Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokaci ba suka tafi sae da
suka fita gari sossae sannan suka yanke daji ……sunyi kusan tafiyar Awa daya
sannan suka isa bakin wani burtu dake gefen wata katuwar kuka……

Tun daga waje suke jiyo ihun mace ……hajiyar ta kalli Fadila tana fadin "Ki
kiyayi bakinki Fadila idan mun shiga ,ina sane sarae baki da kunya to wallahi
wannan mutumin keras yake jira ya wulakanta mutun ……"

Turo baki tayi tana fadin "To ni hajiyarmu ina ruwana dashi ……"

"Na dae gaya maki ki kiyaye sosae……"
Fitowar matar dake ciki ya sasu tsaida maganar da suke ……Sae da suka bar hango
matar sannan suka shiga tare da aje takalmansu a bakin burtun ba tare da sallama
ba ……Dan tsamurmurin tsohone fuska cike da furfura gashi bakikkirin sae Uban

wari yake ……

Yafi minti Talatin yana kallon fadilan sannan ya hade miyau ya juya ga hajiya
dake zaune tana kallonshi ……katon bakinshi dake cike da algae ya washe yana
fadin " Shegen yaro ya hanaku sakat Shafa'u……"

Gyada kai tayi tana fadin "Kwarae kam boka……"

Wata katuwar tukunya ya fito daga bayanshi ya aje gabanshi yana yan surutai
har tsawon minti goma sannan ya dago yana fadin "Shegen yarone mai tsabar riko
da addini ba'a zaune yake ba, uwa uba ruwan ganyen magarya shi ya zame ruwan
wankanshi ba lalle bane asiri ya kamashi ba ……"

"Haba boka akwae wanda ya gagareka a duniyar nan ……"hajiyar ta fada tare da
hade hannunta guri guda

Dariya ya sake yana fadin "Ai Allah baya bamu sa'a akan muminan bayanshi sae
dae idan yana cikin kaddararsu shine sae ya ara mana dan lokaci kadan akansu
amma shi wannan shegen yaro ko kadan baya sakaci da addininshi ……Hajiya Shafa'u
yarinyarki ta fitar man daga burtu……"

A Rude ta kalli Fadilan,saboda sanin halinshi da tayi sam baya da imani ko
kadan duka ta kai mata da karfi tana fadin "Boka ka yafe mata ,ke kuma dan
ubanki tashi ki koma mota mara kunya……"

Tabe baki tayi ta mike ta bar Burtun, Boka kam tun da ta mike ya raka kugunta
da kallo sannan ya juyo yana kallon hajiyar da har yanzu tana rude "Ki shigo
daga ciki bukatarki zata biya ……"ya fada yana matse kafafuwa

Babu musu ta mike ta shiga inda ya sa jan labule ya katange ,shima ya bi
bayanta ……Sae da ya gama lalata da ita sannan ya dauko wani karamin zobe ya mika
mata yana fadin "Komae yayi Shafa'u, ki bawa diyar taki wannan zoben ta aje sae
tsakar dare ta tashi ta kalli yamma ta daura zoben saman hannunta na haggu
sannan tace Zoben zalleni jeka zuciyar Abdulmaleek ka hana mashi sukuni har sae
yazo gareni ……idan har taga zoben ya bace to tabbas zaizo gareta a ranar idan
kuma zoben bai bace ba to aikin baiyi ba sae ku sake dawowa a canza wani salon …
amma a zahiri akwae yarinyar dake cikin zuciyar tashi wadda kuka kawo kwanaki
aka ma wannan aikin…… to ita yake so sossae idan asirin shi bai kamashi ba, to
ita zamu sakawa hauka ta shiga duniyar ta yarda bazai iya rayuwa da ita ba…"

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

[5:10AM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣3⃣

_Haske Writer's Association_*I love you din banza ki daina astrayed kanki baby rapidly da na
bar novel din kin barni……_🌹*

Dan jinjina kai tayi sannan ta karba ta fita a mota ta iske fadilan tana chat

abunta sae da ta zauna sannan ta harareta tana fadin "Ba kyajin magana ko ,idan
da kin ja mana bala'i fa……?

