Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan kiraki idan na sauka. Na bawa
qanena lambarki duk sati zaya dinga sako
maki kati kinji? Ban san lokacin da nace
haba harda wahala kuma? Yayi murmushi 'a
wurinki yake wahala' hmmm to na gode.
Zan kashe wayata sena kiraki idan mun
sauka. Nace to masha Allah. Dai dai lokacin
da muka isa dak, 'keda wa kuma ko kin
turamata lambar ne? Nace a'a ibrahm ne
tayi murmushi yayi kyau, nayi yar daria 'kai
inna na lura kina cikin gwamnatin mutumin
nan. Ai dole humaira yaron daya so naka ba
don wani abu ba sbd Allah kuma dangi da
yan'uwansa basu nuna kyama ba dole a
soshi Kema harda yarinta ke damunki
bazaki abnd nake nufi ba sai nan gaba.
Bakina yayi SUBUL DA BAKA nace ina fa?
Inna gurin shi daban yake a zuciata wanda
yayi sanadiyar rabuwata da ciwona ai
alhairnsa bazai gushe ba a zuciyata. Cikin
raina nace kema kenan inna ni kuma nace
me? Wanda ya cusa min soyayyarsa da
karfin tsiya ba tare dana farga ba. Wayyo
Allah wayyo sarki ya samu cikin damuwa.
Na maida kwallar data zubo min. **
N9,035 muka kirga cinikinmu na awara na
yau inna ta kalleni tana yar dariyar jin dadi.
Kai Alhmdllh humaira mungode Allah ya
taimaki yarima ya rufa masa asiri shine silar
wannan rufin asirin da muke samu. Nayi
murmushi inna kullum sai kin min fadan na
manta dashi gashi ke har yau kinsa
mantawa dashi shin kin kasa mantawa
dashi inna yaushe nima zai gushe a raina?
Ni kuwa kinsan shawarar dana yanke mana?
Nace a'a tare da smiling don na kula zancen
nawa zata kawar. Kinga muna da yan
kudinmu na sana'a da wadanda ke ajiye me
zai hana musa a gina mana daki babba daga
can gurin tukwanen ruwan can mu koma
wann kuma ya koma kicin sbd damuna? Na
buga tsalle kwarai inna kin kawo shawara
amma a gina mana ciki da falo yafi sirri. Ai kudi
na keji humai, inna In
Shaa Allah zasu isa har ayi rara dayawa. To
shikenan dama inaso mu fara siyan kayan
aurenki d an gama kada muji kunya ISA
inna bazamu taba jin kunya ba Allah daiya
kara rufa mana asiri tace amin. Kullum
adduarmu kenan kuma Alhmdllh muna
ganin budi. Babansu amira inna taba kudin
siminti da yashi washe gari aka fara aikin
da misalin 1pm nakaiwa masu ginin abnc
kenan mukaji sallama kallo daya nayi mata
nagane ta jikina ya mutu murus wani
yanayi ya dawo min sabo. Tunda ta shigo
idonta yake kaina da sauri na nufi daki inna
mun shiga 3 ga innar...... Tsaye tabarni tayi
waje da gudu cikin rudu, mashaa Allah jiki
yayi kyau, ta fada tana murmushi. Inna tayi
ajiyr hrt ta karasa tana yar dariya tace
maraba lale sannunku da zuwa. Na fito
daga dakin bayan sun zauna narakasa na
gaidasu kaina kasa. Humaira ya jikinku ya
bayan kwana 2? Nace ya warware Alhmdllh
ina sunkuye da kai kasa. Na mike ina
kokarin kawo musu ruwa da abnc tace
zauna humaira ina zakije?
