Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya kirkire2 ba ma anan kasar
ba har da kasar yaje
yayi bama anan kasar kadi
aka ji da shi ba har
kasar da yake yayi
karatun sa (Germany) sunyi
alfahari da shi a matsayin
dalibinsu da yake
shiga cikin masu jajayen
kunnuwa yana
kirkire2, su dama nasara irin mutanen da suke
so kenan masu baiwa shi
yasa tym din suka
fifita shi, suke ji da shi, da
ya gama karatu suka
nemi rike shi a wani kamfaninsu na kere2
jirage, da gida da albashi
mai tsoka za su ba
shi amma yace ba zai iya
zama can ba gara ya
dawo kasarsa cikin addininsa da ala'adarsa da
en uwansa. Hajiya tace,
Aneesa naji kinyi shiru,
bana son in tauye miki
hakkinki meye ra'ayinki.
Ta sadda kai kasa saboda yanzun har ta fara
kunyar Hajiya tace, na
amince Hajiya, wlh ko
yaya Ishaq ba na gari bane
zan iya miki
biyayya in aure shi balle halayyarsa da
dabi'unsa zuwa
mu'amularsa babu abin
kushewa, amma hajiya
shima ya amince? Naga
fa yana son Aunty safeena sosai. Hajiya tayi
murmushi, ya amince
sannan don yana sonta
shine ba zai kara aure ba?
Ai duk wadda kika
ga mijinta ya kara aure ba wai baya sonta ne,
wani ra'ayinsa ne wani
kuma koyi da Manzon
Rahma (saw) ne, kalilan ne
karawa don
matansu ba su kyautata musu, duk irin son da
yake mata zai iya yi miki
fiye da nata, in dai
kina kyautata masa don

babu abin da Namiji
ke son irin kyautatawa, kamar yin masa ladabi
da biyayya da gudun bacin
ransa don son
abinda yake so in dai bai
sabawa shari'a ba,
da son en uwansa, idan kika rike wadannan to
zaki kama namiji a
hannunki. 94) A wannan rana
magabatn Ishaq suka je
gidansu Aneesam dama
Hajiya ta fara sanar da
Abbansu Aneesa. Su ka ba
da kudin gaisuwa aka yanka musu sadaki
dubu talatin amma
baban sasa yace ko ranar
daura aure ne suna
iya kawowa. A cikin
gidansu Aneesa tsegumi ne ya dinga tashi daga
bangaren Hanne ta
dinga yada habaici a tsakar
gida. Oh! Allah mai
iko wannan auren huce
haushi kenan ko auren me? Allah ya raka taki
gona bamu kwashi
ragowa ba, ita ta
kwasarwa danta, an cuce
shi.
Sai diyarta Haula tace, mama kika sani ko
shima ragowarsa ce tunda
dai dubi irin hidimar
da yake mata ba dangin iya
ba na baba, ga
gidanshi da take zuwa wai hutu, kika san me
suke yi a can Allah sarki
matarsa duk anje an
gane mata sirri ga shi za'a
daure mata miji.
Uwar tace, au dama me ne gaya muku
kwanaki, daman ace daga
hutu sai kunji wani
abu ya bullo kinga kuwa
ashe zancen aure ne
zai biyo baya. Haka suka yi ta wannan
tsegumin da sharrin don
halima ta tanka musu,
bata tanka ba, sai dai ta
bari 'ya'yan Hanne
sun fita sai ta same ta a kicin tace, wlh maman
haula ki bar kushe da
hassada saboda taki ne
ga mai rabo, kin kushe

