Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

36) Tace wlh babu wata er
iska nace da zaka
auro ta rike mini yara,
dama niyyar aurenka
kake yi shi ya sa zaka fake
da son 'ya'ya tunda ni nace 2 sun isheni to ka
auro matan duniyan
nan wlh nafi karfinsu. Daga
wasa sai ta maida
zancen fada, saboda
tsananin kishi dole ya fice ya bar mata gidan.
Magungunan da likitan ya
basu kin shansu tayi shi
yasa aranar ciwo yayi
mata dirar mikiya ga
hayaniyar yara, suka zo suka dameta, ai kuwa
haushin dadyn su sai ta
huce akansu, yana falo yaji
ihunsu, yayi sauri
ya shiga dakin ya kamo
hannunsu yana tambyar menen? Suhail ya
nunata yace, mom
ce ta yi mana bulala wai mu
fita a dakinta. Suje
duk inda za su amma bazai
yiyu ina ji da kaina su zo su dameni ba, da
wanne zanji? Ya fice da
su yana cewa, ai ba su suka
kar zoman ba
ratayar ma ba abasu ba, ba
zaki sake ganin su ba. Ya sami su Aneesa a
kicin yace, aneesa
gasu nan kada ku barsu su
shiga gurin
mamansu, suna damunta,
ko me suke so kuyi musu, komansu yana
dakinsu. Kwanan
safeena uku bata zuwa

ko'ina saboda tana
karatu a university din
Abuja, aranar wata kawarta tazo dubata, tym
din ita da aneesa na
dakin baccinta tana tayata
gyaran dakin. Ta
bar Aneesa a dakin ta fito
falo gurin bakuwarta. Da jin hirar su kasan
aminan juna ne. Safeena
ta shiga zayyana mata
cewa ciki gareta, kuma
ita wlh so take ta cire shi
don ba zata iya wahalar laulayi ba, ga
karatu ga su Suhail
sannan nan da en watanni
ace ta haihu. Kawar
dariya tayi tace, ai hkr
zakiyi ki barshi tunda mai abin na son abinsa,
kina dai ji yace zai
dauki mummunan mataki
idan kika cire masa
ciki. Ke a tunaninki wane
mataki zai dauka? Iyaka dai yayi fadansa idan
ya gama ya koma
fushi daga nan ba zai kai
ko ina ba zai saulo,
dan nasan hushinsa ba ya
kai ko ina duk iya laifin da nayi masa. Kawar
mai suna Aina'u
tace, tace kinsan fa ya taba
ce miki idan ke ba
kya son yaran shi yana so
kuma zai auro wata tayi ta haifa masa, ba kya
ganin zai iya auri
watan? 37) Dariya Safeena tayi
tace, aure! Ai ina jin
Ishaq shi da aure a duniya
dai ya gama shi sai
da ko a lahira, don idan
yace zai aure nima zan dau mataki, mummunan
mataki akan haka,
zan yi adawa da auren
babba ma kuwa, yara
kam bani da ra'ayin tara su,
kamar akuya, dole ya hkr da tsari na. Aina'u ta
murmusa tace. In
kuma Allah ya rubuta masa
'ya'ya da yawa ya
zakiyi? Kinga dole kiyi hkr
ki zazzage masa adadin su. In kuma baki so
wata ta zo ta
amshe ki. Ta tabe baki tace,

