Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba dai
naji dadi ne, tace me ke miki ciwo? Ni
babu
abinda ke min ciwo, haka nan dai naji
jikina da
garin ba sayi min dadi, Hajiya ta
gyara
zamanta tace, ruwa baya tsami banza
amma ni
nasan ba ya wuce matsalar gidanku
wadda a
kullum nuna miki nake yi hkr da
addua zai iya
yiwa mutum maganin duk wata
matsala da ta
sha karfinsa, bana so ki dinga sa
damuwa da
tunani a ranki sai ki ga kinga
kankanuwarki ace

jininki ya hau. Ko ita maman ku ba ki
ga hkr
take yi ba, duk da dai dama ita mai
hkr ce, shi
hkrn ai baya baci, kuma yana da
ranarsa, ku
cigaba da hkr wata rana sai labari
Aneesa ta
sauke ajiyar zuciya tace, shin wai
hajiya idan
akayi aure saurayi da budurwa, suna
son juna
dama kiyayya na biyo baya ne idan
suka
hayyafa? Hajiya tace, sam kiyayya
bata biyi
bayan zaman masoya, in dai sun gina
soyayyatsu ne da tubali mai nagta,
kuma suna
son juna tsakani da Allah. Amma ko
da tsakani
da Allah ne suke son junan indai an
samu
wasu na shiga tsakani, in dai daya
cikin
masoyan ya bada kofar da za akawo
cikas din
abokin zamansa to tabbas zaki ga
mummunar
baraka, ta gifta tskaninsu ko da dayan
shi bai
bada kofa ta wajensa ba, sanna abu
na 2 shine
babbancin ra'ayi, in dai har za su
dinga samun
babbancin raayi na son zuciya bawai
dalilin
daya ya sabi Allah bane, to nan ma
zasu dinga
samun sabani wadda ba abinda zai
biyo bayan
sabanin sai kiyayya. Aneesa ta sake,
Jefo mata
wata tambayar, to Hajiya idan aka
yiwa mutum
kishiya dama dole sai daya ya cuci
daya, shima
mijin dole ya dinga babbanci yana
wulakanta
daya, ita wadda yake so sam ba zaiga
nata
laifin ba ko da tayi? Hajiya tace duk

inda kika
ga abokin zama 2 ko fiye sun hadu a
inuwar
mutum daya idan kika ga sun hada
kai to daga
namiji ne, idan ya kasance adali, in
kuma kika
ga ba hadin kai to ko dai baya adalci
tsakaninsu ko kuma akwai matsala
cikin
matan.
51) Amma yawancin rashin zaman lfy
kishiyoyi
abu 2 ne rashin adakci daga wurin
mijin ko
kuma akwai masu shuga tsakani.
Wadan da ba
su da burin su ga ana zaman lfy.
Akwai wasu
kuma basu ma taka kara sun karya ba,
zaki ga
sun kawo matsalolon, kamar kowa ta
dinga
ganin auro ki akayi nima auro ni
akayi. Babu
ragayya tsakanin juna ko su singa wa
juna
gani2 da sauran su dai. Shi yasa duk
rintsi ya
kasance kai ka zauna da dan uwanka
tsakani
da Allah zuciya daya. To sai ki ga
komai ya zo
maka da sauki. Aneesa ta jinjina kai
tace
wadannan matsalokin kusan sune a
gidanmu.
Shi ya sa ni insha Allah ba zan auri
saurayin da
muke son juna ba, gara a aura mini
wanda
iyaye suka kawo sukace shi suke so,
sannan
bana son kishiya don ni dai gidan mu
naga
isharar zama da kishiyoyi matsala ce
babba,
wanda in bakayi sa'a ba ciwon xuciya
sai ya
kamaka ya kasheka abanza. Ni dai
wlh ina
tson kishiya, kada Allah ya hada ni da

ita.
Hajiya tayi dariya tace ki kwantar da
hankalinki
kishiya ba komai bace face alheri, duk
sharrinta
indai zuciyarki da tsarki sai kin
gagareta, ke dai
kiyi fatan ko da Allah zai hada ki da
ita, to ya
hada ki da tagari. Aneesa taxe ni dai
nasan
Maman kullum burinta alheri ne
tunda Basira ta
zo gidan nan bata taba fadar aibunta
ba, ko
mu muma bata barin mu fada. Ko da
zatayi
mana badaidai ba, mama ta dinga yi
mana
wa'azi da nasiha kenan akan hkr. Ta
ya akayi
basira ke cin Galaba akanta gurin
Abbanmu,
duk makircin da ta gaya masa yake
dauka har
ya dinga yiwa Maman cin mutunci ko
da
yaushe tace, idan kinga haka ta faru
to
jarabawa ce Allah keyi bawansa ya
gani zai iya
yin hkr, idan yayi hkrn sai ya ga
sakyayyar
alheri a tym din bai zata ba, idan
kuma bawa
ya kasa hkr to sai ya ciga ba da ganin
ba
badaidai ba arayuwarsa, ita mamanku
hkrn da
takeyi insha Allahi zai yi mata rana,
ko mu dade
ko mujima.
52) Aneesa sun gama xams din 2nd
term
kenan, Ishaq yayi waya safeena ta
haihu twins
again. A ranaar aneesa tayi tsallen
murna ita
da hajiya aka rasa gane wa ya fi wani
farin ciki.
Ta dubi Hajiya tace, amma dai don
Allah zakije

