Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har sau biyu,sannan ta
kalle ni. Kin san abin da ake nufi da
HADUWAR JINI? Na girgiza kai ta kara
murmusawa. ,Abin da akae nufi shine,kauna ta
cikin jini,haka kawai Allah ya hada bayinsa
cikin hikima tasa. Ma'ana yarima Allah ya hada
jininku ba don komai ba,saboda
hakan Allah ya rubuto. Wallahi ina mai tabbatar
miki,da yana tausaya mana ne
kawai na farko yafi karfinmu nesa ba kusa ba.
Tsarinmu da shi ya sha bamban da
sa.kuma ya fahimci hakan. Shawara daya zan
baki. Kiyi kokarin inga ba shi amsa
gamsasshiya a duk lokacin da yayi miki
tambaya,hakan zai sanya ya daina
damunki tunda halinsa ne.Yarima ba yaro bane
don akalla zaiyi 38yrs ke kuwa
duka fa yanzu kike 15 kawai daiya dauke a
kanwarsa ko yar cikinsa a tunani. Jin
tayi shiru nace to inna yace gobe zai dawo na
dama masa fura, fura? Ta tambaya
tana kallona nace uhm tayi tagumi to bamusan
abnd Allah zaiyi goben ba na mika
mata wayarsa daya bani aro ta karba itama
hannunta yana kyarma don kyaunta
ga wani kamshi da yake fita ta juyata ta kara
juyata Allah sarki humaira yaron nan
tausayi gareshi adana masa zuwa safiya na
amsa ita kuma ta juya ta fara bacci ni
kuma yau baccin sama-sama ne sbd kamshin
yarima daya addabeni (kuji mayya
lol) kamshin da yake a jikin wayarsa harta
hanneyana ma kamshin sukeyi. Saina
tsinci kaina cikin faduwar gaba ina tunanin irin
halayensa. Tun daga kofar shiga
falon na fara fahimtar yau gidan babu lfy kowa
ka gani yayi tsuru-tsuru yana zare
idanuwa ba mazan ba ba matan ba kowa yana
cikin fargaba. Jikina ya dauki rawa
don bana kaunar tashin hnkli a dunia. Takun
farko dazan shiga cikin falon najiyo
muryar gimbiya tana balbala masifa abnd
kunnena ya jiyemin saura kadan fitsari
ya zubo min nayi saurin komawa ta kicin tare da
lafewa a jkin bango ina saurare.
Duk abnd kake takama dashi nima ina takama
dashi yanda kake dan sarauta haka
nima ubana yake sarki na gaji da wann cin
kashin da kake min tun zuwanka! Kullum da irin
salon wulakanci da rainin wayon da zaka 6illo
min da su kana
kunyata ni a gaban BARORI nah! Ya zama dole
ka amsa min tambayar nan INA
KAKE ZUWA KULLUM CIKIN DARE? Na tambaye
ka jiya bayan ka dawo kace min
bacci ka ke ji. Yo yanzu kuma fa? Da kai nake
kayi banza dani,ko za kayimin
izgilanci ne da kasaitar da ake yi maka kirari da
shi? To ka tuna cewa,nan ba
masarautarku bace,don'yan magana na
cewa,sarki a gidan wani sarkin sunansa
BAWA....Ba za kayi magana ba? Lallai zaka amsa
kira a fada yanzun nan,idan ka
raina ni ina ganin sarki yafi karfin raini a
wurinka. Ta banko kofa,tuni kowa ya
kama aikin karya kada ta gane ana sauraronta.
