Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi amsa. Me ki ka yi a kicin da
zai dauke ki wannan lokacin Humaira? Kinsan
kuwa yadda kika sa min damuwa? " koyan
abinci". Na kara fada. Yayi ajiyar zuciya tare
da waji murmushi mai fidda sauti.
To idan za a tafi kicin ba a tafiya da waya ne?
Haushi ya kama ni, wai shi ba ya magana kai
tsaye sai ya hada da tambaya? Kin ji? Ya
bukata. Na ce, na mantata ne kan kujera. Yayi
yar dariya, yace Don Allah ni da a ringa
makale wata ko'ina za ki shiga kada ki dora
min hawan jini, Ko ba a sin kiran nawa ne?
Aifa, na fada a zuci. Kinji ba kya son na kira
ne? Nayi masa shiru. Yanzu me da me kika
koya?? Allah ka raba wannan bawa da
tamabay, na fada a zuci. Yayi kasa da murya
Don Allah ki fada min irin abin d kika koaya.
Ai suna da yawa. Nace da shi. Suna da yawa
har guda nawa kika iya? Duka na iya, ai basu
da wuya. To ji ma koya kin. Wai ina marar
lafiya ka tsaya kana faman tsokana? Wallahi
duk tunanina a zuci nayi wannan maganar, sai
kawai na ji ya tuntsire da dariya. Ga shi nan
kusa da ni, ko na bashi ne?? Nayi shiru,
gabana yana faduwa. Hajiya Humaira
Gimbiya, wannan kasaitar taki ke kara ruda ni
wallahi, Toh ko milk and coconut balls din ne
a koya mun. Wai ko Yarima yana dubiya ne?
Nayi murmushi na ce. Hmmmm Yace meye
humm? Gashi zamu yi tafiyar dare ballantana
na taya ki hirar dare. Ba komai. Na fada da
sauri. Ke a wurinki yake ba komai, ni kuwa
akwai wani abu.... ga su nan sun fito za mu
tafi, kar ki kashe wayarki fa. Na ce to. Sai na
kira. Ya fada. Allah ya kiyaye hanya, Allah ya
bashi lafiya.
Cikin jindadi yace, Ameen. Ban jira ya kara
magana ba na latse wayar. Na kalli wayar ko
me ya sa yake yi min wannan surutun alhalin
ba haka yake wa sauran mutane ba? Ban
fama tunanin ba na ji karam! Ina dubawa na
fa sako. Ina rokonki da ki ringa sakin jiki
muna magana ko a wayar ne tunda a fili kin
kasa. Ina cikin wani hali Humaira na rashin
sukuni da kwanciyar hankali, ga matsalar
ciwon maimartaba, ga ta Fareeda. Sannan ga
ta jama'a, wurinki kadai nake jin zan samu
kwanciyar hankali, ba komai zai haifar da
hakan ba sai kin yi responding da duk wata
magana da zan yi miki, don Allah ki saki jiki
da ni ina rokonki. Murmushi kawai nayi. Ga
tsayuwar kicin ' yan share sharen da na yi da
magriba, don haka gajiya ta taso mini, ina
gama wanka waje karfe tara na kwanta ban
kara sannin abin da ake yi ba sai da na bude
ido na fa karfe shidda da kwata na safe. Na
hanzarta yin alwala na gabatar da sallah
Sannan na koma kan gado na kwanta kafin na
kara hutawa zuwa billowar rana. Da wuri
kamar yadda tayi min alkawari ta zo, don tare
da ita muka yi kalaci. Kamar yarda Yarima ya
umurce ta cewa kwana biyar, to hakan akayi,
amma fa na koya abubuwa domin sai dana
cika littafina mai farka arba'in. Kwana biyu
kenan ba mu yi waya da Yarima ba, kuma na
kasa nemansa. Sai na dauko kamar zan kira
sai kuma na fasa. Zaune nake ina gyaran
kumbar hannuna naji motoci sun shigo, na
mike tare da lekawa ta taga ba hango
zungura zunguran motoci nan na sarauta
masu kofofi hudu. Budewar farko na hango
Yarima ya yi saurin fitowa daga nan na ga an
kamo maimartaba sun nufi babbab gida dake
bayan inda nake. Gabana ya fadi, na dafe kirji
tare da koma kan kujera nayi laggwab. Har
bayan isha'i ban ga Yarima ya shigo ba, nan
jikina ya kara mutuwa. Haka na kwanta ba
don bacci ba, Can wajen karfe sha daya naji
motsin mukulli ana bude kofa. Na runtse
idona kamar mai bacci. Kamshin turarensa ya
fara ziyarata kafin na ji ya shigo Na kara yin
lami. Ya gama yan hidindimunsa duk cikin
dakin ko wanka a nan yayi, sannnan naji yana
kokarin hawa kan gadon inda nake. Na tamke
idona. Ya hawo tare da yaye bargo dana
lullube Shirun da na ji ya yi ya bani tabbacin
kallona yake yi. Na tsargu saura kadan na
bude idona sai kawai na yu saurin juyawa
kamar cikin bacci ai sai naji ya janyo ni jikinsa
tare da maida bargo ya rufe mu. Ai sai na
fara kokarin zame jikina Ya kuwa rike ni
tamau!
