Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baiwa ne ta
bangaren karatunsa, a
aviation har zuwa fita
kasar turai da yayi karatu,
zuwa aikinsa a Nnamdi Azikwe
international airport a
abuja.
Tayi sallama ta shigo, ya
amsa sallamarta
sannan ya nuna mata kujerar da ke
fuskantarshi yace ta zauna,
kafin ta zauna sai
ta tambayeshi Hajiya yace,
yanxun ta shiga
daki je ki gaisheta ki dawo. Taje ta gaida
Hajiya sannan ta dawo
gurinsa ta zauna ta
gaishe shi tace, ina su suhail
da mamansu?
Yace yanzu drive ya kaita gidansu wata
kawarta da sukayi karatu
tare a jami'ar abuja,
za su dameni na tarkata
mata su ya hada mata
da su da mai rainon su Yusra. Sun danyi shiru
ya soma mata dangane da
karatuna ta gaya
masa komai, yace to akwai
kudi zan dinga
turowa ta account din Hajiya na hidamarku ke
da kanneki, don bana son
in kuna cikin matsa
ko yaya take, duk sati
hajiya zata dinga baku
kudin da za kuyi anfani da su, larurar shc kuma
komai ya taso kije ki gaya
mata, bana son
zurfin ciki irin naki, sannan
wayar mama da
take hannunki ki ba Abbanku, bana so ki rike

waya, saboda ina son ki
fito da sakamon sch
ma kyau ta yadda ko da
kinsa mi mijin mun
aurar da ke zaki cigaba da karatun jami'a a
gidansa, Hajiya ta taba
gaya min akwai yaron
da ke son auranki dan gida
ne, ina fatan kina
sonsa ko? Ta sinne fuskarta hakan ya bashi
tabbacin tana son yaron. 67) To tunda kina sonsa sai
ki tsaida shi
banda jajibe2 kinsan
yawancin samarin
yanzun mayaudara ne,
kada ki biye dadin bakin wasunsu basu da kirki,
kina jina? Ta gyada kai.
Ya saka hannu a aljihu ya
dauko kudi dubu
biyar ya mika mata yace,
ga wannan ki rike a hannunki ko da wani abu
zai taso muku, mu
yau zamu wuce insha
Allahu, amma nxt wk
idan na sami tym zanzo, ki
ci gaba da hkr, ki kula da kannenki sosai
kisa ido a karatunsu
kada ki bari suna fashi sai
da kwakwaran dalili
kinji? Tace Insha Allahu zan
kula, mun gode Allah ya kaiku gida lfy,
yace ameen. Tana gidan
har su safeena suka dawo
da yake basu dade
ba, suna dawowa sukayi
shirin wucewa, su sultan suka rike Aneesa
wai saai an tafi da ita.
Ishaq yace tana yin
jarabawa ku bari idan ta
gama sai ta zo can ta
sameku, suka ce to su zasu zauna gurin Hajiya su
jirata ta gama
jarabawar, yace to ku
kuma naku karatun wa
zaiyi muku? Da kyar dai
aka lallaba su suka tafi. Bayan tafiyarsu ta
dawo cikin gida tare da
Hajiya, haka kurum taji
Hajiya taji tana dada jin
tsananin tausayin Aneesa
fiye da sauran yaran. Saboda tafi shakuwa da
maman sannan

yanzun duk wani nauyin
kula da yaran zai
koma kanta, da ma can ita
ce ta jibanci yawancin al'amuransu.