kin fa san yadda
bana son kishiya, ko
sunanta bana son ji. Ni fa ko wata naga za ayiwa
kishiya jin zafi nakeyi,
ina jin ma na fi ta jin kishin
abin. Balle ace ni
kuma, kinsan Allah da ya
kawo min wata gidan nan amatsayin kishiya gara
ya aje macen
banza a waje (kuji banza
mtsssw) wannan
bata dameni ba. Akan kishi
kuma a gidana. In ma rabon yaran ne can
ahaifa masa su awaje,
da dai akawon gida. Kai!
Ina ba zai yiwu ba
ma, ai gara in mutu da in ga
wata mace Captain ya kawo a matsayin
kishiya. Kinsan Allah da
shi da ni da ita zan iya
halaka mu. Gara mu
mutu gabada a huta don ba
ma zan yarda in mutu ni kadai in barsu su ci
gaba soyayya ba
gara a yi mutuwar kasko.
Ke aina"u kin ma san
yadda nake son Captain
kuwa? Ni fa ina jin ko uwar sa ba zata fini sonsa
ba, ita dai ta
haifamini shi, shi ya sa ma
idan naga tana
wani nan-nan da shi har
haushi nake ji, sai in ga kamar zata raba mu ne,
Aina'u tayi ajiyar hrt
tace, safeena kenan
lamarinki sai ke. Ni dai
shawarata ki bar cikin nan
baki san irin albarkar da yake tattare
da shi ba. Aneesa na
ckin dakin baccin safeena
tayi zuru tana jin
wannan zance mai kama da
shirin film. Ita kam duk yadda take tunanin
safeena ashe ta wuce
nan, lallai duk wadda Allah
ya hada kishi tare
da ita ta shiga3. Ko da yake
ma Ishaq baya da ra'ayin kara aure don basu
taba jin ya furta ba.
Tana dakin har kawar ta
tafi safeena ta zo ta
suka cigaba da gyaran

dakin. Ita a tunanin safeena Aneesa bata jiyo
hirarsu ba, kuma ko
da ta ji ba abu ne da ya
shefta ba, tunda ta san
Aneesa babu ruwanta da
abinda bai shafeta ba.
38) Ranar litinin Hajiya
tayiwa Ishaq waya
cewa Mamansu Aneesa ta
haihu, amma yaron
bai zo da rai ba. Sai dai lafiyarta lau. Da yake
ma hajiya na gidansu
Aneesa ne sai ta ba
maman wayar suka gaisa
da Ishaw yayi mata
sannu da jiki. Da ya dawo gida da yamma ne
ya kira Aneesa da sadiya
yake gaya nusu.
Aneesa duk sai ta rude ta
soma sharar kwalla
wai ita gobe gida zata tafi. Yace bayan na gaya
miki maman lfiyarta lau,
munyi ma magana da
ita, baki yarda ba kenan?
Tace ni so nake in
ganta shi ya sa, yace zaki ganta amma ba
gobe ba, saboda nine zan
maida ki gida. Ina
son zuwa nima amma sai
ranar asabar, saboda
gabadaya wannan satin ina da tafiye2 kuma
ba ma kasar nan bane. Ki
bari idan natafi gobe
sai friday zan dawo sai mu
tafi. Ba don san ran
Aneesa ba ta hkr. Tunda babu yadda zatayi$
Ranar da zasu tafi
kayayyaki sosai Ishaq din
ya saya musu na kashin
kansu, don a tafiye2
da yayi naa jigilar fasinja kasashe, acan ma ya
siyo masu tsarabar abayoyi
da takalma da
jakunkuna masu kyau.
Don har mama da
Hajiya ya sayo masu takal wasu en india masu
kyau. Ita ma safeena tayi
masu dinkuna irin
nasu na en gayu en jami"a
don tare ma ta
dauke su a motarta suka je gurin tailor ya
gansu ya babbance

awonsu, saboda sadiya
tafi Aneesa jiki, ita Aneesa
falen2 ce ajiki,
kirjinta ne ke da cika da hips dinta. Suna
hanyar dawowa Aneesa
tace, Aunty naji kince
siket za'ayi mana kala3,
duka ne dubu biyar?
Tace, a'a ko wani set ne dubu biyar, mu dinki a
abuja akwai kyau, amma
da tsada. Aneesa
tace aunty mu a zariya ba
zai wuce dubu daya
daya ba, gashi telolinmu sun iya dinki sosai..
Babu wani babbanci dana
abujan. Ko zamu
amso ne mu bada a can
zarian? Tace ku barshi
kawai, kinsan mu nan Abuja akwai tsadar
rauyuwa komai na abuja
mai tsada ne. Shi
yasa duk wanda kika gani
yana zaune a cikin
garin Abuja, to ya ci ya tada kai ne. 39) Da wuri suka baro
abuja saboda ranar
Ishaq zai dawo shi da su
Suhail akayo tafiyar
saboda rigimarsu. Sai sun
biyo shi, ba arziki ishaq ya sha Safeena ya
shirya su tunda ba
kwana zaiyi ba, ko ma
kwana ne ya kama shi
ba damuwa zaiyi ba. Jikin
safeena har yanxu laulayi take sosai, tunda
har karin ruwan anyi
mata agida, saboda yawan
Amai. Aneesa a
tsaitsaye ta gaida Hajiya
tace bari taje ta duba jikin Mama zata dawo
anjima. Ishaq ya dubeta
yace ku tafi da su sultan
nima gani nan
shigowa, ku gaidata.
Sadiya ta taya ta diban kayanta har sabon troley
da Ishaq ya saya
masu kowa babba, aciki
suka xubo kayansu.
Shara suka iske Maman
nayi a dakinta Aneesa nayin sallama tayi sauri ta
amsa tsintsinyar
tana cewa Mama kece da
shara har kin