abujan kiga 'ya biyun ko? Hajiya tace,
me zanje
nayi? Duk jama'ar da za suje basu isa
ba sai
na je? Tace Haba hajiya shima fa yaya
Ishaq
yana son yaga kinje gidansa, shi ba
wani dan
fari ba amma kin dau kunyar Maman
su sadiya
kin dora masa shima matarsa ai saita
ga
kamar ba kya sonsa ne? Tace indai sai
naje
gidansa ne zata ce ina sonsa tace, to
kada
tace, tunda ita tana sonsa ai
shikkenan. Ana
gobe suna jama'ar zaria ta isa abuja
ciki har da
Hajiya, wadda da kyar da sudin goshi
taje, don
kuwa saida Ishaq ya zo zaria yayi
lallashi
sannan taje, a cewarta bata ga dalilin
zauwan
nata ba, yara dai idan akayi arbain ai
za su zo
ta gansu. Yaran kuwa kyawaawa
tamkar su
Sultan ga shi suma sai ka sha wuya
zaka iya
banbance tsakaninsu. Su ma canza
suna
akayi. Hassana Yasmin, Hussaina
kuma Yusra.
Taron sunan ya kayatar, safeena ta
kece raini
cikin tsaddadun kaya ita da yaranta, ji
take
tamkar ta fi kowace mace sa'ar miji,
koko ita
kadai Ishaq ya mallaka a duniya,
domin kuwa
ya kashe mata kudi ita da gidanta
kamar ba
gobe, dama burinta kenan, kawayenta
na
jami'a su zo ga yadda take bushasha
agidanta. Duk wanda ya zo taron nan
sai da ya
tafi da katuwar jaka shake da abin

arziki mai
dauke da hoton twins da nasu Suhail
a kasa.
53) Aneeesa tana ajin kusa da na
karshe ne a
halin yanzun, ta zama cikakkiyar
budurwa
farace ita tas, irin farin nan mai haske,
tana da
tsayi amma bata da jiki, sai dai
fasalinta mai
kyau ne saboda kirar kalangu da Allah
yayi
mata ga yalwar gashi, kirjinta cikakke
ne ta
yadda zai dauki hankalin duk
mutumin da zai
tsura mata idanu. Shi ya sa ko da
agida take ta
faya sanya gyale, idan zata fita kuwa
babban
hjibi take sakawa. Agidan Hajiya kuwa
tunda
gidan na jama'a ne ko da yaushe bata
rabo da
Hajibinta. In dai za a aiki Aneesa to
ta dinga
cin kar da gaisuwar samari kenan. Da
suka
bata kula su. Sai suka kawo kansu
gida, da
yake Abbanta yayi nata kashedin kada
ya
ganta ta tsaya da wani namiki. Shi ya
sa ko
sun aiko bata fita, idan mutum ya gaji
da nacin
zuwa sai samawa kansa lfya. Mutum
daya ne
har yanzun suke tare da shi, shine
Sagir shima
albarkacin yana kamar dan gidan ne.
Ba a
jamza birki ba. Kuma natsattsa ne shi,
yana
gayawa Aneesa da zarar ta gama
secondary
zai aurar da ita ne. To ita abinda ke
bata
mamaki yace aurar da ita zaiyi, amma
ya
hanata tsayaea da kowa, to ko shine