Hajiya ma haka ta tasa
Aneesa gaba da nasihohi
da en shawarwari
akan yadda zaman gidan
su, da ita kanta yadda zata kame
mutuncinta tunda yanzun
babu mai kulawa da
tarbiyarsu a gidan sai
wanda Allah ya so...... 68) ***************
***************
**************
A halin yaanzu Aneesa ta
shiga ajinta na
karshe kenan na secondary, Iyayen sagir
sun
zo sunyi maganar neman
masa aurenta,
saboda yanzun har ya sami
ya so mayi. Shi ya sa ya ji ya matsu ayi bikin
nasu. Baban sasa
da yake shine waliyyunsu
sai yace ya ba shi,
suka kawo kudin gaisuwa,
aka saka ranar biki idan ta kammala karatunta,
amma ba'a tsayar
da ranar ba sai ta kammala
tukunna. Hajiya ita
ce uwar biki, shi yasa duk
wasu sayayya da uwa keyi idan zata aurar
da diyarta ta dauki
Aneesa sun shiga kasuwa
sun sayi waasu
abubuwan, da suka je
Ummara ma ta siyo wasu. Ranar wata juma'a
Aneesa ta shirya tsaf
cikin atampa kalar
atamafar ya amshi jikinta,
to
dora bakar riga ta yane kanta da gyalen ta sa
pin ta matse. Basira ce ta
aiketa wani gida a
gwarbai, ta fito kofar gida
rike da sakon a irin
babbar ledar nan, a kofar gida taga wani
mutum tsaye, ta tsaya ta
dan risina ta
gaisheshi, duk da bata san
shi ba, yace dan

Allah Alh Ali ya dawo kuwa? Tace bai dawo ba,
amma nasan yana kan
hanya. Yace ko ke
diyarsa ce? Tace eh, yace
yauwa dama wani
muhimmin sako ne, tunda na ganki natsatsiya
bari in baki, don Allah idan
ya dawo ki bashi,
zan kira shi a waya in yi
masa karin bayani. Ya
dauko wani file a bayan motarsa ya mika mata
tare da cewa, don Allah ki
adana sosai kafin ya
dawo, nagode sai anjima.
Ya shiga motarsa ya
wuce. Har ta juya zata koma cikin gidan sai
tayi tunanin bari kawai ta
wuce da shi don bata
sani ba ko abinda ke ciki
sirri ne. Ko wasu
muhimman takardu kada taje ta ajiye tsautsayi
ya same su ta shiga uku, ko
kuma basira tana
iya bin sahu ta dauke ta
boye don kawai
Abbansu ya wulakantata. Idan ko ta boyen
kanneta zata lakabawa ko
ta yaga tace sune,
tunda haka take musu
binciki da ance sunyi
kaza zai kama su da duka kamar Allah ya aiko
shi, shi ya sa take taka
tsantsan bata son laifin
da za'a ce kanneta ne suka
yi, tafi son ace idan
ma dukan ne gara ya doketa, ko da yake
yanzun ta girma da wuya
ne zata yi laifi ya
bugeta, sai dai idan Basira
tace tayi mata abu
kaza daga ranar ya daina amsa gaisuwarta.
Idan tace abu kaza nasu ya
kare ta aiko
kanneta ba zai saya musu
ba, sai ya ga
dama... 69) Ita kuma Aneesa duk
kudin idan Ishaw ya
zo ya bata ko Hajiya ta bata
boyewa take yi
saboda Basira ta fara kulla
mata sharrin wai yawonta take xuwa tana
samo kudi gurin

maza, ranar da ta kulla
mata wannan sharrin
tayi kuka tamkar ranta zai
fita. Shi kuma Abbansu ya hau kai ya
zauna tamkat bai san
Ishaq ke musu hidimomi
ba, alhalin wani tym
din ma agaban shi yake
bata kudin, ya ba Abban ita ma basira idan
tana nan ya bata,
idan kuma bata nan zai
bayar yace a jiye mata,
amma don sharri sai ta
bage da yi maya sharri shi kuma Uban ya yarda
har yana tirketa wai ta
gaya masa gidan uban take
xuwa idan baya
nan ta samo kudi. Tai masa
rantsuwa babu inda take zuwa duk bai
yarda ba tana kuka taje
ta dauko alkurani izifi sittin
kuma cikakke ta zo
gabansa ta dafa alquranin
zata ranste ya kwace yana fada wai zata
janyo masa masifa
