Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in
riga ki isa gidan mugani. Ya fita yana yar
dariya, yau saida muka hadu da amira a
hanya ta makara ni kuma nayi rana a
gurguje muka gaisa ta wuce a kofar
lungunmu na tarar da tankamekiyar motar
mmk ya kamani wato da gaske yake zai
rigani. Daga bangaren yamma a inuwa yake
zaune da wasu jakunkuna manya guda biyar
inna kuma na can gefe idanunta jawur da
alama kuka tayi. Wata irin faduwar gaba naji
wadda ban taba jin irinta ba na karasa
gabanta na dafa guiwoyinta nace inna lfy?
Me kayi miki naga idanunki sunyi ja? Ta
kara fidda kwalla tace dinkuna ne yayo
mana kowa akwati guda sai kayan
kwalliyarki shima akwati guda tsoro
+fargaba ya dabaibayeni da kalamansa tare
da cewar kada mu butulcewa rahmar
Ubangiji domin shima bayin kansa bane.
Taci gaba da kwarar hawaye nima
kawai sai naj kukan ya subuce min
musmmn da aisha ta fara bude min kayan
ina kallo. DonAllah inna kiyi hkr kinga har
kin sa itama ta fara abnka da ruwa-ruwa. Ya
mike na barku lfy inna danAllah kuyi hkr
saina kara zagayowa ya fice. Mun dade
muna sharbe kafin mukai kayan daki su
aisha har an fara gwadawa da takalma kala
5-5. Inna ta kalleni humaira naso kama
yaron nan akan abnd nake zargi amma
saina rasa hanyar da zanbi sbd hausawa
sunce idan baka iya kama barawo ba shi
saiya kamaka. Kuma shirun nawa yayi
amfani domin daga nasihar tasa na gane
cewar haduwar jinin kawai da kuma
tausayinmu da Allah ya dora masa. Tsoro
na daya saka kayan nan mu shiga jama'a
anya baza'a zarge mu ba? Kafin nayi
magana mukaji sallamar baba Alh Sheetu
inna ta amsa ta fito da sauri daman da
hijabi a kanta. Duk muka fito ya kalli inna
me kike nufi da hanamu albashin humaira
ko kuwa kina tunanin zaki cinyesu ne ranar
aurenta kibarmu da siyan kayan daki kinci
bulus? Ya girgiza kai zaki dinga bamu rabi
duk wata kuna amfani da rabi wann shine
babban adalcin da zamuyi miki idan kuma
kin amince zaki aurar da ita ne toh! Inna ta
sunkui da kai a'a yaya ai bansan haka tsarin
yake ba tuni na aiko bari na dauko maka, ta
shigo daki bata ko kalli inda muke ba yace
maza dauko tunda kinaso ki koyawa yarki
son abun dunia shiyasa kika dage abar miki
yayanki don kiyi jari. Inna dai batace komai
ba ta mika masa 10k ba kunya karba tare
da tusawa yace sun cika dama an fada
mana 20 ne nayi ta mmkin ina yaji? Ya mika
mata yar leda daga aljihunsa ungo goron
sanya auren mansura ne wato yarsa sati 2
masu zuwa. Inna ta shigo tare da wasance
maganar makarantar su sumayya. Batayi
min zancen ba nima na tsuke bakina sbd
munga abnd yafi hk. Da dadaare yaxo na
tsinci kaina da faduwar gaba na fita da
kwanon fura ba tare da nace ya shigo ciki
ba sbd banason hirar ta dade kamr kullum
jikin nawan ina jinshi wani iri. Muka gaisa
nace ga fura. Ya karba amma yau kadan ya sha
na maida sauran gida na dawo. DanAllah ka
rage zuwa min dadare kaini ziyarar ma gaba
daya kadaina idan baka iya dainawa ba. Sbd
baki damu dani ba? Ya fada cikin yanayin
takura nace a'a. Da kinsan abnd ya kawoni
yau wllh da baki fada ba amma bakomai.