zai zabo
mata mijin. Ko yana nufin Sagir kawai
zai bata
tunda da shi kadai ya kyaleta suna
tsyawa. In
dai kuwa haka ne, to ta yarda da
zabinsa
kasancewar tana son sagir din, komai
nasa
mai kyau ne, daga siffa har zuri'a mai
kyau
sannan mai ilimi ne duka biyun,
yanzun haka
ya tafi bautar kasa Abia state, a yadda
ya sha
gayawa Aneesa da ya dawo za afara
maganar
aurensu, tunda yana da tabbacin aiki
a hanni
da zarar ya dawo. Zasu iya samun
matsayar
aurensu ta bangaren Yayarsa Hanne
saboda
tun asali tana dawa da wannan
soyayyar tasu,
kullum aikinta kenan sukar aneesa a
gurin
sagir, shi kuma yana nuna mata ko
meye halin
Aneesa zai iya zama da ita, tunda
yana sonta,
can gidan su ma haka take sukar
lamarin sai
ya kasance gaba daya kannen sagir
din sun
tsani Aneesa saboda irin tarin
batancin da
takewa mata, iyayensu mata ne kawai
su ke
son wannan alaka ta Aneesa da Sagir.
54) Basura amaryar Abbansu ta haihu
kusan
shekarar yarinyar daya kenan. Ita
kuma
maman su Aneesa tana dauke da
tsohon ciki,
wanda girman cikin tamkar na en
biyu ne, gashi
tunda ta sami cikin take fama da
lararu har
cikin ya tsufa gashi ta kumbura. Har
anyi mata

gwaje2 sun tabbatar da tana dauke da
ciwon
hawan jini, wanda ya soma taba
lafiyarta.
Wannan lamarin ya tashi hankalin
jama'a
musamman iyayenta da abokan arziki
irin su
Hajiya. Ishaq kam da yaji a washe
garin ya iso
Zaria. Ya sami maman ya tsa ta gaba
da
tambayoyin shin me ke damunta take
tunani
haka har hawan jini ya kamata, gashi
zuciyarta
na neman harbuwa da ciwo. Tayi dan
murmushi tana latsa hannunta daya
daya
kumbura tace, babu abinda da ke
damuna.
Kawai Allah ne ya aiko min da
wannan larurar.
Ina nan ina addu'a kuma ku tayani.
Ya tsurawa
kafafunta idanu sun kumbura sintim
sai sheki
sukeyi. Ya numfasa yace, kafafun nan
babu
maganin da zasu sabesu? Haka ya
zauna yana
ta yiwa Mama magana ta kwantar da
zuciya.
Duk da ta boye masa damuwarta
amma ai ya
riga yasan komai, yasan irin zaman da
sukeyi
a gidan nan ita da yaranta,
musamman
Aneesa. Hajiya na gaya masa komai,
kuma ya
sha gayawa Maman duk wani abu
idan ya taso
na bukatarsu suje direct wurin Hajiya,
kada su
tambayi kowa, ita kuma Mama yau da
gobe
take dubwa shi ya sa wani tym din ko
matsalar
ta taso musu bata yarda Aneesa ta
gayawa
Hajiya, sai su hkr Allah ya kawo musu

agaji. Da
ishaq zai tafi ya bata dubu biyar, yace
kuma
idan wata bukata ta taso a gayawa
Hajiya ko
Aneesa ta gaya masa ta waya, ita ma
Aneesa
dubu 2 ya bata yace ta sayi kayan
kwaliyya. A
zuciyarta tayi dariya tace wai shi
kullum ya
bani kudi sai yace in sayi kayan
kwaliyya, ko
kuma so yake yaga tana kwaliyyar.
Cikin
Mama ya shiga watan haihuwa
shiyasa,
Aneesa ko makaranta ba kullum take
zuwa ba,
duk ranar da maman ta wayi gari ba
karsashi.
To bata zuwa, sai tayi zamanta tana
lura da
mamanta.
55) Ranar litinin Maman ta shirya ta
tafi awo
da yake asibitin kudi ne take xuwa,
kuma
babbar nurse din asibitin gidanta ba
nisa
tsakanin su da gidansu Mama, kuma
tana da
kirki har suna abin arziki da su Mama,
yawanci
ma idan Mama ta shirya da wuri tana
aikowa
mama ta zo tabi ta a motarta, su tafi
asibitin.
Yau ma mama na zuwa ta ganta waje
jikin
motarta tana jiran ta, suka yiwa juna
murmushi. Ita ta soma gaida Mama.
Maman
jafar ina kwana? Ya jikin naki? Ta
amsa da
sauki, amman yau da ciwon mara na
tashi
kadan2, tace Allah ya sauwake bari
mu karasa
asibitin sai a duba ki, ina ganin ma
haihuwa ce
tunda EDD dinki har ya wuce, kila yau