Na makale wayar a siket dina,kada
ma wani ya gani. Kallo daya zaka yi min ka gane
ina cikin tashin hankali. Aiki
kawai nake amma Allah Allah nake ta dawo a
aiko kiran yarima fada nayi amfani
da wann damar na hamzarta kammala tare da
ajiye masa wayarsa koda a
karkashen carpet ne tunda ba mai shiga dakin
saini amma shiru kakeji. Rabi ta
kalleni na tsaye kawai ta matso. Gimbiya fa
batasan baki zoba kwana 2 sbd haka
kadaki bari ta gane kiyi hamzarin kammala
aikinki kinga yau za'a bamu
albashinmu tana cikin fushi kada a kiramu baki
kammala ba. Gaba kawai nayi
zuwa daki dama can kadai ya rage da bandaki
ina tura kofar na ganshi kwance
idanunsa jawur kamar wuta. Kamar dama ni
yake jira yayi saurin tashi zaune ya
tura kofar tare da kullewa da mukulli nayi
saurin kallonsa har lokacin idanunsa
jawur suke fuskarsa murtuk kamar zai fashi... ya
karaso gabana ya kalleni kamar zai fashe da
kuka idanun sun kara ja na
sunkuyar da kaina ya kankantar da murya
kamar zaiyi kuka. Humaira banason
gimbiya na tsaneta wllh... Nayi saurin kallonsa
ya bude min idanu sun kara
rikicewa cikin matsanancin bakin ciki yaci gaba
da cewa ni fareeda zata kira BAWA
sbd nazo gidansu na zauna? DonAllah ki
taimakeni menene shawara? Kwankwasa
kofa mukaji na kalleshi cikin tashin hankali tare
da saurin fiddo da wayarsa na mika
masa ya karba sannan ya dan ware murya yace
waye? Dogari ne Allah ya
taimakeka, lfy? Ya bukata a fusace yace Allah ya
taimaki yarima. Sarki ke
nemanka fada karfe 12 na rana.ya kalle ni cikin
wani yanayi sannan yace. Allah ya
nuna mana. Hannuna ya kamo muka zauna
bakin gado. Na kyale shi ganin kamar
hankalinsa ya dan gushe saboda 6acin rai. Ya
kalle ni,ni kuma na dan zame
hannuna. Humaira ya zan yi da fareeda?kayi
hakuri kuma kayi biyayya ga
mahaifinka, Allah yana nan. Ya tallabo fuskata
ya kara yi min kallo sosai,na dauke
kaina. Ya kara yin kasa da murya. Nayi hakuri
shine tunaninki? Nayi dan
murmushi,bayan wuya sai dadi yarima,sannan
ka daina fitar daren tunda bata
so,dole ka rinka gujewa 6acin ranta matukar
kana son kwanciyar hankali. Kinga
kalle ni". Ya fada... ,Na kalleshi a kaikace ya
nuna min saitin zuciyarsa,wani abu ya tasayan
nan
kamar dutse gaskiya guduwa zan yi,bana zama a
kashe... Na kyalkyalce da
dariya,sai kawai naga ya sakko kasa ya zauna
gabana tare da tsire ni da ido.
Dariya mana baki ko?ya fada kamar zai yi kuka.
Nace,to don Allah ko ni yarinya
yanzu nace zan gudu? Baki sani ba ne wallahi da
gaske nake. Na zaro ido,don
Allah kayi hakuri kada ka 6ata ran mahaifinka.
Yayi shiru,sai kawai ya ba ni
tausayi to shi wa ya ke so?na dube shi a
tsanake tare da ambaton sunansa.yayi
saurin dubana. Na ba ka shawara? Ya daga kai
yanayin yadda ya yi kamar yaron
goye, sai ya bani dariya. Nayi murmushi. Idan
kun je fada ka kama bakinka,kada
kace zaka maida magana saboda gudun yin
SUBUL DA BAKA,ka fadi abin da zai
janyo wata matsalar da tashin hankali.
Murmushi kawai yayi. Tashi ki kawo min
karin kumallo na. Na mike na tarar lokacin suka
gamasaukewa,don haka sai da na
jira tukunna.... Kafin na kai masa ya wanke
kewaye tare da gyara dakin. Na rasa abin da
zance
masa,amma faduwar gabana ta karu. Ina ajiye
farantin wayar nayin kara. Dariya
na ga yana yi kafin ya kara wayar a kunne.
Haba Alhaji nayi fushi,ka jira dawowata
zaka kwana yau don ubanka! Hakan ya fahintar
dani abokinsa ne. Ya ce,kana ta
wannnan albishirinka?...ina ganin Allah ya
amshi addu'ata...I FOUND A LITTLE
BABY THAT I DREAMT ALWAYS TO BECOME MY
BELOVED" ya kyalkyale da dariya
kamar bashine ya gama fushi yanzu ba yace.