Tausayi naji ya bani har saida idona yayi
kwalla nace kayi hkri danAllah. Idan banyi
hkri dake ba humaira ya zanyi? Damuwata
na kawo miki kamr kullum su fareda sun
hada min tuggu mai martaba ya kirani wai
sati mai zuwa sunan nan tafe za'ayi bikinmu
da gimbiya kuma ana gama daurin aure
zamu tafi gaba daya zuwa yola. Gaba daya
hanjin cikina suka kada take suka bada wani
irin kara mai kamar sautin hadari. Ya matso
gabana Humaira mutuwa zanyi banason yin
nesa dake rabuwarmu zata zame.....
Kwallar da nake makalewa ta zuraro kuka
bazai yi mana magani ba ki bamu mafita
domin nasan kinajin yanda nakeji karancin
shekarunki da kuruciya zasu barki ki fahimci
wani abu dake bin jininki... Kiyi mgn kada
nima kiga nawa kwallar. Allah ya sanya
alhairi na fada kamr me koyon mgn, ameen
tunda kin ambaci alhairi saidai inaso kimin
alkawari zanje nayi shawara da mahaifiyata
idan ta amince zanzo in rokeki wani abu
zaki bani? Na kalleshi nawa ne? Kwarai
kuwa mallakinki ne har abada Nayi
murmushi cike da kuruciya ko ince wauta
nace ba komai ko menene tun a yau ba sai
watarana ba idan mahaifiyarka ta amince ka
dawo ka amsa ko kuma tun a yanzu na
baka ka tafi dashi idan taki amincewa saika
dawon dashi. Yayi murmushin dake kara
masa kyau yace what a confidence' kawo
hannunki, nayi hamzarin mika masa sai
naga ya zura min manyan zobuna na gwal
baki bude na kalleshi sai yace na alkawarine
saina sadda kai kasa. Gobe zamuje Kd sai
jibi zan dawo me zan siyoi miki? Nace
bakomai ya watsa hannaye kinyi daidai
gobe kizo da wuri don mu kara bankwana
7am zamu wuce nace to. Maza shiga gida
banda tsawon hira kada a makara. Bacci da wuri
bashi ke sa tashi
da wuri ba sbd uwar makarar da nayi yau
har tafi ta kullum ko wanka bansamu yiba
kwaskwarima kawai nayi inata uban saurin
na isa amma ina! Ana kokarin rufe get har
sun dau hanya sai kurarsu na gani wani irin
zazzabi naji ya rufeni inajin saukar hawaye a
idona. Sashen gimbiya yau aka kiramu
zamu kammala mata kaya tare da wasu
shirye shiryen biki na tsinci kaina cikin
rashin jin dadi ni kadai nasan yanda nakeji a
zuciyata to meke damuna? Yaushe mukai
irin wannan shakuwar da har nakejin haka a
raina? Meyasa nakejin haushin gimbiya a
yau? Wasa sabon aji sabo kuma tirken wawa
bansan cewa na shaku dashi saida dare har
kuka nayi acikin mayafina tsoro da fargaba
suka rufar min na fara zargin kaina kona
kamu da SON SA ne? Bani da yawan
magana haka bani da kazar kazar sosai
amma duk da hk saida inna ta tambayeni
ko banijin dadin jikina ne? Shiru kawai nayi
mata duk wanda ya ganmu a yanzu sai yayi
mmki sbd sauyin da muka samu musmmn
fannin cima da sutura yan unguwa sai
gulmarmu suke kowa da abnd yake cewa
wasu ma cewa suke sata nakeyi a gidan
sarki tuni ftar jikinmu ta fara sauyawa ga
cima me kyau ga sabulai masu gyara jiki.
Washe gari muka shirya zuwa sunan gidan
kawu mande nan mukaga jin zafi da bakin
ciki karara babu kuma wanda ya kula. A
gida bayan mun dawo inna ke shaida min
wai ana gulmar yanzu maza nakebi nayi
murmushin takaici. Maimakon yayi 2days
saida sukayi 4days sannan suka dawo
lokacin gidan ya kacame da hidima duk yan
aiki sun hadu ba maganr sauyi gaba 1 muke
haduwa sai maghrib muke tafiya ba muna
can anata soye- soyenaji ana rade radin ya
iso da bataliyar abokansa harda yan'uwansa
ina jin ana nemana na boye bayan katuwar
tukunyar kaji nida amira muka fito zamu
tafi na hangoshi tsaye sai wurga idanu yake
nasan ni yake nema saina dan boye.
