilki... Ince dazu ba manjibir park kuka je da uncle ba duk wasan da kukayi be ishe Ku ba ko..."Oya ku wuce Ku shige bedroom kuyi bacci...su duka suka hada baki.. " sorry Momi tare da lagwabe kai duka parlou aka fashe da dariya...


"Yauwa gobe Ina so ku shirya da wuri inji Alhaji... zamu je family house meeting... "Toh Allah ya kai mu Alhaji inji mom..sun dade sosai suna hira a parlou sannan kowa ya tafi part nashi.. Inda su Jidda suka maqale ba su kwana ko Ina sai part din sadiq haka ko akayi da yake shi mutun ne mai san yara


Bangaran su alhaji ko sosai suke zuba soyayya tare da gwada wa juna su yadda sukayi kewa...sosai alhaji ke gwada ma Momi salan sa daga nan suka lula duniyar ma aurata


Zaune suke Malam dalha sai amsar hada yake da zabgegiyar bulala shi a hannu burin shi bai wuce ya ga su fatuha sun kasa ba ya wanke su da bulalar... Ke tashi ki bani taki hada cikin tsiwa fatuha ta tashi ta fara karanta wa Masha Allah cikin muryar mai sanyi da dadi ni kaina sai danayi mamaki wai dama fatuha ta iya karatu haka..Malam dalha ko sakin baki yayi har ta gama sannau ya koma ya zauna gwiwa sage...lol


Tsale tsale suke kamar ba dare ba cikin bedroom din sadiq...wasan pillow suke haka shima ya shiga cikin su wasan su ke cikin nishadi haka shima sadiq ya biye masu shima kamar qaramin yaro suna haka har bacci ya kwashe su

Ahankali yasa hannu ya bude wardrobe ya Ciro pic din shi da kausar na maqale a qirjin shi ahankali wasu hawaye mash zafi suka zubo mai yasa bayan hannu shi ya goge...bazai taba mance wannan ranar ba bayan sun gama wasan pillow shi da kausar suka je waje suna wasan ruwa anan su kayi pic din da camera...I miss u my wife.. yana rungume da pic din har bacci ya dauke shi..



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
(We are the best)


19_20

Duk yadda Malam dalha yaso ya daki su fatuha yau dai bai samu hanya ba har aka tashi..

Cikin sallama ta shigo gida... baffa na tsugunne yana shanya zogala... Washe da baki ta gaishe shi.."yar Albarka har kin dawo kenan.."Eh baffa na dawo...Masha Allah ana dai karatu dai ko...."Eh baffa.. Ai haka ake so...qoqarin cire hijabinta take tace... Baffa ina inna..ayo ai yanzu inna ki ta leqa gida su fatsima baki hadu da ita Ba..Eh" bata ida rufe bakin ta ba sai ga inna ta shigo...sun dade suna hira sama sama daga nan Inna ta shige madafi...


Bathrobes ne sanye a jikin su jidda suna ta tsale tsale a cikin dakin sadiq...ahankali shima ya fito daga toilet kamar Wanda ke jin tausayin kasa babu alamar walwala a tatare da shi kasan cewa yau ji yake mutuwar kausar ta dawo mai sabuwa....daddy morning..morning too my little children .. Fridge ya bude ya Ciro fresh milk ya zuba masu a cup's kowa ya sha ...Anuty bilkisu ce ta shigo part din cikin sallamarta ita rabi'a...sadiq na qoqarin ya shirya su Anuty Bilkisu ta shigo..."ah bros yaran nan sun hana ka hutawa ko ....nop ...oya Ku wuce muje baba jinmai na bedroom dina tana jiran ko...ok Momi suka fita a goje ....



