Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momy da Maimartaba ba su ce
komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa
maimartaba daka musu wata irin tsawa da
kowa da ya yi mamaki. Nan da nan kowa ya
na'abba. Wannan ai hauka ne! Ya fada,
sannan ya ci gaba da cewa. Ba ku da
bambanci da dabbobi, musamman kai. Ya
nuna Yarima. Gabana ya yi wani mummunan
faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai
zan koma. A matsayinka na namiji yausha
zaka biye wa mace musamman lokacin da
kishi ya turniki zuciyarta? To kowa ya zauna
zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan
zan fara da abin da ya kawo mu. Ya kalli
Yarima, Ya sunanta? Kansa duke ya ce,
Humaira. Humaira zo daga nan. Ya nuna min
kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni
saboda na san kaina kawai zai sare da adda
shi ne sakamakona.
Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake.
Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba. Na
gode, Allah ya yi miki albarka. Wane ne
mijinki kuma?.saboda har da wannan
tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima
ce min yake yi matar abokinsa. Wayyo duniya!
Wayyo IƱna! Wani sab9n kuka ya zo na ji
kamar na zura a guje. Ko ba kya iya magana?
Na ce wane ne mijinki? Wane ne fa banda
Yarima. Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta
ke zaune. Cikin tsananin bacin rai maimartaba
ya kalle ta.. Kada ki yarda na gane ba ki da
da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani.
Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni,
abinda ya ba wa kowa mamaki. Ya kalle ni,
Humaira ko zan san wane ne mijinki?
Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na
iya furta. YARIMA NE! Amma don Allah ka yi
hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da
son.......Dakata! Bari kukan kada ki sarke.
Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi
ya sa ni da Yarima saurin kallon juna. Ya mike
tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na
mike saboda an bar ni ni kadai a zaune.
Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe
wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko
lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya
ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban
taba shan riwan gidansa ba sai a nan. Sai ka
tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai
hada kan iyalanka. Yana fadar haka ya yi
hanyar waje, saura kuma suka mara masa
baya.
Wani yayan Yarima ya banko mini harara
wacce ta sa dole na yi kasa da kaina. Karaf! A
kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu
da ma. Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana
fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka
shirya da ma don a ci mutuncinta. Yan baya
suka ji abin da ta ke fada, amma shi
maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota. Ta
yunkura tare da shako wuyana ta makare ni
jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta
kwada min abin fulawa ta fasa min goshi. Da
kyara ya kwace ni tana faman dukana da
harbi, ni kuwa sai kuka nake. Hayaniyarta ta
dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina
gidan tana ta hauka. Jikina sai rawa yake yi
saboda tsoro duk na firgice sai bari nake. Da
kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya
daure da bandeji.
Wayarsa ta fara kara ya dauka tun bayan da
ya yi sallama, ban da kalmar TO babu abinda
yake fada har ya ajiye. Ya kalle ni asanyaye.
Maimartaba ne ya ce kar k8 sake ki kara
kwana nan gidan, na maida ki can gidana inda
Zarina ta ke ku..... Wallahi Kano zan tafi, ba ni
kara kwana nan garin, ban iya masifar
Gimbiya ko kadan nan din ma kana ganin ga
manya ba ta j8 kunyar raunata ni ba, ina ga
nan ware daga ni sai ita? Aure ne na yi na
Allah, amma ba zan kuma ba. Idan ita ba ta
da hankali ke ma....... Kwarai ni ma haukan
nake a kan komawa gidanka kam, kai auren
gaba daya ke bana yi, ko dole ne? Na fashe
da kuka. Da ma tun farko ni wannan masifar
nake gudy wallahu. Ya langwabe kai. Allah ya
baki hakuri.
Na hayyako masa. Eh da man duk wanda ka ji
ana ba hakuri ai an gama cutarsa. Haba
Humaira 8na hankalin ki ne yau? Daga turu na
fito karewar hauka. Na mike ina faman hada
kaya a jaka. Ya karaso murya a raunane ya ce.
Don Allah ki yi hakuri, mu gode wa Allah da
matsalar ta tsaya gurin Zarina kadai, kin ga
alherinki ne ya sanya mahaifina ya yafe mini
kan rashin bin maganarsa, shu ya sa aka ce
YADA ALHERI BAYA ka tsince shi gaba.