waya gaya mata ana
rantsu da Alkurani, balle
ita da baya da tabbacin
tana da gaskiyya, akan abinda zata rantse din. Tace
gara ya barta ta
rantse ko da ajalinta ne zai
sauka gara ya
sauka ta huta akan kazafin
da akayi mata. Da ya hanata haka tayi ta
kuka, kusan sati tana
kuka tare da ciwo mai
tsanani da ya kamata,
har sai da Hajiya ta zo gidan
da kanta ta dauketa suka je asibiti, aka
bata magunguna
da allurai. Ta saka file din
cikin ledat nan taga
gara ta tafi da shi idan ta
dawo ta san tym din ya dawo sai ta bashi
bakinta kanin kafarta. Ta
isa gidan da zata kai sako,
ta tarar matar bata
nan amma yanzun akace
zata dawo ta jirata, gashi bata son tayi dare,
saboda yamma ta
gabato sosai, ta so ta bar
sakon sai ta tuna

Basira tace tabata ne hannu
da hannu kada ta ba kowa. Kusan magriba
sannan ta dawo ta
bata sakon sannan ta riko
file dina nan ta taho
gida. 70) Mashin tayi tunanin
hawa saboda shine zai
kaita gida akan lokaci, don
kuwa idan tace
mota zata hau sai ta fito
bakin titi ta shigo ta kuma kafin ta fita lungun
nan sai ta dade. Tana
dan tafiya tana waigen
mashin. Kawai sai taji
tafiyar mutum abayanta, ta
soma taku da sauri saboda tsabar tsoro, can
sai taji an ja gefen
Hijab dinta, ta waigo da
zafin tsiwarta zata
yayyafawa ko waye
masifa, kawai sai tayi ido hudu da sagir, ta sauke
ajiyar hrt tace, Amma
wlh ka bani tsoro daga
sama ko kasa? Yace
daga ina kike ke da
magriban nan. Kin zo unguwarmu ko ki neme ni,
dama ko sabon
gidan mu baki taba zuwa
ba. Tayi murmushi
tace haka kurum sai in zo
gidanku, da dai ina zuwa idan ana sha'ani da su
haulat to amma
yanzu ai da kunya ko?
Yace meye abin kunya
kefa 'yar gida ce a gidan
mu tamkar su Haula, yanzu dai mu karasa ki
gauda su Hajiya sai in
kaiki a hala ta. Ta tsuntsire
da dariya tace, au
ashe kayi hala ban sani ba,
daga mashin ashe mun koma hala. Yace lah?
Baki san mashin din
shine hala ta ba, ai wannan
mashin dinmu
shine halar samari. Ta sake
dariya tace, kai sagir baka da dama.
Gaskiyya ka rakani hanya
kawai in hau mashin da ba
son Aunty Basira ta
aiko ni gurinta ba ta nan
bane na tsaya jiranta da baka ganni ba. Yace,
rabon zamu hadun ne

ya sa hakan ta faru. Amma
fa babu yadda
za'ayi ina kallo ki hau
bayan wani kato ya goya min ke alhalin gani kuma
ina da mashin din
nan. Don Allah zo muje da
yanzun kin gaishesu
ma munfito. Haka nan dai
ya tilasta mata suka shiga gidansu. Da yake
iyayensa masu mutnci
ne suka dinga haba2 da ita.
Ita kam, a darare
ta dofana ta zauna, en
matan gida ne suka gaisheta a wulankce, suna
wani jin kai, ita dai
duk ta kosa su bar gidan.
Tana ji yana gaya
musu, shima yanzun ya
ganta an aikota gidan Alh. Isa tana tsaye tana
jiran mashin shine ya
cqQWe gara shi ya goyata a
nashi mashin ya
kaita gidan da wani kato
ya dauketa, ko ba haka ba Hajiya? Yake
tambyar mamansu
Hanne, er tsohuwa tace,
haka nan ne dana
kana da gaskiyya. Suka yi
ta dariya... 71) Sun fito daidai
barandar gidan kenan.
Sukaji hon din mita zata
shigo, ya dubeta yace,
ga alhajinmu nan ya dawo
shima sai ku gaisa. Ta dafe kirji tace, gaskiyya
ba zan iya ba
kunyarsa nake ji sosai, don
Allah ina zan boye
idan ya shiga cikin gidan sai
in wuce, ya janyo gefen hijb dinta yace, yace
zo ki boye anan ai
yanzun zai shige sai mu tafi.