Kaina kasa naceabnc
zan kawo muku da ruwa, tayi yardariya tace
Allah sarki wllh a koshemuke mungode
Allah ya bada ladarniyya. Kowa na dakin
yace ameen, nakoma na zauna kamr yanda
ta bukata.Hameed ya turoni yace inji lfy kia
barkaratun? Banyi mmki ba sbd nasanamira
ce ta fada masa, inna ta fahimcihalin da
nake shirin shiga don hakatayi saurin gaya
mata abnd ya farugaba 1. Tayi jim to Allah
yasa haka yafialkhairi a gareki inna tace
ameen, tamike mu zamu koma ta fiddo
kudimasu yawa ta aje a kusa dani ga
wannasai jambaki da hoda. Da kyar
naceangode don kunya inna ce tayi
musurakiya har kofar gida.Ko zama batayi
ba tace kai jamaawadannan mutane suna
kaunarmuhumaira. Shiru nayi kawai sbd
zuwanya haddasa min abubuwa da
dama.Koda inna ta lura saitayi saurin
sauyazancen zuwa lbrn ban dariya. Aini
datace kisai jambaki ba wacce ta fado
minarai sai ummu Ahmad Rufai ta
sokotowacce akafi sani da ummu labour ita
fahar kamfanin jambaki sunsan da ita ita ke
banilbr wai wani
mutum yayi sabuwaramarya jawara ranar
data tare ya fitasiyo musu kaza daya dawo
saiya tararta tasa huluna guda 3 a gaba
tanatakuka ya karasa hnkli tashe amarya
yaakayi ne ranar farin cikinmu kina kuka?
Yace kiyi mgn wadannan hulunan fa?Tace
hulun nan da kake gani wannranar da aka
daura mana aure ya rasuwann kuma ana
shirin kawoni gidansaya rasu shi kuwa wann
ranar da akakawoni gidansa ya rasu kaga
kuwa dolenayi kuka ta sake rushewa da
kuka.Da jin haka sai ya cire hularsa ya
jefamata saiki kara kice wann kuma
wandaya gudu ne har ya bar miki kaza
dagidan shine gaba daya haba! Saiyakwasa
a guje! Hahahahahahha bansansanda na
kwashe da dariya ba. Innatace tsaya ma kiji
wani lbrn wasu barayine su 2 suka sato
lemuka basu tsayako ina ba makabarta
suna cikin rabosaiga wani mutum yazo
wucewa saiyaji ana cewa kai ga naka niga
nawa!Haba saiya ruga da gudu ga liman
daisarsa sai yace Allah ya gafarta yanzunnan
da zan wuce ta makabrta najimala'iku suna
rabon yan wuta da yanaljanna, liman da jin
haka yace ai saimuje muji wann ilimi ne
babbab mefadakarwa, suna zuwa sai sukaji
ana toga sauran naka ga nawa sai dayan
yaceka manta akwai saura yace
wannekenan? Yace wadannan biyun
dakewaje fa? Haba! Su liman sai aka
dafekeya wann ya wuce wancan wancan
yawuce wannan hahahaahhahahaah!Wayyo
cikina inna ta sani dariya hardakifawa
Inna na jin dadin dama ina kaunar
labarukan ban dariya. Ta kara cewa, sai
wasu abokai su uku su ka kai matansu
haihuwa asbt sai ga nurse tace ina mai aiki
a twintower? Yace gani tayi dry tace cngrts
matarka ta haifa maka twins. Tana komawa
ba da jimawa ba kadan tadawo ina wandake
aikin 3 crown? Gani kasami yan 3. Dayan
naji najin haka sai yafashe da kuka lfy? Ni
ina aiki a 7up ne... Narike cikina wayyo
duniya inna shi bazai hakura ma azo kanshi
ba yana tsoronkada ace an haifa masa yara
7..nakara kyalkyalewa da dry, cikin dry
nace nima tsaya kiji wani inna akwai wani
mai arziki yanada matarsa daya da dansa
junior da yar aikinsa budurwa kyakkywa
merry da kuma yaron gida suna zaune cikin
jin dadi komai a wadace wata rana maigida
ya kawo giyarsa mai tsada ya ajiye a firij
yafita da niyyar in yadawi ya sha.yaron gida
yabude firij yanaso yasha ruwa sai yayi ido
4 da giya kawai yakwashi giyar yashanye tas
sai yacika kwalbar da yogot.aka duba giya
tazama yogot oga ya kwalaqaYaron gida kira
bulus ya amsa......(dayake nasan duk kunsan
labarannan bari Na tsallakesu ANaM Dorayi) ta
kyalkyale dariya haka
mukayi ta labarai maau ban dariya. Raina
yayi fes namanta da duk wata damuwa.