Abayantakwana 4 nan ya kara kyau da
girma muka wuce bai ganmu ba amira tace
min zakije party? Nace Allah ya tsareni.
Amira ta tabe baki nima bazan je
ba nace mata meyasa? Tace ina gudn dizgi
da wulakanci kinsan halin gimbiya
musamman idan ta ga jama'a nayi
murmushi kawai a kofar gidansu mukayi
sallama ina shiga gida na tarar da inna a
tsaye a tsakar gida ko sallama ta bata amsa
ba tace ina kikaje? Zuwansa 4 nemanki ba
kyanan yace duk an duba gidan sarki ba'a
ganki ba? Yar dariya kawai nayi haba inna
da kinsan girman gidan sarki da bakice haka
ba muna can wani bangare suyar kaji kawai
mukeyi. Na mika mata bakar leda me
dauke da soyayyun kajin da aka bamu nace
inna aiki fa mukeyi shi kuma yana can ga
abokansa shiru kawai tayi ta fitar da naman
daga ledar na dauki cinya ina ci aka fara
kiran sallahr maghrib nayi saurin cinyewa na
tashi na gabatar. Na hada goldenmon ina
sha kenan naji ana sallama a tsakar gida
Aisha ta leka naji tana cewa la yaya sannu
da zuwa gabana ya fadi inna ta kalleni nayi
saurin tashi sbd nasan ma'anar kallon koda
ya ganni sai yayi baya kofar gida ya tsaya
inda muka saba. Yace fushi kikeyi dani
humaira? Nayi shiru kiyi hkri wllh gida na
koma na kammala wasu abubuwan kuma
mamana ta amince nazo na amshi
alkawarinmu. Kafin nan ina son ki shirya zan
aiko a daukeki ko inzo da kaina mu tafi
gurin party ko bazaki halarta ba? Gsky ban
zuwa, me yasa? Hakanan, wllh baiyuwuwa
duk mai hnkli bai wani abu saida dalili. Yace
shikenan dauko min tabarma nima ban
zuwa na kalleshi da mmki yayi murmushi
wllh idan ba zaki ba nima ban zuwa dama
tilastani akayi. Na rasa yanda zanyi da
rigmarsa kullum da wacce zai bullo nace
muje ka tambayi inna, da mmkina inna tace
a dawo lfy muka fito yace ki saka leshin nan
ja da takalmi silver kinji? Na daga kai, zan
tafi saina dawo anjima nace to. Ni kadai
nake bidirina a daki inna tana tsakar gida
ina kwalliyata harda ta saman gira na feshe
turaruka na fito tsakar gida inna ta kalleni
ido waje tana mmki wann kwalliya haka
humaira anya baki wuce gona da iri ba? Na yi
murmushi, nace. " Inna ban yi
kyau ba? " " kin yi kyau, amma kmr tayi
yawa".Na zumbure baki da fadin. " wlh inna
haka ake yayi".Ta harareni, "Ina ruwan ki
da yayi? kin ga wlh ki dunga tuna matsayin
ki, kada ki janyowa kanki damuwa".Shiru
kawai nayi. karfe 9 naji ana sallama, na kalli
inna. " zamu tafi, Ina jin shine ya aiko".Ta
ce a dawo lfy, Allah ya tsare".Na ce
"Ameen". Har na Kai bakin kofa, tace."kada
ki wuce 11 dk abinki"."INA". na ce tare da
ficewa. Sbd tsinin tklm ga rashin sabo sai
na dinga takawa a hnkl kada na fadi, ckn
direbobin gidan sarki na gani da alama bai
ganeni ba. Motoci 4 na tarar a jefe, ya bude
min
Wacce tafi ko Wacce kyau da girma, na
shiga Ina addu'ar neman tsari kmr Klum
idan na baro gida hk ya zame min tamkar
sallah. Yana rufewa naji an janyo ni a
tsorace na kalli gefena, sai kawai naga Yrm.