"AM TELLING YOU. Ya dan saci
kallona. Uhm! I CAN'T EXPRESS BUT JUST
EXACTLY I DESCRIBED. Bana fahimatar
turancin,amma sai kawai naji cewar na tsargu
da hirar. Ya kara cewa. Wlh abokina
HUNDRED PERCENT. Na mike zan bar dakin,yayi
saurin nuna min hannu alamar na
zauna ya na fadin. DO YOU KNOW WHAT? Na
gama kamuwa billahillazi saboda
JUST 3 DAYS bamu hadu ba sai ga zazza6i...ka
dai bari zan kira ka anjima,akwai
STORIES A LOT. Yana gama fadin haka ya ajiye
wayar. Ya kalle ni yana murmushi
idanunsa sun washe sauran dan jan kadan.
Taho 'yar kanwata muyi karin kumallo
kin ji? Ko baki gode da aikin da na yi miki ba?
Na yai murmushi, Na
gode,amma...maganar ta makale saboda sauyin
da na gani a fuskarsa... Haka na dinga cusa
wainar kwan sbd kallon daya tsareni dashi yana
karin
kumallon duk ya samu nutsuwa, baki son kallo
ko? Na daga kai Eh wllh, yayi
murmushi kiyi hakuri zaki saba dashi bansan
sanda nace kallon? Ya kurbi ruwan
zafi kawai bai bani amsa ba wai ke ya maganar
karatunki? Babu nace babu fa
kikace ke bakison ilimine? Nayi murmushi kusan
hakan. sbd me? Ina ganin bacan
alhairin yake ba, istihara kikayi ne? Nayi
murmushi ina mmkin yanda baya gajiya
da tambaya. Gimbiya Humaira ya fada yana
murmushi idanunsa kyar akaina nayi
saurin kallonsa. Sbd yanda naji sunan
banbarakwai. Aka buga kofa waye? Rabi
tace Humaira tazo muje karbar albashinmu idan
ta gama. Nayi saurin mikewa ya
kalleni da Allah zauna na karyar da wuya na
kalleshi yayi murmushi a dawo lfy jeki.
Kayan fa? Idan kin dawo kya kwashe ko baza'a
bamu salala ba? Nayi murnushi
duk na dauka wasa yake zan baka mana nawa?
Ya tambaya duk yanda kake so
yayi murmushi rabi zaki bani harda aikin da nayi
miki yau. Nace to.
,Duk zatona Gimbiya ce za ta raba kudin ashe
wasu ne daban. Muka bi layi nice
ta 2n karshe,ga shi biyan baya sauri shi yasa
muka dauki lokaci mai tsawo,har ku
san karfe 1 saura. Ban tarar da shiba,amma na
tarar da 'yar guntuwar takarda
gefen faranti wanda ya rubuta da manyan baki
cewar 'KIN AMSO? TO KI AJIYE
MIN NAWA KARKASHIN FILO. hakan kuma aka
yi,na ajiye na fito. Da dubu 7200 na
isa gida,saboda na biya basussuka sauran kudin
icce da maggi kawai ya rage,su
kuma ko su Aisha na aika. Inna tayi murmushi
da na gama yi mata bayani tace.
Gwadaki yayi kawai yaga cewa,kina da rowa?
yanxu bada 50 a sawo masa furar
sai nonon ma na 50 ko yagot zaa sanya?"Yadda
ki ka ka gani inna. Na fada. Tace.
A hada masa duka,kin san maza akwai son din
dadi. Yau kam har balangu muka ci
da lemon kwalba. Ana gama sallar isha'I ya
iso,yace na yi masa iso wurin inna.
Bayan sun gaisa yace, don Allah inna ina son
Aisha da sumayya da kuma humaira
suyi min rakiya wani wuri. Jin an ambaci su
Aisha yasa inna cewa Allah ya kiyaye
yarima,mun fa gode. Ni kuwa saura kadan na
kurma ihu don takaici. Ba wai rakiyar
nake ji ba tambayoyinsa da son maganarsa ke
damuna. Muka fito fuskata a daure
su Aisha sai tsalle suke yi don rashin sanin
ciwan kai. Muka shiga motar nan naji
wani tsam!karo na 2 dana ta6a shiga karamar
mota,ranar da ya sawo wa inna
magani sai yau... Wani daddadan kamshi (not
clear)na dai daure duk wurin sai kallona suke
yi,ban
san me suke cewa ba kamar suna wani yare.