Da sauri ta bi
bayansa ya tura kofar
wani daki anan harabar gidan ta shiga, ta nemi
gefen gado ta dan
zauna a tsorace, sai ya da
ya fita ne ta karewa
dakin kallo ashe dakin
sagir ne, sai ta tsorace, ita kam gara ma da ta tsaya
ta gaida Alhajin
ne da ya fiye mata, gashi
sagir ya kutso ta

dakinsa, kada kannensa
suzo su ganta suce dama gurinsa ta zo ta fake
da cewa an aiko ne
gidan Alh. Isa. Alhajinsu na
shigowa yayi fakin
din motarsa. Sagir ya matsa
ya gaishe shi ya amsa, yace sadiq ya dawo
ne kuwa? Yace a'a
bai dawo ba. Yace, ok to zo
ka rakani nan
gidan Mal. Ado ance bai jin
dadi mu gaisheshi. Sagir ya dan kalli dakinsa
yace to alh. Bari in
dauko waya ta a daki. Ya
shigo ya sami
Aneesa a tsaye duk ta
tsorace yace, bari in dan raka Alhaji dubiyar wani
makocinmu ga gidan
nan kusa yanzu zamu
dawo. Tace sagir bari
kawai in tafi kaga dare
yayi Abbanmu ya dawo kada in jawa kaina laifi.
Yace wlh ba dadewa
zamuyi ba yi hkr. Ya fito ya
ja kofar, Alh. yace
ka rufe da key kaga ba
kowa yau aharabar gidan, ko ka manta ranar
da aka kwashe muku
kaya ne. Ya kulle kofar da
mukullin suka fita,
su ka ci karo da kaninsa
Sadiq shi dakinsu daya da hanne, ya mika
masa key din tare da
yi masa rada a kunne
Akwai matata a dakin ka
taya ta hira kafin mu dawo
yanzu. Allah Allah sadiq yake ya bude yaga
wacece, idan ta bashi
fuska ma ya dan rage
ahanya a gurinta, tunda
dai yasan duk en matan da
suke kawowa nan, en hutu ne. Basa kawo mai
mutunci.
Musamman shi sadiq da ya
maida mace
tamkar riga yau idan ya
saka wannan gobe wata zai saka. Shi kam
sagir da wuya kaga
mace ya kawo sai dai irin
marasa mutuncin
nan sun su biyo shi en asha
minti.....MIJIN ARO 1 **11

72) Yana bude kofa ya ci karo da Aneesa tayi
tsuru2 a tsaye. Yayi murmushi yace, au dama
kece, meye abin tsoro ki saki jikin mana ke da
dakin mijinki. Tace haba dakin miji ai ba'a
daura aure ba, tsautsayi ne ma yanzu ya shigo
da ni dakinsa don wlh bansan dakinsa bane.
Sadiq yayi wata munafukar dariya yace,
Tsautsayi! To ai dama akan sami irin wannan
tsautsauyin, balle irinku da kiris ya rage. Sai ya
canza zancen nasa zuwa wata siga, hakan ya
sa tayi shiru. Ya nuna mata gefen gado yace, ki
zauna mana ai yanzu zai dawo. Ta ki zama, ya
mika hannu yace muga file din hannunki na
menene? Tace na Abbanmu ne aka bani
inbashi. Ya matsa wai a dole sai ya amsa ya
gani, da taga so yake ya hada jikinsa da na ta
sai ta sakar masa. A gaugauce sagir ya shigo
dakin yace, don Allah amarya yi hkr, ta so muje
in kaiki gida, ai bamu dade b. Ita dai da sauri ta
mike suka fito tana ta tsoron kada wani ganta
bayan ganin da sadiq yayi mata gashi har ya
neman yi musu wata fassara. Tun a bakin titi
Aneesa tace sagir ya sauketa. Ta karasa, shi
kuma ya koma, sai yace sam, ba zai yiwu ba
ya ajeta a bakin titi, to meye anfanin kawo ta
din da yayi, ita kuma tsoro take ji kada agansu
tare a dauka wani gurin suka je tare, tunda
yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba. Allah ya
taimaketa babu kowa a kofar gidan shi yasa
yana tsayar da mashin din ta shiga gida da
saurinta. Abinda take tsoro shi ne dai ya faru,
saboda Abbansu ta gani atsakar gida da
Basira suna tsaye, ya sakar mata harara yace,
daga gidan ubanwa kike? Ta dubi Basira
wadda ta dauke kanta tace, Aunty Basira ce ta
aikeni... Yace yanxun daga inda aka akeki kike
ko ya?