Gyaran murya Anuty bilkisu tayi a hankali ta shafa gefen fuskar sadiq wanda ya lula cikin duniyar tunani.... A hankali ya dago sexy eye's ball's din shi ya ja numfashi... Sister tare da daura hannun shi saman nata....baby wai meke damun ka ne um gaba daya ka chanza yau a ganka da walwala gobe a ganka ba walwala.... hawayan da ke maqale a idanun shi yayi qoqarin mai dawa ya qaqaro murmushi Wanda iya karshi lips din shi...."sister ni fa ba abinda ke damu na... "Toh shikenan naji me yasa kake Kora masu kula da jidda why?.. Kafi so ka cigaba da kula da ita da kanka bayan kasan hakan ba zai yuyu ba saboda kana zuwa aiki.... "Ka gani baba jinmai ba yarin ya ba ce bata iya dawainiyar ku kai da Jidda sai dai na mom...um gyaran bedroom naka ka hana kowa yama sai ita me yasa baby ka chanza ta ida magana cikin rawar murya .....langwabe Kai yayi kamar qaramin yaro...sis ni fa ban chanza ba kawai dai yan' aikin ne basu ji sis shiyasa dana aje kudi sai su dauka baba jinmai ce d'ai bata daukar abinda ba'a bata ba....." Toh naji yanzu dai ga rabi'a tana parlou ka zata fara gyara ma daki daga yau kafin baba jinmai ta je kauye ta samoma good girl Wanda batada d'an hali..." B'ata fuska yayi ya ce sis kin..... Shhhh please kayi hakauri for some days baby.... toh sis pack ya mata a hannu ta mashi a goshi


Um kayi sauri ka shirya kasan yau akwai family meeting..I now ganinan fitowa ..OK


Rabi'a na takure saman one star cikin yin uniform din ta na yan aiki Wanda bata tunanin...sadiq ko giya wake yasha be yadda ta mai aiki saboda so biyu yana kamata zata mai sata... Anuty bilki ta qaraso washe da baki tace... Rabi'a daga yau zaki Fara aiki anan part din na wani dan lokaci please ki kula saboda na lura ba San aikin naki ya ke ba...to ta ce tana maida numfashi tare washe baki toh anuty.....Anuty bilki tasa kai ta fice


Fatuha!!! Fatuha!!..." Na'am inna...." zo nan wayan nan kayan wakika barmawa su raban ki da wanki har kin manta wai yaushe zaki fara tsaf ta ne fatuha eeeeh..."kin fara girma amma kullun rashin jin ki daduwa yake.... Yi maza ki wanke su tas ki shanya.... Kuka tasa har da birgima Qur'an inna ban iya wankin alqawalin Allah... Bakin ta inna ta bige ta ce.. wallahi in bakiyi wankin nan ba baki zuwa gada' tunda baki san kin girma ba kuma indai baba jinmai ta zo kina ji kina gani zan bayar da tsarabar data yi maki... Matse kwalla tayi ta ce.. Toh inna zanyi Qur'an...Ah karma kiyi ai ba dole.. Inna ta fara tatara kayan zata shige da su daki..jiki a sabule fatuha ta amshi kayan ta fara wankin


Tsaye yake gaban dressing mirror yana feshe jikin shi da turaran intense mai sanyayan kamshi sanye yake da t-shirt blue mai dogwan hannu sai jeans dark blue hannu shi maqale da agogo silver na azurfa farin glass din shi yasa ya fito kamar balarabe ba qaramin kyau yayi ba amma fuskar nan daure.... Qwanqwasa kofar dakin shi akayi ya juyo...yes come in rabi'a ce jiki ba kwari kallo daya ya Mata ya watsar cikin kakausar murya ya ce what.. Um kai nake jira ka fita na gyara bedroom din..wani irin kallo ya qara wurga mata ya matso gap da ita... Kinsan Allah Zan fita ne na Dawo wallahi na shigo daki na naga banga tsinke ba..huh you will see...fuuu ya ja ya fita ya barta sai b'ari take


Ahankaliya ya ke saukowa downstairs fuskarnan tamau dinning area ya wuce kowa ya halara za'a fara breakfast gaishe da iyayan nashi yayi tare da yi masu pack a goshi sannan ya samu waje ya zauna



Anuty bilki ce tayi serving din kowa suka fara cin abincin..mom na lura da sadiq dan ba wani cin abincin yake ba ga fuskar shi daure haka shima abban nashi yake lura.. Inda sabo ya kamata su saba da irin wannan halin nashi yau da fara'a gobe babu....a hankali ya ke cin abinci loma uku zuwa hudu ya miqe.. Son" yes mom... Har ka qoshi.. Eh na qoshi.. Amma kasan ba zamu shirya ba ko wannan ai ba abinci ka cin ba... Abba ya amshe zancan da cewa...shiyasa Jidda bata San cin abinci shiya ke koya mata hakan... Shagwabe fuska yayi.. Abba na sha fresh milk a daki da yawa shiya bana jin yunwa..um lalai dama fresh milk abinci ne inji Anuty bilki.. b'ata fuska ya kuma yi to ni Ina sha na ko shi... Langwabe Kai yayi ya ce.. Angel wai daddy ne ya koya maki rashin cin abinci...no daddy Kai da kake jin plate biyu...kowa na dining sai da yayi dariya har sadiq din Wanda tun tashin shi beyi dariya ba..."Ohni Jidda wato kare daddy ki zakiyi ko ..mom ta ida zancan tana lakace Mata hanci...


Ba ita ta gama wakin ba sai yama likis ta wanke su tas suka fita... inna washe da baki ta ce....ko ke fa diyar baffan ta..turo baki tayi gama tare zubar da ruwan daurayar a maguji... Oh fushi ake dani dan nace ayi tsaf ta sallamar baffa ce ta katse Mata zancan washe da baki ya shigo hade da sallama




Leda dake hannu baffa fatuha ta amsa..ah yar albarka yau wanki akayi kenan... inna ta amshe zancan da cewa kasan ko faman dana sha da ita sannan tayi wanki...ki ce min dai matsa mata kikayi...ai dama Kai baka ganin laifin ta...."Um fatuha dama Ledanan tsarabar yallo ce na makin ..washe hakura tayi tace.. Toh baffa na gode.. Yauwa yar albarka ..inna ta shige qurya ta kwasu ma baffa abincin shi


Cikin jin dadi ta gama wanke yallon da zubo masu inna na su sannan ta dau nata dana fatsima ta fice


After sun gama breakfast kaitsaye family house suka wuce

karku so kuga soyayya dangi ba tsangwama ba tsana sai tsantsan soyayya wanda uwar mazajan su ke gwada masu ba tare data banbanta wani ba


Wani kata farin parlou ne Wanda ya amsa suna shi yasha red carpet mai laushi sai manyan kujeru red n black sosai tsarin parlou ya hadu..Alhaji kabiru ne ya Fara magana cikin muryar shi ta manya da natsuwa yana fadin irin kadarurin da suka samu a kasuwan cin su inda baban nasu ya yanke hukunci za'a raba kudin kashi biyar..kashi 5 nasu kashi biyar na taimakwan Alumma ... Kashi 2 za'a kai gidan marayu kashi 1 asibiti kashi 2 taimaka mamara karfi sosai sunji dadin yadda baban nasu ya tsara abin bayan sun gama tattaunawa akayi addu'a aka tashi kowa ya koma harkar gaban shi


Big man wai lafiya yau sai wani cin magani kake inji majid ya ce..."Alalai ma to wazan ci ma magani kai wallahi ka bani sai shege surutu ya ida zancan ya furzar da iskar bakin shi... Naje nayi surutun in fitsari arhane wani yayi mu gani wani saboda tsabar rashin yin magana shi bakin shi wari ya ke ya ida magana yana dariya ..."oh dani kake ko da gudu majid ya ruga part din ammi sadiq ya bishi...ammi da ke hira da surukanta...
majid ya zo ya boye bayan ta...." Lafiya kai kuma wallahi hajiya ... bai ida zancan ba sadiq ya shigo fuska daure.. Ayo ai sai ka ce min wannan me bakin ran ka tsokano kowa na dakin sai da ya murmusa ... langwabe Kai yayi ya ce..ammi yanzu nine mai bakin rai kin san me yamin kuwa....Alhaji yace" rabu da su aikai d'a wuri nane kaji... Majid ko gwalo ya mai be San ammi ta ganshi ba..to ja'iri Ashe Kai ke Jan shi tashi ka ban guri dariya kowa na parlou yayi... Sosai jin dadi suke family inda suke hira cikin ni shadi



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*ร‰diting Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„

*this page is for you my fan's*

23_24

Tashi tayi daga jikin inna tana zunburo baki gaba, Inna tace "Yar nema ba'a isa ayi maki magana bane ko me?" Haba ladingo wai me yasa kike so ki rinka takura wa yarin yannan ne? Baba jinmai ce tasa baki tace, "Ah kuyi hakuri dai. Indai jiki nane ai ta sauka ko? Inna ta murmusa batace komai ba.