Ana cikin sharcewa ana gyarawa
suka shigo,naji takaici. Shi kuwa kamr mutuwar
tsaye yayi bakin kofa zuwa can ya
tako kusa dani,tare da sunkuyowa yace. Masha
Allah. A hankali. Abin dariya abin
haushi,sai naga mata na faman barbaza gashi
nayi hakuri ta gama kawai tana
sakar min kai na hade shi wuri guda,na cushe
kamar yadda nake yi. Tayi saurin
cewa. OH SORRY YOU NEED HOSE WIFE? Ko
kallon sakarai ban yi ba, nayi gaba
kawai abina. Su sumayya kuwa kowacce hannu
cike da kayan zaki ana washe
baki. Maimakon muyi gida,sai naga ya karya
kwan,shagon da muka shiga sai dana
tsorata don ganin duniyar dake ciki. Ya sami
kujera 2 ya zauna tare da miko min
dayar na zauna. Ya dubi sumayya da Aisha dake
tsaye yacekunga kekunan can?
Sukace eh yace to kowacce ta turo guda 1 ku
zagaya duk abnd kukeso ku dauko
ku zuba aciki. Yaro! Yaro! Wani takaicin sai yaro
wllh bai ida rufe baki ba su ka
kwasa da gudu sukayi gaba na dubeshi nace
mekake nufi? Yace shopping zanyi
musu, danAllah meyasa kakemin haka? Kinason
sanin dalili? Nayi shiru cike da
takaicin na tambayeshi ya tambayeni yayi
murmushi konayi miki bayani a yanzu
bazaki gane ba. Kamr nace masa sbd
mahaukaciya ya daukeni ko? Amma sai nace
kaga kai kake haddasawa kanka fitina da rashin
kwanciyar hankalin gimbiya. Yayi dariya ba wani
abu lokaci ne zanyi magana yace waike baki
kunshi ne?
Shiru kawai nayi sbd bani da amsar bashi.
Samarinki nawa Humaira? Ashirin na
fada, ya kyalkyale da dariya har nayi mmki yace
ashe kin iya gatse? Wllh idan
muna tare sai naji kamar na saceki na gudu.
Nace eyeh? Ya dubeni da sauri nan
da nan na fahimci SUBUL DA BAKA yayi idanuna
jajur nace me nayi maka zaka
sace ni ka gudu? Yanzu kai.... Ke! Ya matso da
kujerarsa wllh wasa nake nan da
nan ya hau yan kame-kamen furta kalmar. Daga
nesa na hango lodin kaya na yo
kanmu ba ka hango masu tura kayan saboda
tsoran da suke yi. Ni tsorata
manayi,tunanina kayan ne suka turo kansu. Sai
kawai na ga su Aisha na mike tare
da salati. Me ke damunku su.. Ya taso babu
ruwanki. Waje na fita na tsaya bakin
mota ina jiransu kawai. Maza 4 suka rako su
kowanne hannunsa da kartin ledoji.
Har muka isa gida bance komai ba,nayi gaba
abina,shi ya jido kayan kafin ya
shiga. Na gama fadawa inna komai. A tsakar
gida ta ta fito tana salatin wadannan
himilin kaya,yana tsaye shi kuma ya goya
hannayensa duka a kirji. haba yarima
har yaushe zaka biye haukan yaro? Inna kada
ke maki ga laifinsu,wlh ni na sanya
su ko humaira? Shiru kawai nayi. Ya kara yin
kasa da murya... Amma inna ayi hakuri. Nan da
nan inna ta gaza cewa komai,sai kawai ta shiga
daki tana yi masa godiya. Ya kalleni ni,dauko
min furar ko baki dama ba? Na wuce
kawai na kyale shi. Zaune yake saman tabarma.
Kofar daki na ajiye kwanon na yi
tsaye. Ya dube ni kawai,sannan ya fara shan
furar. Ga mamakina sai na ga uya
shanye duka ya mike tar da matsawa kofar
daki. Inna na bar ku lfy. Tayi saurin
cewa. Allah yabamu alheri yarima an fa gode.
Su Aisha murya zauu!Aka ce yaya
yarima sai gobe. Yace Allah ya huta gajiya kunji?
Yaya dube ni,yace. Mu je!!!