rike ki
zamuyi. Tayi musrmushi tace, Allah
yasa
haihuwarce nima in huta, saboda
yadda nake
jin nauyin cikin nan kamar an dora
min dutse,
in bacin kunyi hoton kunce min daya
ne, sai in
ce ni nauyin mutum 2 nake ji. Allah
dai ya raba
ni da shi lfy, nurse din tace ameen
maman
jafar. A asibiti anyi wa mama awo
suka ce
insha Allahu zuwa gobe zata haihu.
Amma idan
ta kai gobe bata haihuwa ba, to da
safe tayo
shirin haihuwa ta zo asibitin. Su ka
gaya mata
adadin kudin da zata zo da shi. Da ta
dawo
gida, can sasan su Hanne ta shiga ta
gaya ma
Hanne yadda sukayi a asibitin. Amma
ta iske
Halima anyo mata waya kanwar
babansu ba lfy
ba lfy sosai acan kauyen sun tafi, kila
gobe su
dawo. Hanne tace idan Allah ya
kaimu goben
ba sai ku tafi da Aneesa ba, nu kuma
ma biyo
baya idan kin haihu. Dama maman ta
gaya
mata ne, ko zata ce zata rakata, tunda
bata
san ya haihuwar zata kasance ba,
tabbas
tasan da Halima na nan tare za su tafi
ta
rakata. Da abbansu aneesa ya dawo ta
shiga
dakinsa ta gaya masa, abinda akace a
asibitin,
sai ya kama fada, ni bani da kudi
ahannuna
yanzun da zan baki gobe kije asibiti,
in banda
janyowa mutum jidali, ya za'ayi

haihiwa bata
zo ba, suce aje asibiti. Ko ko su da
kansu ne
zasu janyo haihuwar da su sa mutum
kashe
kudi, to ni bani da su, sai na sama
tym na
amsa abank.
56) Mama ta sassauta murya tace ba
wai
kirkiro mini haihuwar za suyi ba, yau
daman na
gaya maka na tashi da ciwon mara
shine,
sukace haihuwa ce amma sai zuwa
gobe,
abinda yasa suka fi son in haihu a
asibiti
saboda sunce har yanzun kan yaron
bai juyo
kasa ba, akwai hadari. Ina fatan Allah
ya kawo
mini komai cikin sauki, ta mike da
kyar ta bar
masa dakin. Da daddare duk yaranta
suna
falonta. Suna kallo sun saka film din
the
message, ta tashi tsam daga cikin
yaran ta
shige dakinta ta kwanta. Ba barci
zatayi ba,
haka kurum ta ji tafi son zaman
kadaici saboda
hayaniyasu ta dameta. Aneesa da taji
ta shiru
a dakin sai ta biyo ta cikin dakin, ta
zauna
agefen gadon da Maman take, tace
mama har
kin kwanta ne? Tace Hayaniyar ce
bana so
shine, nazo na kwanta idona ma sam
ba barci.
Aneesa ta lura maman kamar tana
cikin
tsananin damuwa, saboda zahiririn
abinda
fuskarta ya bayyanar kenan. Tace
mama hala
zuwa asibitin goben ne ya dameki
kike son

saka zuciyarki cikin tunani. Tayi
murmushinta
da ta saba tace. Babu ko daya, saboda
nasan
duk abinda Allah ya hkunta shine zai
faru
akaina. Ni rayuwarku ke da en
kannenki kawai
nake dubawa nan gaba sai inga
tamkar,
abbanku watarana zai ce ya ga za
daukar
dawainyarku. Aneesa tace, idan zaice
ya gaza
mama ba gaki ba, mu ko da ke kadai
zamu iya
rayuwa, idan yace shi ya gaza damu,
ba ga shi
kina er sana'ar zannuwa ba, kuma ba
laifi kina
dan samu, a ciki Allah zai dunga
taimakonki
kina rufa mana asiri wata rana sai
labari. Ta
sake yi murmushin tace hmmm!
Karama kenan,
tunani na kada wata rana a wayi garo
ni in riga
Abbanku mutuwa, ina nan ma ya ki yi
muku
abinda ya wajaba akansa ina ga bana
nan.
Tace don Allah ki bar fadin haka,
muna nan da
ke sai kin aurar da mu har yaron dake
cikinki.
Sai kinga 'ya'yansa, tace Allah yasa
inga yaran
naku.
57) Kinga kece Babba ki hada kanku,
duk da
Aysha butsararra ce nasan nan gaba
zata yi
hankali tasan ina ke mata ciwo,
yanzun yarinta
ce kawai ke kwasarta. Tace, yanzun
mama
goben ya zakiyi da kudin zuwa
asibitin? Tunda
Abbanmu yace baya da shi, tace Allah
zai rufa
aisiri ina ganin kiyi sammakon zuwa