Kunya ta kamani, na ce, " Ba ni na
gyara".Ya sakeni na matsa nesa da shi Ina
fadin. " Ban son haka, don Allah ka
daina".Ya yi murmushi, sai ya matso na
kara takurewa ya ce. " kin yi kyau kmr
ruwa. Cire 'yan kunnen na baki sarka".Ya
fada yana laluben aljihunsa. A ciro bakaken
'yan kunnena dk sun yi baki sbd tsufa. Ya miko
min wata dankareriyar sarkar
zinare da 'yan kunnen ta.Na make hnn,
"kayi hkr bazan karba ba, sbd wdnn
zobunan ma inna tayi mini fada
sosai"."sanya aro na baki ba kyauta ba, zan
karba idan mun dawo".Jin haka na Sanya. "
Ina alkawarin mu?"Na yi murmushi, " ya na
nan"."Zaki bani ynz? ""Idan kana ganin Ina
da shi a nan din".yayi 'yar dry, " Ai ko
Yaushe kina tare da shi".Na ce, "
Bisimillah".Ya yi Kasa da murya, "kada ki
manta kin fa mallakamin tun kafin ki san ko
menene".Na yi shiru kawai. Ya kama
hnnyna duka biyun. "Humaira Ina barar
soyayyarki, don Allah". A firgice na kalle shi
daidai lkcn mota ta
tsaya. Harabar wurin dankam da jama'a duk
hankalinsu kuma ya dawo ga motocin da
suka tsaya lkc guda. Dogarawa suka rugo
suna bude mini kofa, ta kowane bangare
barori kuma na watsa filawoyi. Abokansa
suka rufa mana baya, naja tunga da sauri na
tsaya, suka yi gaba. Wuri na nema na tsaya
kusa da wata mota zufa kawai ke
tsatsagomini ta ko'ina. Na kasa fassara
yanayin da nake ciki.A hnkl naji an dafa
kafadata, kafin na dago naga an zagaye ni.
Na kalli sauran abokansa, nayi Kasa da
kaina. " she is pretty".Na ji wani ya fada.
Na kusa da shi ya ce."Akwai class I see".A
hnkl yace, "Humaira mu je ki bani kwarin
gwiwa, wlh bana son partyn nan ".
wani ya matso, "kada ki biyewa zcy
Humaira, ki tallafawa mai kaunar ki kada ki
jefa shi...""kan uban can". Na ji saukar
uban zagi kmr daga sama, ckn karaji
Gimbiya ce tsaye tana hura hanci gefenta
kawaye da sauran barori na kewaye da ita.
Na zaro ido Ina yin baya- baya ckn
matsanancin tsoro da firgita. " Ni Zaka ciwa
mutunci? Ni zaka kunya ta a gaban jama'a
ka rasa Wacce zaka hada sonta da nawa sai
BAIWATA? Dama duk zame-zamenka a nan
ka sauke? Haba biri yayi kama da mutum,
ban manta abubuwan da suka ringa
faruwaba, sai dai ka haddasa mata fitina,
bala'i da tashin hkl ita da iyayenta a garin
KANO!" ji kake tas! tas!! mari na wanke
fuskarta ko ta Ina. " shut up! Idiot! " Ya bita da
wdnn kalmomin, "kin isa ki yi
abinda Allah bai nufa ba ne? ko kina ganin
za ki iya hana abinda Allah ya hukunta?" To
bude kunuwanki kmr ydd na sha fada miki,
ba ki daga ckn tsarin matan da nake
muradin aure.Bacin hadin iyaye babu
abinda zan yi da ke a AURAKA! snn ki sanya
wa ranki cewar Zaki yi kishi da baiwar da
kika raina a kirata da GIMBIYA kmr ydd kike
takama da sunan".Ta fashe da kuka,
abokansa suka janye ta suna bata baki,
amma har lkcn bata bar fadin, " ita ka
cusawa wnn bakin cikin, wnn zan bambance
muku MULKI da TALAKA sai an batar da su
a kasar nan! !" Yunkurin cafkota yake yi ana
rike shi, sauran abokan suka yi min zobe
ganin Ina da niyar kwasa a guje. Tashin hnkln ya
hana ni kuka, zcyta ta
daskare kmr dutse, na kalli wnd ke
bangaren damana ckn wani irin yanayi na