Kamar kada nabi shi,haka na daure muka isa
bakin motar. Ya jingina bayansa a
motar tare da fuskanto ni yana kallona. Ya zura
hannu a aljihu ya fiddo ambulan
ruwan kasa mai fadi,ga tudu yace. Ungo kudinki
ni wasa nake yi miki. Na sunkuyar
da kai kawai. Kin ji? Nadai yi shiru. Ki kar6a
nace dare na kara yi kin san halin
Gimbiya,ana can an dake lamba... Allah ka
dauka. Nace dashi. Wallahi wasa nake
yi,kar6i kudin babu inda zan je dasu. Jin ya
rantse yasa na mika hannu,sai kawai
ya fizgo ni na fada kirjinsa,nan da nan na ji
wani irin abin duniya mai wuyar
fassarawa. Ya rikr ni gam!nayi kwance a saman
kirjinsa. Wai fushin na mene ne?
Ya fada tare da sunkuyowa saitin fuskata.... ,Sai
kawai na tsinci kaina da sunne kai a jikinsa. Ya
dago ni yana kallona
fuskata. Na runtse idona ni kaina na rasa kunyar
ta mecece. Kunya ta kuma ake ji?
WONDERFULL ya fada. Ni dai ka sake ni ban so.
Na fada murya na rawa. Cewa
zaki yi na kyale ki ba wai na sake ki ba,wannan
kalmar bata har abada
tsakaninmu. Idan kina son na kyale ki kuma sai
kin fada min fushin da kike yi tun
fitarmu. Ba fushi nake ba. To mene ne? Yadda
yayi maganar ya kara jefa ni cikin
yanayi. Gida zani. Na fada da kyar. Zan raka ki
yau,kada ki damu. Ya fada tare da
kara riko ni. Wannan abu yayi min yawa. Na
fada a zuci. Ga shi sam haka kawai
na kasa kallonsa,da kyar nace. Wannan fa
haramunne. To naji,amma idan na sake
ki kada ki matsa kin ji? Na ce to. Yana sakina na
yunkura zan kwasa da gudu,yayi
saurin maida ni jikinsa yana fadin. Ashe kina da
wayo? To ai ni... Nayi shiru. Sai
kawai na sanya kuka. Yayi shiru,zuwa can ya
sake ni yana fadin. Kina rugawa zan
biki. Na tsaya cak! Goge hawayen,goge su. Sai
kuma yayi shiru. Baki so ko? Nace
uhm. To na bari muje na raka ki gida. Zan je
kawai. Ke dai mu tafi,ai ba roko ki ka
yiba,ni na sa kaina. ,Har tuntu6e nake yi don
sauri,jikina ya yi min wani iri. Zuciyata ta tsaya
wuri 1
cak!yayi saurin shan gabana. Kin kagara ki rabu
dani ne? Nayi shiru kawai. Wai
wannan snkui sunkui da kan na mene ne?
Muryarsa na kara dagula min lissafi,na
ce. Ba komai. Humaira kenan,wlh miskilancinki
na burgeni. Da akwai namiji gidan
nnan yau da a nan zan kwana a dakinsa. Tsoro
ya kamani,anya yarima baya da
ta6in hankali?kamar wanda ya shiga zuciyata,sai
ji nayi yace. Ke ni idan muna tare
rasa hankalina nake yi. Abin nan yafi karfin
kwalkwalwata,sai kawai na hau
addu'o'in tsari a zuciyata da kyar ya kyale ni
kamar zai bi ni cikin gidan. Hakan ya
kara lalata kwalkwalwata tare da tunzura
zuciyata zuwa wani babin tunani. Labule
kawai na daga na fara ce da inna. Inna!inna!
Yarima yana bani tsoro. Tsaye ta
mike. Abin tsoro ne humaira,domin na karanto
inda ya dosa. Na mika mata
ambulan. Kudin dana bashi ne ya maido. Tace
daman na fada miki jaraba ki yayi.
Ta hankada filo kawai ta ajiye. Kinga kaya?nayi
shiru,tace gaba da cewa. Kaya ne
wani abun ma ban san ko mene ne ba. Na
kwanta kawai. Inna kyale su sa cinye
tunda su suka debo. Idan akwai wanda ba'a ci
ciki fa? Nace A'a to
,Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Ina ta fada.
Shiru nayi maganganun nadawomin
cikin wani irin yanayi tare da kwanciya danayi a
jikinsa. Nan da nan tsikar jikina ta
tashi. Fasalinsa ya fado min,na lumshe ido,sai
gefin asuba bacci ya sace ni,kiran
sallar farko na farka. Na tsinci kaina da kosawa
gari ya waye na tafo aiki. Karfe 6
saura muka fiddo kayan nan don kara dubawa
ni da inna,bayan mun karasa lazimi.