warware ina Aisha fah?
Tace na aiketa sannun ku da zuwa, sannu sadiya
kun sha abuja, ashe
har da mazajena aka zo. An
zo mana da
cefane ko ni da Hajiya? Ta
kamo su tana tambayrsu, sultan ya laluba
Aljihuns ya dauko
sabon kudi ya mika mata,
yace gashi kudin
cefanen. Da Mama da su
Aneesa me zasuyi ba dariya ba. Shi ma Suhail ya
kwaso nasa kudin
ya ba mama akayi ta musu
dariya. Su Aneesa
suka gaida Mama da jiki.
Aneesa ta kara da cewa ai ranar da Yaya ya
fada mana kin haihu
dan baizo da rai ba nayi ta
kuka nace gobe
gida zan dawo, maman tace
ai kuka? To idan kika dawo me zaki yi mini?
Tace abubuwa da
yawa zanyi miki mama
tunda na san baki da
mai taimaka miki sai Allah,
yanzun baga irinta nan ba sha naga tarar
kinayi. 41) Ji dadi wai duk wanda
Ya Ishaq yake sayo
musu a Abuja ita baya mata
dadin na zaria. Da
yamma Aneesa ta fidda
tsarabar jama'ar cikin gida ta tafi kai musu, ta
shiga dakin Hanne ta
durkusa ta bata su subulai
da mayuka da
turare, en matan dakin sun
cikin dakin, uwar ta kada baki tace. Ai fa ansha
abuja dole kuyo
tsaraba, balle ana tayi musu
dawainiyya da
'ya'ya ba dangin iya bana
baba. Aneesa na jin haka ta yi saurin mikewa
zata fice taji babbar
diyar Hanne na cewa, ke
ko mama ba dole ba
gidan maiko, tafi tafi ma sai
kiji wata babbar magana ta bullo hadin
zaumuntar dole, ba
dangin iya ba na baba.
'Ya'yan suka sheke da
dariya. Aneesa da sauri har

tana tuntube ta afka dakin Halima, 'ya ta
mutanen Abuja tlfy na
ganki a hargitse? Aneesa
sarkin saurin kuka
nan da manyan fararen
idanunta suka antayo da hawaye. Halima tace
gidanmu ko? Ai
shikenan kin dawo za su
fara halinsu da kina
can abinki kamar kada ki
dawo, dibi yadda kika yi kyau kamar wata
baturiya, hankalinki
kwamce a can, nan ko
tsegumi da gulmace2
kadai za su tsangwami
zuciyar mutum, kai wannan musibaa Allah ka
kawo mana iyakarta
$ yanzun me ya faru kuma?
Aneesa ta share
hawayenta da agefen
hannunta ta gayawa Halima cin fuskar da sukai
mata daga abin
arziki. Halima tayi
murmushi tace kai aneesa.
Wlh kinso zubda
hawayenki a banza ne, yanzun meye sabo a
wajenki cikin halayyar
Hanne da yaranta? Sharri
ko bakin cikinsu
wanenen baki sani ba.
Ishaq dai abin arziki ya hada uwarsa da taki, har
suka zama tamkar
sun fito ciki daya, kuma
'ya'yansu dole kuyi
zumunci. Har gashi muma
muna cin tubarrakinku, ko da yake
alheri halinsune,
amma ai babu abinda da ba
sayi mana na
alheri kuma suna amshewa
suna jin dadi, amma don butulci irin na
mutumin yau, sai
kuma sune za ayi wa
hassada a bi su da kulli.
Shi don Allah ina laifin
wanda ke kaunar naka? Mu kam babu abinda zamu
ce musu sai san
barka. Allah ya ninnunka
ma ishaq arzikinsa ya
kara budo masa hanyoyin
alheri, ki rabu da su ki share hawayenki, kada
ma fatima taji