ce. " ka taimakeni ka maidani wurin
inna".Ya juyo da sauri jin muryata, hnn ya
kama zamu bar wurin. wdnda suka janye
Gimbiya suka tare mu da sauri. "Haba, Ina
kuma zaka je kana ganin mun shawo kan
Gimbiya? sauran 'yan korenta mun ja musu
kunne su yi shiru da bakinsu".Ya kalle su,
"Ba zan attending ba..." Suka rufar masa
kowane da abinda yake fada, da kyar suka
shawo kansa. wnd naji ya kira da suna
sahabi ya karbi mukullin hnnsa zai mayar da
ni gida, har mota ya Kai ni, snn ya saki hnn
yana fadin "komai dare zan zo, kada ki yi bacci
kin
ji?" kmr na wawuro fuskar in cije don
takaici, me kuma zai yi mini? wane bacci
gare ni Ina ckn wnn tashin hnkln? A daidai
Lungu ya tsaya na fita da sauri Ina jin yana
cewa. " Mu kwana lfy ". Amma na yi kmr
ban ji shi ba, zaman da na yi dabas ya
sanya ta kalle ni da sauri, "Lfy? ""Da sauki
inna ". Na fada ina rike kaina."Me ya faru?
"Ta bukata a rude. Na zayyana mata komai.
Ga Mamakina sai na ga ba ta wani razana
ba, ta ce. " Ni dama na yi zargin haka tun
farko, ganin cewar bai furta da bakinsa ba
ya sanya na yi shiru, sbd maganar Hausawa
idan baka iya kama barawo ba shi sai ya
kama ka. Ba zan yi saurin cewa ba zai yiwu ba,
sbd ba mu san hkncin Allah a kan lamarin
ba, kada mu yi masa shishshi har mu saba
masa. Amma da kmr wuya BAIWA ta auri
DAN SARKI, kina karkashin mulkin
gimbiyarsa". Na rike kaina da ke fizgawa
tmkr zai bar wuyana tare da runtse ido, ba
wai son shine ba ni yi ba, a'a ina hangar wa
kaina tashin hnkln da ke gaba. Kmr inna ta
karanci zcyta ta ce. " ynz kam dole runtse
idanunmu, mu kuma toshe kunnuwanmu
akan abinda zai biyo baya. A gaskiya zan
roki yaron nan da ya janye bukatarsa abu
ne mai whl ya rufa mana asiri, ya dubi
maraicinmu". sai ynz kuka ya zo mini. Ta
kalle ni. " ynz kika fara hawayenki su kare a
banza, ko ki janyowa kanki wata matsala" "Ban
katse ka ba, ina son ka gane abu
guda. Yrnyr nan marainiyace, ka ga kuma
ydd muke ba Wani boye-boye ynz, don hk
son da ka ce kana yi mata to ka nema mata
kwanciyar hnkl a rayuwarta. Gsky kayi hkr,
wlh ba zan baka Humaira ba, sbd ka fi
karfinta, ba km daya kukeba kai ni Ina
shakkar son da kake yi mata da
mamaki".Ga mamakin inna ta ga ya zube
gwiwa bibiyu yana kwalla. " Haba inna, kada
ki yi jayayya da ikon Allah mana, akwai wnd
ya fi wani ga Allah ba ya ga mai tsoronSa?
shin ya tsoron Allah ya ke? yin tawakkali da
yrd akan dk abinda ya hukunta".Tausay insa
ya far mata, sai kawai ta sunkuyar da kai. "
Na amince, Allah ya yi mana jagora".sauran
kwalln sk shatato masa."Nagode inna, Allah
ya kara girma, ya kuma bani ikon rike
Humaira bisa yrd da aminci". Yace ameen ya
mike Zan koma sbd
nabar gida kamr sansani yanzu abokaina
basu sami runtsawa ba tace Allah yai mana
jagora yace ameen. Har ya kai bakin kofa ya
waigo donAllah Inna ku toshe kunnuwanku
da duk maganganun da za'a zo muku dasu
tace ISA ta fada tana mikewa shi kuma ya
fice yana fadin zan dawo anjima idan
humaira ta tashi. Kwalla ta zubo min
burinsa ya cika ya rabani da aikina, motsin
inna naji ta sassauta murya ki tashi wann
kwanciyar bata da wani amfani a gareki.