Zuciyar innaZuwar mahaifiyar yama gushe
kwatakwata daga raina. Wayar amira ta
katseni daga dariyar na kara wayar a kunne
lokacin sauran yar dariyar. Turawa sa kwai
nafada cikin zolaya tayi murmushi mai fidda
sauti to ya son ranki? Bugowa nayi ince don
Allag ki aikawa inna wayarki mu yi magana
nanemi tata ban samu ba yaya kuma yace
baya gida.. Nace bari nakai mata wayar da
kaina zan kiraki idan na isa
Na sahidawa inna sannan nasaka
hijabina na tafi. Zaure na tarar dakofar
dakinsa bude nayi mmk da farkoamma da
nayi wani tunani sai nagawautata watakila
lokacn ya shigo. Daisata ko zama banyi ba
ta bugo saidasuka gama sannan muka gaisa
ina yardariya nace naga yayan ma ya
dawo.Ban rufe baki ba tace na ina? Shi
fabaya ma gari bako yayi wllh ko
dagamalufashi ne sun daiyi waya yace
yanahanya. Wann furar ma shina
siyowa.Nace Ayya ta mike bari na kai
masanayi saurin karba haba inna kawo
nakai masa meye amfanina dama
nasanrashin dan aike zaisa kikai da
kankitunda gani ai shikenan. Tayi
murmushito humaira Allah yai albrk yas
amugaaurenku lfy. Nidai nayi gaba
kawai.Kishingide yake na kunna kai
wanikamshin turare ya dokeni fuskarsa
rufeda littafi nayi sallama da sauri ya
dagokai mukayi ido 4 domin kuwa idona
nakansa. Ya Salam! Naji ya fada a hnkl.Ina
wuni ga fura inji inna.ganin bashida alamar
motsawa yasa na ajiye masana juya. A hnkl
yace donAllah dawo!Cak na tsaya tare da
juyowa na kalleshiya daga kai. Karki gujeni
ki dawo gareniwayyo ni ashe yaudarata ake
baki mutuba HAFSAT!!! Gabana yayi
muguwarfaduwa na zaro ido na dafe kirji
Ni? Yamike zai nufoni cikin wani irin
yanayiidanunsa har sun kwao kwalla
sainakwasa a guje nayi wurin inna.
Yadda ta ganni yasata firgici ke Humaira
menene? Itama duk ta firgice.. Shigowarsa
yasa inna yin shiru, nikuma nakara matsawa
kusa da ita sosai..durkusawa yayi gwuiwa 2
kamar mai neman gafara, sai kawai yafashe
da kuka.. Inna wacece wannan? Don Allah
kar kice mini ba Hafsat dita bace, wayyo ni
dafwan, Allah ka kaddareni da jin tabbacin
Hafsat ditace domin nashiga shakkun
wannan sbd ta nuna tsoro a gareni sai
yakara fashewa da kuka dai dai kuma
lokacin Yaya yai sallama.... Na rikice na
rude hankalina ya dunguzuma sai kawai
nima nafashe da kuka ganin cewar wani
balain ne ka ke neman haye min.
Subhanallah inna meke faruwa ne? Inna ta
rausayar da kai tonima sun sakani cikin
rudu wlh. Cikin kuka nace inna yadai
sakamu ni wlh ban san shi ba Yaya, don
Allah yimasa bayani fada masa cewar ko ni
wacece.. Wani kallo yayi min kafin ya kawar
da fuskarsa har lokacin kwalla ke fita a
idanunsa kamar anbude famfo. Nadafe
kaina, shin kowace mace haka take samun
wadannan kalubalen ga maza, kokuwa ni
tawa halittar ke da haka? Da kyar Yaya ya
shawo kansa abinka ga fari mai idanu fuskar
nan tayi jawur, musamman hancinsa,
idanun suka rikide suma sannan girmansu
yakaru... Yanayi yanda inna fa Yaya ke
masa bayanu yasa shi kara nitsuwa,
nitsuwa irinta sauraron magana don a
fahimta. Suna gamawa ya kalleni wasu
siraran hawaye suka biyo baya.. Na yarda
Inna sannan na amince amma don Allah ku
rokar min ita idan zata maye mani gurbin
Hafsat.