wannan maganar ki barsu
da sharrinsu.
42) Da dare ne Maman
Aneesa ke gaya wa Aneesa wani labari da ya
razanar na da ita,
Karama yau fa saura sati
daya a daurawa
Abbanku aure da wata
bazawara anan cikin zariya take can bakin
kasuwa take. Aneesaa ta
dafe kirji tace mama aure?
Yanzun abinda.
Abba zai yi miki kenan?
Alhalin ke da shi ba wata jituwa kuke ba,
sannan zai karo wata a
tsakaninku, me kika yi
masa dai yi miki
sakayyar kishiya? Mama
tace, kash! Karama ban son jin haka daga
bakinki ba, Abbanku
yana da halin auren mace
uku yanzun ya
hadamu, ba shi da rashin
wadata, kuma ni banyi bakin cikin aurensa
ba, addu'ata dai
Allah ya daidaita
tsakaninmu, ya sa hakan
zai
zamo alheri a garemu dukkanmu. Ina fatan
idan ta zo zaku riketa a
matsayin uwa da
kowane irin hali ta zo mu
dogara ga Allah don
shine shahidi. Dakins Aneesa ciki da falo ne,
sai yace su koma dakin
mamansu anan ne zai
saka amaryarsa, Allah ya
sa dakin maman falo
ne da dakuna biyu ciki, sai tace su Aneesa su
gyara daya dakin, ita ta
dauka daya. Gaba
daya gidan Abbansu ya
saka akayi fenti har da
dakin maman sai dai ko tsinke bai bata ba, ko
ya canza mata na fadar
kishiya ba. Hajiya
Ishaq itace ta dinga tausar
zuciyar maman duk
da dai dama ba wai ta tada hankalinta bane.
Hajiya ta bata kyautar
wasu lafiyayyun kujeru
sets da take ajiye da su

awani daki a gidan.
Wadanda masu ne kila ko amaryar ba zata zo
da irinsu ba, nan da nan
Halima ta taya su
Aneesa aka fidda tsoffin
kujerun mama aka
zuba sabbin, ga leda da labule ta siya komai
yayi sabo a falon. Da
abbansu Aneesa ya dawo
ya shigo dakin sai yayi
sororo yana kallon
dakin tayi saurin gaya masa inda kujerun suka
fito labulai da leda ita kuma
ta siya da kudin da
Ishaq ya bata. 43) Tabe baki yayi yace, ai
bansan ke 'yar
gatan zuriar Hajiya ce ban
tada hankalina inyi
miki komai ba, nasan ba
zata kyaleki haka ba. Murmushi kawai Mama tayi
don ya san ita mai
hkr ce, shi yasa ya fadi
haka, kuma ya ma riga
ya san ko da bata masa
hankali ba, amma a zuciyarta sai da tace, oh
Allah mutum bai rasa
abinda zai kyautata mini
inji dadi ba, amma
don bai min hidima ba, ko
ajikinsa, alhali shine ya cancanci yayi fiye da
abinda Hajiya ke mini,
amma babu ruwansa
tamkar zaman Hajiya da
zuri'arta nakeyi. Ranar
asabar aka daurawa Abbansu Aneesa aure,
kuma aranar ne da dare
matar ta tare, wadda a
yadda ya gaya wa
maman cewa 'ya'yanta 3
mijinta tsarain mota yayi ya mtu ya bar marayu.
*************
Zaman su Ya faro abin
sha'wa kasancewar
Fatima( mama) ta kama
girmanta na babban su kuma su Aneesa
kanninta sun maida
amaryar tamkar uwa
kullum ta rugumesu
tamkar 'ya'yanta. Addua
fatima a kullum take kada Allah ya aiko da
baraka, a tskanin
wannan zama nasu da