Ba'aja da ikon Allah sbd har abada bazan
mance alhairin yaron nan ba sanadiyarsa
ina neman rasa cutar tun shekaru masu
yawa nake fama da ita tun magungunan da
alluran da yayi min bai kara tashi ba. Na fahimci
Allah ya dasa masa kaunarki
matsayinsa yafi gaban ya zubda kwalla
akanki ko yaudara yazoyi zan iya mallaka
masa ke sbd yaudarar tazo cikin tsafta sai
gashi ya tsugunna a gabanki ni mahaifiyarki
yana kuka yana rokon amincewata kina
tunanin Allah bazai kamani ba da alhakinsa?
Ko kuwa mun yaba kyautarsa kenan? Ta
girgiza kai tunda fahimci kyautar da yake
mana wllh zan jure duk wani wulakanci da
cin mutunci kema sai kin jure sbd bayan
wuya sai dadi. A matsayina na mahaifiyarki
humaira yanda nasanki da rashin sun
magana tashin hankali da sauransu ina jiye
miki kishi da gimbiya. Sai a lokacin kuka
kuka yazo min da karfi na dinga sharbe
harda majina Ta girgiza kai yanzu kika fara kuka
dama
kin daina wahalar da hawayenki a banza
sbd yanzu aka fara bamusan abnd gaba zata
haifar ba. Mutane muka hango a tsakar gida
ai bansan yanda akayi na ganni a kofar daki
ba hanjin cikina suka kada waya nunawa
gimbiya gidanmu? Na fita daga kofar dakin
ganina ya kara mata bacin rai. Don ubanki
ina kazamar uwarki? Yanda tayi zagin
gabana ya kara faduwa anya zan iya dauke
cin mutuncin iyaye? Yana iya dama inna
tace saina jure. Motsin inna naji a bayana
tana cewa ganinan... Ta nunata da yatsa ba
asiri ba wllh ko tsafi kike da bakar jaba
yarki bazata auru ba munafuka. Tsautsayi
yasa inna ta matso tana bata hakuri ta
kuwa kundumo mata wani mugun zagi ba
tare data girmamata ba.
Zan nuna miki cewar sarki da talaka
akwai bambanci sai kun raina kanku a garin
nan shegu MATSAFA! Maganr ta daki zuciata
anya zan iya shanye wulakancin su? Magnr
ta tunzuro hrt dina tsanarsa ta bijiro min
don shine musababbin karar marurrukan
dake sauka kuncin inna yasa ta tangal-
tangal nayi saurin riketa gabana yana
faduwa kada ciwonta ya tashi aiko nan da
nan ta fara shessheka ina kokarin zuwa
dauko mata magani naji gimbiya na cewa a
dakemu. Kota ina duka mukeji maza da
mata su Aisha sai kuka sukeyi ganin an
hada mana jini daga ni har inna niba dukan
ke damuna ba ciwon inna kada ya
galabaitar da ita amma rashin imani da
tausayi baisa sun kyalemu ba saida muka
matukar galabaita tuni inna ta sume rai
yana kokarin fita ganin haka suka fita daga
gidan jini yana fita a hannuna da goshina Na
rarrafa na dauko mata maganin
su sumayya suna watsa mata ruwa ina
shaka mata maganin. Cikin ikon Allah ta
farfado amma hannunta yaki motsawa, ihun
su Aisha ya tara jamaa lokacn su gimbiya
sun tafi abinka ga safiya ba kowa ya fito ba
mal bala ya kalli hannun yace kamr karaya?