73 MA IS BLANK PAGE
74) Yace maza taje ta nemo masa file din sa,
yanzun zai fita da shi office. Gidan Hajiya ta
shiga tana ganinta tace lfy? Ina zaki da
sassafe? Ta gayawa Hajiya abinda ya faru
amma bata gaya mata gaskiyyar inda ta bar
file din ba, saboda bata son Hajiya taji ta shiga
dakin sagir don ba mutuncinta bane. Hajiya
tace, ki tashi tunda yana jiranki, kiyi maza ki
dauko masa, Allah yasa sun gani sun boye
tunda kawar Basira ce, balle taji furucin da
Abbanku yayi.... Aneesa ta miki tace, Hajiya
dan bani wayarki in kirata inki, hajiya tace tana
daki je ki dauka, bata fito ba a dakin ta kira
numbar sagir ta tambaye shi ko yaga wani file

da ta bari a akan stool din dakinsa, yace ya
gani Amma ya dauka na sadiq ne, shi yanzu ya
fita ta bari zai kawo mata gida. Tace, ai gani
nan a hanya zanzo in amsa na abbanmu ne,
yace yanzun zai fita da shi office. Yace to ki
karasa gidan sadiq na nan. Ko kuma ki bari in
kira shi sai ya kawo miki gida. Tayi saurin cewa
ka barrshi kawai zanje in amsa. Allah ya
taimaka harabar gidan babu kowa, dama tana
tsoron kada wani dan gidan ya ganta, ta shiga
3. Abude din yake, tayi sallama ta shiga sadiq
na zaune yana shafa mai da alama wanka ya
fito, yana sanye da singlet da dogon wando. Ya
dubeta yayi murmushi yace, daga ina haka? Na
ganki a tsorace? Ya sagir din yayi sammakon
fita gurin aiki, tace dama ba gurinsa na zo ba,
file din nan na jiya da ka gani shi na manta na
zo dauka, sagir yace ka bani. Yace file? Na
dauka da shi kika fita? Ai kuwa ban ganshi ba,
ta gintse fuska saboda ta lura yana son maida
abin wasan yara, tace wlh anan na barshi shi
sagir ma yace ya ganshi. Yace ok to dan zauna
bari in sa riga sai ki tayani mu duba. Ta daure
fuska sosai tace, gaskiyya ba zama na zo yi
ba, daukan file kawai na zoyi Abbanmu na can
na jirana, don Allah idan ka gani ka bani. Yace
maida wukar na tsinta, idan na baki wani
tukwici zaki bani? Taji sanyi aranta da yace ya
gani, tace au sai na baka tukwici? To fadi nawa
kake so? Yayi murmushi, ni ba kudi zaki bani
ba, bari kiga tukwicin....
75) Kawai sai taga ya ja kofar dakin yana
juyowa taja da baya tace, sadiq me kake nufi
da nine? Ni fa ba irin en iskan en matan nan da
ka sani bane, in ma banda rashin mutunci irin
naka, ka rasa wadda zaka yiwa irin wannan cin
zarafin sai ni da muke shirin aure da
danuwanka. Ai ko wani ka ga zaiyi min irin
haka, a tunani na sai inda karfinka ya kare dole
zaka kare min mutuncina, albarkacin
danuwanka. Kaga bani file dina in fita a dakin
nan. Ya murmusa, haba Aneesa shi dan uwan
nawa ince jiya nan kika wuni gurinshi ya gama
kwasar gararsa, to meye nima don zaki sammin
ragowarsa. Hawaye ya gangaro a fuskarta
tace, haka dan uwan naka ya gaya maka? To
ni sagir a gurina mai mutunci ne tunda ko
hannuna bai taba rikewa ba, balle mugun
alkabain da kake ikiraran mun aikata. Ni kam!