Ya karkato bakinsa daidai kunnena yana
magana a hankali. Ke ni ne ki kwanta ban yi
niyyar tadaki ba. Amma sai da na zame jikina.
Mene ne haka Humaira? Kina fa wahalar da ni
da yawa Kin yi min rowar muryarki kwana da
yawa Kuma yanzu sai ki hana ni jin dumin
jikinki? Kin ji? Da ke fa nake magana? To me
zance masa dan Allag? Ba ki magana? Ya
tashi zaune. Wallahi ko ki matso konkuwa na
hau kanki. Ba shiri na matsa. Yayi yar dariya.
Matsoraciya duk kya gama Yan kauce kaucen
naki ki dawo hanya......mun dawo me zan
samu na sannu da zuwa? Ya rada min a
kunne, na ji wani yarr!! Kamar na shakare shi
duk na takura Wannan salon kuma ya dawo
da shi? Lallai bone ta ci ni kuwa. Ba fa zan
lamunci shirun nan ba wallahi. Humaira na
gaji da wahalar nan Ko ba kiji ina magana
ba? Ya jikin Baba?? Na fada kamar mai koyon
magana. Da sauki yana nan gidan ma zai huta
na wani lokaci Don haka kada ki sake ki nuna
ina da alaka da ke. Gabana ya fadi ras! Lallai
akwai babbar matsala. Yanzu me zan samu?
Me fa! Duk tunanina a zuci na yi Sai da na ji
yace Me fa ? Hmmmm. Yayi shiru sai na ga
kamar ban kyauta ba Na daure na ce. Ka fadi
me kake so sai in girka maka Bana burin
abinci ya kwana Kuma ban san yau zaka dawo
ba. Ni ba abinci nake so ba. Ban san lokacin
dana ce To me kake so Ya dan kara kasa da
murya kamar wani zai ji Ko dan kiss Ko motsi
ban kara yi ba Kin ji? Zan samu? Humaira da
ke nake Wallahi da Yarima zai gane da ya
daina yi min wadannan tambayoyi nasa. Shi
ne kika kyale ni? Kin ji? Na kara kulewa sai
kace bakinsa aka yi kalmar kinji Don girman
Allah ki taimaka mini Wallahi na kawo wa
raina. Ya kusa bani ma dariya har da magiya.
To tunda kin yi min bukulu juyo ki fuakance ni
Ko hakan ma ba zan samu ba? Na dai yi masa
shiru. Kinji? Wai don Allah kai ba ka san ina
jin kunyarka ba?? Na fada kamar shirin yin
kuka. Sai kawai naji ya kyalkyace da dariya. Ni
ban sani ba. Ashe kunya ta ake ji? Wannan
kunyar bata yi min adalci ba wallahi. Juyo na
rage miki ita Don na lura ke ma ta takura ki
Kin san Allah sai kin zaba Ko ki juyo ko kuma
kiss.