"Yo hajiya mayan kallo ne ya wani kurawa kirjina ido sae kallo yake sakaran
bai ma san duk ciko bane……"ta karashe maganar tana rufe baki

"Mtsew shine sae ki hararashi kuma to wallahi ki kiyayi wancan mutumin ya wuce
duk yarda kike tunani……"

Ko da suka koma gida zoben ta bata tace tayi amfani dashi kamar yarda boka ya
mata bayani……

《》《》《》《》《》

Dan karamin tsoki ya sake ganin turawan da yan mata yan kasar nigeria dake
yawo a harabar hotel din wani uban Feelings ya taso mashi ……Ga mace har mace
amma babu amfani "Wallahi na gaji ……"ya fada tare da dunkule hannunshi guri guda

A hankali ya sauka harabar Hotel din gurin wata da ke ta zaune kusa da ruwa da
alama yar nigeria ce ……kusa da ita ya zauna tare da mika mata hannu ……

Kallon uku saura kwata ta mashi sannan ta yatsina fuska tana wasa da ruwan
dake gabanta ……

Da yake dan duniyane bai bar gurin ba sae da ta saki jiki dashi sossae har
tana fada mashi sunanta raliya ita yar kaduna ce karatu ya kawota india ……sossae
suka hau fira har ta kaisu da shiga room din da take zaune ……Sae da suka shege
ayarsu sannan ya fito ya shiga asibitin gurin Safeena ……

Lokacin ta har fito daga dakin da ake treating dinta tana zaune tana jiranshi
……Da sauri ya karasa kusa da ita tare da rungumota yana fadin "Sorry baby
wallahi chocolate naje samo maki kuma babu masu dadi……"

Dan murmushi tayi tare da mikewa tana fadin "Is Okey ……"

Shafu fuskarta yayi yana fadin "Ya jikin naki baby? ya rage sossae……"

Dan girgiza kai tayi a hankali idonta ya ciko da kwallah ta kasa magana ……deep

kiss ya mata a lips yana fadin "Sorry karki yi kuka kin ji ko ……Very soon zaki
samu sauki……"

Yana rungume da ita har cikin dakinsu sae da tayi wanka sannan ya kawo mata
abinci ya aje ya fita yana fadin "Make sure kin ci sossae baby yanzu zan dawo
nima ……"

Dan girgiza kai tayi tare da daukar wayarta ta kira granny lokacin suna zaune
da Maleek din yana mata bayanin wani magani daya karbo ……Maleek din ta kalla
tana fadin "Safeena ce bara na dauka……"dan girgiza kai yayi tare da maida
hankalinshi gaba daya ga granny din……

"Menene Safeena daga daukar waya sai kuka koma……"Granny ta fada cikin sanyin
jikin

Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sake tana fadin "Granny harda tsutsa yau da
naje asibiti……"ta karashe maganar cikin wani irin kuka kamar ranta zai fita

Shiru granny tayi tana maimata addu'a a ranta bata so ta karyawa Safeenar
guiwa ita kanta idonta ya ciko da kwallah a hankali ta mikawa Abdul Maleek din
wayar don ta tabbata bara ya rasa abunda zai ce mata ba ……ita kam da ta kuskura
ta furta kalma daya to ta tabbata da kuka zata fito……

A sanyaye ya karbi wayar tare da kangawa a kunne ……har lokacin kuka take kamar
ranta zai fita lokaci guda yaji zuciyarshi na bugawa da karfi da ace zai iya
dauke ciwon ya dawo jikinshi babu abunda zai hanashi yin haka ……

"Safeena……" ya kira sunanta karo na farko a rayuwarshi ……Dan sassautawa tayi
da kukan jin muryar Abdul Maleek din

"Safeena ko wane bawa da yarda Allah ke tsara mashi rayuwarshi wani ya kanyi
rayuwa cikin jin dadi daga farko sae a karshe Allah ya sauya mashi da
wahala ,wani kam yana tashi cikin tsanin rayuwa daga karshe Allah ya sauya mashi
da farinciki ……Safeena ki dauka wannan itace kaddararki ba kuma dan Allah baya
sonki ya daura maki ba sae don ya jaraba imaninki ……"Shiru yayi yana sauraren
yarda take fitar da wani irin kuka