Na bar ka da Allah shi zaiyi mana hisabi da kai
ranar gobe kiyama, yanzun ka bani file dina in
tafi ko in yi maka ihu... Dariya ya kyalkyale da

ita yace, kiyi ihu azo a ganki kin kawo kanki
gurin maza, kinga jiya an ganki a gidan nan da
sagir yau kuma kin kanki gurina, kinga sai ta
tabbata jarabarki ta isa. Oya! Yi ihun ina jiranki.
Ta soma kuka saboda tausayin kanta yau Allah
ya hadata da macuci mara tsoron Allah kuma
masharranci. Addu'a ta soma karantowa a
ranta saboda Allah ya kareta daga sharrin da
yake shirin kulla mata, wanda idan ya kulla
mata shi bata da mai shaidarta sai Allah, tunda
gata adakinsu, balle kuma idan zance yaje
kunnen abbansu ta shiga uku, dama ya furta
kalmar zargin wani abu tsakaninta da sagir,
idan yaji haka kuma shi kenan zaice zarginsa
ya zamo gaskiyya. Ta durkusa tana kuka tana
rokonsa ya bata file din don Allah. Da ta so ta
kyale shi ta tafi tasan idan sagir ya dawo dole
ya bashi, to amma tana tsoron me zai faru idan
ta koma gida babu shi, dole idan abu yayi nisa
a san a dakinsu sagir ta bar file din. Da kyar ya
dauko ya bata da sassarfa ta fita a dakin tayi
saurin ta bar harabar gurin...
76) Gidan Hajiya ta fara shiga saboda ta dan
gyara fuskarta ko wanketa ne tayi, dalilin kukan
da ta sha. Hajiya na ganin idanunta jajaye ta
soma tambayar. Kin koma gida ne? Tace ban
koma ba, yanzun na dawo, wani abu ya faru
ne? Tace na dauka ko yayanki ya kira ta wayar
Abbanku ne yayi magana da ke. Tace meye ya
faru? Yanzun ne yayi min waya wai an kwantar
da sultan a asibiti, ciwo sosai yakeyi Typhoid n
Malaria, Tace subhanallahi! Ban shiga gidan
kilan ya kira, Allah sarki sultan ikon Allah kenan
gadonsu fah lullube yake da net, ruwa ma na
gora suke sha, lallai na yarda duk kariyar
mutum sai in Allah yin ikonsa, shiga cikin gidan
sauro ko shan ruwan gora bai isa ya hana
mutum kamuwa da ciwo ba, idan Allah ya nufa
ciwon zai kama mutum kamuwa da ciwo ba
idan Allah ya nufa ciwon zai kama mutum, in
har kuwa mutum yayi taka tsan-tsan da
lafiyarsa yaga cuta bata sameshi ba, ba to
kada ya dauka daga gare shi ne, a'a daga Allah
ne wannan. Kin amso file din? Ta nuna mata,
gashi na ganshi Allah ya taimake ni. Tace, to
maza ki kai masa kada kuma kiyi wani laifin.
Tace Hajiya zaki duba jikin sultan din ne? Tace
zanje gobe Insha Allahu, ina jin ma dake zamu
tafi don sultan din ni dake yake ta kira, shi ya
sa ma Ishaq yace zai kira Abbanku ya roke shi
goben in tafi da ke. Tace, Allah ya sa ya barni,
don nima naji ina son ganin Sultan din. Washe

gari driver ya dauke Hajiya da Aneesa ya kaisu
Abuja, kai tsaye asibitin suka wuce saboda
Aneesa tasan asibitin sun taba zuwa da
safeena. Yanayin yadda suka ga jikin sultan
din abin ya basu tsoro don yana jin jiki sosai.
Yana ganin shigowarsu ya miko wa Hajiya
hannu ta matsa ta rike shi tace sannu Hassan,
Allah ya baka lfy. Ashe haka ciwon ya kamaka
sosai. Ya sake mika hannun gurin Aneesa ta
matsa ta rike shi, tana masa sannu. Safeena ta
matso suka gaisa, suka tambayi mai jiki.