Aneesa kinyi mata
sharri sai ga shi Allah ya bata miji wanda ya fi
kaninki shine kuma ke da
'ya'yanki kuke
hassada, har uwar
yarinyar nan ta bar duniya
ba taba tanka wa sharrin da kike mata ba, ita
da diyarta, hakan bai sa ki
nadama ba yanzu
ma bayan ranta bi ta da
kulli yana cigaba, to
yanzun kina hadawa da dan manya dan masu
galihu ina tsoron ranar da
wannan sharrin naki
zaije kunnen uwar yaron
nan in kina ganin
Aneesa bata da gata shi dan gata ne, kuma shi
wani ne, zasu iya daukar
mataki akan irin
wadannan sharri naki, ki
tsaya kan Aneesa ko
ki gyara bakinki kiyi masa linzami don Aneesa
yanzun matar manya ce,
idan kika ci gaba da
mata bita da kulli mijinta zai
dauki mataki
akanki ke da 'ya'yanki, idan kunne yaji to
gangan jiki ya tsira, Hanne
ta tafa hannu tace,
to kinibabbiya, kina iya
zuwa ki gayawa Hajiya
nayi wa danta sharri sai a daureni har igiya tayi
rara ke kuma sai ki zuba
ruwa kasa ki sha,
munafuka ai fa ke yanzun
nan zaki tare 'yarku
zatayi aure gidan masu kudi, lallai kam! Muna
nan muna sa ido zamu ga
yin auren, auren cin
amana. Ita dai Halima tunda
ta riga ta gama
gaya masa gaskiyya daki ta shige ta barta tana
babatu wanda ta san idan
ta ci gaba da kulata
yau haka za su wani sun
musanyar yawu.
Aneesa kam! Kasa sukuni tayi tunda wannan
lamari ya zamo haka, gidan
Hajiya ma da take
wuni a can kullum yanzun
sai ta soma ragewa,
saboda nauyin Hajiyan take ji yanzu, har sai da

Hajiyan ta sa aka kirata
tayi mata fada sosai
akan wannan matakinda ta
daukarwa kanta,
sannan ne fa ta saki jikinta, wanda Inshaq yace
zauyi wa waya kawo mata
waya ya zo ya kawo
mata ta zabi Nokia mai
tsada har da kayi da
kudi ya sa mata, sau daya Ishaq ya kirata
shima gaisawa sukayi. ***************
***************
************95)
Ishaq tunda ya bar zariya a
mita yake ta sake
saken wannan al'amarin yadda ya kasance. Da
ya koma gida kasa sukuni
yayi sai da ya zauna
yayi shiru yana tunanin
hanyar da zai sanar da
Safeena zancen wanna auren bai san yaya zai
yi mata bayani ta fahimta
ba, saboda ita
baudaddiya ce, duk yadda
ka so ka fahimtar da
ita abu bata yarda tafi aminta da abinda
zuciyarta ta kitsa mata,
balle yanzu. Da ta
zama ma'akaciya dabi'unta
gaba daya ta
canza su, sau da yawa su kan sami sabanin
ra'ayi a zamantakewarsu
shi ya rasa dalili, to
balle yanzu idan yake mata
da wannan mafi
munin zancen a gurinta. Da dare yayi lokacin
kwanciyarsu yayi taje ta
aki yaranta dakinsu ta
janyo musu kofa ta nufi
dakinsa, a bakin gadon
ta same shi zaune ya tallabi kuncinsa da
hannu 2, ta zo ta dan taba
shi sannan ya
dubeta yace, kin kwantar
da su Yasmin ne?
Tace, eh duk sunyi barci, na jika shiru ne a daki
lfy dai kake kwana biyun
nan ko? Yace lfy lau
me kika gani? Lfy ta kalau,
ta girgiza kai tace,
ba lfy kake ba tunda ba haka na saba ganinka
ba, inkuwa lfy jikinka yake

to ba lfy zuciyarka
take ba, akwai wata
mummunar damuwa a
tare da kai..... 96) Ya fuskance ta sosai,
yace zauna muyi
maganar tabbas, zuciyata
akwai abinda ke
damunta, na rasa ta yadda
zan gaya miki ne ki fahimta shi yasa abinke
damuna a zuciya yana
mini ciwo, kin yarda in
gaya miki ba za ki bani
matsala ba? Tunda taji
haka sai jikinta yayi sanyi ta san cewa akwai
wani abu da zai faru
da ita na bakin ciki, kuma
kila daga zaria abin
ya samo tushe, sai dai ba ta
fatan abinda zuciyarta ke ayyana mata
ya kasance
gaskiyya. Ta zauna suka
fuskanci juna sosai
sannan tace, bana fatan
abin da zaka gaya mini ya kawo matsala a
tsakaninmu sai dai in
dama lamarin mai matsala
ne to kaga ba daga
gareni bane. Ya janyo
hannuwanta ya makale su cikin nata ya soma
murza su a hankali ta
sauke ajiyar zuciya, ta
tsura masa idanu tana
sauraronsa. Yace, safeena
kiyi hkr nasan abin da zan gaya miki zaiyi miki
ciwo, aure aka bani
a zaria, kuma babu yadda
zanyi in kaucewa
auren dole na amsa.
Hannuwanta ta fizge cikin nasa tamkar wadda ta rike
rushin wuta, ta mike
tana huci ta nuna shi da
dan yatsanta sannan
tace, daman na san za'a
rina, wannan sintiri da kakeyi a zaria ai yayi yawa,
tuni zuciyata ta
soma ayyana mini wannan
mugun lamarin ina
yakice shi, ashe zai tabbata
akaina ne da gaske. Yanzu kai kamar ka
da Iliminka da
kudinka da wayewarka,
za'a baka aure baka so

