Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki cutune?" Na yi masa shiru. "kiyi
mgn ko kina ganin wancan auren zaki
amince da shi, na dattijo? Kinsan halinsa?
su waye matansa? ko kina tunanin tsufan
ne kawai ba matsalar iyali?
shin yaransa nawa? ko kina da labari mafi
yawa kishin ynz da 'ya'ya ake yi bada
iyayeba? " Na mike, " wayyo ni
Humaira,safwan zan rungumi kaddara, sbd
kai din ma bansan wane ne ba? shin ya 'yan
uwanka da kishiyar mahaifiyarka Zasu
dauke ni? cewar baka da matsala ne zai
tabbatar mini hkn? Na girgiza kai, " safwan
kada ka ya bi kanka, shi yabon kai
jahilcine". " Humaira kiyi tunani, zan dawo
jibi komi kenan, pls kada ki so kanki da
gobe zan koma, amma zan jira hr naji
amsarki. Allah yayi mana jagoranci, zan
wuce ki je ki kwanta, amma kiyi kokarin
tashi ckn dare kiyi nafila, domin neman
zabin Allah".
Ban ce komai ba na wuce ciki, amma ko bai
fada ba dama ina da wnn niyar. kwance
nake na rasa abinda ya ke yi mini dadi, sbd
lallai mgnr safwan shi su waye iyalan
dattijon? Da farko ina tunanin auren sa
shine mafita, amma ynz km hnklna ya
tashi. " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un ".
Har karfe 2 idona 2, na mike nayo alwala na
dinga salloli ina addu'o'i ckn sujjada, snn
ban tashi wurin ba sai da aka yi sallar
asuba. Na tashi da matsanancin ciwon kai,
na samu na kwanta bayan na sha (Boska).
Idona rufe wayata ta fara ruri, na duba
Amira ce. " ya naji muryarki haka Humaira?"
Na fada mata ydd muka yi da safwan, ta yi
shiru kafin tace .
"Turkashi, Humaira ki dage da addu'a nima
ina yi miki nawa kokarin Insha Allah
matsalar ki ta zo karshe". Na yi murmushin
takaici. " Hm Haba Amira, wai har su baba
Auwalu ke cewa, ba zan taba auren mai
rufin asiri ba, don bana fin yaransu, Yaushe
na taba zabin irin wnd nake son aure
Amira? " Ta yi ajiyar zcy, " wlh hassada ce
kawai suke yi miki, don hk kedai ki
fauwalawa Allah komai. Bari ina ina zuwa ga
Gimbiya can tana kirana". Ta kashe. Kmr
abin jira, Kiran Ibrahim ya shigo, naja wani
dogon tsaki, wnn waya tana neman
jawomin matsala, sbd ko motsin tsintsiya
ba a son ji wlh.
Ina dauka bai jira mun gaisa ba yace, " INA
yau zan baro kasar nan ki saurare ni zuwa
gobe da yamma". Na bude baki, amma sai
na ji ya kashe. Da sauri na tashi zaune
daidai lkcn da inna ta shigo, na ce. " kin ji
wai Ibrahim yana hanya". Ta zaro ido, "
zuwa ina? " "Nan zai taho, wai na saurare
shi zuwa gobe da yamma". " Innalillahi
wa'inna Ilaihi raji'un, ni kam a gaskiya ni
kaina mgnr Ibrahim ina fa tangarda da ita,
sbd hatsabibiyar matarsa tnd har ta furta
kisa ko na kasa..." Kiran Amira ne ya shigo,
na dauka, ta cigaba da lallashina tana bani
hkr, nace ba komai, muka yi sallama. Jin wnn
mgn yasa na fada mata mgnr
safwan, ta girgiza kai. " Haba Humaira,
kawai daga ya zo sai a amince da shi mun
san halinsa? " " Nima hk na gani inna. shi
baba bai gaya miki wane dattijon ba? Tayi
dry, " bai fada ba, wlh jiya hr gidan naje ki
kyale wdnn mutanen, Allah ya fi su".