77) Hajiya tace ina su Husaini, yace yanzun
dukkansu dadynsu ya wuce da su gida yau duk
rigima suke jin tunda muka zo da safe suke
kuka, da yake dadynsu ne yake kwana da
Sultan din ni sai in koma fida. Bari in sanar
masa isowarku, ta dauko wayarta ta kira shi ta
gaya masa zuwansu Hajiya yace gashi nan
zuwa. Lokacin da ya shig Aneesa zaune take
gefen gadon tana ba sultan tea, ya dube su
yace, kai! Kai! Aneesa anyi sa'a yau sam yaki
cin komai lallai zuwanki yayi kyau, dama tunda
ya fara ciwon yake kiran Auntyn zariya da
Hajiyan Zariya. Hajiya tace ai gamu munzo
ashe haka jikin yayi? To Allah ya bashi lfy. Yace
ameen... Sannan ya matsa gefen Hajiyar suka
gaisa, yace ina ga tunda kunga jikin nasa sai
muje in kaiku gida ku huta, ko da yamma ne sai
in dawo da ku. Ya kwashe su ya kaisu gida,
suka ci abinci sukayi sallah, sannan suka
dankwanta, bayan la'asar sannan suka sake
koma. Kwanansu daya a abuja a washe garin
na biyunne zasu koma saboda jkin sultan din
ya fara sauki, don daren da za su koma gida
cewa yayi sai su Hajiyan su tafi dashi gida, ba
zai zauna asibitin ba, tace to su tafi ita sai ta
kwana da shi, ishaq yace ai ba zata iya rigimar
sultan ba, don sam basa bacci ciwon yafi
matsa masa cikin dare, da kyar aka lallashe shi
suka tafi, sai kuka yake shi dai akai shi gida.
Sun idar da sallah subahi kenan, hajiya taji an
kirata a waya, Aneesa dake kusa da wayar tayi
saurin miko mata tana cewa Ya Ishaq ne.
Hajiya ta amsa tana cewa, kila har yanzun
rigimar Hassan yakeyi, ina ganin yanzun zan
shirya in iso asibitin jira har mafarkinsa nayi.
Ta kara wayar a kunne suka gaisa da Ishaq ta
tambaye shi mai jki, yace jiki kam Allah ya
kawo iyakar ciwo, don gabanin kiran subahi ya
amsa kiran Ubangiji, yanzun haka gamu nan
tahowa gida.
78) Salati Hajiya ta sa, Aneesa ta matso tana

tambayarta abinda ya faru duk da yake ta sha
jinin jikinta, saboda yadda taji Hajiya ta saki
salati. Hajiya tace Aneesa Hassan ya amsa
kiran Ubangiji, Allah yayi masa rasuwa da
subahin nan. Aneesa rudewa tayi, ta mike
tsaye tana tafa hannuwa tana salati. Hajiya ta
riketa tace, zauna ina zaki je? Inda ya tafi
muma muna nan zuwa mu same shi, yanzu ko
anjima, yau ne ko gobe ne ba sani ba. Tace
mominsu ta sani? Tace ban sani ba ko ya
kirata ya gaya mata, bari in sameta. Ke kika
zauna nan dan ganinki da hawayen nan ita
zata rude. Hajiya ta kwankwasa dakin safeena
tare da yin sallama, daga ciki safeena ta zo ta
bude kofar, tana ganin Hajiya jikinta yayi sanyi,
ta bata hanya ta shiga dakin taga su Yautsa
bisa kujera an har anyi musu wanka mai ake
shafa musu. Duk suka haye jikin Hajiya.
Safeena ta gaida Hajiya sannan hajiyan tace
hassana har kunyi wanka ne? Yau dai ba sch.
Tace, eh asibiti nake son mu tafi da wuri don
kwana nayi ina mafarkin Sultan din yana ta
bina yana kuka wai shi gida zai je akai shi
gida, ni kuma tunda naga ya sami sauki, ko
za'a salleme shi ne mu dawo gida tunda yafi
son gidan. Tausayin ta ya kama Hajiya lallai
safeena bata san danta ya rasu ba, mafarkin
da tayi kuma dama tunda taji yana kuka zaije
gida zuciyarta ta bata anya yarin nan ba
gidansa na gaskiyya yake kuka zashi ba, ita
dai tun jiya ta tsinke da al'amarin yaron shiru
kawai tayi, ashe tunaninta zai zama gaskiyya.
