Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muku ba idan bakyaso kuyi
magana sai mu canza da wani.
Muci gaba ko mu ajiyesa haka?
MIJIN ARO 1**4
Ranar litinin Mahifin Aneeesa bai barta taje
sch ba, tana gida har ya fita zuwa gurin aiki, ta
shirya kannenta suka tafi sch, yayi saura daga
ita sai mamanta a gidan. Ta tashi ta gyara
gidan tas tayi wanke wanke zatayi wankin
yaran sai maman ta hanata tace, Bar wankin
nan masa kiyi wanka in aike ki tudun wada
gurin Ummata. Aneesa da hanzarinta taje ta yo
wanka ta shirya duk da ita Allah bai yo ta mai
son kyale kyalen mata ba, ita ko kwalli bata
sawa daga vaselin sai farar hoda sukenan
kayarn shafarta, har kanwarta mai bi mata ta
fita iya kalailaita ita kam duk wannan baya
gabanta, don dai Allah ya bata kyau dan
asaline shiyasa ko tayi kwaliyya ko baatayi ba
kullum fuskarta tas zaka ganta. Maman ta
gaya mata sakon maganar kudi ce na komawa
asibiti yin hoto, shi Abbansu yayi biris da
lamarin Aneesa tace, Mama ko in ranto gurin
Hajiya tunda wata ya kusa karewa idan aka yi
biyan basukan anko nana ba sai ki bata ba?
Amma Umma sai in ga kamar kina takurata ne,

Maman tayi murmushin takaici tace, karama to
ya zatayi,? Ni nasan abinda yasa ba kya son
zuwa saboda kina ganin idan na aike ki amso
kudi gurinta ranta na baci ba wai bata da shi
bane yasa take bata rai ko bata son bayarwa.
haushi halin ko in kula da babanki ya mini shi
ke damunta tunda ta san duk abinda zan nema
gurin Abbanku baya rasa bane. bayarwa ne ba
zaiyi ba, kin ga kuwa dole uwa taji zafin ba a
kyautatawa diyarta ba$ kta kuma Hajiya ko na
ranta idan na mayar mata ba amsa takeyi ba,
shi yasa bana son zuwa, tashi dai kije gurin
umman, ki gaishesu.Ta mika mata Naira
Hamsin kudin mota ta amsa ta saka hjiba dinta
ta tafi. Tana zuwa dai2 gidan hajiya ta hangi
motar dan Hajiya da ke aiki a Abuja ya zo har
zata wuce taji shai songaitwins da matarsa ke
goyo.Alahyasaita ai tunda aka haifi Yaran take
bala-n son su, lafiyayyu. farare kyawawa da su
tamakar 'ya'yan turawa suke. Tun suna jarirai
wani zuwa da sukayi suka kwana da za su tafi
taje tayiwa Hajiya rada annne wai da su tafi da
ita gidansu ta taya. Auntyn Abuja rainonsu,
Hajiya ta dubeta Galala tace, saboda rainon su
twins zaki bisu Abuja ki bari karatunki? Lallai wannan
soyayya taki da yaran nan
tayi girma, keMa Allah ya sa ki fara da twins
din. tana jin hakan ta fyalle da gudu bata ma
tsaya taga tafiyar en abujan ba. Rokon Allah ta
dinga yi Allah ya sa taga aunty abujan aka zo,
dan taga en 2 ai kuwa tana shiga taga yaran a
cinyar kakarsu. Sallama kawai tayi a falon ta
suri daya tana fadin Hajiya wannan waye na
dauka Sultan ko Suhail? Hajiya tace kema
kenan uwarsu baki gane su balle ni ina jin
wannan ne Hassan. Aneesa tace yauwa ga
sultan kenan. Ta juya ta soma gaida uwar
yaran. dake zaune can doguwar kujera ta