Wallahi.na tabbatar da lallai ya ji dadi sosai a
kan abinda kika aikata, domin ni ina tunanin
fushi da wulakanci wanda zan fuskanta a
lokacin da ya gano abin da nake boyewa, don
ko mahaifiyata ba za ta tsira ba. Shi ya sa na
nace wa aurenki don na san ke alheri ce a
wurina. Wallahi ba ki ji yadda hankalina ya
kwanta ba..... Dole ka sami kwanciyar hankali
mana, ni tunda ka ti silar tada nawa.


Xaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100




Subul da baka 3 page 2
Posted by ANaM Dorayi on 05:17 PM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Ya yi murmushi,
"ya xa a yi na yi silar tada hankalinki?" "ban
sani ba". Na fada lokacin da nake qoqarin
rufe jakar. "Allah ya ba ki haquri, kin ga
maimartaba ya yaba hankalinki kada ki yi
abinda xai sanya ke ma ki fita ransa kamar
xarina". "dole kuwa in yi, domin na tsira da
raina da lafiata.. A gabanka ta fasa min jiki, to
ina ga ba ka nan?". "nima ai bayan idonta
gashi kina mini tsiwa mai ya hana ki rama? Ko
kin san xarina ta gane kin tsorata da ita? To
wallahi ni ba xan tare miki fada ba, domin
akwai lokacin da dole ba na nan kinga kuwa
dole ta ringa ba ki wahala, amma idan ta ga
cewar ke din ba ki tsoronta, to lallai xa ta
shafa miki lafia, don Xarina ba ta fi qarfinki ba ni
a ganina.
Abin mamaki kishiya...". "ka ga malam ni ba
fitina na xo yi ba...". "nima bana son ki yi
fitinar, amma ya kamata ki amsar wa kanki
'yanci, ki nuna ke ma fa MATA ce ba baiwa
ba. Maganar gida kuma wallahi babu inda xa
ki tafi yau a gidana xa ki kwana ke da
axara'ilunki xarina ta qarasa ki". Na fashe da
kuka, sai kawai ya shige bandaki. ***** *****
*****Tashin hankali ba a sa masa rana,
kwana 2 da komawata gidan aka kawo mini
dattawa guda 2 wadanda xa su ringa tayani
aiki, sabanin gimbiya da nata yara-yara ne
majiya qarfi, kuma aqalla xa su kai su 9 ko 10.
Qaton gida ne da babban 'gate' sannan
kowace bangarenta guda. Yau xan amshi girki
don haka magariba na
yi na fara kimtse-kimtse, 2n 6:pm na sallami
su dagwayye ana gama sallar isha ya shigo.
Na kawo masa abinci ya kalleni. "yo ina en
aikin?". Ba tare da na yarda mun hada ido ba
na ce, "sun tafi sashensu na sallame su".
Murmushi ya yi, "to dauko abincin mu tafi
sashena". Gabana ya fadi, amma ban yarda ya
fahimta ba. A falonshi muka xauna mai tattare
da kayan more rayuwa, kujerun kansu sun ishi
mu2m kallo, ban iya tsayuwa fasalta falon
amma ina iya cewa komai ya ji na more
rayuwa, hmmm! Jin dadi sabo na fada a xuci.
(kun ji mu2niyarku an kile an fara 2nanin jin
dadi). Allah sarki su inna qwalla suka kwanta
suka kwanta a idona da na tuno inda na baro
su. Na duqa xan fara xuba masa abincin
kenan naji an ingijeni nayi baya- baya na fada
qasa da qarfi, kafin na yi wani motsi ta biyo
ni da qafa tana harbi, a rude ya taso tare
da ture ta wuri guda ita ma. "ke wace irin
dabba marar 2nani ce fareeda?". "wallahi
wannan munafukar sai na hallakata a
gidannan, don uban...". fas! fas!! tasst!!! ya
wanka mata kyawawan mari guda 3 a jere.