Ko madara tafi guda 10,wasu abubuwan kam
mun kasa gane su balantana mu san
yadda ake amfani dasu. Ta dube ni,idan yazo
kya tambayar mana shi yadda
suke,idan muna iya amfani dasu toh!idan kuma
ba ma iyawa lillahi warasulihi gara
ya mayar a bashi kudinsa da yayi asaraa,ko
yakika gani? Nace gaskiya
kam,sannan da alam dinki zai mana tunda har
ga teloli muka je fa. Tace,su Aisaha
sun fadan. Kinga kudinmu sun kara auki ke
kadai zaki yi sauran musha shagali. Na
karasa maganar ina murmushi. Sai mu yi sana'a
kada mu ajiye haka nan,kinsan
zara bata barin dami. dauko mana su nan in tisa
ko naji sanyi,hadi da sauran suna
cikinjakar filo. Sai da na hure kyandir din kafin
na tashi,saboda hasken daya
gauraye ko'ina wato gari ya waye. Na fara mika
mata na ciki ambulan din ni kuma
ina tisa canjin da suka kwana. Humaira!!! Inna
ta kira ni da karfi,wanda yayi
sanadiyar tashin Aisha da sumayya. Tsaye na
mike ganin bandir din 'yan dubu-
dubu a hannunta ina zare idanu cikin tsoro.
Karkarwa da hannuna ke yi ya taimaka
wa bandir din faduwa kasa. Munfi mintuna 10
muna musayar kalllo kafin tace. ,Akwai abin da
yaron nan ke nufi humaira,lallai kudin nan
koma masa zasu
yi,domin sun fi karfinmu. Idan kin je ki ce inna
na son ganinsa a yau din
nan,wannan alamari yafi karfin tunainmu. Kasa
ce mata komai nayi,na shiga
shiryawa domin na ji an yi sanarwar karfe 7
saura mintuna 13 a rediyon inna. Har
na bar gidan inna ba ta daina sambatu ba,tana
faman mita. Na isa kan lokaci
kamar kullum,na shiga gyaran falo,amma cikin
yau ya fi na kullum saboda sauya
tsarin da nayi. Wanda yana 1 daga cikin
gargadin da Gimbiya ta yi min,cewar duk.
Bayan sati 1 sai na yi hakan. Su kuma 'yan aikin
rana duk bayan sati 2. Lokacin
dana kammala ina goge 10 har da ku san
kwata,motsin fitowarsa naji tare da
kamshin turarensa da ke fadar min gaba a duk
lokacin dana shaka. Kamar kullum
hadin baki,sai ga Gimbiya ta shigo da irin nata
kamshin nan da nan falon ya hade
ya gauraye da wani irin daddadan kamshi. Na
bada gaisuwa ga kowannnesu ba
tare daba kalli 1 daga ciki ba,sannan na ci gaba
da aikina. Ina jiyo sautin
murmushinta,lokacin da tace. Barka da safiya.
Ban ji ya amsa ba,amma wata kila
yayi mata da fuska,nasan kasaitarsa. "Na zo yin
karin kumallo da yarima,tunda ni
an ankasa zuwa har yau ayi dani, nayi gayyatar
cin abninci har na gaji. Kai kuma
ka. Kasa gayya tatat,shine yau ni nazo. Bai dai yi
mgn ba,ta kara cewa. Da za'a
taimakamin yau kadai da na fita da kai unguwa.
Lokacin ne yayi mgn da wata 'yar
shakakkar murya. Yau bani da lokaci,sai dai
wani. Dama nasan haka zakace,wai yarima
wannan halin ko inkulan da kake nuna min
na menene?ta katse shi da fadar hakan cikin
nuna tsananin 6acin rai. "Humaira
zoki bani kalaci. Ya sauya mgnr yana mai kara
kallona.nayi saurin dauke kaina
saboda ganin irin kallon da yake yi min. Na ajiye
kayan,ta kalle ni cikin fushi. Je ki
kawai,zan yi SERVING dinsa. Ya dube ni,zauna ki
bani abinci humaira. Hankalina
ya tashi saboda ganin yana neman haddasa min
fitina da tashin hankali,wanda zai
haifar min da rashin zaman lfy. Rai a 6ace ta
kalle shi,tuni ya maida hankalinsa
gare ni. Haba yarima,me yasa kake neman
gwasale ni a duk lokacin dana ke
kokarin nuna gwaninta a wurinka? Shekeke ya
kalle ta cikin izgili yacekarya ki
ke,dan da baki baza borori a kaina ba... Ni kake
karyatawa a gaban BAIWATA?