amsa mata da sakin fuska, albarkacin tana son
yaranta kamar ta hadiye su, In baya ga haka
ba kowa take wa fara'a a dangin mijin nata ba,
shiya sa ba kowa ke shiri da ita ba. Hajiya
kadai take shakka kuma ita kadai ke kiransu
da sunansu na Asali Hassan da Hussain tunda
aka haife su Hajiyan tace abar musu sunan su
ita kuma uwar yaran ta. cewa mijinta wai
kauyanci ne wannan sunan yayi common da
yawa, tafi son sun unique shine ta zaba musu
sultan da suhail, kuma haka kowa ke gaya
musu. Akkala yanzun yaran sunyi shekra2 da
haihuwa. Suhail shima ya taso daga cinyar
Hajiya yana cewa Aunty nima. Ya mike

hannunwansa wai shima ta dauke shi. Tayi
dariya ta sauke sultan tace yi hkr da ma zan
dauke ka ai. Mamansu ta danyi murmushi tace
ya dauka yawo zaki tafi da sultan tunda ya
ganki Da hijab, haka suke wannan kishin idan
mai rainon su ta dauki daya shima dayan dole
ta dauke shi. ta dauki Suhail din sai sultan ya
fara kuka, haka nan ta hada su ta dauke su
tana nishi saboda yaran kosassune. kujerar da
maman su take ta akaisu ta zaunar da su tace,
ku zauna anan bari in je in kawo muku
chocolate zaku sha? Gaba dayansu suka amsa
eh, ta zo gaba Hajiya tace, Hajiya bari naeTudu
wada gidan Umma, Mama ta aike ni. Tace, to
sai kin dawo ki gaida Umma, idan kin dawo ki
biyo ta nan Yayanki na son ganinki. don tunda
suka zo yace a kiraki, yaunxun kuma ya fita
ganin abokin sa A GRA tace, bari nayi sauri in
dawo.
Tayi Rashin sa'a don bata sami Umman ba
sunje dubiya asibiti, saboda haka dole ta zauna
jiranta saobda muhimmancin sakon da zata
amsa, tunda goben Maman zata koma asibitin.
Har tayi azahar taci abincin ta dan kishingida
sai wajen 2pm sannan Umman ta dawo$ Duka
taji a gadon bayanta Umma nacewa, wacce
raguwarce ke min minshari a daki, daga ci sai
bacci, wannan ai sai ki firgita mtane da
minsharinki. Ta tash tana sosa wajen, ni wlh
kada ki karya min baya ki yiwa mijina asara,
tunda kin san nafi karfin kwartakwashin mijinki.
Haka suka yi ta barkwanci. Aneesa sai wajen
3pm ta bar tudun wada. abakin kasuwa ta
tsaya ta sayi jakar Eclairs don ta kaiwa su
Sultan da tayi musu alkawari. jikinta ne yayi
sanyi tunda taga bata ga motar su a harabar
gidan ba, ba dai sun tafu ba? kila sunje wani
gurin ne ta san dai idan suka zo yawanci
kwana sukeyi. Tana shiga Hajiya ke gaya mata
sun tafi wai Yayanta ya dawo har can gidansu
yaje akace bata dawo ba, kuma basu dade da
tafiya ba. Taja tsaki tace, Amman ai naji haushi
har chocolate din nan da nayi ma su Shuhail
alkawari saida na tsaya na siyo musu, ni na
dauka kwana za suyi, Umman ce na iske sunje
dubiya shi yasa na dade. ta mikawa Hajiya
ledar tace, ga ajiya nan duk ranar da suka
dawo ko da bana nan ki basu. Ko idan daddyn
su ya zo shi kadai ki bashi ya kai musu. tana
amsa tana cewa, oh wadannan yara da a garin
nan suke da sun san suna da uwa mai ji da su.