Da sauri nace an
fidda min miji kayi hkr bana.... Inna ta dalle
min baki. Yayi murmushi mai nuna daci da
kuncin zucia. Humaira sunanki bayyi kama
dana marasa tausayi ba ki tausaya min ko
don halin dana shiga donAllah.yaya ya dafa
kafadarsa wane hali ka shiga safwan? Yayi
dan smiling tsaya kaji LABARI na: ina dan
3yrs mahifiyata ta rasu don haka na tashi a
hannun kishiyarta. Ni kadai ta haifa ita
kuma tana da yara 4, tunda na tashi naga
mahaifina yana yawace yawacen kasashen
dunia don gudanar da harkar kasuwancinsa
wato ba mazauni bane, yana int'l biz. Na
tashi cikin wahala da azaba irinta kishiyar
uwa sai nayi bara gidaje nake samun abncin
da zanci kamar yanda umma ta umarceni
duk da arzikin mahaifina kuwa. Sakamakon
dangin mahaifiyata ba'a nan suke ba yan
asalin yamai ne ta jamhuriyar nijar su kuma
dangin mahaifina an rasa wanda zaiyi
hobbasa kada tayi zuga ya daina basu abun
arziki. Taimako daya da Allah yayi min skul
1 mukeyi da yayanta tayi ta rabamu
Abbana yakiya amma fa ko ruwa bana tfy
dashi. Tun ina kukan yunwa harna daina
gashi ba'a tadamu sai karfe 3. Da mun
koma ggida sai islamiyya hakan ya zame
min jiki abnc baifi na samu sau daya a rana
ba shima sai bayan maghrib idan nayi bara.
Allah mai tausayin bayi na shiga wani gida a
bayan gidanmu naga wata yrny da
sharbebiyar wuka cikin dabara na dauketa
zuwa cikin gidan. Zaune suke ana rabon
wasu kaya kamr tsaraba nayi sallama tare
da gaidasu nace wann yrnyr tafita da wukar
nan tana wasa ai nan da nan suka dau salati
suka rude sukaita samin albrk sukace daga
ranar na dinga zuwa karbar abnc. Abin
mmki Hafsat kullum bata cin abncinta sai
nawa har muka shaku sosai da ita
mahaifinta yasan shakuwqrmu har aka
sanya mata hafsar safwan. Da yake sunsan
ni da lbrn wuyar da nake sha saina koma
kamr dan gidan. Lokcn da tafara girma sai
muka juye soyayya wacce ita tafara bullo da
hakan. Kowa ya fahimcemu har iyaye sun
bani ita. Kwatsam muka tafi karatu akayi
mana waya bata da lfy ana gobe zan taho
ganinta aka karamin waya TA RASU...... Ya
fashe da kuka.... Gashi ban taba soyayya
da wata ba ban shaku da kowace mace ba
sai ita. DonAllah ku taimakeni kuce Hafsat
ce wann wllh kamr su daya. Wani takaici ya
rufeni bawai na rashin tausayin sa bane a'a
kawai yana musulmi zaiyi wasa da
imaninsa. Wallh gwara matsalarsa da tawa
shifa mutuwa tayi ni fa? Gashi da rai amma
yayi min nisa nisan da bani tunanin zai
dawo gareni nima saina fashe da kukan.
Kamr inna takaranci zuciata saita karyar da
murya tace Safwan! Inason ka tuna cewar
kai muslmine wanda yayi imani da Allah ko
kafirai sunyi imani da mutuwa ballantana
kai musulmi ashe kayi imanin wanda ya
mutu zai dawo? Ya girgiza kai a'a inna, ta
bata fuska wallh kayi mana tunda gashi
kana kiran wata da Hafsat. Ina
mahaifyarka? Maiyasa ita bata dawo ba sai
hafsat? To ahir dinka wllh kaji tsoron Allah
kayi imani a mutuwa don akwai ta kuma
duk wanda ya muutu baya dawowa har
abada. Sai naga yana goge kwalla alamar
maganr ta shigeshi. Wann yarnyr sunanta
humaira haifaffiyar nan ce kawar amira ce,
kusan tare mukai goyonsu da mahaifiyarta
gidan su na can gaba da an sha kwana snd
haka..... Bakomai inna wllh kamr ce har
tayi yawa shiyasa.... Allah yafi da haka bai
kamata ka firgice haka ba sbd soyayya har
kayi sabo. Ya karkatar da wuya wllh inna
bazaki gane ba amma bakomi ni yanzu ki
taimakamin da yar taki donAllah... Kafin
inna tayi magana ninayi ina mike nace kayi
hakuri anyi min miji.