Sai me? Bakinsa naji ya hada da nawa Zan
kwace yayi min wani riko. Na rasa inda zan sa
raina don kunya. Ya dauki mintuna kusan
talatin har jikina yayi lakwas. Yana zame
bakinsa na yi saurin cusa kaina jikinsa kamar
in bude kasa in shige abin da dama ya ke so
kenan Ya kara gyara ni tare da rufe mu da
bargo. Sama sama na fara jin nufashinsa
alamar ya sami barci, amma da na motsa sai
ya yi firgigi tare da matse ni. A haka har na
hakura ni ma ban san kokacin da barawon ya
sace ni ba. Ko da na farka ban ganshi ba,
lokacin bakwai har ta wuce. Ban yi mamakin
wannan muguwar makara fa na yi ba, na
hanzarta gabatar da sallah ban tsaya gyaran
dakin ba na fada kicin. Na soya dankali,
sannan na dafa tsokar nama da albasa da
kayan kamshi, sannan na jajjaga tattasai da
dan tumatir tare da albasa duk na ajiye gefe,
na dauko albasa ba yankata faken falen
sannan na daka wannan dafaffiyar tsokar. Na
zuba mai a tukunya na kawo yankakkar
albasar nan na zuba cikin man ta dauka
dahuwa sannan na zuba cijin man ta dauko
dahuwa sannan na zuba jajjagena da
dakakken nama na ci gaba da motsawa kafin
na dauko baked beans shi ma na zuba ciki
tare da kabeji dana yanka, sannan na zuba su
maggi da sauran kayan kanshi. Wannan itace
miyar cin dankali. Bayan na gama na soya
kwai, sannan na hada kunun kuskus. Madara
na zuba a tukunya kofi daya ta gari da ruwa
rabin kofi suka tafaso sannan na zuba kuskus
tare da kara dan ruwa na bar shi ya dahu
lugub ba sanya maburki na burke ba juye a
kwano na kawo flavour mai kamshin madara
na zuba da madarar ruwa peak sai sukari. Na
hada wadannan kaya na shirya wasu a tire na
rufe da dan kyalle na rufe abinci, gyalena
navdauka tare da fita wajen gidan Cikin sa'a
sai ga wani zai wuce na kira shi muka gaisa
yana min kallon rashin sani ban damu ba
nace. Don Allah ka taimaka ka kai wa
maimartaba kace daga gidan abokin Yarima.
Yana ji na ambaci Yarima ya fara kyarma tare
da karba cikin hanzari yayi gaba. Ni kuma na
kima ciki don hada wa yArima nasa. Sannan
na shiga gyaran gidan da yan share share
cikin yan mintuna kamshin freshner da
turaren
wuta ya gauraye ko'ina. Na fada bandaki na yi
wanka, abin mamaki ina fitowa na tarar an
ajiye min wata doguwar riga mai dankaren
kyau. Motsin kwanukan da na ji a falo ya ba ni
tabbacin shi ne ya shigo. Nayi saurin
shiryawa, amma kunya ta hana ni fita, yadda
riga ta kame ni kam kamar daman an auna da
jikina na kalli kaina na kara kallo. Kai duniya
komai na son gyara. Ni kaina na yaba da kyan
da nayi. Ganin lokaci zai kure har sha daya na
niyyar yi yasa na daure nafito, saboda
gabatar da abincin rana. Zaune yake yana
faman latsa waya na dan karasa nesa da shi
kaina kasa ban yarda mun hada idi ba nace
Barka da sfiya, ya karfin jikin maimartaba?
Gaisuwar tayi masa dadi a yadda na fahimta,
yace. Alhamdulillahi da sauki wallahi, na je
ma gida amso masa karin kumallo ne. Ina
dawowa na tarar har ya gama cin wani abinci
ta baiinsa mai dadin gaske, wai an kawao
masa daga gidan abokina shi ne nakr neman
wannan dan iskan in ji ko shi Abdul amma ba
wanda na samu. Shiru na yi tare da mijewa na
kwashe kayan, ga mamaki ya cinye komai. Ya
kalle ni yana murmushi. Kr ni fa na lashe
abincin, kin dai ci naki ki?
Nayi yar dariya, Eh Dariya na baki? Ya fada
cikin wata irin siga mai nuna matsanancin
farin ciki. Ni dai na yi gaba abina in
murmushi. Abin da na fara yi shine gyara kaza
na wanke na jajjaga dan tarugu da albasa
sannan na daka thyme da citta da tafarnuwa
na hade wuri guda na kawi mai na zuba ciki,
sannan na zuba maggi da gishiri na motse na
shafe kazar nan da su ciki da waje, na saka
gefe na dauko albasa davtumatir na yanka
fyalen fyalen, na yanka kabeji kanana na ajiye
gefe. Na dauki kazar na sa a oven tare da
timing mintuna arba'in da biyar. Na wanke
shinkafa da ma na dora ruwan zafi sun tafasa
na zuba, sannan na barta ta dan dahu, sannan
na sauke na wanke na tsane. Na yanka wani
kabeji, karas, kokumba, koren wake da peas
na tafasa hanta na yankata kanana da yar
albasa. Na zuba mai a tukunya kadan yana yin
zafi na juye vegetables dina da hanta sannan
na zuba zuwa kadan na kawo shinkafar na
zuba tare da motsawa, ruwan suka hau kanta
kadan yadda zan ida dafata na rufe. Ina cikin
gyara kayan miya Yarima ya shigo ya sha
uban ado da irin kayansu na sarauta nan da
nan jikina ya dauki rawa na kasa ci gaba da
yankawa. Ya matso tare da shishige min. Me
kike dafawa haka gida ya rikice da kamshi??
Zaka fara ko? Na fada a zuci, amma a fili na
ce Abinci. Zan sami kamar na mutum hudu
zuwa biyar? Insha Allah. Na bashi amsa. Ya
rungume ni very good my princess. Zamu zo
around 2:30 mu ci , kaya na nan su za ki canja
kinji? Nace To. Duk na kagara ya tafi. Ya kai
hancinsa a wuyana. Inason wannan turaren
very sexy. Na dai yi shiru saboda na riga na yi
mutuwar tsaye, ko me ye sexy kuma? Na
tambayi kaina. Gobe dani za ayi girkin nan
gaskiya, yau ma don am busy shi ya sa. Ya
sake ni, sai mun zo cin abincin. Yana fita na
saki wata ajiyar zuciya jikina gaba daya ya
bige da kamshi turarensa. Da hanzari na kara
gyara wasu kajin uku tunda wankewa ce
kawai, akwai a firij na yi musu hadin ta farkon
na kunna dayan oven din nasa su a ciki. Daidai
shinkafar ta dahu na kwashe a katuwar kula
kafin na gama na san ina zan zuzzuba. Muna
da lemuka kala kala don haka ban wahalar da
kaina wajen hada wani juice ba gani har biyu
da mintuna biyar. Na sami babban kwando
na zuba abinci na shirya wa maimaryaba
komai na ajiye gefe, sannan na je na shirya
wa su Yarima nasu a fako a kan table abin
mamaki naji ana buga kofa.
Na san ba Yarima ba ne sabida yana da
makulli, na hanzarta isa sai na ga wani dogari
da kwanonina, na bude ya durkusa.
Maimartaba ya ce a yi godiya sosai. Na ce
yauwa tsaya ka tafi da wannan. Na hanzarta
na dauko lemuka kansa na sanya masa kusan
kala takwas. Na kwashi nawa na yi daki na
tarar ya ajiye min wata danyar shaddda galila
ta sha aiki sosai, na yo alwala na saka,
sannan na fara gabatar da sallah. Ina
kabbarawa na ji motsin shigowarsu, wani
dadi ya baibaye ni. Ya leko Au sallah kike yi?
Ya fice. Koda na gama naci gaba da cin
abincina a tsanake tunda su ma na ji suna cin
nasu ne. Na gama nayi lamo ina jin hirarsu
sai faman santi suke yi, sunabyi wa Yarima
sharri. Wai da man don ya kwashi girki yasa
ya haukace kaina. Na yafa gyalena na leka
muka gaisa, za su fara tsokanata nayi saurim
komawa ciki. Muryar wani na ji yana cewa,
shege ina ka samo wannan shuwa arab din?
Dole Gimbiya ta haulace bala'in nan alkur'an
yarinyar tsoro ta bani......amma da ita zaka
tafi jibi ko? Dadi ya ziyarce ni, ashe tafiya zai
yi jibi? Ni dama gobe ko yau ne. Baka jin
maganar Yarimaan saboda kasaita da jan
girma wannan mutumin akwai isa. Yaushe ne
ta ke haihuwa Gimbiyar? Ciki gare ta ashe?
Na fada a bayyanr. Suka dai gama hirarsu ina
ji suna amarya mun gode amma na yi shiru.
Tunanina da shi aka fita sai kawai na ga
mutum ya shigo alkyabba a hannu. Ya miko
min. Ungo ki kai min daki. Na mike na isa tare
da mika hannu sai kawai naji mutum ya
rungume ni. Haba irin wannan delicious ai sai
da tukwicin hug. Wallahi kwakwalwarki na ja,
na san ko ita malamar taki da ta koya miki
girkin yanzu ba zata hada kanta da ke ba.
God bless u my princesss. Ya sake ni, zan je
na amso wa maimartaba abinci, Umma har ta
kai ga yi min waya. Nace to kawai. Har ya
juya ya dawo Zo ki yi min rakiya. Ya fizgo ni
muna zuwa bakin kofa ya mamayeni ya kai
bakinsa ga nawa, sannan ya saki ji tare da yi
min gwalo, sai kawai abin ya bani dariya
sosai. Shi ma da dariyar ya bar gidan, na
gaya shiga wani farin ciki mara misaltuwa,
Yarima Hameed kenan. Karfe shidda na
marece naji ana kwankwasa kofa, na hanzarta
tare da tambayar waye? Yace kwanoni ne aka
kawo na abinci. Na hanzarta budewa da man
da hijabi a jikina. Kamar jiya ya risina.
Maimartaba yace, ayi masa godiya mai tarin
yawa, Allah ya albarkace ku ya azurtaku, ya
rufa muku asiru duniya da lahira. Nayi
murmushi cike da jin dadin wadannan
addu'oin nace. Amin ya rabbi. Na karbi kayan
ina shirin juyawa gida, sai ga Yarima kamar
daga sama. Gabana ya fadi jikina yayi sanyi,
ya kalli dan sakon da tuni ya zube kasa yana.
Allah ya taimaki Yarima! Ya daure fuska, ya ya
dai? Na maido wa matar abokinka kwanoni
ne, kuma maimartaba na dada godiya, Allah
ya bar aminci. Tashi ka tafi. Ya fada a
hanzarce. Ni kuma nayi ciki da sauri. Ya biyo
ni har kicin. Dama Humaira ke ce ke aikawa
da abincin da maimartaba ke faman yabawa?
Ke ce matar abokina da yake faman fada wa
duk wanda ya ziyarce shi? Waye ya baki
wannan shawarar? "ba kya tsoron hakan xai iya
janyo a yi
saurin fahimtar tsakaninmu 2nda kin nemi
wannan kusancin har an san da ke? Kin ji?".
Ba tare da na kalle shi ba, na ce. "ka yi
haquri". Ya matso kusa dani "ba laifi na ce kin
yi ba, shin kina ganin ba wata matsala ko ba
kiyi 2nani ba kafin ki yanke hukunci?" a qagare
na ce da shi "ba wata matsala in sha Allah".