Tayi dariya ta mike tace, Hajiya bari in karasa

gida, zan dawo da yamma zanyi miki wani
haddadden girki da aka koya mini. tace Yau
laraba kada tayi girkin gidan nan da kenan?
tace, to shikenan. zo ga sakonkinki inji
yayanki. Tace daga kushin din can ki dauko kudi, Ta
mika mata tace wannan yace ki sayi books din
sch da kukayi magana, wannan kuma ki sayi
kayan makeup. Ta amsa tayi godiya ta kara
cewa, kai yayana da tsokana yake ni yaushe
yaga ina kwaliyya? Daga vaselin sai hoda nake
shafawa ai. Mama fada ta kama yi mata da ta
isa gida akan ta dade da yawa, tace wlh mama
Umman ce bata nan sunje dubiya, shine na
jirata. ga sakon tace in gaisheki da jikin. idan
da wata matsala ki yi mata waya$ tace kinga
ma kudi nan dubu biyar Ishaq ya gaisheni ya
bani, Ya dade muna hira yana jiranki, Hajiya
tace masa kin shiga baya nan ko kun hadu?
Tace sun tafi nima da zan tafi gidan Umma ne
naga motarsa shine na shiga gidan, kafin in
dawo har sun tafi, nima kinga kudaden da ya
bani har da books din da na fadan masa, shine
yace na fada masa sunan ya sayo min ko zai
aiko min da kudin in siya. Mama tace Allah ya
saka masa alkhairi, ya karamasa budi, nikam
Ishaq babu abinda da zance masa don ko bai
zo ba garin nan in dai zai turo ma Hajiya kudi
sai kinga nawa kason. washegari Maman da
sassafe tayi wanka tayi shirin zuwa asibiti,
tunda abbansu Aneesa ya ga tana shiri ya
soma hade rai, saboda ya san zata tambaye
shi kudin hoto, da ta ga haka sai bishi dakinsa
tayi sallama a ciki2 ya amsa, sannan daga
baya ko kallonta baiyi ba ya ci gaba da gyara
wasu takardu, ta nemi gefensa ta zauna
sannan ta sake gaida shi , ta dan dube shi
tace, daman yaune zan koma sibiti kuma zanyi
hoto daga nan, yace amma ain naga ya miki
bani da kudi. abar maganar hoton sai karshen
wata ko? Koko dole ne sai anyi hoto a haihu
lfy? Ya kar maganar a hasake idanunsa kyam a
kanta, Ta risinar da idanu kasa tace, nima da
na hkr din sai jiya Ishaq ya shigo ya bani 5k
shine zanje inyi hoto sauran kidin sai in sayi
sauran kayan haihuwar da bamu syab.
Dan Aunty.
MIJIN ARO 1**5
Ya dan tabe baki yace, shikenan Allah ya
taimakeki tunda dama kin matsu kiyi hoton, sai
kije a dawo lfy. Ta mike gwiuwa a sabule
saboda wannan halin ko'in kula da yake bata
wanda tun asalin aurensu ba haka ta saba gani ba, ita

anata hasashen idan zama yayi
zama yau da gobe ne Ma'aurata ke fuskantar
canji a tsarin zamantakewarsu ta fil azal, koko
ta gundure shi ne yake mata haka? Ita kam ta
rasa dalili, kila kuma wani abu take masa baya
so, to in wannan ne ai ta sha tambayarsa sai
yace shi batayi masa komai ba. wani tym din
idan ya kuntuka mata wani abin yaga tana
zubda hawaye sai duk ya damu yayi ta
lallshinta da bata hkr wai shima ya rasa dalilin