Ban jira wata mgn ba nayi waje cikin
fushi.ko zaure ban fita ba wayata ta dauki
kara kmr abin jira, alamun kira ne ya shigo.
sunn Ibrahim ne alamar shi ya kira, na lafe
bakin kofa sbd na tsani tfy ina waya kmr
wata sabon shiga.sllm nayi kafin ya amsa,
sai da yayi wata ajiyar zcy na yi dan
murmushi sbd inda sabo na saba da jin
hk.A hkl yake maganar kmr mai tsoron
furta kalmomin, "Humaira zcyta Zata fashe
kaunar ki ta hanani aiwatar da abinda na zo
yi, ki taimakeni na turo a daura mana aure
ckn satin nan a kawo min ke ko na sami
sukuni".ban San lkcn dana kyalkyace da dry
ba nima ckn zolaya na ce, "to na taimake
ka".
Ya yi murmushi mai fidda sauti wani
abu ya taso min wnd nake ji kullum idan na
kasance ina irin wnn hirar, na runtse ido
kawai. Ya kara narkar da murya, "wlh da
gsk nake na takura mata nake so kusa
dani".Na bude idona ina jin alamar kwalla,
amma na daure na maida su tare da
kokarin kawar da damuwar da nake neman
shiga, na ce. " Ibrahim ka zamo mai adalci,
shin mai zai hana ka tafi da matarka don
Allah ka yafe mata mana". "Baza ki taba
gane abin da nake nufi ba ynz matata ta
wuce muguwa, wlh shaidaniyace, ke dai ki
dage da addu'a Allah ya tserar da ke daga
sharrinta".
Gaba daya jikina ya yi sanyi, gaba na
ya fadi, tsoro ya kama ni, amma sai ban
nuna masa hakan ba, sbd ina son jin tushen
mgnr. Ina 'yar dariya nace. " Nima abin ya
shafeni kenan?" "ku san haka, sbd wai ta ji
ana mgnr neman aure shi ne ta bugo mini
waya jiya da daddare cewar wlh sai ta gano
ko Wace ce, km sai ta kashe ta ko ta yi
sanadiyar nakasata kin ji muguwa". Ckna ya
bada wani kululu. Na zaro ido tare da dafe
kirji. Ya yi murmushi, " kin san wnn ai
haukane, ni dai sai kawai na bi ta da karya
ne dona zauna Lfy.
Ibrahim da na daure na cije ba don
ina sonsa ba, kawai gudun bacin ran inna,
shi kuma ga Inda tashi matsalar take. shi
kansa yana tsoron sharri da tuggu na
matarsa ina ga ni karabiti? shin in fadawa
inna ko in yi shiru? Fadar babu abinda zai
janyo mata sai tashin hkl da rashin
kwanciyar zcy. wayyo ni Humaira ga 'yan
uwan ubana sun tasoni a gaba, kr2 ma sun
hana mini sbd jin zafi da bakin ciki,
Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un. kai dole in
sanar da inna, domin itace mai yi mini
addu'ar da Allah zai amsa da gaggawa. A kfr
gida na tarar da su tsaye kallo 1 nayi musu
na gane 1 daga cknsu shine muka hadu
wurin biya wa su Aisha kudin makaranta na
farkon zango
Ni sai da ma na ganshi na tuna ban kai kudi
an aka sanyo musu baje ba jikin uniform
din. Da fara'ata na karasa sbd ban mance
taimakon da yayi mana ba, na cika mana
#30 sbd babu canji a lkcn, ya ce mu bari zai
bayar. Har Kasa na durkusa don gaida su.