"kar ki dauke ni sakarai, shashasha mana, ke
me ya sa kike da fitina da rashin son xaman
lafia ne? ko don kin ga ina tausaya miki
saboda abinda ke jikinki?". ta harxuqo masa
kamar ta rama marin da ya yi mata. "mene
kai din in ba sakarai shashashan ba?". ya
qara wanka mata wani marin guda 2 qwarara,
ya juya xai dauko kebul (cable) ta ko dauki
wani abin fulawa ta kwada min a goshi. "bari
in kashe ta don ubanta in ga abin da xa ka
yi".
Tana qoqarin qara rusa min shi ya riqe da
sauri. 2ni jini ya balle yana son dauko
tsumma yana tsoron kada ta qara min wani
dukan. Ya fige ta ya 2ra waje kafin ya rufe
qofa ta banko da qarfi. Ganin idan ya biye
mata ni kuma xan rasa jini da yawa ya sanya
shi qyale ta, ya nufo gurina da sauri. Cak! Ya
dauke ni xuwa bandaki sai kyarma nake ina
kuka, tsoro da fargaba sun fi yawa a gabana.
Muka fito, ya janyo wani akwati sai ga kayan
dressing ya ci gaba da gyarawa. Ta xo kanmu,
"aikin banxa aikin wofi, an asirce ka, an
magance ka er talakaka ke wa wannan
kyarmar kuma don ubanki yau na ga yadda xa
ki kwana dakinnan. Na rantse da Allah ko
gawarki ba a yi mata wanka nan dakin domin
ba na hada daki da ke, banxa talaka". Ya
kalleta a wulaqance saboda yau da fareeda
ba ta da ciki, da Allah kadai ya san illar da
xai mata, ya ce "ga ki nan talaka wacce ba
gaji arxiki ba, maimartaba da ya tilasta ya sa
na aure ki Yau saboda munanan dabi'unki na
tsiya
yana dana sanin aurena da ke, 'yar talakar da
ki ke qyama ki ka raina kuma a yau ita ake
alfahari da ita a matsayin suruka". Bai rufe
baki ba ta hargitso masa qa2war talabijin da
ke manne a bango, ta fado bisa sauran
tarkacen kallon da abubuwar glass ji kake
ratsatsatsa!!! Ya dauki waya kamar mahaukaci.
"hello sahabi kana ina? Don Allah idan kana
iya fitowa yi sauri ka xo gidana yanxu". Ni
kam ina can rakube jikin bango kaina kamar
ya bare, ga wata masassara da ta taso mini,
ko tashin hankali ne ya hana ya yi min allura,
ko ya bani magani? Oho! Shi ya fada ita ta
fada, da ya matsa kusa da ita ta nuno shi da
kwalbar glass ya
rasa inda xai billowa tashin hankalin, iyakar
qarshe ya kai. Sallamar sahabi ya sa duk suka
yi shiru daga ita har shi din "Subhanallahi,
innalillahi, Hameed mene haka ya faru? "mtsew!
Shigo idanunka su gane maka
barna da asarar da yarinyar nan tayi min, duk
goshin er mutane, marainiyar Allah...".
"shegiya dai! Domin mun dade da sanin
shegiya ce ba ubanta ya mutu ba..." "haba
gimbiya don...". "yi min shiru munafuki, ina ce
da kai aka hada baki duk abin da aka qulla.