da yasa yake yawan bata mata rai. Ta taba
gayawa hajiyan Ishaq sai tace ta dinga
yawaita nafilar dare da tsananin addu'a insha
Allahu komai zai daidaita, shi ya sa ta kae
kaiwa Allah kukanta, ta rungumi shawarar
Hajiya shine fa wani tym ta kan ga sauyi. kafin
ya sake botsare mata, Haka dai zaman yake
yau fari gobe tsumma. sannan gashi ya sa duk
abinda aka ce kta ko Aneesa sunyi a gidan nan
yake saurin hawa kai ya zauna, ya zama Gabar
wadda bata juri zunguwa ba. tana shiga daki
ta iske Aneesa da kofin shayi tana fifitawa, ta
dubi Uwar tace, Mama ga tea din naki baki
karya ba zaki tafi? Naga kina ta sauri. Ta
mikawa Aneesa hannu tace bani to insha bana
so in makara kinsan asiboitin daga can wuce
gurin hoto gara tafi da uwri. Ta zauna ta soma
kurban tea din, Naeesa ta dubi Maman tace,
Mama kiyiwa Aisha magana tayiwa Yara
wanka ni sai inji da abin karin shirya su, tunda
ni Abba ya hanani zuwa sch idan suka tafi sain
gyara. gidan inyi wanke2 Ta aje kofin tea din tace taso
mini ita
tunda tayi sallar asuba ta bi ta nade a gado
tamkar tare da shi aka halliceta. ai dole ta tashi
ta taya ki wankansu. kema ai ba zamanki
kenan ba agida, ranar mon dole kije sch in
kuma ya hana sai in gaya ma Yayan sasa,
gaba ai da gabanta. Taje ta taso Aysha sai
zumboro baki takeyi, tazo gefen Maman Ta
zauna, Maman ta dube ta tace, ba zama zaki
ba tashi zaki yi ki yiwa Yara wanka don ni
asibiti zanje ita kuma karama aiki zai yi mata
yawa saura na dawo tace min bakiyi musu ba.
Haka aysha ta sirka ruwan wakan da zafin
gaske tana shekwa Yaran suna tsala ihu, suna
zabura saboda zafi. don taga Mama ta fita,
kuma tayi hak ne don Aneesa tayi magana su
yi fada tana jin haushin ta tasheta abarcinta,
dan ta san babu abinda Aneesa ta tsana. irin
kukan 'yan kanneta, ita kuma ta san abinda
aysha ke nufi sai kawai ta shareta ta cigaba da

aikin gabanta. Tana durkushe tana wanke2
bayan ta shirya kanneta suna daki, suna
karyawa sai ga Aysha ta fito daga dakin ABban
su da Uban kayan Wankinsa a tunanin Aneesa
yau Aysha ce zata kai masa gurin mai wanki da
guga na layinsu, har tana mamaki. Aysha da
ko bokitin ruwa bata iya daukowa awaje wai
kunya takeji ita adole ga budurwa, shine yau
sai gata da tilin daurin wanki, da mama ce ta
aiketa da an sha korafi da zumbura baki. 'wsai Aneesa taga Aysha ta dire wanki agefenta
tace, sako daga Abba yanzun zai fito zakiji
bayani. murmushi kawai tayi tasan yau itace
mai kai wankin kenan, to meye sabon abu a
gurinta, kaya ko yafi wannan zata dauka don
ita bata dauki kanta akomai ba, tunda ko ruwa
ne idan nasu ya kare kuma ba na famfo zata
fita ta debo a makwabt. Abbansu yace tunda
kin zama baiwa agogo sarkin aiki, to ga wanki
nan daga yau na daina kaiwa gugda ke zaki
dinga yi idan sun bushe ki goge su...