amarya ta z da ita ya
saje cikin 'ya'yan gidan
tamkat nan aka haifeshi. Ashe tsuge bata
kare ba wai , an sai
biri an sayi kura, en hana
ruwa gudu suna nan
sun sa idanu, ba haka
ransu ya so ba, Hanne da yaranta sun so ne ai
sanadin amarya
wulakancin da akewa
fatima da 'ya'yanta ya
ninka na baya sai ga shi
suka ga akasjin haka, wannan abu yayi wa
Hanne ciwo shiyasa taci
alwashin cikin ire2
amakircinta sai tayi
kutungwila ta haddasa
rikici a gidansu Aneesa, wannan 'ya'yanta take
gayan mat, kaji shirme,
wai yaranta take batawa.
Allah ka ganar da
wanda ya kauce hanya,
rashin lfya ya samo asaline wata ranata da
Fatima bata nan, su
Aneesa sun tafi makaranta
hadda da suke
xuwa a tudun wada wato
Nurul tilawa, duk ranar asabar da lahadi, idan
suka tafi karfe
8am sai 6pm suke
dawowa.
Naku akodayaushe:
(Abduluk)MIJIN ARO 1**8
44) Gida ya rage da Basira amarya sai er
diyarta, tana ta hidimat dora girkin rana saboda
1pm mai mashin zaizo ya dauko abincin da yake
kawai su Aneesa makarantar. Hanne ta shigo
gidan saboda taga abbansu Aneesa ma ya tada motarsa
ya fita. Basira ta dubi hanne,
tace lah sannu mamansu haula, hala en aike
kike nema? Hanne ta tabe baki cike da iya
haddasa husuma, tace yan aike? Ai 'ya'yan
sasan nan basu aikuwa. Ai daga su sai uwarsu
suke rayuwa, ko kin taba ganin yaran na shiga wani sasa
balle a aike su? Ai gidan nan
tsakanin ko da su ido, babu kamar mai kulu2
idon nan irin na uwarta. Mai hali irin uwarta da
bata ganin kowa da kima, Basira tayi murmushi
tace wa kenan? Hala aysha? Hanne tace wace
aysha? Ai aysha ce tayo hali irin na ubanta ai tana shiga
cikinmu, Wannan sumuma kashe
din Aneesa miskila marar magana irin uwarta,

cikinsu fal da mugun abu. Basira tayi murmushi
tace, ni kam kinga kaf yaran nan ba wanda
jinina ya hadu da shi irin Aneesa don tafi aysha
hankali da nutsuwa ga ladabi da biyyaya, ko ubansu na
fadin haka, aneesa bata da kwiuwa
irin aysha. Nikam ita da uwarta basu da wani
aibu bansani ba ko nan gaba ma gani tunda
ban dade ba. Hanne tace ai kuwa nan gaba za
su fito miki da halinsu na asali, amma yanzun
ba zaki gane su ba, tunda ke xuwan yau ce, sai gaba zaki
gane idan suka hadar miki kai su
tasamma korarki cikin gidan. In banda ke wa
aka bari ta shigo gidan, sai ya nemu abu kiji
abu rigidi2 sai kuma kiji shiru, anbi dare an bi
rana an hana auren kema Allah ne ya nufa ga
rabo nan ma kila an samu, tunda jiya nake cema sa ina
amarya, yace kina kwance
massara ta rufe ki har ina masa tsiya yana
dariya, kinga yanzun ko cikin gareki, idan baki
sa'a ba sai an raba ki da shi. Ki bar ganin
matar nan kamar ta Allah kullum cikin hijab
zulum2 mugun abinda ke zuciyarta yafi karfin tunani.
45) Ita dai Basira shiru tayi bayan tace Allah ya
kyauta. Sai Hanne tace, bari in koma gida
dama na leko ne in ga jikin naki na dauka har
yanzu kina kwance ne, ashe kin mike na dole
kina bautar girki, ita da 'ya'yanta sun fice abinsu tunda
sunga kin juri wahala ko ba
girkinki ba dole kiyi, idan kina son zaman
gidansu. Gwiwa ba kwari Hanne ta fita, tunda
sam ba sami yadda take so ba, duk yadda ta
dawo tsegumin Fatima da 'ya'yanta amarya
Basira bai shiga kunnenta ba, amma duk da haka ta sha
alwashin yau da gobe sai tayi
nasara. Hakan ne kuwa ta kasance, don kuwa
yawan shigiwan da Hanne takeyi a boye da
wanda 'ya'yanta keyi sun wa Basira hudubar
tsiya, ya soma tasiri a zuciyarta, saboda yanzu
ta kai ga ranar da ba garkinta ba, bata taya Fatima ko
tsinke balle idan Fatima tana uzurin
fita, cewa tayi ba zatayi ba, duk mai girkin idan
zai fita yayi abinsa kafin ya fita, kuma dole
mutum ya dawo da wuri ya dora na dare,
amma ita Basira daga baya Hanne ta zuga ta
akan idan tana da girki anguwa ta kamata kada ma ta
tsaya bata tym dinta wajen yi
musu girki, tayi tafiyarta dole Fatiman tayi ko
don cikinta dana yaranta, in dan gudar diyarta
ne ta dinga tafiya da abarta, hakan kuwa akayi,
ita dai Mamansu Aneesa ba tace komai ba
idanu ta kawo ta zuba ma Basira tunda ta san zugata
akeyi. Ga kara da take yawan kaiwa