"Dan girman
batayi shirun
irin haka,Zan
yarda bara ki

Allah ki bar wannan kukan Madam……"ya fada muryarshi na rawa , jin
ba ya sashi fadin "Wae meye amfanin jabir da zai barki kina kuka
zo Madam wallahi baran juri kukanki ba ni zanzo na kula dake ta
samu lokacin da zakiyi kuka ba……"

Cikin kuka tace "No Maleek muma sauran kwana biyu mu dawo ……"daga haka ta
yanke wayar

Shigowar JB ce ta sata juyowa a hankali tana kallonshi ……Zaro ido yayi da
sauri yana fadin "Meye haka nake gani Baby……?

Inda taga yana kallo nan ta kalla……irin tsutsotsin dake fitowa daga kasanta ne
suka gangaro kasan kafafuwanta ……azababben kuka ta sake tare da kifa kanta saman
gadon ……

"Kai wallahi baran iya……Tsutsa fa Safeena ke fitowa daga jikinshi ……Kai Bata
yiyuwa wallahi Ina Sonki Safeena amma har ga Allah baran iya rayuwa dake ba da
wannan abun a jikinki ……zan bayar da ko nawane idan mun koma wani yazo yayi
jinyarki amma bani ba……"

Da sauri ta dago tana kallonshi da rinannun idanuwanta ……kafada ya daga yana
fadin "Yeah Safeena ina sonki amma baran iya rayuwa dake ba a haka ……ni zan biya
kudi wani yazo yayi jinyarki harki warke baby ……Sorry……"

Bata ga laifinshi ba har ga Allah sannan ta san granny kadae ke iya jinyarta a
haka ……Wasu hawaye suka zubo mata data tuna cewa yanzu tsofa ya zowa granny ba
komae zata iya mata ba a rayuwa ita kanta granny tana bukatar Kulawa a yanzu ……
Maryam fa ……Runtse ido tayi gam tana girgiza kai ……

《》《》《》《》

Karfe biyu Hajiya ta tada Fadila tare da bata zoben ……a hannun haggunta ta
daura sannan ta kalli yamman tayi kamar yarda boka ya fada amman zoben still na
hannunta bai bace ba ……

Kallon hajiyan tayi tace "Hajiyarmu kinga bai bace ba fa……"

"Ki sake gwada wa mana kila ba yi daya yake bace wa ba……"hajiyar ta fada kamar
bata so wani yaji abunda take fada

Cikin sanyin jiki ta sake maimaitawa amma still zobe be bace ba ……kusan kwana
sukayi suna abu daya amma zobe na nan daram ……kusan asuba fadilan ta kalli
hajiya a hasale tana fadin "Wannan munafukin bokan karya yake babu wani abunda
zai iya……"

,"Uban wa yace maki bara ya iya komae ba kaji mara kunyar yarinya fada
man,uban,wa ya hada auren duka iyayenki idan bashi ba?wallahi ki kiyayi bakinki

……"itama ta fada a hasale don ko kadan bata kaunar ace bokanta bai iya aiki ba……

Tsaki fadilan ta sake sannan ta bar dakin gaba daya ……Falo ta koma ta kwanta
cikin mintuna kadan wahallen bacci ya saceta ……ko sallar asuba ba tayi ba har
kusan karfe 11 sannan ta mike ta koma dakin hajiyar tayo wanka ta fito tayi
breakfast……

《》《》《》《》《》

Tunda JB ya gane raliya bai kara kwana daki daya da Safeena ba ……sannan ko ya
shigo dakin ya dinga dode hanci kenan wae wari dakin keyi ……Tun bata jin haushin
abun har ta fara ……Saboda dae dae gwargwado tana kokarin gyara jikinta duk da
abunda ke fita ……

Sam ita bama taga amfanin shigowar tashi ba tunda ba wani abu yake tsinana
mata ba komae ita zata tashi da kyar tayi abunta bata jiranshi……

Tana kwance kalabar da Maryam ta mata kafin so zo ya shigo rike da leda a
hannunshi daga bakin dakin ya tsaya yana kallonta "Baby ki shirya gobe zamu
wuce……"

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[9:05PM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣4⃣