Ki goge da dutsen gawayi. ya ciro dari 3 ya
mika mata yace, Gashi nan ki sayi sabulun da
sitati. Ta amsa hannu bibbiyu ba tare da wani
bacin rai a fuskarta ba tace, Insha Allahu kafin
ka dawo zan wanke in goge. Adawo lfy Allah ya
bada sa'a. kafin ya fice ne ta bishi da wannan
addu'ar bai amsa ba yayi ficewarsa abinsa. Da
yake Allah yayi Aneesa mai zafin Nama kuma
sam bata da kasala, ta saba da kazar2 shi ya
sa kafin 10am har ta gama wanke2 ta share
dakin Mama da Na Abban tare da hada ruwan
girki. Ga kayan da yawa 15sets cikin ikon Allah
kafin 12pm har wasu sun fara bushewa, Allah
ya taimaketa akwai wutar nepa sai kawai ta
fara gogewa$ Tana cikin gugar ne taji bugun
gidansu ta san kannenta ne suka dawo, tana
bude musu suka rungumeta Jafar yace, Aunty
yunwa nakeji kin gama abinci? Tace naga jafar
ai na sanka chop2 ne. Sai da ta canza musu
kaya sannan ta shimfida musu tabarma a
inuwa ta xuba musu abinci suka soma ci. ita
kuma ta koma aikinta. Can taji ana knockn
kofa tace Amira je ki bude kofa kila mama ce$
A madadin Maman taga ashe kanin hanne ne
ubansu daya( matar baban sasa) yana zuwa
koda yaushe gidan shima ya zama kamar dan
gida. Ta gaishe shi yace Ina Aneesa fah? tace
tana dakinsu tana guga$ Ya karasa ciki ya iske
Aneesa, Ta dube shi tayi murmushi tace, a'a
dan uwanmu kana garin nan kuwa? ko hutu ne
ya boye ka? Yayai murmushi yace wani hutu ne

ga dan makaranta, ke ce ma yar hutu tunda
nazo gidan nan sau 2 ana ce mini kina nan
bakya zuwa makaranta. kinga ai kce 'yar hutu.
Tayi mrmushi, dole ta sa banje sch ba amma
ran monday idan ka zo kamar wannan tym in
bazaka ganni ba ina sch . Yace gaskiya ki din
daina fashi, gaki da brain amma kina son ta
dakushe ki ma 'ya'ya na asara. Ta harare shi saboda tasan
don ya
tsokaneta yace haka shi fa nan dole sonta yake
yi, ita kuma tana ba tym din luv bane yanzun a
wajenta, bayan haka ma kanin Baba hanne ne
babbar makiyarsu ita da uwarta, ko da yake ba
halinsu daya ba, kuma shi ubansu ne daya ba
wani shiri suke sosai ba da baba hannen,
tunda shi dan uba ne kuma acewarta yana
mata katsalandan tunda idan yazo gidan dole
suke aje narkewar da da sukeyi su fito rai bace
suna aikin gidan, ita ganinta yana takurawa
yaranta ne, bata san gata yake musu ba, shi ya
sa ya zame musu kadangaren bakin tulo
abarka ka bata ruwa, har suna suka saka
masa aboye da sunji sallamar sa za su ce ga
kawu sa'idawa nan, ko suce kawu takura. Ya
dan gisnte dariyar da yakeyi, saboda hararar
da Aneesa take masa yace, don nace 'ya'yana
to naki ne ke kadai, inace mu 2 zamu haife su?
Tsaki tayi kawai ta cire iron din daga wuta ta
tashi ta fice ta bar masa dakin saboda
zancensa ya bata kunya, dama wanka take
son ta shiga kawai sai ta sirka ruwanta ta
shige bayi, taga duk ayyukanta har miyar dare
ta daura. Tana fitowa tayi alwala ta shige daki,
har ya kusa gama gugar ma da takeyi, ta tsaya
sororo. tana kallonsa yayi kamar bai san shi
take kallo ba ai jo tayi yace,kin sa fa ni bawanki
zan zama idan mukai aure, shiyasa ma tun
yanzun zan fara bauta miki, ke er hutuce Tace
tym din sallah yayi a gara kaje kayi, ya karasa
goge wandon sannan Ya cire iron din ya mike
tare da zuba mata ido, yace bari inje inyi sallah
in dawo yau akwai latest labari ko ba kya son
ji? tace idan na alheri ne ina so amma idan na
yan matanka ne jami'a akara gaba da shi.