ka amsa, sai dai in dama can
kana so ne amma ba zan yarda baka
akayi ba, gara ka fito
barao2 kace min ka nemo
aure a zaria har an
baka zan fi yarda. Yace, ni
wlh ba ni na nema ba, bani akayi, kuma duk
kudina da ilimi na da
wayewata ban isa in ki bin
umarnin na gaba da
ni ba, har duniya ta nade su
ne sama dani dole inyi musu biyayya, nafi son
farin cikin su da
nawa, nafi gudun bacin
ransu akan nawa, shi
yasa da suka bani auren na
amsa tare da godiya don nasan ba dan
su cutar da ni ne
suka bani auren nan ba,
alheri ne suka kulla. 97) Dama ai ba za su cutar
da kai ba tunda
abin alheri suka kulla
maka, nice dai suka cuta
zasu kulla min abinda ba
alheri ba. Kaiko a family dinku waye ya baka
wannan auren ka
amsa? Yace ba wata bace
sai wadda ta isa
dani, wato hajiyata. Auren
kuma da Aneesa ne za'ayi. Ta ware idanu tace,
Hajiya ta baka
auren Aneesa!!! Yanzu kai
a wayewarka me
zaka yi da wannan
yarinyar? Yace shi yasa nima nake ganin idan kika
kwantar da
hankalinki zaki juya
yarinyar nan duk yadda
kika so, tunda ita ba mai
hayaniya bace, ba zaki sami matsalat zama da
ita ba. Ta dakatar
da shi tace, Ya isa! Ya isa!!
Tun yanzu har ka
zo gaba na kana yabonta,
tun bata zo gidan nan ba, to bari kaji in gaya
maka aure ko kaje
kayi Allah ya bada sa'a,
amma tsakanin ni da
kai babu sauran zaman lfy,
balle ita kanta idan ta zo gidan zata gwammace
gara agidan yari
da gidan nan ban,don ba za

taji dadi da
ma'aurata keji a gidan aure
ba, ai duk macen da tace zata auri mijin wata
to (MIJIN ARO) zai
zame mata, saboda haka
ina nan ina jiran
zuwanta. Ta dauki saman
rigar baccinta da ta cire ta aje bisa gadonsa ta
fice daga dakin,
yana kiranta ko
sauraronsa bata yi ba ta
nufi
dakinta, ta murza key ta rufe kofarta, don ma
kada ya shigo ya dameta.
Kwana tayi kuka da
sake2 abinyi, amma har
gari ya waye bata
samo wa kanta mafita ba, na yadda zata
wargaza auren. Da sassafe
ko sauraronsa bata
yi ba, ta tuta masa sako ta
wayarsa, cewa zata
fita anguwa, bata jira mai zaice ba ta fice, su
Yusra gida ta barsu gurin
mai kula da su.
Gidan aminiyarta ta nufa,
guri daya suke aiki,
ta girmeta da shekaru akalla biyar. Haj. Nuratu
manyan mata kenan masu
juya naira saboda
ba aikin kadai takeyi ba,
tana safara zuwa
Dubai, sannan shi ma mijinta juya shi takeyi
tamkar karamin yaro duk
da yake babban
mutum ne amma macece ke
jan ragamarsa.
Tana ganin safeena ido kode ya jeme da kuka,
ta riko ta suka shiga dakin
barcinta, tana
tsokanarta. Ho! 'Yar lelel
Captain me kuma ya
faru ne? Na dai san ba Captain bane tunda shi
baya laifi kullum cikin
faranta miki yakeyi, kece
ma in 'yan tsiyarki ya tashi
kike gara shi,
bawan Allah inji ki, ni kam namiji ban dauke shi
abin tausayi ba, sai da
kawai ya bauta mini ni
kuma in juya shi yadda
raina ke so. 98) Safeena ta zauna tana