wurin
Malama Maimuna ki gaya mata uzurin
da ke
gabana, sai ta juya min kafin ta hada
kudin
zunnuwan wannan wata sai ta cire a
ciki.
Anees atace, yauwa hakan za'ayi da
har na
soma tunanin gaya wa Hajiya, tunda
Ya Ishaq
yace idan matsala ta taso agaya mata
ko ayi
masa waya$ tace gaskiyya ba za a
gaya mata
ba, dawainiyar da takeyi ita da danta
tayi
yawa, sai kace sune masu alhakin
larurar mu,
haba ido ba mudu ba ne, amma yasan
kima.
Aneesa da mamanta sun kai fiye da
karfe daya
na dare suna hira da tattauna
al'amuran
rayuwar yau da gobe. Maman na jefo
mata en
nasihohi cikin hirar. Da ta fahimci
Aneesa barci
yayi awon gaba da ita sai ta tashi tayi
alwala
ta soma sallar nafila, da ta idan ta
cigaba da
adduointa, har sai da tayi raka'atul
fajr da
sallar subahi sannan ta bar abin sallar.
Tabi
duka yaran ta tashe su dan suma suyi.
Aneesa
tana idarwa ta fita ta hura wutar itace
tasa wa
maman ruwan wanka kansancewar
babu wutar
nepa. Bayan tayi wanka ta shirya tsaf!
Sannan
ta taka a hankali tayi sallama dakin
Abbansu
Aneesa, ya amsa mata, sai da ta nemi
izinin
shiga sannan ta shiga, suna zaune shi
da
Basira ta hada musu tea mai kauri ga

bread a
gefe suna sha, ita kuwa can da
yaranta ya
barsu da koko, idan ma tea za su ha
sai dai su
sha ruwan bunu, saboda ba zai ba su
madara
ba ba kuma gata nan ta ruwa da ta
gari a
dakinsa. Kai duniya ina zaki da mu?
Lahira
akwai aiki a gaban marasa shuka
gskiyya.
Haka ta fada a zuciyarta.
58) Hannun kujerar da ke gefenta ta
zauna,
sanna ta gaisheshi, da taga Basira
bata da
niyyar tanka mata sai ta soma
gaisheta,
sannan ta tanka mata. Mama ta dubi
maigidan
tace, ni nayi shiri zan tafi asibitin, don
kuwa har
yanzu ina jin ciwon marar, da wa
zamu tafi? Ya
wani dubeta yace, da wa zaku tafi da
ya wuce
Aneesa tunda naga ita ta hannun
damanki, jiya
wajen sha dayan dare na leko dakin
na jiku
kuna, kulle a uwar daki kuna
shawarwari ke
baki da abokin shawara sai Aneesa,
idan tayi
aure sai ki koma kiyi da aysha. Tayi
murmushi
tace, ko aure bai raba mu ba, mutuwa
ma zata
iya raba mu. Ta mike tsam, dama ta
dauka zai
ce Basira ta rakata ne, amma tunda ya
fad
haka ko insha Allahu da Aneesan zata
je, don
ko menene ya sameta itace zata fi
tausaya
mata. Tana shiga daki ta tarar da
aneesa har
dama musu koko, ta zuba na Mana a
babban

kofi tana juyawa da ludayi don ya
huce.
Aneesa tace mama ke da wa zakuje
asibitin?
Tace da ke ya ce zamuje. Tace da ni
kuma
mama? Ni ce zan rakaki haihuwa? To
haka
yace na dauka zai ce muje da Basira,
shine na
tambya shi, amma tunda haka ne
ra'aryinsa
sai muje da ke din, babu komi Allah
yana tare
damu. Aneesa cike da damuwa ko
tace. Sai mu
tafi din amma ko in gayawa Hajiya
ne, ko inyi
waya tudun wada. Tace ki kyale kowa
bana
son gaya musu hankalinsu ya tashi,
musamman Umma tunda ita ba zuwa
zatayi
ba, sai dai ta turo wani ya zo, kinga
sai abarta
cikin tunani, gara dai idan Allah ya
saukeni lfy
sai agaya musu hakan yafi dadi. Ta
mikawa
Mama kokon tace, ya soma hucewa
gara
kisha, ni bari inyi sauri in yi wanka
mu tafi.
Mama ta amshi kokon tana kurba a
hankali
sam bata jin dadin bakinta sha dai
kawai takeyi
don kada ta zauna cikin ba komai. Da
za su
tafi ta leka dakinsa shima yana
kokarin fitowa
ne zaije gurin aiki, tace masa zamu
tafi Allah ya
hada fuskokinmu da alheri, idan nayi
maka
wani ka yafe ni, kasan haihuwa
siradin mutuwa
ce ban sani ba ko zan tsallake.
60) Tace eh bata haihu ba, amma
muna iyakn
kokarinmu mu ga ta haihu da kanta.
Amma