Dariya ya kama yi sosai har da rike ciki ita
kam kallonsa kawai takeyi, sai daya gama
sannan yace, Ni wlh ban taba sani ana sona
haka ba har da kishina, lallai zan zo in kama
kaina kada tsautsayi ya sa a ga ina magana da
wata ayi min bulala. Ficewa yayi ita kam ta
bishi da harara tana cewa, kishi? lallai ashe
zan wahala idan akanka zanyi kishi wanda yan

matan jami'a ke rububi. Juyowa yayi yana gab
da ficewa yace bari in dawo kema zan gaya
miki yadda ake ta rububi akanki. Kafin ya dawo
tayi sallah ta shirya cikin doguwar riga ta
zauna tana cin abinci sannan ya dawo ta na
ganin ya shigo tayi sauri mikewa taje ta kawo
masa nasa, don tasan yana iya saka hannu
yace sai sunci tare. Ita kanta yanzun a tsorace
take saboda dan yinin da ya shigo yayi yayarsa
tana iya jin haushi ko kaji wani zance ya fito.
Gaba dayansu da yara suna tsakar gida ne
sukaji sallamar mama tana ganinsa da fara'a
tace aka sagir yau kaine a gidan? Ya risina da
fara'a ya gaisheta. Yara kuma suka rungumeta
suna mata oyoyo ita Aneesa ta isa ta amshi
jaka mama tare da yi mata sannu da zuwa,
dukansu daki suka bi Maman har da Aneesa
suka bar sagir ya kelo yace, Mama ni zan
wuce, tace au zaka tafi to ka gaida gida da su
goggon da Hajiya. Aneesa ta danyi jim sannan
ta biyo shi tsakar gidan sukayi sallama ya tafi.
A daki mama take shaida mata yadda ya
kasance a sibitin, tayi hoto sun tabbatar
yanzun komai lfy tunda sungyara yaron
kwanciya. Aneesa tayi murna da jin haka don
bata son Mama ta samu matsala ko kadan.
Aneesa sun fara shirye shiryen zana xams
dinsu ta JSSce hakan ne ya sa ta zage damtse
gurin karatu da bada himma zuwa wajen sch
saboda dama ita mai himma cema shi yasa
duk wani kuskure da zatayi mata sanadin
hanata zuwa sch. Gashi a tym din cikin
Mamanta ya tsufa, dole suka raba aikin gidan
ita da Aysha ba don ayshan ta so ba, duk da
dai itama ai wannan tym din tana tausayawa
Maman wahala da take ciki.
Ranar talata Aneesa ta dawo sch daidai
gidan Hajiya ta hango motar Ishaq, kamar ta
shiga ta gaishe shi, sai dai ta wuce abinta, don
ta san in dai ba sauri yake ba zai shigo gaida
Mama balle yadda ya san bata cika lfy ba
shiyasa ko waya yayi sai ya tambayi lfiyarta,
har kude ya aje musamman gurin Hajiyarsu wai
da mama ta fara nakuda ayi maza direban
Hajiya ya kaita asibiti don baya son ta haihu a
gida kada asami matsala. Zata shiga gidansu
kenan sukayi kicibis da diyar yayar Ishaq din.
sukayi wa juna murmushi Aneesa tace kamar
fa in shiga gidan Hajiya da naga motar Yaya
sai dai na wuce$ Tace kuma shi ya aiko in kira
ki Mama tace kina sch, amma ta san kina
hanya. Aneesa taka hannunta mu koma ciki in

cire Uniform dina sai muje. in kaji kira samu ne
balle kirian irin na manya masu keta hazo
kullum. Suka fashe dariya. Doguwar riga kawai
ta saka da hijab ta so taci abinci sadiya ta
hana wai taci a gidan ay,Alh ytiakt tayi sallah
a sch. A harabar gidan suka hangeshi yana
ganawa da dafifn mutane, dattijai da matasa
masu son ganin wanda duk xuwa sai yayi da
gaske yake kwatar kansa a gurinsu, shima sai
in sallah aka kira amma duk sai ya sallami
kowa da bukatarsa da ya zo da ita, sannan
yake shiga cikin gida, shi yasa matarsa bata
bari suyi masauki a gidansu da hade dana
Hajiya, sai dai su sauka ahotel. Amma idan shi
kdai ne nan sashensa yake kwana, yafi son ga
shi ga Hajiyarsa. Allah yayi Ishaq mai jama'a
tun yana yaro.