Ni xa a yi wa makirci? ayi wa plan? xa a
qirqira dafa abinci ana kaiwa sarki don
munafunci, wallahi yau sai dai ayi wacce xa a
yi". "Me fa xa a yi bayan na shirge ki kamar
jaka, don ba xan tausaya miki ba 2nda na ga
abin naki ya wuce 2nani...". "haba yarima har
sau nawa xan fada maka ka daina biye wa
mace?". "ka san Allah na dauka wa raina sai
dai yau na kwana prison, amma lallai gab na
ke da na lalata rayuwar wannan...". In taqaice
muku, haka muka kwana a tsaye ana abu guda
1, ko sallar asuba sai da yarima ya fara yo wa
sannan sahabi ya tafi gudun kada ta qara ji
min wani raunin. Suka dauke ni muka bar
gidan, amma sai da yarima ya tare ta sannan
sahabi ya fidda ni dakin, saboda yunquran da
take yi sai ta caka min gilashi a ciki. Iyakar
firgita da kaduwa nayi, 2n ina kuka har na
koma xare idanu, ni kadai na fige kamar
wacce tayi ciwon shekara. Gidan sahabi muka
je, na yi wanka na yi sallah, na nemi ciwon kai
da masassara na rasa, har qara kan da ya yi
min wani jummm! Allah ka raba bawa da
tashin hankali da fitina. Da qyar na sha rabin
kofin tea shi ma don Hafsat ta matsa min
matar sahabi. Ina kwallonta tana goge qwalla,
ta tausaya min. Xuwa can wajen 12 sai ga su
sun dawo. Ban san me suka tattauna ba, tayi
juyin duniya ta fita na qi fita, saboda sam
bana son ganin yarima, don a ganina shine
musabbabin haddasa min wannan fitinar, 2n
farko da bai dawo rayuwata ba kamar yadda
muka haqura da juna da farko, da hakan ba
ta faru a gare ni ba. Ganin ba ni da niyyar fita ya
sa ta ce, ya
shigo dakinta ya same ni. Baqin cikin
shigowarsa ya sanya ni kuka. Ya yi shiru kusan
mintuna aqalla 8-10, kafin ya fara magana
cikin sarqewar numfashi. "kiyi haquri humaira,
na san cewa ke ba mai son magana ba ce,
ballantana tashin hankali irin wannan, amma
komai ya xo qarshe, mai martaba ya amince
da na raba muku gida. Yanxu haka har ya
bamu wani a lowcost cikin estate din da ya yi.
Don haka ya sa kika ga mun dade sai da
muka kammala komai, yanxu haka ana can
ana sauran gyare- gyaren da ba a qarasa
ba". Ke dai da ke kara2 idan na tanka kin
tanka, ya matso kusa da ni, "ko sai xuwa dare
idan kin qara hutawa nan? Na ga can din ma
ba hayaniya, sannan babu aikin da xa ki yi,
saboda su malama dagwayye na can 2n
daxun". Ko motsi ban yi ba. Ya matso tare da
xama bakin gadon.
.....Farko da kuma kullum lallai tana kan
hanya, 2nda a duk lokacin da muka hadu sai
ta nemi xubda jinina. Ka sallame ni na tafi
gida don girman Allah, bana sha'awar xama
da kai ko da da qwayar xarra ne, domin
wannan fitinar somin tabi ce yanxu aka tsoma
hannu, ma2qar ina tare da kai". "kar ki so
kanki mana humaira! Yanxu wannan baraxanar
ce xa ta sanya ki bijire min? Ki iya 2na cewa,
so da qaunar da nake yi miki ya sa na take
dokar mahaifina na aure ki saboda Allah, na
xabe ki fiye da tsinuwar mahaifina da
fushinsa. Duk wannan baraxanar fareeda ta
sami qwarin gwiwa ne daga wurinki, don ta
fahimci kin kamu da matsanancin tsoronta.
Ina qara fada miki, ki tashi tsaye ki qwatar wa
kanki 'yanci, na tabbatar fareeda ba ta fi
qarfinki ba, kawai kin sa wa ranki tsoro ne. Ga
babban takaici ni din da take yi domin ni,
saboda ta fahimci irin son da nake
yi miki baki nuna damuwa a gare ni ba,
babu wata kulawa. Ki nutsu ki kwantar da
hankalinki ke ma ki nuna mata lallai ke ma
mace ce, saboda duk wannan haukan da cin
mu2ncinta ni ba xan sake ta ba domin
al'adata ba ce sakin mace, duk da ba ni
sonta, kuma ba xan sake ta ba ballantana ga
dana ko diyata da ke jikinta". Ya miqe "xan
jira ki a waje ki kimtsa mu tafi". Yana fita na
koma na kwanta wajen mintuna 5 sai ga
hafsat ta shigo, salati ta kama yi tana tafa
hannaye. "kai jama'a, wai humaira kwanciya ki
kayi? To wallahi tashi ki bi mijinki". Na miqe
ganin ta dauki abin da xafi. Ta biyo tana fadin
"wallahi ba ki da wayo yadda kika dace da
mai qaunarki haka, duk wannan fitinar bai
girgixa shi ba, amma kike ja baya da shi?