Dan kallonshi tayi ta cikin mirrow ta watsar sannan ta cigaba da abunda take ba
tare da ta amsa ba

"Wae baby sae wani sha man kunu kike ko nayi laifine?ya fada tare da langwabe
kai yana kallonta

,Tabe baki tayi tana girgiza kai a hankali sannan ta mike tsam ta koma gefen
gado ta zauna tana latsa wayarta……karasa shigowa dakin yayi ya tsugunna gefenta
yana bata fuska kamar yaga kashi "Sorry baby wallahi ina sonki matsalar daya ce
baran iya zama dake ba a haka ,dan Allah ki gafarceni idan munje gida zan samu
wani na biyashi kudi yayi jinyarki har ki warke na tabbata granny barata iya
jinyarki ba tunda tsofa yazo haka Abba shima namijine zan samu wanda na aminta
dashi sae na maki saki daya na bashi kudi ya aureki yayi jinyarki harki warke
sae ya sakeki mu mayar da aurenmu ……"

Binshi tayi da ido lallae JB wawa ne na karshe a tunaninshi wane sakarae zai
aureta a haka har ma yayi jinyarta ta warke sannan ya saketa kamar wani wawa……

Hannunta ya kamo duka biyun "Kiyi hakuri baby wallahi ba yarda na iya ne bana
kaunar jini bare wanda ke fita da tsutsa,Na yarda zan kashe ko nawane don ayi
jiyarki baby ki dawo gareni……"

Har lokacin kallonshi take cike da mamakin maganganunshi a yarda ta fahimta
sam JB ba karamin wawa bane a tunaninshi ita zata yarda idan ta warke ta dawo
gurinshi ……nadamar aureshi ta,zo mata ……Cikin dakewa ta gyada kai alamun ta
yarda da zancenshi "Amma Jabir wa kake tunanin zai aureni a haka?

Yar dariya yayi "Gasunan da yawa baby ,babu abunda kudi bara suyi ba……Ko
wannan,driver naki ai na tabbata zai yarda yadda naga ya damu da rashin
lafiyarki sannan uwa uba ga kudin da zan bashi ……amma dan Allah karki fadawa
Abbanki ni nasan yarda zan ce mashi ……"

"Abdul Maleek kake nufi?……ta tambaya tana gyada kai tare da kura mashi ido

"Eh shi mana ,na tabbata zai iya jinyarki yarda ya kamata na yaba da
kulawarshi……beside ma 10m zan bashi yayi jinyarki sannan nan na kara mashi 10m
tare da gidana dake GRA ya sakeki bayan kin warke……yayi ko?

Juyar da kai tayi sau biyu bata da tabbacin Abdul Maleek zai yarda ……koda ya
yarda ya aureta ta tabbata bara ya saketa ba don ta warke ……Gyada mashi kai tayi
alamun ta gamsu

《》 《》《》《》

11:46am Dae dae suka gashi cikin garin katsina gida Abba yace a wuce da ita
amma sam tace gidan granny take so , Abban cewa yayi a wuce da ita gidan granny
gashinan zai zo a bakin kofar gidan suka iske maryam har ta rigasu zuwa ,da
murnata ta bude motar ta kamo Safeena tana tambayarta ya jikin

Tabe baki tayi tana fadin "Ke ba sauki……"
Ahankali ta gyada kai jikinta a sanyaye sannan ta kamata JB na bayansh har cikin
gidan ,A falo suka iske granny kwance saman doguwar kujera bata jin dadi tana
ganinsu ta mike da fara'a tana taba hannu "Maraba da yan tafiya,ai ban dauka da
wuri zaku iso ba……"

Zama tayi kasan carpet tana fadin "Maryam taikaman da ruwa please……" babu musu
ta mike da sauri ta bude fridge ta dauko masu bottle biyu tare da cup ta aje
daya gaban JB sannan ta dawo ta zauna kusa da Safeena tare da tsiyaya mata ta
mika mata tana fadin "Sannu besty……"
Suna gaisawa da granny Abba ya shigo Abdul Maleek ya kawoshi ……Hannu ya mikawa
JB din suka gaisa sannan ya juya ya gaida hajiya tare da mata ya jiki Sannan ya
juya gurin Safeena "Safeena ya jikin……"

Bata fuska tayi tana fadin "Abba wallahi ba sauki kamar kara man ciwon akayi da
naje can……"ta karashe maganar murya na rawa

"To yi hakuri Allah zai baki sauki kin ji ko "ya fada cikin sigar lallashi
,sannan ya juya gurin JB yana fadin "Jabir ya hanya?