Kitchen din Hajiya Aneesa ta nufa ta shige
ta debo abinci a plate sannan ta shiga falon, ta
iske su zaune. Hajiya na ganin ta da palte a
hannu tayi dariya taceN Hala dawowarki kenan
taje ta taso ki agida ba? Tace da kyar ta barni na
cire uniform, ta hanani cin abinci wai yaya
ishaq na kira na, kila kudi zai raba mana, ta bi
ta dameni in taho yanzun. Hajiya tace kinji
kyale wannan 'yar wautar cikinki ya dauka, In
bakuyi sa'a ba kafin ya shigo gidan nan sai an
kusa magriba. Aneesa tace, ina ce yau zai
koma naga ranar aiki ce gobe. Hajiya tace wani
wani taro suka zo aviation nasu na matuka
jirgin sama, gobe da safe ne taron a goben zai
koma, Yanxun ma da aviation din zai tafi to
jama'a sun hana shi tafiya. Aneesa tace ni na
rasa yadda suke sanin Yaya ya shigo garin
nan, kuma kowa ba zai zo haka ya tafi ba.
Allah ya karawa Yaya budi, Hajiya tace ameen,
to in bai taimakwa wanda baya da shi ba , yayi
me? wanda ka bayar shine rabonka na lahira,
wanda kaci kayi kiba idan ka mutu tsutsa ta
burge shi, idan ma baka ci ba ka tara ma 'ya'ya
da jikoki duk hakan take, yaya ma Allah ya
baka na kwarai ne za suyi maka ddu'a, shi ya
sa nake ba shi kwarin guiwar ya taimakawa
kowa ba 'yan uwa kadai ba. Yamma tayi sosai
sannan Ishaq ya shigo gidan. Ya dubi Aneesa
yace, Aneesa yaushe kika shigo, tun dazun
nace sadiya ta kiraki. tace Yaya tun tym na
shigo dan kana waje da jama'a ne, Kazo lfy? Ya
su Suhail? Yayi murmushi suna nan fly kullum
suna damuna wai su zaria wurin Hajiya ko suce
Auntyn Zaria, sun ganeki sosai Yaran nan.
Tace Allah sarki Yaya yaushe zaka kawo su?

Yace ba su ne za su zo ba, kune zan turo driver
ya dauke ku ke da Sadiya, kuna gama
jarabawa kuje can kuyi mana hutu, suka kalli
juna da Aneesa da sadiya su kayi murmushi,
saboda duniya babu gidan da suke xuwan irin
gidansa sannan babu yaran da suke so tamkar
su lashe irin yaransa don Aneesa tym din suna
jarirai har lasar Kyan kafafunsu takeyi ta tsotsi
Jajayen labbansu, ita dai jinsu take tamkar ta su.
