Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yanke ya fadi saboda yadda ashurun ke magana kamar wanda yayi ma sarki qarya. me ya faru ta fada a taqaice ?dama yallabai ne ba lafiya yanzu haka yana asibiti na zo fada maku ne kuma har yanzu basu dawo ba, zaro ido fatuha tayi tare da dafe qirjin ta tuni hawaye suka fara mata anbaliya, me ya same shi? ta fada bakin ta na rawa, muje ka kaini asibitin sai inka ajeni sai ka biya family house ka fadi da sauri ta shiga motar ashuru ya ja sai asibiti. suna Isa ta bale murfin motar ashuru na gaba tana biye tana kuka suna Isa dakin ashuru ya juya fatuha ta shige ganin halin da sadiq yake yasa fatuha qara sakin wani saban kukan tare da qarasowa bakin gadan, a hankali ta kai hannu ta saman kan sadiq hawayan na sulalo mata ruwan hawayan ta ne ya d'iga a saman idan sadiq. a hankali ya fara ware idanuwashi ya sauke su kan fatuha da taci kuka ta gaji riqe hannu shi tayi tace "Uncle meke damun ka?" murmushi ya qaqaro wanda iya karshi laban shi ya kai hannu ya gogewa fatuha hawayan ta lumshe ido yayi tare da cewa "My dear bana so ina ganin ki kina kuka kinji? ba wani abu bane ke damuna ba kawai fever ne saboda na daina ganin smile din ki ya fadi zancan yana ja mata hanci" smile fatuha ta saki mai kuka kuka tare da kai mai pack a goshi Dr yakub da yanzu ya turo kofa ya shigo. ko sannin ya shigo basuyi ba . tsayawa yayi yana kallan su yana tu a ni, musanman yadda ya ga lokaci daya sadiq ya sauya, gashin kanta ya taba wanda ya leko waje yace fatuha "Na'am" tace tana kallan shi cike da so da kauna, me yasa kika daina kulla da gashin ki? hawaye ne suka sulalo mata ta bude baki za tayi magana sadiq ya daura yatsanshi sama lips din ta shhh a hankali ya kwance dankwalin kanta gashin ya baje a gadan bayan ta ba wai wanke kan ne batayi ba. a'a duk wasu mayuka masu sa kan sheqi ta daina shafawa saboda ko lokacin hakan bata da shi, har yanzu baki son majeed ko? kuka ta saka mai mai cin rai har da shesheqa. rintse ido sadiq yayi tare da shafa gefan face nata kukan ya Isa haka mana bana so naga kina kuka kinji? d'aga mai kai kawai fatuha tayi tare da daura hannuta saman nashi. tace "Shikenan uncle yanzu basma zaka aura? ta zama matar ka? angel ta zama diyarta ko?" kuka ta kuma saki mai cin rai shima haka sadiq bakin ciki kawai ke cin shi smile yayi yace "Nace fa ki daina kuka kuma angel diyarki ce ai" daga kai tayi yace "good!" haka kuma nima naki ne? ko baki so na auri basma? in baki so sai na fasa ya fada yana smile. ba wai bana so bane um bata inda zancan ba Dr yakub yayi sallama dan ya lura sai su kwana suna hira gashi fira da ya ji suna yi kamar cike take da matsala da rudani inya fahimta kenan, sauri tayi ta daura dankwallin ta tare da gaishe da Dr alura ya ma sadiq tare da cewa wanake gani kamar fatuha murmushi ta saki tace "Ni ce" gaskiya naga kin canza, ko duk amarcin ne ya fada yana kallan face din sadiq? take annurin sadiq ya fara daukewa haka fatuha dake zaune kusa da shi kawar da zan can yayi dama face nasu yake so ya karanta idan har ya gane suna son junan su, amma sai dai kowane wani da ban zai aura, insha Allah zai taya su da addu'ar cikar burin su.