Abbansu Aneesa tace Fatima tayi mata abu
kaza ba ya bincike sai ya hau kai ya zauna ya
dinga fada, idan kuwa su Aneesa ne ranar sai
jikinsu ya gaya musu, aysha ce kawai bata kai
kararta saboda ta lura ita er gaban goshin ubance, kuma
kota kai kararta ba ya daukar
mataki, shi ya sa ta hkr Hanne tace ta daina, ta
taya shi som Aysha zasu fi daidaitawa. Ranar
wata monday su Aneesa sun dawo sch kenan
ko abinci ba su ci ba, Basira ta fito ta dubi
aneesa tace, Garin tuwonmu ya kare ga masara can a
buhun bagco ki dauka ki kai mini
sirfe da nika.
46) Aneesa tace, ina Iliya almajiri fa? Tunda
safe da kin bashi da yanzun anyi nikan, tace
banda dama baa uwar iyayi, ke kadai nake jira
ki dawo ki kai mini, shi ai ba bawan gidanku bane da
komai za'a ce sai shi. Kamar tace ga
Aysha nan ai itace kasa da ita, sai dai tayi
shiru saboda ganin Mama ta fito ranta a bace
ta dubi Aneesa, tace ke karama! Basira sa'arki
ce zaki fada ta fada? Ko ko shi Iliyan bawanki
ne, to maza kiyi sallah ki ci abinci kije ki kai bana son
rainin arziki. Allah ya sa Aneesa ma
tayi sallah shi yasa tana tube kayan ta ta
kewaya bayi ta wanke jikinta ta gyara kanta
sannan ta fito ta danci abinci kadan, sai ta
dauki ba buhun tana fitowa zauren gidansu
suka yi kicibis da sagir ya dubeta, ya dubi buhun
hannunta yace, Aneesa ina zuwa haka
ne daga dawowarku sch? Tace wlh an aike ni
ne, daga ina haka yace makaranta, na sauka
anan dan kawai in ganki inji sanyi gashi kuma
fita zakiyi. Tace, to ba gani ka ganni ba, ai kaji
sanyin ko? Yace sosai ma, amma kuma ai ba ganinki kadai
zanyi ba, hira nazo yi. Tace, sai
ka jirani in dawo ai ba zan dade ba. Ya leka
buhun hannunta ya ga tsabar masara yace, ba
dai kace mai kai nika ba? Yace Haba haba, wlh
kin wuce kaiwa tunda kina da kanne, kuma
kuna da almajirai a gidan nan ni bani in kai. Amma
gaskiyya ba zan yada kije bin layin nika
ba. Yana kici-kicin amsar buhun ita kuma ta
hana shi suna haka sai ga daya daga cikin
yaran Hanne zai wuce cikin gida, ya tsaya yace
k. Sagir ina wuni? Yace lfy lau, zo nan ina
zaka? Ba ko ina, yauwa ta amshi buhun hannun yayarka
kaje ka kai mata nika da sirfe
yanzun nan ka dawo ina jiranka anan. Ya
amsa jiki na rawa sagir ya ciro naira dari a
aljihunsa ya mika masa ta fi, ita dai Aneesa
tana tsaye tana kallon ikon Allah, ita kam tasan