"Lafiya lau Abba mun sameku lafiya……"ya fada yana kallon Maleek da ya shigo
lokacin Hannu Maleek din ya mika mashi suka gaisa sannan ya matsa gurin granny
tare da dukawa yace "Hajiya ya karfin jikin……"

"Baka da kunya Abdul Maleeku jiya ya mukai da kai da safe ……"ta fada tana
hararanshi

,Satar kallon Safeena yayi sannan yace "Ayi hakuri tsohuwa……"

"Haba wallahi zaka sameni ne ……"ta fada tana gyada kai ,maryam tayi dariya
tana fadin "Haba granny dan kinga mutane zaki dinga daga mashi murya Abdul
Maleekun ki fane ……" dariya Abba yayi sannan yace "Ka dauko man wayana ……?gyada
kai yayi sannan ya mika mashi tare da zama kasan carpet ya lankwashe kafa ……

Cikin Sanyin murya JB yace "Abba dama akwae maganar da nake so muyi da kai
……"ya karashe maganar yana satar kallon safeena wadda itama shi take kallo tana
son taji me zai fada

"A a ba komae Jabir ina jinka……" Maleek ne da Maryam suka mike zasu fita Abba ya
dakatar dasu "ku zo nan Abdul Maleek damu da ku duk dayane……" Babu musu suka
dawo suka zauna

Cikin ladabi da sanyin jiki yace " Abba dan Allah ka gafarce akan abunda zan
fada……" Sosae jikin Abban yayi sanyi yace "Bakomae Jabir ina saurarenka……"

"Abban tun lokacin da Mummyna ta samu labarin Safeena bata lafiya ta kafe dole
sae na rabu da ita a cewarta baran iya kula da macen dake dauke da wannan ciwon
ba ……Abba yanzu maganar da nake jiya ta kirani tace idan ban saki Safeena ba
zata tsineman Albarka ,wallahi na rasa yarda zanyi da rayuwata har ga Allah ina
son Safeena amma mummyta ta dage akan sae na rabu da ita ……Babban abunda nake
tsoro tsinuwar da tace zata man na tabbata zatayi ……"

Sanyaye Abba yace "Uwa ta wuce yarda kake tunani Jabir tun ,lokacin da ta nuna
rashin amincewarta da auren ya kamata kazo ka fada man ,Jabir tsinuwar Uwa ba
abun wasa bace ka kiyayeta ,Duk abunda mahaifiyarka bata so ka kiyayeshi domin
samun albarkar rayuwa……har ga Allah bazan zargeka ba kayi man halacci sossae na

aurenta da kayi ,Ni kaina mahaifin Safeena na yarje maka daka saketa yanzu Idan
matarka ce bayan ta warke zan sake baka ita Jabir ,Allah yasa hakan ya zama
Alkhairi sannan Allah ya albarka ce ku baki daya……"

A sanyaye ya fito da takarda ya aje gaban Abban sannan ya fita falon da sauri
yana dafe kai kamar mai shirin faduwa "Jabir kabi a hankali karka fadi ……"Cewar
Abban ganin zai fadi ,sannan ya kalli Abdul Maleek yana fadin "Taimaka Abdul
Maleeku ka maidashi gida kada yaje wani abu ya sameshi a hanya ……"Mikewa yayi a
sanyaye ya bi bayanshi

Abban ya juyo yana kallon Safeena sam babu damuwa a tare da ita hakan ba
karamin dadi ya mashi ba "Safeena kinga yarda Allah ya kadarta maki ko,karki
dauki wannan a,bakin komae insha Allahu zaki samu lafiya sannan,ba kasar da zaa
maidaki ni da kaina zanyi jinyarki kinji ko ki ci gaba da addu'a ……"