Ina murmushi nace, "Mun fa gode ". Ya yi
murmushi, " wai ni har ynz gdyr nan bata
karewa? "Na yi 'yar dariya kawai. Abokin
yace ," Nan muka zo gurin musbahu tun
dazu muna nan unguwar sai ga kannenki
(su sumayya) za su tafi islamiya, abin
mamaki yaran nan suka ganeni. shi ne suka
gwada mini gidanku nace bari
"Eh wlh nan baya na je kai wani sako
". Abokin yace, " to madallah, mu zamu
wuce sai wani lkcn ". Na ce, " to nagode ".
Na wuce gida Ina kallo ya Kai masa duka da
harbi na yi kmr ban gani ba, na yi ciki
abina. " wai lfy kika dade hk? ko lbrn ne
naku ya tashi ke da innar taki? " Ta karasa
mgnr tana murmushi, na ce. " Humm bari
inna na zauna tare da ba ta lbrn duk abinda
ya faru hr wayarmu da Ibrahim ". sai na ga
tana dry.Na bata fuska." to me zan yi? "
"Duk ciki banga abin dry ba sai na kuka kika
gani? " " wlh ba komai ke dai ki ci gaba da
addu'ar Allah ya warware mana, wlh nasa
Allah ma ji rokon bawansane, ba zai ki
amsar mu ba, wataran sai lbr, INA lkcn da
Zaki tuko zukekiyar mota ki zo kina alfahari
da mijinki".
Na yi murmushi, " waye inna?" " Allah
kadai ya sanshi". Mafarkina suna nuna min
mijinki sai dai har yau banga fuskarsa ba, ni
na San..." sllmr su Baba Auwalu ne da wasu
dattawa guda 4. Ckn ladabi na gaida su tare
da yunkurawa zan tashi ya dakatar da ni.
Inna ta mika musu tbrm 3 suka zauna, Baba
Auwalu zakakke shi ya fara mgn.Abu 1 ya
kawo mu nan mgnr Humaira gabana ya
fadi. Wani ma'aikacinmu ne yaga Humaira
yana so shi ne ya turo abokansa su ji masa
mgn, to na fada musu gsky yrnyr ba ta aje
kanta nan ba mai kudi take so, ko dan
sarauta ko kuma likita mai kwasar albashi
da tsoka. wnd ta sami daurin gindi daga
uwarta aka maishe da iyayenta maza
banza.
ko da Allah ya azurta 'ya'yanmu da
auran masu kudi ba tallarsu mukai ba, sune
suka biyo su har gida, muna kora suna
likewa don hk nace gwara mu zo su ji daga
bakinku. Tashin hnkl ba'a sa masa rana,
wnn cin mutunci da wulakancin ya isa.Na
kalli dattawan akalla kowanne zai yi 55-56
yrs wai abokinsu ne ke sona, Yaushe ya
ganni, km a Ina? wnn abu daga ji tsarine km
salon wulakanci da tozarta ne. " ku nake
saurare shin akwai wnd kuka fidda mata ko
mu je a amshi sadakin wdnn?" Gabana ya
fadi, ni da inna muka yi kallon-kallo sai
kawai naji kwalla na bin kumatuna. " Allah
kai ne gatana" Abinda kawai nake fada a
zcyta
Inna ta yi Kasa da murya, " Alh. akwai
wnd suka daidaita da shi ynz hk mu yake
saurare sbd hk a yi hkr za a turoshi". Nan
da nan ya fusata, " kin ji ko? me na fada
muku? ku tashi mu tafi idan sun san wata
ai basu san wata ba".Ya kalli baba jamilu, "
ka zama shaida mun baku nan da kwana 7
idan babu wnd yazo, to wlh mlm Datti zan
bawa". Ya kalli dattawan, " ku ce masa ya
zauna ckn shiri don baza mu yrd a yi mana
abin fada a dangin ba, duk take-takenta ta
lalata mana 'ya".