in baya ga 'ya'yan Hanne na tsoronn sagir babu yadda
za'ayi salisu ya kai nikan nan, ko da
kuwa uwarsa ce ta aike shi, sai ta bashi lada
yake zuwa, in ma bai gama ba ko ta bashi
ladan ta bishi da lallashi ba zai je ba, idan
kuma ya amsa to yana fita zai aiko yara da
aiken ya gudu abinsa, idan abin da za ayi anfani da shi
gurin girki ne, har sai wani ya siyo
ta hirka bai dawo gidan ba don sangarta, to
ana gama abincin zata sa aje anemo shi, wai
ya zo ya ci abinci, ko ita da kanta ta dauka
gyale ta tafi nemansa.
47) Suna nan a zauren suna hirarsu ta masoya, su
Haulata suka fito za su fita. Yayi
daidai da dawowar Salisu daga kai nika, agabn
idonsu ya mikawa Aneesa nikan sannan ya ba
sagir sauran chanjin. Suka gaida kawunsu
suka fita, ba su dade ba sai ga su sun dawo.
Aneesa na ganinsu ta san tsugudidi ya dawo da su, tym
din da suka fito za su sake fita suke
ce mamanmu tace in ka gama ka shiga zata
baka sako can gida. Ya daure fuska yace,
daman kun dawo ne ku gaya mata na zo gidan
ban shiga ba gurinta ba? Ku dai ba kwa rabo
da tsegumi, Haula tace mu bamu gaya mata ba dama
tana neman salisu ne, daya shiga
yanzun shine yace ba yawo yaje ba, kainme ka
aike shi idan karyane ta tambayemu. Shine ta
atambayemu, muka ce eh zaka zo kana zaure.
Ya gayara fuskarsa yace, to naji kun kyauta,
shima salisun daga yawonsa ya dawo na aikeshi, shine zai
fake da cewa ni na aike shi,
ita kan Aneesa ta san wannan kai mata nika da
salisu yayi sai ya janyo jidali tsakaninta da
Hanne har da mamansu. Bayan sun fita ta dubi
sagir tace, bari inje in kai nikan cikin gida,
kaima kaje gurin kiran da aka maka. Ai kuwa yana shiga
yayarsa tayi kicin2 dai rai tace,
meye dalilin da za a aiki Aneesa dan ita
shaffafiya da mai ce zaka amsa ka ba dana
don shi bawa ne, ita kuma tafi karfin a aiketa
dole ita ga budurwa, in banda kinibibi ina
kanneta da ba a ba su ba sai nawa yaran. To wlh ahir
dinka kada ka kuma yi mini haka, in
hutu kake nema mata ai da kaine ya ya kamata
ka zo ka dinga zuwa mata aiken, tunda ka
zama sullutu. Yayi murmushi da yake shi mai
barkwanci ne, kuma ba shi da surin fushi, yace
ni ba don zakice na zama sakarai ba ai, da na dawo gidan
nan ko don in dinga tayata
ayyukan da naga take sha kullum. Taja Uban
tsaki, au abin ma wasa ka maida shi? Tunda ka