"kin tabbata?" "eh". Na fada ina shirin gifta
shi na fita. Ya janyo ni jikinsa. "Allah ya yi miki
albarka humaira". Bai qara fita ba, ya ce muje
na taya shi harhada kayansa, sai wajen 9
muka gama, saboda mun yi sallar magariba
da isha'i sannan tambayoyi da yawan
maganarsa suka ringa bata mana lokaci. "wai
humaira don Allah sai yaushe xaki saki jikinki
da nawa?" murmushi kawai na yi "kin san
shawarar da na ke yi yanxu?". Na
ce "a'a". Ya ce "so nake yi idan na dawo na
san yadda xan maida ki makaranta, ko ba ki
so?". Na fadada murmushin kusan xuwa 'yar
dariya "wallahi ina so saboda ma 2ranci". Ya
kalle ni sosai "2ranci kuma?". "eh wallahi, ina
son iya 2ranci sosai". Ya qyalqyale da dariya
"to ko london xan kai ki qasar 2rawan?". Cikin
'yar dariya na ce "da ko ka kyauta". Wasa-
wasa hira ta barke tsakaninmu, nan da nan ya
fahimci lallai ina son ilimi 2nda ga shi ina hira
da shi cikin sakin jiki, abin da ba taba ba. Da
yake hirar ta yi min dadi ban damu da yadda
muka kwanta gado 1 ba, muna ci gaba da
hirar har sai da na lura da irin shige min da
ya yi tare da yadda salon maganarsa ke...
sauyawa nan da nan tsoro da kunya
suka kama ni, amma ina lokacin da na farga
na makaro, 2ni yarima ya kasa sarrafa kansa,
yana faman salo... Ya rasa ta inda xai billo
min nayi shiru, ni kaina na san kukan ba wai
na ciwo ba ne, tsabar kunya ce ya sa na kasa
tsaida shi, saboda ina 2nanin ta inda xan
tashi, ga shi a dakin ya kasa ya tsare. "don
Allah humaira ki yi haquri". Kalmar da yake ta
nanatawa kenan 2n tashinsa. Ganin ba wani
sauyi sai kawai ya dauke ni cak xuwa bandaki
ya hada min ruwan dumi da komai sannan ya
fito. Na sami damar dago kaina daga qasa ina
raba idanu kamar wacce ta yi qarya. Na ma
ba kaina dariya na samu na yi wanka amma
fitowar ta gagareni. Sai na jiyo motsinsa can
bayan daki, ai ko na yi hanxarin fitowa. Ga
mamakina ya gyara dakin tsaf! Ya sauya xanin
gado sai qamshi ke tashi. Ta taga na
hango shi yana shanya xanin gadon da ya
kware, wato wankewa ya yi. Ina cikin saka
kaya ya shigo, ai ko na yi cikin wardrope din
sai kawai na ji yana dariya. "xan je gurin
maimartaba, ki hada abincin da ni don sai
xuwa jibi xan wuce, na fasa tafia yau". Gabana
ya fadi, ni kam na so ya tafi yau din kamar
yadda ya tsara. Kamar kullum na hada abinci
kala-kala, na shirya masa nasa na aika wa
maimartaba sauran. Na sallame shi sallah
kenan na ji shigowarsa da baqi. Har suka
gama ban fita ba, shi ma bai shigo ba, da
suka tashi kuma suka fita tare. Ina xaune falo
ya dawo da qa2war leda. "sorry humaira,
kadaici ya dame ki ko?". Ya qaraso inda nake.
"wallahi 2n fitarmu ina kasuwa don samo miki
abin kore kadaici". Yana maganar yana
bude ledar tare da fiddo littatafan hausa da
fina-finan hausa sabbi, masu kyau. Dadi ya
kama ni, da ma in taba kara2n hausa ko a
gida, musamman littattafan jamila ibrahim
kankia, naja'atu haruna 'najnoor nasimat', da
kuma na xainab dahiru wauwo 'xeedee'. Ya
miqo min littattafan kusan guda 20, a sama
wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee
wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin
nasan dole ya yi dadi. Na yi murmushi "na
gode qwarai". "ga kuma hausa films xo in
koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa
sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba
xa ki iya gane connection din ba duk da a
hade suke ko da remote sai ki sauya". Nace
"to". Tare da matsawa cikin doki da murna,
saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam.
"abin ma ba wuya".
Na fada ina yar dariya. Ya yi murmushi. Gare
ki mai saurin fahimta ba...... Akwai sairan
abinci? Wallahi yunwa nake ji. Eh na dafa
wancan babu na ga ba ku rage komai ba.
Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na
fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan
ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai
madara da kwakwa a ciki. Ya kwashi girkin
nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da
shi, ya cinye nasa duka. Na yi yar dariya tare
da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya
kyalkyace da dariya. Me kike son cewa? Na
kwashe kawai na wuce kicin. Ya ci gaba da
cewa. Ko fiddo maganarki yarinya, so kike
kice ina da ci ko? Kin manta garinku kenan
lokacin da kike ba ji abinci halan? Daren ranar
mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai
ban dariya na dan Ibro. Washegari kuwa
tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai
ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa,
kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna. Na
yi ta murna, tamkar Inna ce gabana. Goma na
safen washegari ya bar gari da alkawarin bai
wuce sati daya ko biyu. Nanji dadin tafiyarsa
saboda na sami damar sakewa in yi karatun
littattafan da ya sawo mini da fina finai.
Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando
kwando aka kawo tare da dumbin godiyar
dawainiyar da ake da shi. Kullum idan Yarima
bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau
uku karanci. Kamar daga sama ranar wata
asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta
guda biyu. Na ji dadin zuwanta sosai, saboda
itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga
bangarensa. Na zubo mata abonci dankayan
makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi
tana mini nasihar na rike mijina, kuma na
dage da addu'a. Da za ta tafi na zubo mata
dambun naman kaji cikin wata katuwar
samira, sannan na kunso mata snack na ba
daya daga cikin barorin na ce ta rike mata. Ta
dinga yi min addu'a sannan ta tafi. Kwanan
Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi
nan zai hau jirgi yau zai dawo. Nan da nan na
fara shirye shiryen tarbarsa. Ga mamakina har
kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina
sauraron zuwansa, amma shiru! Na kira
wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi
matukar tashi. Baccin da ban sami yinsa ba
kenan har garin Allah ya waye.
Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani
labari. Haka na ci gaba da aiki kamar wadda
kwai ya fashewa a ciki. Ina cikin harhada
kayan abincin maimartaba na jiyo alamun
budewar kofa, da hanzari na fito. Ya shigo a
hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi,
kada dai ace maimartaba ya rasu? Ya kamo
hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa
kujera. Humaira tare muka zo da Zarina,
kuma yau maimartaba zai koma fada. Na saki
ajiyar zuciya a hankali. To mene ne abin
damuwar a nan? Na fada a zuci. Ya karkace
kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da
cewa. A dalilin kyautatawarki da abin da kike
aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai
zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu
haka... Na dafe kirji tare da zaro ido ina
shirin yin magana muka jiyo bugun kofa. Da
sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da
gudu. Wallahi su ne! Take na ce Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan
illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna
iza'shi'ta sahlan. Na je na bude ina kara
karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani
tsanani a zuciyata. Su Umma ne a gaba kafin
wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi
maimartaba wasu manyan mutane hudu na
bin bayansa. Sannan dogarawa, a bakin kofa
dogarawan suka tsaya. Rakube nake jikin
oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi
kaina kas. Kutumar uba! Aka biga wannan zagi
da karfi, a firgicr na dago kaina. Ganin
Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce
karshe wajen shigowa. Munafuka! Algunguma!!
Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido,
amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi
zamanta. Da ma ke ce matar abokin Yarima
yar iska? Makircin da kuka hada ke nan ke da
uwarki? To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima?
Na rantse da Allah yau sai ya sake ki..... Ke
wai lafiyarki kalau kuwa Zarina? Duk wannan
cin zarafin da kike wa yar mutane na mene
ne? Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta
kuwa? Cikin dattawan matan nan daya ta
katse ta da fadin haka. Ta hankado keyata na yi
taga taga zan fadi,
kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa.
Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga
maimartaba ya zauna a duke. Ganina jikin
Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara
zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi
la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada
wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da
masaniya kan maimartaba ya haramta aurena
da Yarima ko bayan ransa. Sau biyu tana
kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa
banda kuka babu abin da nake yi, saboda
tashin hankali. Ni ba na Gimbiyar ya fi
damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai
yanke a kaina kawai na ke ji. Wuri ya
harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya
su kuma dattawan wasu na goyon bayan
Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon
bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta
kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta
aibanta Yarima gaban iyayensa. Duk wannan
hargitsin su

Please Login or Register in order to submit comment