idan haka bai yiwu ba dole aiki za'ayi
mata, ki
kira min babanku a wayar maman.
Zan gaya
masa halin da take ciki ne. Jikin
Aneesa nan
da nan ya shiga rawa, saboda jin irin
halin da
Mamanta tashiga. Ta kira lamabra
Abban na su
sai da ta kusa tsinkewa sannan taji ya
dauka,
sai ta mikawa Aunty nurse itace tayi
masa
bayanin komai, kuma tace ya kamata
ya zo, ya
kasance a gurin ko da za'a bukaci sa
hannunsa idan ya kama ayi mata aiki.
Yace
yana nan zuwa idan ya gama da
banki. Ciwo
yayi wa Maman tsanani tace a kira
mata
Aneesa babu yadda za suyi, sai suka
lullubeta
sannan suka kira Aneesan, tana
shigwa taga
halin da Maman ke ciki sai ta soma
kuka ta
rike hannuwan Maman tamau. Mama
tayi
magana kyar, karama har yanzu
Abbanku bai
zo ba ko? Tace, na kira shi sun yi
magana da
Aunty nurse yace yana bank ne,
amma zaizo,
to yanzun na sake kira wai wayar
akashe ta
ke. Maman tayi murmushin nan nata
wanda
yawanci idan abu ya bata haushi a
madadin ta
nuna jin haushi, sai dai kaga tayi
murmushi
kawai, tace. Na so ya zo mu gana
amma kila
Allah ba zai ba shi iko ba, ni na san
da wuya
zan haifa abinda ke cikin nan nawa,
kila Ajali
na ne na kumsa, ko da bamu gana da

Abbanku
ba da sauran jama'ar gida duk ki gaya
musu
na yafe musu ni su yafeni. Allah ya sa
na roki
abbanku gafara yace ya gafarta mini,
ki rokar
min su Umma gafara, sannan ki
cigaba da hkr
da kannenki. Ku hada kanku.....(Cryi
ng) Allah
yayi muku albarka ya kare ku a duk
inda zaku
kasance. Hawaye ya gangaro ta gefen
idanun
Maman, Aneesa kuka sosai takeyi, ta
sa hannu
ta goge wa maman hawayenta tace,
Insha
Allahu kina tare da mu mama, ba zaki
mutu ki
barmu ba, idan kika mutu waye
gatanmu, waye
zai kula da mu kamar ke, ba zaki
mutu ba
mama. Ta sake kankame hannun
Maman tana
kuka. Maman tace, kuyi hkr Allah
shine
gatanku, zai share muku hawaye fiye
dani,
rashi na ba zai nakasa rayuwarku ba,
Allah zai
kasance tare da ku....
61) Aunty Nurse ta budo kofar dakin
ta dubi
Aneesa tace, haba aneesa ya zaki
shigo ki kara
tayar mata da hankali kina koke2
muna kokarin
ganin jininta ya daidaita, amma zaki
sa ya kara
hawa. Aneesa tace maganar mutuwa
take mini
shi yasa nake kuka. Aunty Nurse ko
mutuwar
zatayi, tace sanin gaibu ai sai Allah. Ki
kwantar
da hankalinki Insha Allah ba zata
mutu ba zata
haihu lfy. Yanzu ki koma can gida ku
taho da

wani babba tunda mun sake kiran
wayar
babanku akashe take, gara wani cikin
yar
uwanku ya zo kusa, ba ke ya kamata
kina tare
da ita ba. Gidan kanwar maman shine
mafi
kusa da asibitin, don mai mashin
Naira ashirin
zuwa talatin zai kaita, shi yasa tayi
shawara
zuwa ta kirata tunda neman na
gaggawa ne.
Tana yin sallama a tsakar gida ta
ganta tana
yanka alayyahu, sallamar Aneesa
kawai ta
amsa tace, hala yaya Fatima ta haihu
ne? Don
wlh cikin satin nan kusan kullum sai
nayi
mafarki da ita, yau da na tashi nake
gayawa
Babansu, khalifa yace idan na gama
abin da
nake inje in ganta ko hankalina ya
kwanta,
yanzun haka azhar nayi da zan tafi.
Aneesa
tayi murmushin yake tace, bata haihu
ba,
amma tana asibiti ne zata haihu,
shine akace in
in gaya miki mu tafi, kila ma aiki
za'ayi mata.
Salati ta saka, hakan ne. Ya fito da
uwar
gidanta tace, Maman Nana me ya faru
naji kina
salati. Ta gaya mata abinda ya faru,
ita ma ta
jajanta sannan tace, yi ki shirya ki tafi
barin in
karasa girkin, miko min wayata gata
nan da na
tashi na barta, in kira baban halifa
inshaida
masa. Kuyi ku tafi ko me kenan ki
kirani a
waya nima da na kammala girkin zan
biyo ku