Idan da sabo mun saba da jin wnn klm
dk muka yi shiru ni da inna. suka bar gidan
ckn korafe-korafe, shin me muka tsare wa
su Baba? wnn amsa har yau na Kasa
samunta. Hnkln ya tashi na dinga risgar
kuka shin wa zan fiddo ni Humaira? Abinda
kawai nake nanatawa kenan, inna dai tayi
shiru abinta. Zaune nake bakin kofa ruwan
koko kawai ke cikina, sai 'yar madarar da
na sanya masa gaba daya na rasa inda ke yi
mini dadi. Ni kadai ce a gidan inna ta tafi
gadon kaya barka, Sumayya kuma sun tafi
mkrnta.
Hnkln ba kwance yake ba domin bani
da tudun dafawa, Ibrahim ne hnnna km ynz
ba na ko san jin mai sunan, dama a dosane
muke gashi km ya billo da matsalar
muguwar matarshi har abin na niyar
shafata. Ya zan yi? Ban sami amsar tmbyr
ba wayata ta yi kara, shi din dai ne naji kmr
kar na dauka. Yau ma kmr Klum ya fara
rokona da hr zan ki fada masa, amma sai na
ga 'kara na sanar da shi wata kila shi yana
da dabara tunda inna tayi shiru tun jiya
bata ce min kala ba. Na kwantar da murya
abinka ga Wacce ta sha kuka, ta kara
raunana. Na kira sunansa, gaba daya naji ya
kidime sbd ban taba ba. Ina saurarenki
Gimbiya ". Ya fada ckn zumudi.
Na had iya wasu hawaye da ke shirin zubo
mini na fara mgn a hnkl. " A gsky ina cikin
matsanancin tashin hnkl, iyayena sun tasoni
a gaba akan yin aure shi yasa aka
tsaidamini kr2. Yau ya zo mini da tsoho
cewar ya bani 7 days na turo wnd zan aura,
ko ya aura mini shi, to a gsky Ibrahim a ynz
Ina tunanin auren tsohon, domin ba zan
boye maka ba, a gsky ban taba jin sonka a
raina ba, amma ina tausayinka tare da bin
umarnin mahaifiyata don faranta mata rai,
wnd har na fara jinka a raina. To sai da da
mgnrmu ta jiya tasa na hkr da ki, sbd tsara
da raina, da kuma lfy ta.A gsky kmr ydd
kake jin tsoron sharrin matarka nima hk
nake tsoro.
sbd hk ni dai ga ni ga Allah, sai na fashe da
kuka a hnkl. Iyakar tashin hnkl shima ya
shiga, ya rude."saurara Humaira, dan Allah
kiyi hkr, saurare ni mana". Na dan tsagaita,
"wlh.. wlh Humaira babu abinda zai same ki
ynz hk sbd ke nake neman aiki nan kasar,
wlh ba zan zauna da ke ba a Nigeriar
ballantana ma wani abu ya faru, amma ki
kwantar da hnklki, na rantse da Allah
Humaira duk na fadawa dangi da iyaye don
a yiwa tufkar hanci. kin san kuwa bazan ta
gifta raina akan kry ba don Allah ki taimaka
mini". Na dan ji sanyi, amma duk da haka
na ce.
"To shikenan ba komai ke nan zamu yi mgn
zuwa jibi idan mun gama shawara da inna ".
Ya ce, " Ba matsala ". Ya dinga lallashina
yana ba ni 'yar dry snn muka yi sallama.
Har lkcn dai kaina bai warware ba yana
daure ckn rudani na yi shiru. Rayuwa mai
daci, wayyo maraici yau da mahaifina yana
da rai, wa zaiyi min wnn musgunawar? Na
dinga sharara kuka ba kakkautawa, sai da
na yi mai isa ta snn na yi shiru. Na zaro
wayata na latsa lambar Amira, bugu 1 ta
shiga. Tana dauka tace."'yar halak ynz kuwa
nake batunki".Na ce " ko?" " wlh kuwa ya
gida ya kano? "
"Kano gatanan Amira tayi mini kunci".