sauke ajiyar zuciya
tace, yau Captain ya tabo ni
na daina yabonsa
har abada in dai baya janye
Alkaba'in da ya dauko mini ba. Haj. Nuratu
ta kyalkyale da
dariya tace, hala aure zaiyi,
don nasan
tatsuniyar maza bata wuce
aure in dai sunji su lafiyyayu, ba sa son bin
matar waje to yanzu za
suce aure don ba su cika
son cin tuwo daya
kullum ba. Murmushin
takaici Safeena tayi tace, wlh kamar kin sani
aure zaiyi wai
Hajiyarsa ce ta ba shi
yarinyar a can zaria,
kinma san yarinyar wadda
zaki ga hajiyan nan- nan da ita tamkar wata
autarta, wata fara
sirirya, shegiya sai nono da
duwawu
( Hahahaha kunji fah, ita
ina nata) kilama shi Captain din ya gani suka
tsole masa idanu,
dan na san halin kayana.
Haj. Nuratu ta saka
dariya tace, ai tuni nake
gaya miki namiji ba abin yarda bane, tun kafin
ya saki kuka gara
kiyi maganinsa ta yadda
kina ganin sai yadda
kikayi da shi, to ai ga irinta
nan ya dauko auren er garinsu, en zariya masu
shegen asiri, su
kansu iyayen ba haka suke
barin 'ya'yansu ba,
yanzu ai kinga zama bai
gammu ba, sai ki tashi mu san abinyi.
Safeena ta tashi daga
kishingidan da tayi tace, to
hajiyarmu yanzun
meye abinyi? Tace tashi
zaki yi mu kama hanya dole mu hana auren, wani
kauye zamuje nan
kusa da birnin gwari, zaki
ga aiki da cikwa. Sun
hau motar Haj. Nuratu ne
sukai ta sharara gudu awa daya da rabi
sannan suka isa
kauyen. Haj. Nuratu ta

zayyanewa bokan
abinda ke tafe su, yayi
dariya yace, ku sha kuruminku daga auren har
zarian ba zai kara
yin maganarsu ba, ku tashi
ku tafi. Suka aje
masa kudi masu yawa suka
baro kurgurmin dajin
99) Tun daga ranar Ishaq
bai sakeyi wa
safeena maganar aurensu
ba, ta sa idanu taga
ko zaije zaria nan ma shiru, tun daga tym din
ta soma murna a ranta,
asirinta ya kamshi,
tunda har ta raba shi da
auren da ya rakito ta
nisanta shi da mahaifarsa. Hajiya kuma taji
shiru ba zuwa ba waya,
abin ya bata mamaki,
abinda Ishaq bai taba yi ba
don ba ya sati biyu
bai zo ba mahaifarsa ba, in kuwa bai zo ba to
baya kasar ne, to zai ta
yiwa Hajiya waya yana
bata hkr tare da jin lfiyarta,
sai ga shi yanzu
har yayi wata guda cur! Rabosa da zaria kuma
ko yi mata waya, sai ita ne
wani tym ta kan kira
shi, amma ba ko yaushe
take samunsa ba sai
tayi sa'a, sau biyu idan ta kita safeena na
dauka tace wai baya garin
wayarce ke gida.
Tun daga tym din Hajiya ta
sha jinin jikinta, ta
tashi tsaye da rokon Allah akansa sam, bata
bacci dama ita, kauwama ce
( mai yawan
tsayuwar dare) Kuma
sauwama ce ( mai yawan
azumin nafila ce). Har malamai nagartattu
masu sani tasa suka dinga
taya da rokon
Allah. Gabatowar bikinsu
da aksa ya zo ne tare
da samun nasarar rokon Allah din da akayi
masa, don kwatsam! Ranar
juma'a Ishaq yace
wa safeena zai taho zaria,
abin ya bata

mamaki ba ta gama dawowa daga duniyar
mamakin da ta lula ba,
kawai sai taji tashin
motarsa ya bar gidan, ita
ma mota ta sura ta
nufi gidan Haj. Nuratu suka fantsama kuayen
Birnin gwari, bokan nan ya
tabbatar musu,
tabbas za'ayi aure nan don
kuwa yaga rabon
haihuwa a tsakaninsu. Safeena ta dafe kirji
tace, rabon haihuwa? Na
shiga 3 gashi ai a
haihuwar su Yusra nasa an
juya mini mahaifata
ba tare da ya sani ba, ba zan sake haihuwa ba,
don Allah boka kasan
yadda zakayi ka hana
auren nan don ba zaiyi wu
ina ji ina gani wata
ta zo ta dinga haihuwa ba alhalin ni na daina,
ga shi 'yan mazan da nake
da takama da su
Allah ya amshi daya saura
daya, shima bani da
tabbacin rayuwarsa... 100) Yayi en surkullensa
ya gama sannan ya
dubeta yace, zan iya hana
auren amma ba zan
iya hana samuwar rabonda
ke tsakaninsu ba, ki yarda yayi zina da ita su
haifi rabon da ke
tsakaninsu ba tare da
auren ba? Tayi saurin
gyada kai tace, wlh na
yarda in dai ba za suyi aure ba ko meye suje suyi
ko 'ya'ya gima za'a
haifa masa a waje na yarda
in dai ba zai auro
mace ya kawo mini gida ta
zama kishiyata.*****
*********** Wa 'iya
zubillah!
Kuskuren da mata keyi
kenan da akawo musu
kishiyar cikin gida ta saunna gara a aje kishiyar
titi, ayi ta masha'a in da
rabo ma har a haifar
masa 'ya'ay'ye a titi babu
ruwanta tunda ba
'ya'yan cikin gida na sunna bane! Anya munyi
wa mijinmu da yaran da zai