asibitin. Suna isa asibitin Aneesa ta
nufi dakin
da Maman take sai taji kofar a kulle,
kuma ba
ta jiyo salatin da tafi ta bar maman
nayi ba, a
zuciyarta sai tayi tunanin ko har sun
tafi da ita
dakin yin aikine. Ta kwankwasa ofis
din Aunty
Nurse ta shiga ta zauna ta ganta ta
tallabi
kuncinta da hannu biy2 da ganinta
tana cikin
damuwa sosai.
62) Tana ganin Aneesa ta sauke
hannuwanta
daga tagumi tace, Aneesa kin dawo?
Da wa
kuka zo? Tace da kanwar mama ne.
Abbanmu
ya zo kuwa? Tace bai zo ba ina ta
trying no
amma har yanzu a kashe take. Muje
inga ita
kanwar Maman. Tace naji dakin da
maman
take a rufe, an tafi da ita dakin tiyatar
ne? Tace
eh an tafi da ita, muje takunnan inga
ita
kanwarta din. Kiran maman nana tayi
office
dinta, ban san me ta gaya mata ba,
naga ta
fito a rude tana kuka nayi saurin biyo
bayanta
nace, maman Nana me ya faru? Mama
ta rasu
ko? Ta ruko hannuna tace, Aneesa sai
dai muyi
hkr sunyi iya kokarinsu Allah bai ba
su sa'a ba,
don ba'a kai ga shiga da ita dakin
tiyatar ba
Allah yayi mata rasuwa, tunda sun jira
Abbanku
bai iso ba, yanzu kawai tafiya da ita
zamuyi a
motar aunty nurse. Aneesa jin
numfashinta ta
tayi yana neman daukewa, nan da

nan jiri ya
kwasheta ta tafi yuwww! Zata fadi
maman
Nana tayi yi saurin tallabota ta zaunar
da ita
bisa benci. Aneesa ta soma kuka tana
surutai
wadanda za su kaita ga sabon Allah.
Maman
Nana ta shiga yi mata fada, haba
Aneesa kowa
ma mutuwar nan ita yake jira ko kinfi
Allah
sonta ne da ya bamu aronta yau ya
amshi
abarsa. Ta zubo da hawaye tace,
maman nana
kin fi kowa sanin halin da muke ciki,
mama na
raye ma mun shiga halin garari balle
ta kasa ta
rufe idanunta. Tace mutum baya da
wani gata
sai Allah, shine gatanku babu
mahalukin da zai
zulunce ku sai Allah yayi maganinsa,
ita dai
tata ta kare. A bayan motar Aunty
nurse aka
saka gawar Mama tare da Maman
nana da
wata nurse, Aneesa da Aunty nurse
suka
zauna agaba. Sun baro asibitin da dan
nisa ne
Aneesa ta hango motar Abbansu ya
taho
asibitin, sai taji haushinsa ya kamata
gani take
ma rashin zuwansa akan lokaci shine
yayi
sanadin mutuwar mamansu, don da
ya zo a
tym da ake neme shi ya sa hannu,
dan anyi
mata aiki, amma don kada a dameshi
da kira
ma sai ya kashe wayarsa, ya kyaleta
cikin
azabar ciwo har tayi ajalinta.....MIJIN ARO part10
63). Maman Nana tace,
Aneesa waccan ba

motar kamar ta abbanaku?
Ta dan dubi motar
da jajayen idanunta tace,
ba ita ba ce. Maman nana ta gano haushin
Abban nasu takeji shiya
sa tace haka, sai tace ki
kira wayarsa idan
shine kice mun dawo gida
ya dawo can ya same mu, kada ki gaya
masa abinda, tayi
murmushi irin na mamansu,
murmushin bakin
ciki tace, idan yaji abinda
ya faru zai damu ne? Wannan mutuwar fa mu ta
shafa. Maman nana
tace ya isa irin wannan
shirmen naki, kina nufin
kin fishi sonta ne? Aneesa
tayi en danne danenta na karya tace
wayar sa ta ki shiga,
tana kallonsa ya mike
hanyar asibitin. A kofar
gida suka iske baban sasa,
maman nana ce ta karasa suka gaisa tayi
masa bayanin abinda
ya faru, iya rudewa ya
rude ya kama salati da
surinsa ya shiga cikin gidan
ya sanar musu, nan da nan mutuwar tayi
tambari a unguwar,
dama Aneesa tayi waya
tudun wada ta gaya
wa su Umma, su Aneesa na
isowa en uwan maman suka iso a motoci
maza da mata.
Abbansu Aneesa ma sai
gashi ya dawo jikinsa
a mace saboda jin mutuwar
nagartacciyar matarsa. Aneesa bata taba
tunanin abbansu
zaiyi kuka don mama ta
rasu ba, amma sai ta
ganshi yana kukan
hawaye wasu na korar wasu. Ba a bata tym ba aka
shirya maman aka
sallaceta aka kaita gidanta
na gaskiyya.
Aneesa tana can dakin
maman kwance cikin bargo saboda zazzabi ne ya
rufeta. Ta nemo
layin Hajiya ta gaya mata,
kuka taji Hajiyan