Wallahi da ni ce wani sabon salon shafin
soyayyar xan bude, kuma sai a gaban gimbiya
xan nuna don ta ji haushi". Nayi mata banxa
saboda na fahimci bata
gane irin salon masifar gimbiya ba. Xaune
yake cikin motarsa anaconda sahabi na tsaye
jikin taga ban san abinda suke tattaunawa ba.
Yana ajiye ni ya juya wai xai je gida, umma na
son ganinsa. Kai daure har lokacin da bandeji
a goshina, su dagwayye suka tarbe ni suna
masu jajantawa, tausayina fal a fuskarsu. Nayi
murmushi lokacin da na sami kujera na xauna.
"ashe duk kuna jin wannan fitinar?". "qwarai
kuwa ranki ya dade, wannan tashin hankalin ai
babu dadi yau kam na kusa da ita ya shiga 3
saboda yarinyar nan ba ta da kirki ko alama,
rashin ragowa a ba ya da dadi a rayuwa".
"hmmm" kawai na ce. Wayata ce ta dauki
kuka, nayi saurin dubawa don idan yarima ne
wallahi ba xan dauka ba. Sunan inna na gani,
wani irin dadi na ji har cikin raina, na kalli
dagwayye.
"ina ne dakina?". Ta nuna min da hannu.
"ga shi can". Na miqe tare da daga wayar
saboda bana son maganar gabansu duk da
sun santa. "Assalamu alaikum, inna kashe in
bugo miki kar a cinye miki kudi". "a'a barshi
ina da isassun kudi, yarima ya turo min kati
sosai, da ma wancan bai ko yi rabi ba... Duk
kuna lafia ko?" "da sauqi dai inna". Na fada a
hankali cikin muryar damuwa. Hankali tashe
ta ce "me ya faru ne? Ko mahaifin nasa ya
gano matsalar ne?". "a'a inna ko daya, shi
mun daidaita". Na fada mata duk yadda aka
yi "to me aka yi yanxu kuma?". "gimbiya ce
inna wallahi bana iya masifar wannan matar".
"haquri xakiyi, watarana sai labari". "inna ita
fa har gabansa yi min take yi, ga shi tana
iqirarin sai ta hallaka ni".
"duk kishi ne babu abinda xata yi miki
wanda Allah bai miki ba". Kamar in yi kuka,
wai me yasa inna ba ta ganewa kullum idan
ina kwatanta mata, ga shi ba na son fada
mata raunin da ta ji min kada hankalinta har
asmarta ta taso. "xata daina kiyi haquri dama
xama ya qunshi haka ga masu sabon aure,
kuma na hore ki da kai qararta ma2qar
abinda ya faru tsakaninku bayanan. Yana fada
miki baya sonta a baki, wallahi ba ki san
xuciyarsa ba musamman yanxu da take dauke
da ajiyarsa, duk yadda yake sonki yake kuma
dokinki da kin kai masa qorafin matarsa xai ji
kin fara sure masa. Ko 2nkararsa kika yi da
muhimmiyar magana ba xai wani baki
kyakkyawar kulawa ba, domin xai yi 2nanin
qorafinta xa ki kawo masa. Rayuwar aure
humaira haquri ake yi, kowace mace baki san
irin xaman da take yi ba nata abokan xaman,
amma tayi xamanta...
Haka ki rike sirrin mijinki kuma ki kyautata
zamantakewar zamanki da mijinki.munanan
lafia kalau muke kuma muna cikin kwanciyar
hankali dajin dadi alhmdllh kiyita godewa
Allah ga mansura can yar uwarki mijin
dukanta yake watanni nawa da aure amnan hr
ya saketa saki 3 wanda Allah ya
haramta..yarima ne tsaye bakin kofa ya
kuramin ido cikib tuhuma na da dauke
fuska..Allah ya kyauta inna zan kiyayae insha
Allah inyi yadda kikace..yawwa toh Allah yayi
miki Albarka ki dage da addu'a kada yi sanya
da ibadarki,nace toh a gaushe da mutanan
gidan nace zasuji a gaida su sumayya..ke kika
buga mata ko ita ta bugo miki ya tambayeni
lokacin da na ajiye wayar idonsa kyam a kaina
wallahi na tsani kallo, na fada a zuciya
amma a fili sai nace ita ce ta kira ni, wai me?