haifa a waje da ita
matar da yake so ya auro
kika hana adalci?
Shin meye makomar ki idan kika yi irin wannan
sanadin ranar gobe
kiyama? ***************
********** Boka yace, an
gama yau zan zuba
ma yarinyar rabonsa a mahaifarta, tun da naga
rabon da ke tsakaninsu
mai gaggawa ne, in
yaso hakan sai ya zamo
sanadin fasawar
auren, don idan ta sami cikin akwai abinda
zamuyi masa yayi musun,
cikin ba nasa bane,
idan tace shi yayi mata
kinga zumuncin da ke
tsakaninsu ma duk zai rushe, sai suyi uwar
watsi kowa tasa ta fisheshi.
Safeena da Haj.
Nuratu suka tafa duniya
tayi musu dadi. Naura
dubu dari suka direwa boka saboda suna son
aikin cikin gaggawa kafin
ya dawo Abuja mai
aukuwa ta auku, tunda
yace gamuwa daya
zasuyi ya yada mata rabonsa, to gara ayi
gamuwar da gaggwa ko
hanaklinsu ya huta.
Kwatsam! Hajiya taji ladidi
na murna tare da
hamdala. Bata zaci Ishaq bane, ta dauka wani
abin ne ya faru take
murna, tana fitowa sai
taga Ishaq, murmushi tayi
masa tace, maraba
da dan gidan Hajiya. Ya isa gabanta ya kama
hannunwanta yace, Hajiya
bakiyi fushi da ni ba
ko? Na rasa yadda akayi
har sati 4 banzo gida
ba, yau kawai naji ke da en uwana nake son
gani, kiyi min afuwa, ki
gafarta mini hajiyata. 101) Ta bugi kafadarsa
tace, babu komai muna
tare da Allah sai zai shige
mana gaba ni banyi
fushi da kai ba. Aneesa na
zaune tana jinsu karaf! Idanunsa ya sarke
da nata yayi mata

murmushi yace, a'a
kanwata kina kallona ashe
baki zo yi min oyoyo ba, ga
ladidi da Hajiyata sai murna sukeyi. Ta taso
tana murmushi tace,
sannu da zuwa kazo lfy? Ya
su suhail? Ya ji
dadi aransa yadda komia
zatayi sai tambayi yaransa, shi kam, ko don
haka ma zai iya
aurenta a matsayin tana
mai kauna yaransa.
Yace duk suna lfy, sunce na
gaida Auntyn zariya, sukayi dariya ita da
su Hajiya. Da
yamma bayan ya tashi
daga bacci da yayi tun
zuwansa, yayi wanka ya
sallaci la'asar ya sake wata kaftani ta shadda ya
murza hula ya fesa
turare ya iske Hajiya a
dakinta, tana ganinsa
tace, a'a sai ina kuma? Ina
fatan Anguwan juma zaka je don suna
kewarka? Yace zan
shiga gaida surukaina ne,
ina ita matar tawa
naga sai dari2 take da ni.
Hajiya tace, ta tafi gida amma yanzu zata
dawo daga can ka biya
gidan yayyinka, maman su
sadiq tasha ciwo.
Yace ba dai ciwonta ne ya
tashi ba? Tace shine wannan karon ta sha
wuya, yace idan nutsu
zan fita da ita kasar waje
dob akwai wani
shahararren likitan zuciya
da ita kasar da naga sanarwa aikinsa ta
internet, can zan kaita a
dubata. Hajiya tace Allah ya
taimaka ya baka
iko. Daga gidansu Aneesa
yaje Unguwar juma daga nan gidan yayyinsa
yabi dukkansu ukun
da sauran gidajen en
uwansa. Sannan ya dawo
gida. Washegari tunda
yaga Aneesa tana hada masa abin karya a kicin din
Hajiya yaji wani
abu na masa yawo a
kwanya game da ita,