nayi hadi da salati, daga
nan ta kira Ishaq shima ta gaya masa, shima
ji tayi ya saka
salati yace, what Aneesa!
Mama ta rasu? Kada
ki gaya min shirme, ko dai
babyn da ta haifa ta rasu? Ta sauke ajiya zuciya
irin na wanda ya
sha kuka, tace wlh mama
ce ta rasu har an tafi
kaita ba'a dawo ba. Ta
wayar taji faduwar tasa wayar, hakan ne ya nuna
mata shiga halin
rudani. 64) Ta koma ta kwanta
hawaye na ci gaba da
bin kuncinta, tabbas ba ita
kadai tayi rashin
Mama ba, Ishaw ma yayi
babban rashi saboda yadda yake ji da mama,
tamkar hajiyarsa,
wajen shawarwarinsa
kuma tamkar yayar sa ta
jini yake daukar
shawararta saboda yace duk
shawarar da ta ba shi idan
ya bi ko da
zuciyarsa ba so, daga baya
yana ganin anfanin
abin. Ita kanta Hajiyarsa cewa take shi da
mama ba'a sanin cikinsu,
kuma hakan ne. Don
ko matsala ce da shi direct
yake xuwa ya
gayawa mama ya nemi shawararta haka za su
kasa su rufe Hajiya bata
sani ba, har sai anyi
maganin matsalat, wani
tym din ba idan ba
dalili ba Hajiyar ba ta ma sani, don ko lokacin
aurensa da safeena da aka
sami matsala, da
shawarwarin mama yayi ta
anfani har Allah ya
ba shi sa'ar auren safeena sai ga shi ashe da
rabon 'ya'ya har an fara da
biyu2, ba'a ma san
me gaba zata haifar ba, shi
yasa lamarin aure
ba'a son mutum ya ja tunga da yawa, ko ayi
ranka babu dadi. Da Hajiya
da Ishaq kusan a
tym daya suka iso Zaria, shi

jirgi ya biyo zuwa
kaduna, daga kd direban abokinsa ya dauko
shi daga airpoart zuwa
zaria, ita kuma safeena
gobe driver zai taho da ita
da yaran. Hajiya
kuka ta dinga yi da hawayenta saboda rashin
Mama da sukayi, haka ta
dinga fadan
kyawawan halayyanta
wanda kowa ya sani,
wasu ma sai a tym dine ake tuna su, dama
haka ake so ko bayan
baka a fadi alherinka,
mama kam ta sami yabo
daga bakin jama'a na
kuda ita da na nesa. Hajiya ta tambayi en
uwan mama da suka cika
dakin inda Aneesa
take, suka ce tana cikin
dakin baccin maman
akwance. Ta mike ta shigo dakin ta zauna
gefen Aneesa itama sai
tashi daga kwance
suna kallon juna suka
soma kuka, dole Hajiya
itace mai karfin halin da ta dinga lallashin
Aneesa tare da gaya mata
maganganu masu
sanyaya rai da karfafa
zuciya. Da kika rasa
Fatima ba wai kin rasa jin dadi da gata gaba
daya bane, ni din nan insha
Allah zan maye
miki gurbinta, zan zame
miki uwa da uba, duk
wata damuwarki ki gayan min, insha Allah zan
share miki hawayenka. 65 IS A BLANK PAGE 66) A falon
Mama ta same
shi, shi kadai ne a
falon yana sanye da wani
yadi mai dan karen
kyau, kalarsa dark blue,
shi ya sa ya fito da zallar kyan Ishaq da yake
fari ne har yafi
Aneesa haske, ko da yake
kalar jikinsa na en
hutu ne, luf luf kamar jikin
mace haka yake, ga gashi nan en kanana
kwance a jikinsa,
gaskiyya Ishaq mai kyau
ne ga tsafta koda

yaushe tas2 zaka ganshi,
kamar farar takarda, lallai dole matarsa tayi
kishin abinda don ta
san mijinta mai kyau ne,
kuma irin mazan nan
ne a tsaye masu shegen
kwarjini a duk inda suka shiga, ita kanta tasan
yana da farin jini
don a tarihin soyayyarsu
tayi gwagwar maya
da en matansa da suke
rububin sonsa, balle shi dama tun asali
rayuwarsa dan

Please Login or Register in order to submit comment