Gyada kai tayi a hankali tana jinjina munafunci irin na JB wae mum dinshi tace
zata tsine mashi saboda masifar karya ,Sannan ta kalli Granny da ta rafka uban
tagumi duk abun duniya ya dameta……Ji tayi maryam ta kama hannunta tana fadin
"Sorry besty……"

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

[3:44AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣5⃣

Abdul Maleek kam a bakin mota ya iske JB jingine kamar yana jiran wani ,Kallo
daya ya mashi ya watsar sannan yace "Alhaji yace na maidaka gida……"

"To nagode"ya fada tare da bude frnt sit ya zauna zagayawa Maleek din yayi ya
zauna sannan ya kunna motar suka juya ……Sae da suka fita unguwar sannan JB ya
kalleshi fuska daure yace "Abdul Maleek ina son ka auri Safeena yanzu……"

Wani wawan burki ya taka su duka sukayi gaba tare da dawowa baya suka daki
kujerun da suke zaune ……Wani irin kallo yake watsawa JB din kafin yace "Out of
sense……" ya kunna motar ya ci gaba da tafiya

"Seriously Abdul Maleek zan baka 20m da gida ,ka auri Safeeena har ta warke
sannan ka sakar man ita na aureta……" wannan karon birkin da ya taka yafi na dazu
don har sae da suka sauka saman hanya,Gaba daya ya juyo yana kallon JB din ……

Dafa kafadarshi JB yayi yace "Ka natsu sosae Abdul Maleek na tabbata kudinne
suka rudaka haka ,Zan baka fiye da haka in dae kan Safeena ……Abunda nake so ka
yarda ka aureta kayi jinyarta yarda ya kamata bayan ta warke sae ka saketa ba
tare da ka bari Abbanta ya san ni na saka aurenta ba,Abunda yasa nake son ka
aureta Saki uku na mata na tabbata idan dad dina yaji na saketa cewa zaiyi dole
na mayar da ita saboda akwae kyakykyawar alaka tsakaninsu da Abbanta ni kuma
baran iya zama da ita a haka ba kaga kenan ko yace in maidata auren bara ya
yiyu ba ,kai kuma auren kisan wutane zakayi har ta warke saboda idan ta warke
nazo nace ka aureta zaa dauki lokaci kafin ta fito kila ma har ka fara jin wani
abu game da ita ,dan zaman da zakuyi idan bata lafiya babu abunda zaka ji,
aikin kudi kawae zakayi ……"

Girgiza kai yayi tare da jinjina jahilci irin na JB a tunaninshi kudi
sayeshi ne wae 20m ko yanzu ya tabbata kudin dake accnt dinshi sun lika
yake kokarin bashi ,lallae ya yarda komae ilminka na boko indae babu na
to da kai da jahili duk daya kuke ……ai ko duniya zata hade baya tunanin
gangancin sakin Madam ba,bayan ya sameta ……

zasu
abunda
addini
zaiyi

A jahilce ya kalli JB din yace "taya kake tunanin zata yarda na aureta……"

"Kar ka damu ni zan shirya duk yarda zaayi sae dae ban yarda ka rike ko da
hannunta bane da sunan ta birgeka sannan ban yarda tayi kuka ……"

Gyada kai yayi sosae yana kallonshi ……a cikin manyan jahilae ya yankarwa JB
katon fili ya ajeshi, ji yayi yana fadin "karanto man account numberka na tura
maka 10m yanzu zuwa lokacin da zata warke zan baka sauran ,idan kuma baka da
account din gobe zanje na bude maka a bank……"

Murmushi ya saki mai sauti sannan yakaranto mashi accnt number din "Wane bank
ne "Jb ya tambaya……"UBA" ya bashi amsa a takaice…… idan yaki karbar kudin zai
iya fahimtar wani abu……

Mintuna kadan Alert ya shigo mashi Sae da ya duba sannan ya tashi motar suka
karasa gidansu JB din ,a bakin gate yayi parking JB ya fito da card dake dauke
da numbershi ya mikawa Maleek din "Ka kirani anjima by 9:30 zanyi saving
numberka ……"daga haka ya wuce abunshi

Bayanshi ya bi da kallo tare da tribted dinshi yana fadin "Shugaban wawaye……"
A hankali ……