Inna ta rintse ido mike cikin radadi suka
kamata hannun yayi baya sai kawai ta zube
tare da yin wata kara nima na kurma ihu na
tallabeta jamaar gurin suka rude wasu suka
ruga kiran mai dori kafinsu dawo mukaga
bataliyar abokansa tun daga waje suka
gidan dankam da mutane suka karaso a
kidime basu jira komai ba suka dauki inna
sukai asibiti da ita tuni ya tasa keyar su
Aisha dama ni tun shigowata ya rike
hannuna ya cika da tambayoyi. Bani iya
masa fitsara dana gwada masa yau, kafinmu
isa zazzabi ya rufeni ruf. Ni asibitin ma
tsoro ya bani sbd kyaunsa nan da nan aka
shiga da ita tiyata ni kuma aka bani daki da
gado allura 2 akayi min sai magunguna da
nasha shiys dressn din da akayi min banji
zafi ba ita kuwa inna gurin kare dukan ne
suka karyata kai Allah ya isa! Bacci ya
daukeni wasan kusan 3 na farka gadon da
ke kallon naga inna kwance itama tana ta
sharar bacci. Su Aisha da abokansa suna
zaune shi kuma yana tsaye ya jingina da
bango ya harde hannuwa.
Gaba 1 suka taso zuwa gaban gadon
nayi saurin rufe idona sbd wani abu danaji
yana harbin zuciata. A hnkl naji ana mgn
kusa da fuskata kiyi hkri ki tashi kiyi sallah
tym yana wucewa komai yayi zafi mgninsa
Allah! Da sauri na bude ido jin muryar
sadauki ya kada min kai ya kalli yarima ya
maido kallonsa gareni muna tausaya muku
anci zarafinku kuma zamuyi saurin daukar
mataki wannan cin mutnci yayi yawa they
have crossed their limit! Ga maganarsa ga
kuma sannun da sahabi yake min narasa
wanne zan saurara yarima kuwa har tym
din ya kasa cewa komai da alamu ni yake
kallo amma na kasa bude idona na ganshi
Bayan nayi sallah suka fitineni saina ci abnc
saida na cusa kadan. Sahabi ya kalli sadauki
yace muje ko? Yace su Aisha muje waje
muyi kallon haraba...... Turo kofar da akayi
ne yasa maganr ta makale saura kadan na
kwasa da gudu wata shamkiyar mata ce ta
shiGo da dogarawa 4 a bayanta kallo 1 zaka
mata kagane fuskarce bambancin tana
mace yana namiji. Sadauki da sahabi suka
zube a kasa suna barka da yamma Mama.
Nayi saurin sunkui da kaina inajinta amsa
kasa-kasa a tym din ya taho daga
tsayuuwar da yake sai kawai ya fada jikinta
baice komai ba ita kuma tasa hannu tana
dan bugun bayansa alamar rarrashi, ta
janyo hannunsa zuwa bakin gadona ga
mmkina saita zauna kusa dani shi kuma ya
zauna muka sata a tsakiya.
Nayi saurin sauka kasa na zauna
kusa da kafafunta. Sai naga dogarawan sun
fice da alama umarni ta basu. tace dawo ki
zauna nan ta nuna inda na tashi na girgiza
kai kawai ina mmkn zuwanta a wnn tym
din. Tayi shiru kamr yanda dakin ya dauki
shiru cikin dabara sahabi ya fiddasu
sumayya sanna ya dawo ayi komai a
gabansa. Ta gyara murya toni yanzu
mezanyi mk Hameed? Kamr yana jiran
tambayar ne ya kalleta ido jajur cikin
damuwa yace Mama duk duniar nan baya
ga Allah banida wani gata saike ki dubi
girman Allah zucita tana cikin tsananini ki
rabani da wann auren na gimbiya bani
kaunarta da duk wanda ya shafeta... Ta
katseshi Bazan iyayi maka wann alkawarin
ba sbd mai martaba ya bar wasicci ko bayan
ransa idan baka auri farida ba bai yafe ba.