Hajiya tace yayi min waya yanzu an sallame su
gasu nan ma tahiwa gida. Tace, an sallame
su? Sallama da asussuba? Ko dai sultan din ya
mutu ne ya boye miki yace, an sallamesu?
Hajiya tace, haba mutuwa, in ma mutuwarce
idan yagaya mana mai zamuyi inba hkr ba,
tunda ba mu muka ba kanmu shi ba. Allah ne
ya bamu aronsa, don ya amshi abinsa saimuyi
masa butulci ko waye? Ai kuwa mutwa na
sabon da akayi da mutum shi ake wa kuka ba
mutuwar ba, da bata tsallake kan kowa, duk
zaman ta mukeyi, kinga ki kwantar da
hankalinki mu tsaimayi isoawarsu, ki sa aranki
abinda ya faru daga Allane, ba wain don baya
so Bawan sa bane jarabartasa mu da ta rashi,
a'a jarabawace, bawa baya tawakkali to ya ci
jarabarwar ubangiji, shi yasa muke addu'a
Allah ya sa mu daga cikin musu juriya da
dukkan da dukkan abinda Allah zai dora masa.
79) Kuka safeena ta somayi, ta zauna daf da

hajiya tace dan Allah hajiya idan ya mutu ne ki
gaya min wlh nayi miki alkwarin zanyi
tawakkali kamar yadda kika tunasheni yanzun,
tunda nasan duk son da nake masa bai kai
wanda Allah ke masa ba, fata na Allah ya bamu
hkrn jure rashinsa. Da taga Hajiya ta soma
zubda kwalla sai ta shiga jero salati, Hajiya ta
riko ta tace, kiyi hkr, kiyi juriya, ki yiwa Allah
godiya shi ya baki Hassa yau ya amshi abinsa,
kiyi masa addu'a rahamar Allah, bashi da
hakkin kowa sai dai Allah ya sa mai cetonmu
ne. Hajiya ce ta sa wa su Yusra kaya ita kuma
safeena tana zaune tana sharar kwalla, har
suka ji isowar su Ishaq fargaba ya dinga yi na
yadda zai shigo yace ya tunkari Safeena da
rasuwar sultan, saboda ya santa yanzun zata
hargitsa kanta, bai san Allah ya taimakeshi
Hajiyarsa ta sanar mata ba, ta hanyar nasiha
da lumana, kuma har tayi tawakkali. Yana
shiga dakinta yayi mamakin ganinta a nutse da
Hajabi da Casbaha a hannunta tana ja, sai
hawaye sa suka ki tsayawa sai sharewa take.
Sanyi yaji a ransa lallai kasancewar Babba a
guri ma rahma ne don zai aiwatar da abinda
tunaninka da hikimarka ba za suyi ba, Hakika
ya tabbatar duk iya lallashinsa da dabarunsa,
zai yi wuya ya iya shawo kanta har tayi
tawakkali haka, mutum daya ce zata ladaftar
masa da ita farat daya, itace mahaifiyarta idan
ta iso. Ya zauna wajen hajiya suka sake
gaisawa, yace zamu shigo da shi a ina zaki yi
masa wanka ga mamansu safeena nan isowa
da en gidansu. Tace, ka kawo shi nan dakin
mahaifiyarsa. Ba'a dade ba iyayen Safeena
suka iso da yake tsakanin Unguwanninsu babu
nisa, Mamansu safeena da hajiya ne suka yi
masa wanka suka gyara shi, aka sallace shi
akaje aka binne. Sai da akayi kwana 7 da
rasuwar sannan Hajiya da Aneesa suka koma
zaria cike da kewar rashin sultan, yaro ne
hakurarre mai shiga rai ba shi da hayaniya irin
dan uwansa.
******************************
**************80) A
halin yanzun karatun Aneesa ya zo karshe,
saboda har sun fara zana jarabawar su ta
WAEC, hakan ne ya sa maganar auren Aneesan
ta taso gadan2, shi kanshi sagir duk ya kagara
ayi wannan auren ko don saboda en tsegumi
irin su

Please Login or Register in order to submit comment