Ko da ashuru ya je gida ya fada kusan motar biyu sukayi ko 10 minutes basuyi ba suka iso asibiti,a lokaci fatuha na feeding din sadiq abinci yana ci suna dariya dan ji yake gabaki daya kamar ya warke. turo qofar da akayi ne yasa su waigowa majeed ne ya fara shigowa turus yaja ya tsaya yana mamaki yaushe fatuha ta zo? haka basma dake bayan shi da umma da mom, ashuru ne da shigowar su yanzu shi da su abban ya fada masu yadda a kayi har ta zo dan sakin jikin majeed yayi amma har yanzu ya kasa kauda ido daga abinda ya gani. duk kunya ce ta kama fatuha aje plate din tayi tana qoqarin tashi, sadiq ya riqe hannu ta yadda baza ta iya matsawa daga kusa da shi, dan be iya hakuri da rashin ta kusa da shi kallan shi take tana mai alama ya sake ta amma yaqi dainawa. sai wasa dayake da hannu ta ganin ba yadda za tayi yasa ta hakura basma ko ta cika fam dan ita taso ace ita take kusa da shi ba fatuha ba. shima majeed ba laifi ya dan shaka amma yaki yadda zuciyar shi ta fadi abinda take tunani sai ma watsar da zancan da yayi shi ko sadiq yaqi sankin hannu ta da sunyi ido biyu sai ya sakar mata da lalausan murmushi, mom da ke lura da yana yin su sai suka bata tausayi dan dai kar tayi magana ace gashi, da ba abinda zai sa tace a basa auran amma da tayi magana tasan abinda zai biyo baya ko da su abba suka tanbayi Dr yakub me ke damu sadiq fever ya ce masu a taqaice .

Kiran sallah magrib ne yasa Sadiq ya saki fatuha dan ta dauro alwala lokaci har su mom sun tafi. daga ita sai basma sai majeed da shima yanzu ya wuce masallaci tana Shiga toilet basma ta matso ta zauna kusa da sadiq kasancewar ita Hutu take, ya jikin tace mai cikin yauki da kisisina. lumshi ido yayi tare da cewa "Da sauki" Allah ya baka lafiya sweetheart miqewa tayi daniyar ta mai pack lokacin yayi dai dai da fitowar fatuha daga toilet, bin gadan tayi da kallo ga wani irin kishi dak'e cin ta wanda ita kanta bata san tana da shi ba. juyawa baya sadiq yayi tare da cewa cikin cool voice din shi "Basma kai na ciwo koya naji an tsayamin a kai nauyi yake min ya fada yana kallan fatuha da saura qiris ta fashe" fita tayi d'aga daki'n da sauri ko da ta fita kuka ta saki mai ban tausayi. ta Dade tana kuka sannan ta samu guri a wajen tayi sallah...


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
[6/30, 8:47 PM] โ€ช+234 803 478 2721โ€ฌ: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


83_84

Bayan ta idar da sallah tana qoqarin nade daduma majeed ya shigo lalausan murmushi ya sakarmata tare da qarasowa kusa da ita. duqar da kai tayi qasa tana wasa da carpet din hannu ta, a hankali majeed yasa hannu ya d'ago da fuskar ta, kallan fuskar majeed yake cikin so da kauna. cikin sanyin murya yace "My love me ya saki kuka?" kamar jira take ya tanbaye ta ta fashe mai da saban kuka. rungume ta majeed yayi yana lalashin ta tare da samun daya d'aga cikin kujerin wajan suka zauna. daura kanta yayi a kafadar shi yana shafa mata bayan ta a hankalin cikin sanyi murya yace "My love bana so naga kina kuka? idan kina kuka sai naji nima kamar nayi, meke damun ki ki fada min koma minene zan samamaki indai zai saki farin?" cin da gowa fatuha tayi ta kaleshi, a cikin azuciyar ta tace "Ba komai zakamin ba, ila ka ce ka fasa aure na! ka barni da muradin raina da zabin zuciya ta ,abinda nake son gani safe rana dare wanda bana gajiya da ganin shi, wanda bana gajiya da sauraran shi ta qara rushewa da kuka" gabaki daya majeed rudewa yayi da yanayi fatuha sai aikin lalashin ta yake da kyar ya samu ta daina kuka sai faman ajiyar zuciya da take. daura kanta yayi saman kafadarshi yana wasa da yan yatsun ta masu laushi sun dau mintina suna a h'aka sannan fatuha ta zame kanta daga kafadar shi tana qoqarin tashi .d'ago fuskar ta yayi yasa lalausan hannu shi ya goge mata hawayan ta tare da yi mata pack a goshi runtse ido fatuha tayi tana jin wani irin suya da zuciyar ta kema ta mai cike da tsanar majeed ,hannun ta ya riqe suka miqe a tare sannan ya amshi dadumar hannuta a hankali suka bude kofar d'akin suka shigo .har yanzu sadiq na kwance amma ba bacci yake ba sai basma na gefan shi tana zuba mai iyayi yana saurara, shigowar su fatuha ce tasa shi dan dagowa ya jingi idanuwashi ne suka hango mai hannun fatuha cikin na majeed, wani irin b'akin ciki ne ya taso mai tabas wannan ba jinya aka zo ba zuwa akayi aga gawar shi, lumshe ido yayi dan baya iya jurewa ganin baki'n cikin .zame hannun ta fatuha tayi tare da zama tana facing din sadiq,

Majeed qarasawa yayi wajan sadiq tare da shafa sumar shi yace "Baby!" bude idanuwashi sadiq yayi tare da sakin murmushi riqe hannun shi majeed yayi tare da zama, aika ma sadiq harar wasa yayi tare da cewa "Shine baka da lafiya kakasa fada min baby? wai me yasa kakemin haka ?in abu na damun ka baka fada min saboda ban kai matsayin ba ko ?" ya fada yana lagwabe kai dan shagwabe. fuska sadiq yayi yace "Sorry banyi tunanin fever ya kai haka ba, nayi tunanin har sai naje Lego's nasha magani" um please next time karka sake haka, tam yace tare da mitsin shi na wasa kaci abinci, no! me yasa baka jin yunwa ?so kake ciwo ya cigaba da riqe min kai ko?" plate majeed ya janyo ya zuba abinci shinkafa da miya tasha naman rago a hankali ya shiga feeding din sadiq yana amsa cike da son dan uwa na shi yana ci yana jan shi da hira mai cike da nishadi. dariya sadiq yake can kuma yayi shuru yana bin majeed da kallo , murmushi majeed yayi tare da aje plate din yace "Kallan fa?" smile Sadiq yayi yace "Ba komai" juyawa majeed yayi ya kalli fatuha yace "Sweetheart ku tashi muje na saukeku gida" ok fatuha tace tare da tamiqewa . basma ko pack ta ma sadiq tare da mai sai da safe ta fita. hadiyar zuciya ne ka dai fatuha ba tayi ba sannan suka fice har sun kai bakin kofar mota, fatuha tace "Tayi mantuwa" sa sauri ta koma daki'n sadiq lokaci idanuwashi na lumshe.


A hankali fatuha ta qaraso ta shafa sumar kanshi. bude ido yayi yana kallan ta yace "Fatuha kin dawo ne ki kulla da uncle?" murmushi ta saki tace "Mantuwa nayi um" mekika manta? pack ta mai a goshi sannan tace "Kaga abinda na manta" smile sadiq ya saki tare da janyo ta ta fado saman qirjin shi har tana jin bugun zuciyar shi ,lips din ta yabi da kallo a hankali ya daura finger din shi saman lips din fatuha. kallan shi take me cike da kauna haka shima tafiyar tsutsa sadiq ya rinqa yi mata a lips din . riqe hannu tayi tare da dan cizan shi dariya fatuha ta saki dan shagwabe fuska yayi ta koma kamar baby face , sorry fatuha tace tare da riqe kunnan ta. ja mata hanci sadiq yayi tare da yi mata pack a kumatu, um uncle bari na tafi nabar mutane na jirana a waje ?sauri tayi ta daga daga saman bed din riqe hannun ta sadiq yayi yana binta da kallo itama shi take kalla sannan tasa kai ta fita. tana fita taci qaro da majeed gabanta ne ya yanke ya fadi lokaci daya .ta dan da birce kallan ta kawai majeed yayi bai ce komai ba suka shige mota suka bar asibitin.


Kwanan sadiq uku asibiti aka sallame shi. sosai ya samu kullawa wajan yan'uwan shi tare da soyayyar su, zaune suke saman dining area suna lunch har da basma saboda yanzu ta dawo gidan da zama angel na gefe tana zubama sadiq shagwaba sai ya kai ta shan ice cream mom sai tsiya take mata, basma ce ta kalli sadiq tare da jefa mai kallan so murmushi ya mata wanda iyakar shi laban shi fatuha na zaune tana lura da hakan gabaki daya annurin ta ya dauke dan ji take ma abincin ya isheta. ture plate din tayi tare da tashi ta barwurin kallo sadiq ya bita da shi tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da sakin kuka ,sai da taci kuka ta gaji sannan ta bude bedside drowa wani album ta curo tana kalla pics din tane ita da angel da sadiq tana kallan tana dariya da murmushi mai kuka. haka ta rinqa kallan pics din har bacci ya dauke ta,


Bayan sun gama lunch suka koma parlour suna kallo basma sai jan sadiq take da labari tun be biya mata har ya dan fara sakar mata. amma duk bayan mintina sai ya kalli bedroom din fatuha sallamar majeed ce ta katse mai tunani, da sauri basma ta qarasa wajan shi bros I miss u? miss u more sis yasu umma ta fada suna nan lafiya lau, dan bata fuska majeed yayi matsala ta dake shegyan surutu ko bari bakiyi na huta kin fara tanbayata, haka zaki rinqa yima sadiq? murmushi ta saki tare da rufe fuskarta tabe baki sadiq yayi tare da kauda kai. qarasowa majeed yayi ya zauna kusa da sadiq suka gaisa, sannan yace ina my love? wani irin kishi ne ya rufe sadiq shuru yayi be tanka ba. basma cikin zakuwa tace tana bedroom zunbur ya miqe ya shige a hankali ya bude kofar kwance ya hango ta saman bed smile yayi tare da qarasowa, bacci take rungume da album din a hankali yasa hannu ya zare album din bude album din yayi yana kalla pic din ta da sadiq ya fara gani, kanta na bisa kafadar sadiq suna dariya ya Dade yana kallan pic din, sannan ya bude d'aya shafin ya gansu su uku cikin pic din suna shan ice cream haka majeed ya rinqa bin pics din yana kallo musanman in yaga wanda fatuha da sadiq ne pic din har mamakin irin shaquwar da sukayi yake be taba tunanin shaquwar su har ta kai haka ba ,aje album din yayi yana qoqarin fita yaga sadiq bakin kofa fuskarsa a ha...

*Kuyi hakuri da wanan ina busy Im sorry fan's๐Ÿ‘ insha Allah zuwa gobe zaku samu page mai yauwa love u all*





*ku har kullun salma mas'ud nadabo*
[7/1, 10:13 PM] โ€ช+234 803 478 2721โ€ฌ: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* realhausafulaniwritersforum@gmail.com

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


85_86

Murmushi sadiq yayi tare da qarasowa ya dauki album din da majeed ya aje .ya bud'e sannan shima ya aje tare da kallan bed .fatuha na kwance gashin ta ya baje a bed din, take sadiq kishi ya lulube shi qoqari fita yake majeed shima ya miqe suka fita a tare. ko da suka fito mom na zaune tana kallo basma na gefe angel na assignment gaishe ta majeed yayi tare da yi mata pack cikin fara'a ta amsa tare da tanbayar shi su umma yace "Suna lafiya" sannan suka fita da sadiq.


basu zame ko ina ba sai family house, bangaran ammi suka fara shiga cikin sallama suka shiga ammi na zaune tana kallo washe da baki ta amsa. "A'a wanake gani?" ta fada tana gyara dankwalin ta dan tselankwa na dauk'a baka zuwa ai zama su sadiq su kayi saman two star suna murmushi. mai gida ai na dauka baka zuwa godiya? mu dau zunkudediyar budurwa mu baka amma ko leqe? yar dariya sadiq yayi wanda iya karta laban shi dan shi a gaskiya har mantawa yake da basma a matsayin matar da zai aure ya ke. ammi ce ta katse masu zance da cewa bari na kawo maku fura, to ammi! amma dai taji nono? ina ruwan ka da abinda zata ji? nifa dan mai gida nake badan kai ba, kai har gajiya nake da ganin ka wallahi dariya majeed ya saki naji ba komai ai danayi aure kin bar ganina wallahi, wani miyau mai daci sadiq ya hadeye tare da kallan majeed ta qasan ido, kai dai ka Sani sannan ammi ta shige kitchen ta dauko masu fura a fridge tasha nono ta aje masu aiko sun sha sosai sannan suka rinqa zuba fira suna cikin hira Alhaji babba ya shigo shima aka dasa da shi. sai kusan yama likis sannan suka wuce part din umma inda umma ta rinqa nan da sadiq dama can dan gaban goshin tane bale kuma yanzu da zai aure auta sai da suka sha fira sosai kiran sallah magrib ne ya tashe su dauro alwala su kayi suka wuce masallaci.


Bangaran su fatuha ko tana tashi wanka tayi, sannan ta shafa lotion mai kamshi tare da zura after dress din ta black ta mata kyau sosai sai dai tayi yar rama kadan saboda tunani parlour ta fito ta iske basma na kallo cikin fara'a ta qaraso ta zauna kusa da ita. yar hira suka taba sama sama sannan suka shige kitchen kusan a tare suke aiki'n. inda baba jinmai ke ta bin fatuha da kallo saboda gabaki daya yanzu fatuha bata walwala ga wata yar rama da tayi haka dai suka rinqa aikin bayan sun kamala basma da rabi'a suka kwashe kulollin suka kai dining area a lokacin ne baba jinmai ta ja fatuha gefe tana mata yar na siha kan tayi hakuri kar ta jama kanta ciwo ta rinqa cin abinci dan ta lura kwana biyu nan bata cin komai, kuka tasa mata lalashin ta baba ta rinqa yi har ta samu tayi shuru tana qoqarin goge hawayan ta basma ta shigo kallan ta tayi tace, "Fatuha me ya saki kuka?" murmushi fatuha ta qaqoru wanda iya karshi laban ta tace, "Albasa ce ta shigar min ido" eyya sorry ke je ki wanke fuskar to tace tare da fita d'aga kitchen din. ko da ta shiga toilet sana'ar ta cigaba wato kuka sai da tayi san ranta ta fito kaya ta chanja tasa riga da skeet na atamfa ash mai ratsin pink masha Allah kayan sun mata kyau sai dauri da tayi kasan cewa Hutu take ko sallah ba tayi ba. fitowar yayi dai dai ta shigowar su majeed mutuwar tsaye majeed yayi ya bita da kallo dan ba qaramin kyau ta mashi ba ,haka shima sadiq ji yake kamar yaje yayi hug nata cikin sauri sauri majeed ya qarasa wajan ta tare da sakin smile yace, "My love kinyi kyau" murmushi fatuha tayi wanda iya karshi laban ta sadiq na tsaye baki'n kofa dan ko qarasowa ya kasa. rungume ta majeed yayi yana magana cikin cool voice din shi "My love kullun qara kyau kike ?ji nake kamar na janyo lokacin auran nan" sadiq dak'e gefe sai hadiyar bakin ciki yake dan har ya fara ganin jiri a hankali yake jefa kafar shi da be san inda zai wurga ta ba, har ya samu ya haura upstairs tun kan ya Isa bedroom ya fara tari da bin bango ya Isa toilet tari kawai yake tare da jini zamewa yayi a qasan toilet yana mai da numfashi tare da cire bottles din rigar shi dan ya samu iska ya dau mintina goma yana a haka .a hankali ya ja jiki ya koma bedroom kayan jikin shi ya rage yasa jallabiya ya bude bedside drowe ya ciro magani. ya sha tare da shigewa blanket saboda fever dake damun shi a yanzu lumshe ido yayi wasu hawaye masu zafi daya na bin daya.

Sakin ta majeed yayi tare da yi mata pack a goshi kallan kofa tayi wayam ba sadiq ba alama. haka shima majeed, oh sweetheart kin ga kin rudani da yawa ko sadiq na manta da shi ya fada yana dan langwabe kai , fatuha da ta cika tap dan qiris take jira ta fashe daurewa kawai take tace, "Ai sai ka bishi ta fada tana qaqorin shigewa bedroom" hannun ta ya riqe tare da saki'n murmushi ya dawo ya rungume ta ta baya rintse ido tayi tana jin wata tsanar shi cikin muryar kuka kaku tace "Majeed please ka bari? so kake su mom su fito su ganmu haka? ta fada tana qoqarin kwace kanta" um to me dan sun ganmu how many day's ya rage ki zama tawa . naji duk da haka ai da kunya ta fada tana samai kuka sakin ta yayi yana bata hakuri ko sauraran shi ba tayi ba ta shige daki tare da fadawa saman bed ta saki kuka.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na bakin ciki. inda ciwo keta cin sadiq dan yanzu sosai yake zubar da jini duk da yana shan magani da zai sa yaji sauki, amma abun sai gaba yake dan har ya fara fida rai da duniya,


Cikin kayan ta na uniform take shiri duk da jikin ta ba kwari ,bayan ta kamala ta fito su mom na zaune suna break cikin natsuwa ta gaishe su tare da zama ta janyo cup zata hada tea. kamshi turaran da ya doki hanci tane ya sata waigowa, sadiq ne sanye cikin uniform din shi masha Allah yayi kyau sai yar rama da yayi gaishe da mom yayi tare da yi mata pack ya ja kujera ya zauna .cup fatuha ta janyo zata hada mai tea ,murmushi basma tayi tare da amsar cup din tace "Fatuha barshi kawai na hada mai ?tunda ke kinga school zaku karki makara"
miqa mata cup din tayi jiki ba kwari ta zauna tana juya nata tea din idanuwan ta tap da kwalla .taki yadda ta dago idanuwan ta? kuma taki shan tea din. tana gama had'a tea din ta miqo wa sadiq yana miqa hannu zai amsa ya saki cup din ya fadi tea din ya bare a dining area dagowa fatuha ta yi saboda tea din ya zuba mata. kallan sadiq take shima ita yake kalla, lalausan murmushi ya sakar mata, ah yaya sadiq tea din be bata maka kaya ba ko? ba komai basma ok bari na hada ma wani barshi kawai nama koshi dan bata fuska tayi, tana kallan shi tace "Yanzu baza ka ci komai ba?" mom ce tace "Kyale shi indai wannan ne ya saba da haka" to kawai basma tace tare da fara tatare inda tea din ya zube .


Kasancewar yau majeed be zo daukar fatuha ba yasa sadiq ne ya sauke su a makaranta. duk da ba wata magana sukayi ma juna ba amma hakan ba qaramin dadi ya masu ba, Basuki su dawa ma a haka .



*2week letter*

Biki ya matso gadan gadan yasa mom ta samama amaran mai gyaran jiki. gyara su tak'e sosai dan har sun fara murjewa da kyau da sheki dan yanzu ko bari mom batayi su sadiq su ga amaran.




Please Login or Register in order to submit comment