) Ya dubi Hajiya yace, Hajiya kinji ni shiru
ko? ina gurin jama'a. Me zan samu inci anjima
idan na dawo sallah? tace ban san me kake so
ba, amma anyi birabuskon shinkafa miyar
ganye ko tuwo kake so? Yace ayi min tuwon
semo sai in ci da miyar, Yamma tayi da anyi
min kubewa danya. Hajiya tace da ka sani ka
gaya min a waya ko ka aiko amma, yanzun
ladidi ta gaji sosai tun rana take tsaye a kicin$
Aneesa tace Yaya in yi maka girkin? N iya miya
mai dadi har da tuwon, wanda kaci rannan a
dakin Mama ma ni nayi shi fa. Yayi murmushi
yace Kai Aneesa ni kam ban taba jin labarin kin
iya girki ba, nasan dai kin iya wainar flour da
shasshaka da meye ma dayan? Tayi saurin
cewa Allah da gaske nake na iya girki ka
tambayi Hajiya ma ko ita ina mata, kuma yayi
dadi. Ya juya gun Hajiya dake sauraronsu tana
mursmushi, Hajiya wai da gaske 'yarki ta iya
girki? Kada tayi min in kasa ci ta sani neman
restaurant a daren nan. Hajiya tace don iya
girki 'ya ta iya, amma tun da ka fara ko kwanto
to ba zan yarda ta yi maka ba don kada yau
hannunta yayi gardama, kace dama bata iya
ba. Yayi Murmushi yace, dama kawai bata iya
ba, amma bari tayi min ai daga gwadawa jirgin
sama ya tashi. duk sukayi dariya. Aneesa da
murnarta ta nufi kicin saboda Allah yayi ta mai
son girki ce, shi yasa a duk tym din da ta shigo
gidan Hajiya bata da tashar kallon sai ta
girke2, kuma duk abinda ta gani sai shiga
kitchen din Hajiya ta gwada, don ta san
Mamansu ba zata juri wannan shirmen ba, a
cewar hajiyace mai bata dama tayi duk abinda
take so, ko da babu abun girkin yanzun zata
tada driver ko ladidi ta aike su su siyo.
MIJIN ARO part 7
35) Ta hana shi magana
don kuwa Allah yayi
mai son yara ne. Tun tym
din da ta sami cikin
su suhail tamkar ya maida
ta cikinsa haka yakeji. Balle tym din da

akayi scanning akace
en 2 ne duk boys. Sai ya
ninka kulawar da
yake mata da ko yaya ta yi
mosti sai yayi mata sannu da tace uhum zai ce
menene ko me kike
so? Haka da aka haife su
sun sha gata iri2. Ta
dube shi tace, Captain
yanzun meye abinyi? Yace meye ko abinyi illa mu
godewa Allah da
kyautar da yayi mana. Ta
gintse fuska
gaskiyya ba zan iya
wannan wahalar laulayin ba. Ga shi na irin na su
Suhail ne tym din babu
wuyar da ban sha ba. Su 2
ina kwanciya asibiti
duka2 shekarunsu 3 ne fa,
ina laifin ma su sami shekara 5 zuwa 6. Ni
kam gaskiyya ba
zan juri wahaka ba gara
tun wuri musan
abinyi. Ya daure face
tamkar ba taba dariya ba. Ba yace me kike nufi? In
zubda gudan jinina
yabi kwararo? Sam ba zai
yiwu ba. Haihuwa da
kika ce ba zaki sake ba sai
su Suhail sun shekara 5. Kika ce zakiyi
plannin wannan kin
matsa mini ne na uarda da
yake Allah ba ayi
masa wayo ko dabara
kuma ba ayi masa dole kinga gashi baki cika
shekarun da kike so ba
ya baki cikin. Maganar cire
shi kam babu ita ba
da yawuna ba. Kuma ko da
wasa kada kiyi gangancin cire mini ciki wlh
zan dauki
mummunan mataki a kan
hakan. Likitan ya
shiga bashi baki. Pls captain
be a man, kada kayi fushi kasan halin mata
su tunaninsu
karami ne. Ka bari kuje
gida sai ka lallasheta.
Kowa zuciyarsa a kuba
suka dawo. Safeena kam tun asali ma bata so
sukayi haihuwar fari
ba da wuri ba, saboda bata

son hayaniyar
yara, sai gashi Allah ya
hada da en 2, har cewa tayi daga kansu ta gama
haihuwa, shi kuma
yace haihuwa yanzu ya
fara bayan su wasu en
biyun na nan zata kara
tace. Ba dai ita ba sai dai ya auro wata tayi ta
haifa masa yaran, sai
yace ai kuwa dai auro duk
sai ta hada da su
sultan ta rike duk zai bata
kyautar su. Sai cewa tayi wlh babu wata er iskar
da zata shigo mata
gida.....

Please Login or Register in order to submit comment