Ya sassauta murya mama yarinyr nan bata
da hnkl ki dubi inna... Sun karyata sannan
dubi raunukan da sukaji mata ita da
humaira shin Sarauta hauka ce mama? Ni
nace inason yarnyr nan wllh har yanzu ban
sami wata amsa dg gareta akan abnd tayi
musu shin meyasa zucoyata bazata buga
ba? Kina ganin wanda yayi wann aika-aikan
bazai iya kisan kai ba? Kafiya gareka
Hameed ina jiye maka fushin mahaifinka
kana sane da cewa bazai amince maka ka
auri wacce ba jinin sarauta ba gaba na ya
buga da karfi taci gaba da cewa...
Zuwan nan kadai ya fahimtar dani
wani abu wllh na yaba da kunya nutsuwa da
kuma hnkl kana da tabbacin kai sarki yabar
wasiccin ka gajeshi idan ka tsaya akan wann
ra'ayin lallai sarauta zata bar hannunka har
abada. Wani abu naji ya tsikareni jikina yayi
sanyi lakwas. Mama ya kira sunanta cikin
wani ayanayi ta amsa ta kalleshi cikin
jimami, duk dunia ba wanda yasan
damuwata halina da kuma al*amurana
kamar ke sbd ko tari nayi ko a bayan idonki
saina sanar dake dn hk nakeso kibani
mafita ayau wllh mamana zuciyata tana min
zafi. Ina kallon sadauki ya matso kusa dashi
ya dafa kafadarsa daidai tym din inna ta
farka na mike zuwa gareta amma saiya
rigani. A hnkli mama ta iso inna ta kallemu
sai tayi smiling. Sannu ya karfin jikin ne?
Mama Ta fada tana kallon hannu daya
karye, da sauki ta fada tana kokarin tashi
muka kamata har maman ta zauna saman
gadon ganin hk yasa na koma na zauna
yana ta koakrin mu hada ido amma naki.
Mama ta dafa hannunta sannu inna,
murmushi kawai tayi. Ganin hk ta fara
magana donAllah kuyi hkri an zalinceku an
shiga hhakinku amma danAllah kuyi hkri.
Inna tayi shiru ta kauda kai, bazan gaji da
baku hkri ba wllh inajinku har cikin raina
domin duk abnd Hameed zai so ina son shi
kamr yanda nake kin abinda bayaso. Nayi
farin cikin ganin Hameed ya sami wacce tayi
masa kuma ya furta yana kaunarta da
bakinsa.
Abnd na dade ina mafarkin gani yau
gashi Allah ya tabbtr min dashi sbd kowa
yana tunanin ko bashi da lfy ne baligi kamr
sa ace baisan SO ba kullum sai yace bai
sami wacce tayi masa ba don har dariya
mukeyi masa tare da yan'uwansa idan yana
suffanta yanayinta. A gsky na gasganta
halayen Humaira dan zuwan nan da nayi
nasan Hameed nice mahaifyarsa nasan
kuma wayeshi wllh bazan taba jayayya da
kaunar da yake mata ba nasan na gsky ne
daga Allah. Kamr yanda nayi farin ciki ta
wani fannin kuma ina bakin ciki sbd lokacin
daya tsinci kansa cikin kaunar wacce yake
mafarkin samu a lokacin ne mahaifinsa
yasha alwashi akansa. Nasan halin
mahaifinsa da tsatstsauran raayinsa akan
duk abnd ya zartar mutum ne me zafin
gaske me kishin sarautarsa baya kaunar
talaka ya shigo masarautarsa da sunan
haduwar jini duk kaunar da yake wa dansa
zai iya yafeshi akan wann. Bani ba har inna
saida ta razana da wann maganar a hnkli na
zame na sulale kasa jikina ya dauki zafi
sosai. Taci gaba da cewa shiyasa ayau abun
ya daga min hnkl sosai jin kalaman da yake
fada min a waya nasan zai aikata abnd yake
fada. Ta kalli inna kaunar da yakewa
Humaira ya zarta tunani amma ina da wata
shawara guda, mu duka mu dage wajen
fadawa Allah yanda ya hada wannan
soyayya da yardarsa zai warware komi cikin
sauki idan abun zaiyuwu yafimu sanin tsarin
yanda zaiyi haka idan bazai yiwu ba. Ta dafa
kafadar inna danAllah muyi hkri wata rana
sai

Please Login or Register in order to submit comment