Juya kan motar yayi wani farinciki na ratsa shi wani bangare na zuciyarshi kuwa
tsoro yake kar Abban ya ki yarda da wannan zancen bogin ba……

《》《》《》《》

Cup ta mika mashi tana fadin "Alhaji Safeena ta dawo amma bara ta zauna
nan gidan ba fisabilillahi, Me yasa baku daukeni a matsayin mahaifiyarta ba……
kusan kwana biyu fa kenan duk tunanina zata dawo nan amma shiru……"

"Ba haka bane ba Fateema Safeenarce ta matsa dole sae gidan hajiyarta zata
zauna ,kuma naga da nan da can duk daya ne kawae fatanmu Allah ya bata lafiya……"

"Ameen amma ya mijin nata yace ,nayi tunanin ko gidanshi zata zauna ma……"ta

fada cike da son sanin halin da ake ciki

Bai kawo komae ba a ranshi ya fada mata yarda sukayi da jabir din ya kara da
fadin "Ni kaina nayi mamakin saki ukun dake cikin takardar don duk tunanina bai
wuce saki daya ba sae daga baya nayi tunanin kila mahaifiyar tashi tace ya mata
haka ……fatana Allah ya sa hakan ya zama alkhairi garemu baki daya……"

Hannu ta daura bisa kai tare da sakin kuka tana fadin "Amma dai wannan dan
iskan yarone shikenan don bata lafiya sae ya kama ya mata saki har uku Alhaji
……" Ganin abun nata ya koma hauka ya sashi shareta ……

Wayarshi ta hau ringing ya kalleta "Dan Allah kiyi shiru zan amsa waya " Tare
da daukar wayar ya kanga a kunne ……

Daga dayan bangaren JB ke fadin "Abba naje office dinka an fada man kana gida
yanzu haka ina bisa hanya zan iya karasowa gidan koko sae kadawo na sameka
office din……"

*ZAN RAYU DAKE.."Ka karaso mana jabir ……"
"to Abba"
Falo ya sauko ya zauna Aunty Fatee ta biyoshi baya ,Cikin yan mintina Jabir din
ya iso har kasa ya gaidashi sannan ya gaida Aunty fatee ya zauna "Ya Abban naka
Jabir……"
"Lafiya lau Abba yace ma a gaidaku ……"
"Muna Amsawa ai jiya munyi magana dashi na fada mashi ba laifinka bane jabir……"

Dukar da kai JB din yayi sannan ya saka hannu ya fito da ticket guda biyu tare
da mikawa Abban "Abba gashi visa ne na nemawa Safeena zuwa asibitin Madina a
dubata to da tare dani na zamu tafi sae Mum dita tace baran je ba ,to Abba kawae
sae na maida Sunan Abdul Maleek don na tabbata zai kula da ita sosae ……"

"Wane irin abune Jabir taya zaka daurawa mutun wahala ba tare da saninshi
ba ,duk da Abdul Maleeku karkashina yake baran iya take hakkinshi ba sannan
Abdul Maleeku ba muharramin Safeena bane da zaiyi jinyarta kaje a soke wannan
Visar ba mai yiyuwa bace Jabir……" ya fada cikin daga murya

Kwantar da murya yayi yana fadin "Abba tun ina can na kira Abdul maleek din na
fada mashi kuma ya yarda sosae ,bara ma na kira maka shi……"

"Dama ta ya zaiki yarda ,Ban taba sa Abdulmaleek wani abu ba yaki yi
man ,wannan karan baran shiga hakkinshi ba ……"

"Wallahi Abba ya yarda ,da sunanka zan saka sae yace na sa nashi zai tafi da
ita,……"ya fada cikin kwantar da murya

"Idan ya yarda shi Muharramintane da zasu tafi a tare har yayi jinyarta?

"Abba Safeena bata da aure yanzu , Kana iya ba Maleek din aurenta kafin sun
tafi tunda sae sati mai zuwa tafiyar ,Ni kaina na yaba da hankalinshi wallahi
babu wanda zai iya kula da Safeena kamar shi ,dole Wanda zai kula da safeena ya
zama mai rikon Addini

Please Login or Register in order to submit comment