"kuncin me Humaira?" Ta fada ckn
damuwa. " Amira zaman gida ya janyo mini
matsala". Na zayyane mata abinda da faru,
ta fara salati, snn na fada mata kuma ydd
muka yi da Ibrahim. Na ci gaba da zubda
hawaye. " sbd hk ni ynz gsky Amira zan
amince da dattijon da in kai kaina halaka".
"A'a Humaira, amma yaya ya fadamin akwai
wani abokinsa safwan, kinga shi Yaro ne
bashi da matsala..." " wlh Amira baki ji ydd
na tsane shi ba, Sam bana kaunarsa don bai
kwanta mini a rai ba".Ta ce, " Innalillahi
wa'inna Ilaihi raji'un. Ynz me ye mafita?"
Na ce, " Dalilin kiranki kenan, dan ki nema
mini ita?"
Ta yi shiru, har sai da na ce, " Hello".Tace
"ina jinki Humaira, wai nazari nake yi,
amma ki bari zuwa gobe gobe zan kira ki".
Na ce, "Ba matsala ". kafin inna ta dawo
har na daura sanwar awara, duk da jikin
nawa ba dadi. Ina shirin fara tuya ta shigo,
" sannu Humaira ". Abinda tace dani kenan.
Na ce, " sannunku inna da hny". Ta matso,
" kin kuwa ci abinci? ko ba ki ga tsakanin
jiya kawai zuwa yau ydd kika yi zuru-zuru
ba? "Na dai yi shiru. " kada ki sanya
damuwa ga al'amuranki, ki fauwalawa Allah,
shi ne mai maganin damuwa". Na ce, " to".
Ta fiddo kullin nama har da zafinsa da
lemon kwali ta miko mini, na samu na
cunkusa da kyar kada ranta ya baci.Aiko sai
gashi naji dan karfi-karfi.
Da daddare muna zaune aka aiko sllm dani.
Na sami kallon inna naga ni take kallo, na
cewa yaron. " ka ce ina zuwa". Ya na fita na
kalli inna ckn muryar kuka, " shin inna me
fitar nan zata yi mini? Wlh yaron nan banda
shirme babu..." " kwarai kuwa gara ki zauna
a cigaba da zarginmu tunda yara ne ba
masu mota ba ko? " mikewa kawai nayi ba
tare da na kara cewa komai ba, idona Taf
da kwalla. Raina kmr ya fita, zcyta sai zafi
take yi sbd kuna, wayyo ni Humaira. Ina
fita na kalleshi, sai naga safwan ne wnd
muka hadu gidan su Amira. Da ban yi niyar
gaida shi ba, amma sai na daure muka
gaisa. Idanuna suka suka zubo da hawaye
na kalleshi, " Don Allah ka yi hkr zan koma
gida akwai aikin da nake yi".
Yayi murmushi, " To naji, amma kukan fa na
mene ne? ko duk aikin ne? " Na runtse ido
mgnrshi ko na ce tmbyr ta soke ni kmr
mashi. " Humaira ban boye miki
damuwataba, don me Zaki boye mini taki?"
Na kalle shi, " Ba ni da damuwa sai Wacce
kake neman saka ni ciki, don Allah ka rabu
dani na koma gida ". Na rushe da kuka tare
da durkushewa. Shi ma durkushewar yayi,
tare da sassauta murya. " Haba Humaira
ynz Amira ta kirawo yayanta muna tare, ta
sanar da shi wayar da kuka yi. Don me zaki
damu kanki? ki share hawayenki gani na zo
zan je na gabatar da kaina wurin iyayenki,
wlh Zaki same ni mijin da kowace mace ke
mafarkin samu, zaki yi alfahari da aurena".
A tsiwace na kalleshi ina girgiza kai, yayi
Kasa da murya.
"Ki yi hkr, nasan baki sona, to wlh zan yi
hkr har zuwa lkcn da Zaki so ni, ni ma
marayane Humaira, matsalar mu daya ynz
haka nima irin auren da za a yi miki ake son
yi mini a gidanmu". A langabar da kai ckn
zubar hawaye, " safwan wlh ba zan iya
amsa maka ba..." "sbd me? " Na kwantar
da fuska, " Baza ka gane ba ". Ya yi
murmushi, " zan gane Humaira, fada mini
shin

Please Login or Register in order to submit comment