kokwanto na me ni da uwata? ni ma ai uwata
ce ko? na zaro ido ashe ba a zuciya nayi
maganar ba,na lura ta yi masa zafi sai na hau
kame- kame yayi saurin tarata cikin kunar rai
"don me zaki fada mata rikicin da ake ciki,ko
duk salon rashin kwanciyar hankalinta ne kike
bukata?
rainin hankali duk duniya akwai wanda ya
kaini tattalin kwanciyar hankalin inna. "mst"
ya buga tsaki wallahi humaira kina da matsala
yasa kai ya fice rai a bace mamaki ya kamani
ni na bishi da ido. kamar abin jira wayata ta
kara kuka nayi saurin ridota na ga sunan
amira a hanzarce na daga domin ina da
bukatar nemanta ni kaina. hello kira ni don
allah kiran gwandala daya ce ba kudi
tuni ta mutu alamar kwandala dayar data
ambata an cinye ta babu bata lokaci na kira
ta. kaji manya ta yarima bada kanki a sare.
nayi murmushi nace ke ni bana son iya shege
da man wallahi ni ma ina da niyar kiranki a
yau dinnan. dan allah? nima tun dazu nake
neman ki bata shiga ba daman na fada maki
an sanya rana nan da wata shida bikin yayi.
a'a toh allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna
mana lokacin lafiya. safwan kuma ya sami
addmission saudi arabia zai cigaba da karatu
yace shi da nigeria har a bada . nace allah
sarki, amira baki tambayata ya zamana ba ?
nayi mata tambayar dan na kau da wanchan
zancen. hmm ai ko ranar juma'ar nan da abin
ya tuko ni har zan kira ki sai na ga cewa ke fa
har yau baki ce min komai ba toh ni
kuma binciken me zanyi? nayi murmushi,
hmmm ke dai bari na kwashe duk labarin kaf
na fada mata sanna na cigaba da cewa "wai
amma duk wanna fitinar ni yarima yake gani
da laifi shin amira ina ni in fada da gimbiya
lillahi warasuluhu? "tabdi" ta fada da karfi.
nace maccen da kemin wannan illar har
yaushe zan biye mata ranar da ta kunso wuka
ta luma min fa? lallai kam ta kara fada "yanzu
haka fushi yake yi da ni,wai na ki sakin jikina
da shi yana ganina da wani gaggarumin
laifi."ikon allah ta fada tana kara jinjina
maganar. "ba ma kisan ina cikin matsala ba
sai na fada maki cewa ,yanzu ya gama min
fadan don me zan sanar wa inna,kuma wallahi
amira ni ban ma fada mata gimbiya ta ji min
rauni ba shine yayi fushi ya fita, kiji faa? "ke
kam bone ta ciki humaira. wallahi
kuwa na fada a marairaice. to iya gimbiya ta
san inda ka maida ke ni yanzu? ni ban sani ba
amma kema kin tabbata komai daren dadewa
sai ta gano ni matukar ba baruwa nayi da
yarima ba. ta ja dogon tsaki tace " ke wallahi
bnaza ce saboda wata banza sai ki rabu da
mijinki maimkaunar ki haka humaira? wannan
furuncin naki fa zai sanya matsala ta afku
tsakaninki da yarima. wai inna ta baki labarin
yadda ya mayar da gidan ku? gabana ya fadi
nace " kamar ya fa? tace "wai baki sani ba?
ko daya ni dai na rabe da kullum mukan yi
waya da inna sai ta ce kada na gaji da yiwa
yarima godia" "lallai to wallahi kin san gidan
honorable? na hanga nace kwarai, saboda duk
shiyyar unguwarmu babu gidan daya kama
kafar gidan honorable nura nasimat." to ko
kofar gidan ku be kai ba a yanzu wurin kyau
da tsari ke yan aikin inna biyu fa da me mata
abinci da me mata shara da goge goge. "
tsakanin ki da allah amira"? " na rantse da
allah ta fada tana yar dariya. shiyasa nace
maki wlh ki daina wannan furucin , yarima
baya taba iya rabuwa da ke. da yayi maki
fada yanzu har yai fushi ai da sai kiyi tunanin
cewa inna fa mahaifiyarki ce amma ya nuna
damuma fiye da taki, ke bama abin
alfaharinki ne ma kina in a wanna zamanin
akeyin fito na fito da surakai? to wallahi ki
gaggauta zuwa ki bada hakuri sannan kada
matsalar gimbiya ta sanya kiyi watsi da
masoyinki, baraka ta shiga a sami rauni
wannann shine babban burinta. nayi kasa da
murya " amira nagode allah ya bar zumunci".