Shin zuwa kika yi neman tashin hankali da
neman rigima,ko kuwa gaisuwa ce kika
kawomin da gaske? Ya fada yana mai kare mata
kallon raini. Ta sassauta
murya,tace. Zuwa nayi in faranta maka rai
saboda... To ki bi abinda nakeso,bana
son shisshigi,nan sashena ne ina da ikon yin duk
abin da naga dama a harkokkin
gidan,sai ki bari ranar da naje inda kike irin duk
yadda kike so shi zan bar kiki
aiwatar. Ya na gama fadin haka yace. Zo ki bani
BREAK humaira. Jin Gimbiya tayi
shiru yasa na dukusa ina zuzzuba masa,sanan
ita ma na hada mata tayi min wani
mugun kallo,kafin tace. ,Sanya ki nayi? Shi
kenan ya janyo min abinda nake gudu!
wammamn mgn ita
kawai nake maimaitawa a raina,kamar nayi ta
kurma ihu. Ta daka min tsawa. Ki
kayi wa mutane tsaye munafukla,wuce ko na
harfe ki da kafa,mai kama da
aljannu!!! Wannan kalma tayi min zafi,sai kawai
naji kwalla sahr! Shi ma ya fusata
yayi mata tsawa. Tsawar danaji har cikin
raina,saboda na san fitina kawai zai kara
janyo min,yace. Kiranki nayi,ko na aika miki da
katin gayyata?don me zaki zo ki
haddasa min fitina? A hanzarce ta dube shi
daidai lokacin na bar falon,amma duk
da haka ban daina jin amon muryarsa ba,yana
balbala mata masifa. Daga jin
muryar kasan kuka take son yi. Yarima zan
hadddasa maka fitina da BAIWA? Mene
alakarka da ita?shi yasa na lura kana yi mata
wani kallo na daban? Ke!kada ki
kullan sharri... Ta mike tsaye tana fadin. Lallai
zan dauki mataki a kan
wannan,domin bazan ta6a daukar rai ni ba. Na
juyo karar buga kofa alamar ta fita
na rushe da wani irin kuka. Ba motsin dana ji
kawai ba,turarensa maya ganar dani
cewe shine ya shigo. Kukan na mene ne?saura
kadan na dauko ta6arya na kwada
masa don takaicin wannan tambayar ta rainin
hankali da ya wurgo min. Zaki yi
WASTING hawayinki a wofi, domin ita ba Allah
bace da zaki damu kanki daon tana
ganin kin yi mata laifi.saboda hauka da tsabar
son kai ta mance ni ne mai laifin,ko
kuwa fib karfi take son nunawa?kizo muje muyi
kalacin kada yunwa... Na dora
hannu saman kai na kurma ihu,ina fadin. Ni
kam kana neman haddasa min fitina
alhalin ni din ba wata bace,iyayena ba wasu
bane dazu su kare min. Da sauri ya bar kicin din
ganin alamar su Rabi na da niyyar zagayowa ta
baya.
A rude suke,kuma a kaidime gaba daya har da
mutuminsu suka hada baki. Lafiya
'yar fulani?sai a yau na san wannan suna ashe
haka suke fadamin idan bana
nan,ko suna kwatancena. Na dago kaina jage-
jage da hawaye. Don Allah rabi ku
yafe min abinda nayi muku iya zaman da muka
yi,karshin zaman gidan nan yayi.
Ta dube ni kamar ita ma zata yi kuka tace.
Wallahi muba kiyi mana komai ba
yaushe ma mgn ta hada mu ballantana ki 6ata
mana rai?laifin me kikayi wa
yariman? Zanyi mgn ya shigo duk suka tsorata
tare da ja baya suna kame-kame.