maisheni abokiyar wasanka, to ni zan gamu da
Aneesan gobe idan aka aiketa ba zata kai ba yarana ba,
sanin halin yayarsa tasa yasa ake barkwancinsa gefe ya
soma magana ta fahimta
da fadin gaskiyya da ya ba mata akan
zumuncinsu da ta riga ta tarwatsa.
48) Allah ya hanne a bar maganar wasa,
Aneesa ko ba soyayya tsakanina da ita ai er
uwar salisu ce, ta jini ko ni kawunsa bance yaje mata aike
ba zai iya zuwa mata ba, idan tace
yace gaskiyya in ma da wani abu tsakaninsu
da iyaye bai kamata ku dinga saka 'ya'yanku a
ciki ba, saboda zumuncinsu kuke ruguzawa
tunda idan ki ba zu kuyi ba tsakaninku, su dole
ne suyi zumunci da juna tunda alakar jini ta hada su,
kuma alakar jini wlh ta tafi gaban
wasa, xumunci dole suyi shi tunda Allah ne da
kansa yayi maganar zumunci dole suyi shi
tunda Allah ne da kansa yayi maganar zumunci
kuma duk wanda baiyi shi a duniya ba, dole zai
yi shi alahira, to ba gara ayi shi tun a duniya ba cikin
dadin rai da kaunar juna. Tunda
rayuwar duniyar 'yar kadan ce ta lahira tafi ta
duniya tsayi nesa ba akusa ba, itace mara
iyaka. Tayi murmushin da bai kai ciki ba, tace
sagir kenan, in dai wa'azinka akansu Aneesa
ne na riga na saba jinsa da dai akan wani abu ne kila zan
dauka, amma banda wadancan
gara ma ka kyayeni, tun kafin namu zumunci
ya baci ni da kai. Yayi murmushi a ransa yace,
in dai zumunci ne da ke ai da tuntuni ya lalace
da ace ina daka ta taki, in banda ni cikin en
uwa wa yake jurar halinki, har cewa ake yi ba ni da zuciya
inji en dakinmu. Yace ai ni da ke
zumuncimu babu mai raba shi, tunda ko
alahira sai munyi shi, wannan zumuncin yaran
nan nake son ki kule musu shi gam2 tinda dai
kece babba a gidan nan. Inbanda Goggo ita
kam ba a sata alissafi, tunda mara lfy ce amma Allah
yanxun kece uwar gidan nan. Ko shawara
za ayi dole a ce kece kan gaba. Ta tabe baki,
naji nasiharka yaya sagir, ka tashi ka tafi. Yayi
dariya ya kwanta bisa doguwar kujerarta yace,
ni ba yanzun zan tafi ba sai naci tuwon dare.
49). Tsarin zaman gidansu Aneesa yanzu ya chanza
kwata2, babu wani kwanciyar hankali,
saboda Basira yau gobe yasa ta dauki zugar
Hanne dadin munafuncinma, yaran hanne
yanxun dakin Basira suke wuni en matan. Duk
ranar girkinta ba yin abinci yadda za'a koshi, in
ma miya ce ta kara kana cin abinci to baka isa ta kara
maka ba, sai dai ka ci gaya ko ka hkr

da abincin, mama da ta lura da gayya Basira
keyin hakan sai tana dafa musu wani idan
basu koshi ba, nan ma Basira ta gaya ma
maigidan, yace sam bai yadda akara yi masa
girki 2 ba. Idan mutum bai koshi ba ya hkr, wai sharri ne
kawai za ace a gidan sa ba adafa
abincin isasshe. Sai mama tanayin miya ta
ajiye idan basu koshi ba sai su siyo biredi suci
da miya, anan ma ta kai masa tsgeumi yayi ta
fada wai munafinci ne... Mama sai dai ta shige
kuryar daki tayi ta kuka don bata da wanda zata gaywa,
yayai mata maganin abin sai Allah
shi yasa ta kai masa kukanta. Yawanci idan
lamarin gidan ya ishi Aneesa, in dai mama bata
da girki ranar sai ta gudu gidan Hajiya abinta
tayi kwanciyarta ta huta, saboda gidan bata
isa ta kwanta ta huta ba, abbansu na ganinta akwance
zaice mazata tashi taje ta ya auntyn
su aiki, to akan taya aikin watarana sai ta kai
kararta tace tayi mata kaza ba daidai ba. Tana
kwance bisa kujerar hajiya idanuwanta na bisa
Tv da remote a hannunta tana latse latse daga
karshe ta kamo tashar saudi qur'an, tana kallon yadda
yara kanana ke kwararo karatun
qur'ani cikin murya mai dadi ga tajweed sun
fiddawa. Tana tallabe da goshinta tana
sauraron amma idanunta a rufe, har hajiya ta
fito daga dakin baccinta, tazo gefen Aneesan ta
zauna tana cewa, jikine ko garin ne yau naji ki ba surutu
ne balle dan girkin da ake mini, me
ya faru?
MIJIN ARO 1**9
50) Aneesa ta girgiza kai tace, ba
komai

Please Login or Register in order to submit comment