Duk wata tsaraba data kawo haka ta bajewa fatuha kayan zaqi fatuha ko baki har kunne dan dadi saboda har da bakar alawa, wato (chocolate) haka shima dan uwan nata da matar sa ta basu nasu tsarabar sosai sunji dadi musanman ladingo wanda take ganin baba jinmai ta dauke ta tamkar ciki daya suka fito, so da yawa tana fifitata kan jauro din ma saboda karamci irin na baba jinmai da sani darajar Dan adam, sosai suka ji dadin wannan tsarabar.


A guge fatuha ta qaraso gidan su fatsima kawo mata nata tsarabar saboda dama ta mata alqawari duk sanda baba jinmai ta zo, to zata kawo mata bakar alawa"(chocolate) .



Washe da baki ta qarasa..tace "Fatsima! Fatsima!ohni fatuha lafiya nagan ki haka? ko yauma tsokana kukayi inji gwagon fatsima" washe baki tayi ta ce "Wallahi gwogo baba jinmai ce ta zo yau shine na kawo wa fatsima tsarabar ta."Ayya ki ce min mutan birni sun zo, Aiko fatsima na kewaye ki jira ta tafito, bata ida rufe bakin ta ba fatsima ta fito washe da baki." Tace "Fatuha, na'am tare da qarasawa wajan ta" ke baba jinmai fa ta zo Qur'an... Dan girman Allah? washe baki ta kuma yi ta ce ."Tayi tsarabar baka alawa " Eh Qur'an gama taki nan na kawo maki, Ah kai amma naji dadi ,haka suka shige akurkin dakin fatsima suna ta hira tare da sharan ce muta ne' inna da ke tsakar gida sai cewa ta ke Allah ya shirye su...



A gajiye ya dawo gida briefcase din shi da ke hannu yaran shi *ola* ya amsa" cikin sallama ya shigo falon, Mom ne zaune a parlou tana kallo angel na kusa da ita tana bacci, A hankali ya qaraso yayi hug din mom ta baya... Yace "Wash mom am tied." Juyowa tayi suna facing din juna Ta Amsa mai da cewa "Sorry son ka je part dinka kayi taking shower lunch inka na jiran ka.." Ok, face din Jidda ya dan shafa.. sannan ya haura upstairs..



Yana shiga part na shi bathroom ya wuce yayi wanka ya fitu sanye da bedrobe White.. Ahankali ya nufi dress mirror ya fara shafa lotion mai kamshi yabi ko ina na jikin shi da shi,kai tsaye Wardrobe dinshi ya nufa ya curo three quarte black sai armless t-shirt ya sa , ba qaramin kyau yayi ba masha Allah.

Cikin na tsuwa ya ke sakowa daga downstairs ya qaraso parlour inda ya bar mom har yanzu nan take... Dining area ya nufa, ya ja kujera ya zauna rabi'a na gefe ahankali ta fara saving na shi Tuwan shinkafa miyar agushi wanda taji kaji da yan ciki kamshi sai tayi yake ,Sai data gama serving nashi sannan ta mike, harara ya dala mata dan shi kwata kwata yan' aikin kona mai rai suke musanman yan'mata wanda ba abinda suka sa gaba sai halin bera, wani wawan tsoki ya kuma ja wanda yasa rabi'a kyarma, dagowa yayi da sexy eye's ball's din shi yace... "Keeee!Tunda kin gama zubamin abincin ai sai ki tafi ko? ko sai kin gama qaremin kallo eeeeeeeye."


Mom dake parlour sai data ji tsawar da Sadiq ya daka ma rabi'a juyowa tayi ta ce..."Why son! Wai me yasa kai kullun sai an jika da masu aiki ne baby? gashi nan yanzu garin fadan ka ka tada angel daga bacci...." Bata fuska yayi kamar qaramin yaro ya ce..."Mom ni wallahi bana san yan'aikin nan wallahi

Please Login or Register in order to submit comment