Humaira zo ina son ganinki. Ya na fadin haka ya
juya. Rabi ta matso tace tashi
kije watakila yafe miki zai yinaga kamar yana
tausaya miki. Ni ba zan jeba. Duk
suka zabura da fadin. Kin yafe aikin ne? Nace,Ai
yazama dole,saboda wacece ma
keyi domin ta ita ya hada min gwarmai(rigima) a
wurinta. Bamu gane ba. Inji
harira. Na fada musu badakalar da ka yi yanzu
a falo,duk suka hada baki suna
INALILLAHi. Yau ke kin bani. Allah ya tsare ki da
shiga wakafi don da wuya idan
baki yi yariba. Na rushe da kuka cikin wata irin
kidima. Zubairu yayi dan tsaki tare
dayin kasa da murya. Ba zata yi tari ba,domin
yarima SON HUMAIRA yake yi!!! Duk
muka kwalala masa idanu cikin firgita abinka ga
dan duniya sai yayi murmushi
yace ,Wallahi na fahimmace haka tun ba yau
ba. Saboda haka kada kiyi wa kanki
salalar tsiya,arziki ne ke binki. Ya kara yin kasa
da murya. Don Allah humaira kin
san ya mu cikin barorinki?mu kam daman
Gimbiya...tishe kunnuwa na nayi tare da
fasa wata irin kara. Yarima muka gani tare da
dka musu wata irin tsawa yana mai
korarsu,wai sune ke kara tsoratani. Ina kallonsu
ta bayan taga sun la6e. Shi kuma
ya fara magana a hankali. Rigimar Gimbiya
humaira yawa gareta kullum da abin da
zata tsiri. Fitar nan da nayi wurin mahaifinta ta
kai ni kara,wai na fifita ki a
kanta,kin ga duk ta zubar da kimata wurin
iyayenta. Yanzu hak na baro tana mgn
da mahaifina,ban san abin da zatace masa
ba,ta 6ata ni gurin nawa. Ta
durkuso,sannan yaci gaba kiyi min mgn na sami
saukin abin da nake ji azuciyar
ann koda kuwa ba mai bdadi bane. Kada kiyi
fushi dani a lokacin da nake bukatar
taimakonki. Lokacin ne daba ni da wani gata sai
wanda kika bani a matasayina na
marayan Allah. Kamar na shake yarima nake
ji,sai kawai na kara fashewa da kuka.
Yau ni HAMEED na gata kaina! Sai kawai ya fice.
Na duke ina shawarar na tafi
yanzu ko kuwa na bari loacin ya cika? Ban
karasa yanke hukunciba naji an fizge
ni. Na dago kai sai kawai naga yarima ya rike
hannuna. Dukewa kawai nayi ban
dagi ba,sai da naga mun shiga sashen Gimbiya
kawai sai na kara maida kaina
kasa. Shin dukanta zai yi?cin mutunci ko kuwa?
Ganin mun doshi dakin kwananta
ya samya nayi hanzarin kallon shi.
Naku
ANaM Dorayi Amadadin Zainab Dahiru Wauw
nakecewa muhadu a kashi na 2


Subul da baka 2 page 1
Posted by ANaM Dorayi on 07:10 AM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Kwance take rub da ciki da gani tana
cikin damuwa mukayi sa'a ba kowa da gani
korarsu tayi. Ya jefar dani gefe ya isa bakin
gadon tare da tallafota ya tada ta zaune
kallon da take masa me dauke da mmiki,
sha'awa tare da tambayoyi masu yawa ya
durkusa gabanta yace fareda ki gafarci
yarinyar nan ta tsorata da fushinki ki yafe
mata domin kaunar da muke yiwa juna.
Kallo daya zakayi mata kasan ta fara rasa
hnklnta don hk tayi saurin kallona tace na
yafe miki Humaira dama bakiyi min komai
ba, idona shabe-shabe da hawaye saiga
murmushi ya subuce min. Ta maida
kallonta gareshi dahra tym din bai tashi dg
durkusonta da yayi ba saima kallonta da
yake yana smiling na tuba nima a gafarce ni
amaryata kuma gimbiyata... Ban jira amsar
da zata bashi ba nayi waje tare da karayin
godiya da goge hawayena kowa ni yake
kallo sbd ta gabansu muka wuce, banga su
rabi ba don hk na wuce dakin kwanansu
don na gyara gashi lokcn ya kusa. Ko rabi
banyi ba ya shigo har kewayen na kalleshi
tare da banko min harara kinsan Allah yau
saina kai kararki ga inna na gaji da irin
salon rigimarki wllh. Na mulmula maganar
tare da lailayata kafin nace rigima ta wuce
irn naka kuma kafin ka kaini kara nizan fara
kaika In Shaa Allah. Haka kikace? To bari

Please Login or Register in order to submit comment