Amin amin, na gode sai munyi magna. na
dafe kaina tsananin tausayin yarinma ya
mamaye zuciyata kmr kaina zai bare. a
hankali na mike ,rabi na goge wasu zannuwan
gado nace "ina yarima ne ko ya fita?" "A'a
yana dakin chan" ta nuna min da hannu na bi
sirdaden da ta nuna na sa hannu na murda
gaa mamakina naji ta bude. na shiga sai na
ga tankamemen falo ne daa yaji kayan gayu
irin na zamani. na hango kofa daga yamma
alama nan dakin yake na hanzarta isa tare da
budewa. jin an bude kofar yasa shi dagowa
da sauri na lura da idanunsa sun yi ja matuka,
shi dai kam bacin rai na haddasa masa jan
idanun, na fada a zuci saboda yadda na san
idanunsa farare tar har wasu ruwa kake gani
kwance saboda haske. ganin nice sai kawai ya
maida kansa ya
kifa kamar yadda yake kwance ruf da
ciki.tausayinsa ya kamani ,naji kamar na dago
shi na rumgume a yadda naji sonsa ya karu a
raina. sai dai miskilancina bazai barni aikata
hakan ba, na zauna bakin gadon gab da
kafafuwansa ko motsawa bai yi ba. na rasa
inda zan fara, toh me zan ce masa? daraba ta
fado min. "amma yarima wannan kwanciyar
ce fa aka haramta saboda ta yan wuta ce
babu kyau yin ta" a hankali ya juya amma sai
ya bani baya ya kalli can. raina ya bani fushi
yake yi." allah ya baka hakuri" na fada a
hankali. bai dai ce komai ba bai kuma motsa
ba, nan da nan kunya ta baibaye ni naji duk
na tsani kaina. na tuna irin dizgi da wulakanci
sa da gimbiya ta sha, ba shi da wuyar dizgi ai
sai na raina kaina. Na yunkura zan tashi gwiwa
sake ina
nadamar kawo kaina, sai kawai naji an ruko ni
ta baya."ina zaki je kuma? haka ake lallashin
maigida idan yayi fushi?" na sunkuyar da
kaina, ya buga tsaki "ni di wanna kunyar
wallahi tana kwarata....zo na koya maki yadda
ake bawa maigida hakuri" ya shiga yimin
cakullulo tun ina zillewa har na hau kyalkyata
dariya sai kawai ya kura min ido, nayi saurin
rufe idona shi kuma ya kai bakinsa ga nawa
nan da nan yaren ya sauya.******** Cikin
kwana uku ya bude min ido ya koya min son
sa da tarairayarsa muka bude sabon shafin
soyayya.na yi nadamar rashin sakin jikina da
nayi tun farko na gane cewa lallai ba karamin
so yarima ke min ba, ban da shagwaba babu
abinda yake zuba min , duk yadda na wasance
dole wani abun idan yayi min shi sai naji kunya,
shi kuwa banda
zagi babu abinda yake yiwa kunya, wai kunya
na kwarar sa (mata a rike kunya domin ita ce
adon mace, wallahi duk yadda kuka dade da
miji ki rika nuna kina jin kunyar sa wasu
lokutan musamman lokacin da kuke kebe
kudai yana karawa mace martaba da kima a
idonsa). Kullum cikin zabga karya yakeyi a
asibiti cewar yayi tafiya ne maimartaba ya
aike shi. Washe gari ya kama zai koma gidan
gimbiya kamr kar ya tafi nice me kwarin
gwiwar bashi magana, da kyar ta tafi wajan
karfe biyar na yamma. kullum yana zuwa da
safe mu gaisa da marece kuma ya dawo yi
min sai da safe, ina lura dashi sam
walwalarsa ta sauya amma sai kawai na share
na san shi da mutuniyar ne ni dai allah ya min
alamnashara. Rnar da zai dawo ina ta

Please Login or Register in order to submit comment