zuciyarsa na kitsa masa
wani mummunan lamari wanda ba yanzu
bane hakan ya kamata
ya bijiro masa a zuciya ba,
amma yaji shedan
na ta rinjayarsa. Wata irin
matsananciyar sha'awar Aneesa yake ji
wanda bai taba jin
sha'awar diya mace ya
bijiro masa irin haka
ba. 102) Yayi kokarinsa ya
danne abin amma ya
gagare shi, saboda duk
gilmawar da tayi sai
yaji abu na masa yawo a
tsokar jikinsa, surorinta ne kawai ke
masa gizo, a daddafe
yayi sallar magriba ya
shigo yana ganinta abin
ya dawo masa sabo. Ya
dubeta yace, kinyi sallar magriba? Tace nayi,
yanzun na idar
gama abincinka can. Yace
bar abincin nan ina
Hajiya? Tace, tana daki ina
jin ta idar da sallah yanzu. Ya sami Hajiya a
daki a zauna gefenta
bisa carpet yace, zan fita
anguwa ne, amma
zaki bani aron 'yarki ta
rakani, ko nayi ba daidai ba? Tace, Gaskiyya
ba zai yiwu ka fita
da ita ba, tunda ba matarka
bace, mai zatayi
maka idan ta rakaka? Yace
Hajiya kin manta dazun nan su baba Ali suka
zo gidansu suka
kawo sadakinta iyayenta
sun amsa sunce sun
bani. Amma wannan ba
hujja bace da zai sa I fita da ita ba. Zata dai
rakani ne nan GRA gidan
abokina Captain yawale
zamu duba wasu
kayan sawa na mata ne da
matarsa ta kawo daga china, ko a gidan zan
iya hado lefen
tunda babu abinda bata
sayarwa har
akwatuna. Haka ya kashe
Hajiya da dadin baki ya dauko Aneesa a
motarsa suka nufo GRA.

Aneesa tunda ta shiga
motarsa sanyin Ac da
kamshin turarensa ya
kashe mata jiki tayi lakwas, shi kam sai
kallonta yake yadda tayi
masa kyau shi kansa ya
san idan ya aureta zai
more sosai saboda
yarinyar tana da abubuwan
da yake so ajikin mace. Tun
kafin su iso inda
zasuje, taji kirjinta na
bugawa, bata san dalili
ba, har suka is wani dandasheshen gida a cikin
GRA. Mai gadi ya zo ya
bude musu gate suka
shiga ciki, ita dai tunda ta
zauna a falon gidan
bata ji motsin masu gidan ba, illah kukan
tsuntsaye bataji tsoron
komai ba, don ta
tabbata Ishaq ba zai
halakar da ita ba. Can ya
fito da lemu mai sanyi ya mika mata, ta amsa
ta ajiye ya zo ya matsa
mata wai ta sha kafin
masu gidan su fito, can sai
ya fito yace ta
shigo ciki ta gaida Hajiyan sai ta duba
kayayyakin. Wani dakin
barrci taga sun shiga,
yace ta zauna bari ya fito,
ita dai dama jiri ta
soma ji shiya sa ta kosa ta zauna, tana zama
sai ta soma ganin taurari
taurari suna gilmawa
daga nan sai taga dindin,
jikinta duk ya mace
sama2 take ganin abinda ke faruwa, Ishaq ya
kwantar da ita flat a gadon
nan ya rabata da
rigar jikinta, tayi kokarin
ta hana shi amma ta
kasa, jikinta ba kwari, shi kanshi jinsa yake
tamkar ana azalzala shi ya
aikata abinda
zuciyarsa ke raya masa, bai
san kuma
takamaiman dalilinsa na aikata wannan cin
amanar ba.
KARSHEN BOOK 1

Ebook din nan yazo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf Namba daya a fadin Africa
.
Ga mai bukatar wasu hausa ebooks din sai yayi maza maza ya ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo
akan adireshi http://hausaebooks.cf
.
Wanda yake son a mayar mai da littafinsa ya koma ebook sai yayi sauri ya samemu a shafinmu na
facebook ta hanyar bin wannan adireshi http://fb.com/hausaebooks Sai yayi like da mu sannan ya
sanar da mu dukkan abun da yake bukata
.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment