Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hanne da suke ta kai kawo da sukar
wannan auren. Kamar yadda mahaifin Aneesa
suka sa tym da zarar ta kammala jarabawa, shi

yasa sagir yaje ya sami mahaifinsu don a sake
komawa a tsayar da takamaimai rana tun da
yanzu an riga an sa ranar da zata kammala
duka jarabawarta. Sagir ya sami mahaifinsa da
maganar, shi kuma sai ya kira iyayensu sagir
din don ayi shawara, ashe Hanne na gidan
dama tsegumi ya kawota, ita ma matsayinta na
babbar yayarsu, sai duka aka kira har da ita,
alhajinsu ya gaya musu dalilin kiran nasu suka
nuna zahirin murnarsu, aka fara shawarwarin
wace rana za'a fitar cikin watan biki, ana
wannan shawara Hanne bata ce uffan ba, tayi
shiru ne tana sakesaken ta hanyar da zata
bullo da shirinta yadda zaiyi tasiri a zuciyar
mahaifinsu ta gyara zama ta soma cewa, Alhaji
ni dai ina da magana dangane da wnnan auren
da ake son likawa kanina, yace ina jinki tace
gaskiyya Alhaji wannan yarinyar tuntuni na
gaya muku bata dace da sagir ba, ni dai a
matsayina na er uwarsa na bashi shawara yaki
dauka ni kuma ba zanso abinda zai cutar da
shi ba. Mahaifiyarsu Hanne tayi caraf tace,
kece dai kike ganin aibun yarinyar nan tunda
ba kya kaunarta, amma mu ai banda abakinki
babu wanda mukaji ya taba aibunta ta, in
kuma da tana da wani mugun hali da anyo
tattaki an gaya mana, wlh ki kiyayi kanki 'ya'ya
mata ne kina da suMIJIN ARO 1**12
81) Hanne tace ni wlh gaskiyya ce nake fai in
banda shi dan uwa nane, babu ruwa na da
wanda zata aura ko cikin gidanmu waye bai
san halin Aneesa ba, kwanakin baya fa
zubarwar da yarinyar nan muna gani, a gidan
nan. Babu irin sakarcin da yarinyar nan batayi,
kwanaki fa sadiq yazo yake cemin har gidan
nan take biyo sagir ko da yaushe, shine ma
yace sai da ya fattataketa yace kada ya kara
ganinta a dakinsu, tunda sagir din aurenta zaiyi
ba shashanci ba ne a tsakaninsu, banda
dakinsu sagir ma babu inda bata zuwa kuma
ana zuwa ana gaya min. Haka kuruk kuma sai
in kyale dan uwana ya auri shashar mace, ga
shi tunda yana sonta bai zai taba ganin aibinta
ba, gaskiyya alhaji wannan abin dubawane.
Alhaji yayi alamar tunanin can sai yace,
wannan maganar ba wai nayi na'am da ita
bane. Amma zanyi bincike akai, kuma bai
kamata koda za fasa auren ayi da irin wannan
zance marar dadi ya fito daga garemu, ba
musamman ma ke Hanne akwai zumunci
tsakanin ku da su. Kada in kuma jin irin
wannan zance daga gareki. Kema kina da

'ya'ya mata kuma ba zaki so ko da sunyi
badaidai ba a zo ana yayatawa, balle idan
basuyi ba, kinga ranki ba zaiyi dadi ba, kuma ki
sani wlh duk abinda kayi wa dan wani za'ayiwa
naki, walau khairan ko sharran, Ina gargadinki
da kiyiwa bakinki linzami. Idan dan wani yayi
abu mara kyau to kayi masa addu'a shiriya
don baka san me gaba zata haifar ba, kai
dinnan baka isa ka shiryar da naka ba sai in
Allah ne ya shirye su, saboda haka duk mu taru
mu nemawa 'ya'yanmu da na sauran musulmi
shiriyar Allah. Allah ya shiryar damu dukkanmu,
ameen.
82) Shiru Hanne tai maganar mahaifinsu ta
ratsata, tabbas! Zancensa dutse, to amma ita
fa auren Aneesa da sagir din ne bata so, ita
kuma ta rasa hanayr da zata tarwatsa auren
shi yasa ta bullo ta wannan sigar, idan tayi
nasara hana auren sai ta nemin Allah gafara.
( Ji wani shirme Allah ai baya gafarta laifin dabkayi wa
bawansa sai in bawansa ne ya yafe, to
shima sai ya yafe maka). Duk wata hanya da
Hanne zata bi sai da ta bi, tayi kutun2 ta hana
auren sagir da aneesa! Balle tana ganin inda
sagir ke aiki yana samu sosai har ya mallaki
mitar kansa, shiyasa ta sha alwashin Aneesa
ba zata aure shi ta huta ba, ita gata nan da na
en matan turus! A cikin daki babu mijin aure, in
bayan sagir kaninta ne da tuni ta hada aurensa
da Haulat to babu hali, saboda sun haramta ga
junansu. Ta so ta hada shi da yar kanwar
hajiyarsu, mahaifinsu yace sam! Kada ma ta
soma, ba zai yiwu ba tunda ta kushe wancan
auren ba ta isa ta jona shi da wata ba, duk
wadda ya akawo yanzun ita zai aura, babu
kuma wanda ya isa ya hana shi auren duk
yarinyar da ya kawo ko wacce iri ce. Abban
aneesa yaji ciwo sosai da Alhajin su Sagir yayo
tattaki da kansa ya bashi hkr, dangane da
fasawar auren yaran nasu, magana ta fahimtar
juna yayi tsakanin su inda ya haisda masa ce
wa dan uwansa ne ya ba sahgir 'yar sa, ahaka
dai zancen auren ya sha ruwa wanda shi Sagir
har kuka yayi wa Aneesa akan shi dai ita yake
so, ba zai yarda ya auri wata ba, bai nuna
mata hanne ce sanadi ba. Bai san ta fara jin
komai a bakin 'ya'yan hanne ba, ita kam ta
rasa irin wannan kiyayya da hanne ke mata ita
da mahaifyarta, da uwarta take nunawa daga
baya sai abin ya koma kanta, duk wani sharri
da mugun alkaba- sai ta dora mata shi, ita ko
tunani batayi abinfa da kayi wa dan wani na

sharri watarana za'ayi wayi gari ya iya komawa
kan danka idan ba abin alheri kayi sai kaga ya
sameka kaima da zuri'arka. Shi yasa kullum
muyi nufin kulla hairan kada mu nufi kowa da
sharri gara ayi ma sharri da kayi ma wani.
83) Wannan lamari ya tashi hankalin Aneesa
da duk wani masoyinta musamman Hajiya. Ita
kanta Aneesan har ta rame don a daddafe ta
iya gama zana jarabawarta saboda zuciyarta
na cikin halin bakin ciki da damuwa, ga babban
zullumi da take fada da shi wani furuci da
mahaifinta ya kira yayi mata na cewa ta fitar da
wani mijin kafin su zana jarabawarsu na Neco
don da zaran ta kammala ba zai jira komai ba
zai daura aurenta ga duk wanda Allah ya nufa,
saboda ta bangarensa akwai mutanen da suke
zuwa neman aurenta dana ya dakatar da sune
saboda akwai wanda take so, ciki ma harda
abokansa, kuma idan tym yayi koda abokinsa
ne zao daura mata aure. Damuwa tayi wa
Aneesa yawa lokacin tana kwance a doguwar
kujera a falon hajiya, hajiya ta fito daga daki ta
zo ta zauna a gefen Aneesa itama tayi shiru,
tausayin Aneesa take sosai saboda irin
abubiwan da ke kunnowa rayuarta kai! Ta
dubeta tace, Aneesa bana son inga kinzo kin
takura kanki da tunani. Duk abinda kika ga ya
sami bawa daga Allah ne, dama da kaddararsa
ce hakan kuma bawa ba wuce kaddararsa,
yanzu kina ganin kafin ku gama jaravawa
akwai wadda zaki fitarwa da mahaifinki
amatsayin miji? Aneesa ta numfasa tace, babu
wani a yanzu don na riga na kori kowa, amma
ina rokon Allah kafin wa'adin nan ya cika ya
kawo min nagari zan gabatar masa idan ban
samu ba. Na amince duk wanda yabani zanyi
biyayya inshaAllahu, albarkacin biyayyan sai inga alheri.
Hajiya tace ki kwantar da
hankalinki, insha Allahu sai kin auri miji na gari fiye da
sagir. Zasu ga sakayyar Alkhairin da
Allah zai yi miki, sai sun sha mamaki indai ina
raye ba za su ga naka sunki ba, da izinin Allah.
Bayan tafiyar Aneesa wani tunani ne. Ya darsu
a zuciyar Hajiya wanda itace zata iya sanadin
faruwar haka, wanda daddaden buri ne aranta
saboda irin kaunar da ke tsakaninta da Fatima
wannan shine abu na karshe da zatayi don
ganin zuri'ar Fatima bata tozarta a doron kasa ba.
84) Wayarta ta sauka ta kira Ishaq, Yana ganin
sunan HAJIYATA a screen din wayarsa sai
yayi murmushi saboda abin da ya jibanci
Hajiya ko ita kanta jinsa yake har cikin ransa,

sabida sanin duk duniya baya da
kwatankwacin Hajiyarsa, don har tsiya yayin sa
ke masa idan yace Hajiyata, sai su harare shi
suce, dadin Abin dai ba kai kadai bane balle
kace Hajiyarka. Ya kanyi murmushi ne yace, ni
dai nasan tawa ce, in kuma karya nayi sai
atambaye ta gata nan, dariya kawai suke yi
don sun san da an tambayeta cewa take yi shi
kadai ne nata su ba nata bane. Yayi sallama
tana amsawa yace, Hajiyata ina kwana? Ya
jama'ar zariya, ya su Aneesa. Tayi murmushi,
tace duk lfy kowa yake. A ranta dadi take ji
idan ya tambayi Aneesa saboda irin kaunar da
yake wa yarinyar da wuya ne suyi waya bai
tambayeta ba, idan ma tana gidan sai yayi
magana da ita. Ita kam, addu'a takeyi Allah ya
dorar da wannan kauna har karshe rayuwarsu,
Allah sa nufin da ke zuciyarta ya kai ga nasara.
Tace, wannan hutun karshe makon zaka sami
zuwa zaria kuwa? Yace indai kina son gani
nane ai sai in aje komai in zo, ko gobe ne ko
yau ne zan aje in amsa kiranki. Tayi murmushi
ita kam, bata da haufi akan Ishaq. Saboda
ladabinsa a gareta, tace ba zan shiga
rayuwarka aikinka ba, ka bari kanar jum'a ko
asabar kana iya zuwa ne maganar bana
gaggawa bane. Dan halas din kuwa ranar
asabar ya iso zaria kafin sallar azhar . Aneesa
na gidan Hajiya, ita hajiyan ta sa tai masa
lafiyayyen dambun cous2 wanda yaji hanta da
koda da kayan lambu, kamshin duk karade gidan. Shi
kanshi daga isowarsa kicin din ya
shiga ya iske Aneesa da ladidi a kicin din. Ya
dubi Aneesa, yace wannan irin kamshi haka,
me kuke hadawa ne mai lagawadar kamshi
haka, tun daga bakin titi nake jiyo kamshi?
85) ladidi tayi dariya ta nuna Aneesa tace ka
ganta nan tunda aka ce zaka zo tace ita zata
yi maka girki, ni ban ma san sunan abinda ta
girka ba, gashi nan ya cika gida da kamshi. Ya
dubi Aneesa yana murmushi yace, ai ni yanzu
na yarda dai kanwata kin zama gwanar girki,
bansan yadda za'a yi ba, kuma ga aurenki ya
matso, idan kika tafi gidan miji, kilan can zan
dinga yin waya ana sam mini na angon. Rufe
fuska tayi saboda kunya. Shi kam dariya ya
dinga mata yace, bari in sassauta belt da neck tie dina
yanzu zan fara dibar girkin nan dama
da yunwa na shigo zaria, sukayi dariya.
Aneesa sai da ya fita a kicin din ta ba shi da kallo yau
shigar suit yayi nasu ruwan kasa,
sunyi masa kyau tamkar wani bature ga hadadden

kamshi da ya baza musu a kicin din
ya fice abinsa, kai Allah yayi haddaden gaye
anan wurin inji aneesa a zuciyarta. Sai da
Ishaq yaci yayi hani'an yaje sallah daga can ya
kuma gana da jama'arsa ya shigo gida, ya
nutsu sannan Hajiya ta nemi ganawa dashi a
dakin baccinta suka nutsu saboda zancen da
zasuyi yana neman sirri da nutsuwa. Ta dube
shi ya nutsu agefen gadonta akasa bisa wani
tum tum mai taushi tace, ba wani abu yasa
nace ka zo ba illa ina neman alfarma da nake
son kayi mini, kuma ina ganin babu wanda zai
yi mini wannan alfarma inji sanyi a raina inji
bana kokwanto sai kai, ina fatan zaka share
min hawayena. Baki ya bude yana mamaki,
Hajiyata yanzun don kina neman alfarmar wani
abu a gurina har sai kinyi kokwanto, ai ni kin
fice neman alfarma a gurina sai dai ki bani
umarni take in bi umarnin indai ba ya sabi Allah
bane, kada kiyi kokwanto a kaina, fadi ko
menene kike so in dai bai fi karfin arzikina ba
zaanyi miki. Ta gyara zama tace, ba wata alfarma nake
nema cikin arzikinka ba, saboda
ni babu abinda baka yi mini ba, kai dan halas
ne na gasken gaske, Allah yayi maka albarka
ya albarkaci zuri'arka ya biyaka da aljanna. Ta
danyi shiru tana jinjina lamarin, shi kuma yayi
shiru cike da ladabi, umarninta kawai yake jira
ya cika idan kuma bukata ce yayi gaggawa
biya mata ita, don kuwa ji yake ko da fansar
ransa ne ta umarta zai iya badawa.
86) Can tace, kasan nayi maka waya dangane
da maganar auren Aneesa ka riga kasan
komai. Yace kwarai kuma zancenta aurenta na
raina don kuwa har na fara shirye2 na jira
kawai nake inji ansa takamaimain tym sai in
sanar da ke tsarin da nayi, don bana son kowa
ya wahalar da kansa daga ke har abbanta da
sauran en uwa, nine zan dauki ragamar yin
komai, a yadda nake kaunar Mama da zuri'arta
wlh babu abinda bazanyi musu ba. Hajiya ta
numfasa saboda zancen da zata dauko ba
wannan bane, ya sha bambam da duk wani
shiri da yake yi a auren na Aneesa, tace ai
maganar shirye2 ma ka aje ta agafe saboda a
halin yanzun an fasa auran Aneesan, Ya juyo
anfasa? Me ya faru? Tace mu dai takamaimai
bamu san me ya faru ba daga can ba, amma
mahaifin yaron ya zo ya bada hkr yayi kalamai
na fahimta, cewa dan uwansa ne ya ba shi
diyarsa shi kuma babu yadda zaiyi, shiyasa ya
umarci sagir din ya amsa. Idanun Ishaq suka yi

ja, ransa ya baci yace, amma wannan
wulakanci ne, yarinyar nan bata kula kowa sai
dansa nima har ina gargadinta tunda shi take
so, kada ta kuskura ta kula wasu tarkacen
samari, ashe zai yaudareta ne, ni ban yarda an
bashi wata ba dama can mayaudari ne, Hajiya
tace kada ka ji zafin yaron nan, shi sam bashi
da laifi, tunda har nan ya zo yayi mini
gamsashen bayani, kuma na yarda da bayaninsa, kawai
mu dauka ba matarsa bace,
shi yasa hakan ta kasance, ni dai yanzun
burina, Allah ya bata miji na gari wanda ma ya
fishi. Yace Insha Allahu Aneesa zata sami miji
mafiyinsa, akwai wani abokina dan zariyan nan
da muka taba zuwa gidan nan da shi ya ganta,
yayi ta damuna da zancenta sai na gaya masa
ta tsaida miji, tunda hakan ta kasance zance
masa ya zo su daidaita.
87) Hajiya tace, kabar maganar wani abokinka,
dama ni tun asali bana son Aneesa tayi aure
inda dangin miji zasu dinga tsagwamarta, to
gaskiyya dama en uwansa ba wani son auren
suke ba, musamman Hanne da kannen ta,
iyayensu ne ke so, shi ya sa da haka ta kasance ai banji
ciwo sosai ba, shine yanzun
nake son kayi mini alfarma a matsayina na
mahaifiyaka wadda nasan na isa da kai, ka
auri Aneesa don kai ne nake ganin zaka rike
mani ita da zuciya daya. Ishaq ya dubi Hajiya
duba na ya zanyi da wannan lamarin, yace ni in
auri Aneesa Hajiy? Kina ganin ba zata shiga
cikin matsala ba tsakaninta da Safeena,
saboda safeena wayayya ce ta fita wayewa da
wayau, sanna abin dubawa kuma safeena sam
bata kaunar kishiya, ni kaina ina tunanin irin
matsalar da zan fuskanta da ita duk ranar da
nace zan kara aure, tunanai na ko da zan kara
aure zan auro dai2 da ita ne wayayya ba
wadda zata sha wahalarta ba, amma aneesa
ba zata iya kishi da safeena ba. Hajiya ta
girgiza kai tace, amma ka bani kunya tunda
har kake tunanin ba zaka iya sarrafa matarka
ba da gidanka, ina ce safeena karkashin ka take? Kaine
zaka juyata ba ita bace zata juya
ka ba, to ni mahaifiyarka nayi maka Umarnin
auren Aneesa, wanda ina fatan alheri na kulla,
don kuwa ina hangi wannan alherin tare da
zamanku, idan kuma ba zaka iya ba saboda kada ran
matarka ya baci tunda bata son
kishiya sai in nema mata wani nagartaccen
mijin cikin en uwana, wanda nasan ba za su watsa mini
kasa a ido ba, za su share min

hawayena. Ishaq yayi shiru yana jinjina irin
wannan kauna da Hajiya ke wa Aneesa wanda
har bata kaunar yarinayar ta shallake zuri'arta.
Hakika yarinyar natsatsiya ce mai hkr da hankali ga shi
son addinin ya ratsata kwarai
mutum zai so ta zamo uwar 'ya'yansa don
samun tarbiyya ta gari a gidansa. Shi kam!
Yana kaunar yarinyar irin kaunar da zaiyiwa
duk wanda jininsa ya gauraya da nasa, jin
yarinyar yake tamkar Hajiyarsa ta haifeta, a matsayin
autar Hajiya yake ganinta, sai dai bai
taba jin ko so ko tunanin wai shi Ishaq zai auri
Aneesa ba, illa dai wannan kaunar.
88) Ya dago idanunsa cike da danuwa ya dubi
Hajiyarsa yace, Allah ya huci zuciyarki Hajiya,
ni idan ban share miki hawayenki ba, waye zai
share miki? Wlh ko da ba Aneesa da nake jinta
araina ba, zan iya aurar duk yarinyar da kika yi
mini umarnin in aura balle Aneesa da ta rayu
tare da mu, tarbiyarmu ke gareta, komanta irin
namu ne haihuwarta ne kawai bakiyi ba, amma
kinfi kowa sannin cikinta da bayanta. Ki
kwantar da hankalinki, na anshi auren er
lelenki, ina fatan zaki taya mu da addu'a Allah
ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, ya bamu
hkr zama da juna tunda kinsan babu wata
soyayya a tsakaninmu. Murmushi Hajiya tayi
irin murmushi nan mai bayyanar da farin ciki, ta
dubi Ishaq tace, ni kam ka gama min komai a
duniyar nan tunda ka amince zaka dasa daga
inda na tsaya, wajen tallafawa rayuwar
Aneesa, kwarai bana son rayuwarta tayi nisa
da cikin zuri'ata. A kullum addu'a ta kenan,
ashe Allah ya ga zuciyata da alherin da ke
cikinta shi ya sa ya canza lamarin auren nan
har gashi ya dawo cikin zuri'ata. Zanyi muku
addu ba zan gushe ba har karshen rayuwata,
tunda kun ginu akan kaunar juna to na tabbata
kauanarku zata rikide ta zamo soyayya da
izinin Allah, aneesa yarinya ce mai shekarun da
ba su haura sha takwas ba, kai kuwa ka haura
shekaru talatin, kai namiji ne mai ilimi mai
wayau fiye da nata, kaine zaka koya mata yadda
zata soka ba sai na gaya maka ba, kasan kuma a irin sigar
ladabi da biyayyar da zata
shiga gidanka da shi da kyakkyawar tarbiyar
da take da shi, da su zata samo soyayyarka a
gareka. Allah yayi muku albarka ya albarkaci
wannan auren da za'ayi yasa alheri muka
kulla. Dukkansu shiru sukayi na kusan mintuna
2, kowa da inda zuciyarsa ta nufa, ya dubi
Hajiya yace, kin sanar da Aneesa wannan

maganar? Tace ban sanar da ko ba daga ni sai
kai sai Allah dake tare da mu kawai ne muka
sani, yanzun nake son in kirata a gabanka in
gaya mata.
89) Yayi saurin duban Hajiya yace, ki barta sai
na tafi kinsan akwai nauyin juna a tsakaninmu.
Tace ai na so ne tun yanzun ku fara fahimtar
juna, amma tunda ka ce haka shikenan. Sai ka
saya mata waya ku dinga yin magana. Yace
zanyi ma Ali waya sai kawo mata su kyau ta
zabi wadda take so. Tace, yauwa kafin ka
wuce kaje ka sami babanka Alh. Sani da dan
uwansa kayi musu bayani, sai su kai gaisuwa
gidansu Aneesa. Ka turo da isassun kudin
gaishuwar in ma sun bukaci sadaki, sai a bada
tunda bai fi wata 2 ne zata kare karatun ba, da
ta gama ne yace zai aurar da ita, kaga
shikenan ayi a ahuta. Ishaq yace yanzun dai
suje su yi maganar neman auren, komai zai iya
biyo baya daga baya, ke naga duk kin matsu
ayi abin da gaggawa ne. Tace eh dole in damu
ayi saboda ubanta hutsumin mutum ne, yadda
idan bata kawo masa miji ba, zai daura mata
aure da wanda rabonsa ya rantse ai kaga ba
zanyi yayi mata auren wulakanci ba, yarinyar
da gatanta da komai a dauketa a aurar ga ko
wane irin miji, in dai ina raye ba zan bari duk
da ba iko na bace. A falo ya iske Aneesa zaune
tana cin abinci, ladidi na kicin tana goge2.
Aneesa na ganinsa tace Ya Ishaq ba dai har
zaka tafi ba? Yace zanje uguwan juma ne
yanzu zan dawo in wuce. Tace yaya ni yau
banji kace girkin da nayi maka yayi dadi ba,
kada ka sa Hajiya da Ladidi su yi mini dariya.
Yace yanzun nan dama zance girkin ki yayi
dadi, ya ma fi na kullum ga tukwicinki nan, Ina
ladidi ta amshi na na taya ki da tayi. Ya
kwalawa ladidi kira ta fito daga kicin din tana
amsawa, ya mika mata en dubu guda 2 tayi ta
godiya ta koma bakin aikinta. Aneesa kuma
dubu biyar ya bata, ta amsa tayi godiya ya fice.
Asalain Family house na su yaje a unguwan
Juma, gidan mahaifin Alhajinsa wanda a yanzu
kannen mahaifinsa ke zama da iyalensu.
90) A zauren gidan ya same su su duka biyun
bisa manyan tabarme dake shimfide a zauren.
Yayi sallama ya shiga Zauren Alh. Sani ya dube
shi yana murmushi yace, a'a kaga direban jirgi
ne da ranan nan, sannu da zuwa. Suka
gaiggaisa suma dattijan kawari ne irin
Alhajinsa shi ya sa ko da mahaifinsu ya rasu
sune suka maye masa gurbinsa. Saboda

dattakonsa da rikon zumuncinsu, ba irin
zumuncin yanzu ba da ba'a abu domin Allah
sai don ganin idon iyayenka idan suna raye,
idan basa raye sai ayi wa dan danwa rikon
sakainar kashi. Ishaq ya zayyane musu abinda
ya kawo shi, suka taya shi murna. Ya kawo
kudi dubu ashirin yace su kai na gaisuwar duk
yadda akayi zai kira yaji, ya kawo dubu biyar2
ya ba su. Alh. Sani yace Madallah an gode
Allah ya kara budi, munga kayan abinci direban
ya kawo Allah shi albarka. A mota Ishaw tunani
kawai yake yi, shi kam! Aransa bai jin son
Aneesa ko kyas! Illa kaunarta da tausayi da
suka gauraye da jininsa, shi dai umarnin duk
abinda ya shafi Hajiya tace masa yake bi don
ya faranta mata rai, tunda ya lura in har ya
kuskurewa wani umarnin nata akan auren nan
to zai daina ganin farin cikinta, shi kuma da ya
daina ganin farin cikinta gara shi ya sallamar
da nasa farin cikin tunda yasan yanzun rigima
ce zata bullo a gidansa muddin ya gayawa
Safeena zancen nan, don bai san ya zata dauki
lamarin ba, tabbas! Ya san zayi ban kwana da
zaman lfy a tsakanin, kaga kenan zaiyi
bankwana da farin ciki, yana komawa ya
gayawa Hajiya yadda sukayi, sannan yayi
sallama da su ya wuce Abuja. Aneesa har zata
tafi gida sai Hajiya ta kirata dakinta tace ta
zauna zatayi magana da ita ne. Sun danyi
shiru na en sakonni sanna Hajiya tace, Aneesa
yanzu kina ganin akwai wani da zaki fitar nan
da wata biyun da abbanki ya gindaya miki? Ta
girgiza kai tace, Hajiya wa nake kulawa? Duk
fah na gama korar samarin babu mai zuwa ko
wa shakkata yakeyi, yanzu bani da zabi idan
Allah kawo min wani to, idan bai kawo min ba
haka zan hkr da duk wanda Abban ya zaba mini.
91) Hajiya tace kada ki damu ni nayi miki zabi,
amma bansani ba, ko kice ba kya ra'ayin
wanda na zabar miki. Tace Haba hajiya wlh ko
kuturu ne kika zaba mini zan aura a yadda
matsayinki yake a gurina, balle nasan duk
wanda zaki zaba mini nagartacen ne wuya za'a
same shi da wata mummunar illar duk yadda
kika yi dani dayane. Hajiya ta numfasa tace,
nayi miki miji kuma ba wani bane sai yayanki.
Ta ware idanu tana al'ajabin sai tana jin
tamkar kunnenta baiji sosai ba, ta tambayi
Hajiya, Hajiya wane yayan nawa? Tace yayanki
na nan gidan ina fatan ba zaki watsa min kasa
a idanuna ba. Aneesa ta sauke nannauyar
ajiyar zuciya tace, Hajiya ban zan taba watsa

miki kasa ba, amma ai yaya Ishaq ba tsaran
aure na bane, ya fi karfin matsayi na, yayi min
fintinkau, sannan matarsa tafi karfina,
wayayyace ba irina ba ce, kuma da kunnena
naji tana fadin yadda ta tsani kishiya, wai ko
wani akace za'ayiwa haushi take ji, to balle ita,
wlh ina tsoron wannan furucin nata. Hajiya tayi
dan murmushi tace, kuruciya manya to Aneesa
ai babu matar da zakiji ta furta tana son kishiya
da bakinta, kuma ba wai kishiyar ita kanta ake
tsoro ba, a'a makircin da zata shigo da shi
gidan ake tsoro, wata bayannanen makirci
wata boyayye na karkashin kasa, za'a yiwa
wadda aka tarar har sai an fiddo ta gidan ta
bar yaranta, wata kuma da alheri take shigowa,
ta gidance zata ce sam bata yarda ki zauna ba
zata shiga ta fita da makirci tabi karkashin
kasa harda bin malamn tsibbu. Sai kin fita kin
bar mata gidan, haka suke cewa wai gida nasu
ne miji na su ne. To duk idan akayi hkr ke ta
gidan kika tsare gaskiyya kikayi nufin idan ta
zo zaki zauna lfy da ita, ki riketa da zuciyarki
tsakani da Allah. To ko ta zo da mugun hali
gidan da izinin Allah sai kyakkyawan kudurinki
ya ruguza nata, idan kuma itace ta zo da nufin
alheri ke ta gidan sharri a zuciyarki nan ma zaki
ga Allah ya dorata bisa kanki, har ma ace daga
zuwanta ta koreki. Alhalin zuciyarki ce babu
kyau, amma duk idan zuciyar kowa ya tsarkake
babu wani mai mugun kulli tsakaninsa da dan
uwansa sai kiga zaman lfy ya wadata gidan.
Gaskiya gidan nan akwai matsala tundana dawo na
fuskance shi. Ya kamata mu gane mu magance matsalar
da kanmu dan ci gaban gidan. Dan wannan maganar ma
banso yiba. Dan Allah a kiyaye.
MIJIN ARO **part 13
92) Ki kwantar da
hankalinki da alheri a
zuciyarki zaki shiga gidan.
Ni ma da na hada
auren ba da wata manufa
na hada ba, fatana shine ya kasance alheri na
kulla, in ma kinje
gidan ki taddata da wani
mugun kudiri a ranta,
to ke kada ganin haka
yasa ki canza alherin da ke xuciyarki, ya rikide
mugun nufi, ki bar
zuciyarki da alherinta
Insha Allahu zaki ci ribar
kyakkyawan kudurinki.
Yanzu abu daya nake son inji daga gareki, kin

amince ko baki amince
ba? Kada kiyi shayin gaya
minin gaskiyya
kuma bana son ra'ayinmu
ya sha banban a gaban mahaifinki don yau
za'aje gidanku da
maganar. Shiru kawai
Aneesa tayi tana
sauraron jawabin Hajiya.
Ita kam! Gaskiya ta fada Ishaq yafi karfinta,
don kuwa shi ajin farko
ne a komai don hadadde ne
na shiga gasa, ga
kyau ga kudi ga tsabta da
addini da taimakon addinin ga son 'yan uwa da
taimaka musu, ita
dai har yau ba taba ganin
aibu ko wata illar
tasa ba, komai yayi birgeta
yakeyi sai take jin itama duk ranar da tayi
arzikin kudi irinsa
halayyarsa zata dinga
kaman tawa, ita kam!
Ba zata ce bata sonsa ba,
saboda tun asali sun gidan tare ne kusan ma a
inuwa daya suka
rayu don tun tana
tsumman goyo take
karakaina a dakin
mahaifiyarsa, shi yasa suka taso daga iyayensu har su
kaunar junansu
sukeyi, da abu ya sami
daya nan da nan zaka
ga sun taru sun kokawa
juna idan na bakin ciki ne haka idan na farin ciki
ne tare da yinsa, sau
da yawa idan yayo waya
zaizo zariya sai taji
farin ciki, ya cika ta duk sai
ta kosa ya zo ta ganshi, balle idan yace da
'ya'yansa zai zo, har
mafarkin takeyi saboda
yaransa kyawawa ne
irinsu masu kwarjini
kamarsa. Ita dai bata san dalilin da yasa take jinsa a
ranta ba ashe
akwai wani alheri da Allah
zai kulla ne a
tsakaninsu nan gaba, wai
ita aneesa zata zamo matar captain Ishaq! 93) Shararren
matukin
jirgin saman da

gwamnatin tarayya ke ji da
shi saboda
fasaharsa da baiwar da
Allah yayi masa ta

Please Login or Register in order to submit comment