Washegari ya kama sauran kwana 2 tnd
safe safwan yazo, na fita. Ya kalle ni, " yau
ma kukan ne? " " A'a.Na fada a gajarce. "
To gani ina mgn ta kwana? " " Na fidda
wani" " wane ne? " " wani ne na fada kaina
a Kasa. "Bashi da suna? " " yana da shi". "To
fada".
Na yi masa shiru. " Haba Humaira, me yasa
ki ke son koyon karya, km da alama kmr ba
halin ki bane". "Ya za a yi na yi maka karya?
" "wlh karya kike yi, sbd hk ni zan je na
gabatar da kaina". Na yi saurin dago Kai. "
A'a wlh kada kaje, ban turaka ba". Ya
kyalkyale da dry. " kin kama kanki, ni zan
tafi sai kin ji daga gareni, sbd na lura baki
da tunanin kanki, baki da shawarar kanki,
haka baki da zabi".Yana gama fadin haka
yayi tfyrsa. kmr na kirashi ya dawo muci gaba
da
tattaunawa har ya fahimce ni, amma na
kasa. Na koma gida rai jagule. Ina ckn
damuwar abinci Ibrahim yayi sllm hr ckn
raina gaba na ya fadi, ya bada kululu. Da
inna suka yi mgn snn ta ba mu wuri. Ya
kalle ni ckn tausayawa, " wayyo Humaira dk
kin rame, sannu ko wane tsanani tafe yake
da sauki. Inna ta yi min bayani, na kuma
gamsu, km nima ta fahimce ni, sbd hk zan
tafi gida jibin itace ranar karshe, zamu zo
da iyayena a yi komai, yau kinga yaushe na
zagaya dangi har aka yi mgn? Gobe kuwa sai
na sanar jibi tunda safe mu
taho". Na dai yi shiru kawai, rayuwata ta
kara jagulewa. " zan wuce, ki ci gaba da
addu'a, zan aiko Yaro da kayan ki, suna
waje ckn mota".Ya ajiye min bandir din
kudi ya mike. Inna ta karaso, " yaronan ya
bani tausayi Humaira, ki yi hkr da shi dk ya
Snr da ni komai, kuma na amince da shi".
Shiru kawai nayi mata. Da magariba ina
zaune ina lazimi, yaro ya shigo ana sallama
da Humaira. saura kadan in kurma ihu. Na
kalle shi, " kace ta daina fita, sbd an yi mata
miji, mata aure ce ynz". Inna da ke sallah
ta yi gyaran murya. Takaicina ya karu, wai inna
me ke damuta?
Na fita raina kmr garwashi, zcyta sai zafi
take yi. kamshin da ba ni taba mantawa ya
daki hancina, nayi saurin kallonsa. Tsaye
yake ya harde hnny a kirji, ni yake kallo, na
durkushe sai kuka. Ya sunkuyo, " ki yi hkr
Humaira, nasan kin yi fushi dani, wlh
Humaira ba laifi na bane. ki daina kuka don
Allah, menene damuwarki zuwa nayi muyi
maganinta tare, Amira ta sanar dani
komai". kuka nake, me ya kawo ka a wnn
lkcn, me yasa kazo ka famamin ciwon da
yaki wankewa? " Innalillahi wa'inna Ilaihi
raji'un, don Allah ki saurare ni..." Na mike, "
Don Allah ka tafi, wlh bani son
ganinka a rayuwata, ba don na tsanekaba,
a'a sai don na tsira da mutuncina, kai kuma
ka gama da iyayenka lfy..." " saurara..."
Nayi gida da gudu. Abin mamaki na kasa
sanar da inna ko waye, ita kuma bata tmby
ba. Zaune na kwana, duk wnd ya sani a da
ynz ya ganni sai na bashi tausayi, nayi
muguwar rama ga baki. Tashin hnkl sai
ranar da adadi ya cika da safe, misalin karfe
10.30 na safe sai ga baba Auwalu su uku da
buhun goro. jikina ya dauki rawa da yake
zaune muke ni da inna a bakin kofa. Ya kalle
mu a wulakance, sannan ya nefo ni
da 20k. " To barkanki, wlh da na ba tsoho
ha goran daurin aure nan mun dauki 2, Kuyi
amfani da wnn, Na daura miki aure da wnd
kika turo yau da safe karfe 9.30. Don haka
ki shirya gobe zaku wuce babu mgnr taro".
Na kalli inna itama ta kalle ni. kash!!! Nima
ku nake kallo masu kr2, da wane ne aka
daura auren da shi? safwan ko Ibrahim? Me
ya kawo? mu tara a ltf na 3

Subul da Baka 3 page 1
Posted by ANaM Dorayi on 05:11 PM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Inna ta yunkura ta shiga daki suku ma suka yi
hanyar waje,Ashe zaman tabarma ne nake ga
bai mata ba.A firgice ya shigo babu ko
sallama yana fadin inalillahi wa inailaihi
raji'un daga ni har inna maka mike tsaye cikin
firgici inna take tambayarsa lafiya ibrahim? Sai
kawai ya durkushe kasa idanun sa jawur inna
ya aka yi haka! cikin rashin fahimtar inda ya
dosa tace da akayi me yace inna waye kuma
hameed.yarima ne hameed meya faru mutuwa
yayi? A'a da ransa shine mijinki yanzu an
daura muku aure,inna ta dafe kirji wa! Tirkashi
inalillahi wa inailahiraji'un Nayi saurin
karasawa kusa da ibrahim na
rushe da kuka ina fadin ka rufamin asiri kaje
kace kaine zabina zan iya jure ko wace wahala
amma banda ta gimbiya da mahaifin yarima
wayyo ni humaira na shiga uku ! Ke bana san
shashanci da hauka ina ma yazo kasar yaushe
yasan abinda ke faruwa. Wannan abun yi Allah
ne saboda haka na
fawwala masa komai Allah yasa haka shi ya fi
alkairi a gare mu baki daya ya mike tsaye
yafita muna zaune muka jiyo sallama wa
yarima zai shigo kanshin turarensa ne yafara
yimin sallama.
Daga kurya nake cikin duhu,shi kuma ya zauna
daidai inda aka ajiye fitila na qura masa
ido,ya qara haske da qiba,yayi kyau har yau
kasaitar nan tasa na nan,sai faman basarwa
yake yi,yana 'yar yamutse fuska. takaici ya
qara kama ni na harareshi,nan ma SARAUTAR
zai nuna? Cikin girmamawa ya gaida inna. tun
kafin yayi magana inna ta jero masa
tambayoyi."Haba yarima? don me zaka yanke
hukunci ba tare da shawararmu ba? talauci
haukane? yarinyar nan marainiya ce meyasa
zaka nemar mata tashin hankali fiye da
kwanciyarsa? ya zatayi da mahifinka? humaira
na iya kishi da Gimbiya?" Ya dago kai
fuskarsa a washe yace"Inna ku kwantar da
hankalinku,wallahi. billahi ba ni da niyyar cuta
ko yaudararku maganar mahaifina yanzu haka
yana kwance rai a hannun Allah kuma ina da
yaqinin insha Allahu zanyi amfani da wannan
damar mu daidaita dashi,tunda har yana
ganin ya hore ni da yin biyayya gareshi,kuma
na aikata hakan zan lallabashi ya yafemin,ya
janye maganar ko bayan ransa." Yanzu haka
ana zargin 'yan uwana ne suka jefa shi cikin
wannan halin,domin su gaji sarauta. akwai
rikici da muke ciki inna,amma hakan bazai
taba shafar Humaira ba da iznin Allah. Kafin
inje ga maganar zamanta da Fareeda
(Gimbiya),ina son ki sani cewa,mahaifan
Humaira suna son ganin cewar sun
wulakantaku ko ince suna son ganin kun
wulakanta. dalili kuwa,nayi bincike sosai a
kansu. yanzu haka da muka je maganar
neman aure,ban nuna musu vewar ni din dan
sarauta bane,asali ma na kasance mai
qasqantar da kaina tare da nuna ni din talaka
ne mai neman taimako matuka. Sunyi SUBUL
DA BAKA mai tarin yawa a cikin jawabansu a
inda suke nuni da lallai basu son Humaira ta
fi 'ya'yansu wadatar dace da miji mai rufin
asiri. Maganar Ibrahim shima nayi bincike a
kansa
lallai mutumin kwarai ne kuma ya fito daga
gidan manya masu mutunci. Matsalar matarsa
inda ake nuni da cewar,tafi karfinsa fiye da
tunanin kowa,yana tare da muguwar mata
wacce tana iya yin ko wane irin ta'addanci,da
mugun abu akan duk abin da ta ga zai kawo
mata cikas a rayuwa. Wannan dalilin ya qara
tsorata ni,ga shi na ji hirarsu da Amira. Kuma
da alama kamar Ibrahim din shi ne wanda
yake tsayayye a gareta. Nazo don Allah mu
warware matsalar wallahi har ga Allah banzo
da niyyar auren Humaira ba,amma sai ta qi
saurarena wanda ya nuna min tamkar rike ta
ke dani a zuciyarta,tana ganin kamar nine sila
ta duk matsalarta. Mahaifiyatace ta bani
shawarar nazo wurin magabatanta na kawo
kaina,ba tare da mun san cewar za'ayi
maganar daurin aure ba. Munyi haka da
niyyar daga baya sai ta sami wani ta aura ni
kuma na janye. Saboda haka kada muyiwa
Allah
shishshigi,hakan ya rubuta sai muyi fatan ya
zamo alkhairi agaremu inna. Kada hankalinku
ya tashi,ni ke cikin rikici,amma duk da haka
bana cikin rudani. Na farko yadda zan shawo
kan Maimartaba. Na biyu rudanin da muke
ciki da 'yan uwana. Na uku ya zanyi da
rigimar Gimbiya idan ta sani,bazan sanar da
ita ba sai na sasanta da mahaifina,in ba haka
ba tabbas zata raba mu har abada!" Na
runtse ido cikin radadi ina hango rayuwar da
zan shiga saboda na tabbatar auren Yarima
ba hutu bane a wurina. "Maganar zamansu
da Gimbiya ba matsala bane,domin ni ke iko
da gidana duka qarqashina suke,wallahi inna
ba zan taba amincewa da takura,zalunci ko
tashin hankali a gidana ba." Ya tsagaita da
bayanin nasa kamar yadda dakin ya dauki
shiru. Na kalli inna,sai naga tana zubar da
kwalla. Hankalina ya qara tashi. Ya muskuta
da fadin"Inna kuyi hakuri don Allah,gobe a
bada mata hudu zuwa shida wadanda zamu
tafi da su,domin su ga gidana hankalinki ya
kwanta. Idan kuma zaki bi ke ma to mu tafi da
ke..." "Kai bana son sakarci!" Sai naga yayi
'yar dariyar nan tasa ta qasaita. Ya mike
tsaye"Inna ayi ta hakuri,sai mun zo su shirya
gobe da wuri za mu wuce,wajen karfe takwas
zuwa tara domin mu isa da wuri,kada muyi
dare."
Tafiya muke yi, amman idanuna na gefen titi,
Sumayya da Aisha sai faman tsalle suke yi.
Motar su yarima ke gaba tamu na biye dasu,
Babban abinda ke damun zuciyata shine, idan
mun isa wace tarba za,ayi mana? Ya za a
karbi wannan al'amari? Ina tsoran tashin
hankalin Gimbiya, musamman idan mukayi
tozali da ita ga cewar na aure Yarima a
matsayina na na BAIWARTA. Munyi tafiya mai
nisan gaske inda ake dauke hanya muka kutsa
cikin daji, nan ma munyi tafiya mai dan nisa
wanda su baba har sunfara korafi sannan
muka isa wani gidan gona katton gaske. Acikin
gidan gonar ma sai da mukayi tafiya
mai nisan gaske kafin ya tssaya gaban wani
tankamemen gida, Goggo Huraira matar Baba
imrana kadai ta biyo daga bangaren babana,
itama ganin kwaf yakawo ta. Mata hudu muka
tarar gidan, babu abinda babu na more
rayuwa a gidan, aka kaini wani daki mai
dauke da gado kawai sai mudubinsa, ga kuma
wata kofa a rufe wacce nake kyautata zatton
bandaki ne. Abinci aka dinga shigowa dashi
kala kala cikin wasu manyan kololi, Goggo
huraira ta dinga raba idano tana yaken dayafi
kuka ciwo. Hannu baka hannu kwarya suka
ringayi abinka
da sabon shiga ga farfesun kaji dana kifi, suna
gamawa wasu maza suka shigo da katon
gasasshen rago bisa wani dogon tebir, Goggo
Huraira tazare ido, bayan fitar su, takalli su
inna karsum wai wane ne wannan yaron?
YARIMA!!! Nabata amsa takara fiddo ido tace
amma ku munafukai ne, shine baku fada tun
wuri ba? Su goggo suka kalleta a mamakance
kamar zasuyi wani abu sai sukayi shiru, da
dare yarima yashigo yace ko akwai abinda
ake bukata? Suka ce a a, dare yamika, gari
yayi tsit babu abinda akeji sai minsharin su
goggo ciki yacika da kayan dadi, nikuwa nayi
lamo ina tinanin yadda wannan aure nawa zai
kasance.
Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi
murmushi yace babu komai. Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.
Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.
Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi
murmushi yace babu komai. Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.
Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.
Gaba daya jikinsu ya dauki rawa suka zube
suna faman godiya. Ni kuma da yake nasan
wannan kadan ne daga cikin aikin yarima abin
bai zamo mini sabo ba kamar su. Na fashe da
kuka lokacin da na ga cewar, motarsu ta bada
wuta zasu tafi. Goggo ta leko kai daga tagar
motar tace. "To yar banza mai kashin tsiya
kukan me kuma kike yi? Wanna aljannar
duniya da Allah ya kawo ki har kina da bakin
kuka, marar mutunci ko zaki yiwa Allah
butulci ne ya rabo ki daga tsiya. Hannuna naji
an kama mun yi baya. Da sauri na kalle shi,
Yarima ne fuskarsa a daure da alamar
maganganun sunyi masa zafi. Ni kuwa banji
komai ba saboda na saba da wadanda ma
suka fi wadannan. Bisa kujera muka zauna
yanayin zaman yasa nayi wata irin kunya ta
kama ni. Na yunkura zan mike ya dawo dani
na fada saman jikinsa na rasa inda zan sanya
kaina don tsananin kunya. Ya rike hannuna
duka biyun tare da tsare ni
da wannan mayen kallon nasa mai narkar da
duk illahirin jikina. Inason furta ya sake ni
amma na kasa sai faman motsa baki nake yi
kalmomin sun gaza fita. Yayi yar dariya yace
Ba fa zan sake ki ba sai kince I Love You
Naku Tabdijan! Ashe zamu shekara a haka kenan!
Na fada a raina. Wai mai yasa kike mun rowar
maganarki Humaira? Ko don kin ga tana kara
kayata zuciyata ne? Na rufe idanuna ko ya za
a yi in san haka? Baza kiyi min magana ba?
To bari na cije bakin da ke yi min rowar
sai...... Nayi saurin bude idona. Yayi
murmushi yace Matsoraciya goge wadannan
hawayen muyi magana. Nayi saurin kallonsa
alamar ya sake ni. Ya
kashe min ido daya. Ki goge da jikina mana?
Bansan lokacin dana balla masa harara ba, ya
kyalkyace da dariya. Wannan irin horo? Ya
sake ni, amma yayi saurin sanya hannusa
yana goge min fuska. Hankalinka ya kwanta
yau hannunka ya taba fuskata. Na fada a zuci.
Na yunkura zan tashi ya dakatar dani. Tsaya
gimbiya, ai yau sarautar hannunki ta ke. Ya
mike tare da zama kasa daidai kafafuna.
Wallahi bani son irin wannan abunda yarima
keyi mini. Na kara daure fuska tamaubabu
alamar fara'a ko kadan. Ya kwantar da murya
a nutse yace. Humaira kina da tsoro?
Tambayar tasa tazo mini a hagunce kamar ya
fahimce ni, sai yace. Ma'ana kina iya kwana
gidan nan ke daya? Nayi saurin daga masa kai
alamar iyawa.
Tsakaninki fa da Allah kina iya? Bana son ki
kwari kanki idan baki iyawa na samo maki yar
kwana. Ina iyawa, na fada da kyar. Abinci fa
kin iya dafawa ko a kwao mai koya miki?
Kamar zance na iya amma kuma wata zuciyar
ta gargade ni dana ce a kawo., saboda
yanayin abincinsu da namu lallai akwai
bambanci mai girman tazara. Na ce Aa. Ya
kalle ni da fadin. Ban gane ba? A kawo na
fada a hankali. Da kyau ya fada yana
murmushi. Kina son mai share share ko za ki
iya da kanki? Allah sarki Inna ita mai lalura
yanzu wa zaiyi mata share sharen? Na girgiza
kai, zanyi da kaina. Lokacin idonuwana suka
ciko da kwalla. Ya matso kusa dani, kiyi
hakuri. Yarima ya ishe ki da tambayoyi, ke
kuma ba kyason tambaya ko? Na dai yi shiru
kawai. Wadda zata koya miki abinci ita zata
nuna miki komai na gidan nan. Koda wasa
karki nuna mata ke matatace. A firgice na
kalle shi. Ya kawar da fuska yace Zan sanar
da ita ke matar abokina ce Haka sauran
wadanda ke nan shiyyar saboda gudun
matsala kafin Allah yasa mu daidaita da
maimartaba. Wayyo ni Humaira na shiga uku!
Kwallan da nake kokarin mayarwa suka fito
day bayan daya. Kiyi hakuri Humaira, wallahi
duk saboda kwanciyar hankalinki zanyi haka
Kada ki damu Allah na bayan mai gaskiya
kinji ? Yau zan wuce mu tafi da maimartaba
Eygpt idan an dace muyi kwana hudu zuwa
biyar Idan kuma an sami akasin haka to sai
yadda Allah yayi.
Take kwalla suka karu ni kuma haka Allah ya
tsaro min tawa rayuwar?? Ya kalle ni, Don
Allah Humaira kada ki sanya wa kanki
damuwa kinji? Da na dawo zamu je Kano ki
gano su Inna kiyi kokari ki kwantar da
hankalinki yadda za su ga cewar ba ki cikin
matsala. Kuma insha Allah idan komai ya
daidaita ina son dawo dasu kusa damu
Saboda Inna na bukatar kulawa. Naji wani
sanyi a raina tare da goge kwallan da ke
fuskata Ya miko mini sabuwar waya yana
cewa Akwai lambata da ta Inna a ciki Kada ki
saka lambar kowa sai da izinina kinji? Nace to
Wayarsa tayi kara ya dauka Hello!..........ok
Ina kan hanya gani nan isowa Ya dawo da
dubansa gare ni Ya shiga wani daki kusan
mintuna hudu Ya fito rike da wata leda Ina
kallonsa ya bude wata dirowa ua dauko wani
dan kwali karami ya gama yar diminiyar sa ya
fita. Na kwanta dabas kan kujera. Allah gamu
gare ka Har kusan karfe daya ina nan zaune.
Kofa naji
ana kwankwasawa na leka sai ga wata
katuwar mata tsaye. Na bude mata sai fara'a
take yi. Yanayin gaisuwar da muka yi da
yadda ta ke magana na gane cewar ba
cikakkiyar ba hausa bace. Tace nice wace zan
koya miki abunci. Ta fada tana mai fata'a
sosai. Nima cikin sakin fuska nace mata. Ba
matsala. Na kawao mata lemu a firij din da ke
falon mai sanyi da ruwa Sanana na kalle ta
Don Allah ki bani mintuna kadan zan yi sallah.
Ta risina cikin girmamawa har mammaki ya
kama ni. Tace As u said Madam no problem
Toh ai kinji fa ni fa bana son turanci yayi yawa
a magan Ko kuma ayi shi cikin sauri domin
karatun nawa yanayinsa akwai da rauni.
Lokacin dana fito nayi mamakin ganinta dana
yi a bakin wata kofa. Tayi hanzarin karasowa
kusa da ni. Yauwa madam muje. Na bi
bayanta sai na ga ashe kicin dinne To ya akayi
ta sani?? Ban sami damar samu amsa ba Ta
katse ni da cewa Yallabai kwana biyar ya
bamu Saboda haka ki dauko biro da takarda
ki ringa rubutawa Saboda gaba rana daya kina
iya mantawa da wani abun Na kalle ta sosai
nace Bani da biro gashi ni bakuwa ce a gidan
Tayi murmushi tace Ayya bari na baki Ni ina
dasu.
Nafisa A. Mamawa
Tabude jaka ta fiddo wani dan book da biro
tamiko min, A kullum zamu ringayin abubuwa
uku zuwa hudu, ko fin haka idan akwai time,
tabude wani katon firij dake kicin din, shakare
yake da kayan lambu da naman kaji dana
dabbobi, wani kuryar daki dake kicin din
shima cike yake da kayan abinci na
buhunhuna dana kwalaye, ga doya, dankali,
kwai, da sauran tarkacen, ta debo dankali
tace hajiya zan ringa yimiki bayani kina rubuta
wa, nikuma inayi a aikace kina gani, na ce to.
GIMA POTATOES ABUBUWAN DA AKE
BUKATA, dankalin turawa, tattasai, Attarugu,
Tumatur, albasa, gishiri, curry, thyme, karas,
pies, green beans, green pepper, alayyahu,
kwai. A fere dankalin turawa kar a yanka, a
barshi haka da girmansa sai ki daka tattasai,
attarugu, tumatur da albasa, kisoya sai kisa
ruwa kizuba dankalin, kisa su maggi, gishiri,
curry, da thyme, ki yanka kayan lambumki irin
carrot, pies, green beans, green pepper,
alayyahu. Sannan ki fasa kwai kamar biyar ko
fin haka kisama masa curry da albasa da
maggi kisoya shi. Kiduba dankalin inya dauko
Dahuwa sai kijuye soyayyen kwan da sauran
kayan lambun.
Banda alayyahu, shi ki samasa ruwan zafi ki
tsane shi, saiki sa namanki ko kifi ko kibarshi
haka, kibar kayan lambun suyi laushi ruwan
kuma yayi kauri, sai kisa albasa da alayyahu
kirage wuta, tayi dariya tace yanzu zakiji shi a
bakinki, a time din data gama yawuna har
tsinkewa yakeyi domin yunwa nakeji nakuma
na cika flet na kuma gefe, gaskiya yayi dadi
wannan gima potatoes din, tayi dariya tace to
kidai rage wuri ga abinci na biyu mai suna,
KABBANI RUS RICE, abinda ake bukata
nama, albasa, maggi, kayan lambu,
tafarnuwa, Cinamon, Cadamon, mint,
Attarugu, Yogot, basmati rice, ki yanka nama
kanana sai ki tafasa, kidan soyashi sama
sama, kiraba shi biyu, kidauko basmati rice ko
kuma wadda kike amfani da ita kidafata
ruwan naman sama sama sai ki yanka karas,
garlic, pies, albasa, ki hada su guri daya, sai
ki daka attaruhu banda tattasai kisoya kizuba
su karas, nama, garlic, maggi, da dai sauran
su, ga wanda bai shan yaji ana iya amfani da
tattasai zalla cinamon, cadamon, mint, sai ki
zuba yogot cokali uku ko hudu, in kina son
zaki dayawa, idan kuma bakiso sai ki zuba
kadan, to your taste. Idan kin gaggauraya sai
ki juje guntun ruwan
silale a ciki idan yatafasa sai ki sa albasa
kirufe ta, kirage wutar har ya tsose yadahu,
zaki iya mata sos din albasa da garlic da
attarugu ko sos din tumatir kawai ko kici
haka. Idan kikayi wannan sai ki sami
mangwaro tunda gaki gidansa akwai manya
manya nan sai bare bayan saiki yanyanka shi
kicire kwallon, sai kizuba tsokar mangwaron
atukunya kisa citta, kanunfari, kuzuba ruwa
kidora a wuta yadahu sosai yafara fashewa sai
ki burge shi kikara ruwa kitace kisa sugar da
fulawa kisa firij.
Ta koya mata abinci da dama( na tsalake ne
saboda nasan dayawanku kun iya
musamman...inma da wadanda basu iyaba
bazasu wauce abokanainaba su kuma insunaso
sai suyimin magana prvt loz).
Bayan ta koya mata komai. Tayi mata rakiya
har bakin kofa, nace Don Allah kiyi hakuri bai
bar min komai ba....gurin is not clear. Tayi
dariya tace wallahi ya biya ni har da doriya, ni
ke da godiya Madam. Naji dadin samunki mai
far'a da son jama'a wallahi domin hausawa
na cewa shimfidar fuska tafi ta tabarma. Sorry
not clear.Amma gobe kizo da wuri don Allah
Na fada ina murmushi. Insha Allah da wuri
zan zo yau ma akasi aka samu Na gode sai
goben. Nace Allah ya nuna mana lafiya. A
kujera na bar wayata na dauko ina latsawa na
ga an kira har sau goma sha uku (13 missed
calls). Na fido ido, ina dubawa na ga Hameed
wato Yarima. Na zauna tare da kura wa wayar
idanu saboda a gaskiya bana iya kiransa. Na
latso lambar Inna, bugu daya ta shiga. Tayi
sallama murya a washe. Wa ke magana? Inna
Humaira ce. Sai naji tayi yar dariya. Humaira
kuna lafiya? Kalau Inna, su Aisha su iso lafiya?
Tace lafiya lau, ya suka barku? Nace kalau. To
Allah yayi muku albarka Kiyi mana godiya mai
tarin yawa wurin yarima don Allah. Ya kira ni
dazun yace zasu yi tafiya , don haka ki kula da
kanki, ki kuma kular masa da gida Allah yayi
muku albarka. Nace Ameen. Mun dade muna
hira inda na lura Inna kamar ba cikin
damuwa, sannan muka yi sallam hankalina ya
kwanta. Kamar abin jira, kiransa ya kara
shigowa. Gabana ya fadi ba wai kiran ke bani
so ba, a'a tambayoyi na tsana a rayuwata. Na
kara wayar a kunne tare da fadin. Assalamu
alaikum. Ya amsa cikin zakuwa tare da ci
gaba da fadin. Ina kika shiga ne tun dazun ina
ta kira shiru, ni duk kin tada min hankali.
"Kicin" na

Please Login or Register in order to submit comment